Showing 105001 words to 108000 words out of 180068 words
murmusa ta ce "Yarinyar da ta biyo Sakina daga kama har siffa Ina zata yi nauyi?
Da uwarta ta dauko ne zata dame ni".
Ya dan yi dariya ya ce "Sai yanzu ma na ji haushi Umma da na nasan hakan zaki yi ta wahala da ita, da an bar mata sunan na ki".
Ta zuba masa ido ta ce "Kana tunanin zan k'i jininka dan bana son zuri'ar su Safiyya?
Kafin ya yi magana ta zarce da fa'din, "idan ina kallon yarinyar manta wa nake yi da uwarta, kawai ina kallon ta ne a jininka, na da'de ina yiwa matarka da ya'yanka tanadin soyayya mai yawa.
Tunda ban samu damar da zan nuna wa matar ka zahirin kauna ba, to babu wani abu da kiyayyar da nake masa zai shafi jininka".
Idonsa ya cika da kwallar tausayin uwarsa. Domin ya fara yarda yana son Guduyo. Rabuwa da ita kuma yana nufin tashin hankali a gare shi, domin nutsuwa zata yi masa tutsu. Kansa ya kulle kwarai da gaske. Da ya rasa abin cewa sai ya durkusa gabanta ya ri'ke hannunta ya ce "Na gode sosai Umma. Allah ya kara miki lafiya da nisan kwana."
Daga haka sai ya mike ya fice da sauri domin sosai ya shiga rudani.
Yayin da Umma ta bishi da kallo hawaye na bin kumatun ta. Bata tantamar gayya kawai Safiyya ta yi mata da Gudalenta. Tabbas ba dan Abba ba da ta nuna musu karshen gayya.
Bata son su, bata kaunar ko hanya ta hada su, amma tunda karfin kaddara tasa jinin Gudalenta sai ya hadu da nasu, to zata yi iyakacin iyawarta bata bari kiyayyar da take yiwa ahalin ta shafi yaran Gudale ba.
Amma ko yau ta samu damar da zata wula'kanta auren zata yi.
Shiyasa take fatan Abba ya yi tafiya mai nisa ta yadda zata nuna wa Halimatu kuskuren auren danta da ta yi. Amma Abba baya tafiya mai tsayi.
Ta sani kuma ta'ba auren Halima tamkar ta'ba nata auren ne.
Ta saka tissue ta goge hawayen idonta a fili ta ce "Allah ka ara mini dama, Allah ka nuna mini lokacin da zan kunsa wa Safiya da '
yarta fiye da bakin cikin da suke kulla mini".
****
Kwanaki suna ta shudewa tamkar walkiya, Kamar wasa har na kwashe kwanaki tara da zuwa gida.
Ba karamin Jin da'din zama nake a gaban mahaifiyata ba, kulawa take bani ta yadda da hali numfashi ma yi mini zata yi.
Ba abin da nake yi sai dai na shiga bandaki ta zo ta gasa mini jikina sosai, sannan abincin da nake ci ganye fa fruits ne mafi yawa saboda na samu sau'kin yin nishi.
Ko hidimar Amna bana yi tunda idan aka Kai wa Umma ita tun safe sai azahar. Nono kawai zan bata Mama ta cigaba da rainon ta. Ko da daddare barci nake sosai bana sanin me Mama take ciki da jaririya sai rikicin nata ya tsananta ne zata tashe ni, da zarar ta koshi kuwa zata ce na kwanta na huta ta fice da ita.
Bana aikin komai, a dalilin tausayina da take ji, gma dalilin lokacin haihuwa ta ba karamin wahalar tiyata ta sha ba, bata san c.s ba kamar operation bane.
Zuwa lokacin kuma ciwon nawa ya ha'de sosai kiris ne bai warke ba, aikin ya yi kyau.
Hutu da nutsuwar zuciyar da na samu ya sanya na yi wani irin kyau, na motse sosai, duk wani kumburin da na yi ya sace, kirjina ya sake cika.
Ni da kaina na sani na murje na yi kyau.
Mussaman da kullum Yaya Gudale zai shigo ya duba ni safe da dare, muyi hira cikin nutsuwa.
Ga Kuma *Aisha lame* da baibaye ni da mayukan oriflame na alfarma da fata take sake zama ta kasaitattun mata. Har da wani hadadden seti na tsarki. Wanda ba karamin Jin da'din su nake yi ba.
