Showing 72001 words to 75000 words out of 180068 words

Chapter 25 - Sabo Da Kaza By Surayyah Dee

18 Dec 2025

8757

nake bu'katar ganin ba".
"Na mi'ke din amma a zuciyata na kudire idan har ni zan nuna masa, Wallahi ba zai gani ba.
Duk maganar da ya yi baisa na bu'de ba.
Ya hassalo ya ce "Anya kuwa Sadiya zaki yi albarka?
Mijin da sai ya 'daga sawunsa zaki rabauta kike yi wa wannan gadddamar?"
Cikin rawar murya na ce "ka ji tsoron Allah! Wacce irin amarya ka dauke ni ne?"
Hawaye ya balle mini.
Jikinsa ya dan yi sanyi ka'dan.
Ya taso ya same ni inda nake tsaye.
Ya ce "Da ga maganar fatar baki zaki dinga yi mini kuka?
Kuma yanzu ya kike so na yi da rantsuwar da na yi akan sai na ga ni?"
Na yi kasa da kaina na kasa bashi amsa.
Ya sanya hannunwansa ya yi sama da rigar, da kyar ya samu ya fito da su, ya dago ya kalle ni ya ga na yi kicin kicin da fuska tamkar an fa'da mini sakon mutuwa.
Ya koma ya zauna yana cewa "kar ki sauke rigar nan".
Sai da ya gama kallonsa har ya gaji.
Sannan ya numfasa cikin dakushasshiyar murya marar amo ya ce "you can sit down".
Maimakon na zauna a falon sai kawai na juya zuwa dakina, ina tafe ina gyara rigata.
Yayin da shikuma ya shiga wani irin al'amari mai wahalar gane wa.
Washagari da safe sai da na kammala aikin gyara gidan sannan na soya Samomsa na dafa shayi.
Na karya, na shiga wanka.
A gurguje na shirya. Kamar jiya haka na nufi dakin oga Gudale".
A zaune a tsakiyar gadon na same shi.
Na gaishe shi, ya amsa ciki ciki.
"Na kammala".
Haka kawai na fa'da ya hayayyako mini.
"Ke dai Guduyo hankalinki a sama yake wallahi. Ace wai baki iya komai ba, sai dafa abinci da fita sassafe! Baki san me zaki yiwa mijinki dan ki samu yardar mai duka ba?"
Na yi jigum ina kallonsa da dukkan idanuwana cike da mamaki na ce "ka dai so ce mini bani da hankali ne kawai amma banda haka menene bana yi maka?"
Ya girgiza kai ya ce "Yi tafiyar ki kawai"
Na marairaice na ce "Kudin mota".
Ya zuba mini ido ya ce "kina nufin ba ku'di a hannunki?"
Kai tsaye na ce "Babu".
Nam ma sai da ya gama hargagaginsa na an cuce shi.
Ban tanka ba ya zaro 'dari biyar ya bani.
Har na kai bakin 'kofa ya ce "idan kin dawo 'Danwake zaki yi mini".
Na ce "Tom".
Na fita ina ayyana yau ban samu arzikin rakiyar ba kenan.
Ashe shi yana cikin halin son kasancewa da ni, amma ba damar hakan tunda bai yarda yana sona ba, bayan haka Umma bata son hakan ya kasance a tsakaninmu.
Da na dawo na shirya masa 'danwaken, domin ina da dakken yaji mai da'din gaske.
Ya ci iya cinsa, amma ya kasa yaba mini, bare ya ce thank you.
Na tuna mijin Sakina komai ta girka masa sai ya ce Na gode. Bare kuma a ce shi ya zabi abin da za'a yi masa.
Ya dinga yabawa tare da godiya.
A haka muke gungurawa, zaman ba wani fahimta a cikinsa har muka cinye kwanaki wata.
Ranar asabar bana mantawa ya sanar mini zai je Lagos jibi, zai yi kwanaki biyu zuwa uku.
Duk da ba wani da'di muke yi ba, sai da na ji gabana ya fa'di, na tsinci kaina a cikin rashin Jin da'din tafiyarsa.
Da ace na samu fuska a wajensa cewa zan yi zan bishi, to ina.
Na yi masa addu'a.
Abba kuwa ticket din jirgi ya siya masa.
