Showing 60001 words to 63000 words out of 180068 words
kula".
Ya sake 'daure fuska ya ce "Wallahi matu'kar baki fito mini da kayan da Ashiru ya siya miki ba, ba zaki taba gane kaina ba".
Na yi shiru a hankali na ce. "Wannan dispenser 'din ce sai kuma wani dinner set yana kicin".
Ya yi shiru tsawon lokaci sannan ya ce "Tashi ki dauko mini".
Na tashi na dinga lalube a kicin har na ga inda aka saka, Àllah ya so ma ba'a bude ba.
Na kasa 'dauka saboda nauyinsa, da 'kyar na dinga turo shi har na iso falo.
Ina 'dan haki na ce "gashi."
Ya yi mini lalataccen kallo ya ce "Sai ka ce wanda kika yi wani abin a zo a gani kike wannan haki".
Na yi kasa da kaina ba tare da na ce uffan ba.
Ga mamakina cak ya kinkimi kwalin ya fita da shi, sannan ya dawo ya dauki dispenser ya fice.
Jimawa ka'dan ya dawo ban san yadda ya yi da su ba.
A tunani na matsala ta kare a tsakanin mu.
Ashe ban fara ganin matsaloli ba ma.
Ya hau dinning ya ga shinkafa.
Ai kuwa ya dinga sababi ba zai ci shinkafa da daddare ba.
Jikina na rawa na ce "Yi hakuri bani minti na ka'dan na samo maka abin da zaka ci".
Na shiga kicin na fito da meat pie guda uku na soya masa, na dafa shayin da ya ji citta da kaninfari.
Na kai masa. Sanin da na yi idan ban zauna ya gama ci ya barni a wajen ba, na yi laifi. Kan dole na ja kujera na zauna ina kallonsa yana ci cikin yanga da basar wa.
Yana kammalawa kuwa ya mi'ke ya haye sama ya bar ni.
Na dinga mamakin wannan wulakanci na Gudale.
Na kalli kaina na dinga jin ko dai ban kai mace bane da har ya iya kauda kai akai na irin haka, shin wula'kanci ne ko kuwa rashin so ne?.
Da na ga tunanin zai yi mini yawa, sai kawai na je kicin na wanke yan plates din da muka bata.
Na juye miya da shinkafar na sanya a fridge, na wanke kulolin.
Na kashe fitilu da fanka.
Na shige daki, wanka na yi, na fito da alwallah na yi sallah, na yi shafa'i da wutiri.
Na dinga addu'a irin ta 'dazu, yanzu kuma na 'kara da ro'kon a sanya mini ha'kuri mai yawan akan lamarin Gudale.
Na jima ina addu'ar sannan na tashi na dauko maina na kamfanin oriflame na shafe jikina.
Na sanya rigar barci, na kwanta ba tare da na fesa turare ba, saboda yadda man da na shafa ya karade ni da kamshi mai da'di.
Na yi barci mai da'di a dalilin mafarkin da na yi na haifawa Gudale kyawawan yara masu kama da shi.
Da nisha'di sosai na tashi.
Haka kwanaki suka dinga wucewa har na samu sati guda a gidan aurena.
Wanda kwanaki bakwai din farko ma cikin ha'kuri na yi su.
Domin bai saurare ni ba, bare mu fahimci juna, tun ina saka ran zamu shirya har na fara cirewa da naga na doshi sati biyu kullum al'amarin nasa na sake cabewa.
Kullum sai Sakina ta yi mini waya, tana tambayar lafiya muke?
Da walwala nake amsa mata lafiyar mu kalau. Domin ina jin kunyar na yi mata 'korafi akan Gudale.
Domin ba karamin abin kunya bane na ce na fara fuskantar wula'kancin sa, zan yi dukkan juriya dan kada kunya ta a idon masu guje mini aurensa.
Ranar Monday din da ta yi daidai da kwanaki na goma sha shida a gidan.
Sassafe na tashi na shirya masa abin karyawa.
Nima na karya, na yi shirin tafiya a asibiti, tunda yanzu asibiti zamu yi second semester din.
Doguwar rigar shudin voile na sanya wanda jikinsa akwai jajayen stones.
Ban 'daura dankwalinta ba sai na sanya. Wani Dan karamin hijabi iya kafada a dalilin labcoat zan sanya. Ban saka turare ba, illah na goga roll on din oriflame shima a wajen *Aisha lame 07036662633* muka samo shi.
