Showing 75001 words to 78000 words out of 180068 words
School ban je ba yau".
"Eh daure dai ki shirya din! Idan muna tare zaki warware, za kuma ki ji da'din".
Ya fa'da yana hawa 'kafar bene dan dauko mukullin mota.
Na bishi da kallon takaici, wato Yaya Gudale takaicin sa yawa ne da shi. Na murguda baki hadi da gatisne.
A dole na bishi muka fita, kasan raina kuma haushinsa fal.
A motata muka fita.
Bamu zame ko ina ba sai filin koyon tu'ki.
Ya dinga nuna mini yadda zan yi. Sama da awa guda muna zagaye, sai dai gaba'daya a takure nake a dalilin yadda
ya matsa mini da shafata.
Duk yadda zai yi jikinmu ya ha'du haka ya dinga yi tamkar dama so yake ya samu damar yin hakan.
Kafin mu bar wajen sai da na yi zagaye uku da mu a filin.
Cike da farin-ciki yake cewa "Da wuri hannunki zai fa'da Guduyo.
Zan kai motar a saka miki *L* nan da lokaci kankani zaki fara fita da kan ki".
Ya biya da mu Al-amir restaurant muka ci abinci ganin magahriba ta gabato sosai.
Ga mamakina gidan Sakina ya zarce da mu.
Sakina ta dinga ina ka saka da mu, ta yi dabarar jana daki muka bar Gudale da yaranta a falo.
Maganganu masu nauyi ta yi mini a dunkule wanda suke nuni da cewa na yi kokarin dinke distance din dake tsakanin mu.
Ta fahimci da sulhu ya dawo, na ja aji ka'dan na ha'kura tunda na sani a bau'de yake.
Cikin 'kasa da mintina talatin sai da tasa ni na hadiye wasu irin supplement din Gangariyar Jakadiyar G.H.T.
*Faseelat mai gyaran ciki da wajen Mata*
*Kina fama da tumbi ko kurajen fuska?*
*Kina fama da ulcer ko basir?*
"Kina fama da dryness, to kukan ya Kare domin zan hadaki da wacce zata Baki ingantattun supplement din da babu kwange cikin farashi mai sau'ki*
*Faseelat 07039269802*.
Ta bani wanda bata bu'de ba, na tafi da shi.
Muna fito wa ya kallemu ya ce "Haj Sakina an buga, an bar ki.
Dafatan dai kin fahimci manufar gaisuwar da muka zo yi miki"
Tana harar sa ta ce "Na san dai Halimatu ce zata zo ta gaishe ni, amma ba kai ba".
Ya kalle ni ya ce "fa'da mata ba kisan zaki zo ba".
Na 'ki tankawa, yayin da Sakina ta rakomu har waje tana yi masa tsiyar bai kawo mata tsarabar komai a fataucin da ya je Ikko ba, sai ya dauko ni ya kawo mata tamkar dai so yake ta fahimci zuciyarsa bata da karfin jurewa kudirinsa.
Sanin da ya yi magana ta yi masa mai harshen damo ya sanya ya waske bai ja maganar ba. 'kunshin da ta kai ni ma ya so yin maganar kawai sharewa ya yi. Amma na sani zai yi maganar.
A hanyar mu ta komawa ya dinga ja na da hira, har na dinga mamakin ashe ya dan iya magana cikin sakin fuska da taushin harshe?
Ba abin da yake so irin na sake jiki da shi kamar da.
Tun a gida Sakina sallar Isha ta same mu. Dan haka mun riga mun yi sallah.
A falo muka yada zango. Ba kunya ya ce mini ban ta'ba kai masa ziyara dakin sa ba.
Cikin son na nuna ban fahimce shi ba, na ce "Sau nawa ina zuwa kuwa?"..
Ya girgiza kai ya ce "ke fa kina zuwa ne bayan kin shirya fita makaranta, ko idan bana nan ki je ki gyara, shikenan fa".
Na yi murmushi na ce "Ashe kuwa ina zuwa".
Muna kallo, yana rike da hannuna yana ta murza mini, duk ya sa jikina ya mutu, Ina jin wani irin al'amari na shiga ta da nake jin tamkar wanka ya kama ni, saboda yadda nake jin na zama wet.
Ban sani ba ko tasirin maganin da Sakina ta dirka min ne.
Uzziri ya kama shi, ya haye sama.
Kafin ya dawo na kashe komai na shige dakina na rufe, na yi wanka, na yi kwanciyata bayan na rufe kofata da makulli.
