Showing 177001 words to 180000 words out of 180068 words

Chapter 60 - Sabo Da Kaza By Surayyah Dee

18 Dec 2025

8746

da mijinta da Amnah suka koma Germany. Yayin da Abba mai bin ango tuni ya koma kasar Turkey inda yake Masters dinsa. Autanta Ja'afar ne ka'dai aka bari shima jibi Yaya Gudale zai mayar da shi makarantar Nigerian Turkish da take Abuja, yana
ajin karshe S.s.3.
*Shekaru biyu a gaba*.
A kwana a tashi babu wahala, tuni na yaye Arif.
Na koma jami'ar Bayero ina masters degree. Wanda da kyat da sudin goshi ya bari.
Ina karatun ne dan ina so amma da tuni na ha'kura. Domin tun hudun dare Zan tashi, sai na gama da hidimarsa. Duk yadda nake da yan aiki har biyu to ba zai yarda ya ci abincinsu ba. Dama kuma sai da ya kafa hujjar karatuna ba zai sa ya samu gibi a kulawata ba.
Ya dai yarda zai ajiye mini yan aiki su taya ni gyaran guda da kula da Yara.
Amma hidimarsa kwaya daya ba zai rage mini ba. Na yarda da hakan tunda karatun nake so.
A wannan lokay a yi matu'kar zubewa, amma fatata ta yi k'yau tabbacin mayukan Oriflame na Aisha suna tasiri, ga kuma lafiyayyen abinci.
Kawai jarabar Gudale da rashin samun hutu ne damuwata, kullum ina makaranta, idan na dawo gida kuma hidimarsa ba yar ka'dan ko mai sau'ki ba ce. Domin dai dai ruwa idan zai sha sai na zuba masa.
Idan yan tsiyar suna kusa ma Sai na shirya tsab zan tafi sai ya ce "Na koma na yi shigar yaku bayi.
Ko kuma ya ce "Na tafi da Arif ai ba mai rikici bane.
A hakan dai nake lallabawa har na samu na kammala.
Ranar wata asabar ina zaune a gefensa.
Rarrashi nake yi tamkar wanda na yi masa laifi.
Cikin kwantar da murya na ce "Daurewa zaka yi na je makarantar nan."
Ya ha'da rai ya ce "Asabar din da zan samu mu yini tare ma sai kin fita, nifa kina kwarata Guduyo, tsakani da Allah kina cutata".
A sanyaye na ce ",Na yi tuba Dadin Afrah! Kara ha'kuri watanni suka rage mini".
Ya yi shiru can ya ce "Karfe nawa zaki je?"
Da sauri na ce "sha'daya zan fita zuwa azahar in sha Allah Ina hanyar dawowa".
Ya kalli agogo ya ga Tara da rabi.
Ya nisa ya ce "Tunda kin sa mun karya da wuri.
Zo ki mini tausa kafin lokacin fitar ya yi."
Gabana ya yanke ya fa'di domin nasan ba iya tausar zan yi ba.
Na tuna daren jiya bai tsallake ba, haka da asuba ma, yanzu ma idan ba sa'a na yi ba, ba zan tsallake ba.
Ya kallo ni ya ce "Tausar da zaki yin ne yasa kika wani zabura?"
Na kasa magana illah ido da na zuba masa.
Ya girgiza kai ya ce "Tashi ki je! Allah ya bani ladan hakuri. Allah ya bani iko na yi ta kyautata miki. Ya bani ha'kurin rakinki. Ba dama na ta'ba ki, ko na ce ki yi mini kaza sai kin nuna na fitine ki. Amma da yake duniya ne a gaban ki, ai bakya k'osawa da zirga zirga a titi da sunan makaranta, duk sanyi, duk damina".
Kullum kina study room kina nazari. Amma da zance ki shigo d'akina shikenan duk wani rauninki zai bayyana".
Murya na rawa na ce "Ba hakan bane Dadin Afrah ka yi ha'kuri".
Ya girgiza kai ya ce "ke ce da ha'kuri Guduyo. Amma kar kiji da wai, matu'kar kina mini irin hakan Wallahi zan warware al'kawarin da na yi miki, na bazan k'ara aure ba.
Dan kuwa ba zan yarda ki jefa ni a halaka ba, gara na saba alk'awari zai fi mini sau'ki".
