Showing 111001 words to 114000 words out of 180068 words

Chapter 38 - Sabo Da Kaza By Surayyah Dee

18 Dec 2025

8740

sa za'a fahimci halin da nake ciki a kuma yi uzziri*.
*Na gode sosai*.



# Team Gudale.
# Team Guduyo.
# Surayya Dee ✍️.
# Ana tare 🤝.
2/8/23, 10:25 - Buhainat: *Ummu Muhammad collections*
*Tana sayar da dukkan nau'in sutura masu kyau zababbu kuma masu sau'kin farashi*
*Tana sayar da takalma da jaka masu kyau*
*Tana ha'da lefe*
*Tana ha'da kayan haihuwa*
*Tana sayar da Data*
*Tana yin adashe, Kuma fasihiyar Tela ce*
*Tuntube ta a wannan lambar 08063358662*
*Siyan na gari aka ce maida ku'di gida"


*SDK*
*67&68.*

Na hadiye fishina na gabatar masa da meat pie da lemo.
Ya dinga jaye jayen magana, har ya tisa ni a gaba muka fita.
A hanya ya kalle ni ya ce "zoben gold zan siya miki, kinsan ban siya miki komai ba as gift duk iyayen yarinyar ne suka yi komai.
Farin ciki ya mamaye ni na murmusa ka'dan na ce "Thank you".
Da kaina na zabi wanda nake so ya biya ku'din babu musu.
Muka dawo ana shirin yin la'asar. Ya shiga da yarinyar wajen Umma ya wuce masallaci.
Tunda ya dawo yake rawar jiki, ban samu kaina a hannunsa ba dai da yammaci ya yi sosai.
Al'amarin Gudale na matu'kar takura ni domin rashin nauyinsa da cikakkiyar lafiyarsa na sake kara masa jarumta domin yana shafe lokaci mai yawa yana abu daya. Ya iya biyar da ni, yana murza ni yadda yake so ne, yana kuma sarrafa ni ta yadda zan dauwama a cikin sonsa da kulafacinsa, na kan manta duk wani kayan takaicinsa da zarar na shiga hannunsa.
Sa'ar da na yi bashi da ha'kuri a wannan fagen, dana fahimci hakan sai nake iyakacin kokarina ina nuna kawaici da alkunya akan lamarin ta yadda nake samu na ja zarena a other room.
Duk wulakancinsa matu'kar bu'katar abin ta ciwo shi sai ya tattaro duk wani siffar kamala da rarrashi da kuma wayo dan ya same ni yadda yake so.
A haka rayuwar ta cigaba da gurgurwa yau fari gobe baki. Amma a gareni bakin yafi yawa domin ban huta a hannun Gudale ba ban huta da shagulatin bangaron da Umma take yi mini ba.
Wani lokacin ma idan ta zaunar da shi ta karanta masa karya da gaskiya sai ya zama sanadin fada a tsakanina da shi, sai ya share ni. Wani lokacin na yi ta bibiko ina bashi ha'kuri a dalilin an jarrabi zuciyata da gudun bacin ransa.
Wani lokacin kuma na daure na zuba masa ido.
A haka har Amna ta cika shekara guda.
Yarinya mai matu'kar kyau gashi tana samun kulawa, ga kuma suturu irin na 'ya'yan gata tsadaddun gaske. Ko ina yarinyar ta shiga daukar ido take yi. Antin Zaria bata dauki al'amarin Amnah da wasa ba. Daidai lokacin nima na kammala karatuna na fito da sakamako mai kyau.
Na fara bautar kasa a asibitin Malam.
A lokacin Amna ta yi shekara daya da rabi. Tuni Umma ta yayeta a dalilin mai sunanta tana kasar Jamus tana wani course na shekara daya tare suka tafi da mijinta. Saboda shi ya yi ritaya.
Dai dai lokacin Yaya Gudale ya fara wani irin zazzabi, ba dama na fara dafa abinci zai fara amai.
Ban isa na saka turare ba, bare shi ya saka da kansa. Ga yawu, duk wani laulayin ciki haka ya bayyana a tare da shi.
