Showing 51001 words to 54000 words out of 180068 words

Chapter 18 - Sabo Da Kaza By Surayyah Dee

18 Dec 2025

8735

ni tamkar Al'amin. Duk sanda kike da matsala ki tuntu'be ni kaitsaye, bana fatan ma matsalar ta same ki, sai dai dole ta kan zo ta inda aka zata da ta inda ba a zace ta ba."
Idona cike taf da 'kwalla na ce "Na gode".
Ina tuna maganganun Sakina da ta ce na za'bi Ashir yafi Gudale nutsuwa da Sona.
Na gasgata hakan domin kuwa ru'danin da na gani a tare da shi, yafi kama da yanayin da mutum yake tsintar kansa a ciki idan ya tafka asarar abu mai tsananin darajar gaske.
Har muka isa gidan Sakina jikinmu a mace yake, na dinga jin wani iri.
Na sani nafi jin Yaya Sadik a raina, na fi jin nisha'di idan ina tare da shi, hakanan shi nake fatan ya rungume ni a kirjinsa.
Amma a wannan ranar na tabbatar ina son Yaya Ashir ma.
Mussaman da ya kasance irin mazan nan da basu da girman kan da zasu fayyace wa mace yadda suke jin ta a zukatan su.
Tare da shi muka shiga gidan, sai dai Bata nan, ta je gidan Aunty Maimuna. Yan aikinta kawai muka tarar.
Ya ce "To mu je na kai ki gidan.
Zuciyata 'daya na amince, dan nasan idan Gudaleya ji tare muke da Sakina zai iya zuwa gidan Anti Maimuna ya same mu, muka fito.
Muna fitowa daga layin sai na ga tamkar Gudale a gaban wata motar.
Sai ban amince shi din bane kasancewar 'dan gefen fuskar na gani sannan gilashin motar a zuge yake rif kamar yadda tamu take a zuge.
Bugu da 'Kari bansan motar ko wanda ya mallake ta ba, bayan haka da kansa ya ce sai ya yi la'asar zai fito, yanzu kuwa ko azahar ba'a yi ba.
Duk nisan da ke tsakanin Sallari zuwa Badawa lay out inda gidan Anti Maimuna yake, a ranar sai na ga tamkar 'kiftawa da Bismillah har mun isa duk kuwa da ba gudu yake yi ba.
Da na laluba sai na gane nutsuwar da na samu a hira da Yaya Ashir ne ta hana na fahimci lokaci mai yawa muka shafe kafin mu isa.
A tsaitsaye ya gaisa da su! ya barni tare da su, dama kuma na ce ya kai mini kayan da ya saya mini gida.
Tunda zai karbowa Yaya sa'ko a wajen Umma.
Na rako shi 'kofar gidan ina 'kara yi masa godiya, ya shiga motar ya tayar ke nan. Ni kuma ina tsaye, ina kallonsa. Fuskata 'dauke da wani irin murmushi da yake fitowa tunda ga 'kasan zuciyata.
Kawai sai ga motar nan da na gani dazu.
Kafin na gama tunanina. Horn din da Yaya Ashir ya yi alamun dai gaisuwa ga Gudale ne ya katse ni.
Yayin da na daskare, na sani sai yayi mini tijarar ina sauraron ma'kiyinsa.
Ya fito a motar yayin da abokin nasa ya ja motarsa ya yi gaba a abinsa.
Sanye yake cikin gajeran wando 3 quarter fari 'kal, rigar kuma t shirt ce mai gajeran hannu kalar lemon green. Bayan Riga kamar koyaushe an rubuta *Gudale*. Kafarsa sanye da farin takalmin da ya dace da kayan jikinsa.
'Kamshinsa na turaren Chris Adams ya baibaiye wajen.
Kallo 'daya na yi masa, na gane baya cikin sukunin zuciya, dan kuwa gaba'daya idanuwansa da suke ki'dama ni, a jirkice suke tamkar dai wanda ya tashi a barci, ko kuma wanda yake cikin 'karamin maye.
Ya wuce ni tamkar bai ganni ba. Na bishi a baya ina jin tamkar ya tsaya mu yi hoto saboda yadda kwalliyar da yayi ta yi matu'kar burge ni.
Duk kuwa da a zuciyata ina ganin bai kamata ya fito a hakan ba. Sai dai shi a wajensa wannan shigar is common.
Kusan a tare muka shiga falon.