*07036662633*.
Da daddare ya iske ni a dakina, na yi fes da ni, dakin sai kamshi turaren wuta yake yayin da nake kamshin turaren Al haramain Madina.
Da walwala ya ce "Tana ina?"
Na murmusa na ce "Wai Yaya Gudale kunyar fa'din sunanta kake yi ne?
Na ce maka Amnah Antin Zaria ta sanya mata. Anti Sakina kuma ta ce Ablah, sai ka zabi wanda yafi kwanta maka."
Ya yi murmushi ka'dan ya ce "kunyar 'yar fari nake yi, kada ace bani da kunya. Kinsan ban taba jin Umma ta fa'di sunan mai sunanta ba, haka Mama ban taba jin ta gatsa sunan Yaya Abdallah ba."
Ya bani dariya sosai na ce "To ai su mata ne, ko baka ga su Abba suna fa'din sunayen su ba?"
Ya ta'be baki ya ce "To ke ai ba kya kunyar, shiyasa ni nake yi. Kullum ki tasa ta a gaba kina kallon da baya kare wa nan gaba manta wa zaki yi da ni tunda kin samu 'ya.
Na sake yin dariya na ce "Hoh Yaya Gudale".
Ya yi kicin kicin da fuska alamun seriousness ya ce "Guduyo yau kwananki tara".
Zuciyata ta tsinke a dalilin kwanakin da na diba zasu cika nan da kwanaki uku.
Na kasa cewa komai amma na yi matu'kar razana.
Ya jima yana nazarina ya numfasa ya ce "Yanayin ki ka'dai ya fahimtar da ni, kin shirya yaudara ta ne. Wato kin fi jin da'din zaman ki anan akan zama da ni?"
Da sauri na girgiza kai na ce "Ba hakan bane Yaya Gudale! Ka fahimce ni dan Àllah. Ciwona bai kame gaba'daya ba, sannan duk wacce za'a kai mini ta zauna da ni, ba zata kai Mama kulawa ba. Ka yi hakuri na yi sati uku plz Abban Amnah".
Na fa'da da sigar rarrashi da shagwaba.
Ya mike tsaye ya kafe ni da kallon da yake ki'dima ni.
Ya kankance ido ya ce "Uban Amna zaki ce, ba Abbanta ba. Na rantse miki da girman Ubangiji idan kika canja mini magana to tabbas nima kuwa zan zarta da kudirina. Ni zaki mayar dan iska Guduyo?"
Na yi kasa da kaina na ce "Shikenan ka huce! zan dawo gatan".
A fusace ya ce "Ba ni wasu daga cikin kayanki na fara yin gaba da su".
Na ce "To".
Na nuna masa wadanda bama amfani da su.
Ya dauki bedsheets ya zuba ya daure.
Ya sake zuba mini ido yana kuma murza yatsunsa alamun kashedi.
Murya a kaurare sosai ya ce "Billahillazi Guduyo idan kika saba al'kawarinmu komai zai faru a tsakaninmu. Na fa'da miki gaskiyar magana kenan".
Ya kinkimi uban kayan da ya daure su da kyar.
Na kwanta na yi lamo. Abin duniya ya taru ya mini yawa. Ta yaya zan kalli idon Mamana na ce mata zan koma gidana?
Wa zan fa'da wa ya fahimce ni.
Wata zuciyar ta ce mini Abba.
To idan Abba ya hana ni koma wa, ta hanyar tsawatar masa shin ya zan yi da hukuncin Gudale? Idan ma bai sallama ni ba, to babu shakka sai na hadu da kalolin fishinsa masu tayar da hankalina.
Na sauke nannauyar ajiyar zuciya lah shakka zan yi komai dan na tsira da auren Gudale.
A fili na ce "Allah ka kawo mini agaji".
A haka barci ya kwashe ni. Da safe ya shigo muka gaisa kamar kullum. Ya kalli Amna a hannuna har ya dan yi mata wasa, sannan ya tafi wajensu.
Haka na yini ina tufka da warwara. Da daddare sai gashi ya sake dawo da bedsheet din, ya sake jidar wasu kayan.
Washagari kuwa yinin zullumi na yi ta yaya zan iya yin wannan danyen aikin a gobe?