Bai fita daga wanccan k'angin ba, wasu irin marurai suka fito masa har a hammata sosai ya ke jin jiki.
Tsakaninsa da abinci sai farar taliyar hausa da manja.
Ruwa sai an nemo masa na borehole mai zartsi.
Tausayi yake bani domin shi ko pure water baya sha sai na roba, amma cikin lokaci kalilan rayuwa ta yi juyin waina da shi.
Kowa ya tsorata aka dinga fargabar ko wani ciwo ne ya shige shi mai tayar da hankali.
Yayin da ni kuma nake ta fari ina budewa, komai nawa ya cika, na yi wani irin kyau na ban mamaki.
Tsawon lokaci yana fama da amai da zaben abinci.
Bai samu kansa ba sai da ya shafe wata biyu. Amma maruru kam sauki suka yi, domin da wani ya warke, wani zai dawo.
Duk wani gwaje an yi masa an ce lafiya lau.
*Asibiti*
Wani zuwa asibitin Gudale ya yi, wani likita da ya gaji da zaryar Gudale a asibiti ya ce "Anya ba Madam ce ta bar maka laulayin ciki ba? Wannan ciwon naka ina tantama idan ba laulayi kake yi ba."
Da mamaki Gudale ya ce "Dama ana iya yin haka ne Dr?"
"Yes of course wasu mazan idan matansu suna da ciki suna tsintar kansu a irin wananan yanayin amma ya banbanta da yadda kowa yake yin nasa. Sannan masu yi din basu da yawa.
Jikin Gudale ya yi sanyi. Ya dawo gida cikin waswasi mai yawa. Ya fara sanya mini ido sosai.
***
Ba zato washagari ya bini asibiti ya sanya aka mini test ai kuwa sakamakon ya nuna ina da ciki na wattani uku, a kuma lissafin jinyar Yaya Gudale ya fara ne tun cikin bai fi sati biyu ba.
Muka dawo gida yana ta sababin ya gode da muguntar da na yi masa, me nake nufi da shi ne da zan turo masa ciwo ni kuma na yi ta yin kyau ina sake yin takama?".
Na dinga rarrashi ina gintse dariyar da take neman subuce mini, ina tuna shekaranjiya ma sai da naga yana share kwalla yana fa'din ya Allah kasa ba ciwon hanta ne ya same ni ba.
A hankali na ce "Allah ne mai ikon saka ciwo ko bayar da lafiya. Ka kuma sani da ina saka ciwo Yaya Gudale a cikin hayyacina da kai zan yiwa rowar sa, haka nam da ina da ikon cire maka wannan halin da kake ciki da tuni na yi. Ka yi hakuri".
Hakan muke ta tafiya, sai da cikina ya shiga wata na biyar sannan ya samu ikon cin abinci, ya kuma daina yin marurai.
Sai me? blBa sai kuraje a baki kuma suka baibaiye shi ba. Ko ruwa sai da dabara zai sha, kusan kurajen nan sun fi wahalar da shi akan jinyar domin komai ya saka a baki da azaba zai hadiya. Ya yi matu'kar zubewa.
Rannan ya siyo youghrt amma yana sawa a baki ya mike tsaye.
Tausayi ya kama ni. Na ce "Sannu Yaya Gudale na ga kuma babu yaji a ciki".
Ba'kin ciki ya kama shi ya nuna ni da yatsa ya ce "ke kina da bakin yi mini magana? Muguwa kawai, ai na sani kulawar da na baki a cikin Amna kika raina, sau daya tak na ce miki mai langwai shine kika dinga tashi cikin dare kina buga mini Tabbati yada da Izaja'a ko? To ki je an karbi addu'arki sai dai ki sani kama tu dini tu danono zan miki. Ba zaki kuma ganin sassauci a waje na ba. Ke wannan da kina da dama wataran sai dai cikin dare ki daure ni. Na ji saukar bulalar lalle a jikina tsabar yadda kike da cikina. Kuma ki bi a sannu mugunta fitsarin fako ce."
Gaba daya lamarin dariya yake bani kwarai da gaske, bansan ya aka yi ba dariyar ta kwace mini, na dinga yi ba kakkautawa.
