Showing 171001 words to 174000 words out of 180068 words
"Da kanka kake fa'da mini? Kai da baka so na ji wannan maganar?"
Ya murmusa ya ce "Na tabbatar sai Sakina ta fa'da miki ai. Kai Àllah ka yafewa Sakinata".
Kai-tsaye wajen Baban Yara ya nufa.
Ta cikin gidan ya shiga, ya gaida Mama ta amsa masa da sakakkiyar fuska tamkar komai bai faru ba.
Ya zauna suka dan ta'ba hira, a dalilin ta zubo masa danwake.
Yana ci suna hirarsu tamkar ba surukai ba. Ko da yake ita ganin Al'amin take yi masa, shima kuma kallon uwa yake mata fiye da suruka.
Yana cikin ci Al'amin ya shigo, ganin Gudale ya saka bai zauna ba, ya gaisheta a tsaitsaiye ya juya zai fice.
Mama ta ce "shigo ka zauna Al'amin."
Bai musa ba, ya dawo ya zauna.
Ta kalli Gudale ta ga yana cin abincinsa amma ya daure fuska tamkar bai ta'ba dariya ba.
Ta ce "Baku gaisa ba Sadik".
Ya sake ha'de rai ya ce "Na amsa sallamar da ya yi ai".
"Mama ta sassauta ta ce "Ka amsa amma ko shi bai ji ba tunda a shake ka amsa din. Ni din ma dan ina cikin masu tsananin ji ne.
Menene hakan kuke yi, na sani kullum kuka ha'du sai kun yi fa'da amma ba irin wannan ba.
Ku ha'du a gabana babu mai cewa dan-uwansa kala-kanzil?
Wanne irin abune hakan kuna girma kuna cin kasa?
Al'amin da yafi Gudale sassauci ya ce "Kure ni ya yi Mama! A gabansu Yaya fa ya tsaya ya nemi zaginsu."
Gudale ya mike ya ce "Aminu har gaban abada babu ni babu kai. Ina ce kai ne ka boye mini Guduyo?
Da taimkonka Sakina ta shirya komai.
To na riga na sallamaka na ha'kura da kai, da ikon Ubangiji kuma ba zaka ji na mutu a dalilin rashin dan-uwa namiji ba, Yaya Abdallah da su Yaya Ammar sun ishe ni. Ga Abbas nan ma. Bayan bita da kullin da kake yi mini a cikin gidana, hakan bai isheka ba sai ka mini sharrin na zagi su Baba.
Allah ya so nima d'ansu ne.
Nan da nan Gudale ya lauya zance murya ta fara rawa yana fa'din "Wato ni Ubana ya mutu shine ka zage zaka dake ni ko?
Waton yanzu bani da wata alfarma a gidan nan tunda bani da dan-uwa namiji bani kuma da Abba ko?
To Alhamdulillah shi Baban bai dauka a yadda ka dauka ba. Asalima yanzu zuwa na yi mu fita unguwa tare. Kai kuma ka je na sallamaka ai dan kana ganin na kwallafa raina akanka ne shiyasa kake mini iyashege.
Hawaye ya zubo wa Gudale ya ce "Ka nuna mini Guduyo ce taka, ita kake kishi, ka je ranar tashin alkiyoma zamu tsaya gaban Ubangiji ya bi mini kadin soyayyar da na wanzu ina yi maka amma ka butulce mini, ka nuna mini wata kusan ta fi wata.
Abin da Sakina da Antin Zaria basu iya ba kenan. Basu san banbanci a tsakaninmu da ku ba"
Ya zaro tissue yana goge hawayen idonsa.
Mama da Al'amin jiki ya yi matu'kar yin laushi.
Ganin hakan da Gudale ya yi sai ya sake hakikance wa yana fa'din "Allah ya rufa mini asiri ina da Aman wataran shi zai zame mini dan-uwa. Ka riga ka shayar da ni mamaki Aminu".
Mama ta goge k'walla ta ce "Gaskiya Al'amin kai ne da laifi, ya fika gaskiya."
