Showing 54001 words to 57000 words out of 180068 words
din bana so.
Duk da a zuciyata ba hakan bane, domin har addu'a nake yi Àllah ya nuna ikonsa auren ya tabbata.
Da kyar Abba da Baban Gusau suka daidaita lamarin.
A tsukun motarsa ta iso. Saboda lalallaba shi da Abba yake yi, ya sake ha'da masa da sabuwar wayar da tafi kowacce daraja.
Ya Kara masa yawan ku'din sayayyar da zai yi.
Duk da hakan ba irin borin da bai yi akan a jawa Ashir kunne, ya kiyayi shiga lamuransa ba.
Aka cigaba da shirye shiryen biki, babu wata fahimta ko shiri a tsakanin ango da Amarya.
Kawai Abba ne yake ta kokarin daidata mu, domin nima an gyara mini waccan motar ta dawo tamkar sabuwa, to dama ba'a jima da sayanta ba, gata ya sanya mai ita ya ce ba ya sonta.
Hatta waya nima Abba ya canja mini, amma bata kai darajar ta Gudale ba.
Maimkon Yaya Sadik ya huce saboda wannan tagomashin da ya samu, sai ya sake gindaya gaba mai tsananin gaske a tsakaninmu. Saboda wai na ci amanarsa, na kuma yi masa rashin kunya, ashe wasa farin girki. Tanadin tsiyar da yake mini masu girma ne.
Duk hidimar bikin ta bangaren Gudale Abbas ne yake yinta a dalilin Yaya Al'amin baya jin da'din ko in kula da Gudale yake nunawa auren, shiyasa shima ya ja ya dake, ya fake da hujjar tunda ni ce amaryar ba zai shiga harkar yara ba.
Fa'din yadda aka shirya mana gidanmu bata baki ne.
Domin yadda gidan ya tsaru, haka aka sake kawata shi da jere na alfarma.
Tun sauran kwana goma masu shirya gida suka je suka shirya shi.
Kwanaki ka'dan dangin Mama suka je, Suka jera mini kayan kicin da sauran tarkace irin su zannuwan gado, da su frames masu tsada.
A bakinsu nake jin haduwar gidan, mussaman Aziza da ta jani 'daki.
Tana cewa "Gidanki ko a birnin Santabul ya kai gida sis".
Na dinga dariyar Aziza saboda iyashegenta.
Tun a wannan rikicin na fara gane zuciyar Yaya Gudale mai 'kullaci ce, mai wahalar a gane inda ya dosa ne.
Amma so ya sa idona ya rufe, na kasa yin jarumtar ha'kura da aurensa dan shine zai fi zama alheri.
2/10.
Aka 'daura aurenmu a massalacin Dangi na Aliyu bin Abi Dalib. Daurin auren da ya samu dafifin al'umma.
Hatta abokan kasuwanci da karatun Abba na 'kasashen k'etare sai da suka halarci 'daurin aurenmu.
Zuwa wannan lokacin Sakina ta ware da ni, sosai take hidimar bikinmu ka'in da na'in.
Kusan komai na hidimar bikin ita Abba ya 'dora, da taimakon Antin Zaria.
Shiyasa Umma bata samu damar yiwa bikin rikon sakainar kashi ba.
Abinci da nama tamkar wanda Abba ya yi shekaru masu dama yana tanadinsu, Raguna aka dinga yankawa sai a bankare su ana gasawa, kowa sai da ya yanki yadda yake so.
Bare kaji da kifi. Ruwa da lemon kuwa wanka ne ba'a yi da su ba, hatta almajirai sun tabbatar bikinmu na ya'yan gata ne.
A aurenmu ba batun a 'boye wani nau'in a abinci a bawa wasu isasshun mutane.
Abincin da ake bawa manyan mutane, hakan ma talakawa suke zuwa su dibi da kansu.
Mafi yawa mahalarta bikin sun fi kwatanta shi da bikin Tsohon Gwamnan jaharmu Mahmoud shinkafi da amaryarsa Takwarata Halima Babangida.
Saboda ba karamin bajinta aka yi ba.
Kowa sai da ya gamsu bikin na yan gata ne saboda yadda Abba ya kambaba shi.
Haka Sakina kusan duk bayan awa biyu zata saka na canja kaya, ga mai kwalliya a gefe, mussaman da aka yi sa'a aka tanadar mini wasu irin mayuka da powder na garari masu 'kara kyau da taushin fata, sannan basa bari na yi gumi bare aje ga jallin kwalliya ta cabe.
