Showing 27001 words to 30000 words out of 180068 words
ya sanya jar T-shirt an rubuta Gudale da babban ba'ki a bayan rigar. Kansa cike da suma ba'ka sidik irin ta fulanin Yola, ta sha gyara sai sheki take yi. Sosai ya yi kyau, kuruciya da 'karfi a tare da shi muraran.
Ya zauna kujerar da take fuskantar wacce nake zaune.
Ya 'dago muka hada ido, yana mini wani irin kallo mai sanya 'ya'ya mata diriricewa.
Na dinga jin wani irin al'amari na ratsa ni, na dinga kame-kamen kunya. Da kyar na ce, "Don Allah na kawo maka abinci ka ci?"
Ya harare ni sosai tare da cewa, "Kin ta'ba ganin na ci shinkafa da wake da yaji da mai?"
Da sauri na ce, "To na yi maka indomie mana?"
Ya yi shiru! Tamkar ba da shi nake yi ba. Sai da na maimaita har sau uku. Ya numfasa ya ce, "Je ki yi mini, amma idan kika da'de ba zan jira ba".
Da sauri na mi'ke ina cewa, "Ba zan 'da'de ba In Sha Allah".
Ina shiga kicin din Umma na jona ruwa a butar ruwan zafi, sannan na hau yanka albasa a zagaye (slice) sai da na yanka da yawa sosai, sannan na jajjaga atturuhu. Na kunna gas, daidai lokacin butar ta kashe kanta, tabbacin ya tafasa.
Sai da na soya albasa da atturuhun sama-sama, sannna na zuba ruwan zafin, na zuba indomie din, na rufe. Na bude firij ina duba ko zanga wani abu. Ai kuwa na ga wani kwano shake da soyayyun kaji, da alamu suka nuna pepper chicken ne.
Da kyar na banbaro, na zuba su a container da zata shiga microwave don dumamawa.
Mintina ka'dan suka kammala.
Jiki na rawa na shirya masa a tray tare da ruwan roba da dole shi yake sha, ha'di da lemon Lacasera, tamkar mai gida. Na dauka da rawar jiki na kai masa, na tarar da shi ya kishingi'da ya dora kafa daya kan 'daya, yana wayar da na tabbatar da mace ce.
Na ajiye masa a kan side table din da yake kusa da shi.
Na zauna ina sauraron yadda ya makale murya yana magana 'kasa-kasa tamkar ba Gudale ba, da kullum maganarsa a kausashe take.
Haka kawai na ji raina ya baci, kishi mai tsananin gaske ya turnike ni. Ba yadda za a yi kuma na ce masa don me yake yin waya da wata? Na mi'ke da nufin bar masa wajen tun ban fara zunduma ihu mai gigitarwa ba. Har na je bakin kofar barin falon na ji ya bude murya sosai ya ce "Guduyo."
Na juyo a hankali! Alamun dai shi nake sauraro.
"Zo ki kwashi abincinki ba zan ci ba, ni za ki zo ki dangwararwa ki yi tafiyarki?
Zo ki kwashe mini su, tun raina bai fi haka tafasa ba".
Na dawo na zauna, cike da rawar murya na ce, "Ka yi hakuri to".
"Ki fa tattare mini su tun ban watso miki ba".
Na fara kuka ina cewa, "To ai na ba ka ha'kuri".
Ya kafe ni da ido yana kallona sosai. Ya nisa ya ce, "Mene ne yasa ki kuka?"
Na sunkuyar da kaina kasa ina shasshekar kuka sosai.
Ya dinga fa'din, "Ba na son haka, tsakani da Allah ba na so, me na yi miki for God sake?"
Ya hau bude plates din yana fa'din, "Dauko wani cokali mai yatsun ki taya ni ci".
Na girgiza kai alamun ba zan ci ba. Ya mi'ke yana cewa, "To kwashe su ba zan ci ba, tunda ba ki san abin arziki ba ke sam".
Cikin muryar kuka na ce, "Dazun nan fa ka ga ina cin abinci, na koshi ne".
"Ba ruwana da koshinki".
Ya fa'da kansa tsaye. Na mi'ke na yi kicin na dauko cokalin na zauna ina taya shi ci din, duk da ba wani ci nake yi ba.
