Showing 150001 words to 153000 words out of 180068 words

Chapter 51 - Sabo Da Kaza By Surayyah Dee

18 Dec 2025

8749

zan fa'dawa uwata magana da nufin raini ko izgilanci ba, to kema kin wuce hakan, tunda ke din uwace mai girma a wajena".
Ai kuwa a kufule ta ce "Bana son iyashege kin ji! Ta ina na zama uwarki?
Inda ni uwace kya zage ni akan idona?"
Gudale ya kyafta mini ido.
Na daure na ce "Na yi kuskure ba zan sake ba, ki yafe ni Ummah".
Ta kuwa dinga sakin maganganu masu ciwo, tana cewa "mu je mu biya Malaminmu aikinmu ya yi kyau, mun samu duniya yadda muke so, amma a lahira gidan haya ne ya kamace mu, domin duk mai yin surkullen da zai jarabta namiji, ko shiga tsakanin d'a da mahaifi shine talakan lahira".
Na yi kasa da kaina, kuma abin mamaki sai ban ji bacin rai ba, bare na yi kuka ba dan komai ba illah yanayin Gudale da ya nuna yana cikin tsaka mai wuya.
Kallo daya zaka masa ka gane ba karamin karfin hali yake na ha'diyar cin mutuncin da ta sanya ni a gaba tana yi mana ni da uwata ba.
Amma da ke ta shiga rigar Abba, sai ban damu ba, asalima sai na gane ba karamin gigita zaman lafiyarts muka yi ba, ba dan komai ba sai dan ta kasa kaimu kasa, bata ganmu a taskun da take fatan ta ganmu ba".
Sai da ya gama iyakar cin mutuncinta kaina na kasa, ban kara tankawa ba, har ta gajiya dan kanta. Na dago na kalleta, fuska da walwala na ce "Ki k'ara ha'kuri Umma! Ki kuma yafe mini".
Daga haka na mike na ce "Allah ya kara lafiya".
Ta ce "Ban da naci irin naki , wacce mace za'a yiwa irin haka amma a kasa ganin fishi a fuskarta, anya kuwa wannan kina da cikakken hankali?"
Na dan sake fa'da'da walwalar fuskar na ce "To wa zai yi fishi ne da uwarsa Umma?
Ai komai kika yi mini, kin kai ki yi, kin kuma cancanci hakan ne."
Ta ja tsaki mai tsananin gaske.
Yayin da Gudale ya biyo ni har bakin kofar fita ya ce "Na gode sosai, ki je ki jira ni. Ina nan zuwa yanzun."
Ko kula shi ban yi ba, na fi kofar gadern na shige wajenmu.
Na dauki na kira Sakina ma sanar mata komai.
Tana bu'de baki sai cemin ta yi "Kin yi asarar hali Halimatu! Ya sake ki amma ki kwañan masa a gida?
Gidan na uwarki ne ko na Ubanki?".
Jikina ya sake na ce "Idan na tafin ma Baba dawowa da Ni zai yi, to ai gara ma na yi ha'kurin ba sai na raba bacin rai da su ba."
Ta bani amsa da cewa "Hakane! Ni kuma kin raba bacin rai da ni ai.
Amma kuwa duk nacinki sai na fa'di wannan maganar. Domin wajibi ne idan aure ya mutu a fa'da, hakanan idan an yi kome a fa'dawa shaidu saboda kafa hujja".
Na bata rai tamkar tana ganina na ce "Ke ka'dai kin isa ki yi shaidar ai".
Ta ce "Zaki ga wanda zan kafawa ja'irin mijinki hujja da shi".
*Dakin Umma*
Yana shiga ta ce "koma ka juya salamamme, akan idona kake wannan rawar kan akan wannan sundumar ko?"
Ya bata rai ya ce"Umma fa'da mini me zan yi miki ki yaba mini ne akan Guduyo?
Kina kallon irin kwanjin da nuna mata, har gabanki na kawota ta baki hakuri, amma Munu data Yi muku tijara a Yola ba wamda ta bawa hakuri asalima bata yarda ta yi muku laifin ba, illah tana ganin an danne mata hakkinta na Yar adam.
Badan na bata baki ba da tuni ta gayyato muku yan Human right.
Amma wannan da take ta lallaba ku, kuma Yar gidannan ce amma an k'i ta fir.
