Showing 66001 words to 69000 words out of 180068 words

Chapter 23 - Sabo Da Kaza By Surayyah Dee

18 Dec 2025

8730

da ta lakanci mayukan da suka dace da kowacce irin fata walau dry ko oily. Tun lokacin yanmattancina na gasgata mayukan oriflame da *Aisha lame* ta za'ba mini su, har yau kuma ban canja ba, domin kuwa duk tsiyar Gudale da kansa yake bani ku'din siyan mayukan Yana fa'din yana ganin amfanin su.
Tuntu'be ta Dan samun naki nau'in man da zai dace da fatarki mussaman a wannan season 'din na hammattan.
07036662633. Na gasgata ta.
Sai da na kammala komai, dakin ya kaure da kamshin kayan da na yi amfani da su. na fita kamar wacce zata je kicin sai kawai na shige dakin su Afrah na rufe na yi kwanciyata.
Har barci ya fara 'dauka ta na dinga jin bugun kofar tare da 'kiran sunana.
Na yi tsaki sosai na yi bakam.
Da safe kuwa, da wuri na fito na shirya masa abin karin kummalo.
Ya fito cikin shadda getzna fara 'kal.
Kyau iya kyau ya yi, duk da fuskarsa a 'daure take, idonsa na gefen dama jini ya kwanta a ciki tabbacin yana cikin bacin rai mai tsananin gaske.
Na yi kamar ban gane ba na ce "Ina kwana? an kammala abinci".
Bai ko kalleni ba, bare ya amsa, ya fice da Aman.
Na yi murmushi na ce "wanzami bai son jarfa.

Kai tsaye wajen Umma ya nufa, ya same ta ta idar da walaha. Yayin da Amnah take kan gado tana barci, Afrah kuwa tana tare da Antin Zaria a 'daya dakin.
Ta karbi Aman tana yi masa wasa.
Ta shafa cikinsa ta ce "Da alamun cikin nan bai cika ba maigidana".
Nan da nan ta 'kira Abida ta dauke shi tare da cewa "ki ha'da masa tea ya sha".
Ta zuba masa ido sosai ta numfasa ta ce "Ya jikinka?"
A hankali ya ce "Da sau'ki Umma! Dama zan fa'da miki ne zan je Gusau".
Da azama ta ce "Yanzun?"
Kai kawai ya daga mata. Ta zuba masa ido sosai tana nazartar sa. Cike da kulawa ta ce "A cikin halin da kake ciki na jinya zaka dauki mota ka tafi har Gusau? Idan baka damu da rayuwar ka ba ni na damu dan haka ba inda zaka je".
Ya yi kasa da kansa ya ce "Ki yi hakuri ya zama dole ne, idan ba zuwa na yi ba, ba zan ta'ba samun nutsuwa ba."
"Fa'da mini me zaka je yi"
Ya yi shiru domin a yanzu ba zai ta'ba iya fa'din laifin Guduyo a gabanta ba.
Dan haka sai ya ce "Zuwa zan yi na gaida Baban kawai".
Ta ce "To sai ka samu lafiya sannan zaka je din".
Ya yi shiru amma yana jin tamkar ya yi ta ihu, ba abin da yake so a yanzu irin ya samu kwanciyar hankali. Ya tabbatar kuma ba zai samu ba, sai ya samu aminci da Guduyonsa.
Cikin rauni ya ce "Zan iya zuwa Umma".
"Ba fa zaka je yau ba wallahi".
Jin ta rantse ya sanya shi ha'kurin dole.
Ya tashi yana cewa "To shikenan bari na koma na dan kwanta".
Ta amsa da ambaton "Hakan ya fi".
Ya shigo da sallamh ya tarar da na yi wanka na gyaran gidan tsab, ina zaune a falon ina karyawa cikin nutsuwa. Sanye nake cikin dankararen leshin da Kawata ta zana shi da kanta, ta yi oder, Ni kaina leshi ba karamin shiga raina ya yi ba, sannan ban ta'ba ganin wata da shi ba, saboda selected oder ne na manyan Mata. *Amyas newly & faily items* kenan.
Murmushi na yi na yadda na samu hayar gida cikin sau'ki da rahusa a kuma area mai kyau da tsaro a hannusu. Na sake tuna sadda suka zo har guday suka sayi kujeruna cikin aminci da mutuntawa.
Na tuna injin wanki na hannu mai kyau da na siyawa Aziza a hannusu tamkar sabo Kuma cikin farashi mai rahusa.
Idan kuna neman komai da ruwanki to samu *Amyas newly & fairly used items*
Komai na su cijin tsari da sauki da kuma.mutuntanta abokan huldarsu.
O8083909947.