Ya cinye abincinsa.
Ya sassauta ya ce, "A bangaren abinci ba ki da matsala Guduyo".
Na daure fuska ba tare da na amsa ba. Ya kafe ni da ido ya ce, "Ban gane ba?"
Cike da ta'bara na ce "Na gode to".
Ya mi'ke yana cewa, "Wallahi kin same ni da yawa, ban san dalilin da idan kina wannan kumburar nake jin babu da'di ba, bayan duk wulakancin da kike mini."
"Hmm! Allah ya ba ni ha'kuri Yaya Gudale da za ka zauna ka dinga yi wa wata macen 'yar murya akan kunnena."
Ya yi shiru amma ya zura mini manyan idanuwansa masu kaifi. Ni ma na zuba masa nawa tsawon lokaci muna hakan. Ban san ya aka yi ba nawa idon ya fara zubar da hawayen da ban san manufarsa ba. Ya koma ya zauna ya ce, "Wai na tambaye ki mana. Shin kishina kike yi ne?"
Cikin murya marar amo na ce, "Ba na son ka jajibo wacce za ta raba zumuncin da yake tsakanina da kai ne, musamman idan ta gane ni din ba Sakina ba ce a wajenka."
Ya ce, "Wallahi Guduyo wani lokacin sai na ji tamkar kin zarta Sakina a gurina, idan mun yi fa'da fa ba na jin da'di, idan ba kya gidan nan sai na ji ya mini girma, idan na tuna aure zaki yi nan gaba sai na tsinci kaina cikin faduwar gaba mai tsananin gaske".
Wani irin dadi ya kama ni, na murmusa na ce, "Fiye da hakan nake ji Yaya Sadik! Kawai ka daina kula kowacce mace, ni ma na daina kula kowanne namiji shike nan sai mu daina bacin rai da fargaba".
Ya sake nutsuwa tamkar ba shi ba ya ce, "To ta yaya kin san dai dole za ki yi aure, su Abba ba za su bar ki ba".
"Ai dai ba za a mini auren dole ba, sai na ce ba ni da saurayin da nake so".
Kafin ya ba ni amsa Abba ya shigo falon ya gan mu, muka dinga 'kokarin gaishe shi.
Ya kalle mu ya ce, "Ni ba Sadik ba ne ya ce mini na masa iyaka da Halimatu ba?"
Ya shafa kansa ya ce, "Abba ai ta yi tuba, ta nemi gafara".
Ya murmusa ya ce, "Ai na san tsakaninku shi yasa na ce babu ruwana a shirginku".
Ya wuce fuskarsa da yalwataccen farinciki.
Ya nisa ya ce, "Amma ina son Nusaiba Makole! Ina da hope a kanta, sannan zan fa'da mata ke ce favorite sistana".
Na mike na hau kwashe plates din na kai su kicin, na dawo na dauki wayata a kusa da shi.
Na juya na fice. Ina jin sa yana faman ambaton "Guduyo kar ki sake yin wani zunubin, ni za ki tashi ki bari ba excuse? Na rantse miki idan ba ki dawo na riga ki tashi ba, ba zan karbi tubanki ba".
Na waske na 'ki dawowar.
Washegari Juma'a na ro'ki iyayena akan zan je na yi weekend gidan Sakina. Saboda na nisanci Gudale sannan kuma na damu da fishinta, domin ba yadda za a yi Sakina ta iya yini zir ba ta neme ni ba.
Amma gashi har kwana da yini ba ta mini waya ba, tabbacin na 'bata mata sosai.
Ilai kuwa domin da na isa gidanta, na tarar da ita mijinta da yaransu duk suna falonsa, kasancewar tamkar yar gidan, haka nake a gidan Sakina, yasa na bisu falon. Abin mamaki mijinta da 'ya'yanta ne suka dinga mararin gani na.
Ita sai ta mi'ke ta bar falon.
Da kulawa minjinta ya kalle ni ya ce, "Halan kin yi wani gingimen laifi, domin duk rikicin Sakina ba ta yi da ke, amma na lura fishi take yi da ke mai yawa".