Kamshinsa kawai ya isheka har washagari.
Na dauko hand bag 'dina wanda special order ce ta *Umm Muhd collection 08063358662*.
Na saka duk abinda zan bu'kata, na rataya na fito bayan na sanya flat din takalmi mai stone jah, sannan kuma mai igiya ne.
Mai da powder kawai na shafa, amma sai na yi wani irin kyau tamkar dai wata amarya mai karama.
Na hau saman, bayan na saka labcoat din.
Yana kwance cikin bargo, amma idonsa biyu.
Daga bakin 'kofar na gaishe shi na ce "Zan je asibiti".
Ya tashi zumbur ya na 'kare mini kallo.
Cikin takaici ya ce "Tsakani da Allah an gama da ni, ban ta'ba sha'awar auren wacce bata kammala karatun ta ba.
Amma kawai aka yi mini 'karfa 'karfa, wato ma sai da kika shirya zaki fa'da mini? To me ya hana ki yi tafiyar ki kawai?"
Na danne 'bacin ran da ya taso mini na ce "I taught kana sane da two weeks suka bani, amma ka yi ha'kuri".
Ya ce "kina nufin a haka za ki tafi? Kin ci kwalliya tamkar me zuwa party anya Guduyo kin san hukunce hukuncen Shari'a kuwa?"
Na kasa cewa komai.
Kai tsaye ya ce "je ki canja wannan kayan ba zaki fita da su ba".
Ban ce komai ba na fita.
Na sanyo riga da siket na atamfa, na koma.
Tun kafin ya yi magana ya dinga girgiza kansa tabbacin ba su yi masa ba. Da yatsa ya ce "kin ga yadda siket din ya kama ki kuwa?
Koma ki canjo wasu".
Raina ya fara baci , amma na daure na ha'diye fishin nawa.
Haka na sake komawa na sako wani yadi tamkar na rariya, an yi masa dinkin straight gown. Na 'dora labcoat din, sannan na sanya farin hijabi mai hula, ya sau'ko har kafadata.
Na sake komawa yana zaune a tsakiyar gadon.
Ya kalle ni ya ce "Asali fa harkar kiwon lafiya akwai munafunci a ciki, dan menene mace musulma ba zata saka hijabi har 'kasa ba?"
Na sunkuyar da kai 'kasa ina addu'ar Allah ya sanya ya barni na tafi, Ni dai.
Dan na lura jidali yake nema na da shi.
"Yauwa na tuno! Menene Ayu din da kike mini fatan na zama, tunda kin ce kada an saka sunan ki a ciki, sai nake ta zullumin kada na yi tambaya a ga tamkar Kan nawa da motsi".
Dariya ta kwace mini sosai saboda tsakaninsa da Allah ya yi maganar.
Na ce "Na janye yi ha'kuri ni kaina ban san shi ba, a talabijin na ji an fa'da".
Ya daure fuska ya ce "Ai idan kuna biye dramar yan wasan kwaikwayo da labarin novels kun dinga shiga cikin garari kenan, domin zama ake ana shiryawa dai-dai da ra'ayin da zai ja hankalin mutane.".
Na ce "Ai kuwa Yaya Gudale suna debe kewa da cire takaici, kawai kowa da yadda yake kallon su ne, amma ai akwai masu fadarkawa da kuma darussa wanda babu son zuciya".
Ya canja maganar da cewa "To kuma sai na tashi zan nema wa kaina abin da zan ci tunda shi ka'dai ne hakkin da kika gamsu ya zame miki wajibi ki yi mini?"
Ya fa'da a tunzure ka'dan.
Na kasa gane wannan jirwayen nasa.
Amma sai na basar na ce "Na kammala tun tuni".
"Me kika yi?"
A hankali na ce "Irish na soya maka sai na yi maka miyar albasa"
"To daga yau kar ki sake soya mini dankali ki saka a flask, na fi son sa a plate da zarar an kwashe shi daga mai".
Da sauri na amsa da cewa "zan kiyaye".
Ya kalli farin Tom's din da yake 'kafata.
Ya mike da nufin ya shiga toilet.
Da sauri na ce "sai na dawo".
Bai juyo ba ya ce "ki jira ni Malama".
Na sauko ina jin zuciyata na tafasa,na gane dai so yake sai na makara.