Ya wuce wajen cin abinci ya zubo ya dawo falon ya zauna kusa da ni.
Har ya kammala zaman kurame ne a tsakaninmu.
Kallona kawai yake yi na sani kwalliyar da na yi ta ki'dima shi, sau tari



yana yawan tambayar inda ake zabga mini dinkuna na garari. Da kansa ya nemi shagon telar Dan ya gasgata maganar da na fa'da masa cewa mace ce. Domin a farko ya dauka namiji ne yake auna ni saboda tsananin yadda idan aka mini dinki suke zama a cikina na yi cass, duk da ina da jiki.
*Umm Muhd collection* kenan kwararriyar tela kuma shahararriyar yar kasuwar da bata saba al'kawari duk abin da kike so zata kawo miki har gida, dangin sutura, hatta kayan kicin, zababbu rantsattsu kuma a saukaka miki. Tabbas ni shaida ce. Wanda duk yake group dinta zai shada hakan 08063358662.

Ya kasa ha'kuri ya dube ni ya ce *"Halah* fa'da mini matsayina a gidan nan".
Ba ja in ja na ce "Mai gida mana".
Yana kallon nawa dai ya ce "Amma saboda kin samu daurin gindi shine na zama banza, na zama abin wula'kantawa a wajen ki?
Sau nawa zan baki ha'kuri? Me zan yi ki gane ina son ki? Me zan yi dan na samu zaman lafiya da ke? Kin hana ni nutsuwa, kin gigita mini zaman lafiya ta, ya ya kike so na yi ne?".
Na yi shiru na 'ki tankawa.
Ya sake cewa "Tunda kika dawo a cikin rarrashin ki nake amma kin kafe kamar Dutse.
To gaskiya zan fa'da miki na gaji, *Haka ya isa(Fatima Aminu Baba).*"
Nan ma na yi shiru bance komai ba.
Da ya gaji da jiran amsa ta. Cikin bada umarni ya ce "ki tashi ki je ki gyara mini dakina".
A gajarce na ce "Na gyara tuntuni! Shiga ka gani."
Bai musa ba! Ya tashi ya nufi dakin.
Ya ganshi a tsabtace. Komai a kintse, haka ban'dakin ga kuma kamshin turaren mutanan gabas na tashi.
Ya kwada mini kira "Hal Mohammadah".
Na zum'bura baki na amsa sannan na mi'ke na tsaya daga bakin kofar dakin.
Na ce "Ga ni".
Yana mini wani irin kallon da yake rikita ni, ya kashe murya ya ce "Gyara ya yi kyau! Na gode miki, Allah ya yi miki albarka".
Na amsa da "amin" a kasan ma'koshina.
Ya matso kusa da ni ya kamo hannuna ya ce "Shigo mana Guduyo ki ji abin da zan fa'da miki".
Ya jani har tsakiyar dakin ya yi 'kasa da murya ya ce "Taya ni mana mu yamutsa shimfi'dar nan. Ba dan ni zaki yi ba, ki duba Ubangijin da ya wajaba miki yi mini biyayya."
Na tsuke fuska sosai ba tare da na ce uffan ba, idona ya cika da 'kwalla na kasa magana.
Ganin hakan ya saka ya fara kokarin rage tufafin jikina.
Bakina na rawa na ce "Ba zan iya ba".
Da sauri ya dinga fa'din "Zaki iya baby nah! Bari a fara 'din"
Na fisge jikina na shammace shi na fito kusan a guje.
Ya biyo ni muka fara kokawa, ganin da gaske zai kai ni 'kasa ya sa na fara kuka ina cewa "Na rantse sai na fa'dawa Baban Gusau baka daina wula'kanta ni a falo ba".
Tamkar na watsa masa ruwan zafi haka ya sake ni a zabure.
Murya a dashe ya ce "Ba anan nake nufin yi ba Wallahi! zo muje ki taimake ni dan girman Allah".
