Showing 138001 words to 141000 words out of 180068 words
yana yi mata korafin wannan ba kashe wuta ta yi ba. Ai kamata ya yi ta ce "Ni Sakina idan ina da mutunci a wajenki na kashe wannan maganar kar ki kuma tayar da ita. A yadda nasan tana girmama lamarinki shikenan zata sassauta ta dawo da walwalarta.
Amma yanzu kin yi magan ba wani motsa kwanji babu jarumta".
Ta bashi amsa da cewa "ba zan takura mata ba, domin bansan abin da kake k'unsa mata ba. Ai tunda har ka bari ta fara yi maka irin wannan tutsun to lah shakka zuwa gaba ba zaka ji dadinta ba. Ka gaggauta fahimtar al'amura a dai-dai Namoriki".
"To ba dole ta taurare ta dinga yi mini iyashege a gaban bare ba, ta yadda itama amaryar zata samu kofar wula'kanta ni, tunda kun riga kun zugeta ta gane kun tsaya mata. Ai ni kam nan kusa bansan namijin da ake cusawa ba'kin ciki irina ba.".
Daga hakan ban sake jin amsar da ta bashi ba.
Tunda sun fice. Ya jima sosai kafin ya dawo, domin har na kammala abincin da na dora bayan fitarsu, miya ce kawai ta rage.
Ina kicin ya shigo ta k'ofar kicin din, tunda yanzu anfi shigo wa ta k'ofar baya.
Ya tsaya daf da ni yana ta son sai mun kalli juna. Na bata rai sosai ba tare dana tanka ba. ya ce "Babu kyua doguwar gaba mussaman ace mace ce take yi da miji".
Na ce "Ai kuwa bana gaba Yaya Gudale domin kullum sai na gaishe ka, yanzu kuma gashi na dora tukunya saboda kai, dan ka gane tabbas Sakina uwata ce ba wai yayata ba".
Yasa hannu ya murde gas din ya ce "To zo ki ji." Ya ru'ko hannuna. Na ce "Bari na wanke hannuna kaga yanzun nan na gama yanka albasa".
Yana tsaye na wanke hannuna tas, na goge da tawul.
Na bishi muka je har dakinsa. Ya dinga bare bare, yayin da na yi cak da ni.
Dake a matu'kar bu'katar ya kasance da ni yake, hakan ya dinga yin komai a yunwace. Na dinga mamakin irin wannan rawar jikin tamkar baya samu yana sauke lalurarsa.
Rabon da ya lalace mini a shimfida irin haka tun ban fara aiki ba, domin a wannan ranar duk wani nau'in da zai yi dan ya dada mini ya yi.
Duk kokarinsa dan na mayar masa da martani kememe na k'i. Ni da kaina na dinga mamakin yadda aka yi na ji bana sha'awa ko enjoying din dukkan kokarinsa. Asalima ban amince dan ina so, ko dan na yi masa afuwa ba. Na amince masa ne dan ya tabbatar da gaske Sakina tana da mutunci a duniyata.
Duk tsawon lokacin da ya dauka yana kid'ansa da rawarsa ban nuna gazawata ba.
Yana kammalawa na tashi na zura rigata na yi dakina.
Sai da na yi kuka sosai domin ji na yi gaba'daya ba'kin cikin tarayyar ta kama ni. Karon farko da na fara jin tsanar al'amarin gaba'daya.
Na jima ina kuka sosai sannan na shiga wanka.
Na fito na shirya tsab da ni. Na koma kicin na cigaba da karasa aikina.
Ina shirya abincin a dining ya fito, sanye cikin kananun kaya da ya karbe shi.
Kallo daya na yi masa na gane yana cikin damuwa mai yawa.
Na dauke kai na ce "Ga abinci".
A sanyaye ya ce "Yanzu Guduyo abin da kika yi kin kyauta? Na rantse da Allah gara ace baki amince ba gaba'daya akan wannan wula'kancin". Ya girgiza kai cikin rauni ya ce "shikenan! Babu damuwa".
Na bata rai sosai na ce "Yo dama ai tunda ka samu irin wanda kake so ai komai na yi maka ban iya ba, komai zaka ce ba daidai ne ba".