Gaskiya Umma ki yi hakuri na rok'e ki."
"Na rantse maka da kudirar Allah matu'kar tana son zama da kai sai ta ajiye aikin nan, dan ba zan yarda ta ka Yi ta cutuwa ba, tunda baka so to kuwa sai dai ta zauna ta zama cikakkiyar matar aure."
"Shikenan na ji na yarda! Amma kema ki dan sassauta, ki rage zafin da kika dauka da ita".
Bata kula she ba ta ce "Na gama maganata."
A falo ya dawo ya same ni, ina ta share hawaye.
Ya zauna daf da ni yana cewa "Yi hakuri kin ji Guddin Abba! Tashi ki shirya mu je shopping, duk abin da babu ko kike da bu'katarsa kawai ki rubuta. Kwanaki ma kin ce ya kamata na siyawa su Amnah dan kunnen gwal ko?
To muje sarkoki ma zan siya musu tunda iyayensu ai sun siya musu dankunnen tuni."
Haka ya dinga rarrashi, yana ta da'din baki a kokarinsa na wanke abin da yayi mini.
Akan dole na bishi muka fice, Wanda hakan ma sai da ya tunzura Umma da muka dawo ita kuma ta shigo duba Munubiya, ta kalle shi ta ce "A haka kamar namiji, nan kuwa shangadawa ne. Wai macen da bata dauki al'amarin uwarka da girma bane kake yiwa irin wannan gudun zuciyar, ba dan tausayin maraici kada ya yi maka yawa ba, da na ce maka kaico. Amma tunda ba yin kanka bane, barka a hannun Allah ya tsare mini kai".
Shikenan na ajiye aiki hakan ba karamin batawa mahaifiyata da Sakina rai ya yi ba, amma tunda na riga da na ajiye dole aka ha'kura aka zuba mini ido.
Ranar wata asabar sai ga Baban Gusau ya zo takanas wajenmu no da Gudale, har falona ya shigo, ya dinga yiwa Gudale fa'da da nasiha, ya dinga tuno masa kalaman Abba akan aurenmu. Ya ce "Ranar da Sakina ta mini waya ta sanar da ni barnar da ka yi ban iya runtsawa ba, duk da ta ce mini ka janye."
Kan Gudale a k'asa ya ce "A mini afuwa Babanmu. Tsautsayi ne da kaddara, In sha Allah hakan ba zai sake maimatuwa ba".
Yayin da ni kuma ya dinga yaba mini akan ha'kurina, ya tabbatar mini nan kusa kafin a samu yarinya mai hakuri irina zai yi matu'kar wahalar gaske. Amma da sannu zan ga ribar ha'kurina. Addu'a sosai ya yi mana sannan ya ce "Duk abin da ya taso shine Babanmu gaba'daya. Na dinga kukan rashin Abba! Har ya yi zaton ko bacin ran da ya wuce ne ya dawo mini sabo.
Ya mini al'kawarin zai dinga bibiyar zamanmu ba zai yarda da zaman k'wara ba, amma na yi ha'kuri for now.
Sannan ya ja kunnen Gudale akan ban da k'auro tunda ya hana aiki, to lallai lallai kada ya sake ya ji labarin ban wadatu da komai ba.
Ba a jima sosai ba munubiya ta haifi yan biyu duka mata, sai dai bakwaini ne.
Dayar ma bata zo da rai ba, dayar kuma aka saka ta a kwalba.
A wannan haihuwar ma Sai da Gudale ya kunsa mini ba'kin cikin ta hanyar cewa "Ya gode da addu'a, ai ya tuno tun lokacin aurensu na ce masa Yan biyu zata haifa, to ya ga ni, an haifi yan biyun kuma ya tabbatar da na so da na yi masa addu'a ko namiji daya a samu".
Na kalle shi na ha'diye dariya da takaicinsa. Domin na riga dana gane duk nisan zamani Gudale ba zai canja gaba'daya ba.
Maganar maitar da Umma take jifana da ita a wannan lokacin ta fito na ji har kunnena wai ni ce na yi sanadin haihuwar tun lokacin yin ta bai yi ba. Saboda tsananin ba'kin cikin da nake yi da cikin.
To na je burina ya cika amma hakkin kisan rai ya rataya a kaina.