Shi kuwa ko a jikinsa domin a gaban Mama ya fita da wasu kayana da ya ya daure da zani.
Da tambaye shi ina zashi da kaya ya ce wanki zai kai, sai ta gamsu, bata sake bi ta kai ba.
Kafin wayewar gari duk na hargitse na susuce gaba'daya na zama wata iri abin tausayi. Da ya shigo cikin Shirin tafiya office, ya kalle ni ya ce "Zan dawo da rana na tarar kin koma ne, ko kuwa?"
Na yi sororo na kasa bashi amsa. Ya sassauta ya ce "Na fa'dawa Abokiyar aikina ta yiwa mai kawo musu yan aiki magana ina so.
Kin ga zata taya ki ayyukan gida da raino duk da dai jaririyar zata fi zama wajen Umma ne. Kuma yau din nan ta ce mini an samu yarinyar tana gidanta, shin na dauko miki ita yau ko sai gobe?"
Baki na rawa na ce "ka barta kawai sai jibi. Sai da daddare zan koma idan Mama ta tafi kai wa Baba abinci".
Ya daga kai cike da gamsu wa. Ya sunkuyo ya bani peck a dukkan chicks dina.
Tare da cewa *"Thank you my Hala love".*
Ya fice ya bar ni da tararrabin wannan rashin mutuncin da zai sa ni yi.
Na sani cikin supplements din *Fasilat* da nake sha har da wanda yake daidaita jikin mace ta yadda kitse marar amafani yake zagwanyewa cikin gaggawa. Amma zullumin da nake ciki ya sake taimakawa wajen sake zubewata.
*Shin kina gyara kanki kuwa?*
*Shin kin jarraba kayan G.H.T?*
*Idan kina fama da basir, infections, da ulcer ga magani ya zo miki cikin yardar Allah*
*07039269802*.
Har Bayan sallah isha na kasa tashi na tafi. Ina cikin wannan yanayin sai sallamar Abida na ji yar kanwar Umma ce ta zo daga Yola. Ba jima wa sosai ta shigo dakina ta ce "Wai na bada Amna in ji Ummah".
A sanyaye na nuna mata karshen gado inda take kwance.
Na sani kuma ba Umma ba ce ta aiko ta ba.
Yaya Gudale ne. Basu fi mintina ashirin da fita ba, ya fara kiran wayata ba kakkauta wa. Na dauka, ga mamakina sai ya sassauta murya ya ce."Ran autar gidanmu ya dade kamar tuwo"
Dariya ta subuce mini, na ce tare da naka Yaya Gudalen Umma da Sakina".
Ya lankwashe harshe ya ce"
"Muna ta jiran ki, ni da Bebinki fa. Ko na zo mu taho tare?"
Na girgiza kai na ce "Ba sai ka zo ba, kawai ka jira ni a kofar garden."
Ya ce "Tom " tare da katse wayar.
Ina zaune ilahirin jikina bari yake yi mussaman kafafuwana, ga fargaba mai yawa. Duk sanyin da ake yi sai da jikina ya dauki dumi.
Kusan awa guda ina zaune na kasa tashi, bare na tafi, gaba'daya kaina ya kulle.
Bana son wannan tsarin, amma kuma cike nake da tsoron abin da zai biyo bayan bijire masa.
Kafin na yi wani abu wayata ta hau kuwwa.
Ganin shine sai da zuciyata ta sake tsinke wa. Na dauka na kasa magana a dalilin yadda harshe na ya yi mini nauyi.
Cikin fishi ya ce "Kin ga Halima zaki dawo ne ko kuwa na koma cikin gida? Ya zaki jingine ni, sauro yana ta cizona sama da awa guda amma kin kasa fito wa".
Murya na rawa na ce"Na kasa tashi ne, jikina rawa yake yi Yaya Sadik".
Ya yi shiru domin ya sani idan har na ce masa Sadik to ina cikin yanayi mai nauyi da nake bu'katar uzziri ko sassauci.
Ya nisa ya ce "me ya kawo miki barin jiki da wannan zullumin?"
Da sauri na ce "kunyar su Mama da tsoron fishinka".
Shi ma da sauri ya ce "Bar shi a kunyar dai domin na gamsu da hakan, amma ban gamsu kina tsoron fishina ba, da hakane da tuni kin da'de da dawo wa.