Farko so ya yi mu tafi tare, amma Gudale ya bada uzzirin zan samu gibi a karatuna tunda ba a weekend tafiyar ta Fado ba.
Na yi masa cincin da dambun nama masu dama tamkar wanda zai kai wata.
Da zamu yi sallama ya zuba mini ido sosai ya ce "Ubangiji da kansa ya shimfi'da dokokin aure. Dan haka har zuwa ranar da zaki gaji da zama a karkashin ikona wajibi ne ki yi mini biyayya, ki kuma kiyaye mini amana".
Daga haka ya ja akwatinsa ya fice ba tare da ya bani damar cewa 'kala ba.
Na bishi da Ido, a hankali na furta "Allah ya dawo da kai lafiya.
Na koma daki ina jin hawaye na cika mini idona.
Na kalli kudin da ya bani, ban 'kirga ba amma na sani zasu kai dubu goma.
Tunda ya tafi ni dai bai Kira Ni ba.
Ni kuma da na kira ma layin a kashe ban same shi ba.
Ban kawo komai a raina ba, amma na matsu na ji muryarsa, na matsu na ji halin da yake ciki. Duk yadda ya nuna mini rashin soyayya, tawa zuciyar sonsa take kamar me.
Addu'a nake ba kakkautawa Allah ya karkato mini da hankalinsa kaina, mu yi zama mai cike da soyayya da mutuntunta wa.
Daga tafiyar kwana biyu ko uku sai gashi an shafe kwanaki goma an doshi sati biyu.
Juma'a biyu kenan da tafiyarsa, sai Abba ya shigo ya duba ni da yamma.
Ya tambaye Ni ko muna waya da Sadika.
Na ce "Tunda ya tafi bamu gaisa ba". Ganin da Abba ya yi zan rikice ya sanya ya ce "lafiyarsa fa kalau, ya kira ni sau biyu, amma ba da layinsa ba."
Na dan ji da'di ka'dan tunda lafiyarsa Lau.
A hakan sai da aka shafe kusan wata biyu bai dawo ba, bai kuma neme ni ba.
Ni kuma na gwada kiransa ya fi sau cikin buhu.
Amma kwatakwata layin ba ya shiga.
A wannan lokacin ne raunina ya fara bayyana, mussaman da na fara fahimtar kalamansa da ya ce har zuwa sanda zan gaji da auren sa.
Kenan guduwa ya yi ya bar ni?
Idan na gaji sai musan yadda zamu yi ni da Abba.
Karatu da rashin nutsuwar da nake ciki suka sanya ni a gaba, na fara ramewa a tsaye.
Dan ma na yi sa'a mayuka na zababbu ne ko a cikin oriflame 'din ma latest ne.
Shiyasa ban yamushe ko 'bacin rai ya sanya na yi duhu ba.
Bana gajiya wajen yiwa *Aisha lame* jinjina, a kullum bansan adadin matan da suke tambayar lambar wayarta ba dan fatarsu ta yi kyau da taushi irin tawa to.
A wannan lokacin kowa ya ganni sai ya tanka ramar da na yi.
Kowa sai ya tambayi anya lafiya nake kuwa?
Amma sai ba'a wani damu ba, aka yi ta jingina mini ciki ne yake wahalar da ni.
Wata juma'a da Abba ya zo gani na, na kasa boye damuwa ta na yi ta kuka mai ta'ba zuciya.
Tsawon lokaci bai katse ni daga kukan ba.
Sai da na yi shiru dan kaina. Sannan ya numfasa ya ce "kara ha'kuri Halimatu! Komai zai wuce ya zama tamkar ba'a yi ba.
Hakan da Sadik ya yi ba ni ko ke ya tozarta ba. Da sannu zai gane kansa ya yi wa".
Ya zarce da yi mini nasiha mai shiga zuciya, ya kuma sake jaddada mini ba wanda ya yi hakuri bai ci ribar rayuwar nan ba".
A haka na cigaba da zama cikin ha'kuri da juriya, na kuma gane tabbas aurena ne baya so shiyasa, ya yi hakan saboda haka nima sai na mayar da akalar addu'ata wajen Allah ya yi mini za'bi.
Duk da a 'kasan zuciyata nafi son ya sauko, ya karbi auren da dukkan zuciyarsa.