Sosai abin ya so zama rikici domin mahaifiyata ta fara gazawa da wula'kancin da ake yi mini, amma Baban Yara ya danne maganar aka ha'kura akan dole.
Haka rayuwar ta dinga tafiya, diyar Munubiya ta fito daga kwalba, sai dai ba'a jima ba, itama ta bi yar'uwarta.
A lokacin kuma Yaya Gudale ya fara zazzabi da kuraje, ga amai lififi dai.
Ya kalle ni ya ce "Duk kirkin da nake yi miki wananan karon ma sai kin yi mini bakin hali Guduyo?"
Na. Ya yi dariya na kame bakina.
Sai dai wanann karon bai fi sati biyu ba ya wartsake.
Ba laifi bai yi mini tsiya sosai ba. Kuma komai nake so zai bani.
Na fara cikowa, hankalina ya fara kwanciya. I
Daidai lokacin kuma zalamar Munubiya kaina ta sake tsananta.

*Dakin Munu*
Zaune suke suna gado suna dan lashe lashe da tsotsensu ita da kawarta, sun yi nisa cikin sha'aninsu, kawai Umma ta tura kofar dakin a dalilin, ta Dade tana zaune a falon amma bata ji motsin mai d'akin ba.
Kawai sai ya yanke hukuncin lekawa ta gani ko a kwance take tunda kullum Munubya cikin bada uzzirin nata da lafiya take.
Ai kuwa ta yi mugun ga ni domin halin da ta gansu a ciki abin ya shallake hankali, ita a duniya bata ta'ba zaton da gaske mace zata nemi yar'uwarta mace ba. Kai wannan aikin ya munana Ubangiji ka shirye mu, ka tsare mana imaninmu.
Salatin da Umma ta saka ne ya dawo da su a hankalinsu, wani abin mamaki sai basu nuna wani tashin hankali kamar yadda ita ta kadu ba.
Kawar Munubiya wacce babbar mace ce da ta girme mata ta nisa ta kalle ta ta ce "Baby wannan fa?"
Ta kawar da kai ta ce "Uwarsa ce"
Ba kunya ta ce "Ai kuwa duk da ta tsufa ba za'a rasa mamora a jikinta ba, da ganinta lokacin da take cikin kuruciya an zuba mata halitta ta kerewa sa'a."
Murmushi kawai Munubiya ta yi ta ce "Tsufanta ne ya hana na shigo da ita harkar ai, amma da ace mun yi zamani da ita me zai hana a moreta?".
Sai kawai Umma ta fashe da kuka ta juya da nufin fita.
Yayin da k'awar Munubiya da take kusan tsirara, ta yi wuf ta ru'ko Umma tana cewa "Ki kalli tsaraicina ki tafi salin alin, ai ban yi lalacewar hakan ba".
Yayin da Munubiya ta mike itama babu kunya a yadda take ta rufe kofor ta rike Umma gam, yayin da waccar din ta dinga lalubar Umma tana ta dukan mazaunanta".
Iya hakan dai suka yi mata sai dai na tsawon lokaci.
Kuka ba irin wanda bata yi shi ba.
Sai da suka gama tozarta ta, sannan Munubiya ta ce "Wallahi tallahi Umma idan na ji wannan maganar a bakin wani sai na yi k'ararki".
Da azama d'ayar ta ce mata "Dauko mini jakata na shaka mata powder mu tub'eta tas ta yadda zamu dauki hotonta mu watsa sai mu ga k'aryar yadawar da zaki yi, idan kina son Allah ki fa'di wannan maganar, ki ga yadda zamu yi kaca kaca da mutuncinki."
Munubiya ta ce "Bana Jin shakkar hukuncin da zaki saka tijarraen danki ya yi mini, domin a yanzu ba zamansa nake yi ba, zaman shawo hankalin surukarki da kika tsana nake yi, domin sonta nake, tana burge ni fiye da sangartaccen danki da yake abubawa tamkar wanda kika shayar da shi nonon tinkiya tsabar iskancinsa, dama a cike nake da ke ta yadda kike kishin danki, to yau dai kin tabbatar baya gabana. Tashi ki tafi idan kin k'aryatamu, kika fito da maganar wallahi sai na kai ki k'ungiya an kwana da ke. Mun kuma watsa hotonki ki barwa y'ay'a da jikoki tsarabar tarihin arziki".