Ai kuwa ya fusata kwarai da gaske a wannan lokacin tashin hankalin dana fuskunta ba ka'dan bane. Domin ina ji ina gani ya haramta mini kunna gas. Ya je ya lodo mini gawayi. Ya kuma yi rantsuwar da shi zan dinga girki tunda ya gano ina da hannu wajen halin da yake ciki, ta baya son warin gas ba kuma zai mini uzziri ya cutu ba.
Ya haramta shigo da ruwan sha ko da pure water ne kuwa.
Tsakanina da pure water sai na je asibiti.
Amma matu'kar a gidansa ne sai dai na sha wanda yake sha.
Haka nan ko roll ya kwashe su ya haramta mini sakawa. Ranar da na dinga ro'kon ya bar ni na dinga saka roll saboda kada na dinga bashi, gashi ina shiga cikin jama'a.
Ai abin da ya biyo baya ba mai sau'ki bane, wai wa nake da shi a waje da zance za'a ji ina tsami? Shine mijina shi kuma tsami tsamin yake sha'awa, yake muradi.
Ya kalle ni ya ce "Ashe kirkina yawa ne dashi lokacin da kika dinga mini amaye amayen ba kya son turarena, haka na tattra na barshi. Har dakin na canja a sama wanda babu irin wannan kamshin amma baki gode mini ba. Da kika dawo kina son kamshin kuwa har fesa wa nake yi ya hau kaina duk dan na burge ki, ashe ke kina nan kina mini tanadin mugun nufi."
Ya girgiza kai ya nuna kansa ya ce ni kika yiwa wannan iyashegen ko? Kuma dan munafunci da son zuciyar jama'a ayi ta faman cewa kina sona. Barin Sakina da har gorin soyayyar da kike yi mini take yi.
To ki ki saurari hukuncin da zai biyo baya.
Umma tana sake yi masa famfo, tana fa'da masa duk namijin da yake yiwa matarsa laulayin ciki to tabbas idan bai tashi tsaye ba ta gama da shi kenan, domin komai sai ta zartar irin wadannan matan sune matan jaraba, matar da zata saka namiji ya zagi uwarsa.
Wannan cikin na shiga tsananin kunci kala kala domin ya gasgata maganganun Umma. Mussaman da take yawan ce masa zaka dinga jin idan baka tare da ita ka shiga kunci ko gidan ya yi maka fa'din gaske da kuma kunci, to tabbacin an rubuce ka a allon karfe ne.
Kafin watan haihuwa ya tsaya na kumbura na yi sab'o sab'o ga haki tabbacin jinina ya hau.
Wannan haihuwar ma aka tabbatar ba zan iya ba sai dai a sake yi mini c.s.
Ku'din da ya bani na siyayya bai wani kai ya kawo ba. Ban yi korafi ba, domin fata nake na rabu da cikin lafiya. Komai zai biyo baya mai sau'ki ne.
Ranar 21 ga watan July aka sake fito mini da kyakkawar jaririya ta, katuwar gaske tamkar bata san taskun da nake ciki ba.
Gashinta sak irin na Gudale baki sidik har idonta dan sai da aka datse shi sannan take iya bude ido.
Tun tana jaririya ake fadin ni ta iyo sai dai ta kwaso abubuwa da yawa na Babanta.
Ban saka Gudale idona ba sai da na yi kwana uku da haihuwa a dalilin duk sadda zai zo ina barci.
A ranar da muka hadu din bai iya boye abin da yake ransa ba.
Ya tsaya a gabana ya ce mini "kin kyauta Guduyo bayan addu'ar jinya sai kika sake yin addu'ar ki yi ta jera mini mata, na sani kin ro'ki Allah hakan tunda lokacin haihuwar Amnah sai da kika tabbatar mini sai kin fara haifar mata.
To kije ki karaci mugun yancinki, tunda na gane harshen ki da dikon baki nake jin tsoron kalamin bakinki domin komai kika fa'da sai ya zama wajabat".
Na zuba masa ido ina mamakin wai menene matsalar Gudale ne?
