Showing 42001 words to 45000 words out of 180068 words
kuwa Iyah Basiru ta tabbatar kayanta amintattu ne, Shiyasa *G.H.T* suka karramata*.
*07039269802*.
*Dakin Umma*.
Sai da ta idar sannan ta kalle shi ta ce "Menene kake ta faman huci tamkar marar lafiya".
Cikin karaya ya ce "Abba ne! Ummah Abba ya kassara ni, wai aure zai yi mini, sannan ya rasa wacce zai bani sai wannan kumburar yarinyar dan kawai yana son sai na dauwama cikin firgici".
Hawaye ya 'balle masa. Yayin da Umma ta fashe da kuka mai sauti.
Sosai take kukan tunda ga 'kasan zuciyarta, ta jima tana yi, hakan ya sake kassara Gudalenta, nasa hawayen da yake yi ya tsaya cak.
Ya rarrfo ya isa gareta, ya ru'ko hannuta ya dinga rarrashinta cikin tarin soyayyar da babu algus.
Ta kalle shi ta zuba masa ido ta ce "Na jima ina yiwa matarka tanadin soyayya marar iyaka, na jima ina dakacen zuwan matarka domin ba zan yi surukunci da ita ba, zan mayar da ita tamkar su Ramla ne.
Ashe ashe ba zanga hakan ba, Ashe wacce ba'kin cikinta zai dangana ni da kushewata zaka aura, Ashe dai da gaske Safiyya na haifarwa kai?"
Ta 'karisa cikin kuka har da 'kwarewa.
Shi kansa ba ya son auren, amma bai ji tashin hankali kamar wanda ya kula Umma na ciki ba, 'kasan ransa sai hasaso 'kirjin Guduyo yake yi, ya jima yana fatan ya samu damar da zai gansu a zahiri.
Amma bai ta'ba hararo ta zamo matarsa ba, duk kuwa da yana damuwa da lamarinta, ya tsani ya laluba gidan bai ganta ba, ko da kuwa ba zasu yi maganar arziki ba. Da kansa yake tambayar kansa menene manufar hakan? Menene dalilin da yake Jin fargaba idan ya tuna zata yi aure?
A hankali ya ce "Kin ta'ba ganin an 'kwacewa uwa 'danta Umma?"
Da sauri ta ce "Na sha gani yafi sau dubu".
Ya sake ri'ke hannunta sosai ya ce "In sha Allah! Ban da ni Ummah! kuma yanzu zuba ido zaki yi a kwace miki ni?"
Cikin kuka ta ce "Ina ce Abbanku ma an kwace mini shi bare kuma kai da komai naka zai koma karkashin kulawarsu, ai ni kuma tawa ta 'kare. Sai dai na yi fatan Ubangiji ya baka ikon yi mini addu'a bayan na kwanta dama. Amma batun zan ji da'dinka ai na cire rai. Tunda ka ha'da kai da Ubanku zaka auri irin jaraba, irin raba zumunci, irin ja'iran bayi masu kwana a tafe, duk sammakon mutum sai dai ya tarar da haular su Safiyya sun riga shi".
Duk ru'danin da yake ciki sai da ya ji tamkar ya yi dariya.
Amma ya sani idan ya yi dariya yana nufin ta sake 'karfafa zarginta ne.
Dan haka ya gintse ya ce "To ki yi duk abin da zaki yi dan auren nan ya sau'ka daga kaina, kin sani Ummah Yan lukatayen mata basa burge ni, bana son su. Ki fa'dawa Abba bana so, ya riga ya daure ni da jijiyoyin jikina ne. Saboda ya ce su Abdullahi basa ta'ba yi masa musu, sun yarda ya isa da su. Shiyasa na kasa yin bore mai yawa a gabansa. Amma a zahiri an 'kuntata mini iyaka".
A fusace ta ce "Yo ai biyayyar yaudara ce da tuggu, biyayya ce irin ta bani manda na baka gishiri.
Da ace bashi da arziki sai ya yi sati ma basu zo sun gaishe shi ba, bare kuma aje ga jallin zai zartar da hukunci a kansu ya zartu. Ta yi 'kwafa! Tare da cije yatsanta alamun dai tana cikin takaici mai tsananin gaske.
A marairaice ya ce "ya zan yi ne Ummah? Bana sonta Wallahi".