A sanyaye Al'amin ya ce "Ni fa Mama Anti Sakina ce ta saka ni a maganar nan, ban san komai ba, waya ta yi mini ta ce Na shiga lamarin tafi son ace akwai namiji a cikin maganar, hatta inda Guduyo ta zauna Wallahi Anti Sakina ta samo mata".
Gudale ya sake fasuwa ya ce "kin yarda da maganata yafi son guduyo da ni?
Ban da hakan da ya ga Sakina tana tare mata fa'da, nima ya tare mini mana? Kana tunanin Sakina bata sona ne ita? Baka ji a ranka cewar zata ji babu da'di a ranta ba?
Ace duk yadda nake da kai ba zaka taimake ni ka rufa mini asiri ba?
Na je gidanka yafi sau ashirin, har tsugunna maka na yi idan kasan inda matata take ka fa'da mini, amma ka yi funfurunfus. Sannan duk wannan ta'addancin da ka yi mini bai ishe ka ba, sai da ka sake nuna mini Baban Yara kai ya haifa zaka shiga tsakanina da shi. Domin Yayar Kwalli ai duk matsayinmu daya da kai a wajenta. Shiyasa nima na ware dukkan karfina ban yarda ka kai ni k'asa ba.
Tun kuma a ranar na tabbatar bani da dan-uwa namiji, idan har kai da nake so zaka iya mini hakan to kuwa kowa ma zai tozarta ni.
Dan haka na tattra na ha'kura da kai, haka Àllah yake son gani na, yan'uwa mata ya za'ba mini, na kuma gode masa.
Idan Allah ya raya mini Aman ya wanke mini takaicin daka kunsa mini".
Ya fa'da kuka na kwace masa na gaske.
Al'amin da ke zuciyarsa mai taushi ce sai ya ki'dima ainun.
Ya zabura ya isa kusa da Gudale ya ru'ko shi yana fa'din "Baka fahimce ni ba Sadik. Share hawayenka, dan Allah kada a shigo a zaci wani abin ne. Kasan idan Baba ya ganka a hakan hankalinsa tashi zai yi. Tunda baka fahimce ni ba, ka yi hakuri ni na manta komai".
Gudale ya fizge yana cewa "Babu sauran aminci a tsakaninmu, gaisawa na yarda zamu gaisa daga hakan kuma kowa tasa ta fisse shi."
Sai lokacin Mama ta ce "A a Sadik ba hakan za'a yi ba, tunda ya baka ha'kuri to ka huce magana ta mutu."
Ya bata rai yana cewa "Kada ki shiga Mama dan kuwa ni na shafe shi a sahun dangina "
Mama ta kalle shi ta ce "Ina baka ha'kuri kana sake turje wa? Sai yaushe zaka girma ne duk sadda kuka yi fada kai ne mai kafiya?"
"Yo Mama ai shi yake tsokano ni, ni gaskiya kada ki shiga, ko Baba ma na fa'da masa babu ni babu shi da Sakina, na bar su aniyar moda ta bi randa. Guduyo kuma tana can mun shirya, ko yanzu na ce ban amince ta kula ku kai da Sakina ba zata yi mini biyayya, ba sai na ga karshen shiga sha'anin aure da kuka k'ware ba.
Alfarmar d'akin ka'aba sai Gudidina ta nuna muku kune bare a tsakaninmu. Sai ta kunya ta ku".
Mama ta ce "Ya baka ha'kuri fa! Nima na baka ashe babu wata alfarma da zaka yi mini Sadik?"
Ya kumbura yana cewa "Haka kike mini fa tun fil'azal Mama! Idan na shata layi da Aminu Kan dole sai kinsa na goge."
Ta sassauta ta ce "To ba ha'kuri ake yi ba. Kowa ka ga ni a duniya ha'kurin da yake yi yafi da'din da yake ji yawa. Al'amin miki masa hannu ku yi musabaha a kore shaidanin da ya shiga tsakaninku".