2/8/23, 10:25 - Buhainat: *SDK*.
*89&90.*

*Ummah*
Ta fi wata tana cikin razani da kad'uwa ta kuma kasa bu'de maganar gaba'daya ta tsorata da Munu, yayin da take tsananta saka ido a tsakanin Halimatu da Munubiya
Tabbas ta yi nadamar zabowa Gudalenta Munubiya, sai dai kuma wasiwasi mai yawa take yi, domin gani take tamkar makircin Safiya ne ya sanya suka yiwa Munubiya wannan kulunboton ta yadda za'a kyamace ta, shikenan y'arta sai ta mallaki Gudalenta ita ka'dai. Ba'kin ciki kan ba'kin ciki ke nukurkusarta ba ka'dan ba, ta rasa yadda zata tsoma ranta.
Gaba'daya ta susuce, ko barci ba sosai take samu ta yi ba, domin kuwa abin na cinta, barazanarsu ta hana ta fito ta fa'di masifar da ta gani.
Bare ta samu sassauci.

Ban san me ya samu Umma ba gaba'daya ta yi laushi, amma kuma ni ban samu sassauci ba, na kuma lura ta daina rawar kai akan Munubiya.
Yayin da cikina ya cigaba da girma. Ba abin da Gudale yake fatan na ambata masa irin na ce na miji zan haifa, yayin da ni kuma na kame bakina ina ce masa "ka yi fatan ma na sauka lafiya mana."
Ranar da na soma fa'da masa hakan bacin rai ya yi tamkar ya dauke ni wata bokanya.
Saboda fitattike wa ya yi wai ai na ce masa sai an haifa masa girls guda biyar, yana sane bai manta mugun fatan da na yi masa ba.
To ya tabbata ya haifi mata biyar reras, uku suna can suna jiransa ranar k'iyama su kama hannunsa suna Abi Abi har sai sun sada shi da aljannah".
Na kyal-kyale da dariya na ce "Har da wanda basu ya hara a haifa masa ba ?"
Ya sha kunu kuwa! Ya ce "Annabi ne dai ya ce "Wanda yaransa uku suka mutu suna k'anana, idan ya yi hakuri zasu ceshi shi, wani ya ce ko mai biyu? Annabi ya ce na'am. Sai wata ta ce har da mai guda daya? Annabi ya ce har da mai guda daya. Kinga ni kuwa zan samu albarkacin Little Adama da twins".
Na murmusa domin yadda ya hakikance yana kiran little Sakina da sunan Adama wai shi a dole sai na ce ba sunan da nake so a saka mata ba kenan.
Ya gyada kai ya ce "Allah ya yafe miki Guduyo! Kin mayar da ni abin dariya, sai kawai ya zaro tsinken tsintsiya ya miko mini.
Na karba ya durkushe a gabana yana fa'din "sai na nuna masa abin dariya a jikinsa.
Ai kuwa na tsunture da dariyar sosai.
Ganin ya fitattike akan sai na yi pointing abin dariya a jikinsa ya Sanya na nuna kansa.
Ya kuwa mike yana nuna kirjinsa yana cewa "Kaina da motsi kike nufi ko Guduyo?"
Na kuwa sake kyakyacewa.
Ya tunzura ya ce "ki gaggauta tuba tun ban kwashe miki karama kin kasa samun rabauta ba".
Na sake yin dariyar na ce "Allah ya huci zuciyar Gwanki na Guduyo Baban Amnah".
Shima dariyar ta kwace masa ya ce "Na rantse tunda kika ce kaina da motsi idan ba sai na koyo allura ba.
Ta yadda zan dinga danne ki Ina yi miki alluran masu tabin kai idan yi so sai mu yi jinyar tare.
Kuma ba Gwankinki bane na Munubiya ne. Addu'ar da zaki dinga yi mini ki samowa su Afrah brother shine kike yin kyashi, kai Guduyo zuciyarki da fa'di take Wallahi".
Dariya ta sake kwace mini. A fili na ce "Allah ga Gudalen Abba ayi masa afuwa, ka san yadda ka sanya mini sonsa, Ubangiji a kintsa mini tunaninsa".
Ya girgiza kai tare da cewa "Kin ci bashin kirana marar tunani. Tabbas baki barni haka siddan ba Guduyo".