Ba da'dewa ya fito, yana kallona ya wuce ya fice.
Motar da ta zama mallakina ya yi amfani da ita ya kai ni har cikin asibitin Murtala.
Da zan sauka ya zaro 'dari biyar biyu ya bani, yana cewa "kina gamawa ki hau adaidaita ki dawo, ban amince ki tsaya a ko'ina ba".
Na kar'ba ina godiya, domin dai na ga alamun sassauci ka'dan duk da yadda ya sanya na hargitsa kayana.
Ina tafiya ina tunanin menene ma'anar shaguben da yake yi mini na bansan komai a hakkinsa ba sai dafa abinci?
Yana nufin ni zanje 'dakinsa da nufin wani al'amari ya shiga tsakanin mu ko kuwa?
A fili na ce "Tabdi jam! Rashin ajin nawa bai yi tsananin hakan ba, zan dai cigaba da tattala kaina ta hanyar riko da kayayyakin Fasilat da ta zaba mini masu koluluwar amfniyda gyara mace. Tun yanzu nake jin sauyi da nisha'di sosai a tare da gangar jikina. Har na gasgata idan ka samu kwararriyar da hada kayan G.H.T. kamar na yadda Faseelat take yi, to kin yi bankwana da infection da dryness in sha Allah.
*Faseelat G.H.T.
*Tuntube ta a wannan layin domin ita din kwararriya akan sana'arta, kayan ta ingantatu ne sannan zata yi miki sauki kwasha kwasha ta yadda zaki gamsu ta zarce sauran*
*07039269802*.
# Team Gudale#
# Team Guduyo#
# Surayya Dee ✍️
# Ana tare 🤝.
2/8/23, 10:23 - Buhainat: *Wannan littafin na ku'di ne, biya 500 ku'din karatu ta wannan asusun*
*2384876855*
*Surayya Ibrahim*
*Zenith Bank.*
*A tura shaidar biya ta wannan lambar*
*08032773332*.
*Akwai harda copy na littafin *Kasaita*
*Na marubuciya Maryam Kabir Mashi*
*Mai so ta yi mini magana akwai shi a hannuna yanzu haka 1-3 ne*.
*Faseelat mai gangariyan supplements din da suke karawa mace dandano da Kuma daidaita zahirin surar mace*
*Shin kina fama da basir ko ulcer?*
*Shin kina fama da tumbi?*
*Shin kina fama da rashin ni'ima?*
*Kina bu'katar mayuka masu gyara fata?*
*Kwantar da hankalinki kukan ki ya zo karshe domin Faseelat karshe ne a wannan fagen ga ta da sau'kin farashi*.
*Ki tuntube ta a wannan layin 07039269802*.
*SDK*
*41-42.*
Present.
Yauma 'kiran sallar azahar ne ya ankarar da ni, daga dogon tunanin da nake yi.
Na tattara littafan da na tara a gabana, amma ban samu sukunin bibiyarsu ba, saboda yadda nake son na tariyo zamana da Gudale ya shiga zuciyata, tabbas sai na yi bita a nutse cikin adalci sannan na auna shi a ma'auni dan na yi hukunci na gaskiya.
Sai da na sauke farillah, sannan na shiga kicin.
Ina kicin 'din su Amna suka shigo, dake yanzu ta kofar kicin ake shigowa. Sanye suke cikin dogoyen riguna iri daya, cotton masu tsananin kyau, a yanzu da Kaya suka ta'azzara da tsada na sani ba 'karamin ku'di zasu lashe ba.
Hatta hular kansu mai karshen tsada ce itama kuma iri 'daya kalar lemon green a dalilin flower rigar koriya mai haske ce.
Kafafuwansu sanye cikin takalmi tamkar sandal amma an'kawata shi da stones masu 'daukar ido.
Sai 'kamshin turaren *kidiz* suke yi. "Momy"
Suka ha'da baki wajen kirana sannan dukkansu suka rungume ni.
Na dinga jin farin-ciki na mamayata, ba abin da nake so sama da wa'dannan yara.
Zan yi komai, haka zan bar komai dan rayuwarsu ta inganta.
Zamansu a Abuja ya sanya na sake fahimtar wani darasi a rayuwa.
Tabbas mahaifiya 'daya ce a fa'din duniya, amma idan mutum ya yarda zai yi uwaye 1000.