Kai madallah da kayan oriflame mussaman jakadiyarsu *Aisha lame *da zata nuna miki nau'in da suka dace da fatarki ga turaruka masu sanyin kamshi.
*07036662633*
Abin da ya yiwa auren cikas daya.
Rashin walwalar ango, domin gaba'daya ya ki yarda ayi hidimar cikin walwala.
Ko dinner din da aka yi daren jiya. Da 'kyar aka sanya ya halarta, haka ya zauna fuska babu annuri duk da yadda yake sanye da tufafi na kololuwar daraja, sai daukan ido muke yi, amma babu farin-ciki a kan fuskokinmu.
Tun ranar alhamis ake biki.
Ranar asabar din daurin auren da yamma Su Abba da Baban Gusau, da Yaya, da Maman Kebbi da kuma Babanmu.
Suna zaune a falon Abba cikin matsanancin farin-ciki.
Sadik suka sanya a gaba da nasiha iri iri.
Akan ya zauna da ni lafiya cikin adalci.
Ba'a jima ba Yaya ta iso dakinmu da muke zaune da 'kawayena mafi yawansu counsins 'dina ne da kuma Sakina da ta saje cikinmu, saboda bata da wani jiki duk da dai doguwace sambal.
Na saka dankareren leshin da aka samo shi a *Amyas newly & fairly items*. Dinkin ya yi matu'kar zama a jikina mussaman dana kasance mai fafffadan kugu.
Riga da zani ne, amma idan aka daura zani sai a rantse doguwar riga ce.
Ankammala gyara mini daurin 'an kwali kenan Yaya ta iso cikin dakin ta ce "na ta so ".
Da sauri Sakina ta ware wani hadadden mayafi tsadadde cikin order *Umm Muhd collection*
Haka ma takalmi da jakar da na sanya a wajenta aka samo su.
Wani irin kyau na yi ba 'dan ka'dan ba, sai walainiya nake yi.
Komai ya yi fiye da yadda ma na zata.
Sakina ta dauko turaren da ta zuba mini su a lefe. Ta fesa mini ka'dan, nan da nan 'daki ya kaure.
Hatta Yaya sai da ta ce "Sakinatu wannan turaren na alfarma ne, da alama ya lashe ku'di masu nauyi, sai dai Kuma ya ci kudinsa, abin a saya ne".
A hankali ta fa'di sunan turaren, ta san turarukan oriflame amma bata san wannan ba.
Yaya ta ce fa'da mini sunansa Sakina! Zan fa'dawa Juwairiya ta saya mini ko Ashir".
Da murmushi Sakina ta ce "Ni zan siya miki Yaya! Ai basu ka'dai ne yaranki ba".
Da annushuwa Yaya take cewa "Sakinatu 'diyar Abba! Allah ya miki albarka, ya albarkaci zuri'ar ki".
Cike da farin ciki ta amsa da "ameen".
Amma dai Sakina fa'da mini sunan turaren ko Ashir zai daure ya sanya a lefensa".
Da dariya Sakina ta ce "Ho Yaya! To ki kwantar da hankalinki da kaina zan siyo masa indai yana so.
Ri'ke ni Yaya ta yi muka fita, har falon Abba!
Kowa ya bu'de baki a cikinsu zai yi mini shaidar ha'kuri!
Suka dinga nanata ha'kurin da nake da shi yanzu zai ninka na da ne.
Tunda zaman aure ha'kuri shi yafi komai yawa a cikinsa.
Shikuma mai girma Ango jan-kunnen da aka fi yi masa shine ya zama mai sassauci da afuwa.
Ya yi mini adalci tunda dama kanwa nake a gare shi.
Idan na yi masa kuskure kar ya 'dauki mataki a cikin fishi.
Duk abin da ya taso mu yi kokarin magance shi a tsakaninmu, idan hakan ya ci tura sai mu saka wanda muka amince da nagartarsa.
A take Baban Gusau ya mi'kawa Yaya sadakina tunda shine waliiyina, inda wani abokin Abba 'dan Sudan ya karbawa Yaya Sadik auren.
Bisa al'adar gidan amarya ake bawa sadakinta a hannunta kafin a kaita dakinta.
Ta miko mini tana cewa "karbi sadakinki da Bismillah Halimatu".
Kaina a 'kasa cikin lullubi na karba din, ban duba ba, na mikawa Maman Kebbi! Ita kuma sai ta bayar a baka daga baya.
Baba dai bai ce komai ba a dalilin duk shine karaminsu, illah albarka da ya sanyawa auren da kuma fatan alheri.
A lokacin Abba ya ce "Yaya Idan kun yi sallar la'asar ku shirya ku kaita, ba sai duhu ya yi ba".
