Showing 6001 words to 9000 words out of 180068 words
zan iya jarumtar rabuwa da Sadik, to kuwa sun sani bala'in da nake fuskanta ya kai intaha.
Antin Zaria ce ta bude zaman da addu'a don kore shaidanun da suke labe. Cikin rarrashi ta ce, "Haba Guduyon Gudale! Na dauka maganar ta wuce haka nan, kowa ai ya san kin yi hakuri. Dukkanmu kuma ba za mu sake zura ido ba tare da muna bibiyar zamanku ba, na sani akwai guraren da duk yadda kuke zaune lafiya da mijinki sai kin yi hakuri kin kawar da kanki, amma idan kika ga ha'kurin zai zama na zalunci, kar ki fa'da wa kowa, ki fa'da mini, ni din yayarki ce, kin sani kuma na haifi wanda ya fi ki. Don haka ni din uwa ce, idan har kika yi hakuri wannan maganar ta wuce, ni kuma na yi miki al'kawarin ba za ki sake ha'kurin cutarwar da yake miki ba, ni da kaina zan raba ku, na kuma baki mafakar da su Baba suke mana barazanar duk wacce ta kashe aurenta ba ta da gurbin zama a gidanjensu."
Hawaye ya balle mini, ina jin tamkar na bude baki na zayyane musu irin ta'addacin da yake yi mini, na kalli Sakina na ce, "Kin fi kowa sanin irin azabar da nake sha a wannan zaman, taimake ni ki fa'da musu, ko su za su ji tausayina."
Da sauri ya ce, "Ni da kaina na gamsu ban kyautata miki ba, Sakina ta sani, Ubangiji Ya sani, to mu bar shi a hakan. Ina rantsuwa da Wanda ruhina ke hannunSa na gane kuskurena, na canja, zan kuma gyara, na yarda wadannan mutanen ukun su ne shaida a kan ba zan ci gaba da yin abin da yake cutarwa ne a gare ki ko 'yayanmu ba. Ya Abdallah lauya ne, Antin Zaria tana cikin kungiyar kare hakkin mata, ga su nan a zaune su ne shaidunki, na kuma gamsu idan ba su ga canji ba, su yi fatali da zumunci, su gurfanar da ni a gaban kuliya, idan har ban yarda na rabu da ke cikin mutunci ba. Fatana dai yanzu ki ba ni wata damar, ki yafe mini." Cikin rauni sosai ya karasa maganar.
Ya Abdallah ya mi'ke ya ce, "Halimatu let gone be by gone, na rufe wannan maganar, ki yafe ta, na sake jaddada miki na kashe ta. Ubangiji ya kiyaye gaba. Anti ni kam na yi gaba sai kin fito."
Suka mike ita ma tana jan kunnensa har da rantsuwar tabbas idan bai canja ba, wallahi da kanta za ta gurfanar da shi, tunda abin da yake yi tabbas cin zarafi ne.
Sakina ce ta kasa yin magana saboda yadda take tsananin kaunarmu ni da Ya Sadik, shi yasa ba ta maraba da duk abin da zai ta'ba aurenmu, ta kuma lura a yanzu fishi nake yi da ita a dalilin ina ganin tamkar ta yi son kai ne a tsakanina da shi
Suka tafi, ya bi su zuwa waje, bai wani jima ba ya dawo, ya sake zama a jikina sosai ya ce, "Tashi ki yi wanka, mu je ki rokar mini Antin Zariya ta bar mana su Amnah."
Kafin na yi magana yaran sun shigo da gudu, ganin Babansu a kusa da ni yasa suka yi turus, Aman kawai ya 'karaso ya fa'da mana yana gwalan-gwalantunsa.
Sanin da na yi yarana suna bu'katar jin dumina yasa na tashi na isa gare su, ai kuwa suka rungume ni, amma sun kasa yin wani kwakkwaran motsi saboda ganin Babansu. Na ja su muka yi dakina, suna ta ba ni labarin Abuja, da irin makarantar da suke zuwa. Fes suke cikin nutsuwa da walwala tabbacin suna samun kulawa ta musamman, kyaunsu ya matu'kar fitowa, kasancewar farare ne 'kal masu dogon gashi irin na fulanin Yola.
Afra kam irin jikina ta yo rugugu sai ta zama tamkar 'Yar turawa saboda farinta da gashinta, buloras ke nan.
Ya shigo yana ri'ke da Aman a kafadarsa, a darare suka ce "Daddy ina yini?"