Nan da nan hawaye ya b'alle mini na ce "Ba fa na yi maka musu Yaya Gudale. Ina yin kokari kai ma ka sani, amma kullum baka yaba mini, kuma yanzun na ce ba zan yi bane?"
Ya ce "Baki ce ba, amma yanayin ka'dai ya nuna mini ba zaki saki ranki yadda zan samu farin cikin da nake bu'kata ba.
Yana rufe baki na fa'da masa na ha'de bakinmu.
Ban samu kaina a hannunsa ba sai goma da kusan rabi, a gaurguje na yi wanka na shirya.
Dake y'an kirkin na kusa ya dauki Arif muka tafi tare, tunda Afrah da Aman suna islmamiya.
A mota ya jira ni na kammala muka dawo, yana sake jaddada mini al'kawari yana nan, ba zai karya ba, sai idan ni na so.
Muna isa gida ya ce wajen Baban Yara zai je, idan zan je Bismillah.
Na bishi sanin ban masa laifin da zai kai k'arar da zai kunyata ni ba.
Muna isa k'ofar falon ya durkushe ya fara rararfe tamkar Arif.
Baba sai fa'di yake "Assha Sadik yau ba azo an yi moping ba, zaka na'de k'ura a jikinka."
Bai tashi ba kuwa har ya isa gaban Baban ya durkusa guiwa biyu.
Cikin rauni sosai ya ce "Yauma godiyar nake son na sake yiwa Abba kuma baya nan?"
Baban Yara ya ce "sau nawa zaka yi godiya ne Sadik?"
Ba kunya ya ce "Ina Jin da'din zama da ita ne Abba.
Na gode sosai Abba! Allah ya jikanka".
Baba ya biye masa ya ce "Dama na fa'da maka ko ina kwance zaka gode mini".
Baba da taya bera bari ya kalloni ya ce "Kara kwantar masa da hankali Halimatu! Sake yiwa aure biyayya, kin sani bani da burin na ga aurenku ya dire har a aljannah. Allah yayi miki albarka da zuri'arku gaba'daya".
Ya mayar da hankalinsa kan Gudale ya ce "Madallah da Sadik! Na sani Ubangiji zai mayar mini da kai yadda nake fata".
Daga hakan kuma sai ganin Gudale na yi ya koma ya zauna ya nutsu ya ce "Baba barka da yini ya jikin?"
Na kyal-kyale da dariya domin sai yanzu na gane waccar gaisuwar da ya yi ta Abba ce, ta yanzu ce ta Baba. Ho diramar Gudale idan kana gani ba ruwanka da kallon tv, yak'i yarda ya girma. Har yanzu bai bar kowa ba. Kuma ya koyawa Baba diramar shima.
Ya hareri na ya ce "Na rantse muka koma gida sai na baki tsinke kin nuna mini abin dariya a jikina.
A gabana, a gaban Baban Yara kike wannan dariyar anya kina son karamarki ta dire Guduyo?"
Na gimtse dariyar. Baba kuwa uffan bai ce ba.
Na zauna na gaishe shi, sai kuma muka dinga hira har Mama ta shigo ta same mu.
**
Mun kammala karatun sai jele muke yi a gaban profs dan.mi samu mu karbi result din mu.
Abokiyar karatuna Sajida.
Har gida ta kawo mini super wax da wani uban laxe cikin wani kawataccen kwali tamkar box.
An rubuta Rabiu & Sajida.
Na dainga yi mata murnar auren da ya zo mata. Tunda sa'anni muke shekaru talatin kenan. Amma sai da na yi Mata dan bikin ko da wasa bata Nina ba sai da Abu ya kankama.
Ta yi murmushi ta ce shine ya bu'kaci hakan tsohone mai iyalifa.
Wata'kila matar ce baya so ta sani tunda ya yi ta yun'kurin auren baya yiwuwa, wata'kila kuma sirri yake so.
Na yi murmushi na ce "Allah ya ka'dai fitina ya sanya alheri. Ko tsoho ne ai namiji ne sannan ya tara ai. Tunda k'awaye ma ya narkar da kuda'de ya bamu wadannan kaya haka."
Muka yini da ita, har Yaya Gudale ya same ta, suka gaisa sama sama ya haye sama.
Ta kalli ni ta ce "Mijinki bashinda sabo".
Na ce "Haka yake, baya sakewa da kowacce mace inba ni ba. Kada ki dauka wula'kanci ne".