Ya zura hannu a aljihunsa ya fito da key din motarsa ya dam'ka a hannuna.
Ya ce "Na baki motata! Duk 'kasar da kike so zan kai ki, zan saya miki bangle din gold."
Da karfi na ce "Bana so! Duk ka had'awa amaryarka, Ni kuma ka bar mini abina tunda kofar 'Dan-agundi ne".
Ya tunzura ainun ya ce "Haka kike da kafiya? Ba kisan rarrashi da ban ha'kuri ba?"
Na ce "A wajen ka na koya".
Ya zauna ya dafe kansa, yana ambaton Innalillahi wa Inna ilaihir rajiun.
A kausashe ya ce "fa'da mini me kike nufi da nine Halima?
"Ina nufin ka sahale mini, na je na samu wanda zai so ni da dukkan na'kasuna. Tunda a wangale kake jina, 'yar slim kake so, ba Abuskutu irina ba. Na sani zaka sake samo wacce ta yi daidai da taste dinka. Uwar maza ba uwar 'ya'ya mata Irina ba. Don haka nima ka bani damar da zan samu wanda ya dace da ni".
Ina rufe baki ya dinga fa'din "Innalillahi wa inna ilaihir raji'un" da 'karfin gaske.
Shudewar mintina goma muna haka. Ya dago muka ha'da ido, duk jijiyoyin kansa ta fito ta yi ru'du ru'du.
Na dauke idona daga kallonsa.
"Ba zan iya rabuwa da ke ba, na baki ha'kuri, manyanmu sun baki.
Me yasa zaki tsananta irin haka, me yasa ba zaki ha'kura ba?"
Kai tsaye na ce "saboda ban san ha'kuri ba, ban kuma iya shi ba."
A hankali ya ce "Ban san wata halitta a doron 'kasa da ta zarta ki ha'kuri da *Yakana(Takori)* ba."
"Cikin ido na kalleshi na ce "A da ne! a lokacin da nake tsananin son ka, nake tsananin son na rayu da kai.
Amma a yanzu babu sauran ha'kuri a tsakaninmu tunda na gane baka so na, bani da mutunci a idon ka.
Na riga na fa'da maka, na ha'kura da komai.
Na fa'da hawaye yana silalowa daga idona"
Cikin rauni sosai ya ce "Don't do this to me Halimatu! Ina son ki, ina son na rayu da ke, ki taimake ni ki yi ha'kuri.
Zan miki wani al'kawari da zan dauwama ina ro'kon Ubangiji ya bani ikon cika miki shi matu'kar kika yafe mini".
Na gallah masa harara na ce "Ri'ke al'kawarinka idan ka auro Fauziya sai ka yi mata. Ni kam ba abin da nake so daga gareka irin ka sahale mini, ko na sha'ki iskar da babu takura a ciki.
Sanin kanka ne akwai wadanda suka fika dacewa da ni, kamar yadda na fahimci ban dace da kai ba a yanzu".
Ya zuba mini ido sosai yana jin wani irin tashin hankali na kekketa shi.
Bakinsa na rawa ya ce "Ni kika fa'dawa hakan? Ni ko Guduyo?"
Ba kunya na ce "Eh".
Ya mi'ke ya sake fita. Ni kuwa ko ka'dan ban ji tsoron abin da zai biyo baya ba.
Ban tashi a wajen ba, ya sake shigowa! Ya shige dakinsa.
Yayin da tunanin da nake yi ya dinga kutso mini.
Ba abin da nake bu'kata irin na samu lokaci irin haka na cigaba da hakaito al'amuran da na fuskanta.












# Team Gudale#
# Team Guduyo#
# Surayya Dee✍️.
# Ana tare 🤝.
2/8/23, 10:25 - Buhainat: *Wannan littafin na ku'di ne, biya 500 ku'din karatu ta wannan asusun*
*2384876855*
*Surayya Ibrahim*
*Zenith Bank.*
*A tura shaidar biya ta wannan lambar*
*08032773332*.