Ai kuwa Yaya Sadik ya ce "Abba!
Sai kuma ya yi 'kasa da kansa, ya kasa maganar.
Cike da kulawa sosai Abba ya ce "me zaka ce Sadiki? Fa'di muna sauraron ka".
Kansa a kasa, a hankali ya ce "Dan Allah Abba bana son gayyar nan da sunan rakiya plz".
Cikin rashin fahimta Abba ya ce "rakiya kamar ya ya, wacce irin gayya Kuma?"
Bai dago ba ya ce "Ni bana son wannan dafifin da sunan kai amarya".
Da sauri Abba ya ce "Tunda al'ada ce kuma musulunci bai hana ba, ban ga aibun sa ba. Ina ce yau ne kawai, gobe zasu sake rakata ne?"
Yaya Gudale ya yi kasa da kai ya 'ki tankawa dokin hukuncin bai yi masa dai-dai ba".
Yayin da zuciyata take luguden fargaba wato so yake na tafi ni ka'dai ko yaya ne nufinsa?
# Team Gudale.
# Team Guduyo.
# Surayya Dee✍️
# Ana tare🤝
2/8/23, 10:23 - Buhainat: *Wannan littafin na ku'di ne, biya 500 ku'din karatu ta wannan asusun*
*2384876855*
*Surayya Ibrahim*
*Zenith Bank.*
*A tura shaidar biya ta wannan lambar*
*08032773332*.
*AMYAS NEW & FAIRLY ITEMS*
*Suna sayar da atamfofi da lesina da kuma dogayen rigun na alfarama*
*Haka nan suna siyan kayan electronics idan kina bu'katar canji, ma'ana zasu kayan ki cikin daraja, sannan zasu sayar miki da nasu cikin farashi mai rahusa.*
*Hatta kayan furnitures, suna siya, suna sayarwa*
*Kina son siyan fili ko gida?*
*kuna neman gidan haya?*
*Kawai tuntu'bi mahukuntan a wannan lambar*
*08083909947*.
*SDK*
*37-38.*
Baban Gusau ya ce "Sadik kana son mutane 'kalilan su raka ta ne?"
Ya kasa magana a dalilin kwarjini irin na Baban Gusau.
Abba ya ce "shikenan Yaya da ke da Binta ku rakata duk mai son zuwa sai ya je daga baya".
Jin hakan ya saka Gudale 'dagowa ya ce "Dan Allah Abba zan tafi da ita".
Kafin kowa ya ce komai Abba da Baban Gusau sun ce "Madallah! Ko wani gidan za'a kaita ai zamu iya wakiltaka ka kaita dakinta, bare kuma dakinka zaka kaita da kanka, ai ba darajar da ta wuce hakan".
Kawai sai ji na yi Baban Gusau ya riko kafa'data ya mi'kar da ni, bayan ya ru'ko hannun Sadik ya mike, ya kama hannuna ya dam'ka a nasa.
Ya ce gata nan tafi ka kai ta! Amanarta na baka, nine Ubanku dukkan ku, sannan kuma nine wakilinta, ba wanda zan sassautawa a cikinku idan na same shi da laifin musgunawa 'dan-uwansa.
Allah ya albarkaci aurenku, ya sanya albarka da farin ciki a gidanku".
Hawaye ya balle mini, wanne irin abu ne haka Yaya Gudale ya yi?
Ba kunya ya dinga ja na, maimakon ya fita da ni ta ta waje, saboda sau'kin jama'a.
Sai ya bi da ni ta cikin gida, ta inda ake shiga garden.
Aka dinga kallonmu.
Muna shiga ya rufe 'kofar, sannan ya ja ni fii har ba'kin 'kofar mashigar falon.
Ya sanya key ya bude. 'Kamshi ya bugi hancina. Muna shiga ya wancakalar da hannuna tare da cewa sai ki laluba dakinki, ko ki tabbata a nan"
Ya isa bakin kofar ya tura ya rufe har da murza key.
Ya wuce cikin sauri ya barni a tsaye tamkar gunki.
Da kaina na tambayi kaina wacce irin amarya ce ni?
Na jima a tsaye na rasa inda zan sanya kaina.
Na dinga tuno 'kawayena da na halarci kai su dakin aurensu.
Ta yadda ake zama da su a dakunan su, ana hira da farin ciki.
Su kuma suna zaune a gefen gadonsu da ya sha lullubi na alfarma.
A karshe iyaye su watse, su bar amarya da 'kawayenta ana ta hira cikin shakiyanci.
