Showing 114001 words to 117000 words out of 180068 words
a yanzu ri'ke dubu daya wahala take yi mini. Gudale ya rufe bakin aljihunsa, komai na amfani ina da shi, amma fa babu kudi a hannu. Ko Abba ne ya bani ku'di ko Yaya Abdallah, ko kuma Baba ya bawa su Amnah kudi matu'kar ya kyalla ido ya gani, to kuwa sai ya san yadda yayi ya karbe su da sunan rance. Bansan meyasa ba yake ba'kin cikin ya ganni da ku'di.
Tun Sakina tana mini fa'dan na daina bashi tunda duk wanda ya zo gidana ba zan iya bashi kyautar kudi ba. Sai dai ko kayan kwalliyata zan na diba na bayar, suma da suka k'are na koma cewa a gaida gida.
Su Anti Maimuna suka fara raddin rowa ce da ni, su zo gidana da yara amma ba zan iya kyauta ko ta allura ba. Ai sun san ba hakan nake yiwa dangin uwata ba.
Wadannan matsalolin da suka kewaye ni ya sanya na yi murnar aikin ba ka'dan ba.
Nan da nan kuwa Gudale ya ci layar shifa ba zan yi aiki ba.
Na kafe sai na yi, rikici har gaban Abba.
Ya kuwa fatattake shi ya ce "Kana da son zuciya Sadik! Ina ce dukkan sisters dinka aiki suke yi. Ko Ummu da bata aiki kasuwanci take yi mai karfi, akan me zaka hanata bayan komin yaya kaima sai aikin ya taimake ka?"
"Abba kowa da ra'ayinsa ni fa ko makarantar nan da kyar na ha'kura ta kammala. Ni fa tashin hankalina na dawo ban ganta ba. Ni gaskiya bana so. Menene bana ajiye mata? Bayan siyayyar da har yanzu kana yi mana duk watan duniya Abba. Nima Ina yi gata nan a zaune ka tambaye ta. Ni gaskiya nafi son ta zauna a gida ta yi aikin tarbiyar yara. Ni kuma na fita na nemo, amma ba zan iya wannan al'amarin ba."
Abba ya murmusa ya ce "Sadik manya, wato na da'de banga yaro mai akidar rikau irin ka ba. Aikinta na ceton rai ne, shiyasa muka karfafa ta yi karatun dan ta taimaki al'umma mussaman yan uwanta mata. Yanzu kuma ka zo da wani maganar banza, na baka umarnin ka barta ta yi aikinta".
Tunda ga lokacin muke cikin rashin nutsuwa domin ya ja kafe shi ba zan yi aiki ba, mussaman da yake zargin Yaya Ashir ya taimaka wajen samuwar aikin.
Yayin da nima na kafe zan yi aikina tunda ina so, ina kuma da bu'kata.
A wannan sadarar ya sake birkice mini abu ka'dan zai ha'da mu, zai zabga mini mari, ko a gaban su Amnah ne.
Idan ta ga ya mareni din nan idan da safe ne ko rana idan ta ta fice to sai an yi kwanaki bata leko ba.
Idan ta je ta dinga rawar jiki tana cewa Ummah "Daddy ne ya doki Mummy".
Yayin da Umma take Jin da'din hakan tana sake samun nutsuwar ban fi karfin danta ba, ban halaka shi ba.
Ba kuma ta ta'ba nuna masa ma ta sani ba, bare ta tsawatar masa.
Sati biyu da fara zuwana aiki tashin hankalin da yake mini ya tsananta.
Domin ya riga, ya kudire tunda an masa karfa karfa to lah shakka ba ni Jin da'dinsa.
Wani mari da ya yi mini daga maganar fatar baki sai da jini ya kwanta a gefen idona ga yatsun hannunsa a ru'du ru'du a fuskata.
Ya fice ya barni ina wani irin kukan da shi da kansa ya taba shi kwarai da gaske.
Daga na ce masa ya daina fishi tunda ban yi masa komai ba, ya daina tayar mini da hankali haka nan.
Shikenan ya mini wannan barin makauniyar tsananin gigitar da na shiga a wajen na zube na fashe da wani irin kuka ina fa'din "Allah na tuba, na sani musun da na yiwa Abba da Mahaifiyata ne. Allah a sassauta mini haka nan".