Domin na ci alwashin ni ba zan kai kaina dakinsa da kaina ba. Sai ya ajiye girman kai ya fa'da da bakinsa barobaro.
Ba kuma zan sallama masa kaina da wuri ba, bayan wula'kancin da ya yi mini kala kala masu cin rai. Har da yi mini yawon 'ki.
Da ya sauko, ya dinga buga mini kofa. Amma na yi funfurunfus. Ya yi iyakar kokarin sa akan na bu'de masa amma ban bude kofar ba.
Tunda na idar da sallah ban koma ba, kai tsaye kicin na shiga, na hau aikin yin snacks.
Na kammala agogo ya nuna mini karfe takwas har da kwata saboda na yi da yawa, tunda abin da da yafi son ci kenan.
Ban soya wanda zamu ci ba, sai da na kammala gyara gidan fes. A nutse nake aiyyukana saboda sai sha biyu nake da lecture.
Ina tsaye a kicin din sanye cikin cotton din rigar barci guiwa. Da takalminta take zuwa, da kuma band. Na kame gashina dake tsefe da band din.
Na kunna gas kenan na ji shigowarsa.
A Dan tsorace na gaishe shi.
Bai amsa ba illah iyaka ya zuba mini ido yana kallona hannun sa na'de a 'kirjin sa.
Yayin da kallon yake ratsa ni har cikin kaina.
Murya a dashe na ce "Ina kwanaa?"
Ya amsa a takaice.
Ya numfasa ya ce "Na fuskanci kin matu'kar raina ni Guduyo".
Kaina na kasa na ce "Da na yi maka me?"
Da azama ya ce "kina nufin duk yadda na dinga buga miki kofa baki ji ba?"
Na ci magani na ce ban ji ba".
Ya make kafa'da ya ce "alright! Shikenan na yafe miki bacin ran da na kwana a cikin sa".
Dariya ta kusa subuce mini. Da zan iya da na ce masa kar ya yafe din.
Amma na san idan na fa'di hakan zamu kwashi 'yan kallo ne, dan haka sai na kame bance komai ba.
Ba zato kawai na ji ya rungume ni ta baya, ya kwantar da kansa akan kafa'data yana shinshinata.
Jikina ya amsa. Na fara kokarin zamewa, murya na rawa na ce "Ka bari dan Allah man da na dora zai kone kar ya janyo mana gobara".
Ya sassauta rikon amma ba gaba'daya ba.
A hakan na yi aikin.
Duk inda na saka 'kafa nan yake mayar wa. Har cikin dakina yana biye da ni.
Da zan shiga wanka ba irin ro'kon da ban yi masa ba, akan ya kyale ni na shiga toilet amma tuburan ya kafe sai dai mu shiga tare shima wankan zai yi. Alhalin sai da ya yi wankan sa ya fitto.
Na kalli agogo na ga tara ta gota.
A hankali na ce "Yaya Sadik ka yi wa Allah ka bar ni na yi wanka na karya, ina da abubuwan yi a gabana".
Ya dauke kansa tamkar ba da shi nake yi ba, tabbacine kuma na ba zai kyale ni din ba.
Har toilet din ya bini, na rasa inda zansa kaina.
Kawai sai na yi brush, na yi kwaskarima na fito, domin ba zan iya tubewa a gabansa ba, kamar yadda yake fatan mu yi wankan tare.
Hijab na sanya sannan na shirya a takure. Saboda yadda ya tasa ni a gaba da kallon 'kurillah.
Sanin da na yi baya son na zuba masa abinci da kaina ya sanya ban yi gigin zuba masa ba.
Ya zuba mini ido ina kai *fan cake* bakina.
Ya ce "Ba zaki bani bane?"
A hankali na ce "ga shi nan. Wa zai hana maigida abincin gidansa?"
Da'di ya lullube shi har fuskarsa ta bayyana hakan.
Kai ni kam bansan mai son girma irin Gudalen Ummah ba.
Fuska a sake ya ce "To zuba mini mana, matu'kar kina kusa ai komai yi mini zaki yi".
Na murmusa na ce "Na dauka sai kuturu ko yaro 'kan'kani ake yiwa irin wannan hidimar".
Nan da nan ya ce "Ban son raini fa kin sani, ban son kananun maganganu".
Na yi shiru na zuba masa ido, na kuma zuba masa abincin kamar yadda ya bu'kata.