Na dan yi 'yar dariya na tashi tsaye na ce, "shiryawa na zo mu yi"
Na fice, ina jin sa yana fa'din "Zumunci irin na ku madalla da shi".
Na shiga dakinta na tarar ta shirya da alamun ficewa za ta yi ta bar mini gidan, duk kuwa da ta kammala aikinta ta dawo gida.
Na rungume ta ina cewa "Afuwan ya Ukti".
Ta ture ni tana cewa, "Ba abin da za ki fa'da mini kuma, tunda akan gaskiya kika rufe ido kika zage ni".
Na dago a razane na ce, "Ni na zage ki Maman Nana?"
"Ban sani ba!"
Ta fa'da a gajarce da alamun fishi. Na marairaice na ce, "Ba karyata ki zan yi ba, amma wallahi ni ban san na zage ki ba".
"Halima! Wata maganar da za a fa'da maka ai tamkar zagi ne. Nuna mini kika yi son ki da Namoriki ne ba na yi. Shin a duniya akwai wacce zan so ya aura sama da ke? Babu wallahi sai dai duk da hakan gaskiya daya ce daga kin ta sai bata. Wai har ki bu'de baki ki nuna mini akwai bambanci a tsakaninki da mu. Ni kuwa na rantse miki ke da Sadik ba ku da maraba a wajena".
Na dinga ba ta ha'kuri a dalilin ba karamin hasala ta yi da maganar tawa ba.
Da 'kyar ta huce, sai dai ta ce, ba za ta kuma ce mini komai akan Gudale ba, ta riga ta fa'da mini gaskiyar magana, tunda ta ga ba yarda zan yi ba. Ta sakar mini 'kotar gatari na hadiya idan zai yiwu.
# Team Gudale.
# Team Guduyo.
# Surayya Dee.
# one love ana tare🤝.
2/8/23, 10:22 - Buhainat: 🌺 *SABO DA KAZA* 🌺
*NA*
*SURAYYA DAHIRU Gwaram*
```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.```
```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️
____________(�?)______________
https://www.facebook.com/profile.php?id=100069755834980
•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·�?
*Gargadi*
*Hakkin mallaka nawa ne ni ka'dai! Dan haka ina jan kunne kada ayi kuskuren ta'ba labarin nan.*
*Ko karatan shi a kowacce kafar sadarwa ba tare da izinina ba*.
*Biya ku'din karatunki ta wannan asusun*
*2384876855*
*Surayya Ibrahim*
*Zenith Bank.*
*Ki tura shaidar biya ta wannan lambar*
*0803277332*
*Second to the last free pages*
*Page 17&18*.
Na dinga ba ta ha'kuri, duk da dai ina nan kan bakata matu'kar Gudale ya furta, mini kalmar da nake fatan jin ta a bakinsa, to kuwa ba shakka ba zan tankwabar da ita ba.
Da zarar mun yi aure zan saita abina, na mayar da shi irin yadda nake fatan ya zama.
Muna cikin haka sai jin muryarsa muka yi yana cewa su Nana ina babarku?
Sakina ta fita tana ce masa, "Kai yanzu Antin da za ka ce ne kake mini 'kyashi. Ka tsaya gaban 'ya'yanka kana cewa wai ina babarsu? Wacce irin magana ce wannan marar da'di haka?"
Ya dauke kai ya ce, "sannu gyambo".
Ya kalle ta ya ce "Ki cewa wannan katuwar yarinyar ta zo nan".
Ta galla masa harara ta ce, "Ni za ka aika? Ka ji kunya wallahi, na rasa irin wannan bibikon da kake yi wa Sadiya! Da alamu dai duk yadda kake jin kanka din nan, kake kuma kushe ta, ka riga ka yi saken da ta zame maka tamkar fitila a rayuwarka idan babu haskenta sai ka kasa sakat. Amma don rashin kunya, sai ka bu'de baki ka yi ta kushe ta kana wulakanta ta, don kawai ka ga ita yarinya ce mai son zumunci da 'dinke shi".
Takaicin Sakina ya kama shi ya nisa ya ce, "Allah ya yafe miki hakkina da kika dauka. Amma ina ba ki shawara ki gaggauta zubar da yawun bakinki na tabbatar yanzu a gurbace yake saboda kin ta'ba zuciyar Ummanki. Ina jiye miki tsoron fishinta Sakina!"