Ya kalle su yana jin takaicin nisan da ya haifar a tsakaninsa da 'ya'yan cikinsa. A hankali ya ajiye Aman ya buda hannuwansa ya ce, "Amnah, Afrah come to your daddy, why are you doing this to me, am I stranger?"
Suka isa a sanyaye ya rungume su yana jin son su na sintiri a sassan jikinsa, hawaye ya goce masa sai fadin "Astagafirillah!" yake a hankali.
Ya mi'ke ya fita da su, na bi su da ido, na kalli agogo, na ga biyar saura na yamma na kishingi'da ina labarto wa zuciyata wasu al'amura na tushenmu, wanda na sani, da wanda na ji labarinsu.
# SURAYYA DEE ✍️
2/8/23, 10:22 - Buhainat: 🌺 *SABO DA KAZA* 🌺
*NA*
*SURAYYA DAHIRU*
```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.```
```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️
____________(�?)______________
https://www.facebook.com/profile.php?id=100069755834980
•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·�?
*Godiya ta tabbata ga Allah(S.W.T.). Tsira da aminci su tabba ga Annabin Rahama(S.A.W).*
*SADAUKAWA GA IYAYENA GUDA HUDU*
*ALHAJI MUHD TUKUR*
*HAJ FATIMA LADI ALI*
*ALHAJI DAHIRU ALI*
*HAJ MARYAM HAMISU KANO*
*ALLAH YA JI'KANKU DA RAHMA YA BAKU ALJANNAR FIRDAUSI*.
*FATAN ALHERI GA MIJINA*
*(M.I. NASHE)*.
*JINJINA GA SHUGABAN KUNGIYAR LAFAZI WRITERS*
*SADIK ABUBAKAR*
*Na gode da kokarinka akan rubutuna*.
*Assalamu alaikum sister's! Barkanmu da sake ha'duwa a cikin sabon littafina.*
*Hakika na yabawa kaunar da kuka nuna mini akan littafin *Halin Yau*. *Ba abin da zance muku sai dai fatan Ubangiji ya saka muku da mafificin alheri*.
*Ina fatan zaku bibiyi wannan labarin sannu a hankali dan jin da wanne sa'kon ya zo.*
*Ina addu'ar Allah ya bani ikon rubuta dai dai, ya hana ni rubuta barna*.
*JAN HANKALI*
*GABA'DAYA WANNAN LABARIN 'KIR'KIRARRE NE (FICTION) BAI FARU BA. HAKAN NAN SUNA DA GARURUWAN DA SUKE CIKI BANA KOWA BANE, NA ZABE SU NE TA YADDA ZASU 'KAWATA LABARIN.*
*IDAN KIN CI KARO DA ABIN DA YA YI KAMANCECENIYA DA RAYUWAR KI TO AKASI NE. MANUFAR LABARIN JAN KUNNE DA HANNUNKA MAI SANDA AKAN WANNAN RAYUWAR MAI CIKE DA RU'DANI. BA WAI SHAGUBE GA RAYUWAR WANI KO WATA BA*.
1&2.
*Free page.*
*Tushe*
Asalin kakanmu Alhaji Zubairu Lawal Moriki, 'dan asalin 'kauyen Moriki ta cikin 'karamar hukumar Zurmin
jahar Zamfara ne. Bahaushe ne, kuma Bafulatani, domin mahaifiyarsa Bafulatanar daji ce, kyakkawan dattijo fari tas. Ya taso cikin tsari da 'ka'idar tarbiyar Bahaushen Arewa mai tsananin ri'ko da dokokin shari'ar Islama.
Fataucin dabbobi ne ya kawo shi garin Kano har ta zame masa tamkar gida. Domin kuwa sannu a hankali ya kwaso iyalinsa suka dawo kano gaba'daya. 'Ya'ya biyar mai dakinsa Maimuna (Adda) ta haifa masa, duk da sun binne wasu da dama a dalilin tana wabi.
Hajiya Hafsatu ita ce babba (Yaya ta 'Kwalli) ba ta ta'ba haihuwa ba, sai dai kuma yan'uwan nata ba su ta'ba bari ta ga gurbin rashin haihuwa ba. Sai dai kawai motsawar da zuciya za ta yi idan sha'awar ganin jininka ta motsa. amma ba don kukan wani abu ba, domin 'ya'ya biyu 'yan uwanta suka bata ta goya, ta kuma aurar. Dukkan abin da ya shafi yaran kuwa yana hannunta. Ramla da Ashir. Mace mai zafi idan aka tabo ta, mai son dinke barakar zumunci, duk inda ta ga zumunci zai samu tawaya yanzunan za ta yi dukkan mai yiwuwa ta 'dinke shi.