Ni shaida ce babu jahilci ko na digo a tare da shi. Sannan a birni aka haife shi, ya kuma girma a cikin birni. Ya girma a tsakiyar zakwakuran masu ilimi da azanci. amma idan ya yi wani kalaman sai ka yi zaton wani sabon tuba ne da bai san komai a addini ba. Haka nan sai ka yi zaton bai ta'ba shiga aji da nufin daukar kowanne irin ilimi ba.
Kalaman sa idan yana cikin fishi ko abu ya zo masa ba yadda yake so ba, yafi dacewa da kalaman mutanan da basu taba shiga aji da nufin neman kowanne irin ilimi ba, mussaman wadanda suka rayu a karni na ashirin. Domin a wannan karnin na 21st century da duniya ta samu cigaba na ban mamaki ko mutum bai je makaranta ba, zai samu ilimin da zai fitar da shi a cikin duhun jahilci mussaman idan yana cudanya da masu ilimin.
Amma gaba'daya Umma ta taka muhimmiyar rawa wajen gurbata tunaninsa da kalamansa.
A hankali na ce "Har yau ba'a haifa maka 'ya'ya mata ba Yaya Sadik! Sai a gaba ma In sha Allah. Dan Allah ka nuna mini bolar yara mata. Ka dinga gode wa Allah wasu da yawa sunan suna neman haihuwar Ubangiji bai basu ba, ba dan ya manta da su ba, sai dan haka yake son ganinsu ya kuma gwada karfin imaninsu, domin Ubangiji baya kuskure. Amma kai ya baka, ya sake k'ara maka amma kana yi masa izgilin ba jinsin da kake so ya baka ba. To ni ina sonsu, ina fatan su zama tamkar su Antin Zaria matayen da sun zarta wasu mazan sau dubu, asalima da bazar su wani namiji yake taka rawa.
Ya kafe ni da ido ya ce " cabdi jam! Allah ya jikan ki Umma ba dan kin mutu ba. Na gasgata ki da kike fa'din Halimatu ba matar arziki ba ce."
Ya girgiza kai ya ce "Zaki san kin zage ni, zaki san kin ce mini mata sun fini anfani sune garkuwata. Yau duk zan tona miki asiri a gaban Umma! Zan fadi irin musguna mini da kike yi, zan fallasa irin tsananin ha'kuri da nake yi da muguntar ki".
Tsakin da ban yi da niyya ba ya subuce mini mai karfin gaske.
Ya ce "waton har Uwata ma baki bari ba? Kakar Amnah kika yiwa tsaki ko?"
Hawaye ya balle mini na ce "Duk abin da kake mini Allah na kallon ka ai. Na tabbatar idan na mutu a yau kai ne ka kashe ni. Tun ina da ciki kake gana mini azabobi daban daban, yau kwana uku bamu ga juna ba, ka zo ba sannu, ba komai ka tisa ni a gaba da cin mutunci da wulakanci ba ruwan ka da halin da zan shiga. Ba komai da sanin Allah ai"
Jikinsa ya dan yi sanyi ka'dan. Ya fice ba tare da ya ce mini kala ba. Yana fita Sakina ta shigo na dinga dabarar dauke hawayen idona. Ta dinga tambayar ba'asin kukan nawa. Na kasa bata amsa saboda har lokacin ina ganin ba karamin muzanci bane na fa'di halin da nake ciki da Gudale mussaman a gaban Sakina da ba irin togaciyar da bata yi mini ba.
Ganin da ta yi na hadiye kukan na kuma boye damuwar da nake ciki sai itama ta bar maganar.
Ashe tuntuni ya yiwa yarinya huduba da Saudat sunan Umma kenan.
Tun ina asibiti Sakina ta lankaya mata Afrah.
Goyon ciki da haihuwar Afrah yana cikin thought time din da bana manta wa domin wahala da wulakancin dana fuskanta a hannun Gudale. Har na gane ashe lokacin haihuwar Amnah da nake ganin bai yi wani zumudi ba, amma kuma yana dubata yana lekenta sannan da ta fara kwari yana daukarta duk kuwa da damketa yake yi. Ashe ba karamin kulawa da soyayya ta gani ba. Domin wannan yar ko kallon inda take ba ya yi. Na sani dan ya sake jefe mini takaici ne. Ya kuma ci riba domin akai akai nake share hawaye.