Ya tumbatsa tamkar zai fashe. Ya girgiza kai ba tare da ya ce komai ba.
Ya zauna ya zuba abinci, sai dai cokali biyu kawai ya yi ya mike ya bar mini abina.
Abin ya mini ciwo ba ka'dan ba.
Yana fita kuwa hawaye ya goce mini.
Bai sake dawowa ba sai dare.
Ya tarar da ni a falo ya kaikace ya ce "Goben nan ki dawo mini da Afrah gidan nan, domin ai ba bayar da ita na yi ba, da za'a rike mini ita fiye da watanni uku, kina tashi daga asibitin da kike zarya kullum da sunan aiki ki wuce ki dauko mini yarinya if not daga ke har Sakinan zan gwada muku iyakacinku".
Na murguda masa baki na ce "Yar da baka so ne kake wannan maganar akan ta yanzu ko kunya baka ji ba?"
Ya shige daki yana cewa "ki bari goben ta yi ba'a dawo mini da ita ba, ki ga irin kwanjin da zan nuna, ko bana sonta ai dai ni ne ubanta, kuma ko laulayin da aka mini k'ofin na yi a cikinta ka'dai ya isa a girmama umarnina".
Na kyale shi, illah iyaka na k'udiri aniyar ba zance wa Sakina ta bani Afrah ba, duk kuwa da nima na matsu ta dawo, domin yarinyar tana debe mini kewa saosai ta shiga raina fiye ma da Amnah.
Washagari kuwa sai ga Sakina ta kawo Afrah da daddare tana cewa "Akan me ba zan ce ta bani ita ba zan tsaya zagaye zagaye?"
Hawaye ya goce mini na kalleta cikin ido na ce "Billahillazi Maman Nana ban ce koami ba. Bani ce ba, kin dai san shi sarai".
Ta ce "share hawayenki na yarda da ke, shima kuma na gode masa tunda har ya kasa zuwa ya daukota da kansa ai mutuntata ni ya yi, shiyasa ya goce ya ce kina son y'arki a gaban ki".
Na kame baki na ce "oh Yaya Gudale zai iya ha'da yakin basasa Wallahi".
Shikenan Afrah ta dawo na kuma gane hikimar Gudale ta dawo da yarinyar domin kuwa na samu sau'kin K'uncin da nake ciki. Na dinga kyakayata dariya kenan idan tana yin gwarancinta.
Na daina zama shiru, domin idan tana kusa da ni. Ina biye ta muyi ta hira ina jin nishadi mai yawa.
Yayin da shima zai yi ta kutso kansa a tsakaninmu. Na lura yana amfani da yarinyar ne dan ya sanya murmushi a zuciyata.
Tabbas wani lokacin ina biye shi mu yi hira amma fa haka siddan bazan fara yi masa magana bà, matu'kar ba gaisuwa ba ce, ko kuma maganar abinci. Inka dauke wadannan to na dinke daga dukkan neman soyayyarsa. Zuciyata ta rinjayar mini Munubiya ce type dinsa, ita yake so, ita yake gamsuwa da ita to na bar mata, ba kuma zance ya sake ni ba, sai idan shine ya gaji dan kansa.
Sannan zan bashi kaina domin sauke nauyin da Ubangiji ya wajabta mini, amma kuma bashi da alfarmar da zan biyar da shi cikin soyayya da nisha'di, tunda na bayan da na wanzu ina yi basu kubutar da ni daga tozarcinsa ba, to kuwa a yanzu da yake da wata da yake so, take yi masa irin amfanin da nake yi masa ba abin da zan yi masa na kubuta daga wula'kancinsa.
Wata uku da yin auren na dauki hutun shekara.
Kullum ina gida al'amarin kishin da ya takura ni, ya yi matu'kar yi mini sau'ki a zuciyata, domin na tattra su na watsar hatta lamarin Umma da a kullum yake sake tsananta a kaina ya daina damuna tunda na fahimci da gaske tafi son Munubiya a kaina shikenan nima na jingine ta da dukkan zuciyata, sai dai gaisuwa nake yi mata ta girma da arziki.