Anti Maimuna sai ina ka saka take da shi.
Ni kuwa dai a farko zuwan namu ta karbe ni babu yabo, ba fallasa.
Sai dai bata iya ha'diye abin da ke ranta ba.
Sai da ta ce "Ta tabbatar Sakina na biyo, bata ta'ba ganina a gidanta haka siddan ba.
Dan haka ta riga da ta gane inda na ajiye ta.
Na yi sukuri saboda yadda take maganar cikin fishi!
Da kyar na ce "ki yi hakuri Anti ba hakan bane, makaranta ce take 'boye ni".
"Amma ai bata 'boye ki daga zuwa wajen wadanda kika gamsu 'yan uwan ki bane ko?"
Ta tambaye ni a 'kufule sosai.
Na ji duk na muzanta saboda yadda Sakina ta bagarar da ni, sannan Gudale ya kishingi'da ya ri'ke kai tabbacin bashi da lokacin da zai kare ni kamar yadda yake yi idan 'yan mutuncinsa na kusa.
Na kasa magana, hawaye ya cika mini ido 'kiris nake jira a dalilin dukkansu uku na ga fishi suke da ni muraran.
Tsakani da Allah kuma duk na Sakina ya fi damuna, sannan na Gudale. A dalilin Anti Maimuna dama ba wani muhimimanci ne da ita a duniyata ba, asalima ban cika ko tuna ta a cikin jerin 'Yan uwana ba.
Saboda tsananin izza da wulakancinta, da kuma yadda take taya Umma wula'kanta mana uwa.
Shu'dewar mintina ka'dan muna zaune jigum jigum.
Na mi'ke jiki a sanyaye na ce "Na tafi".
Ai kuwa nan da nan Anti Maimuna ta sake hawa, tana fa'din maganganu wai ba dama a mini maganar gaskiya sai na 'dau fishi, saboda kawai mu 'yan gadara da isa ne, aiki ya samu mijina.
Sai lokacin Sakina ta ce "Ya isa haka Anti dan Allah! Ke Halimatu koma ki zauna, tare zamu tafi".
Na koma na zauna ina jin takaicin ke 'din da Sakina ta ce mini alhalin tasan bana son a ce mini ke.
Komawar da na yi na zauna 'din bai yiwa Anti Maimuna ba sai da ta 'kara da fa'dawa Sakina cewa "Ai dama wajen ki ta zo, na tabbatar idan na rantse ba zan yi kaffara akan tasan kina nan ne, shiyasa ta zo mini".
Ha'kuri dai Sakina ta bata da 'kyar ta bar maganar bayan ta ja kwafar da take isharar tana ciki da ni.

Ta kalli Yaya Sadik ta ce "Gudalen Umma how far?"
Da 'kyar ya bude idonsa da suka sake jirkicewa ya ce "Bana jin da'din yanayin ne, kuma kamar zazzabi nake ji."
Ta tashi da sauri ta dauko masa ruwa da pracetamol, a baki ta bashi tsabar gata. Ni da Sakina muna kallonsu.
A zuciyata kuma na sani hakan ba zai hana idan ta yi masa abu sa'banin ra'ayinsa ya nuna mata iyakarta ba.
Sakina ta mi'ke da nufin shiga toilet.
Yayin da Anti itama ta yi kicin ta mayar da tumbler din hannunta, sannan ta saka 'Yar aikinta ta shiryo mana abinci da kuma ruwa da lemo, da ta fito sai ta shige 'daki wajen Sakina.
Kamar jira nake yi su bamu waje.
Na muskuta na ce "Yaya Sadik sannu! da alamun kana jin zazzabin nan."
Ya 'dago kansa da kyar cikin muryar gargadi ya ce "Kar ki sake bu'de bakinki da nufin yi mini magana! Na riga na barwa Ashiru ke, dama dole aka yi mini, yanzu kuwa ba zai yiwu na aure ki ba, alhalin na tabbatar kina tarayya da wani 'katon da zuciyarsa bata nufina da alheri. Ke ko zumuncin ma bana bu'katar yinsa da ke. Na yafe ki.
Me za'a yi da wacce kullum sai ta jefa zuciyarka cikin 'bacin rai da firgici. Ba zai yiwu ace kina jefa ni cikin garari da jinya ba. Last warning! ki kiyaye Ni".
Na manta kashedin da ya yi na kar na yi magana.
