Showing 36001 words to 39000 words out of 180068 words
rabauta a sanadinta*😁
*SADIK*
Da daddare Sadik ya je wajen Abba a dalilin tunda ya dawo da rana yake ta barcin gajiya.
Bayan sun tattauna akan lamarin tafiyar da ya yi zuwa Nijer, sai kuma suka koma kan maganar ginin da ya dawo ya tarar ana daf da kammalawa.
"Ai Abba ginin nan ya yi kyau duk da dai ban samu na shiga ba, amma ko daga nesa aka hango an san ya ginu, sannan wanda ya tsara ya cika fasihin magini.
Murmushin jin da'di Abba ya yi tare da cewa, "Sai ka shiga ka gani za ka gaskata kwararren masanin abin ne ya yi aikin, sosai tsarin zai burge ka."
Gudale ya yi mamakin yadda Abba ya sauko yake yi masa magana cikin sakin fuska, tun akan aikin da ya samo masa ya 'ki yi shike nan ya ninka watsi da lamarinsa. Amma abin mamaki yau har da dariya yake yi masa duk da ba tuba ya yi ba.
A ran Sadik sai yake ganin ko don ya yi kwanaki baya nan ne.
Hira sosai suka yi cikin nutsuwa. Tamkar ba Gudale da Abba ba.
Ba su ankara ba har goman dare sannan suka yi sallama.
Washegari sassafe Sadik ya nufi makaranta saboda kowanne 'dalibi zai gabatar da binciken da ya yi a Jamhuriyar Nijer.
*Guduyo*
A makaranta ina ganin sa da zai tafi gida, ya dauke kai ya wuce tamkar bai san ni ba.
Don haka ni ma na yi 'karfin hali ban yi masa magana ba.
Ina kallon sa ya shiga motarsa ya yi tafiyarsa ya bar ni, hakan ya tabbatar mini da gaske ya zafafa lamarin.
Ban ji dadin hakan da ya yi mini ba duk da sai karfe shida zan kammala. A lokacin kuma sallar Azahar aka idar.
Sukuku na karasa daukar darusan a dalilin fishin Gudale ya dame ni.
Na iso harabar gidan na tarar da motar Yaya Sadik bayanta a burme sosai tabbacin wani ne ya buga masa ita.
Na wuce ina fatan Allah ya sa iyakacin asarar ke nan, ba ta shafi lafiyarsa ba.
Na shiga na tarar da shi tare da Yaya Al'amin a wajen Mama yana fa'da mata ikon Ubangiji ne ya sanya motar da ta debo bulo masu yawa ba ta ramutse shi ba.
A ki'dime na ce, "Allah mun gode maka! Sannu Yaya Gudale' Ubangiji ya tsare ya mayar da alheri".
Ya waske ya ki tanka mini.
Na zauna ina ta jan maganar da nufin na samu ya kula ni.
Mama ta ce " Haba Yaya Sadik ya kuma haka, yar 'kanwarka tana ta yi maka sannu amma ka 'ki amsawa?"
Kai-tsaye ya ce, "Ai ba zan amsa mata ba Mama! Kuma ba 'kanwata ba ce na riga na yafe wa Sakina ita tuntuni su je su 'karaci 'kulle'kullen munafuncinsu da sunan zumunci ".
Yaya Al'amin ya ce, "Wai kai sai yaushe za ka zama mutum sak? Ina ce 'dazun Ubangiji ya nuna maka 'kamshin mutuwa?"
Cike da takaici Ya ce, "ba zan zama mutum ba sai ka daina shiga abin da bai shafe ka ba Al'amin".
Mama ta mi'ke tana cewa "Ubangiji dai ya nuna mini kun girma, girman da babu shiririta".
Yaya Al'amin ya ce, "Wannan addu'a tsakani da Allah da Sadik ta dace domin ni dai mutum ne sak Mama".
A hassale ya dubi Al'amin ya ce, "Ni kuma a jinsin dabbobi nake ko kuwa jinsin Jinnu? Ka daina cin mutuncina".
Cikin rashin damuwa Yaya Al'amin ya ce, "Na yi din Sadik da'din abin ma ba zan doku a hannunka ba".
Da azama ya shiga kwadawa Mama Kira yana cewa "Mama zo ki ji abin da Aminu yake mini, gaskiya na gaji, tsakani da Allah sun takura mini shi da Sakina! Ki ja masa kunne, ya daina zalunta ta ta hanyar yi mini kutse akan abin da bai shafe shi ba".