Ai kuwa ya tsaya cak, tabbacin maganar ta shige shi ainun.
A sanyaye ya bar gidan. Na jima ina kuka Afrah da take rarrafe ta rarrafo ta kwanta a jikina. Hakan da ta yi kuka ya sake goce mini.
Na tuna dazu da na shiga wanka ta dinga tsala kuka amma ubanta yana jin ta yana ganin ta bai kula ba.
Ko a zaune muke a falo duk wasan da zata yi ba zata taba rarrafa wa wajensa ba.
Tausayina da nasu ya kama ni, na fara nadamar kafewar da na yi sai Gudale. Na dinga ganin wautata da na yi zaton zan iya sauya shi.
Na jima ina kuka, sannan na sunkuci y'ata na shiga kicin da yafi kusa da ni. Na wanke fuskata na dawo falo na zauna ina shayar da ita, ina ta sakin ajiyar zuciya.
A hakan Sakina ta turo kofa ta shigo. Ganin ta zuciyata ta nemi karye wa. Amma na tattaro dukkan jarumta na ha'diye kukan.
Muka gaisa tana bina da kallo. Ta kasa hakuri ta ce "Yanzu Na Moriki ne ya miki wannan marin amma da yake ke jaka ce kika na'de kafar sake zama da shi, har kina shayar masa da yarinyar da baya gode miki hidimarta?"
Idona ya ciko taf da k'walla ina jin bai kamata Sakina ta gane na kasa wanke allon nawa ba.
Na ha'diye kukan na ce "Faduwa na yi na bugu a gefen idon ai sa'a ma na yi."
Wani irin fishi na ga ni a tare da ita.
Ta mike ta ce mini "kazar ubanki da wannan maganar Halimatu". Hawaye ya kwace mata ta ce "Zaki zauna ya kashe ki ne? Bayan hawan jinin da kike fama da shi, shine kike son sai ya manna miki ciwon zuciya? Ni zaki kallah ki ce mini faduwa kika yi? Shin wannan shatun yatsun na uban waye a fuskarki?"
Na yi kasa da kaina na ce "zafin da ya gigita ni ne na mari kaina ban sani ba."
Ai kafin na rufe baki kawai ta rufe ni da duka, tana yi tana danna mini ashariyoyi kala kala.
Daga karshe kuma sai ta rungume ni tana fashe wa da kukan da ban ta'ba ganin ta yi irinsa ba.
Hakan ya sanya nima nake kukan da na dade ina son yi a kafadarta ina boye wa dan kada na kunyata.
Tsawon lokaci muna kukan ba Wanda ya rarrashi wani. Sai ita ta yi karfin halin tashi ta dauko mini hijabi, ta miko mini bayan ta dauke Afrah da ta yi barci.
Ta ce "Tashi mu je Abba ya ga wannan dabbacin masoyin na ki".
Na daure fuska sosai. Na ki yin ko da motsi. Juyin duniya na ki tashi, da ta bude mini wuta na ce mata "Ba inda zani sai na gama aikina.
Ta ce "Ina Atika?"
Na sake bata rai na ce ta tafi garinsu.
Ganin yadda na ha'de rai, sai ta shige dakina ta shimfi'de yarinyar ta dawo ta ce "To tashi na taya ki aikin".
Sai da muka kammala tas.
Na yi wanka zuwa lokacin jini ya sake kwanciya sosai a idona.
Ga mamakin Sakina da ta ce "Na tashi mu tafi".
Na murtuke na ce" bansan wannan maganar ba, ni na riga na yafe masa".
Ai kuwa ta mike jiki na rawa ta ce "Wannan kuwa shine karya Halimatu. Ni zaki yiwa irin wannan iyashegen? Ki sani aikin da ko a gidana bana yinsa dan kawai mu tafin, mun gama kin yi wanka sannan ki ce ke ba inda zaki je. Na rantse miki zan yi miki duka, ko kuma na kira Abban ya zo ya same ki anan tunda bai isa ki je masa da damuwarki ba, shi sai ya zo ai tunda baki da kunya da mutunci".