Da sauri na ce "ka daina saurin hassala, ka daina yanke hukunci cikin zato Yaya Gudale! Gidansu na je shine Yaya ta ce ya dawo da ni gida fa. Kuma saboda Allah sai na ce ba..."
Ai kuwa ban 'karasa ba, a dalilin yadda ya yi wani tsalle ya sha'ke mini wuya, da 'karfin gaske na dinga 'ko'karin 'kwatar kaina amma ina, 'karfin nasa tamkar na mashayin 'kwayar Tramol ne."
Tun ina juriya har na gaza, na dinga wani irin 'ka'kari, shima na kasa a dalilin na fara galabaita.
Sama sama nake jin yana cewa "Gara na kawar da ke, da gallaza mini da kike yi. Allah wadaran Ashiru! Allah ka gigita mini shi, fiye da yadda ya gallaza mini, yake 'kuntata mini".
Kamar daga sama Anti Maimuna ta diro cikin falon, da azama ta iso, sai dai duk yadda ta so ya sake ni, bata samu dama ba.
Yadda Anti take maganar ya sake ni cikin kara'di ya sanya Sakina ta fito a hanzarce.
Bata yi yun'kurin saka hannu don ta 'kwace ni, kamar yadda Yayarsu take yi ba.
Ranta a bace ta ce "Na Moriki saketa"!
Ta sake maimatawa nan ma bai ji ba, yayin da ni kuma nake 'dan'dana ku'data.
A kufule ta ce wa Anti "matsa.
Da sauri ta matsa, tana cewa "Sosai ya sha'keta, Gudale kar ka yi kisan kai mun shiga uku".
Sakina ta ri'ke hannunsa idonta cikin nasa ta ce "Yi ha'kuri ka saketa sai mu yi magana".
Ga mamakina da Anti Maimuna sai kuwa ya sake ni, ta hanyar ingiza ni na fa'do daga kan kujerar.









# Team Gudale.
# Team Guduyo.
# Surayya Dee.
# Ana tare 🤝.
2/8/23, 10:23 - Buhainat: *Wannan littafin na ku'di ne, biya 500 ku'din karatu ta wannan asusun*
*2384876855*
*Surayya Ibrahim*
*Zenith Bank.*
*A tura shaidar biya ta wannan lambar*
*08032773332*.

*SDK*
*35-36*

Na dinga numfarfashin wahala da 'bacin rai.
Na kifa kaina akan lallausar kafet din da yake shimfide ina kuka sosai.
Kukan da ya ta'ba Sakina 'kwarai da gaske. Ta dago ni, ta zaunar da ni akan kujerar da ta yi nisa da wacce Gudale yake kai.
A hankali ta ce "Me kika yi masa?"
Na kasa bu'de baki na yi mata magana a dalilin yadda nake kuka sosai.
Ta dinga lallashina, tare da shafar bayana, sai da ta ga na 'dan sami nutsuwa.
Ta mike ta koma kusa da Gudale da shima yake faman haki saboda yadda yake cikin fishi.
A hankali ta ce "Na Moriki! Annabi (S.A.W.). Ya yi ta jan kunnenmu kar mu zamo masu saurin fishi. Idan kuwa har mun yi fishin to mu kiyaye zartar da hukunci a sadda muke cikinsa.
Na ro'ke ka! Ka daina biyewa zuciyarka a sanda kake cikin fishi, saboda Allah abin da kake yiwa Halimatu fa bai kamata ba.
Kwanakin baya a gabana ka mareta.
Yanzun kuma ka sha'keta ko matarka ce ita fa ka wuce iyaka, bare ba hakan bane, gaskiya wannan cin mutunci ne, na sani ba zaka so a ce wani ne yake yi mata hakan ba".
Ya zuba mata ido cikin fitar hayyaci ya nuna ni ya ce "Indai bata kiyaye ni ba! Ina tabbatar miki watarana sai na sumar da ita.
Na ce kar ta mini magana, amma saboda raini ya shiga tsakani na da ita, sai da ta yi".
Ina kallon yadda Sakina ta tsananta kallonsa ta ce "wai har yau maganar ba ta wuce ba ne? Saura kwanaki ka'dan ku zama abu guda kai da ita, idan kana irin haka hankalin iyayenmu ba zai kwanta ba Na Moriki".
Da sauri ya ce "Allah ya sauwa'ke na zama abu guda da wannan munafukar yarinyar, muguwa kuma ma'hainciya".
