Showing 183001 words to 186000 words out of 249044 words

Chapter 62 - Abokin Rayuwa By Khadeeja Candy

03 Dec 2025

14984

fahimce ni kuma zaki min uzuri, lokaci yayi da ya kamata ki san komai..."

Sannu a hankali Turhan ya yi mata shimfidar da zata mikar da ita zuwa cikin ajinsa har ta dauki karatunsa, tun da ya fara bata ce masa uffan ba har ya kai karshen littafin data kasa fahimtar haruffansa balle ta haddace karatun ciki. Ya fada mata ya aure wata mata matar kuma ita ce wanda ya zo da ita a matsayin baiwa haka kuma ya sake ta a yanzu amman zai dawo da aurensa da ita, haka zalika yana da ya a tsakaninsu, sannan ya fada mata yawan zuwan da yake Nigeria har ya dade yana zuwa nemanta ne. Da farko zancen ya rikice mata ne har ta rasa muhallin dorashi kamin hankalinta ya janyo tunaninta bayan ya nuna mata hoton Fatima.

"Mabsoot bikhibalak"

Ta furta tana jefar da hannu idonta ya fara tara hawaye.

"Ka ci amanata Turwhan, taya zaka yi aure bayan idona? Saboda bana haihuwa? Ko kuma saboda mahaifiyarta bata so?"

"Ki zargi komai ban da mahaifiyata, domin bata taba nuna miki kiyayya ba, matar da baki taba sha'awar gani ba?"

Ta tsaya cak tana kallonsa kamin ta mike tsaye ta taba masa.

"Barakallahu fika Turwhan"

Ta juya sai yayi hanzarin mikewa tsaye ya rike ta.

"Idan har zaki ji babu dadi wannan abun da na aikata ki yi tunanin yadda matar da na wulakanta zata ji? Kuma na yi ne ba dan kai na kadai ba har da ke?"

Ta juyo da karfi.

"Idan har baka sonta taya ta haihu da kai? Bayan duk wannan yanzu kuma kana fada min zaka dawo da ita? A tunaninka zan iya zama da kai bayan duk wannan abun da ka yi min? Balle kuma har zaka zauna da matar da bata wuce matsayin mai kula da gidana ba? Aure ya kare tsakanina da kai.

"La la la, khalas al-mawdu‘ intiha. Ana ‘ayza talaaq"

Furta cewar sai dai ya sake ta ya karya masa guiwa sai dai be karya zuciyarsa ba domin a yanzu Fatima kawai yake hange. Ya kama hannunta ya rike cikin sigar rarrashi ya ce.

"Za mu iya fahimtar juna mu gyara komai, ki yi uzuri, ki karbe ni tare da yata"

"Ba zan karbi uzurinka ba, kuma har abada ba zan taba son yar wata ba, har karshen rayuwata, Lihaddy akher nafas fi ḥayāti"

Ta furta hakan har sau uku tana hade hakora, kalmar ba zata taba son yar wata ba har karshen rayuwarta ya saka Turhan ya saki hannunta domin Fatima yarsa ce, ba yar Aisha kadai ba, be ce ya shirya rabuwa da ita ba, ko rusa aurensa ba, domin ba zai yarda ya maimaita irin wacan kuskuren da ya aikatawa Aisha ba, sai dai kuma hakan ba shi yake nufin ya jure a ciwa yarsa ko mahaifiyarta mutuncin ba. Ta kalli hannunta daya saki ta kalleshi fushi ya dauketa ta fara shure kayan abincin da abinci dake ciki tana ihu tana la'antarsa da kalmomi marasa dadi. Kamin ta fara bin sitting room din ta fara hargitsawa tsabar bala'inta be iya kwana a gidan ba sai fita yayi ya kwana a hotel, washe gari ko da ya dawo be same ta a gidan ba, ya samu ta yi ma gidan barna duk wani abu mai glass sai da ta fasa shi hatta kwalbar turare bata bari ba.

Wanka yayi ya canja tufafi sannan yayi ma khadimansa su gyara bangaren, ya fito ya nufi fadar mahaifinsa ko'ina ya bi kallonsa yan'uwansa suke, sauran Khadiman gida kuma sai ya sauke ido ake satar kallonsa, kowa yana mamaki da abun da matarsa ta fada jiya cikin ihu da hayaniya. Yau ma da ya shiga mahaifinsa be tanka masa ba.