*Ummma*
A dakinta take tana gyara wardrobe dinta.
Misalin 'karfe karfe uku na yammacin laraba.
Kamar daga sama ta ji sallamarsa ya shigo mata daki.
Ta zuba masa ido sosai.
Yayin da shi kuma yake sosa kansa alamun kunya da rashin gaskiya a tare da shi.
A hankali ta ce " Gudale"
Kafin ya amsa ta zarce da cewa "ko wata uku baka gama rufawa ba har ka dawo?
Haka muka yi da kai?"
A hankali ya ce "Umma na kasa jurewa ne, kullum na kwanta mafarki nake yi marasa da'di, bani da nutsuwa ko ka'dan, ina jin tsoron hukuncin da Abba zai zartar".
Ta yi kasake cikin son nazartar sa.
A hankali ta ce "Kana nufin ka amince zaka zauna da kinababbiyar yarinyar nan?
Kana nufin zaka ha'da mini jinina da haular gidan mai Ashafa?"
A dunkule ya ce "To ya zan yi? hakan na cikin 'kaddarar da bazan iya kauce mata ba. Ki yi hakuri ni kai na a cikin takura nake, amma Fishin Abba nake guje Mana, mussaman matakin da zai iya dauka akan ki. Ina matu'kar kyamar na zame miki dan kuka mai janyo wa uwar sa jifa.
Cikin rawar murya ta ce "Sun yi galaba! Su je sun samu, na sani a yanzu ma ba a hayyacin ka kake ba.
Kiran ye suka yi maka.
Oh ni Saude Ubangiji ka mini maganin abin da ba zan iya yiwa kaina ba. Allah ka mini maganin wadannan halittun masu mtofi a cikin kulle kulle, masu rubuce sunan namiji a allon karfe".