Sai Alhaji Abubakar Moriki (Abba) shi ne na biyu, dattijon arziki mai tsananin ri'ko da ka'idojin shari'a, masoyin zumunci da kyautata shi. Dukkan karatunsa ya yi ne a bangaren addini, a 'kasar Sudan ya yi digirinsa na farko a fannin sanin ilimin Hadisai. (Hadith Science) Daga nan ya wucewa 'kasar Masar ya sake zurfafa iliminsa a kan sanin a fannin Shari'a da rabon gado. Dukkan karatun tallafi ne na gwamnatin tarayyar Najeriya.
Daga nan kuma sai ya fa'da harkar kasuwaancin safarar zobo da 'karo a tsakanin 'kasashen Africa. Sosai ya samu daukaka a harkar, ba 'karamin nasibi yake samu ba, domin idan ana lissafa attajirai, babu shakka za a saka Alhaji Abubakar Moriki.
Matarsa 'daya Hajiya Saude (Umma). 'Yar asalin garin Yola ta jahar Adamawa ce.
Kyakkawar mace fara 'kal mai cikakken diri, mai yalwataccen gashi, sai dai gajeriya ce.
Mace ce mai izza da jin 'kai, ta tsani wani ya rabe su, kasancewar mijinta shi ne garkuwa a danginsa.
'Ya'ya shida Ubangiji ya azurta su, biyar 'din farko dukkansu mata ne kyawawan gaske domin dukkansu ita suka biyo, suka sami tsayin mahaifinsu duk da mijin nata ba baya ba ne wurin kyakkawar sifa, sai dai ko kusa ba a hada kyaun mace da namiji, sannan farinta da dogon gashinta baki sidik sun shahara, sai ta zamo tamkar Balarabiya. Haka 'ya'yanta suke farare dogaye, masu gashi, duk irin yadda Ubangiji Ya azurta ta da samun wa'dannan kyawawan yaran kuma masu lafiya, ita ba ta gode ba, domin ba abin da take so irin ta haifi namiji. Hafsat ce babba, wacce ya yi wa yayarsu magajiya, sai Maimuna (Ummu) mai sunan kakarmu, sai Juwairiya, Ramla, Sakina, sai autanta da ya ci sunan sahabin Ma'aiki Abubakar ake ce masa Sadik kasancewar sunan Abbban ke nan, ita kuma ta ce Gudale.
Sai Hajiya Binta Moriki (Maman Kebbi) da take aure a Kebbi tana da 'ya'ya uku Shafa'atu, Adnan da Ashir.
Sai Alhaji Ssni Moriki (Baban Gusau) da ya kasance dan kasauwa mai sayar da suturu, a cikin babbar kasuwar Gusau, a can kuma yake zaune da iyalinsa. Mutum mai tsauri da fe'de gaskiya, komai 'dacinta, marar daukar wargi. Matarsa 'daya da yara biyar, Fatima, Abubakar, Maimunatu (Ummj), Abbas, da Farisa. Abbas kuma yana tare da mu, tun daga karatun sakandire da ya yi a Science Dawakin Kudu da su Ya Sadik shike nan ya zama dan Kano, duk sa'anni ne da su Ya Al'amin, Kuma duk Gudale ne 'karaminsu.
Mahaifina Alh Ibrahim Moriki (Baban Yara) shi ne autansu, kusan Alhaji Abubakar shi ya yi masa komai tunda ga kan hidimar makaranta, har ya zuwa aure. Ma'aikaci ne a hukumar ilimin bai 'Daya. Mahaifiyata Safiyya (Mama) 'yar Kano ce, ta fito daga unguwar Magashi, cikin babbar zuri'a, ina nufin masu haula da yawa ba wai ku'di ba. Matsakaicin kyau ne da ita, sannan tana da dan jiki, da manyan idanuwa dara-dara, sannan wankan tarwada ce, yayin da Baba ya kasance fari tas! Lokacin da aka auro Mamanmu, Umma tana goyon Ramla ne, sosai suke zaman lafiya, domin Mama tana gama gyara bangarenta, matu'kar mijinta ya fita to kuwa za ta rufe ta tafi wurin Umma saboda a gidansu na gado suke zaune wanda Abba ya fadada shi, ya zamanantar da shi, a cikin unguwar Hausawa 'Yan-Babura.