"A gafarce ni, na san ina da tarin laifuka"

Bayan kamar Minti biyu mahaifinsa ya kalleshi.

"Na yi zaton ba zaka zo ba ai, saboda ban isa da kai ba"

"Ban isa ba, kai kayi kira na kasa amsawa, da baka isa da ni ba da ba za a kawo maka rokon abun da a cikin aikata shi babu adalci ba"

"Wata wuta ce aka ce ta kama a wani gida, aka roki na kasheta, da na bincika dalilin tashinta Sai aka fada min har da ɗana a gurin assasata, shin hakan gaskiya?"

"An riga ni sanar da kai tashin gobarar data haifar da hayakin sanar da duniya abunda ake ciki ne, amman ina da wannan nufin a yanzu da nake ganin lokaci ne daya dace kowa ya san komai"

"Aka ce ka yi aure? Tatsuniya ce ko kuma dai ana kokarin kunna fitina a cikin masarautar ne?"

Turhan ya natsu Sosai ya sanar da mahaifinsa yadda auren ya afku da kuma yadda boye lamarin har zuwa yau. Yayi zaton zai fuskanci fushi da natsa daga gurin mahaifinsa ne sai gashi ya tsinkayo mahaifinsa na murmushin kasaita ya kalleshi cike da alfahari.

"Wani lokacin akan dora mana nauyin abun da ba za mu iya sauke ba, sai da hikima da yawa, na yaba da kokarinka na boye auren kuma na jidadin da yarka take hannunka, jininmu baya zama a ko'ina sai a kusa da mu"

Turhan ya kalli mahaifinsa cike da damuwa.

"Be zama lallai Fatima ta zauna kusa da mu ba, idan mahaifiyarta ta zabi, zama a Nigeria ina tunanin ba ni da zabi da ya wuce na bi ra'ayinta domin gyara laifin da na aikata"

Mahaifinsa ya sake dubansa.

"Baka aikata laifi ba, ko mace bata cancanci auren dole ba balle kuma kai, baka bukatar zama da matar da baka so kuma bata cancanta ba"

"Ta cancanta, saboda kyauta ce daga gurin mahaifiyar da bata jidadin zaman gidan miji ba, mahaifiyar da bayan danta da yi ma kyauta bata da wani, mahaifiyar da aka hanata ganin danta na tsawon shekaru, aka hana ta shayar da shi, na wofintar da Aisha ne saboda tsoron kallon da za'ayi min, da kuma tunanin kamar ni laraben mutum na fi wata fatar matsayi, bayan kuma har a gurin Allah ba haka ba ne, ada can bana son Aisha, amman a yanzu ina jin zan iya mutuwa ita ta rayu, ta ba ni sanyin idaniyar da ban samu ba a gurin matar da nake ganin ta fita matsayi, Ya Abiy ina son Aisha so mai tsanani, ina son yarta son da be da misali, ita ce ta maida ni uba, wannan shaukin ba zai taba gushewa ba, na aikata abun da na aikata ne saboda son zuciya, amman da na runtse ido ban ga kyau a makanta ba, anya idan mahaifiyata aka yi ma ko yata, zan iya jurewa? Amsar ita ce aa, ko ban fada ko na nuna ba abun yana a zuciya"

Sarkin yayi shiru na tsawon lokaci kamin ya ce

"Karka manta da asalinka, kar ka bari mahaifiyarka ta saka maka kalmomi marasa amfani a kanka"

"Ba zan taba mantawa da asalina ba, ni dan wata mace bakar fata ne daga arewacin Nigeria, kuma dan Sarkin Sudan balarabe mai asali, Mahaifinta bata saka min kalmomin manta asalina ba, amman ta fada min yadda mahaifina ya mu'amalance ta, wanda ya sha banban da yan'uwana da nake gani a Masarautar, kuma laifinta shi ne ita bakar fata ce kawai. Bana son yata ta tsane ni, ko kuma ta kalleni da laifin dana aikata saboda son zuciya shiyasa ba zan ki mahaifiyarta ba, mahaifiyata ta cancanci girmamawata a kowane irin hali, duk uwar da zata dauki cikin danta ta raine shi ta haife shi ko wace uwa ce ta cancanci biyayya daga gurin ɗanta"

Sarki Mohamed Abdou ya dauke kai kamar mai jin kunyar Turhan, kuma ya gagara bayyana bacin ransa.