Da taushin murya Mama ta ce, "Rabu da shi ka ji tunda ya zama babban kwabo, yi ha'kuri ka yafe masa, dauki girman kawai Abubakar Sadik".
Nan da nan kuwa fishin ya koma don na lura Yaya Sadik yana ba'kin cikin fikon da Yaya Al'amin ya yi masa.
Abin da yake ba ni mamaki kuma shine Yaya Al'amin din ya fishi girman jiki bare a ce ko don ya fi shi girma ne.
Tsawon lokaci suna zaune a falon kafin Yaya Al'amin ya ce, "Tokara ka tashi".
Ya yi kamar bai ji shi ba.
Sai da ya maimaita sannan ya ce "Atafau ba zai iya tafiya ba 'kafarsa da bayansa sun yi masa nauyi ainun sai lokacin na lura ashe 'kafarsa na'de take da bandeji irin wanda masu 'dori suke yi. Ashe wai targa'de ya yi a kafar ya kuma bugu a bayansa. Amma abin ya zo da sauki kwarai da gaske.
Al'amin ya ce "Ai kuwa sai dai na dauko baro na saka a ciki, don na gaji da kinkimarka alhalin ban huta da rashin kunyar ka ba".
Ba zato muka ji ya ware murya tamkar yaro karami yana cewa "Baba! Baba!"
A gigice Baban ya fito sanye da jallabiya Yana tambayar jikin ne, ko dai asibiti za a koma?
A shagwabe ya ce, "Cetona za ka yi a hannun Aminu cewa ya yi wai idan muka je dakinmu sai ya murtsuka ni tunda dai yau sai yadda ya yi da ni. Don haka ba inda za ni a nan zan kwanta, ko kuma ka taimaka ka kai ni wajen Umma tunda ya ce sai dai ya saka ni a baron kwasar shara"
Ya gama maganar yana murtsuka idanuwansa a zuwan kuka yake yi.
A take Baba ya rufe Yaya Al'amin da fa'da yana fa'din "Dan-uwanka ya ha'du da tsautsayi ba za ka tausaya masa ka taimake shi ba? Ban da ma da kwanansa a gaba ina ce da yanzu ba ka san irin ki'dimar da zaka shiga ba a dalilin rashinsa".
Daga ni har Yaya Al'amin mun zuba wa Gudale ido tare da ta'ajjibin irin lauya zancen da ya yi tamkar a wasan kwaikwaiyo.
Baba kuma ya hau kai ya zauna yana ta faman yiwa Yaya Al'amin sababi.
Ni ban ta'ba ganin wanda yake fatan a dauke shi idan ba shi da lafiya ba irin Yaya Gudale. Kallon sa na yi na kalli 'kafar na gano ba ciwon gaske ya ji ba, 'yar buguwa ce sai kuma kujewa da 'kafar ta yi.
Amma ya shagwargwabe ya lanjare saboda ya sani shi din 'dan gata ne ta ko ina.
Duk gidan ba wanda yake gwada iyashegensa.
Haka Yaya Al'amin ya ciccibe shi suka tafi.
Zuwa dare dukkan ahalin 'yan 'dakinsu sun bayyana in ka dauke Antin Zaria da bata 'kasar.
A bakin Sakina na ji cewar Umma ce ta 'kirasu cikin gigita ta sanar musu cewa Gudale ya hadu da tsautsayi.
Sun cika masa falon da kayayyakin dubiya tamkar masu gasa a tsakaninsu.
A wannan lokacin ba 'karamin wahalar da Yaya Al'amin ya yi ba, domin kuwa hatta alwallah sai ya yi masa wai ba zai iya ba. Bana mantawa da wannan jinyar tasa. Saboda na sha ganinsa yana tsalle idan ba kowa a tare da shi tabbacin bandejin karya ya na'de kafar da shi.
Ya fake da ciwo yana zuba shagwaba son ransa, yana kuma ganawa Yaya Al'amin da Yaya Abbas azaba ta hanyar yi masa hidima.
Tsawon sati yana jinyar iskanci, sannan ya ware bayan Abbas ya ci masa mutunci ta hanyar rantsuwar ba zai sake yi masa komai ba ko zai shi'de.
Hakan ya yi matu'kar batawa Yaya Sadik rai, domin ya tsani a daga masa murya.