Wallahi Halima! Kin ji rantsuwar dan musulmi ko? To yau a gidana zaki kwana matu'kar da aurena a kan ki.
Bana magana biyu".
*Na ce ba? Kinsan wani hadi da ake yi wa asalin man ridi da kwakwa da ba'a samun original din su sai a wasu kebantaccun jahohi?*
*kina fama da matsalar cinyewar gashi ko kuma rashin tsayinsa?*.
*Kina neman ha'din da da zai sanya fatarki laushi da sulbi, kuma cikin saussaukan farashi? Tuntu'bi wannan lambar dan samun naki cikin sau'ki. Kaya mai inganci shi yake siyar da kansa.*
*Sister Zainab 08039315577.*
# Team Gudale.
# Team Guduyo.
# Surayya Dee ✍️
# Ana tare 🤝.
2/8/23, 10:25 - Buhainat: Ina masu neman kasuwanci da zasu yi daga cikin gidan su??
Oriflame suna ba ma mutum damar tafiyar da kasuwanci a duk inda yake a fadin duniya
Kungiyar mu ta The BBMs Goal Achievers za su gabatar da training ga wadanda suke da sha'awar fara kasuwanci su da Oriflame a kyauta
Kyautar register da Oriflame daga daya zuwa bakwai ga watan Janairu (1-7)
Oriflame na da kayayyakin kula da fata, kwalliya,turare da supplements, maganin infection da sauran su
Abun da ake bukata shine iya jarin fara kasuwanci ki sai kuma zuciyar jajircewa da hakurin neman na kai
Hanzarta kiyi magana ta nan 07036662633.
*Cikin fuwacewar Ubangiji na samu na yi wannan, na gode da uzzirinku*.
*SDK*
*65&66*
Jin hakan ya sanya na mi'ke na sanya hijabi na na fito na leka dakin Mama cikin sa'a tana bandaki tana wanka.
Da sauri na fito ko rufe mata kofar ban yi ba.
Na doshi hanyar waje cikin matsanancin
Ina kofar garden din kuwa, yana tsaye tamkar gunki.
Ina jin ajiyar zuciyar da ya dinga saki.
Ya rike hannuna ya rufe kofar muka shiga cikin gidanmu. A falo muka yada zango.
Na zauna hawaye ya goce mini. Ya kalle ni tsawon lokaci ya kasa cewa uffan tabbacin kukan da nake na sharbe ya ta'ba shi.
Ya yi gyaran murya ya ce "Kina nufin ba'kin cikin dawowa gare ni har ya yi tsananin da zaki dinga irin wannan kukan mai dafa zuciya?"
Na kasa cewa uffan, sannan hawayen ya ki tsaya wa.
Ya sassauta ya ce "Ban yi miki hakan da nufin takura ko zalunci ba. Hakan shine kwanciyar hankalina, na tsani na shigo gidan na ga ba kya nan ko ban ji motsin ki ba.
Ni ka'dai na san halin da nake ciki a dalilin rashin ji ko ganin motsin ki. Kema kuma shaida ce tun kafin mu yi aure bana son ki yi mini nisa. Yanzu Kuma cike nake da fargabar kada Abba ya sake ri'ke mini ke".
Ganin ban daina kukan ba ya sanya ya matso gare ni sosai ya rungume ni yana bubbuga bayana ya ce "Ya isa hakan idan ba so kike na gamsu zama da ni ne ba kya marari ba. Zan fada miki gaskiya ko ba zamu yi magana ba, nafi son na gan ki a tare da ni, wulgawar ki ka'dai tana saukar mini da nutsuwa. Ban dawo da ke dan na musguna miki ko dan na yi miki sanadin bacin rai ba. Haka nan ban yi dan na ci mutuncin iyayenmu ba, na yi ne dan na samar wa kaina nutsuwa da aminci. Na kuma nuna wa kowa irin yadda nake son ki nake kuma da iko akan ki.
Amma ke sai fama kike da kunci da bacin rai, shin gidan bariki na kira ki, ko kuwa gidan raya sunnar Ma'aki?"
Ya yi shiru yayin da hawayena ya tsaya cak illah ajiyar zuciya da nake ta saki a jere.