"Mahaifita ta dandani daci mai tsananin kashe halshe daga gurin mahaifina, a yanzu kuma da ɗanta ya kawo sai take ganin ta cancani kauna da biyayya, da kowace dakika tsoron rasani take, ni ma kuma ina fargabar rasata saboda ciwon dake neman rayuwarta, Ya shugaba kuma mahaifina tambaya ce mai nauyi na amsa cewa ina da muhimmanci a gareka ko akasin haka, saboda na zama farin tuwo daga bakar tukunya, be zama lallai ka kaunaci abun da nake kauna ba, saboda ni ba Laraba ce ta haife ni ba, amman dai bakar matar nan daga arewacin Nigeria tana da matukar muhimmanci da kima a idona, ina kyautata zaton ba zaka hana ni yi mata biyayya ba, domin Annabi S. A. W ma ya ambaci uwa sau uku sannan ya ambaci uba, saboda muhimmancinta"

Mahaifinsa ya kalleshi, hawaye ne suke saukowa a fuskar Turhan ba na wasa ba.

"Idan an yi min izinin ina son na kama hanyar komawa gobe, kuma zan dawo ne kadai idan mahaifiyata ta samu farinciki da ta dade tana nema, kuma na samu matar da ita kadai nake muradi a yanzu"

Ya risina cike da biyayya.

"A gafarci halshena idan yayi kure, na barka lafiya"

Ya mike tsaye ya share hawayensa ya fice daga fadar. Masarautar ya bari gaba daya, ya tafi gurin abokansa da ya nunawa Fatima a waya tun a kamin ya karaso, biyu suka goya masa bayan dawowa da Aisha dayan kuma ya nuna masa ya karbi yarsa kawai ya barta ta yi tafiyarta tun da har ta nuna bata bukatarsa. Ya dawo gidan ya shiga bangarensa sai ya samu an gyara komai an kwashe duk wani abu daya fashe, wasu abubuwan kuma an maida su a muhalinsu.
Ya shiga dakin da matarsa ta fi zama ya zauna a kujerarta sai tunani yake kala kala can kuma ya mike tsaye ya fito daga dakin ya shiga dakin da komai nasa yake ciki, yana kokarin cire rawanin kansa ya hango wani karamin kwali a kan gadonsa, ya karasa kusa da gadon ya dauki kwalin ya bude. Sai yayi arba da ticket din first class na jirgin da zai tashi daga Khartoum zuwa Abuja a gobe, ga kuma manyan kudi mai kauri a ciki da wata yar karamar takarda.

"Rihla sa‘īda, Allah yisahil tareeqak"
(Safe journey, may Allah ease your way)

_Ṣāḥib al-Jalāla Mohammed ʿAbdou_

Turhan ya kai zaune da jallabiyar dake jikinsa yana murmushi, ya dade zaune yana sake karanta kalmar da ba zata canja daga haruffa ko ma'anarta ba, sake shiri yayi sannan ya fita zuwa bangaren mahaifinsa sai ya samu an shirya liyafar abincin dare da yaran da suke gidan ya zauna aka ci abincin tare da shi, bayan an gama ya shiga bangaren mahaifinsa duk yadda ya so ya samu wata dama ya yi kibabbantacciyar magana da mahaifinsa be samu dama ba, domin mahaifinsa be ba shi wannan damar ba. Daya fito sai ya dauki motarsa ya tafi gidan iyayen matarsa ita ma dai be samu ganinta ba domin ko kofar gate di gidan ba a bar shi ya shiga ba.
Da ya dawo sai ya hada kayansa da abubuwan bukatunsa tsab cikin akwai har biyu sannan ya kwanta, washe gari da wuri Khadima ta kawo masa abun karyawa ya karya yana video call da Fatima saboda ta fitini Ammy da kukan rashin Turhan da Emily a kusa, sannan yayi wanka ya shirya ya sake kiranta video call be kashe kiran sai da suka shiga jirgi aka umarci kowa ya saka maka wayarsa a airplane mode.




AMMY POV.

"Jirgin nan zai zo?"

"Eh"

Ammy ta amsa mata tana shafa kanta.

"Zai tafi biya ya dauko Momy ne? I miss her so much"

"Aa Momy sai idan ta huta zata zo"

"When?"