*SDK*
*43-44*


Hakan da Sakina ta yi mini sai na zama very guilty. Domin kafatalin makusantan sa ba wacce nake jin nauyin ta irin Sakina.
Shudewar mintina goma suka fito tana ri'ke da shi sosai.
Na kallesu ina jinjina girman soyayyar dake tsakaninsu.
Na tuna irin tijarar da yake yi mata.
Na tuna irin rantsuwar da ta yi akan babu ita, babu shi.
Har cewa ya yi idan ta sake zuwa masa gida sai yasa Yan ta'addah sun dauke ta kowa ya huta da wuyar zaman ta.
Ita kuma ta kafe matu'kar ni ce matar gidan kuwa zata zo a duk sadda ta so.
Amma idan wata daban yake aure, idan ya ganta a gidan sa ya tabbatar ba Sakina Abbansu ya ra'da mata ba.
Amma a yau sai na gane soyayyar da ke tsakaninsu ta daban ce, duk wani cin alwashin da suke yi na babu su, babu juna iya lebensu ne, ko kan harshe bai hau ba, bare kuma zuciyoyinsu.
Bansan me ya saka harshena ya yi mini nauyi ainun ba. Na kasa bu'de baki na yi musu magana, ko da kuwa iya sannu ne.
Na koma na zauna a sanyaye! Aman ya kwanta a jikina tabbacin dai yana samun nutsuwa a jikin nawa.
Mama na yiwa waya idan tuwo ta yi ta aikowa Aman! Kai tsaye ta ce bata yi girki ba, na san kuma dalilin da ya sanya ta hana ni.
Har wajen takwas na dare ba su, babu labarin su.
Ina zaune, ina ta faman tubka da warwara.
Sai ga su sun dawo, ya 'dan ji sau'ki ba kamar lokacin da suka fita ba, tabbacin ruwa aka 'kara masa.
A falo ya zauna.
Yayin da Sakina ba ta zauna ba, ta ajiye masa ledar magungunansa, tare da cewa "Ka 'karantawa kanka damuwa, ka dai ji abin da likita ya fa'da maka".
Ta juyo ta kalle ni ba walwala ta ce "jininsa ne ya yi 'kasa a dalilin baya samun barci da kuma wadataccen abinci.
Shiyasa ulcer ta sake bada gudunmawa.
Ki kula da abincinsa da maganinsa".
Na ce "To" a hankali.
Cikin rauni ya ce "Sakina kin ce zaki bata ha'kuri a madadina! Dan Allah kar ki tafi baki kawo 'karshen wannan dambarwar ba.
Da gaske na ke yi bazan iya daukar abin da Guduyo ta dauka ba. Ta fini karfin zuciya, ki huce Sakina dan Allah".
A hankali ta ce "Amma na ce ka kwantar da hankalinka ko?"
"Ta ya ya hankalina zai kwanta kin zuba ido kina kallon yadda na zama a gidana, alhalin kina da damar da zaki kashe mini wannan wutar! Anti Sakina dan Allah ba zan iya ba".
Ya fa'da cikin rauni sosai.
Ta nisa ta ce "yanzu baka gamsu komai ya wuce ba?"
Ya sake shagwabe mata ya ce "ki fa'da mata ta dinga dafa mana abinci, ta daina yi mini rashin kunya, sannan ta dinga zuwa 'dakina, ko kuma ta daina rufe mini 'kofar 'dakinta".
Nauyin maganganunsa suka kama Sakina ta ce "To zan fa'da, za kuma ta gyara".
Ya lumshe ido ya ce "Na gode Anti".
A fili ta ce wannan "Antin dai ba har zuci bane".
Ya sake cewa "Da gaske nake Antina ce ina da yar'uwar da ta zarce ki ne?"
Ta murmusa ta ce "Sai Guduyo".
Ya langwabe kai ya ce "Ita ai yanzu ta ture ni akan matsayina, ta 'ki yarda da dimbin soyayyar da nake yi mata.
Shin an ta'ba yiwa wani 'dan-adam rashin uzziri iri na kuwa Sakina?".
Ta ce "Ai kuwa uzzirin da ta yi maka ba kowa ake yi wa irinsa ba".
Ya girgiza kansa ya ce "Na gamsu ta yi mini, amma yanzu ina rokon a sake yi mini.
Pls Sakina! Ki yafe mini, na tabbatar idan kika huce gaba'daya Guduyo zata yafe mini. Ke ce ita, na sani".
Ya fa'da yana ru'ko dukkan hannuwanta.
Ta zuba masa ido sosai sannan ta ce "Tunda har na dawo maka da ita, ai kuwa ka san na yi ha'kuri".
Ya sassauta murya ya ce "wannan na dole ne Sakina! Ki goge komai a zuciyar ki.
Wallahi na canja, zan yi mata adalci, zama na Fisabidillahi zamu yi".
Na lura jikin Sakina ya yi laushi tubus.