# Team Gudale
# Tewm Guduyo
# Surayya Dee ✍️
# Ana tare 🤝.
2/8/23, 10:25 - Buhainat: *SDK*
*69&70.*
Jin hakan da ta ce "Na zube na rike mata kafa ina kuka ina cewa ta yi ha'kuri ta taimke ni. Idan Abba ya ji kashe mini aure zai yi".
Wani irin matsanancin tausayina ya danneta ta zauna kan gadon ta sake fashe wa da kuka. Ta yi iyakacin yin ta. Ta tashi ta wanko idon ta a bandaki.Ta tsaya ta kalle ni ta ce "Ba zan ta'ba iya wannan ha'kurin na ki ba. Soyayyar da kike yi ta wuce ka'idojin hankali. Ha'kuri a irin wannan k'adamin cutar wa ne Halimatu".
Ta daga kai ta numfasa ta ce "Allah ka sassauta mata wannan jarabtar, Ubangiji mun sauke nauyin zumunci, Allah ka kawo mata mafita."
Hawaye ya balle mini, haka kawai nake jin Soyayyar Sakina tana bin dukkan jikina. Ina jin ta fiye da yadda nake jin Yaya Al'amin.
Na goge idona da tissue ina fa'din "Na gode! Ki taimake ni kada ki fitar mini da wannan sirrin, dan Allah".
Ta girgiza kai ta ce "To! Amma ban miki al'kawarin wataran ba zan fa'da ba."
Tana shirin barin dakin ya shigo. Ya tsaya yana kallonmu kowanne da k'walla a idonsa, jikinsa ya sake mutuwa. A sanyaye ya ce "Sakina me ake tattauna wa ne, ke da yar dakin naki?"
A banza ce ta ce masa takaici da bakin ciki".
Yayin da ni kuma na ce "Sannu da dawo wa".
Nan da nan ya samu kwarin guiwa ya ce "yauwa Gudidina ai ina ta kiran wayar ki, na ji me zan taho miki da shi, rashin daukar da baki yi ba, shine na dawo, na ga ko lafiya?".
Na murmusa na ce "Da na je gyaran sama ne, na manta ta a can, ka yi ha'kuri ban ji ba ne".
Sakina ta sandare, tana kallon ikon Allah.
Ta juya ta tafi, amma tamkar ta shake ni.
Sai da taje bakin kofa na ce "Anti Sakina na gode, sai mun yi waya. Bakin cikin abin da na yi ya sake turmushe Sakina, mussaman ha'kurin da na bashi, da kuma rashin biyo ta da nufin taka mata.
Ina rufe baki ta dawo a hankali, tamkar ta yi mantuwa sai kawai ta shammace ni ta sakar mini rankwashi mai zafin gaske a tsakiyar kai, tare da dungure kan ta ce "Shasha kawai".
Cikin kasala Yaya Gudale ya ce "A gabana Sakina? Ki fita a idona fa".
Yanayin yadda yayi maganar ba karsashi ya tabbatar mata a tsorace yake. Ta nuna shi da yatsa ta ce "Na rantse Na Moriki idan ka sake kama sunana yanzun nan zan yi maka sanadin da zaka wula'kanta, ka ga iyakar iyashegenka. Idan kuma ka musa sake bu'de baki ka mini magana! Mugun bawa azzalumi kawai".
Sanin idan ya tanka mata kwabarsa ce zata yi ruwa sai ya yi mukus, ya buge da fadin "Afrah barci take yi ne?".
Abin da bai ta'ba tambaya ba kenan ni ban yi zaton ma ya rike inkiyar tata ba.
Tsaki Sakina ta yi ta ce "munafiki, marar ragayya".
Ta dan dakata ko zai yi magana, amma sai ta ji tsit.
Ta girgiza kai ta tafi. Tana tafiya ya saki ajiyar zuciya mai karfi ya ce "kinsan bata nufina da alheri, na sani ko baki ce mata komai ba fuskarki ka'dai ta isa dalilin da zai sanya ta ya'ke ni, ta kuma kai ni kasa. Na sani tana son ki da dukkan zuciyarta. Amma ki sani bata kai ni a wajen ki ba. Sannan duk damuwar da zata yi da ke, na ninka ta, haka nan son da nake yi miki ya wuce misali, ya wuce irin wanda take yi miki. Ni da kaina ban ji dadin yadda marin ya shige ki ba, In sha Allah na daina dukan ki. Na gode da hakurin ki a kaina, na gode sosai da soyayyarki".