Ba a barin amarya sai abokan ango, sun zo an sayi bakin amarya.
Sannan a mayar da su gida bayan an yi musu alheri.
Amma ni nawa kawayen ma suna can na barsu ko sallamah bamu yi da su ba.
Gashi hannuna babu waya tana wajen Sakina.
Kan dole na ja jiki na shiga dakin da Sakina ta ce mini shine dakina na kasa.
Na tarar da anyi shimfida ta alfarma, akan dankareren gado.
Na fa'di jagwab ina jin hawaye na goce mini.
Ban taba ganin doguwar rana irin ranar da aka na shiga gidan aurena ba.
Ba dan komai ba saboda yadda nake Jin tsananin takurar da na yi.
Na da'de kafin na ji ana kiran sallar la'asar.
Na tashi da 'kyar na doro alwallah, na kalli mayafin na tabbatar ba zai mini sallah ba.
Na rasa yadda zan yi.
Na bu'de drower na tarar da kayana na gida wanda nake sonsu da Sakina ta kawo su tun wanccan satin reras a jere.
Na 'dauko hijabi na tada sallah.
Na idar, ina kwance lamo.
Ina jin wani bacin rai na saka'da ta, na rasa gane manufar Gudale ta yi mini irin wannan wulakanci, ya rabo ni da cikin jama'a, sannan ya zo ya rufe ni.
Ya kasa marabta ta a matsayina na bakuwarsa a ranar farkonmu.
Hawaye ya dinga gangaro mini, ina tunanin wacce rayuwa zan yi da mutumin da na kallafa shi a raina, alhalin shi bai san sassauci ko ragayya ba?.
Biyar ta wuce na jiyo muryar Gudale a falo saboda ban rufe kofar dakin ba, sannan da 'karfi yake maganar.
Da na kasa kunne sai na gano waya yake yi, kuma da Sakina.
Ya 'daga murya sosai ya ce "Wallahi ba wacce zata zo mini gida a yau dai.
Duk nacin ki, bazan bu'de ba, idan kayan ne da gaske ki bawa Abbas, idan na fito sallar maghrib zan karbar mata".
Bansan me ta ce masa ba.
Na ji yana cewa "Eh na ce gidan nawa, da na ki ne?"
Ya katse wayarsa, ina jinsa har aka fara kiran sallar maghrib, sannan ya fita.
Yana fita kuwa aka dauke wuta, na rasa inda zansa raina, zafi, da duhu suka yi mini 'kawanya.
Ko bai rufe ni ba, ba iya fita zanyi ba, bare ya rufe ni ruf.
Bai shigo gidan ba sai da aka idar da sallar isha da lokaci mai tazara.
Ya dawo yana haska gidan da fitilar wayarsa.
Yana janye da akwatin kayana. Har cikin dakin ya shigo ya ajiye akwatin a tsakiyar dakin.
Sannan ya juya ya yi tafiyarsa, ba wani magana ba komai.
Hawaye ya silalo mini, kafin na yun'kura na ga an dawo da wutar.
Hakan ya bani damar ganin jakar hannuna a gefen akwatin, da kuma wata farar leda.
Jikina na bari na janyo jakar, na bu'de na 'dauko wayata.
Na sake dauko ledar na bu'de na ga lemo mai sanyi, da kuma ruwa, sai wata 'yan robobi guda biyu. 'Daya dauke da pepper chicken, 'dayar kuma wainar shinkafa ce, ga yajin kulikuli an nade shi cikin poil peper.
Na manta ni amaryace, na dinga cusa wainar nan da ta yi mini da'di ba ka'dan ba.
Ina ci, ina zare ido tabbacin yinin yunwa na yi.
Na cinye, na ji ba inda ta je mini.
Na koma kan aminiyata kaza, nan ma sai da na ci karfinta, sannan na ji ta ishe ni.
Na kora da lemon fanta.
Sannan na yi gyatsa, na yi Hamdala. Sai na tsinci kaina da yiwa duk wanda suke zama da yunwa a dalilin jinya ko talauci addu'ar samun sassauci.
Yunwa masifa ce, mabudin aikata barna ce, Allah ka wadatamu da lafiya da kuma 'koshi.
Na kishingi'da ina Jin sau'kin damuwar da nake ciki.
Sakina ta fado mini, ina jinjina yadda ta damu da ni, na tabbattar Sakina tana mini so irin na wanda kuke same parents.
'Kwalla ta cika mini ido ina jin wani irin al'amari na shiga jikina akan halayyar Sakina.