Na riga shi kammalawa.
Na kalleshi na ce "Zan tashi".
"Zuwa ina?"
Na ce "makaranta! kada na yi latti".
Ya zuba mini ido sosai ya ce "Na dawo jiya! Ki yi sammakon fita ki barni gadin gida, saboda kawai bani da wata daraja ko 'kima a idon ki".
Na yi shiru, ina ganin ikon Allah.
Kafin na ce wani Abu! ya ce "Yau alhamis ki ha'kura da makarantar nan, zuwa Monday tunda ba wani abu muhimmi zaku yi ba".
Idona ya ciko da 'kwallah na ce "gaskiya muhimmin abu zanje yi, ban ta'ba ganin inda scientist suke fashi babu dalili ba".
Hakan kawai na fada "ya ce "Na rantse miki da Allah babu inda zaki je yau. Idan kuma kika sa'ba mini akan haka wallahi zan iya dakatar da karatun gaba'daya, tunda na fahimci karatun yafi lahirarki muhimmanci".
Hawaye ya balle mini na ce "A Ina na ce maka yafi lahirata?"
Kai tsaye ya ce "Baki fa'da mini haka ba! Amma kin nuna mini ni ba komai bane a wajen ki, alhalin kuma nine lahirar ki".
Takaici ya kama ni bansan yadda aka yi ba na tsinci kaina da cewa "Kai ne lahira ta, amma na sani ba zaka taimake ni wajen ganin na rabauta da samun dacewa a can ba, tunda ba sona kake yi ba".
A hanzarce ya ce "Lallai Guduyo! Ashe mummunan zato kike mini irin haka?
Bayan tunanin ki ne ya nemi kassara ni na dawo babu shiri".
Na zuba masa ido sosai ina mamakin furucinsa.
# Team Gudale
# Team Guduyo
# Surayya Dee ✍️
# Ana tare 🤝.
2/8/23, 10:25 - Buhainat: *Wannan littafin na ku'di ne, biya 500 ku'din karatu ta wanannan asusun*
*2384876855*
*Surayya Ibrahim*
*Zenith Bank.*
*A tura shaidar biya ta wannan lambar*
*08032773332*.
*AMYAS NEW & FAIRLY ITEMS*
*KOMAI DA RUWANKA KENAN*
*SUNA SIYEN KAYAN DAKI SECOND, SUNA KUMA SAYARWA*
*SUNA SIYAN KAYAN ELECTRONICS, SUNA KUMA SAYARWA*
*SUNA SAYAR DA KAYAN KICIN*
*SUNA BADA HAYAR KAYAN AMARYA*
*SUNA SIYAR DA SUTURU NA ALFARMA*
*SUNA SAYAR DA FILI DA GIDAJE, SUNA BADA HAYAR GIDA*.
*KU TUNTU'BE SU A WANNAN LAMBAR 08083909947*.
*SDK*
*49-50.*
Da rawar murya na ce "Ba dai tunanina ba".
"Waton 'karya na fa'da".
Ya tambaya rai a 'dan bace.
Na kasa bashi amsa. Na tashi na barshi a wajen, ya dinga kirana na wuce tamkar ba da ni yake yi ba.
Ina shiga 'daki na haye gado na fashe da kuka sosai.
Jim ka'dan ya shigo a fusace, kukan da ya ga ina yi sai ya sanyaya jikinsa.
Murya a dashe ya ce "Bana son haka! Kar ki tayar mini da hankali haka siddan".
Ban ce masa komai ba, haka nan ban daina kukan ba.
Ya zauna a bakin gadon. A hankali ya ce "Shikenan bani da damar da zance ki yi kaza, ko ki bar kaza sai ya zama abin kuka da 'bacin rai a wajen ki?
Har ni kike yiwa zaton ba zan baki damar da zaki rabauta ba?"
Na yi shiru ina cigaba da kukana kasa 'kasa.
Ya numfasa ya ce "Ke ce kike yiwa rabautar ki rikon sakainar kashi.
Tunda kika zo gidan nan kin ta'ba zuwa 'dakina da nufin sauke hakkin da ya rataya a kan ki?"
Kukana ya tsaya cak! Mamakinsa ya kama Ni! Ashe dai da gaske jira yake na kai masa kaina.
Na rasa gane manufar Gudale. Bai ta'ba ganin alamun ina kule kulen maza ba, ko shima da nake sakar wa fuska har ya mini abin da bai kamata ba, amma dai bamu ta'ba yin lalata ba, bare ya yi tunanin nasan komai. Ba zan ji nauyin nemansa da kaina ba.