Matu'kar zaka mutuntunta mutane, ka yi hakuri da cutarwarsu, ka tsananta addua. To da sannu Ubangiji zai daidaita maka lamurunka da su har ayi ta zaton tamkar ka asirce su ne.
Antin Zaria ta wuce Yaya a gareni, ko kuma Yayar miji.
Uwace ta sosai domin ta yi mini abin da uwa ce zata yi mini babu gajiyawa.
Na sani 'ya'yan Gudale take hidima da su amma da ban yi hakuri da shi ba, da ban yi ha'kuri da cutarwar mahaifiyarsu ba, da ban girmamasu ba, da sun bar ni da ya'yana cikin halin wula'kancinsa.
Da ban yi juriya ba, da ban samu gata da goyon baya a wajen Sakina ba. Tunda tun farko ba abin da fa'da mini dan ta kubutar da ni shiga matsalar da take hango mini idan har na kasance matar Gudale.
Hakanan yaran da ban tsaya na nuna musu soyayyar da kowa yake fa'din na ma'kala su a raina ba, da ban hango tarin soyayyata a zuciyarsu ba, wata'kila da tafiyar nan da suka yi da basu yi kewata ba. Kamar yadda na tabbatar basa kewar mahaifinsu.
Ni kuma ba zallar soyayya irin ta batanci nake gwada musu ba, soyayya ce mai cike da tarbiya da kuma tausayi, saboda ubansu ba su yake son a haifa masa ba.
Ya'ya maza yake so wanda zasu zame masa garkuwa.
Shiyasa ni kuma nake tsaye akan su dan kar su rasa soyayyar uba, su kuma rasa ta uwa.
Na yi imanin wanda Ubangiji ya azurta shi da yara mata, ya masa arziki mai yawa. Domin kuwa tausayi da jin 'kai sai mata, matu'kar an musu kyakkawar tarbiya, An kuma yi sa'a sun tashi akan wannan tarbiyar. Shiyasa nake hana idona biyu da daddare nake yi musu addu'a da fatan Ubangiji ya shirya mini su, su zama masu albarka masu amfani, Ina fatan su zama tamkar su Antin Zaria.
Na durkushe kan guiwoyina, na janyonsu, kowacce na gefen hannuna.
Na kallesu da murmushi mai yawa.
Amna ta ce "Ina yini Momy?"
Afra ta ce "Momy ina kwana?"
Na ce "sai yanzu kika tashi ne Afrah?
Kina jin Ablah ta ce ina yini, ke kuma kika ce ina kwana, bayan yanzu ba morning bane Noon ne".
Tasa daukkan hannu ta rufe fuskarta wai ita kunya.
Muka yi dariya ni da Amna.
Na ce "To me zan dafaa mana tunda ban riga da na 'dora abincin ba?".
Amna da ta gaji Babanta wajen son snacks a matsayin abinci ta ce "Akwai meat pie a fridge?"
Na ce "Gaskiya Babu Ablah".
Afrah kuwa ni ta biyo daga siffa har dabi'u kawai dogon gashinta mai sulbi da kuma wasu daga kammanin Babanta , suka kara mata kyau sosai fiye da Ni. Amma da ke jikina ta debo Yar duma duma ya sanya take da farin jini kwarai da gaske.
Ablah kuwa ba inda ta bar Sakina, duk yaran Sakina ba mai kama da ita tamkar Amnah.
Ta ce "Momy to mu ci Indomie mana, amma ni dai a saka mini cinyar kaza".
Na yi dariya, yayin da Amna ta ce "Ai shiyasa kullum kike zama fatt bon bon".
Na ce "to kuje ku yi sallah kafin na gama mana".
Har sun fita sai Afrah ta dawo ta ce "Momy ina 'kanin Ablah?"
Na yi murmushi na ce "Yana tare da Dadi".
Ta ce "yanzu idan muka zo wani hutun zan ga kin samo mini nawa 'kanin?"
"Ho Afrah je ki yi sallah! Ai na dauka ma ba zaki koma Abujan ba".
Ta ruga da gudu tana cewa "Zan koma Momi! Dadinmu na Abuja baya fa'da, baya dukan Mama. Baya zare ido, baya cewa sai mun zauna a waje 'daya, sannan yana yawo da mu a mota".