Washegari kuwa sai ganinsa aka yi ya wartsake yana yin al'amuransa da kansa.
A kuma ranar suka je tare da Abba da kuma Sakina sabon gidan da ake ginawa
*Sakina*
A dalilin Sakina na samau labarin irin kuranta ginin da Gudale ya yi. Tsarin ginin ya yi matu'kar burge shi, 'katon falo ne mai dauke da dakuna uku , kowanne da ban'dakinsa, biyu a jere daya kuma a can gefe.
Kafar a benen maa falon take. Daga gefe kuma ga dinin area da kicin hadi da store.
Sannan za'a iya shigowa ta cikin kicin din. Akwai kofar baya Wanda zaka fita waje sannan anan dinma akwai kafar bene, ma'ana zaka iya hawa saman ba tare da ka shiga falon ba.
Saman kuwa dauke yake da falo da manyan dakuna biyu da kuma kicin. Tsarin ya tsaru sosai, sannan ya kawatu da mables da kuma wall papers hakanan fitilu da fentin dukkansu masu koluluwar tsada ne. Farin-cikin da Yaya Sadik ya nuna akan gidan ya sake karfafa wa mahaifinsa guiwar gabatar masa da kudirinsa.
Sakina tana gefe sai ta ji Gudale na fa'din "Ai kuwa Abba wanann gidan ya fi da cewa da 'Dan kwalisa kamar ni".
A hankali Abban ya ce "Wacce kwalisar kuma Sadik? bayan ba ka shirya nema na kanka ba, sai dai ka na'de kafar wando ka yi ya'ki da duk wanda ka ce kana bukatar abu bai yi maka ba. Alhalin guntun gatarinka yafi sari ka bani".
"Ya marairaice ya ce "Abba! Ka sani duk mai suna Abubakar ba rago bane, ba mai kwange bane, sannan ba gajiyayye ba ne.
Daure ka cigaba da yi mini Addu'a da sannu za ka yi alfahari da ni". Abba ya dara ya ce "Allah ya nuna mini wannan ranar, domin ina fatan! ka kwantata yi mini irin biyayyar da su Abdallah suke yi mini, Ni na za'ba masa matar aure ya karba babu nusu, kawo yau din nan da suka haifi yara biyu ba'a ta'ba jin kansu ba. Haka ma 'kaninsa Babangida. Madallah da Babanku Ibrahim da iyalinsa.
Har yau din nan bai ta'ba mini kallon wa nake a wajensa ba, yana mini kallon uba ne mai cikakken iko akansa da dukkan Ahalinsa.
Sakina ta ce mini dukkansu jikinsu ya yi sanyi da lafazin Abba, mussaman Gudale da yake jin tamkar *Dabaibayi*(Marigayayiyya Halima Amma Rip). Ko shagube Abba ya yi masa.
Sun fito harabar gidan suka ga fulawowiyin da za'a dasa lodi guda a gefe, nan gaba ka'dan idan aka dasa su zasu sake 'kawata gidan.
A fili Gudale ya ce, "Abba idan ka tashi yi mini gini irin wannan tsarin nake so Dan Allah. Sannan yadda wannan yake a tsakiyar filin haka nake bu'katar nawa saboda ka sani bana shiri da zafi, wannan kuwa za'a samu yalwatacciyar (ventilation) iska.
Cikin rarrashi Abban ya ce, "Ai ni ba zan yi maka gini ba, ko su Abdallah da na yi musu, ai sai da na tabbatar suna fita suna nema, sannan na yi iko da su, suka nuna mini na isa. Shin Basu cancanci na yi musu komai ba?"
"A sanyaye ya ce "Ni ma ina kammala karatun zan fara neman na kaina, sannan komai ka ce na yi , ko bana so zan yi dan kuwa ni nafi cacnanta na yi maka cikakkiyar biyayya."
Da'din kalaman suka sanya Abba cikin ki'dima ya ce "Na shaida Ubangijina ba zai juyar da addu'ar da nake yi maka ba. Alhamdulillah! Ubangiji ya sake shirya mini kai. Saboda yadda ka kyautata harshenka ina tabbatar maka na mallaka maka wannan gidan."
Sakina sai ganin Gudale ta yi akan guiwoyoyinsa yana faman godiya da fatan alheri ga mahaifin nasu.
