Showing 126001 words to 129000 words out of 180068 words

Chapter 43 - Sabo Da Kaza By Surayyah Dee

18 Dec 2025

8738

mamaki.
Ni kuma na daure fuska sosai.
Ta zuba mini ido ta ce "Menene daliliinki na kin binsa? Bana son fa'dan rashin gaskiya". Nan da nan na fara hawayen takaicin Gudale.
Ganin hakan jikinta ya yi sanyi, ta fice, sai ta yi dabarar turo mini Nana da kanneta Na'im da Haydar, da kuma Afrah da take lafe a jikina tunda suka dawo daga gidan Kakanin su Nana.
Muna idar da sallah ta gabatar mana da abinci, ga mamakina sosai na ci abincin ko dan na tara yunwa ne, ko kuma dan ina tare da Sakina ne?.
Cikin Sa'a mijinta baya kasar yana Dubai. Dan haka kwañan zaune muka yi. Ta dinga fahimtar da ni yadda zan kama kaina.
"Ba ruwanki da matarsa, kar ki zalunceta, kaddara ce ta sanya gidanki itama shine gidanta. Ba kuma laifi ta yi ba. Babban abin da zaki yi shine kada ki yarda a raina ki, ki kame, ki masa biyayya da dukkan iyawarki, ki yi masa kawaici domin a yanzu sai kin yi ha'kuri a dalilin sai ya yi d'oki da zumudin samun sabon abu kamar yadda yake dabi'a ce.
Zai ta yin abubuwan da zaki ga tamkar da gayya yake yinsu. Ba kuma da gangan din yake ba, ko dan ya musguna miki ba, yana yi ne saboda d'oki a lokacin ke kuma zuciyarki cike take da ciwo da kunci sai kiga kin sake tunzura. Kada ki bari ki dinga saka ido akansa ko matarsa, ki tattara ki jingine su, ki tallafi kanki, ki rungumi aikinki da y'ay'anki, har zuwa lokacin da zata zama yar gida ku zama d'aya".
Na ce "To ki tsananta yi mini addu'a Maman Nana"
Ta ru'ko dukkan hannuwana ta ce "Allah ya taimake ki, ya ninka miki hakuri da juriya, sannan ya baki azanci da hikimar zama.
Kinsan fa gaba'daya zaman kishi azanci da hikima kawai yake bu'kata, ba munafunci da asirce asirce ba".
Na girgiza kai na ce "ki dinga saka ni a hanya, har na fahimta".
Ta ce "In sha Allah kuwa, duk dai ke din y'ar-iska ce, yanzun nan za'a fa'da miki yadda zaki yi, dan ki samu k'ima sai kawai ki je gabansa ki saki baki ai Maman Nana ta ce mini kaza da kaza, ai Yaya Al'amin ya ce kaza da kaza, Abba ma so yake ya rabamu, me za'a yi da halinki Halima?".
Hawaye ya goce mini na ce "Billahillazi da ne! Ai yanzu na yi hankali".
Ta saki kwafa ta ce "Da saura dai, idan za'a duba ta abin da kika yi ko kallonki ba zamu yi ba. Kiri kiri kin bak'antamu ni da Al'amin a wajen Namoriki. Alhalin duk dan kin yi mutunci muke yi miki komai, amma ke giyar soyayya ta bugar da ke hatta iyayenmu ma sai da kika nuna musu irin buguwar da kika yi a soyayyarsa".
Kunyar kalamanta suka dirar mini na rasa me zan ce. Sai kawai na buge da cewa "ki yi hakuri dan Allah kada ki barni da kaina".
Ta ce "Ya wuce ai Abba ma ya roka miki afuwa, ya ce ba yin kanki bane, maza irinsu Namoriki jarabta matansu suke yi".
Washagari sai wajen goma muka tashi. Shima wayar Gudale ce ta tashe ni.
Ina zaune ina mamakin barcin da na yi. Amma da na tuna bamu kwanta ba sai da aka yi sallar asuba sai na janye mamakin.
Sakina ta sanya hijabi ta fita tana cewa "Ai tunda kina gidan nan kuma ba zai barni na sarara ba.
Ta bud'e masa kofar falon tana yi masa sababin ba zai yi ha'kuri ba week muna dan runtsawa.