"Ban sani ba tukuna, amman a yanzu idan ana son ganin mahaifiyarki ko kuma a daukota a ina kike tunanin za a same ta sanyin idaniyata?"

"A waya"

"Bayan waya"

"Gidan gurin Uncle Aliyu, ko Vito"

"Aliyu yana ajeta a gidansa ne? Da kuka zo garin nan a gidansa kuke zaune?"

"Aa"

"To da kuna PH ma a gidansa kuke zaune?"

"Aa a gidan Vito ne, shi yana dukan Momy ne shiyasa bana son shi, kuma baya so na yana hade rai"

"Shi Viton Momynki ta aure shi ne?"

"Aa ba zata aure shi ba, ba zamu koma gidan ba, za mu zauna a nan da daddyna ko? Da Momy ko?"

"Haka muke fata"

Fatima ta mika mata wayar da har yanzu bata san yadda zata sarrafata ta kira ba, amman ta iya shiga YouTube da Gallery ko Camera.

"Zaki iya kiran Momy? Ita ma zan yi magana da ita"

Ammy ta karbi wayar ta shiga gurin kira ta gwada kiran Layin Aisha da sunan da Aliyu ya saka mata a wayar wato Emily, sai ta ji wayar a rufe.

"Ba a samu"

"Sake kira"

Ta sake gwadawa"

"It the same thing"

"To kira Uncle Aliyu ki ce ya bawa Momy"

"Basa tare, kin san a ina za a iya samunta?"

Ta yi shiru can kuma ta ce gurin Vito. Ammy ta yi shiru tana nazari.

"Amman Momy ma zata dawo? Ina son na ganta?"

"Zata dawo Fatima"

Ammy ta amsa mata sannan ta sauke ajiyar zuciya.



KAMEELA POV.

Ta shiga bangarensu da mamaki tun a falo ta labarta musu komai, sai Hajiyarsu taja tsaki.

"Aikin kenan, daga Aliyu sai abun da ya shafi Aliyu"

Anty Shafa ta kalli Mahaifiyarsu.

"Hajiya, abun be baki mamaki ba?"

"Miye abun mamaki a ciki? Wata kila ta fadi hakan ne saboda Kameela ta daina zuwa can, daman idan ba neman suna ba yaushe zaka kashi sirrinka ka fadawa kishiyar uwa?"

Kameela ta ce.

"Ba wai ta fada ne kawai saboda na daina zuwa mata da maganar ba ne, domin na ga tsananin bacin rai a tare da ita, har fa marina ta yi, kuma idon ta ya kumbura kamar ta yi kuka"

Can kuma ta juyo har lokacin tana dafe da kuncinta.

"To kuma ma idan ba tsananin bala'i ba ta ina Mama Baraka zata zama mahaifiyar tsinaniyar Emily nan? Ta ya ta ina? Kwata kwata ma basa kama fa, kuma ita Emilyn nan ma fa ruwan turawa ne da ita, fara ce sosai mai jan gashi da blue eyes, amman dai ga dukanin alama akwai wata a kasa"

Hajiya ta tabe.

"Ita fa kishiya ba yar'uwa ba ce, ba mamaki wani abun ta shirya, amman dai anjima idan Alhaji ya dawo, zan kwankwasa kofar na ji ko zata yi kara"

Kameela ta haura sama ta shiga dakinta da mamaki da kuma tsananin kishin ace Emily yar Mama Barakat ce, idan har wannan abun da hankali ba zai dauka ba ya tabbata ai ita kam an gama da ita gamawa ta musamman.

"Kai ba ma gaskiya ba ne, ai ba hadi hanyar jirgi dabam mota dabam"

Ta zauna cike da kewar mijinta da son sanin halin da yake ciki. Wayarta ta dauka zata gwada kiransa sai wani bangare na zuciyarta ya hana ta yi haka sau hudu sai a biyar ta gwada kiransa, wayar na shiga gabanta ya fadi ta mike tsaye tana safa da marwa a dakin, wayar ta katse be daga ba, ta sake gwadawa be daga ba daga karshe sai yayi rejecting kiranta. Ta zauna baki gado tana hawaye domin tana tsananin kaunar mijinta.