Muka yi sallama na rakata na dawo.
Na ha'da ruwa da lemo da meatpie na nufi dakinsa.
Kallonsa kawai na yi na gane yauma ya tuna baya, ya afa abar.
Hankalina ya yi matu'kar tashi ainun.
Na ajiye masa na zauna na kalle shi idon nan ya ciko da k'wallah tsabar cajin da take yi masa.
Ba'kin ciki mai yawa ya rufe ni.
A fusace na ce "Tabdi jam! Ashe baka bar wannan dabi'ar ba Yaya Gudale?
Ina ka biya haka?"
Kallona kawai yake ba tare da ya iya bu'de baki ya amsa mini ba.
Na fusata na ce "Idan baka ji tausayin mu yan'uwanka mata ba, ai sai ka ji tausayin manyan ya'yanka mata ne.
Haka zasu taso su dinga ganinka lokaci zuwa lokaci kana cikin rashin nutsuwa ka dawo mahaukaci, haka kake son Aman ya dinga ga ni daga gareka?
A hakan zai zame maka aboki kuma garkuwa?"
Jikinsa ya yi sanyi ainun.
Na mike na nuna shi da hannu na ce "Kunya dai kam ka ji ta Wallahi".
Nan da nan ya zabura ya mi'ke ya ce "Na rantse kika zage ni sai jikinki ya fa'da miki, ance miki na sha da yawa ne ta yadda zan kasa fahimtar komai?
Gajiya na yi, shiyasa na sha dan na wartsake."
Idona ya ciko na ce "Ba dan ka wula'kanta kanka ba har na iya daga maka murya Yaya Gudale?
Sai dai kada ka shiga ru'du na rantse maka ko zagina ka yi idan na saka kafa na fita ba zaka kuma ganina da sunan matarka ba".
Ina rufe baki ya koma ya zauna ya yi lakwas a hankali ya furta "I come in peace".
Tausayinsa ya yi matu'kar kama ni.
Na fice na samu gefe na yi kuka na gaji.
Na sauka k'asa na shiga cikin yara muna ta hidima duk kuwa da bani da sukuni.
Ana kiran sallar maghrib ya sauko ya yi wanka amma idon nan ya ka'da sosai sannan da kyar yake tafiya.
Ya kalli Aman da tuni ya yi alwallah yana jiransa ni kuma ina ta wasiwasin ko zai iya fitowa ma.
Amma da yake Ubangiji ya sanya shi a cikin bayi masu son sallah sai gashi ya fito.
Ya rike hannun Aman suka fice.
Ni da Afrah da Arif muka yi a gida.
Ranar ko dakinsa ban je ba, ba zan iya tuna yaushe rabon da na yi masa hakan ba.
Muna cikin haka ranar bikin Sajida ta zo.
Dake na share shi, kwanaki biyu bana ko bu'de baki na yi masa magana, duk ya rikice da son mu shirya.
Da kansa ya kai ni har wajen bikin. Wani shahararrren Hall.
Ya zauna ya jira ni a mota.
A hanyar mu ta koma wa sai neman magana yake yi, ni kuma na kame bakina na k'i kula shi.
Har muka iso gida bai ha'kura da nacin magana ba, ni kuma ban kula ba.
Washagari juma'a da yamma ba sai tashin hankali ba.
Wai Anti Maimuna ce ta dawo gida.
Da kuma wani irin ihu ta shigo, hatta ni da bangarena yake da tazara da cikin gida sai da na ji kururuwarta.
A ki'dime Gudale ya fice dama dawowarsa kenan parking kawai ya yi.
Ina son fita amma dai na ha'kura tunda abin a kofar Umma ne bana son tashin hankali, tunda dai lallaba wa nake yi.
Ashe wai aure mijinta ya daura dazu da aka idar da sallar juma'a.
Bai fa'da mata ba sai bayan ya dawo daga daurin auren.
Shine ta kasa ha'kuri ta fito ta bar masa gidan.
Tashin hankalin da ta shiga ba ka'dan bane.
Hatta su Sakina sai da suka taya ta jin ciwo, ko ni nan na ji babu da'di domin ko yaya aka taba naka sai ka ji ciwo.
Kan dole Baban Yara ya mayar da ita da daddare bayan ya yi mata wuta wuta.