Sai da ya lallaba ni, ya kusance ni, a haduwar kuma sai da ya tafi da kaso saba'in na bacin raina. Da muka nutsu, muka yi wanka kuma ya kwashe ni muka fice, bayan ya dauko ya Amnah. Ya din ga yi mana siyayya ba ji, ba ga ni.
Afrah na sabe a jikinsa. Karon farko da ya dauketa, haka Amnah yana ri'ke da hannunta.
Ya dinga nan da nan da ni, hakuri yake bani duk da dai bai furta ki yi ha'kurin kai tsaye ba.
Amma komai nasa ya nuna nadama da neman afuwa.
Bamu dawo ba sai dare domin sai da ya wuce da mu wani hadadden restaurant muka yi dinner sannan muka dawo.
Ya gama parking kenan Sakina ta leko harabar gate din mu. Na fito daga mota na karasa wajenta ta ce "Kin je ya kalallame ki ko? Gobe ma zai sake yi miki, tunda ke ba zaki dauki mataki ba".
Na dan bata fuska na ce "sai ya jiyo ki ya zaci kamar na fa'da miki wani abin ne?"
Ta kame bakinta da sauri ta sandare tana kada kai a matu'kar razane.
Ya yi wucewar sa bai ko kalli inda take ba. Yayin da Amnah ta yi wajenta tana cewa gun Umma zan biki".
Itama ta yi tafiyarta bayan ta ri'ke Amnah tana cewa "Ni dai ban ta'ba ganin Halima sakarya ba sai akan ki.
Mafi yawa masu suna Halima jarumai ne, masu mutuntata jama'a, sun kuma san ciwon kansu, basa yarda da wulakanci haka siddan.
Amma ke kam sai na tashi tsaye akan ki, al'amarin naki akwai ban mamaki kwarai da gaske.
****
Tun wannan marin da ya yi mini, da irin sassaucin da na yi masa, sai muka sami sau'kin rikici. Duk da dai wani lokacin zai iya kwanaki yana mini yar shariya, sama sama.
Samun aikina ya zo mini da abubuwa guda biyu.
Da farko matsalar rashin ku'di ta kau mini domin bai taba kallon ku'dina ba.
Sai dai me? Bani da sukunin zuciya a dalilin rashin walwalar Yaya Gudale, domin ya matu'kar kyamaci aikin. Zamanmu ya koma wani iri, gaba'daya babu da'di a yanzu har wata jarumta ya koyo, ko kuma maganin barci yake sha oho? kullum dare karfe tara tana yi idan ya fara barci sai asuba.
Idan ya karya ya fice sai dare zan ganshi tunda ni sai yamma nake dawo wa.
Kwata kwata ya yanke duk wata hulda a tsakaninmu. Idan tura ta kai bango ne zai nemi hakkinsa. shima babu nisha'di irin na da. Duk wani styles da lashe lashen da yake ki'dima ni da su ya daina.
Babu fa'da, amma kuma babu kwanciyar hankali, babu walwala ko ka'dan.
Na fara ramewa a tsaye, na fara susuce wa. Hatta a asibiti an lura da rashin nutsuwar da nake ciki. Na dinga kewar zamanmu na watannin baya.
Duk iyashegen da yake yi mini gara wanccan zaman akan wannan.
Muna cikin haka na yaye Afrah.
Har na yi zazzabi da ciwon nono na warke bai sani ba, bare ya mini sannu.
Ba'a jima da yayen ba ya fara irin zazzabin da yayi a cikin Afrah. Marurai suka ce mu je zuwa.
Rannan ya tubure mini idan nasan ciki ne da ni ba zai yarda ba, domin ba zai sake yarda ya sha azabar da ya sha wanccan karon ba. Tunda na riga na tabbatar masa ba'a fara haifa masa yara mata ba. Ya sani yanzun ma macen zan yi ta rokon na sake haifa tunda ya lura cikin ruwan sanyi nake yak'arsa. To wadannan din dana haifa sun ishe shi.