Ta nisa ta ce "Aure dole za'a yi shi, tunda ya ce idan har ka bijire masa ni ce.
Dan haka zaka karbi aure! Amma idan har kana kishina kar ka sake ka shiga harkarta! Kar ka bari a zauna lafiya! Kar ka ta'bata, domin kuwa tabbas zata gado saurin haihuwa a wajen uwarta, tunda sun ga da maiko haka zata yi ta haihuwa ratata kamar da gayya dan kawai a tabbatar an gama da kai. Ka yi ta cusa mata ba'kin cikin da zata barka da kanta, daga nan sai kawai ka sallama musu ita, ta dawo gaban uwarta, mai tsautsayin daukar kara da kiyashi sai ya kwasheta shegiyar yarinya makira irin jaraba.
Me za'a yi da zuri'ar gidan mai Ashafa, masu karyar malumta suna yin 'kulunboto. Har abada ba zan so ta ba tunda har cewa ya yi idan har na bada matsala sai dai mu bar masa gidan ni da kai.
Idan komai ya lafa sai ka samo zabin ranka Yar shawalwala da zaku da'de bata tsufa ba, irin zuri'a da suke da yakana da adalci".
Ya amsa da cewa "shikenan ki kwantar da hankalinki duk yadda kike so hakan zan yi miki, nan duniya ba abin da nake so irin ki, ina sane da tarin soyayyar da kike yi mini, na san irin tattalin farin-cikina da kike yi. Dan haka zan yi komai dan na sanya ki cikin nutsuwa ko da hakan na nufin bacin ran wasu ne".
Wani irin Da'di ya mamayeta, ta hau murmushi tana cewa "Hankalina har ya kwanta, amma ka dage da addu'a sannan ina farin-cikin yadda ka yi fatali da ita a tsukun nan, ina fatan ka sake ninkawa".
A hankali ya ce "Ni yanzu da ta shigo dakin nan ma ji na yi tamkar na yi mata 'kamshin mutuwa kawai tsabar takaici".
Da sauri ta ce "A a Gudale banda shake wuya, kawai dai wulakanci da kankancin da aka san namiji da shi zaka fara nazarin su dan ka yi bitar su dallah dallah amma ban da duka. Masharanntan halittu ne, yanzun nan sai su burma mutum ya kwana a ciki".
Ya nisa ya ce " To na ji! Amma ki kwantar da hankalin ki! Ta yadda nan gaba ba za'a zarge ki ba".
Ta sake murmushi ta ce "Ashe dai Gudalen nawa akwai dabara! Zan ajiye komai, zan bar shi a zuciyata, duk da kuma ba zan iya nunawa lamarin soyayya ba".
Da sauri ya ce "dama Ina nufin kar ki bari kiyayyar ki da lamarin ta bayyana a siffarki ko ayyukanki.
Tsawon lokaci suna tare suna tattauna makomar auren.
****
Murnar da nake ciki sai da ta bayyana kowa ya gane ina cikin yanayin da yayi mini da'di.
Mama ta dinga tambayar menene ya sanya ni wannan nisha'din haka?
Sai kawai na yi murmushi na ce "Ba komai".
A daren aka yi rasuwa a Moriki matar Baba Yakubu 'dan-uwan su Baba ne da suke first cousins.
Sassafe aka shiryawa Mama da Umma da kuma Yayar 'Kwalli tafiya yin TA'AZIYA, bisa jagoranci Yaya Al'amin yayin da jibi, Yaya Abbas zai kai su Abba.
Baba ne baya Jin da'di shiyasa Abba ya ce matan suje.
Bana manta wannan tafiyar saboda yadda ta yamutsa hazo.
Bana wajen amma Mama ta bani labarin har na ji tamkar ina wajen.
A hanya suna tafe ana hira, kusan dukkan hirar Umma gugar zana take yiwa Mama.
Mafi yawa Mama kuma bata iya bu'de baki ta mayar mata da marta ni ba.
A hanyar dawowar sune abin ya faru, tun tafiyar bata yii nisa ba Umma take ta faman cewa "Oh Allah ya ji'kan Rahamu! Yar gata da ita, uwar ya'ya mata, ki gansu reras sun cika 'dakin, ya'yanta mata shida aurararu ance har kansilan garin ma surukinta ne.
Wanda Àllah ya bawa yaya mata ya karrama shi ba ka'dan ba.