Dadi ya sake kama Abba ya ce, " Tashi abinka, idan Àllah ya kai mu gobe bayan na karya ka zo zan sake ba ka wata kyautar da tafi wannan gidan daraja da kima. Tunda yanzu ka san godiya, na tabbatar za ka yi farinciki fiye da wanda kake ciki a yanzu, na sani za ka yi mini godiya sosai".
*Kina son canjin kayan daki, ko kina son renting din kayan amare?*
*Kina son zababbun atamfofi ko leshina?*kina son kayan a
*Kina son mallakar filin da Babu takaddama akansa?*
*Ki tuntu'bi AMYAS NEW & FAIRLY ITEMS*
*Komai kike so zaki samu*
*Ina sake tunasar da ku suna sayan kaya Kamar yadda suke sayarwa*
*08083909947*
*Dare*
*Abba*
Bayan ya kammala shan shayi, suna falon suna kallon labaran karfe 9. Ya kalli Mai dakinsa ya ce, "Zan fa'da miki in sha Allah watan jibi da kwana biyu auren Sadik da Halimatu".
A farko ba ta fahimci lamarin ba, sai ta dauka kawai had'awa za a yi a rana guda.
Don Haka sai ta ce "Wai a ina ka samo masa yarinyar ne?".
Ba wata fargabar komai ya ce "Yata Halimatu dai ta gidan nan ita ce matar".
A zabure ta tashi domin kwarai da gaske ta ki'dima.
Tsawon lokaci tana kokawa da numfashinta da 'kyar ta iya cewa, "Ni kam kana gwada mini iyakata akan 'ya'yan da ni na haife su cikin matsananciyar wahala kan wahala, ta ya ya za ka yi wannan ha'din? Indai ba don ka yi nufin na dawwama cikin ba'kin ciki ba ne. Gaba'daya 'ya'yan Safiyya maza ne, shike nan kuma yanzu Gudalen da na samu da 'kyar bayan shafe lokaci mai yawa ina addu'ar samunsa sai a sake bawa Safiyya dama a kansa?".
Ta fashe da kuka tana fa'din dama mutuwa ta zo mata kafin ta ga wannan mugun lamarin.
Ran maigidan nata idan ya kai dubu to kuwa ya baci.
Da kakkausar harshe ya ce "Saudatu! Na riga da na yanke hukunci kuma Wallahi ba canji. Ko mutuwa kika yi ba zan fasa ba, haka zalika ko ni na mutu ba za'a fasa ba, domin na barwa mutanen kirki su cika mini wannan burin.
Abin da za ki gane daya ne, wallahi idan har Sadik ya turje mini akan wannan auren tabbas ke da shi za ku bar mini gida, sai ki tafi can ki aura masa 'diyar da ta fi 'diyar Ibrahim a wajenki. Gobe zan sanar masa, ki shirya! matu'kar ya bijire mini, Wallahi ba wanda zai sa na sake zama da ku, domin ba zai yiwu na dinga sarrafa 'dan uwana da dukkan Ahalinsa ba, amma kuma ban isa, a cikin nawa Ahalin ba".
# Team Gudale.
# Team Guduyo.
# Surayya Dee.
# Ana tare 🤝.
2/8/23, 10:22 - Buhainat: *Wannan littafin na ku'di ne, biya 500 ku'din karatu ta wannan asusun*
*2384876855*
*Surayya Ibrahim*
*Zenith Bank.*
*A tura shaidar biya ta wannan lambar*
*08032773332*.
*Fitar da labarin nan laifine da yake dai dai da satar dukiya*
*Gudale dai ya ce bai zaci za'a yi masa hakan ba*
*Kuma yana hankalce da masu yin 'kafar ungulu a gidan cin kaza*😠.
*SDK25&26*.
*Umma*
Lafazinsa ya sanya kukanta tsayawa cak. 'kiyayyar Safiyya tana sake girma a zuciyarta, a take kiyayyar ta sake yin reshe tana sake shafar Halimatu. Ita da kanta ta shaida ashe a da ba 'kin Sadiya take yi ba, domin a wannan ranar da aka zartar da hukuncin aurenta da Gudale sai ta gane a ranar ta ji tana yiwa Safiya da 'diyarta Sadiya tsana fiye da komai a doron 'kasa.
Dalili 'daya ne ya hana ba zata tafi ta bar masa gida ba. Safiya ce dalilin! Domin idan har ta tafi ya tabbata ita ta yi nasara akanta. Duk wani bala'in da zai sameta a gidan aurenta ba shakka ta dalilin Safiyya ne ko 'ya'yanta, wacce irin fitina ce wannan?