02-11-22.


# Team Gudale#
# Team Guduyo#
# Surayya Dee ✍️
# Ana tare 🤝.
2/8/23, 10:25 - Buhainat: *Wannan littafin na ku'di ne, biya 500 ku'din karatu ta wanannan asusun*
*2384876855*
*Surayya Ibrahim*
*Zenith Bank.*
*A tura shaidar biya ta wannan lambar*
*08032773332*.


*SDK*
*47-48.*

Cikin rarrashi ya ce "A cikin nutsuwa nake Ummah! Ba abin da aka yi mini".
"Yo dama ina zaka fahimci surkullen su?
Kawai dai na barsu da Allah! Ban da haka ta ina ka dace da Halimatu? Yarinyar da ta tsotsi nonon makirci da shiga tsakanin tsaftacciyar soyayya, masiffafun mutane gadan jaraba".
Ga mamakinsa sai ya ji kalaman Umma ba su yi masa da'di ba. Domin idan ya ce ba kewar ta ce ta dame shi ba ya yi 'karya. Hakanan dawo wa ya yi dan ya sauke abin da ya dame shi akan ta.
Ya mi'ke yana cewa ki daina damuwa! Nan duniya ba abin da ya fiki daraja a waje na. Sannnan ba abin da zai shiga tsakaninmu".
Cikin karaya da zallan bacin rai!
Ta ce "Kayyah".
"Abba yana gida ne?" Ya tambaya, nufin kauce wa maganganun ta.

"Eh yana nan"
Ta bashi amsa a gajarce.
"Umma mu je ki raka ni, gaba'daya a tsorace nake! Sai yanzu nake ganin ban kyautata masa ba".
Ta tabe baki ta ce "Ai shi kana jin tsoron fishinsa! Ka damu da bacin ransa. Amma ba ruwan ka da halin da zan shiga a dalilin rashin dace da suruka. Wai Halimatu zaka zauna da ita? Buskutar yarinya da nake fatan ta fadi ta ji ciwo a kashin kafarta ta yadda kafin likita ya samo 'kashinta ya yi mata dori ta na'kasa ta zama gurguwa."
Ya mi'ke ya dafa kafadarta a hankali ya ce "Ina rantse miki da girman Ubangiji ba matar da zata wula'kanta ki na zauna da ita.
Ba matar da zata zame miki barazana. Ban sallama ta ba, ki amince da Gudalenki Umma".
Ta saki ranta ka'dan ta ce "je ka dai, yanzu sai ya ce "Da sani na ka 'ki dawowa da wuri, ba kuma ka kirashi a waya ba, tunda ya da'de yana mini shaguben ya san kana kira na".
Kan dole ya nufi falon Abban.
Ya same shi a zaune kasan kafet gabansa manyan littafai ne birjiki, da alamu suka nuna yana wani nazari ne.
Ga mamakin Gudale da fara'a saosai Abba ya yake masa barka da zuwa tamkar dai ba laifi ya yi ba".
Ya zama wani iri saboda yadda Abba ya kashe shi da kunya.
Suka gaisa lafiya lau.
Abba har tambayarsa da fatan ya samu Nasara a tafiyar da ya yi.
A sanyaye Sadik yake amsa masa.
Abba ya sake cewa "Har ina tunanin ya za'a yi da interview din da zaka yi a F.I.R.S. Sati mai zuwa ashe ka samu labarin".
A hankali Gudale ya ce "ban ji ba, kawai na dawo ne, na ga zaman zai yi yawa".
A gajarce Abba ya ce "Madallah".
Da kyar ya mi'ke ya fita saboda jikinsa yana bashi Abba dungu ya yi masa.
Ba laka a jikinsa ya yi sallama da mahaifin nasa ya nufi gidansa.

