Showing 84001 words to 87000 words out of 180068 words

Chapter 29 - Sabo Da Kaza By Surayyah Dee

18 Dec 2025

8758

an yi an gama?
Saboda Allah daga yin aure har zamu haihu bamu mori amarci ba?"
Na kalle shi na ce "mun zarce watanni biyar fa da aure. Ai bai yi wuri ba. Sa'anin aurenmu fa sun fara nauyi.
Ya gallah mini harara ya ce "wattannin aurenmu zaki lissafa mini ko watannin fara yin auren? Shikenan daga dan ta'ba ki sai ki yi ciki ban gama gane komai ba. Gashi duk kin wani sake kin yi yaushi, sannan ba dama a more ki".
A hankali na ce " Ai kuwa ba dan ta'bawa ka yi mini ba! Kai ma ka sani, sannan nan gaba in sha Allah zan ji sau'ki tunda ga magunguna an ba ni".
Ya mi'ke ya fita yana fa'din shi kam wallahi an cuce shi, daga yin ciki na wani zama ragajab tamkar wacce ta haihu da yawa. Baya ga haka bai gama gane komai ba an fara masa amai daga nan kuma sai kashi da kukan jinjirai.
Mamaki ya sanya na bishi da ido, na kasa bu'de baki na ce komai.
Yana bu'de kofar falon Abba yana kokarin shigowa.
Ya dawo da baya ya bashi hanya Yana cewa "Abba sannu da zuwa".
Yanayin Abba ya nuna tamkar ya ji maganganun Gudale da yake yi, amma bai ce komai ba.
Ya ce gaishe ni ya zo yi, ya ga fitarmu, sannan Sakina ta yi masa albishir din albarkar da ta sauka mana.
Murnar da Abba ya yi ita ta wanke mini takaicin abin da mai cikin ya cusa mini.
Ya dinga yi mana addu'a da fatan alheri.
Gefe guda kuma jirwaye ya dinga yiwa Gudale akan muhimmanci gode wa ni'imomin Ubangiji.
Ya tafi Gudale ya bishi a baya cikin sanyin jiki.
Haka muka cigaba da mirgina wa, ban samu kan Gudale ba sai da cikina ya shiga wata uku da kwanaki. Amai ya tsaya mini, na daina zazzabin dare, sannan kasalar ta yi matu'kar raguwa, sai dan abin da ba za'a rasa ba.
Sai ya zama kuma na koma kamshin turarensa nake matu'kar son na sha'ka, shiyasa kullum ina ma'kale da shi ba gajiya. Shi da kansa sai da ya ce "Ashe cikin ba zai hana mu komai ba?"
Kaina na saman kirjinsa na ce "gajen ha'kuri ka yi dama".
Shikenan sai zaman namu ya dawo normal mussman da bana nuna masa gazawa a shimfida. Na lura Gudale idan bai samu yadda yadda so a wannan fagen ba, to lah shakka babu zaman lafiya.
Na sani ina matu'kar 'kuntata da jarabar sa har na fara fargabar dawowar sa, domin ko abinci ya dawo ci, sai ya kusance ni babu daga 'kafa. Idan na nuna ba haka ba sai ya zama sanadin da zai kwanaa ya yini bai ce mini 'kala ba. Ko ya yi ta habaicin duk hidimar da yake yi da ni, ba dama na yi masa abin da yake so, me za'a yi da sangartacciyar mace mai langwai.
Ko ya yi ta fa'din 'kamshin aljannah a wannan yinin ko daren ya haramta a gare ni domin ban yi abin da ya yarda da ni ba.
Yawan kusantar da yake yi ya haifar mini da wani irin ciwon mara mai tsananin gaske.
Da zarar ya kammala idan na dinga magogo sai an 'dauki lokaci kafin na samu kaina.
Tun yana ganin abin iskanci ne har ya gamsu da gaske nake yi. Ya dan rage yawan nema na amma dai kullum zai yi. Sai dai ba kamar da ba, ya rage ne kawai, a lokacin na gane mabu'kaci ne sosai sannan ya 'daura 'damarar sai ya mayar da ni mabukaciyar.