Umma sai kuka take tana cewa duk yadda take da Hajiya Laraba uwarsa amma ta yi mata hakan?
Sai lokacin na tuna irin abin da Umma da Maimuna suka so yi mini kenan lokacin auren Munubiya.
Amma da yake ni din yar gata ce ina da Abba sai burinsu bai cika ba. Irin alherin da na samu a sanadin auren ba dan kishi ba, da sai na ce ya yi ta yin auren duk shekara. A karshe kuma auren ya watse babu albarka, babu kuma mutunci.
Sai gashi da na yi ha'kuri, ina zaune Ubangiji ya saka an yiwa Anti Maimuna abin da ta jagoranci ayi mini.
Tana cikin wannan tashin hankalin ya dauki amaryarsa suka wuce London.
Wani abin mamaki ashe Sajida ce amaryar.
Na ki'dima da buwayar Ubangiji.
Idan na so nima yanzu sai na je gidan na k'i zuwa part dinta tamkar yadda ta dinga yi mini akan Munubiya, kai wato ba k'aramin bakin ciki na hadiya ba. Amma ba zan iya hakan ba domin saka alheri da sharri babban jihadi ne da yake kawo zaman lafiya a zamantake wa mussaman a sha'anin zumunci.
Sannan ita din diyar Abba ce, ko ba komai ta ci arzikin ubanta.
Kwanaki hudu kenan ina fishi da Gudale. Gaba'daya bashi da nutsuwa, ba abin da yake so irin na kula shi.
Dana zauna na yi tsam da raina sai na gane addu'ar da Abba ya yi mini yana hawaye ne Ubangiji ya kar'ba.
Ya roka mini Ubangiji ya hore mini Gudale sau ba adadi. Ya roka mini a cika masa zuciya da soyayyata mai naci, da tausayi mai hana zalunci.
Tabbas Ubangiji ya kar'ba domin duk iyashegensa idan yaga ina kuka to fa shikenan dukkan rauninsa zai bayyana.
Idan kuwa har ya yi mini laifin da na yi fishi da shi to bashi babu nutsuwa.
Har sai ya samu aminci daga gare ni.
Hawaye ya goce mini a fili na ce "ko irin su Abba guda nawa ne suka yi saura a wannan duniyar?"
Na daga hannuna na ce Allah ka jiqan Abba".
Da daddare ina zaune ni ka'dai a dalilin ya kwashe yara sun fita bayan ya yi juyin duniya na bisu na k'i.
Suka dawo da ledoji niki niki a hannunsu Afrah da Aman da kyar suke jansu.
Yayin da shi ya shigo daga 'karshe sabe da Arif da yayi barci.
Ya tsaya yana kallona ya ce "Maman Amnah kin ga Arif ya yi barci".
Na dauke kai na ce "Na ga ni, kwantar da shi".
Haka kawai na ce "ya juya yana cewa "To" cikin murna domin kuwa duk maganar da zai yi bana cewa ko uffan".
Ya dawo falo ya dauki babbar leda shake da dogayen riguna da takalma ya turo mini gabana yana cewa "ga naki"
A hankali na ce "Na gode."
Yayin da su Afrah suke ta gwada na su.
Ya yi jim yana kallona ya ce "Amma dai bana son na kawo abu ba'a bude ba ko?"
Na tura baki na ce "Ai zan bu'de ne, ba dai nawa bane". A sanyaye ya tashi, ya yi dakinsa.
Sai kuma tausayin yadda ya kwantar da kansa ya yi matu'kar kama ni.
Kwanaki biyar ai nasan ba karamin ragaita yake ciki ba.
Cikin dare kuwa ya kasa ha'kuri ya zo ya jani.
Jikinsa na rawa yake cewa "ki taimake ni, na yarda na yi kuskure ai ba zan sake ba. Yanzu ma tsautsayi ne, nafi shekara ban sha ba.
Kuma idan zan sha din bana sha ta bugar da ni"
Na watsa masa kallo na ce "Àllah zaka yiwa wayo Yaya Gudale?"
Ya girgiza kai ya ce "Astagafirullah! Na yi tuba bazan sake ba, ki yarda da ni, idan na ce na daina abu ina kokarin kiyayyewa. Tunda na yi al'kawarin bazan sake zagi ko dukanki ba, na karya al'kawarin?"
Na girgiza kai.