Tsakanina da Gudale kuwa distance mai yawa ya shiga tsakaninmu domin har lokacin ban sauya masa a sabuwar mua'amalantar da na tsiro a tsakaninmu ba. Ya yi rarrashin amma na kasa sakewa, matu'kar zai bu'kace ni to kuwa lah shakka sai dai na zame masa tamkar gunki, duk abin da zai yi kuwa. Abin yana matu'kar damunsa.
A kuma wannan lokacin halayyar kowa a tsakaninsa da Munubiya ta bayyana.
Na farko ita bata son takurar da yake yi na rashin son fita. Ita kuwa matu'kar ta raya zata fita sai dai kawai ta sanar masa zata je waje kaza da sigar labari ba sigar naman izni ba. Wani lokacin ma indai yana wajena sai dai muji tashin motarta.
Baya ga haka daga dukkan alamu bata iyawa da jarabarsa domin duk yadda nake masa wula'kanci ta hanyar zama masa tamkar gunki baya iya ha'kura ya barni da abina. A kuma matu'kar matse yake dawo mini. Sai dai bai ta'ba cewa ga matsalarsa da ita ba.
Matsala ta biyu kuma matu'kar ita take girki indai har ya wuce taran dare a wajen Umma lah shakka ba zata bude masa kofa ba.
Sai dai ya koma ya kwana a mota.
Domin akwai ranar da ta yi masa hakan ya kira wayata akan na bu'de masa kofar wajena zai shiga dakinsa nima fir na ki tunda na ji irin knocking din da ya dinga yi mata amma baiwar Allah ya yi funfurunfus.
Sai kuma matsalar da na kasa fahimtar ta nake kuma jin tsoron na nemi a wayar mini da kai.
Munubiya wani irin kirki take yi mini, girmama ni take yi fiye da yadda take gimama Gudale. Ta ja Afrah a jikinta, tana kashe mata ku'di fiye da yadda ubanta yake mata.
Duk inda zata Afrah na gaban motarta, ba dan karfin soyayyar da ke tsakaninmu da Afrah ba da sai yarinyar ta koma wajenta tsabar yadda take tattalinta, sai dai Afrah jele take yi tsakanin sama da kasa domin kuwa ba karamin kulafacina take yi ba. Ba dan haka ba ai da tuni ta bar ni domin irin kayan wasa na alfarmar da ta tara mata a sama, duk wanda zai fita wata kasar a cikin danginta sakon Afrah na mussaman ne.
Daga haka kuma sai ta tsiri zaman wajena duk sadda na dawo daga aiki na huta to zata zo mini, ba kuma ta zuwa hannu Rabbana.
Kullum da abin da zata kawo mini na ci, ko na amfani.
Ni kuma na sake da ita, domin ban ga alamun cutarwa a tare da ita ba. Ko wajen Abba zani sai na jata mu tafi tare. Hakan kuma ya sake nutsar da zuciyar Abba ya dinga murna yana sanya mana albarka. Ya dinga gode mini, yana yaba mini.
Amma da zamu shiga wajen Umm tare sai ta nuna banbanci, sai ta nuna ita ce tata, tun Munubiya bata fahimta ba har ta gane. Dan haka sai itama ta fara ja baya da Umma domin idan muka je bata yarda ta gaisa da Munubiya a falo sa ta kai za xza za z za za xzaz za a xzaz zax za za za zaz za zazz za xza za z z zaz z a xza z da za za xza zz zzzz zaxzaxz xza xza za zzazz z zz z xzaz zzzza zzz za zaz z zaz z zaz z zz xza zazzzazza xza zxa za xzsa zazz xzaa za za za z xza xza za xza za xzaz zaza xza z az z za xza zaz zx za xasxza xzazzza xzz😆😆 ta har uwardaki tana ta ina ka saka da ita. Ba kunya kuma ni ta bar ni a falo a wula'kance.
Ta dinga tambayar Munubiya me take so, dafatan bata da matsala a gidan?
Akan idona Umma ta sha fa'da mata "Ta sake ita ma matar gida ce, bayan hakan idan an sha gabanta a wajen Abba to ta sani ita din tata ce, zata kuma yi yaki da duk wanda zai musgunawa farin-cikinta.