Zaman dai ba yabo ba fallasa, har na shiga wata na hudu.
Muna ta Shirin fara yin jarrabawar gwaji na second semester (Test) kawai Asuu ta tafi yajin aikin gargadi na wata 'daya.
Dalibi baya son srike amma ni sai ya zo mini a dai-dai saboda yadda nake shan wahala. Tunda na samu cikin nan ban huta ba, sai dai karfin hali kawai, ga ciwon mara da ciki lafawa suke yi ba wai na daina ne gaba'daya ba.
Da daddare ina kwance akan gadona ina charting da yan'uwa cikin *Moriki* family group din mu na WhatsApp.
Kamar jifa sai Yaya Ashir ya shigo nan da nan group din ya cika.
Ana ta hira cikin jin dadi mussaman da yake ana daukar lokaci ba'a hadu hakan ba a dalilin kowa tasa matsalar ta ishe shi amma yau kam har su Antin Zaria duk an hadu.
Yaya Ashir ya yi tagging 'dina ya ce "Ke kam kina gari ne? Kin yi wahalar ga ni".
Na tura emojin din dariya tare da cewa "Ina nan mana! Ai duk kallon kowa nake yi, ba wanda ya sake le'ko ni sai Anti Sakina".
Nan da nan aka fara raddin wa nake 'kira ina gaisa wa da shi? Suma sun 'kyale ni da Sadik tunda ya mamaye kowa a wajena".
Na sake yin dariya ina fa'din ba hakan bane, amma ai sune manya ya kamata su dinga 'kira suna jin lafiyata, a dinga turo mini goron juma'a".
Sosai aka yi hira, har waya aka dinga buga wa wadanda basa online akan su shigo yau ana zumunci.
Mutanan Gusau da Kebbi duk sun fito an yi da su.
Gudale ne kawai ya makale bai ce komai ba amma ina ganinsa yana online din.
Da Antin Zaria ta yi tagging dinsa tana cewa ya fito, sai ya gabatar da uzzirin yana cikin aiki ne ya gaida kowa kyauta.
Sai goma aka rufe hirar aka yi bankwana, bayan Yaya Ashir ya sakawa duk wanda ya girma katin 500. Yayin da Yayyen nasa suka ce ai su ya kamata ya bawa ba mu ba. Shima ya kafe sai dai su bashi. Aka rabu cikin farin-ciki mai yawa.
Na yi wanka na dauko sabon turaren Oriflame, na feshe kayana da shi, yayin da na goga roll on dinsa.
Kai *Aisha lame* 07036672633. Madallah da kayanta da farashinsu.
Na hau sama a hankali sai dai me? Ina zuwa na ji kofar a rufe, na dinga murda kofar amma shiru, na koma knocking nan ma shiru.
Na koma kiransa a waya, amma sama da sau goma tana ringing bai dauka ba.
Har na shiga daya dakin zan kwanta sai na ga sai na yi wahalar dauko bargo.
Sai kawai na dawo kasa, idona taf da hawayen ba'kin ciki. Na dinga tunanin me na yi masa to? Nasan dai har ya dawo daga sallar isha, ya ci abinci kalau muke.
Na dinga juyi, ina tunaninsa, na kasa jurewa na dauko wayata ña ga karfe dayan dare har da mintina uku. Na shiga doka masa 'kira, karshe sai ya kashe wayarsa ga'badaya.
Ranar rabi da rabi na yi barci, har zuwa asuba.
Ina idar wa, na fita falo na zauna, ya dawo ya ganni ya wuce. Na bishi da sauri ina cewa "Ina kwana?" Kamar ba zai amsa ba sai kuma ya amsa din a takaice.
Muka isa har dakinsa ina tsaye ya haye godo ya lulluba har kansa tabbacin ba zai saurare ni ba.
Na sassauta murya na ce "Me yake faruwa ne, me na yi maka? Ni bana son irin haka! Idan wani abin na yi da ya bata maka Allah ya baka ha'kuri, shike nan?"
A gajarce ya ce "To je ki abin ki, ina bu'katar ka'daici ne".