Ina jin Amnah ta ce "kin manta Afrah damu yake zuwa shopping mu zabi abin da muke so. Sannan ya ce idan bamu koma ba, a Kano ba irin makarantar mu ta can mai 'dakin barci da na wasa".
Ban ce musu komai ba, illah iyaka na da'de da fahimtar suna jin da'din zamansu a Abujan, sannan na gane mijin Antin Zaria na matu'kar kaunar su, yana nuna musu soyayyar da mahaifinsu bai muna musu ba. Duk kuwa da ya manyata, dan a matsayin jikokinsa suke.
Na gama dafa mana indomin na samu madaidaicin tire mai circle mai dan zurfi na juye a ciki.
Na daukar musu kananun lemon Ribena ni kuma na dauki pure water mai karancin sanyi, yayin da na daukar musu marar sanyin gaba'daya.
A falo muka zauna bayan na shimfi'da mana ledar cin abinci.
Sai da suka cire rigunansu suka zauna daga su sai best da pant dinsu mai kama da short nika.
Muna ci suna bani labarin Kayan da'din da yake gidan Maman Abuja tunda su basu santa da Antin Zaria ba.
A haka ya dawo ya same mu.
Aman na rungume a jikinsa da alamun barci ya yi. Ya zauna yana kallonmu, yaran duk suka yi 'dif, suka zama a takure.
Shi da kansa bai ji dadin yadda suka zama ba.
Ya waske ya ce "Amnah wa Afrah ba gaisuwa?"
Suka hau fadin"Dadi ina kwana" cikin rawar murya.
Sun manta matashiyar da na yi wa Afrah dazu cewar yanzu ba safiya ba ce.
To babu sabo ko shakuwa a tsakaninsu.
Afrah da ba sosai take jin tsoronsa kamar Amnah ba, ta mike ta wanko hannunta, ta dawo ta isa kusa da shi tana leken fuskar Aman dake barci sosai akan cinyoyinsa.
Ta mika hannu tana cewa "Kanin Abla ya kara girma Momy".
Tana rufe baki ya ce " ke ba kaninki bane Afrah?"
"Eh ai sunansu 'daya da Ablah! Da na yiwa Momi kuka shine ta ce idan ya girma, nima zata samo mini nawa 'kanin Baby boy mai kyau! Sai a sa masa Afreen. Ka ga Amnah wa Aman! Afrah wa Afreen".
Ya zuba mata ido yana jinta har cikin ransa, yarinyar ruwa biyu ce, kammanin Guduyo da nasa duk ta ha'da sannan mai wayo ce sosai tamkar dai Yar tsofi.
Ya janyo ta jikin sa karon farko da nufin nuna kulawa ba dan rashin lafiya ko dan ya hukuntata ba.
Ta 'da'dare ta ce "Dadi am sorry! Na yarda 'kanina ne".
Ta fa'da tana tunanin laifi ta yi masa.
Cike da alhini ya ce "Fa'da miki zan yi, ki sake ro'kon Momi akan ta cika promise 'din samo miki na ki 'kanin domin ta ce mini ta fasa".
Ta juyo ta zuba mini ido ta ce "Momi kin fasa wai?"
Na girgiza kai na ce "ban fasa ba Afrah"
Ta kyale-kyale da dariya sosai tare da cewa "Na sani Mominmu ba 'yar wuta ba ce, tunda Mama ta fa'da mana mai 'karya 'dan wuta ne".
Dukkanmu muka zuba mata ido, kafin na ce wani abu. Amnah ta ce "Momi kuma promise kika yi mata, ba kyau rashin cika al'kawari".
Mamakin yadda yaran suka 'kara wayo ya kama mu gaba'daya.
Na bagarar da maganar da cewa Amnah "dauke tray din ki wanko hannun ki'.
Ta tashi da sauri ta yi abin da na umarce ta.
Na mayar wa da Afrah rigarta, yayin da Amnah ta saka tata da kanta.
Rashin sabon da babu a tsakaninsu da shi ya sanya Amnah cewa "Afrah zo mu tafi wajen Maman Abuja, ta ce dama zamu fita unguwa".
Da gudu suka fita, na bisu da kallo ina jin tamkar su dawo na cigaba da kallonsu.
A sanyaye ya ce "Halah ba gaisuwa? Ba barka da zuwa, balle a bani ruwa na sanyaya ma'koshina".
Na yi kamar ba da ni yake ba.
Takaicin share shin da na yi, ya