Tausayi da jin kai ai sai wajen mata, ga tarin falalar da zaka samu aljannah ta dalilin Yaya Mata uku bisa sharadin ka raine su, ka tarbiyantar da su cikin adalci da kamewa har zuwa aurensu.
Annabi ya ce Aljannah ta tabbata ga wadannan iyaye.
Amma ban taba jin falalar haihuwar 'ya'ya maza ba".
Yaya tana budi baki sai ta ce "Ai kinsan tun a jahiliyya ba'a son haihuwar ya'ya mata saboda ana jingina musu rauni, ana ganin wahala kawai ake yi da su babu riba, domin ana aurar da su, shikenan wanine zai more su. Amma 'ya'ya maza fa? Garkuwa ne a ko ina, sannan duk runtsi dai suna nan a gida, za kuma suyi kowanne irin aiki dan su nemo".
Da azama Umma ta ce "idan sun kasance jarumai ba, domin dai wasu ai gara matan da su tunda zuciyarsu a mace take. Mace imaninta yawa ne da shi, abin burgewa ta janyo maka surukuta da manyan mutane masu mulkin kasar".
Duk da Mama ta san jirwaye take yi mata, bata sanya musu baki ba.
Sai da aka koma hirar Yaya Al'amin da Yaya Sadik.
Nan ma Yaya ce ta canja hirar saboda ta lura janye janye magana Ummah take yi.
Dan Haka sai ta ce "Wai ya ake ciki kan maganar auren 'Ya'yan naki ne Safiyya?"
Da mamaki Mama ta ce suwa kenan?"
Abbas da Aziza mana?"
Ta yi murmushi ta ce "Yaya ai Babanta ya ce zai bashi! Amma sai ba'di sannan zai kammala shirinsa, kinsan hidimar aure da yawa abin ka da masu 'karamin karfi dole a shirya a hankali".
"Hakane kam domin kowa yana jin yau din nan"
Yaya ta fa'da a gaggauce.
Sai kuma ta sake cewa "wadannan mashiriritan nan Al'amin da Sadik, da alama sai an nemo musu dan ban ga alamar suna da 'yanmata ba. Jiya na gama yi da Ashir zan laluba na samo masa yarinyar kirki, ya dinga dariya yana fa'din kar na soma".
Murmushi Mama ta yi tare da cewa "Ni bana biye ta wadannan, Ni ta auta nake yi."
Yaya ta ce
"Yo Halima ba ta tsaya ruwan ido ba, ai idan Abbansu ya gaji da bata dama sai da taji ya yi mata miji".
Da sauri Mama ta ce "Da ya yi mini maganinta wallahi!
Sadik da Al'amin ai ko zancen aure basa yi shekaranjiya da daddare fa da kin ji yadda suke musun wa zai zama shugaban kasa, wa zai zama gwamana a tsakaninsu sai ki zaci yara ne kananu.
Sai da na gaji na ce da Al'amin tunda Kaine babba sai ka barshi ya fara za'ba.
Sadik ko ya ce shi president zai zama, yayin da Al'amin ya hakura zai zama gwamanan. Na dinga dariyar su tamkar dai an tabbatar musu sune 'yan takara saboda yadda suka dage suna cece kuce.
Na biye musu har ina hango kaina na zama uwar shugaban kasa, kuma uwar Gwamna".
Yaya ta dinga dariya tare da cewa "kema shiriritar ki yawa ce da ita. Allah ya biya bakin ki to".
Umma ta cika ta yi fam saboda zuciyarta ta kitsa mata ai da gayya safiyya ta yi wannan maganar domin tana son ta sanar da ita idan Gudale ya zama shugaban kasa ita kuma ta zama surukar president, sannan ga 'danta zai zama Gwamna.
Wato izgili take yi mata. Hakan ya sake zafafa Kiyayyar auren a zuciyarta alhalin har lokacin Mama da Baba Basu san maganar auren ba, bare har ta yi mata
Suna dawowa ta zaunar da Gudale ta ce "Ko na mutu ban yarda ka yi siyasa ba".
Ya yi Dan murmushi ya ce me zan yi da siyasa? Allah na tuba".