Na zauna a akan side durowa na fara yi masa kuka ina fa'din "Ni bana so, bana son haka gaskiya, ka daina yi mini fishi, jiya ko runtsawa ban yi ba, dan Allah ka barni na samu sukuni kasan dai bani da lafiya".
Ya dago a tunzure ya nuna mini 'kofa ya ce "out"
Na 'ki tashi, sannan ban daina kukan ba, sai ma volume da na 'kara tamkar wanda yake duka na.
Ransa ya baci 'kwarai da gaske ya ce "Amma kuwa Sadiya zaki saka na miki duka sai ki yi kukan da dalili. Ban miki komai ba ki zo ki tasa ni gaba da kururu wa, wanne irin al'amari ne wannan?
Shikenan! Bari ni na bar miki 'dakin tun baki janyo na miki dukan da dukkan *Moriki brothers* zasu mini ca akan ki ba. Tunda na gane a yanzu ma da kike dakin aure har da rabo, ba'a daina mini magana da ke babu shamaki ba. Ai wlh ba zan yarda ba".
Na yi matu'kar ka'duwa da wannan furucin wato hirar jiya ce ta bata masa, me aka yi to? na yi shiru cikin bugawar zuciya. Murya a dashe tsabar al-ajabi na ce "Yanzu gaisuwar da aka yi cikin jama'a ne laifi? 'Yan uwana kuma 'yan uwanka sune abin bacin rai dan kawai mun gaisa?"
Haka kawai na ce "ya sake hassala wai na yi masa rashin kunya.
Yana kumfar baki ya ce "shin Ashiru Al'amin ne shi?
Ko yanzu na fàdi na mutu ba abin da zai hana Ashiru shiga sahun zawarawanki tunda ba kunya ne da shi ba, bare ya yi mutunci.
Saboda ke tabbattaciya ce shine kika wula'kanta ni, kika yi ro'ko, wai ki rasa wa zaki ro'ka sai Ashiru. Shikuma jiki yana rawa ya turo miki, amma da yake shedani ne yasan ya yi ta'addanci shine ya ha'da da su Farisa. Saboda yasan zan kalubalenci hakan. Wato ba ke kawai ya bawa ba, amma ai kowa ya san albarkcin ki suka ci kudinsa, tunda shi matsolo ne".
Raina ya baci sosai, amma na ha'diye na ce "shikenan na yi kuskure ba zan sake yin magana ba, matu'kar ba da mata bane".
Ya ta'be baki ya ce "Ina ce jiyan ma tagging dinki ya yi?
Ke kuma shikenan kika balle da magana har da su ro'ko, ai tozarci kam kin yi mini, amma ki jira sakamakon da zai biyo baya".
Duk yadda na so maganar ta wuce Gudale bai yarda ba. Domin gaba ya dauka da ni sosai. Abinci ya daina ci, ya daina dawowa cin abincin rana, da daddare kuwa duk naci na ba zan shiga masa dakin sa ba.
Kwana uku muna haka, hankalina ya kai kololuwar tashi, ga rashin cikakkiyar lafiya, ga masifar fishin Gudale.
Gaba'daya na birkice, na rasa inda zan tsoma raina.
A wannan lokacin na 'kara gane wa ina cikin jarrabawar tsananin sonsa. Wani irin so nake yi masa da ya wuce ka'ida, shiyasa nake shiga tasku idan yana fishi.
Ranar asabar da wuri na kammala yi masa samosa, ina addu'ar Allah ya sanya ya ci. Na gyara kicin da falon, sannan na yi wanka, na shirya cikin leshi dinkin bubu ne amma dinkin ya yi matu'kar tsaruwa. Anfi ganin iri irensu a mujallar ado da kwalliya. Madallah da dinkin *Umm Muhd collection* mai komai da ruwanka.
Yo komai yi take yi indai na sana'a ne gashi kuma kayanta da sauki, kuma zababbu, na sha fa'da Ni shaida ce. Da wahalar gaske ka ga abu kana so ace ka jira. Komai available ne wajen *Ummu Muhd collection.08063358662*.