Dake so yake ya samu tabi bayansa ina jin yadda ya lankwashe harshe ya ce "Goma fa! Da kuma tun takwas na zo fa? Kuma saboda na barku ku yi barci ku more ya sanya na bari sai yanzu, ashe ban yi gwaninta ba?"
Ta wuce wajen yan aikinta Dan taga aikin da suke yi.
Yana zaune a falo har ta dawo ya ce "Ina kwana?"
"Ta dan murmusa ta ce "Yau kuma?"
Ya waske da cewa "Ba dama na miki abin kyautata wa ki karba ki gode mini?"
"Lafiya lau Namoriki shikenan?"
Ya ce "Ina y'arki ina y'ay'ana?"
Ina jiyo dariyar da ta saka tare da cewa "Yau kuma har da tambayar Yara? Allah ya yafe maka kawai".
Ta wuce ta barshi.
Ta le'ko ta ce shiga ki yi wanka ki fto mu karya".
Ban musa mata ba.
Na yi hakan. Na fito na tarar ta ajiye mini sabuwar doguwar riga free size, hade da inner wears sabbi.
Na sanya na shirya fes tamkar bani da damuwa. Ina cikin fesa turare ta shigo ta ce "wow Autar gidanmu fa akwai taswirar kyau". Na murmusa dimples suka bayyana.
Na ce na gode sosai! A ina kika samu inner wears size dina?"
Ta waske ta ce "Ina dasu dama".
Muna zuwa falo na ganshi suna cin abinci da su Nana. Ga Afrah akan cinyarsa tana fama da cinyar kaza. Ita kam tana son naman kaza, tamkar ni.
Mamakinsa ya kama ni, na kasa tuna when last ya dauki Afrah.
Yarinyar da bata samu kulawarsa ko ka'dan ba. Matu'kar zai dauketa to lah shakka ya kuntata mini ne, yake neman shiri, tunda ya riga ya gane yarinyar tana cikin weakness dina. Ba dan komai ba, sai saboda banzatar da ita da yake yi, gara Amnah ta samu kulawarsa sau dubu a kanta. Wani ikon Allah kuma Amnah ta fi jin tsoronsa ko dan yana zaneta da tsintsiya ne yayin da Afrah kuwa bai ta'ba dukanta ba.
Muka karya cikin walwala sai saka ni yake yi a cikin maganarsa yayin da ni kuma nake sharewa.
Ya ce "muje Guduyo! Zaki raka ni unguwa ne".
Na girgiza kai na ce "Zamu fita tare da Maman Nana sai mun dawo tukun".
Ransa ya baci ganin Sakina bata tanka ba.
Ya mike ya ce "zo mana Sakina"
Ta mike suka shiga dakinta.
Dake kofar a bude take na kasa kunne ina jiyo su.
"Sakina kin ga bana son haka! Ta ya ya zaki zuba mata ido tana mini wannan iskancin a gabanki? Haka kawai ta zo ta kwana baki hanata kin nuna mata daidai ba, na ha'kura na bar ta domin neman masalaha, yanzu na zo daukar ta, ta ce fita zaku yi still baki ce komai ba. Tsakaninki da Allah hakan dai-dai ne?"
Ta ce "To ni ina nasan baka so ta kwana ba? Kuma yanzu Abba ne ya ce mu je ta za'bi furnitures din da take so, bisa adalci idan mun je ta za'ba sai na mayar da ita a maimakon gobe ta sake fito wa."
A hankali ya ce "shikenan Sakina! Saboda Allah abin da ake mini ya dace, ke ya kamata a fa'dawa ko ni? Amma babu damuwa ku dawo lafiya".
Ya fito a fusace ya tafi, wani iyashegen Afrah har da kukan zata bishi.
Na dinga mamakin abin da ta yi, tana kallona amma wai shi take son bi.
Muka zare jiki muka barsu da yan aikin Sakina muka fita.
Irin kayana da Sakina ta zabar mini sai da na ce "Sun yi ku'di da yawa".
Ta ce "Ku'di masu yawa Abba ya bayar ni kuma ba zan yi miki kyashi ko kwange ba"
Hawaye ya balle mini na dinga jin kunyar da na cewa Gudale ni ba yar kowa ba ce, domin na yi imani sai an yi tsananin dace ne kayan Munubiya zasu kai nawa. Domin duk yadda aka siya mini kayan alfarma a farkon aurena, na yanzu sun keresu daraja. Hatta talabijin sai da aka dauko mini tafkekiya kuma new modern ban da kuloli na alfama.