******
Ina kwance a kujera mai uku ya turo, ya shigo. A farkon na yi zaton gizo yake yi mini.
Sai da ya shigo janye da akwatin kayansa na tabbatar ba gizo bane.
Ko motsi ban yi ba, bare na tashi.
Ya jima yana kallona, murya a bude ya ce "Baki gan ni bane?"
Cike da rashin damuwa na ce "Na ganka mana! Sannu".
Ya wuce janye da jakarsa sama.
Sai da ya yi wanka, ya fito zuwa masallaci.
Bai bata lokaci ba ya dawo.
Ya jima a falo yayin da nake dakina kan sallayar da na idar da sallah, amma ban tashi ba.
Ya shigo ya zauna a bakin gado.
Karon farko da ya shigo dakina ya zauna tunda na je gidan.
Na kammala na ninke su, na fice na bar shi a ciki.
Ina zama a kujera ya karaso a fusace.
Cikin fishi ya ce "Amma kin san bana son a tashi a barni ko?"
Kai tsaye na ce "Na gama uzzirin da nake yi ne. Ban sani ba ko baka gama abin da ya kai ka 'dakin ba".
Ya hassalo sosai, amma ban san dalilin da ya sanya, ya bar maganar ba.
Ya zauna ya ce "Sammin ruwa na sha! Idan da abinci a taimake ni da shi".
Ban ce komai ba na tashi na zubo masa jollof din Macaroni da soyayyar plantain a plate.
Na ha'do da ruwa da lemo. Na nufi dinin area.
Ya ce "kawo mini nan".
Na 'dora masa akan center table din da yake kusa da shi.
Na koma na zauna ina cigaba da kallona. Bansan me yasa ba, ban yi zumudin zuwansa ba, ban yi farin cikin dawowarsa ba ko ka'dan, duk da zuciyata cike take da son sa kuwa.
Da kansa ya kai plate din kicin. Na yi mamakin hakan da ya yi amma ban tanka ba.
Da ya dawo, sai ya zauna akan kujerar da nake kai wato 2 sitter.
Ina kallonsa yana mini kallon kurillah, na yi kamar ban gani ba, na mayar da hankalina akan kallon da nake yi.
Cikin wani irin yanayi ya 'kira ni "Guduyo"
Ban amsa ba, na zuba masa ido tabbacin ina sauraron sa.
"Fishi kike yi da ni?"
Na janye idona na ce "me ka yi mini?"
"Nima haka na ga ni"
Ya fa'da cikin rashin damuwa.
Ba zato na ji ya ru'ko hannuna ya ce "Ban cika damuwa da lalle ba, amma wannan ya mini kyau sosai.
Kitson kan ki ma ya yi mini. Kwalliyar barka da zuwa aka yi mini?"
Ban kalle shi ba na ce "Nasan zaka dawo ne? Bare har na yi maka wani shiri?"
Ya yi shiru cikin rashin abin cewa.
Ya yi karfin halin cewa "Ilhama aka cusa miki! Dan na same ki fes da ke".
Takaicin sa ya kama ni.
Da sauri na ce "Bikin couse mates dinmu muka yi, kwalliyar bikin ce".
A razane ya ce "Biki?"
Ba ja in ja na ce "eh"
Nan da nan yanayin sa ya canja ya ce "Da iznin wa kika je gidan kunshi, wa ya lamin ce miki zuwa biki?"
Kai-tsaye na ce "Da Sakina muka je 'kunshin, da zan je bikin kuma Abba na tambaya".
Ina rufe baki ya ce "Sakina zata ha'du da fishina wallahi! Ni a duniya na tsani karambani da katsalandan. Amma ba laifin ta bane ai.
Raina ni kika yi shiyasa kika fita ban sani ba."
Na yi shiru ina sauraron sa cike da mamaki.
Na saci kallon sa na ga ya yi kicin kicin da fuska tamkar an fa'da masa mummunar kalma.
Tsawon lokaci muna hakan sai kuma abin ya sake ciyo shi ya ce "Da zan tafi ban ce miki asibiti ko makaranta kawai na yarda ki je ba?"
Na kasa bu'de baki na ce masa komi saboda yadda ya bani dariya sosai ya dage yana sababi shi a dole ga
Mai-gida.
Sai da na shanye dariyata sannan na ce "Ai ban ji ka fa'di hakan ba, na dai ji ka ce idan na gaji da zaman auren na fita".
Ya nuna ni da dan yatsan sa cikin fishi sosai "Ke kar ki kawo mini maganar banza kin ji".
Na dauke kallo na daga gare shi tare da cewa "Ashe ban fahimci Yaya Gudale dai dai ba".
Ga mamakina sai na ga ya ha'diye fishinsa, ya sassauta murya ya ce
"Shikenan abar maganar haka nan, fa'da mini me ya faru da bana nan".
Cikin rashin damuwa na ce "Ba abin da ya faru sai alheri. Na kammala zuwa asibiti, na koma makaranta"
"Ba ki yi kewata ba?"
Da azama na dinga girgiza kai tare da cewa "Ban yi ba ko ka'dan, dan kuwa na dauka sai ka shafe shekaru baka dawo ba".
Ya tsananta kallo na ya nisa ya ce "fishi kika yi tabbas".
Na murmusa na ce "matu'kar zaka yi mini adalci ai kasan shekarun baya ma da nake bording da baka shiga cikin ayarin masu kai mini ziyara ai idan na dawo bana kula ka, saboda ina mance duk wanda ya mance da ni ne, bare yanzu kuma da na sake yin hankali. Akan me zan yi fishi dan kawai ka yi hijirar watanni uku kacal? Na dauka zaka yi shekarun da zamu gaza ne ni da Abba har akai ga yi mini gaiba".
Ya fusata ya ce "Ban son wannan zaro maganganun da kike yi, kar ki tunzura ni Guduyo. I come in peace".
Na ta'be baki na ce "menene abin kada na fusata ka dan na fa'di gaskiya? Ai kasani dai idan muka gaza dole Abba ya saka alkali ya sahale mini, dan na samu wanda zai kwashe ni".
Nan da nan idonsa ya juye, jijiyoyinsa suka bayyana. Murya a dakushe ya ce "kin ci mutuncin mijin da Allah ya za'bo miki, daga dawowa ta sai cin karo da bakaken maganganu?"
Na sake yin fuska na ce "Daga fa'din gaskiyar magana? Dan Allah ko yanzu ka ce baka yi, baka ji a ranka akwai wanda zai fito ya na'de dukkan kunya ya dauke ni ba, ko da hakan kuwa zai ya mutsa hazo Dan m rikici?"
Kafin na rufe baki ya kamo hannuna ya murde da iyakacin karfinsa, zafin ya gigita ni na fashe da kuka mai hade da hawaye.
Yana huci ya ce "gaggauta tuba, ko na karairaya ki, sai ya dauke ki a nakashe".
Azaba ta sanya ni cewa "na yi tuba".
"Ban karbi wannan tuban ba."
Da sauri na ce "Yi hakuri Yaya Sadik! Allah ya baka ha'kuri".
Ya sake ni, ya koma kan kujera ya ce "Idan kika ce zaki dinga motsa mini kishina Billahillazi ke ce a wahala Guduyo, domin zan illata ki ne a banza. Sannan ki rufe mini bakin ki, nima yanzu zan yi miki smiling tabbacin na karbi tuban ki. Na kuma rufe maganar".
Yana mini wani irin kallo da murmushi ya ce "Bari na je na duba motocin can! Ki shirya zamu fita".
Yana rufe baki na girgiza kai tare da cewa "Bana jin da'di shiyasa ko

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login