Na fito falo hannuna dauke da tsinken turare irin dogayen nan. Na ma'kala na zauna ina kallon agogo goma na safe saura ka'dan, Ina ta tunanin jiya Abba juma'a Abba bai shigo mini ba, tunda yanzu ya sabar mini in dai ya dawo masallaci sai ya shigo mun gaisa Baba ne kawai bai fi sau uku ya zo mini ba.
A Raina na ce "Da Gudale wani ne yau sai ya barni na shiga cikin gida nima na ji da'di tunda aka yi mini aure watanni kusan bakwai sau hu'du kawai na shiga.
Ina tsaye ya fito cikin kwalliyar kananun kaya.
Farar riga ce mai tsada samfurin Bvulgari sai shudin jeans ya gyara sumar nan sai she'ki take yi, kamshin turarensa yana karade ko ina.
Na Sha gabansa ina cewa "YAU kwana uku kana punished dina, a ka'idar sharia kwanan uku ne karbabben fishi. Dan Allah ka huce hakanan, ko dan bebinka da yake cikina ya samu kuzari".
Ya kalle ni ya watsar ya wuce ya nufi waje.
Na bishi har muka isa kofar da zata sadamu da cikin gida.
Na sake shan gabansa murya na rawa na ce "Dan Allah! Allah ya baka ha'kuri, bana iya cin abinci, ga'badaya bani da sukuni, alhalin kai ne ka zafafa lamarin nan, amma na yarda ban yi dai-dai ba, na baka ha'kuri ai sai ka ha'kura."
Ya kankance ido ya ce "Tunda ba zan ha'kura ba ke ki ha'kura ki fita a harkata mana. *Kamar ni Sadik Abubakar Moriki* matar aurena zata dinga ro'kon wani majanunin bawan daya addabe ni, ya zame mini barazana a duniyata.
Na rantse ba zan fasa fadar an cuce ni ba. Abba ya takaice ni wallahi! Haka kawai ya manna mini auren da babu yardata alhalin ra'ayina da naki is pararell.
Na yi matu'kar ka'duwa, amma da ke so hana ganin laifi sai na ru'ko hannunsa ina hawaye na ce "Allah ne ya kaddara auren ba Abba ba! Ina son zama da kai, amma akan abu ka'dan sai ka rufe ido ka nuna mini dole aka yi maka ka aure ni, ko kuma kana zaune da ni akan tilas". Na lura jikinsa ya yi sanyi da kalamaina.
A hankali na ce "Taimake ni mu je ka karya, samosa na yi maka. Ka yi hakuri".
Na ru'ko hannunsa muka doshi falon dai dai lokacin Abba ya turo kofar da muka bar jikinta tamkar almara.
A hankali ya ce "Sannu Halimatu ya jikin? Jiya ban samu shigowa ba, saboda na wuce ta'aaziya".
Na zare hannuna na gaishe shi cikin girmama wa. Ya amsa yana ta mini sannu da sanya albarka.
Haka Yaya Sadik ya gaishe shi ya masa masa babu yabo, babu fallasa.
Ya juya yana cewa "Ba sai na shiga ba, tunda mun gaisa."
Muka shiga falo, na zuba masa, ina ta rawar jikin ha'da masa shayi.
Da haka na dinga lallaba shi, har ya huce. Dan rashin ta ido kuma shikenan ya fara nanukata, idan na yi magana akan ya bari na huta sai ya ce "kwanakin da ya dauka bai yi ba yake fanshe wa. Ba yadda na iya haka nake biye masa, na yi masa yadda yake so
Ai kuwa sai ciwon ciki ya taso mini haikan na kwana na tashi da shi, rannan da yammaci sosai na je fitsari sai na ga jini jini hankalina ya yi matu'kar tashi.
Na fito a gigice, na yi sa'a yana gida ya dawo daga wajen aiki.