Haka kawai nake fakar idon Sakina nake dauke hawayen da yake ta kutso mini a dalilin karamcin irin na Abba da Sakina.
A wajen muka bar kayan domin su zasu je su shirya komai.
Muka je har gaban Abba ta bashi dukkan recit din siyayyar da aka yi, ya dinga sanya mana albarka, yana sake tausata, yana cewa komai kike so ki fa'da mini. Fatana kada ki bari a samu matsala ta bangaren ki, idan kika yi mini hakan kin biyani, ina tabbatar miki kuma ko na mutu ba ba zaki wula'kanta ba. Zan baza masu sa mini ido a cikin zaman aurenki".
Murya na rawa na ce "Madallah da Abba! Na gode sosai, Ina fatan Ubangiji ya baka aljannar da ya tanada saboda masu zumunci".
Sakina ta amsa da "amin".
Daga nan na tashi na basu waje, na gaida Umma na wuce wajen Mamah.
Ina ganinta na rungumeta tamkar yadda nake yi mata ina cikin shekarun kuruciya. Kukan da na hadiye ban yi a jikin Sakina ba, shine ita nake mata, a dalilin nasan nan gaba zan bu'kaci na sake yin kuka tunda dole nasan gwagwarmaya na gaba.
Cikin kuka na ce "Mama har da ke ake boye mini abin da ya kamata ace na sani?"
Ta ce "Nima sai shekaranjiya na ji. Sai ki k'ara, ha'kuri, kan ha'kuri tunda yanzu zai auro surukar da za'a so a nuna mata dukkan gata da soyayya."
Na dinga kuka ita kuma bata hana ba, har sai da Yaya Al'amin ya shigo sa'be da dansa da ya yi wayo sosai.
Ya ajiye shi ya sake hannu ya dago ni a jikin Mama ya sanya akan kafadarsa yana fa'din "Daure mana kinsan yadda kukanki yake dafa zuciyarta kuwa? Na sake barkewa da kuka, ina fa'din na gaza Yaya Al'amin"
Ya ce "Baki gaza ba, har abada kuma ba zaki gaza ba. Karin auren namiji ba shine matarsa ta gaza ba. Ki yarda ibada ne domin Allah ne ya halatta. Ita kuwa ibada ana yi ne, ko ana so, ko ba a so.
Ki k'ara ha'kuri, komai zai wuce, ki nutsu dan ki karfafa guiwar Abba. Ya damu da halin da yake ciki, ya kuma ce yana son mu fa'da miki ki yi hakuri, ki daure, komai zai daidaita miki."
Haka Yaya Gudale ya shigo ya tarar da mu.
Ya coge a bakin kofar falon. Mussaman da Mama tana kicin.
Ya numfasa ya ce "Sakina ta gama nata famfom yanzu kuma kin dawo Al'amin yana d'ora wa.
Ya shigo ya tsaya kusa da shi ya ce "Dan Allah dan darajar Annabi me na yi maka ne Al'amin? Bana nufinka da sharri, har yau har gobe kuma kana cikin muhimmai a duniyata. Amma sai ka dinga kokarin shatale ni, jibi yadda ka wani rungumeta tamkar yarinya yar k'aramar. Tsakanina da Allah ana mini ba dai-dai ba. Ai ni nafi kowa cancantatar na yi mata irin wannan rarrashin, amma kun zugeta tana guduna tamkar ajali. Bayan tun shekaranjiya da ta ji maganar auren nan ta tashi hankalinta, ta tashi nawa duk wani yun'kurin rarrashinta da nake yi ta tankwabar amma ta je wajen Sakina, yanzu ta dawo wajen ka alhalin na tabbatar ku duk gadar zare zaku shirya mana, tunda na gasgata bakwa nufina da alheri".
Uffan Yaya Al'amin bai ce masa , domin ya riga ta hauro, idan kuwa ya bu'de baki ya sani sai sun yi rikicin da zai tashi hankalin iyayenmu. Dan haka ya sake ni, ya mike ya fice.
Ya kalle ni ya ce "Zo mu tafi! Tun jiya kike gara ni, ina binki kina tozarta ni, wai ya kike son na yi ne?".