Yayin da ni kuwa ban ji komai ba.
Ta kalle ni fuskarta ba walwala ta ce "Tashi ki samo masa abin da zai ci kafin ya sha magani".
A hankali na ce "Ban dafa komai ba".
Ta zuba mini ido sosai ta ce "cewa na yi ai ki samo masa ba wai ki kawo ba".
Girman Sakina ya sanya na mi'ke na doshi kicin din. A raina kuwa ba karamin takaici nake ji ba, domin na riga na ci alwashin ba zan sake 'dora tukunya saboda shi ba, ba zan sake dafa abinci na bashi dan ra'din kaina ba.
Na sani bai son jollof din taliya tsurarta, wacce babu vegetables a ciki.
Dan haka na dafa a hakan.
Na zubo masa plate na Kai gabansa na ajiye.
Na koma na dauko kifi a fride wanda na Riga na soya, na yi pepper fish.
Na yi warming dinsa, na zuba mana taliyar a plate daya na dora kifin a kai saboda na sani Sakina masoyiyar kifi ce fiye da nama.
Na saka fork guda biyu, na kai gabanta tare da cewa "ga abinci Maman Nana".
Ta ce "Ya baki saka masa kifin ba shi?
Na ce "Bai dame shi ba ne".
Ina kallonsa yana ta juya abincin nan. Amma ga mamakina sai na ga yana ci a gaggauce tamkar dai ya samu abin da yake tsananin so.
A zuciyata na ce "Ashe dama wulakanci ne, ba ci ne baka yi ba.
Muka ci abincin mu da Sakina tana yi tana bawa Aman a baki.
Muka kammala ta yi haramar tafiya, na rakata har harabar gate.
Ta kalle ni ta sassauta murya ta ce "Ki dinga bashi abinci, sannan ki daina jan doguwar magana a tsakanin ku, komai ya ce kawai ki ce "To".
Nan da nan na fara kuka na ce "Na gane dai yanzu so kike kawai ki koma bayan sa".
Cikin rarrashi ta ce "Ai na sha fa'da miki ke da shi 'daya kuke a waje na, ba wanda ya fi wani. Kin sani a koyaushe ina bayan ki ne. Ba dan kin fi shi ba, sai dan kin fi shi gaskiya da ha'kuri. Sannan ba zai yiwu na zuba ido na bari ki wula'kanta ba, a ko'ina zan baki kariya.
Hakan kuma ba shine dalilin da zan 'ki fa'da miki gaskiya ba."
Ta yi shiru tana kallon yadda nake kuka 'kasa 'kasa.
Ta sake sassauta murya ta ce "ki yi shiru! Ki ji me zance miki Sadiya".
Na dan nutsu ka'dan. Ta yi waiwaye dan ta tabbatar babu kowa a kusa da mu.
Ta numfasa ta ce "Ulcer ke damunsa. Ki kula da lafiyarsa ta hanyar bashi abinci mai kyau kuma marar yaji.
Shin idan bai koshi ba, ta ina ma zai dinga kwadayin ki bare ki ja shi a kasa?
Idan ba kya kwalliya ta ina zaki ki'dima shi ya rasa nutsuwa?
Shin idan ba kya ta'kaita magana a tsakaninku yaushe zai damu da sai kin yi masa magana?
Idan ya fita ki shiga ki gyara masa dakinsa.
Na sani yanzu ya gane yana sonbki, amma so nake sai ya gane ke ce duniyarsa! kuma dole ne ya zauna dake cikin mutuntunta wa.
Amma hakan ba zai faru ba sai kin iya takun ki."
Hawaye ya 'balle mini na ce "kina nufin na dinga zuwa 'dakinsa kenan?"
Da sauri ta ce "Idan ba ya gidan ki shiga ki gyara masa, amma ban ce ki je masa kwana ba. Ai na yi miki al'kawarin sai ya gane kuren sa akan furucinsa, sai ya 'karyata kansa da kansa."
Bakina na rawa na ce "Na gode sosai".
Mun jima a wajen sannan ta tafi.
Na dawo na tarar basa falon.
'Dakina na shiga, ga mamakina sai ganinsa na yi, har ya yi wanka yana sanye da wata cotton 'din jallabiya marar nauyi maroon kala.
Yana kwance akan gadona ya saka Aman a gabansa da yake barcinsa cikin nutsuwa, shima ya yi masa wankan.
Ban ce masa 'kala ba, na shiga na yi wanka na kuma yi alwallah.
Na shirya cikin lallausan kayan barci, riga mai dogon wando. Wanda order ne na mussaman cikin tarin odar *Umm Muhd collection* 08063358662.

Har yanzu ban daina amfani da kayan Oriflame ba, tunda na yi sa'a

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login