# Team Gudale
# Team Guduyo
# Surayya Dee ✍️
# Ana tare 🤝.
2/8/23, 10:25 - Buhainat: *Na ce ba kinsan wani hadi da ake yi wa asalin man ridi da kwakwa da wani man da ban kama sunansa ba, da ba'a samun original din su sai a wasu kebantaccun jahohi?*
*kina fama da matsalar cinyewar gashi ko kuma rashin tsayinsa?*.
*Kina neman ha'din da da zai sanya fatarki laushi da sulbi, kuma cikin saussaukan farashi? Tuntu'bi wannan lambar dan samun naki cikin sau'ki. Kaya mai inganci shi yake siyar da kansa.*
*Sister Zainab 08039315577.*


*SDK*
*55-56.*

A hanzarce ya nufi asibitin premier da ni, tunda shine mafi kusa.
Gynecologist na ga Ni! aka kammala dube dube da gwaje gwaje aka gano cikin ne bai zauna dai-dai ba, sannan bakin mahaifar a bude take.
Take suka kwantar da ni, aka fara shirin yi mini yar 'karamar tiyata.
Suka gyara zaman cikin sannan aka daure bakin mahaifar.
Kwana uku a asibitin, gatan da na gani a wajen danginmu ba ka'dan bane, na sani kuma ina sake samun soyayya dan kasancewata matar Gudale.
Abba ji yake tamkar ya taya ni numfashi.
Haka dukkan sisters dinsa kullum sai sun zo da kayayyakin ciye ciye.
Mama ce a wajena.
Haka brothers dina da iyalansu tamkar mai ciwo sosai haka aka dinga zarya da dawainiya akai na.
Antin Zaria itama sai da ta zo a ranar ta koma. A lokacin na sake gane soyayyar da ake yiwa Gudale mai girma ce.
Domin komai yi masa ake yi, duk wanda yake kusa aka kawo bill ko wani magani sai dai a biya ba wanda yake jiransa.
Hatta Umma da ba wani sakar mini fuska take yi ba, sau biyu ta zo duba ni.
Ranar da aka sallame ni Sakina tana asibitin da ke da daddare ne. Sai dai dokokin da aka sanya mini masu yawa ne, babu hawa bene, babu mua'amalar aure, babu daukar abu mai nauyi, babu garaje yayin tafiya ko wani al'amari, hatta shara duk an ce babu. Har zuwa lokacin da komai zai daidaita.
Aka sanarwa mutanan gida an sallame ni zamu dawo ba sai sun zo ba.
Take Abba ya kira Sakina a waya ya bada umarnin idan mun je gidan ba wajena za'a kai ni ba.
Wajensa za'a kai ni, ya saka an gyara mini dakina da nake kwana kafin aurena.
Nan da nan na ji babu da'di mussaman yadda na lura Gudale ya matsu a sallame ni, kullum sai ya tambayi likitan yaushe za'a sallame ni?.
Sannan na sani tun fil'azal baya kaunar na tafi wani waje. Shi dai ko ba zai mini magana ba, ya dawo ya ganni a gida shine burinsa tun ban zama matarsa ba, na shaida wannan.
Har cikin zuciyata ban so wannan hukuncin ba. Amma ban isa na bu'de baki na cewa Abba bazan bi hukuncinsa ba.
A kofar gidan muka tarar da Gudale yanayinsa dai babu damuwa kuma babu walwala.
Sakina ta taimaka mini na fito a motar, ta ri'ke ni muka shiga cikin gidan. Yayin da ya debo kayayyakina.
A dakin da aka gyara mini muka zauna. Mama bata wani jima ta tafi wajenta bayan sun gaisa da Umma.
Abba da kansa ya shigo har dakin ya mini sannu, ya kuma ce mini "Komai kike so ki ci, ko kike bu'kata ki fa'da, kin sani dama nan ne gidanku".
Na amsa da "To" cikin girmamawa.
Zamana gaban Umma ya sake fahimtar da ni da gaske bata sona amma abin mamaki ta damu da cikin jikina.
Domin idan zan yi wanka 'Yan aikinta take turowa su taimaka mini ta hanyar surka ruwan, tunda ta ji ance jijjiga mai karfi tana iya sawa cikin ya fa'di shikenan komai sawa take ayi mini. Ni ce dai bata cika yiwa sannu, ko nuna tausaya wa ba.
Hakan bai dame ni ba, mussaman da yake kullum Gudale a dakin nawa zai zo ya karya, hakan abincin rana, da daddare ne yake ci a wajenta.
Indai yana gida to yafi zaman dakina. Mafi yawan hirarsa ta adadin kwanakin da zan yi na koma ne.
Tun yana girman kan ya bayyana mini ya yi kewata har ta 'kure ya fara fa'da bayan na yi sati a gidan Abba.
Wanda kwanakina goma rabona da gidansa kenan.
Ranar litinin da ta yi dai-dai da 'daya ga watan October ranar hutu ce a gaba'daya fa'din tarayyar Nigeria. Saboda a irin wannan ranar aka 'yanta 'kasar daga hannun turawan Birtaniya.
A ranar tun taran safe ya shigo ko

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login