Sosai Umma take jin da'din zama da Mama, saboda biyayyar da take yi mata, musamman yadda take hidima da 'ya'yanta, barin Ramla da barci ne kawai yake raba su.
Mamanmu ba ta cika shekara a gidan ba ta haifi Abdallah, lamarin da bai yi wa Umma Da'di ba, ta ji babu dadi sai dai ba a samu canjin mua'amala ba. Kafin Mama ta cika shekaru hudu ta hada yara Uku duk maza Abdallah, Azzubair (Babangida) da kuma Ammar.
A wannan lokacin kuma Umma ta fito da dukkan munanan dabi'unta, sosai ta dora karan tsana a kan Mama da ya'yanta, babban ba'kin cikinta yadda haihuwa ta tsaya mata cak ga kuma wata ta zo tana haifar maza duk shekara, nan gaba hasken da yake kofarsu zai koma kofar Safiya da Ibrahim. Ta fara hana 'ya'yanta zuwa bangaren kanin mahaifinsu, sannan kuma idan Maman ta zo, ba za ta ga fuska ba, 'dan abu 'kank'anin zai faru za ta fara habaicin har gobe mijinta shi ne garkuwarsu.
Sosai Umma ta takura wa Mama har ta kai fargabar ta yi ba'ki take yi, saboda yadda take fuskantar tozarci.
Hakurin Mama yasa ko Baba bai fahimci halin da suke ciki da Umma ba, sai da tafiya ta yi nisa. Shi ma rashin ganin su Ramla a gidansa ne, ya kuma lura Mama ta rage shiga wajen Umma. Kasancewar shi ma mai son zumuncin ne, sai ya yi kamar bai fahimci matsalar a wurin matar yayan nasa take ba, yana yi wa tasa matar wayo da dabara ta hanyar cewa ita ce 'karama, sannan ai ya lura ita ta janye daga jikinta, ya lura ba ta zuwa 'kofarta kamar da.
Ana cikin haka Umma ta haihu, again dai mace ce, ko ka'dan ba ta yi farinciki a zuciyarta ba balle ta yi godiya.
Aka yi sunan Sakina babu wani armashi, saboda ta riga ta dora rai a kan boy ne a dalilin ta yi scanning an tabbatar mata namiji ne, sai kuma ga kyawawar budurwa ta iso. Watan Sakina goma Mama ta sake haihuwar Al'amin, Wohoho! Ina wuta Umma ta jefa ta, a lokacin mahaifiyarmu ta fuskanci wani irin tashin hankali da matsatsi, domin an kai jallin da ko tsakar gidanta ya gagare ta fitowa, kullum tana 'daki, haka 'ya'yanta, sannan duk shedantar Umma ba ta yinta idan maigidanta Abba yana gida, musamman da yake mai yawan tafiye-tafiye ne sai abin nata ya sake bun'kasa.
Tashin hankalinta yadda duk tafiya ba ya banbance tsakanin 'ya'yansa da na 'kaninsa, hatta keke da ya ce ba ya son 'ya'yansa mata su hau, duk ya saya wa su Abdallah kowa da nasa, haka indai yana gari to da Abdallah yake yawo ko'ina, daurin aure ne, ko ta'aziyya ko yawo haka, duk dinkin da zai yi tare yake yi da shi. Haka makaranta 'daya suke zuwa da 'yayansa shi ne kuma yake biya gaba'daya.
Wannan ya sake ki'dima Umma tana ganin tamkar gazawarta ne yasa ta kasa haifar namiji duk kuwa da ko a fuska mijinta bai ta'ba nuna mata cewar 'ya'ya matan da take haifa masa ya gaji ko baya so ba, duk haihuwa sosai yake murna da hidima ya kuma zaba musu kyawawan suna.
Cikin ikon ubangiji watan Al'amin goma.
Umma ta haifi 'danta lafiyayye sak ita ya biyo shima, fari kal, mai gashi domin gashin har idonsa yake, tun yana jaririnsa dan tsurut ne babu nauyi, ma'ana ba jiki. Ga mamakin Umma Abba bai yi wani zumudinsa fiye da su Sakina ba, domin har zuciyarsa bai ji yaron ya 'dara Abdallah a wajensa ba, ke nan shi ba yanzu ya yi 'da ba.
Wannan al'amarin ya sake tsananta kiyayyar Mamana a zuciyarta, ta gaskata asiri take yi don ta mallake su ga'badaya.