Al'amin da kullum shi yake zama k'arami idan za'a yi musu sulhu, babu musu ya mi'ka hannunsa yayin da Gudale ya yi fuska ya mi'ka masa na hagu.
Ganin hakan da Mama tayi sai suka tuna mata lokacin kuriciyarsu. Shaukin wanccan lokacin ya debeta, ta murmusa ta ce "Sadik hagu fa! Mai farawa da hagu kuwa ba shi da rabo mai yawa".
Ya dauke kai shima sanin da ya yi ta yi magana ne irin yadda take yi masa yana yaro.
Ya ce "Ba zan bashi hannuna na dama ba sai ya yi tuba Mama! Sai ya yi al'kawarin babu shi babu yi mini katsalandan a gidana. Sai ya yarda Ni da Guduyo daya ne tunda ya nuna mini ban fita a wajensa ba".
Ya juyo a marairaice yana cewa "Mama yaushe ya samu Guduyo din da zai juya mini baya akanta?
Ina ruwansa da duk abin da zan yiwa Baba! Shin ni ba Babana bane kenan?
Ai da suka ga zan ta'ba su Yayar ba sun fito mini da Mata babu shiri ba?
Maganin biri karen maguzawa, har yau kuma ina nan akan bakana wlh kai da Sakina idan baku kiyaye ni ba, sai na mayar da ku y'ay'an kuka".
Al'amin ya fara hauro wa ya mayar da hannunsa jikinsa.
Mama ta ce "Bana zai kara shiga tsakaninka da matarka ba alakwari ne wannan ni na yi maka shi. Amma dai kaima ka daina yi masa rashin kunya, shekara guda cir ya baka, ni uwarku na yi muku sulhiy, duk wanda ya tayar da maganar to ya nuna ban isa ba ku gaisa yanzun Nan. Sadik bashi hannunka.
A wannan karon bai noke ba ya mi'ka masa dama tare da cewa "Assalamu alaikum".
Al'amin ya amsa tare da mika nasa hannun yana cewa Wa'alaika Salam ya Aki".
Shikenan sai Mama ta tashi ta karo musu danwaken tana fa'din to ku ci tare kuna hirarku kafin Baban naku ya fito."
Ta fara tafiya Al'amin ya ce "Amma Baki ja masa kunne ba yau, ya daina ce mini Aminu".
Ta kalli Gudale ta ce "ka ji baya so, ka bari kada shima ya fado maka naka wanda baya so.
Nan da nan Gudale ya xey "Ai na huce da shi, kinsan kuma sai mun bata ne nake fa'da masa hakan.
Ni duk wanda ya takura mini Ina fa'da masa asalin sunansa ne da ya dace da Yan gargajiya.
Yanzu wa ya ta'ba jin na cewa Ashiru, Ashir?
Har abada Ashiru zan ce masa, tunda baya ra'ayina baya nufina da alheri".
Mama ta murmusa ta ce Allah ga Sadik nan ka yafe masa, ka so shi".
Al'amin ya ce "Ni fa Mama?"
Ta ce "Àllah ka so Al'amin ka yafe masa shikenan?"
Gudale ya ce "kin yiwa kishiyarsa addu'a ina zai iya ha'kura bai tanka ba".
Farin-cikin da Baba ya yi da ya gansu suna cin abinci a kwano daya ba dan ka'dan bane.
Ya kasa boye murnarsa. Ya kalle su ya ce "Allah ya kore shaidanin da zai ruguza soyayyarku.
Allah ya yi muku albarka".
Ku gama ku zo mu tafi gaba'daya. Al'amin ka taya shi bawa Yaya ha'kurin katobarar da ya yi mata."
Hakan kuwa tare ya zuba su a mota suka tafi.
Ya dinga kallonsu cike da farin-ciki.
Baba sai Hamdala yake yi ba dan komai ba sai dan yadda ya ga y'ay'an nasa a tsaye cak sun zama zaratan matasa.
Tabbas y'ay'a maza abin ado me a wajen uba, garkuwa ne a cikin gida. Haka nan bango ne a wajen yanuwansu mata matu'kar an yi sa'a suna cikin nutsuwarsu.