Ya fa'da da muryar gargadi.
Mijin Sakina ya yi dariya domin Gudale mutuminsa ne, ba ya gajiya wurin kallon diramarsa.
Ya ce, "Gaskiya Sakina ya kamata ki sakar wa Namoriki mara ya yi fitsari, a hakan kike son ya dinga ce miki Antin?"
Da sauri Yaya Sadik ya isa gabansa ya mi'ka masa hannu yana cewa, "Assalamu alaikum! Shi yasa ba na kaunar na zo gidanka ba ka nan, har zuciyata na san ka fi Sakina nufina da alheri".
Baban Nana ya sake yin dariya ya ce, "To ai matsanancin son da take yi maka ne ya sanya ni ma nake taya ta son naka".
A fili Yaya Sadik ya ce, "Ashe dai hatsabibiya ce Sakina? Namiji har namiji, amma yana yi wa mace fadanci?"
Ya koma gefe yana cewa, "Allah ka dubi Gudalen Umma, Allah ka dora shi akan matarsa. Ubangiji namiji nake son zama a gidana".
"Yawwa Namoriki taya ni jaje, ni kaina ina yawan tuhumar kaina akan lamarin Sakina".
Ya fa'da cikin iyashege. A hasale Sakina ta ce, "Ai sai ku ta yi".
Tsawon lokaci yana tare da Baban Nana suna hira, har sai da ya shirya ya fita sannan ya dawo wajen mu.
Ya kafe akan zuwa ya yi ya dauke ni mu tafi gida.
Sakina ta dage akan ba inda zan tafi, tunda kwanaki biyu zan yi, to kuwa ba dalilin da zai sa na tafi har sai ranar Lahadi.
Shi ma ya kafe akan mutuwa ce kawai za ta dakatar da shi daga tafiya da ni. Sosai rikici ya kaure a tsakaninsu tamkar yara kananu. Ya kalle ni ya ce, "Sawunki a likkafa ki zo mu tafi, don wallahi ba za ki kwana ba, bijire wa ra'ayina yana nufin kin za'bi Sakina ne a kaina".
Yana rufe baki ta ce mini, "Wallahi kika bi shi ina rantse miki da girman Ubangiji na yafe masa ke, ba ni ba ke, ba zan yi gaba da ke ba, amma Bilhillazi babu sauran aminci ko zumunci a tsakaninmu. Za'bi na gare ki".
Na yi sukuri ina jin ina ma a ce mafarki nake yi.
Ra'ayin wa zan girmama a tsakaninsu? Na yi imanin ba ni da 'yar-uwar data ke so na sama da Sakina! Ba ni da wacce ta zarce Sakina.
Sakina na cikin jerin mutanen da suka 'daga darajata, ta hanyar zame mini tamkar sha'kikiyata, akan komai tana tsaya mini, har cikin zuciyata ban cika gane ba cikinmu 'daya ba.
Asalima saboda soyayyar da take mini ne ya sanya Umma ba ta cika sakar mata fuska tamkar sauran 'yayanta ba, hakan kuma bai sa ta fasa jana a jiki ba. ita take kula da dukkan suturuna, domin mafi yawan tsadaddun dogayen rigunan da nake tu'amalli da su ita ce, haka nan duk wani gayun da zan yi ita ce, tunda ita akwai saka sutura ta garari, don haka kusan tare take yi mana sayayya ba wai kunce take ba ni ba. Wani lokacin kuma haka zata tisa Abba, Baba, Yaya Abdallah a gaba sai ta karbi kuda'de a hannunsu. Don kawai ta dinga saya mini suturu na alfarma, ban da wanda take yi da aljihunta.
Shi yasa nake daukar ido, a idon Gudale kawai nake shan kushe. Na nisa ina jin matu'kar ba a dakin mahaifiyata nake ba, ba inda nake jina comfortable sai a 'dakin Sakina. A da ban damu da kwalliya ba, idan na yi wanka na shafa Vaseline na goga roll on to shike nan zan saka kayana, ko powder ba sosai ba. Na fi kauri a kicin, na fi jin nisha'di a girki sama da 'bata lokacina wajen yin kwalliya.