Rainon Abubakar ya banbanta da duk 'ya'yan da Umma ta haifa, wani irin gata take nuna masa tamkar dai ba ta samu haihuwa gaba'daya ba sai da ta shekara talatin a dakin miji. Komai na yaron a wajenta mai girma ne, ba ta ha'da shi da komai, tun mijinta na yi mata fa'dan kar ta lalata shi, har ya ha'kura ya koma yi mata addu'a.
Shekarar Sadik wanda Umma take'kiransa Gudale biyu aka aurar da Hafsatu 'yar wajen Umma ta farko aka kaita Zariya, saboda nan ne garin mijinta, kuma malami a Jami'ar Ahamadu Bello, daan boko na gaske, tun kafin auren ya sama mata gurbin karatu a Jami'ar inda za ta karanta Tsumi da Tanadi (Economics).
Hakan yasa Umma ta 'ki haihuwa tuburan ta dakatar da ita da 'karfin tuwo a cewarta ta barwa Yara.
Wani abin da ya damu Umma yadda Sadik ya bijire mata daga hana shi zuwa sashinmu, duk juyin da za ta yi sai ya zo wajen Al'amin, kullum cikin saya masa kayan wasan da za su dauke masa hankali take. Amma da zarar gari ya waye tofa zai tafi, ba zai yarda ya dawo ba, sai ya yi barci sannan Abdallah zai kawo shi.
Watarana yana ta kukan zai tafi ta ri'ke shi ta hana, Abba ya gane dalilin kukansa aikuwa cin mutuncinta da ya yi ba ka'dan ba ne, ya ce matu'kar dansa ne to dole kuwa ya so jinin Ibrahim.
Shike nan sai ya zama rabi-rabi, har ya fi zama wurin Mamanmu.
Mama kuwa tun haihuwar Al'amin ta dinga 'bari, duk cikin da za ta samu sai ya bare, a haka har aka shafe shekaru tara da haihuwar Al'amin yayin da Sadik yake da takwas, shakuwa ce mai tsananin gaske a tsakaninsu, hakan nan sosai Ya Sadik ya shaku da Mamanmu.
Na iso duniya ne cikin cire tsammanin haihuwa daga iyayena, sannan ba 'karamin wahalar gaske Mama ta sha wajen haihuwar ba, hakan ya zama sanadin da aka juya mata mahaifa gaba'daya.
Idan mai karatu na biye da kyau, zai gane mu biyar ne 'ya'yan Ibarahim Moriki, ni ce kuma 'ya mace tilo da na biyo maza hudu, kamar yadda Ya Sadik ya biyo mata biyar ya zama namiji tilo.
Na taso cikin gata iri-iri, ba daga iyayena ba, ba daga yayye ba, haka nan ba daga Abba da iyalinsa ba, kawai Umma ce ba ta sona, take adawa da duk abin da mijinta ko 'ya'yanta za su yi mini. Ta yi juyin duniya Sakina da Sadik su daina kula ni amma ina, domin duk miskililancin Gudale zai dauke ni, shi yasa mafi yawan hotunan muna yara ina hannunsa, ko ina kan cinyarsa, muna da hotuna ni da shi muna yara kala-kala.
Wani ikon Allah yadda Ya Sadik ya fi zaman sashinmu, ni kuma na fi zaman sashinsu saboda Sakina, tunda aka yaye ni, na yi wayo kullum ina gurinta, duk zare idon Umma da muzurunta ba na fasa zuwa ko fasa zama, sai idan Sakina tana makaranta, domin duk inda za ta je tare da ni take zuwa.
A lokacin an aurar da duka 'ya'yan Umma Sakina ce kawai ta rage.
Sakina ita ka'dai ce mace domin tsararrakinta duk maza ne, Al'amin da Sadik. Don hakan shakuwa ce a tsakaninsu ba ka'dan ba. Sai dai ba zai yiwu ta dinga yawo tare da su ko kwana ba, sai ya zamana ta ja ni a jiki duk da karancin shekaruna, tunda shekaru goma ta ba ni cif, tare muke kwana, ita take mini wanka ta shirya ni.
Wata irin shakuwa ce ta musamman a tsakaninmu, hakan ba 'karamin da'di yake yiwa Abba ba shi yasa ma ya dawo da ni bangaren gaba'daya. Umma ce take kyashi da hakan, take yawan hantarar Sakina a dalilin ita ta janyo ni. Da wayona da