A duk sadda na tuna amsar da Munubiya ta kalli idon Umma ta fa'da mata sai na ji faduwar gaba dan tsananin mamaki, amma sai Umma ta waske ta yi kamar bata ji ta ba.
Ba tsoro bare faragaba ta ce "Umma ai kuwa Abba uban kowa ne, domin idan muka je gabansa yana mua'amalantar mu eqaul da Maman Amnah, idan kuma abu zai bamu ni yake dankawa a hannu ba dan ya daidaita matsayinmu ba, sai dan na ji a jikina nima yarsa ce, amma duk sadda muka zo nan sai Maman Amnah ta muzanta domin ni ka'dai kike mua'amalanta da karamci. Na fara zargin kaina, domin ita bata hana Abbanta ya karrama ni ba Umma".
Dake akan idona ne sai ta yi mukus.
Yayin da ni kuma na mi'ke na ce na tafi saloon.
Daga nan na wuce wajen mahaifiyata, tsananin ki'dimar da na shiga ya sanya na fara rarratabwa Mama katobarar da Munubiya ta yiwa Umma.
Cikin son a bar maganar ta ce "Halima ba ruwanki, kada ki saka musu baki a shanninta da surukurta. Ban yarda ba, ban amince ki yi maganarsu da wani ba. Ita kanta kishiyar ta ki kada ki sake ki yi maganar Umma ko ta su Maimuna da ita bare randa munafunci zai fashe ya tashi da ke, ke dai kawai zuba musu ido kina gefe kina istigifari da hailala. Na ji da'din yadda kika ha'kura, gashi yanzu komai ya wuce."
Na yi murmushi a zuciyata kuma na sani kawai sauki abin ya yi.
Sai kuma matsalar Munu ta biyu da na kasa ganewa.
Domin bayan waccan kirkin da take mini, sai take yawan son ta rungume ni, kullum ta zo sai ra rungume ni a zuwan oyoyo. Sai kuma abin ya zarce da bubbuga bayana cikin hikima.
Ban gama fita a wanccan mamakin ba sai ta tsiri da bani peck a kunci tamkar dai gaisuwar larabawa. Dake mu anan bama irin wannan dabi'ar sai abin ya zame mini some how. Sannan a farkon zuwanta bata yin hakan.
Sannu sannu kuma indai zamu zauna to ta dinga murza mini hannu tana yaba cikar hannuna. Tana fa'din na yawaita yin lalle domin ba karamin kyau zai yi mini ba.
Kaina ya kulle na kasa fahimtar wannan abu na Munubiya. Shaidan sai hasaso mini abubuwa akan ta yake yi. Amma tunda bani da tabbas sai nake yi mata uzziri.
Amma me? Sai abin yake sake tsananta har ta kai zata bar Gudale a sama ta taho wajena. Wani lokacin ya ha'kura wani lokacin ya biyota su tare mini.
A fili kuma take fa'din gaskiya Ubangiji ya mini komai nawa a cike ga kuma murya mai fitar da amo.
Randa ta fadi hakan a gaban Gudale ya tunzura ya ce "Ba ya so.
Ta yi murmushi ta ce "zuwa yanzu ya kamata ace ka gama fahimtar ina yaba abin da yayi mini babu jin kunya. Ina kuma bagarar da abin da bai yi mini ba babu jin nauyi".
Ya nuna ta da yatsa ya ce "Na fa'da miki da babbar murya bana so, amma idan baki yarda ba, ki cigaba, amma ki sani, ba zan miki hakurin da kullum nake yi akan ki ba, matu'kar kika tsiri yi mini irin wannan iyashegen akan Guduyo".
Ta ta'be baki ta ce "Sadiki kenan, mamaki kuma na nawa?
Ai sai yanzu nake ganin gaskiya kaddara ce ta zabo maka manyan matan da basu kamace ka ba.
Mussaman Maman Amnah yadda take din nan Babban zaure".
Ya cika, tamkar zai fashe amma ya kasa cewa komai ya mi'ke ya fice da alama wajen Umma ya nufa.