Amma tasirin Sakina a rayuwata ya sanya ta cusa mini son yin kwalliya sosai, duk da ba na son mai nauyi, a kullum na fi son light make up.
Ita ta koya mini shafa manyan mayuka masu fito mini asalin kalar fatata, duk da ni 'din fara ce tas, amma saboda fatar tawa ta ha'du da wacce take martaba ta sai na dawo tamkar ka taba jini ya fito, sannan ta yi taushi da sulbi.
Na yarda da Sakina, na yarda mayuka da turarukan *Aisha Lame* Jakadiyar Oriflame da suka yi sabo da Sakina saboda nagartar kayanta da sauki, sannan ta 'kware wajen zaba wa mata man da zai yi daidai da fatarsu. A dalilina da Sakina Allah ka'dai ya san adadin matan da muka ha'da su da *Aisha Lame* saboda yadda fatarmu take daukar ido tamkar mun ha'da jinsi da Larabawan Saudiyya.
Na dago ido na kalle shi na ga yana mini wani irin kallon da a ranar ya fara yi mini irinsa.
Na sake diriricewa musamman da na saci kallon Sakina yadda ta 'dauke kanta tamkar ba ta san ina wajen ba.
A hankali na wuce zuwa cikin 'dakin sosai, na kwanta akan gadon.
Hakan ka'dai da na yi ya fahimci ba zan bi shi ba ke nan. Ya yi matu'kar ka'duwa da kunyata shi da na yi.
Murya a dusashe ya ce, "Guduyo kin za'bi Sakina kin bar ni ko? Kin nuna mini duk abin da nake gani akan idonki da ayyukanki a kaina 'karya ce da yaudara muraran".
Na runtse idona, na sake 'dora hannuna akan fuskar don na 'boye hawayen da yake zuba.
Ya kalli Sakina ya ce, "Kin yi nasara! Sai dai kuma a wannan karon za ki gane ba na tsoron ki."
Ya 'daga murya ya ce, "Guduyo da kin san asarar da kika tafka a dalilin wannan matakin da kika dauka da sai kin shimfida tabarma an miki jaje. Wata magana mafi soyuwa zan fa'da miki a hanya, wani albishir zan miki, amma na gode Allah da ya sanya na gane inda kika ajiye ni kafin na kai ga furtawa. Zan adana maganar tawa don na gane ba ke ya kamata ki ji ta ba".
Na zabura na tashi zaune, na kalle shi na ga still dai wannan shu'umin kallon ya ke yi mini.
Na mi'ke da nufin bin sa Sakina ta ce, "Kina fita ki tabbatar kin manta da ni wallahi".
Kawai sai na zube na saka mata kuka sosai. Ta nuna shi da yatsa ta ce, "Wallahi yau za ka gane iyashegenka ka'dan ne Namoriki, duk sha'kiyancinka ba za ta bi ka ba, ja'iri annamimi kawai".
Bai ce mata komai ba ya 'daga murya ya ce, mini "Gudidina! Za ki bi ni, ko kuwa kina tare da wannan kazallahar?"
Na kasa magana, ya jima yana ta yi mini kalamin jan hankali, da al'kawarin dadda'dar magana za mu yi. Ganin ko motsi ban yi ba, yasa ya tunzura ya ce, "Shike nan na gode sosai".
Ya nunata da yatsa ya ce, "Sakina ina rantse miki da girman Ubangiji sai na nuna miki iyakarki, sai kin gane ba na daukar wulakanci ko ka'dan, ya mi'ka mata dan yatsansa yana fa'din mu kunce, don kuwa yau din nan zan warware dukkan amincin da yake tsakaninmu".
Ta share shi domin uffan ba ta ce masa ba. Bare ta ba shi yatsanta su kunce din.
Cikin kara'di ya ce, "Tunda kika jingina mini anamimanci sai mun kunce ko za ki shi'de wallahi".
Ta yi tsaki ta shige ban'daki.
Ya sassauta murya sosai ya ce, "Yanzu Sadiyayye ni kika kunyata, kika tozarta a gaban masu yin mini hamayya? So kike na kwana cikin bacin rai ko?"
Na girgiza masa kai.
Ya sake kashe murya ya ce,