Ya ce "To bare kuma laifin da Allah nake yiwa. Kinsan nafi sonsa, nafi tsoronsa da ke ko?"
Na daga kai da sauri na rungume shi ina cewa "Madallah da Gudalen Umma"
Shikuma ya kankame ni yana ta sakin ajiyar zuciya.
Can ya dago ni ya ce "Guduyo idan kinsan kina biye Sakina kuna rubuta sunana a cikin kulle kulle ku ji tausayina ku bari.
Nifa burina na zama namiji a gidana. "
Na yi murmushi na ce "Ai dan kasan ka yi laifi ne, amma waya Kai ka fishi kan abu ka'dan ma.
Kwanakin baya ka manta kalar fishin da
ka yi mini akan kawai na yi lalle ba tare da anyi hutun school ba".
Ya dauke kai yana murmushi ka'dan ya ce "Ato na dai roki a mini a wannan laminin. "
Shikenan muka shirya.
Sai dai duk sallar farillah ko ta nafila sai na roka masa shiriya, sai na roka masa lafiya da habakar arziki, hakanan kullum sai na roki Ubangiji ya cigaba da hore mini shi, ya kuma cika zuciyarsa da soyayyata da tausayina.

*Shekaru goma a gaba*.

Zuwa wannan lokacin almura sun daidutu, hankali da girma sun ratsa mu.
Yanzu haka yara biyar ne a gabana bayan Afra, Aman, Arif, sai na yi Afreen mai sunan Sakina. Sai kuma autana Aryan mai sunan Baban Yara".
Amnah ce dai har yau tana wajen Antin Zaria a yanzu haka ta fara karatun medicine a kasar Sweden.
Afrah kuwa tana shekarar karshe a secondary gaba'daya iu juye ni sak. Duk cikin su ita ka'dai ce mai kama da ni kwabo da kwabo har garin jiki, ita har ta fini gashi da fari ma, tunda sun yi sa'a Umma ta sam musu. Ragowan yaran kama suke da Gudale da Sakina.
Komai na tafiya daidai sai dai ha'kuri da kullum a cikin yinsa nake.
Har yau din nan Gudale bai canja halayyarsa ba.
Yanzun na zai tuntsure ko ya lauya zance kuma dole ka sauko domin sai ka ji tamkar ka zalunce shine.
Umma tana nan tsufa ya cimmata ainun.
Babu soyayya a tsakaninmu har gobe sai dai kuma ta sassauta kiyayar da take yi mana.
Mussaman da har gobe taimakekeniya ne a tsakanin yan k'ofarmu da tasu. Mune bangonsu, suma sune namu.
Kowa kuma yana cikin rufin asirinsa.
Kullum sai Mama ta je ta dubo ta, ta zauna da ita bisa umarnin Baban Yara, tunda Maman ta fita dan k'wari, ita take taimaka mata wajen wanka da hidiida yan aiki ba zai yiwu suyi mata ba.
Muna zaune a falo daga ni sai shi yana mitar aikin da Antin Zaria ta samo mini na lakcarin a jami'ar tsohon ministan ilimi Prof. Mk Bichi. Da yake tana da hanya kuma jamia ce mai zaman kanta sau uku kawai zan fita a sati.
Sakina ta shigo mana a yanzu ta zama babbar mace sosai.
Ta kalle shi ta ce "gemai gemai da kai ba zaka bar kishi da fitina ba Namoriki?"
Ya girgiza kai ya ce "Nafi son na ganta kullum a tare da ni".
Ta ce "Yi ha'kuri ka barta ta je ta koyar da ilimi, karatunta mai daraja ne barta ta yad'a shi a tsakanin alumma."
Ya durkushe a gabanta ya ce "To yayata, yadda kika ce hakan za'a yi. Na amince saboda ke, amma idan kulawar da nake samu daga gareta ta yi rauni tabbas zan janye, zata dawo ta zauna ta kula da iyalinta, ki zama shaida."
Sakina ta murmusa ta ce "Autan Umma baban soyayya! Ina yinka over".
Ya murmusa ya ce "Bayan Umma ke da Guduyo ne mafi soyuwa a zuciyata Sakina. Na gode sosai. In sha Allah har a filin barka sai Abba ya jinjina miki."
Na durkushe tamkar yadda ya yi a gabanta na ce "Madallah da Sakinan Abba. Madallah da yar'uwa irin ki, madallah

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login