Ta yi tsaki ta ce "Mummys boy".
Yayin da ni kuma na sake tsorata da lamarinta, na kuma sake fahimtar zaman nasu ya fara tsami, amma shi da Umma suna ta boye wa.
A hankali Umma ta fahimci Munubiya ba zata huce mata takaicina ba, domin zuwanta uku da bak'inta amma sai dai Munubiya ta karbe su a falona bata yarda ta tashi su tafi wajenta.
Shikenan sai kuma teburin rikicin ya juya.
Aka koma fa'da wa Gudale mun kai Munubiya an mallake mini ita. Ai farkon zuwanta ba hakan take yi ba.
Amma yanzu tafi fifita al'amarina sama da na kowa hatta shi kansa uban gayyar.
Abin duniya ya yiwa Umma zafi tun tafiya bata yi nisa ba, ta fahimci ba zata yi nasara ta hanyar Munubiya ba.
Yayin da Gudale ya shiga wani irin tasku domin dai ya kasa daidaita wa da Munubiya a dalilin shima baudadden halinsa ya bayyana mata, yayin da ita kuma ya fahimci kwata kwata babu son auren a ranta, kawai dai ta yi aure ne dan shekarunta sun fara turawa amma ba dan ta dauke shi da muhimmanci ba.
Ga kuma matsalar nima na ki sarrafuwa masa.
Gaba'daya na cure na zama tamkar katako ya ka'da ya raya amma na ki canja wa.
Wani dare bana mantawa yayi juyin duniya na yarda mu yi cikin dadin rai, har da cewa" iya na yau kawai zaki yi mini, sai sadda kika so kuma, dan Allah kin ji Guddin Abba".
Na ture a ranar ma sai na ki yarda da wanda baya so din, domin a falo na yi kwanciyata. Tabbacin ba zan yi ba gaba'daya.
Ya dinga rarrashi har ya tunzura ainun ya turmushe ni a wajen, kamar watannin baya. Yana gamawa ya ce akan wannan kofar d'an agundin kike yi mini irin wannan iyashegen. Na tabbatar ba haka kika barni ba Guduyo".
Ai shikenan muka sake hawa dokin fishi, kowa na yiwa dan-uwansa kallon mugu azzalumi.
Mun debi kwanaki, babu ko gaisuwa, tunda ni ce mai gaisuwar, na kuma daina, tunda ina fishin ya sake wula'kanta ni a falo, ya kuma yaba mini bakar magana.
Dake a wannan bangaren bashi da hakuri sai kawai ya kai karata gaban Abba. Na dinga jinjina yadda ya kaikai ce ya fa'dawa Abba cewar ina gudunsa fiye da wata uku. Sannan ya kira Sakina dan ta yi sulhu amma ban ji ba, to ya kawo maganar gabansa ayi masa adalci.
Ina durkushe gaban Abba kunya tamkar kasa ta tsage na shige.
Yayin da shi kansa Abba ya Jima bai iya bude baki ya ce kanzil ba.
Haka kawai ya rarrago ni, akan Abba yana nemanmu, ashe dan ya fa'di wannan babban al'amarin ne a gabana.
Murya a dakushe Abba ya ce "Halimatu ina ta murna kin karbi girman da ya hau kanki da hannu biyu, ina farin-cikin kin kwantar da hankalinki, ina cikin murnar kina tsaye kan kafafunki ashe ke kin zubar da komai ne kin kama iska?"
Nan da nan Gudale ya ce "Ai da bude maganar na yi sosai Abba wallahi da ka fahimci kwali kawai ta kama ba iska ba."
Abba ya nuna shi da hannu ya ce rufe mini baki marar kunya kawai."
Ya kame baki har da saka hannu ya ri'ke bakin yana cewa na yi tuba, amma dai a bi mini kadina dan darajar Annabi kada a dau maganar nan sakwa sakwa".
Abba ya sassauta murya ya ce menene matsalarki Halima? Fa'da mini me ya miki?"
Hawaye ya balle mini, cikin kuka na ce "Wula'kanta ni ya dinga yi, a farkon aurensa, ya dinga zaluntata