Tsoro ya kama Sakina a dalilin furucin da yake yi a kaina.
Ta kalle ni, ta ga na yi sururu ido duk ya ya ko'de.
Ta mayar da kallonta gare shi, cike da son jin mai ya kawo wannan takaddamar.
Ta ce "Saboda Allah me ta yi maka Na Moriki?".
Kamar ba zai yi magana ba, sai kuma ya tunzura ya ce "Ba 'dazu na yi miki waya akan ke da ita zaku raka ni na sayi kayan da zan saka a biki ba? Tunda haka Abba yake son na yi, na amince har zuciyata, tare zamu je da ku.
Na je jiya takanas na sanar mata, da kanta ta ce mini, zata zo gidan ki da wuri, sai mu yi amfani da motar ki, tunda weekend ne kina gida!
Tun 'dazu nake buga mata waya. Amma ta 'ki 'dauka, ashe tana can tana yawon barba'da hadi da iskanci da Ashiru! Ni zata wulakanta?
Sannan ta zo ta ce zata mini maganar banza".
Ya karasa cikin matsanancin bacin rai tamkar ya rushe da kuka .
Tsawon lokaci Sakina tana kallonmu duka.
A ranar ta fahimci Gudale yana sona, amma bai fahimci yana son ba bare ya tattala soyayyar.
Ta gane matsanancin kishina ne ya turnike shi. Ta dan samu sau'kin ru'danin da take ciki na zan auri wanda ba ya so na.
Ta sassauta murya sosai ta ce "Ashir din ne kake wannan tashin hankalin dan ka gansu tare, shin ba 'dan-uwanta bane?".
Da hanzari ya ce "Gara na ganta da Anas akan na ganta da shi. Ta sani Ashiru idan ya samu damar da zai 'batar da ni tsab zai aikata hakan saboda yadda yake tsananin adawa da ni".
"Ka sassautawa kanka akan wannan kiyayyar da kake yiwa Ashir baka san ranar da zai yi maka ba".
"Wallahi Sakina duk wani arzikin da zan same shi matu'kar sai ya biyo ta hannu ko hanyar Ashiru to na haramtawa kaina wannan arzikin".
Ya ja tsaki sosai.
Ya sake cewa har zuciyata bana sonsa, mutumin da ya zame mini cikas, sannan dake zuciyar sa 'baka ce, duk matan duniya bai ga wacce zata burge shi ba sai wannan abar"
Yana nuna ni, yana 'kyabe baki, ido kuma sun kankance tsabar masifa.
Ya sake zabura ya ce "Sakina In Sha Allah Ashiru ba zai yi albarka ba, ba zai rabauta ba, tunda juninsa nunkufurci ne da izgilanci".
Sakina da ta fahimci Kishi ne yake yagalgala shi, sai ta takaita maganar ta hanyar cewa "To na kashe wannan maganar, amma Wallahi idan ka sake yi mata irin wannan sha'kar tabbas sai Abba ya ji, ai kishi ba hauka bane".
Ya kuwa tunzura ya ce "Ummu" kina jinta ko?"
Dake haka yake kiran Anti Maimuna Kamar yadda su Abba suke kiranta.
Wanne kishi zan yi akan wannan yarinyar, ba sai da so ake kishi ba? Sanin kowa ne auren dole za'a yi mini, takura mini aka yi, yanzu kuwa zan na'de kafar wando na tan'kwabar da auren idan yaso a mini baki na dinga tsince tsince a kwararo kwararo. Allah barshi a dinga nuna Abba ana ga wanda ya tsinewa tilon 'dansa akan ya'ki yarda ya yi masa auren dole".
Anti Maimuna ta ce "A a ba hakan za 'a yi ba, ka kwantar da hankalinka, ka bi umarnin Abba! Kana ganin wanda ba su kai ka a jikinsa ba ma yana kirarin ya isa da su. Tunda musulunci addinin adalci ne, ya baka damar auren mace sama da daya, daga baya sai ka auri zabin ranka".
Tana direwa Sakina ta ce "Anti ki fa iya bakinki! Kar ki zo ki ji kunya"
Yayin da nake gefe ina fama da 'bacin rai sosai a raina, na dinga jin tabbas idan har Gudale ya mi'ka kudirinsa na fasa kar'bar aurena gaban Abba.