Mama ta fito ta ce "Tashi ki bi mijinki ku tafi".
Haka ya tasa ni a gaba muka tafi ina kuka sosai.
Muna zuwa na yada zango a falo ina wani irin kuka mai cin rai.
Ya zauna kusa da ni ya ru'ko ni, na zabura na fizge cikin kuka na ce "Kar ka kuma ta'ba ni, bana so, bana son ganinka."
Ya yi shiru ya ce "Na sani zanga abin da yafi hakan, ba dai kin je an miki famfo ba?. Ba komai! Na gode. Ace wai Al'amin zai rungume ki ya rarrashe ki, amma ni bani da wannan damar. Kuma idan an tashi ace bani da kirki, ni murdadden mutum ne. Ina cikin tasku, ina cikin ba'kin ciki. Abba kullum na tsugunna gabansa da nufin na gaishe shi, mu dan yi hira da shi dan na ji da'di, amma ba zai yi mini hakan ba. Sai dai ya bige da magana akan ki, da ya bu'de baki zai ce kada na zalunce ki, kada na cutar da ke, kada na wula'kanta ki, amma ke an zuba ido kina cusa mini ba'ki cikin da yake neman kassara ni babu damuwa. Allah ya saka wannan shine kankarar zunubaina."
Na share shi. Ya dinga son na bu'de baki na yi magana ni kuma na ki. Ya gaji ya mi'ke a matu'kar sanyaye ya ce "Shikenan! Shikenan Guduyo".
Ko kallonsa ban yi ba.
Sintiri ya yi shi yafi sau biyar. Har dare ban kula shi ba, bai gaji ba.
Wajen goma na dare ya ce "Tashi mu shiga ki yi hakuri kin ji. Ina tabbatar miki ina jin kwatankwacin damuwar da kike ji. Ki yi hakuri tun sadda kike wannan tashin hankalin bani da sukuni. Ki ji tsoron Allah ki daina tayar mini da hankali haka nan. Kin je kin kwana lafiya lafiya a gidan Sakina. Amma kina dawowa kin dawo da masifa alhalin na barki ne dan ki samu nutsuwa. Ki yi ha'kuri, ki bani dama na yi biyayya Abba ya za'ba mini ke, na yi masa biyayya, yanzu kuma Umma sai ta ce bana mutunta ra'ayinta. Ni bani na ce ina sonta ba".
Na katse shi ido tamkar garwashi na ce "Bani da hurumin kana so, ko baka so, ai nima ba sona kake yi ba aka baka. Itama kuma hakan ne saboda gata da ya kewaye ka. Wata'kila itama ka fa'da mata kumbusar matarka ba sonta kake yi ba, baka ita aka yi, akan tilas."
Karon farko da naga ya shiga rudani dan na gasgata shi. Ya ru'ko hannuna ya ce "Billahillazi! Na rantse miki, ban taba maganar ki da ita ba. A farko na dauka kin fahimce ni saosai, saboda yadda kike sona da dukkan na'kasun da kowa yake mini kallon sun baibaiye ni. Ta Yaya zaki yi tunanin bana son ki, ta yaya zaki yi mini kallon zan ce bana son ki a gaban wata mace? Me yasa ba zaki kwantar mini da hankali a lokacin da nake cikin cankacakare ba? Me yasa Kika zabi ki bijire mini, ki gigita ni akan me Guduyo?"
Ya dinga lallaba ni. Har na bu'de baki na ce "Shikenan na ha'kura. Ina fa'din haka ya ce "To taso mu je, ni nasan ba zaki ta'ba juya mini baya ba, domin na yi imanin son da kike mini garanti ne da babu algus".
2/8/23, 10:25 - Buhainat: *MURNAR ZAGAYOWAR RANAR HAIHUWATA*
*14/01.*
*Yau ne ranar birthday dina, a taya ni addu'a, Allah ya maimata mini, yasa na wanye ragowan kwanakin da suka yi mana saura cikin imani da kuma lafiyar da zan yi ibada da godiya bisa dinbin ni'imominsa gare ni*
*Allah ya jiqan mahaifana mussaman uwa mahaifiya.*
*Mama*
*Ina ma kina raye na yi miki murna da barka ranar da kika tsallake siradin da Ubangiji da kansa ya ce wahala kan wahala ne.*
*Na gode! Na gode!*
*Allah ya jikanku, ya sanya kuna aljannah, da dukkan musulmin da suka rigaye mu*.