A kausashe ta ce "Safiyya ce ta mini habaicin zata zama surukur shugaban kasa, ni kuma idan ina raye ba zan so hakan ba, dan hakan kar ka yarda ka shiga harkar siyasa halaka ne, kar ka yarda ka dauki hakkin da ba zaka iya sau'ke shi ba. Domin mulki al'amari ne mai wahalar wa".
A fili Gudale ya ce "Ki tsananta addu'a Ummah! Ki nemawa kanki tsari daga sharrin shaidan da na hassada.
Mummunar dabi'a ce da take ruguza komai".
Kuka sosai ta fara yi har da gunji, kuka na zallar bacin rai, yafi kama da kuka irin na kaicon yadda 'kaddara zata bawa Safiyya damar yin suruki da Gudalenta.
Ya dinga lallashinta da cewa "Ban da abin ki Umma ina ce idan na zama shugaban kasar ke kuma kin zama uwar shugaba, sannan auren ai ba nisan kiwo zai yi ba. Bare ki yi ta bacin rai a banza".
# Team Gudale.
# Team Guduyo.
# Surayya Dee.
# Ana tare🤝.
2/8/23, 10:22 - Buhainat: *Wannan littafin na ku'di ne, biya 500 ku'din karatu ta wannan asusun*
*2384876855*
*Surayya Ibrahim*
*Zenith Bank.*
*A tura shaidar biya ta wannan lambar*
*08032773332*.
*Kun san za'kwa'kurar jakadiyar G.H.T.?*
*Tana gyaran amare*
*Tana da bada amintattun supplement din da yake dagargazar sanyi*
*Tana da supplement din da yake zai-zaye kitse, ya ke fidda zahirin surar mace*.
*Tana da wanda yake ha'de mace ko ta fara manyata kuwa.*
*Fasilat tana da komai na wannan bangaren har da na ulcer da basir, Wanda basu da illah a lafiyarmu*.
*Haka tana da wanda yake saukar da ni'ima da sanya 'dumi a jikin mace*
07039269802*
*Gudale ya ce a nemo zakwa'kuran masu Gyaran amare su gyara masa Gudidi*
*Na kuwa samo wanda na gamsu na kuma amince da kayayyakin su*
*Dan haka kuma ku zo ayi muku naku gyaran domin kuwa Tested and trusted ne*🥰
*SDK29-30.*
Da 'kyar ya lallaba ta ta yi shiru. Ya fita yana mamakin tsananin 'kiyayyar da take yiwa Mama.
Tare da ta'ajjibin yadda mata ba sa raina 'dan karamin abu, su yi ta kambaba shi ta yadda zai zama 'katon laifin da zai yi sanadin damalmalewar al'amura masu yawa.
Sai bayan su Abba sun je Moriki sun dawo. Sannan ya sanarwa Baba da Yaya ya yanke hukuncin aurena da Sadik nan da lokaci ka'dan.
Dukkansu ba wanda ya yi inkarin hukuncin nasa, duk da sun san akwai na'kasu a tare da Sadik.
Murna suka yi da fatan alheri, mussaman Babana.
Yana dawowa gida ya tarar da ni tare da Mama muna kicin muna jefa 'Dan-wake.
Daga bakin 'kofar ya tsaya ya ce "idan kun kammala ku zo akawai maganar da zamu yi".
Muka kammala aikin cikin wasi-wasin maganar da za'a yi.
A nutse ya ce "Alhaji ne ya zartar da hukuncin auren Halima da Sadik nan da wattanni biyu. Na sanar muku, dan ku sani, ku bi lamarin da addu'a".
Wani irin farin ciki ya mamaye mini kalbi, yayin da Mama ta sunkuyar da kai 'kasa tana jin 'kunan rai.
Ta dago idonta da ya cika da 'kwalla ta dubi Baba ta ce "Baban Ammar anya wannan lamarin zai yiwu kuwa?
Ummansu ba zata so wannan ha'din ba. Ina jin tsoron abin da zai biyo baya, gaskiyar magana maganin kar ka ayi, kar a soma."
Da 'bacin rai ya ce "wato kina son ki ce mini na nunawa Alhaji bashi da iko akan 'yar da na haifa?
Kina son na nuna ina 'kyamar bawa tilon 'dansa aure alhalin duk matan duniya bai ga wacce ta dace da 'dansa ba sai tawa ' 'yar.
Wato kina son ki ruguza mana zumunci? ita ai bata iya tarar gabansa ta nuna bata so ba, tunda ta sani yafi karfin ta.