Na yi shiru ina sauraron nishinsa. Bayan ya gama maganganunsa, da alamun kuma yana jin jiki ba ka'dan ba.
Na rasa me zance sai kawai na zabi na fa'di gaskiyar magana. Na sassauta na ce "Ciki ne da ni Yaya Sadik shiyasa ma na yaye Afrah. Wata uku kenan."
Ya yi shiru amma ya tunbatsa da fishi. Ya kasa magana. Ya girgiza kai ya ce "Kina musguna mini Guduyo! Amma babu damuwa, na zuba miki ido ki cigaba da bijire mini, saboda kawai Abba ya damka ragamar aurena a hannunki. Na ce bana son aikin da kike yi, amma anki a saurare ni. Yanzu kuma kin yi mini k'ofin duk sanda kike da ciki sai na shiga tasku mai yawa. Abin da na sani bazan sake d'aga miki hannu ba, tunda idan na dake kin ma, na fiki shiga tasku, amma zan dauki matakin wannan abin da kuke yi mini."
Haka ya dinga jinya sosai a wannan karon har muryarsa sai da ta dashe.
Bai samu kansa ba sai da cikin ya shiga wata shida.
Watarana ya fito ya tarar da ni ina cin indomie da naman kaza Afrah tana gefena ina bata.
Ya tsaya ya kare mu da kallo Ba'kin ciki ya shake shi a dalilin tunda na samu cikin kuma aka haramta masa cin kaza, duk da ya samu lafiya, amma shi da nama sai kallo. Ya sha rufe ido ya ci, yana gama wa kuwa zai yi ta sheka amai.
Har aka kai jallin ko ganin ta ma ya ha'kura da yi.
Ya nisa ya ce "Idan Ubangiji ya ha'da mutum da mace irin ki Guduyo tabbas nau'i ne na azabar duniya.
Na da'de da gane ke din maketaciya ce ta gaske. Na ta'ba ganin wanda yake yiwa matarsa lififin ciki a duniya kuwa?
Wallahi tunda uwata ta haife ni ban taba ko ji ba, bare na ga ni. Amma na gasgata Umma da ta ce "Kina neman kassara ni, ta yadda zan zaci duk mata hakan suke yiwa mazajensu wannan mugun fatan ta yadda zan tsorata da su.
Amma ai an gama, ba sai na sake yarda kin yi cikin ba, bare ki yi ta gana mini azabobi iri iri".
Ya fice na bishi kawai da ido. Bakin ciki da dariyar yadda ya susuce ya birkice ya sanya na dinga dariya ina k'yak'yatawa.
Abin da sani na kuma kudire wa raina ko wanne bala'in zai yi ba zan yi tsarin iyali ba. Tunda Umma bata son na haihu da yawa, to kuwa idan zan samu dama duk shekara sai na dire mata jika har sai ta gamsu duk tijararta bata isa hana Allah zartar da ikon sa ba. Sannan ko ta yi nasarar raba ni da danta to na bar mata rundunar da a kullum yaumin sai ta tuna ni, ta ji ciwo a zuciyarta mai kullaci.
****
Dakin Umma.
A zaune ya tarar da ita akan kafet din gaban gadon Amnah na gefenta tana cin cheese.
Tana ganinsa ta takure sosai, sai da ya zauna ta ce Dady "Ina kwana?"
Ya amsa a takaice.
Umma ta ce "Je ki wajen su Dala ki jira ni"
Ai kuwa ta fice da sauri dama so take ta tashi, sai dai tun kwanaki da ta ganshi ta fice da gudu ai kuwa ya tafi da ita gida dan yasan Umma ba zata bari ya daketa ba. Shiyasa ya tafi da ita gaban uwarta ya saka tsinken zabori ya zane ta yana tambayar shi dodo ne ko kuwa cinnaka ne? Da zata ganshi ta gudu.
Shiyasa bata sake gudu ba, sai dai ta takure gefe daya.
Ya zauna ta kalle shi ta ce "Sannu