Ya tabbatar Al'amin da Gudale da suke sune kananu ma sun ishi su Sakina a matsayin iyayensu.
Komin kankantar namiji ya kan zama uba a wajen mace.
Ya kalle su ya ce "Ku taimaki Abdallah, ku taya shi kulawa da yan'uwanku mata, ku bibiye su, ku dinga kai misu ziyara, ku yawaita yi musu alheri. Domin har tsufan mace tana karkashin jagorancin namiji ne. Kada ku barsu su yi kukan rashinmu. Kada kuma kuyi abin da zai ta'ba darajarsu a gidan aurensu. Kada ku haifar da tazara a tsakaninku da su.
Ta waya ka'dai zaku iya sanya farin-ciki a zukatansu.
Mata da yawa basu da iyaye, a kullum suna kukan basu da wanda zasu tunkara da matsalolinsu, suna ha'kuri na dole saboda rashin iyaye. Amma idan aka yi sa'a tana da tsayayyen dan-uwa namiji sai ta samu sau'kin al'amuranta. Ku kula da yan'uwanku, komin ku'dinsu, komin shekarunsu suna bu'katar ku".
Har suka isa gidan Yaya nasiha yake musu akan raunin da y'ay'a mata suke da shi, da kuma tarin kalubalen da suke fuskanta a wannan rayuwar.
Shi yasa yake ta fito da maganar a bayyane dan su fahimta.
Yaya ta marabce su da farin ciki, ta dinga godiya tare cewa tuni ta yafe ta manta komai.
Amma ta sake jan hankalin Gudale ya zauna lafiya da matarsa, ya kuma yi mata adalci, ya yi ha'kuri da ita. Auren zumunci sarkakkiyarsa yawa ne da shi.
Ta rufe maganarta da sanya musu albarka.
Baba ya dinga yi mata godiya.
Daga gidan Yaya yawo suka yi sosai. Sune ta'aaziya, sune dubiya a asibiti. Sune ziyarar gidajen su Anti Maimuna har kan Sakina.
Sai yamma lis suka kammala.
Suka dire a gidan Guduyo aka yi raha aka yi nasiha. Gudale ya daddage yana yi mata nasiha tunda ita kadai ce kanwarsa, sannan yadda ya mata nasihar tamkar ba shine mijinta ba.
Fadi yake ri'ke mijinki gam, kada ki bari a shiga tsakaninku, ki kunyata duk mai kokarin shiga tsakanin ki da uban y'ay'anki".
Baba ya dinga dariyar jin da'di yana fa'din you are always like that Sadik, u you will never ever change".
Al'amin kuwa da yasan yarfe ne yafi yawa a nasihar, kuma da su ake sai kawai ya maze ya yi kamar bai gane ba.
Da zasu tafi ya raka su har kofar gida sannan ya koma gidansa.
2/8/23, 10:28 - Buhainat: *GAISUWAR GIRMA Da JINJINA GA MANYAN MATA KUMA IYAYENA*
*BA ZAI YIWU NA KAMMALA WANNAN LITTAFIN BAN MIKO GAISUWATA DA GODIYAR SOYAYYA DA K'WARIN GUIWAR DA KUKE MINI BA, KALMAR GODIYA HAKIKA TA YI MINI KA'DAN SAI DAI KAWAI NA CE UBANGIJI YA SANYA ALBARKA DA FARIN-CIKI A AL'AMURANKU FIYE DA YADDA KUKE MINI. KUN FAHIMTAR DA NI, NI DIN Y'AR GATA CE MAI UWAYE KARIMAI MASU TSAYUWA A CIKIN AL'AMARIN DIYARSU CIKIN KOWANNE BIGIRE*.
*WALLAHI INA ALFAHARI DA KU, FIYE DA YADDA KUKE ALFAHARI DA RUBUTUN Y'ARKU*.
*HAJIYA SALIHA ABUBAKAR ZARIA*
*HAJ RABI SANI MADAKIN GINI*
*HAJ HAFSATU C SODANGI*.