Amma ke da yake kin raina ni, kin tari gabana kin fa'da mini akan idona".
Ya numfasa ya ce "Sai dai ki sani shure shure baya hana a yanka dabba, haka nan *sabo da kaza* baya hana a yanka a cinye. Wallahi akan wannan maganar zan sassaba miki fiye da zaton ki! Mutuwar Halima ko ta Sadik ne zai sa a dakatar da auren nan, amma ko ke ce kika mutu ina tabbatar miki ba za'a fasa
ba".
Na sake yin kasa da kaina, ina jin rashin da'din yadda Baba ya fusata yake ta fa'da ba sassautawa.
Amma a 'kasan raina ina goyon bayansa na kar ya yarda ya bi maganarta ayi mini ta le'ko ta koma.
Da rawar murya ta ce "Baka fahimce ni bane, amma ka yi hakuri. Akan me zan 'ki Sadik? Har zuciyata ina sonsa, uwarsa nake ji. Amma na barwa Allah ya zame mata jagora a hannunsu".
Jikina ya yi sanyi, yayin da Abba ya ce 'yanzu kika yi magana".
Da hakan na tashi na barsu.
Sai da Baba ya fita, Mama ta shigo ta same ni a dakina ta zauna kusa da ni, ta ce mini "Kina ta rawar jiki, akan wannan ha'din. Ban yi zaton son da kike yiwa Sadik ya girmama haka ba. Tunda kika taso kike ganin tsana 'karara a idon uwarsa. Kullum a can kike kwana, amma abincin da zata baki ki karya yafi karfin ki sai idan akan idon Abbanku ne.
Har yau da kike cikin shekaru ashirin ba zaki tuna me ta yi miki na kyautatawa ba, ba kuma komai kika yi mata ba, laifina ne ya shafe ki.
Amma har kike murnar ki zamo surukarta, anya kinsan jidalin da mace take fuskanta idan ta ha'du da kiyayyar uwar miji?"
Na yi 'kasa da kaina ina jin rauni, na kasa magana saboda gaba'daya na rasa me zan ce.
Sai da ta yi waiwaye dan ta tabbatar ba wani a kusa da mu.
Ta ri'ke hannnuna ta ce "ki fa'dawa Abbanku baku shirya da Sadik ba. Idan ya nemi Jin ta bakin ki, ina tabbatar miki baki dace da shi ba, nutsuwarsa ba mai yawa ba ce, ko ni da kika ga baya taya uwarsa yin gaba da ni, dan yana morata ne, da kuma shakuwa. Amma ai kinsan yadda ta tsananta sonsa, ta kuma dora dukkan buri akansa. Ba zata so ki ba, ba dan komai ba sai dan nice uwar ki. Shima kuma ba zai zabe ki ya bar uwarsa ba. Idan kika kafe sai shi, ina tabbatar miki zaki yi rayuwa ne mai tattare da takura da tsananinl, fiye da wacce nake fuskanta a wajen ta. Kina gani dai ba irin wahalar da ba na sha a hannunta har yau, Abin kaicon kuma bamu ha'da miji ba, ba kuma uwar miji ba ce. Amma har yau din nan ina rayuwa ne cikin zullumi saboda masifarta. Shin so kike abin ya yi mini yawa? Ga bacin ran da take cusa mini, sannan kuma na fara tararrabin damuwar da kike ciki".
Na yi shiru! Tsawon lokaci ina tunanin mafita. Gaskiyar magana ban ji zan iya cewa na fasa ba, domin ni ka'dai nasan yadda nake jin Gudale a raina. Duk sallah kafin na ro'ki komai sai na ro'ki Allah ya sanya na zama matarsa, sai da addu'a ta amsu sai kuma na yi wasarere da cikar burina akan wani dalilin da bashi da tushe.
Jin na yi shiru ya sanya ta fahimci ba zan yi abin da take so ba.
Ta sake ri'ke hannnuna sosai ta ce "Halimatu ba zan so ki nace akan wannan auren ba, kar ki kafe, ina jiye miki tsoron fa'dawa tarkon da ba zaki iya subucewa ba".
Nan ma na yi shiru! na 'ki yin magana.
Ta mike ta ce "Na fa'da miki gaskiya tunda kin biyewa burin zuciya ai shikenan,