Ya sake ri'ke ni sosai ya ce "ki toshe kunnan ki, kome za'a ce kada ki damu, kin nuna mini soyayya, kin bi umarnina, na yaba, na kuma gode miki. Duk wanda ya tare ki da nufin yi miki raddin kin dawo da kan ki, ki fa'da musu umarnina kika bi, Allah kuma ya yaba miki domin shi ya wajab ta miki yi mini biyayya.
Tashi ki wanko fuskarki, ki zo ki ci kazar da na siyo miki.
Na kasa tashi, da kansa ya mikar da ni ya kai ni har ban'dakin ya tallafa mini, na dinga jin farin-cikin yadda ya ke tarairaya ta sai dai kuma zuciyata ta yi nauyi kwarai da gaske.
Muka dawo falo, da kansa ya dauko plate, ya ha'do da flask din tea da duk abin da zan bu'kata dan ha'da shayin nan.
Karon farko da naga yana mini abu na bauta ba dan yana bu'katar na yi masa wani abu in return ba.
Ya zauna ya kalle ni ya ga idona cike da hawaye.
Ya saki nannauyar ajiyar zuciya ya ce "oh my God! Wai menene matsalar ki?
Waton kin fi jin tsoron cece-kucen mutane akan bacin raina?"
Na girgiza kai na ce "kunyar Baba da Mama nake ji, na fito na dawo dakina basu sani ba, wanne irin kallo zasu yi mini, ya Abba zai kalle ni? Alhalin dama ya ce mini bani da kunya, yanzu ne zai tabbatar da rashin kunyata".
Na fa'da ina rushe wa da kuka sosai. Kukan da na rusa ya yi sanadin tayar da Amna a bacci.
Da sauri ya janyo ta, karon farko da ya dauke ta.
Ya dora kafadarsa, sai dai kallo daya zaka yi ka gane bai iya daukar jarirai ba da gaske, saboda yadda ya damke ta tamkar za'a zo a warce ta.
Ya dinga zagaya falon da ita.
Amma fir ta ki yin shiru. Na bu'de baki na ce "kawo ta".
Ya kuwa iso da sauri tabbacin dama so yake na karbe shi.
Ina fara shayar da ita kuwa ta yi shiru, yayin da shi kuma ya dinga rarrashi na, har da sanya hannu ya goge mini hawaye.
Cikin sigar rarrashi ya ce "Bari na je na wanke ki a wajen Mama da Baba ni kunyar ta kashe ni. Idan na yi hakan shikenan zaki daina mini wannan koke-koken?"
Na daga kai da sauri.
Ya mi'ke da azama ya fita.
*Falon Baba*
Kamar jifa haka Baban Yara ya ga Gudale ya shigo masa falo yana zaune yana kallon labaran tara a N.T.A .
Ya kalle shi ya ce "Koma ka mini sallamah".
Ya juya yana kunkunin a daina yi masa abu kamar har yanzu bai girma ba.
A fili Baba ya ce "Allah dai ya shirya ka Sadik".
Labule ya daga ya sake shigowa bayan ya ce "Assalamu alaikum" a hanzarce.
Ai kuwa Baba ya ce "Ka sani ai matu'kar ba zaka tsaya na baka iznin shigo wa ba, ba zan saurareka ba, tunda na sani kana yin irin wannan iyashegen ne idan kana cikin gaggawa".
Ya sake juya wa yana cewa "A gaskiya Baba kana sake tsananta wa, da dai baka yin haka, dabi'ar Abba ne yin hakan da baka yi koyi da shi ba.
Assalamu alaikum ya Babati! Sadik ya shigo?"
Ya fa'da da 'karfi.
Sadik ya shigo"
Baban ya fa'da cikin murmushi sosai. Har cikin zuciyarsa da jininsa yake jin Sadik. Sannan tabarar da yake yi masa tun yana yaro karami bai bari ba, ya dade da gane Sadik yana zama yaro kankani idan yana gabansa, sannan yafi sakewa a gabansa fiye da gaban mahaifinsa.
Ya durkusa a gabansa sosai, ganin hakan da ya yi ya alamatar da Baba akwai babban al'amarin da zai gabatar masa.
Kansan a kasa ya ce "Baba kasan dai Ni mutum ne da bana son ana takure ni. Amma shi Abba ya na'de kafar wando sai ya nuna wa Iyalina dukkan raunina akasu bayan tun