*SDK*
77&78.

Na kalle shi ido cikin ido na ce "wannan ne kuma ba zan iya ba. Na roke ka, dan Allah ka bar ni na samu sukuni".
Ya kafe ni da ido na sani ba dan tsoron Abba ba da duka zai nada mini.
Ya sauke ajiyar zuciya ya ce "zuwa yaushe zaki samu samu sukunin?"
Na ce "Ban sani ba, ina dai bu'katar hutu da nutsuwar zuciya."
Ya sassauta ya ce "Baki ga kamar haduwar tamu zata fi saurin saukaka miki damuwar da kike ciki ba?
Kina lissafin adadin kwanakin da na dauka ina ha'kuri, ina tattala lafiyarki kuwa?"
Na ja tsaki na ce "Kai da ba gamsuwa kake yi ba, kuma kana dakon tsukakke ba sai ka bar mini nawa ba?"
Ya kufula ya ce "kin ce kin ha'kura me ya kawo wannan maganar? Ina lallaba ki ne saboda ki samu kwanciyar hankali".
Na ce "Saboda ka samu dai! Idan kuma saboda ni ne, to barni na dauwama cikin damuwa da tashin hankali yadda ka saba sanya ni".
Daga haka ya tashi ya koma daki ba tare da ya sake cewa komai ba.
Washagari lahadi dukkan ahalin gidan muka hadu a gaban Abba inka dauke Antin Zaria.
Hatta Yayar Kwalli ta halarci zaman.
Yaya Abdallah ya bu'de taro da addu'a.
Yayin da Abba ya yi nasiha mai shiga jiki, ya dinga nanata mu ri'ke Sallah, mu yawaita sadaka, mu kuma yi zumunci. Ba sai uwarku daya ubanku daya bane zaku yi zumunci. Ku sada zumunta da wanda ya yanke muku zumunci. Annabi ya yi ta wasiyya akan kada mu yi shirka, kada mu zubar da jinin mumini, kada mu tauye mudu, kada mu zalunci makwabatanmu, kada muci mutuncin junanmu. Ku yawaita istigifari domin mabudice na dukkan alheri. Ku sada zumunci, ku ji tausayin junanku, sannan ku zama masu afuwa da sassauci.
Jikin kowa ya yi sanyi.
Ya yi gyaran murya ya ce "Yaya kinsan wannan gidan asali na mahaifin mune, Ni da kanina Ibrahim muka gace shi.
Duk da dai na fadada shi kwarai da gaske ta hanyar siyan gidajen da suke jikinsa.
Dukkanku ku zama shaida kofar Ibrahim tasa ce halak malak.
Yaya ta ce "me ya kawo wannan maganar Alhaji" ta fa'da murya na rawa.
Yayin da Umma ta yi wuki wuki tasan ita yake kafawa hujja ba y'ay'ansa ba.
A sanyaye ya ce "Ina jin tsoron shaidan a lokacin da babu hujja".
Ya numfasa ya sake cewa "Auren Sadik kwanaki shida suka rage ga wanda Ubangiji ya kaddara masa ga ni. Ina son kowa ya saurare ni da kyau.
"Na yi amfani da fa'din Allah da ya ce ya bawa namiji damar ya auri abin da ya yi masa da'di daga mataye bibbyu, uku, ko hurhudu, a karshe ya ce idan ba za'a iya ba ayi daya.
"To shi ya ga zai iya, ya zabi ya yi kari, ni kuma ba zan matsa ba. Sai dai ina son ku zama shaida akan abin da zan fa'da domin ya zama an yiwa kowa adalci.
"Sadik! Zaka kara aure amma ina son na rok'e ka idan har kasan a zuciyarka baka son Halima kada ka munafunci kanka ka magantu domin idan har ka yi aure kuma wula'kanci ya biyo baya ta kowacce fuska ba zan maka uzziri ba. Domin hakki ne akanka ka kiyaye mata mutuncinta a gaban danginka".
Umma da Anti Maimuna suka yi wuki wuki domin dai shaguben Abba ya yi saurin ta'ba su.
Ya zarce

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login