A ranta ta gasgata Safiyya irin zuri'ar kara da kiyashi ce daukar marar sani. masu raba 'da da mahaifi, masu raba soyayya, kazalika masu rabaka da jama'a saboda tsananin kissa da bariki.
Cikin fishi ta tashi ta yi 'dakinta cikin matsanancin kuka.
Tana kuka tana tunanin shikenan duk tanadin gatan da ta yiwa matar Gudale ya bi iska kenan? Domin matu'kar Halimatun Safiyya ce matarsa, ta tabbatar ko murmushinta ba zata samu ba, bare aje ga samun soyayyar da take yiwa surukurta ta'kidinta.
Tabbas an cuceta iyakar cuta. Sai dai kuma ta lashi takobin yadda Safiyya ta hanata kwanciyar hankali, ta hana ta sakat itama yanzu zata sake takura mata, zata sake zafafa gabar da take tsakaninsu haka zalika zata hanata kwanciyar hankali ta hanyar saka autarta cikin uku.
Tunda bata da ikon tankwabar da auren, to kuwa zata hana kwanciyar hankali da walwala a cikin rayuwar auren, matu'kar uwa tana da tasiri akan 'danta.
*Umm Muhd collections*
*Komai da ruwanka ce fa*
*Ku tuntu'be ta ta*
*Abba da Gudale*
Washagarin ranar kuwa da misalin sha'daya na safe Gudale ya isa cikin gidan nasu, yana cikin wasi-wasin irin 'kyautar da za'a bashi da zai yi murna fiye da murnar da ya yi da aka bashi tsalelen gida ba tare da ya yi zato ba. To ko wata tsadaddiyar mota Abba zai bashi saboda tun ranar da ya yi hatsarin da bayan motar ya burma bai sake hawanta ba. Ya sani ko Abba bai canja masa ba, to kuwa lah shakka Umma da yayyensa zasu saya masa wacce tafi tasa da ta samu lahani daraja.
Ya tarar da Abba shi ka'dai yana shan shayin moringa (zogale).
Gefe kuma yana kallon tashar Africa TV 3, inda Abban ne yake gabatar da shiri akan rabon gado da hukunce-hunkuncesa.
Da walwala sosai ya dinga marabtarsa, har shi da kansa Sadik ya tabbatar akwai babban al'amarin da mahaifin nasa zai 'dora masa. Wannan soyayyar, wannan haba-habar akwai abin da zai biyo bayansu mai matu'kar nauyi.
Kusa da 'kafafuwan Abban ya zauna sosai daga kasa.
Kofin shayin ya mi'ka masa tare da cewa, "Bismilla" Cikin tarin 'kaunar da mahaifi yake yi wa 'ya'yansa.
Da azama ya kar'ba yana jin ba zai iya tuna rabon da Abba ya ba shi abin da yake ci ba. Bisa al'adarsa matu'kar ya ba ka sauran abin da yake ci to ba shakka tamkar ya sanya maka albarkasa ne.
Sau tari a gabansa Abba zai ba wa Abdallah ko Al'amin abin da yake ci ko sha amma shi ya hana shi.
Abin na matu'kar ci masa tuwo a kwarya. Ya tuna amsar da Abba ya ba shi lokacin da ya masa korafin ba ya masa irin yadda yake yi wa su Al'amin.
Kai-tsaye Abban ya ce, "Su din sun yarda sun bar ra'ayinsu sun bi nawa, sun yarda na isa da su, sun kuma amince na fi su tunani da hangen nesa akan al'amarin rayuwa. Shin ba su cancanci soyayya da albarkata a kowanne bigire ba?"
A wancan lokacin shiru kawai ya yi amma bai fahimci manufar mahaifin nasa ba, ya fi yarda son sa ne ba ya yi kawai. Don haka ya daina damuwa bare ya yi abin da suke yi na biyayya da kyautatawa.
A yau Abubakar Sadik sai ya tsinci kansa cikin nutsuwa mai yawa, irin nutsuwar da sai wanda ya yi sa'a ya kuma yi gam-da-katar din samun mahaifin da yake haba-haba da yaransa zai fahimta.
Ko zafin shayin bai ji ba, nan da nan ya kurbe tare da ajiye kofin tangaran mai dauke da sunan kamfanin Abba