*HAJIYA HALIMA D'ALHA SHEHU*.
*HAJIYA HALIMATUS SA'ADIYA*.
*GODIYA*
*FANS DIN SURAYYA DEE*
*HAKIKA DUK MARUBUCIYA DA MAKARANTA TAKE TAK'AMA*.
*DUKKAN WACCE TA SAKA KU'DI TA SAYI RUBUTUNA HAKIKA NA GODE MATA, NA KUMA YABA MATA, INA FATAN UBANGIJI YA FINI YABAWA.*
*INA FATAN UBANGIJI YA HORE MINI LAFIYA DA AZANCIN DA ZAN YI TA YI MUKU RUBUTUN DA ZAMU KARU GABA'DAYA*
*MADALLAH DA KU! MADALLAH DA KARFAFA GUIWARKU. SURAYYA TANA GODIYA*.
*INA KAMMALA MUKU WANNAN LITTAFIN CIKE DA ALHINI DA KEWARKU DA ZAN YI*
*GUDALE YA YA JINJINA MUKU, YA KUMA CE MATU'KAR KUKA LAZIMCI ISTIGIFARI ZAKU RABAUTA*
*ALHAMDULILLAH*
*MARUBUTA*
*TABBAS KUMA KUN TAKA MUHIMIYYAR RAWA A RUBUTUN SURAYYA*
*DAN HAKA NA YABA NA KUMA GODE WA KOKARINKU, ALLAH YA CIGABA DA TSARE MANA ALKALAMANMU*.
*AUNTY SUMAYYA TAKORI*.
*JAMILA JANAFTY*
*LUBNA SUFYAN*
*ZAINAB MAZAWAJE*
*AYUSHA MUHD*
*SAFIYYA UMM ABDUL*
*FADILA LAMI'DO*
*BINTA ABBALE*
*KULSUM BAFFA AZARE*
*HASSANA DAN LARABAWA*
*ZEEY KUMURYA*
*SAKINA YAZID*
*DONUT FAIRY*
*DA DUKKAN MARUBUTAN LAFAZI WRITERS ASSOCIATION*.
*GORON GAISUWA*
*GA YAR'UWATA DA MUKA FARA GINA DABI'AR GUDALE TARE*
*SISTER ASMA'U A3*
*(MAMAN MAMA)*.
*DA KUMA AMINIYATA*
*HAUWA SAID YIDIE GOMBE*
*(MAMAN MAMA)*
*ALLAH YA BAR ZUMUNCI YA SHIRYA ZURIA*.
*FATAN ALHERI GA*
*DUKKAN DALIBAN UNITY KACHAKO GABA'DAYA KWATA, MUSSAMAN AJI NA 2008*
*SON SON BISIBILLAHI*.
*TUIKUICIN LITTAFIN GA*
*SCHOOL DAUGHTERS DINA*
*8 BABIES*
*MUSSAMAN TA KARFEN*
*HAFSAT RILWAN BELLO*
*(BABY GIRL)*.
*ALHERIN ALLAH YA ISKE KU HAR GADON BARCINKU*.
*99&100*.
*Prologue*.
Ya dawo ya same ni a inda suka bar ni.
Ya zauna sai farin ciki yake yi.
Ya kasa yin shiru ya ce "Guduyo anya akwai farin-cikin da ya wuce cud'anya da jininka?"
Na girgiza kai na ce "Babu".
Ya saka hannu ya jani jikinsa ya ce "me ya sanyaya miki jiki haka? Alhalin kamata ya yi ki yi farin-ciki mai yawa".
Na numfasa na ce "Tausayin Baba ne ya kama ni.
Tunda Abba ya rasu gaba'daya wani irin tsufa ya yanko masa. Abubawa da yawa bai san ya yiwa kansa, bai san matsaloli da yawa ba, saboda Abba shine jagoransa, baya sanin duk wani rikicin da zai taso, amma tunda Abba ya kauce al'amura suka dabaibaye shi ba tare da yasan yadda zai dinga warwaresu ba.