Ni kuwa zan taimaka masa dan Abba ya rushe maganar gaba'daya. Zan fadawa Abban nima na fasa, na yarda ya mayar da aurena kan Ashir! Na gaji da bala'in Sadik.
Nan gaba idan ban yi sa'a ba, shine ajalina. Raina ya sosu 'kwarai da abin da ya yi mini, mussaman yadda yake ta nanata baya sona.
"A hankali na ce "Nima ai dole aka yi mini! Amma saboda girman Abba ya zarce komai, shiyasa ban bude 'kofa ko guda da wani mahalu'kin zai fahimci hakan ba.
Na yi maka al'kawarin matu'kar ka fa'da masa ka janye aurena, ni kuwa ba zan ji kunyar fa'da masa dama ba so nake yi ba. Ina tabbatar maka kuma a ranar da aka sanya ta aurenmu, ba fashi a ranar zan yi aure. Domin ina da masu sona da ko a ranar ka ce ka fasa, su kuma zasu kar'ba cikin murna da godiya mai yawa."
Maganar ta buge shi ya mi'ke a harzuke Sakina ta ri'ke shi tana fa'din "Ba zaka sake ta'ba ta ba".
Na sake hassala na ce "Bar shi ya doke ni, ya janyowa kansa fishin Yaya Ashir dan kuwa sai na fa'da masa, idan ka fi karfina, ai shi baka fi 'karfinsa ba."
Hatta Sakina ta ka'du da kalamaina, bare Anti Maimuna da kuma Madugu uban tafiyar.
Ni kuma shak'enin da ya yi ne, ya 'bata mini rai har nake jin zan iya fa'da masa komai.
Ya dinga 'ko'karin isowa inda nake zaune, yayin da Sakina take ingiza shi.
Ni kuwa Ina zaune ko gezau ban yi ba, Ina jin na shirya faruwar komai.
Anti Maimuna ta ce "Tashi ki koma daki, kar ya zo ya miki abin da za'a ce bai kyauta ba alhalin kema tsiya ce fal cikinki".
Haushin ta ya sake tunzura ni, na ce "Da yake anan ne, amma da a gidan Sakina ne na tabbatar ba zai ma fara ta'ba ni da sunan duka ba, bare har ya yi mini abin da zai zama kaico".
Ta nuna ni da yatsa ta ce "ki shiga hankalin ki! Ni zaki yiwa rashin kunya?"
Na yi 'kasa da kai ina gungunin ta yi hubbu ra'as tsakanina da Gudale ma'ana ta nuna son kai.
Ta yi sororo tana mamakin abin da na yi mata wata'kila bata ta'ba zaton zan iya yi mata hakan ba.
Ni kuma abin da bata sani bane na da'de ina son na sami dama akanta dan na nuna mata ku'di da mulkin mijinta bai ta'ba sawa na yi mata wani kallo na daban ba, da ya wuce gidanmu guda.
Bana fatan na zo gaban ta da sunan ta yi mini kowacce irin alfarma tunda bata ganin darajar iyayena mussaman uwata. Ni kuwa ba abin da zai sa na ji nauyin yi mata iyashege idan ta shiga harka ta.
Na sani yanzu gadara zata dinga yi mini a matsayin ta na yayar Gudale.
Ni kuwa idan an 'kaddara ma ya zama mijin nawa, ita da Anti Juwairiya na sani baza su so ni ba, bare su mini karar ni kanwarsu ce ba wai matar kaninsu ba.
Dan haka ba zan takura kaina sai sun so ni ba, bare na yi ta yi musu fadanci da biyayyar dole.
Akan idona take fa'din bayan aurenmu ya nemo zabinsa ya aura.
Na kalli Gudale yaddda ya rungume Sakina yana sakin ajiyar zuciya! Ba kuka yake ba, amma yana cikin matsanancin tashin hankali.
Na da'de da gane duk da Sakina ba wani finsa da yawa ta yi ba, yafi sonta yafi raga mata.
Da kyar ta lalla'ba shi ta sanya direban Antin ya kai shi, akan muma zamu zo yanzu.
Tashin hankali sosai Gudale ya yi akan wannan maganar, tun ina ganin abin wasa ne, har na gane da gaske yake yi, domin yadda yasa abin a ransa sai da zazzabin takaici ya kwantar da shi.
Har sai da iyaye suga shiga maganar domin kuwa kafewa ya yi, ya fasa auren.
Ni ma kuma na kafe akan na fasa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login