A kwana a tashi na shiga watan haihuwa, a wannan lokacin kuma Munubiya ta dauke hankalinta a kaina, sai dai bata fasa yi mini kirki ba, bata fasa yiwa su Amnah alheri ba.
Ina gicciye Akan sallaya bayan na idar da sallah ina ta tunanin abin da zai biyo baya idan na haifi mace.
Ga mamakina sai ban ji fargaba ta kama ni ba. Domin na riga da na fara tsikewa da halayyarsa, amma idan na tuna da idon Abba ma bai fasa yi mini iyashege ba, tun ina a asibiti, to ina kuma a yanzu?.
Idan na yi yun'kurin na ro'ki Ubangiji ya sanya abin da yake cikina ya zama namiji ne, sai kunyar hakan ta kama ni, domin wasu ma su kawai su sami cikin ne matsalarsu, so suke su ga jininsu. Ni kuma ya bani amma na tsaya rokar kalar jinsin da nake so.
Na sake tuno kissar da Àllah da kansa ya bamu a cikin kur'ani na Iyalan Imaran (Ali Imran).
Mahaifiyar Nana Maryam irin yadda suka so su haifi namiji, har suka yi bakancen idan namiji ne zasu sanya ya zama mai yiwa masijdil akasa hidima.
Amma da Ubangiji ya tashi ikonsa sai ya basu Nana Maryam, duk da basu so hakan ba, amma sai suka karba da godiya, suka yi mata addu'a, suka nema mata tsari daga shaidan suka kuma nema wa zuri'arta tsari gaba'daya.
Hakan kuma suka yi mata tarbiyar yiwa masallacin hidima kamar yadda suke son namijin ya zama.
To gashi har yau din nan da Ubangiji ya sanya albarka a sha'anininta, ya tsare ta, kusan shekaru dubu uku da faruwar al'amarin amma Ubangiji bai shafe tarihinta dana iyayenta ba.
Sai ma ya zabeta ya saukar da babbar izina akanta da danta dan ta zama aya ga masu hankali.
Idan ina tuna wannan ayar, ina kuma tuno sakayyar da Allah ya yiwa Abba da ya bashi yara mata, shi kuma ya zama bawa mai godiya, ya karbesu da farin-ciki, ya yi musu tarbiya cikin adalci da tausayi, ya kuma aurar da su a hannaye na gari.
Ubangiji sai ya shirya masa su, ya daukaka su, ya kuma mayar masa su abin sha'awa a wajen kowa, domin ko Anti Maimuna da Anti Juwairiya ai ba wai basu da kirki bane gaba'daya, ra'ayin uwarsu suke girmamawa mussaman akai na.
Kowanne irin jinsi aka baki yar'uwa yawaita godiya, kada kuma ki yarda ra'ayin namiji ko na danginsa ya sanya ki butulcewa Ubangijin da ya baki y'ay'a mata, yawaita yi musu addu'a, ki kuma tsaya ki basu tarbiyar da gobe za'a yi alfahari da su.
Ya shigo ya same ni a hakan na kalle shi a jirgide na ga ya yi wanka ya shirya, ya yi kyau sosai. Kamshinsa na tsaddden turaren Chris adams ya cika mini dukkan kafofin hancina.
Ya ce "Fita zamu yi da Munubiya, zan rakata mu dubo sister din Mum dinta da bata da lafiya, shekaranjiya waccar ta dawo daga Egypt."
Ina daga yanda nake na ce "Ku gaishesu. Dan Allah kuma ka turawa Maman Nana ku'di a sake karo siyayyar kayan haihuwar nan. Kasan dai kayan da muka siya ba wasu masu yawa bane".
Ya make kafa'da ya ce "Ba zan bata ba Wallahi.
Ke nifa waccan Dubu Sittin din da na baki Billahillazi dan kada ki sanya ni a gaba da koke koke ne. Amma ban da hakan ace duk yawan yan'uwana dan zaki haihu sai na yi wata hidima?
Wallahi ban da nasan halinki da koke koken banza da kafiya tamkar mutanen farko da ko wando ba zan siya ba, idan ya so idan anyi haihuwar su bada dankwali ko rigarsu a na'de musu y'arsu a ciki, ba nine da kunya ba. Ina ce ke na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login