_______________________

Sannu ‘yan uwa mata! Kin gaji da kayan da ba su da salo, ba su da inganci? To yanzu lokaci ya yi da za ki sabunta wardrobe ɗinki da kaya masu kyau, masu ƙima daga Khadeeja Candy Store

Muna da abaya masu kyau irin na zamani, masu sauƙin sakawa da jituwa da dukkanin lokaci whether ki je wurin biki, ko casual outing.

Kuma fa, ba abaya kawai ba muna da bedsheet masu launin kwantar da hankali, masu kyau a gani da taɓawa. Idan kina son daki ya zama kamar hotel, to bedsheet ɗinmu sun dace da ke

Kayanmu masu kyau ne, farashinsu? Ai sai kiyi mamaki sauƙi ne sosai. Muna nan a Kano State, kuma muna delivery zuwa ko’ina!


Ki danna follow yanzu, ki biyo mu a TikTok https://www.tiktok.com/@khadeeja_candy_store?_t=ZM-8wBOKC1rSVi&_r=1

da Instagram https://www.instagram.com/khadeeja_candy_store?igsh=bTk2aG13cmFkZjM0


Ki ga sabbin kaya masu kyau da rangwame.

Zaki sami kayan Kitchen masu inganci, kayan sakawa na zamani, da electronics masu ƙayatarwa duk a farashi mai sauƙi.

Za ki iya saka tufafinmu ki fita lafiya, kitchen dinki kuma ki kawata shi da kayan Kitchen dinmu, da bedsheet dinmu kuma za ki yi barci cikin annashuwa komai daga shagonmu!

Baki da lokaci? Muna da sauƙin oda ta waya ko WhatsApp - 08036126660 muna aika kaya zuwa ko ina!

To me kike jira? Biyo mu yanzu a WhatsApp https://chat.whatsapp.com/HGRV2NYIoaCF7SIvPOIv08


Ba kawai kaya ba ne salo ne, ƙima ce. A Khadeeja Candy Store.
Ki zo yau, ki ɗanɗani bambanci, Khadeeja Candy Store inda kyau da salo ke haɗuwa.
[7/29, 10:20 PM] 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆: https://chat.whatsapp.com/GATlsEHRyd2HW1OjrdF5AL?mode=ac_t



*🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒*


*© Khadeeja Candy*



Page 5️⃣9️⃣



BAYAN WATA UKU...

ALIYU POV.

Ya sauke wayar tare da sauke kafafuwansa dake kan karamin taber.

"Tun da aka sallamoka asibitin nan baka zauna ba Aliyu kullum cikin neman yarinyar nan kake"

Ya kalli Ummi.

"Tun kamin na dawo daga Asibiti abun da nake ta kokarin yi kenan, kuma ai baki yarda na bar asibitin ba sai da na ji sauki radau idan ma akwai abun da ya fi jin garau na ji"

"Allah yasa a dace har yanzu babu wanda ya samu labarin Emily"

"Ameen, zan tafi gobe, tare da Mama Barakat ki taya mu da addu'a"

"Allah ya tsare amman da ka hakura har sai ka samu kwanciyar hankali tukuna, bana son ka jefa kanka a cikin wata matsala"

"Babu wata matsala In Shaa Allahu, kwanciyar hankalina yana tare da samun Emily matukar ban san halin da take ciki ba ba zan taba samun kwanciyar hankali ba, wata kila tana cikin mummunan yanayi shiyasa har yanzu bata waiwayi yarta ba, wata kila kuma ta gaji da rayuwar ne ta hakura a haka"

"Jikina ya fi ba ni kamar tana tare da yaron nan da ya saka aka doke ka"

"Abu ne mai wahala ta koma gurinsa, balle kuma shi da a yanzu yake boya? Daddy ya fada min dan Information kadan ake nema ana samu za a kama shi domin an tara masa duka laifukan da ya aikata kuma yake aikatawa, kin ga abu ne mai wahala ace yana tare da ita"

"Haka ya fada min, yanzu haka baya gidansa, babu wanda ya san inda yake, shiyasa nake jin tsoron tafiyarka Aliyu, kar ace shi ma yana nan yana neman hanyar da zai cutar da kai"

"In shaa Allahu babu abun da zai iya"

"Idan ka je a kwana daya zaka dawo?"

"Eh zan dawo a kwana daya saboda ke Ummi saboda ki samu natsuwa"

Cikin yanayin damuwa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login