Ta aiko mini da abinci, saboda ta san na yini ban ci ba, ta kuma sani 'kaninta ba zai damu ya ciyar da ni ba, duk kuwa da hakkin akansa ya rataya.
A fili na ce "Allah ka wanke mini zuciyata! Allah ka cika mini ita da alheri kamar yadda ka cika zuciyar Sakina da Abbanta
Na shiga 'bandaki na wanko hannu da bakina. 'Kasan kafet din na kishingi'da ina duba wayata, ina kallon status 'din jama'a dauke da hotunan bikina suna mini fatan alheri.
Ni da kaina mamakin kaina nake yi, saboda yadda na yi wani irin shu'umin kyau, kyaun fatata na matu'kar ki'dima ni.
Madallah da mayuka da kayan gyara na *Aisha lame da Faseelat*.
Ban 'bata lokaci sosai ba, na kashe datar na fito da caja na jona caji.
A inda nake kwance barci mai nauyi ya yi awon gaba da ni.
Ban farka ba, sai karfe shida na safiya.
Na tashi ina istigifari, tare da tunanin wanne irin barci na yi haka, da ban ji 'Kiran sallah ba?
A gurguje na 'doro alwallah! Na tada Sallah.
Na idar, ina zaune ina zikirin safiya.
Na kammala ina sake jin barci na 'diba na, ban yi mamakin yadda nake barci ba, saboda yadda na tara shi ba ka'dan ba.
Na sake kwnaciya, ina mamakin yadda na iya kwanciya da kayan jikina.
Ban sake gane inda nake ba sai takwas da rabi na safe. Na bu'de akwatina na fito da tawul da setin kayan wankan oriflame wanda suka dace da farar fatata, ya kuma dace da dry skin 'dina. Na shiga ban'daki, cikin Sa'a na kunna hita ba jimawa kuwa ruwan zafi ya iso famfon.
Na sirka ruwan wanka mai dumi sosai dan na wartsake gajiyar da nake fama da ita.
Na fito wankan daure da tawul, cikin nutsuwa na shirya, na yi matu'kar kyau cikin jan tattausan swisss material kirar kasar Dubai odaer din *Amyas newly & fairly items*.
Sabon da na yi da siyayya a wajen *Amyas* na 'karyata batun da ake cewa kayan mata yafi tsada.
Na dauko turare ina fesawa na dinga jiyo ana kwankwasa kofar falon, na yi kamar na fita na bu'de sai kuma na fasa, a dalilin fargabar ha'duwa nake yi da Gudale.
Na zauna bakin gado ina sake jin kwankwasa kofar na sake tsananta.
Kafin na yi wani abu, na ji wayata ta hau kuwwa, na tashi na dauko ta akan madubi.
Ina dubawa na ga Yaya Sadik ne.
Zuciyata ta harba da tsananin gaske.
Na daure na amsa, na kanga a kunne.
Cikin fa'da ya ce "Ba ki ji ana kwankwasa 'kofa bane?"
Na ma'kal'kale murya na ce "Ban ji ba! Barci nake yi".
Ya ja uban tsaki ya ce "Mai 'karya dai 'dan wuta, turaren uwar waye ya ke kawo mini ziyara har nan?"
Na sani turaren da na sanya ne saboda yadda yake da kara'de waje cikin 'kan'kanin lokaci.
Amma na waske na ce "Anya kuwa? Bansa turare ba fa".
Ya ja tskai ya ce "Munafuncinku ya 'kare a kanku ke da Sakina".
Na yi shiru ban amsa masa ba, illah iyaka na ji da'din yadda turarena ya isar mini da sa'ko a wajensa.
Ya ce "Zaki fito ki bu'de ko kuwa?"
Na shagwabe murya na ce "Fisabidillahi ina ba'kuwarka, kuma amarya ka ce na fita bu'de 'kofa da sassafen nan, sai ka ce Amaryar buzuzu?"
Da sauri ya ce "Oh kin dauka kin kai ta buzuzu a wajena?
To amaryar buzuzu ta kere ki, tun jiya ya kamata ace kin fahimci hakan".
Na murmusa ka'dan na ce "Ina tausayinka ranar da zaka zama tamkar ango irin *Ayu*. Ni kuma a ranar zan baka raddin na wuce duk yadda kake tunanina."
Da hanzari ya ce "Guduyo menene *Ayu* kuma?"
Dariya ta so kwace mini saboda yadda ya yi tambayar a 'dan tsorace.
Na ce wani halittar Allah ne mai tsananin son mace, mussaman matarsa".
Ya nisa ya ce "A wanne jinsin yake?"
Na ce "ba mutum bane,