Yayin da shima yake cike da takaicin na yi masa addu'a ya mini laulayi mai zafi, sannan na bishi da fatan na haifi mace to na je burina ya cika. Sai na yi rainon ta ni ka'dai.
Ai ya yi tasa wahalar. Yanzu kuma sai na yi tawa. Dai-dai da pant bai kara akan kayan da na tsinto tun kafin haihuwar ba. Sai dai bani da matsalar kayanta tunda ina da sabbin kayan Amnah da bama ban bude ba saboda yadda take da kayan jarirai kamar na hauka.
Haka wannan din ma yan'uwansa da nawa sun baibaiye mu da da rigunanta da duk abin da zan nema.

Watan Afrah uku idan ka ganta sai ka zaci ta yi watanni biyar. Domin kuwa ta zama buleliya ga gashin Gudale ta debo yayin da shi kuma na Umma ya kwaso.
Ta zama abin so da sha'awa har tafi Amnah sha'awa saboda ita wannan mai jiki ce.
Shi da ya kudire ba zai nuna kulawa akanta ba, na sha ganinsa yana satar idona yana yi mata hotuna mussaman idan na shiryata na zaunar da ita cikin kekenta na koyon zama mai kyau. Matu'kar ina kicin ko daki ya dinga yi mata hoto kenan, ko ya kafe ta da ido yana murmushi, amma fa ba zai dauketa ba, ba kuma zai yarda ya yi akan idona ba.
Amnah kuwa tafi zaman wajen Umma domin idan abin nasa na kusa kuskure kadan zata yi irin na yaro zai cire tausayi ya zaneta da tsinken tsintsiyar kwakwa. Na sani kuma da gayya yake yin hakan sai ni kuma nake daurewa ko a fuska bana nuna takaicin da nake ji bare na tofa wata magana ya ci mutuncina.
Shiyasa ta fi son zama wajen Umma, tsoronsa take ji sosai.
Yayin da Umma take ji da su tamkar tsoka a miya abin kamar almara, ita bata ji takaicin haihuwar matan da nake yi ba.
Na taba jin tana fa'dawa kawarta ai Gudalena komai nawa ya debe shi, hatta haihuwar mata a farko, ga yaransa nan lafiyayyu kyawawa. Kuma abin burgewa jininsa yafi yawa a jikinsu.
Ko wannan mai sunan nawa da ake ganin kamar uwar a jikinta ai dan dai tana da garin jiki ne, amma haka na yi goyon Yayar su ta Zaria katuwa tana rinjayata.
Addu'ar da nake yi musu kada Allah ya sanya nono yayi tasiri akan su. Su gado nunkufurci da wuyar zama."
Kawar tata dake itama hamshakiya ce ba wai yar fadanci ba ce, domin itama nata mijin ya tumbatsa da arziki. Kai tsaye ta ce " Ai kuwa tasirin nonon uwa a wajen danta dole ne. Kamar yadda kika yi tasiri akan ubansu haka suma tasu uwar zata yi. Kawai a cire son zuciya a masu kyakkawar tarbiya a barsu kuma suga girman uwarsu, domin duk wahalar da zaki yi dasu dai, ba ke ce uwarsu ba. Wataran ma sai su iya nuna miki waccan facalar ta ki, tafi kima a wajensu saboda tasirin nono. Kar ki shiga shirginta da ya'yanta domin har abada d'a mallakin uwarsa ne".
A sanyaye Umma ta ce "Na jiki kuma zan kiyaye, sai dai nima har abada bana sonta, ba kuma zan so ta ba."
"Kar kice haka domin baki san me gobe zata zo miki da shi ba. Ki daina damuwa k'awata".
Jin motsin zasu fito ya sanya na yi azama na zagaya na bace dan kada ta ce ina yi mata labe.
Tun a ranar na sake ganin girman Hajiya Bilki domin tun fil'azal bata yarda da son zuciyar Umma zata fa'da mata gaskiya sai dai ba kasafai take dauka ba.
A wanna tsukun na samu offer aiki da asibitin Malam.
Sosai na yi murna domin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login