A yanzu da ya tisa ku a gaba yana yawo da ku sai na fahimci yana son ya koya muku juriyar daukar nauyi ne.
Ya sani idan baku saba ba zaku sha wahala kamar yanzu da nauyin ya koma kansa yake shan wahalar gaske.
Allah ya jikan Abba".
A sanyaye Gudale ya ce "Ameen Gudidina! Kin sake fahimtar da ni manufar Baba wanda duk ban kawo hakan ba. Àllah ya bamu ikon daukar nauyin da zai hau kan mu".
Na amsa da "Ameen Abban Amnah".
Ya murmusa ya ce "kinsan dai tun farko ina yin kawaici akan Amnah tunda yar fari ce, bare kuma yanzu da na bayar da ita.
Dadin Afrah zaki dinga ce mini tunda na fahimci an kara mini matsayi, na tashi daga Yaya Gudale. Na koma sweaty da kuma alkunya da Yaranmu".
Na murmusa ban ce komai ba.
Tun daga lokacin muke rayuwa cikin farin-ciki da mutunta juna.
Ina iyakacin bakin kokarina na kiyaye abin da zai ha'do mu rikici.
Kullum a cikin gyaran kaina da gidana nake.
Sai dai duk da hakan idan ya so rikici, kan abu kalilan sai ya botsare mini.
A hakan dai muke ta lallabawa.
Ba zato kawai ya sanar da ni satin sama zamu wuce Umrah ni da shi da Afrah da Aman da kuma Ummah.
Na dinga tunanin yaushe ya dauki passport dina?
Tunda ina da shi a dalilin shekaru uku da suka wuce Abba ya biya mini na sauke farali.
Sai da ya kammala komai sannan ya fa'da.
Har zuciyar Umma ta ji babu da'di amma ta ha'kura akan dole, mussaman da ta ji da ita za'a yi tafiyar.
A babban hotel muka sauka. Ni da Gudale dakinmu daya, yayin da Umma da su Afrah suke daki daya.
Mun yi ibada, mun kuma sha soyayya. Na dinga kokarin k'ulla kyakkawar alaka mai karfi da Umma. Amma ta ki bada damar hakan. Sai na ha'kura tunda dai ta sauko sosai bata cika aibata ni ba, to na gode da hakan ma.
Bangles din da ya yi al'kawarin siya mini ya siya, warwaro guda biyu. Da kuma wani murtukukeken bangle guda daya.
Jikina ya yi sanyi da irin ku'din da suka lashe. Gold yana zuba tsada, haka ya siyawa Afrah, babbar sarka da zata jima bata saku a wuyanta ba.
Ya ce "Nasan Antin Zaria ta da'de da siyawa y'arta, gara kema na daure na siyawa taki y'ar".
Na dinga goge k'wallar farin ciki, hakika na gamsu da soyayyarsa, ni da shi ban san wanda yafi wani son dan-uwansa ba.
Wannan tafiyar shine mafarin dawowar Afra! Domin tunda muka dawo ya shafawa idonsa toka ya ri'ke ta.
Hakan kuma ya zo akan gabar su Antin Zaria zasu sake komawa kasar Germany zata yi shekaru biyu.
Aikuwa ta ce tare da Amnah zasu tafi shikenan baki alaikum ba'a samu bacin rai ba.
Sai dai zasu zo nan da watanni takwas ayi bikin Junaid.
Bamu jima da dawowa daga Saudiya ba, Yaya Gudale ya fara wani ciwon ido azababben gaske.
Ido na warke wa hakori ya harbu
Na tabbatar a Saudi na samo ciki.
Kusan sati uku yana magogo.
Kowa ya ganshi sai ya tausaya.
Umma kuwa fa'di take "cikine da matarsa. Ai shikuma indai za'a yi masa haihuwa fa babu shi babu sukuni. Ban da dai yadda Allah ya tsara, hakan za'a yi ta yaya za'a zuba mini ido ina yi masa wannan tanadin tsiyar.
Shi kuma a yanzu da baya kaunar ta shiga shirginmu fa'di yake