Kafin na ce wani abu ya riga ni cewa "Na gama nazartar inda kika dosa, sai dai abin da baki sani ba shine.
Matu'kar ba zaki sauke mini wannan hakkin ba Wallahi ba zaki rabauta ba. Dan ba zai yiwu ki yi ta wula'kanta ni, kina ci mini mutunci sannan ki ce zaki ga haske a al-amuran ki ba."
Hawaye ya balle mini, da rawar murya na ce "Duk wula'kanta ni da ka yi tun farkon maganar auren nan har zuwa guduwar da ka yi ka barni ban ce komai ba sai kai?
Dan Allah fa'da mini wula'kanci ko cin mutuncin da nake yi maka".
"Gasu nan birjik! Ki fita ban sani ba, Ba zaki zo mini hira ba, sai dai kawai ki share mini daki, ki mini abinci, alhalin wannan hakkin zan iya daukar mai yi mini na biya".
Murya na rawa na ce "Na gane bani da daraja! da gaske dai Ta buzuzun ma ta fini kima a idonka.
Banda haka a ina aka ta'ba yin haka saboda Allah. Ko a wajen Allah bani da laifi tunda dai ban bijire maka ba. Kai ne baka nema ba, ni kuma ra'ayi ne bani da shi akan lamarin shiyasa ban nema ba".
Ya nisa ya ce "Allah dai yana ganin komai, tun yaushe nake miki hannun ka mai sanda, kin gane sarai, amma kika nuna mini baki fahimta ba, akan me ba zaki taimake ni ba?
Kinfi son sai na ajiye dukkan girmana. Shikenan kin ci riba! kuma na sani jiya kina ji na kika 'ki bu'de mini 'kofar nan".
Na yi masa shiru tunda gaskiya ya fa'da.
Ya mi'ke tsaye ya ce "Zan fita! Ba zan jima ba, ku'di zan samo mana na dawo, ki yi list din abin da bamu da shi, da kuma wanda kike bu'kata. Idan na dawo sai mu je mu yi shopping".
'kala ban ce ba! Har ya fara tafiya ya juyo ya ce "Na ce zan fita amma kin mini shiru?
Haka kika ga ana yi wa miji?
Anya Guduyo kin shigo gidan nan da nufin rabauta da aljannah kuwa?"
Na nisa na ce "A dawo lafiya".
Ya tafi yana cewa "Ameen"
Na tashi na zauna ina rasa ajin da zan ajiye Gudale.
Na lura yafi mahaukaci cusa takaici.
*Gudale*
Cikin gida ya shiga, sai da ya je ya gaida Baba da Mama.
Sannan ya fito zuwa shashinsu.
Ya tarar da iyayensa suna karya wa.
Ya gaishe su, suka amsa fuska cike da kulawa mussaman Abba.
Jikin Gudale ya yi kwari saboda ya gamsu Abba bai dauki zafi da shi akan tafiyar da ya yi ya jima, ba waya ba aike ba.
Dan haka ya bararraje a gabansu tamkar yaro 'kan'kani.
Abba ya gama nazartar sa ya ce "Ya ya ne Sadik?"
Kafin ya yi magana wayar Umma da ta bari a falonta ta hau 'kara. Dan haka ta mi'ke da sauri.
A shagwabe ya ce "Abba ba ni da ku'di a account dina, tafiyar nan ta cinye mini su. Ban son zama haka a gida".
Da walwala Abba ya ce "Gidanka ai da abinci bana jin akwai abin da babu! Domin duk sati sai na yi mata aika, na kuma bata ku'di".
Ya marairaice ya ce "Da so nake yi, na yi yadda ake yi Abba".
"Me ake yi?"
Abba ya tambaya a hanzarce.
"Na kai ta ta yi shopping! Kuma na fara koya mata tu'ki! Zan dinga zuba mata mai a mota, sannan ku'di garkuwa ne Abba, ajiye su a daki ka'dai zasu taimake ni. Ba zan so ta bu'kaci wani abu na ce mata babu ba".
Mamaki ya kama Abba matu'ka da gaske, ya nisa ya ce "Ban jin zata bu'kaci wani abin, hannunta da ku'di fa".
Ya bata rai sosai ya ce "Abba ni ba ruwana da ku'din ta, so nake yi na dinga yi mata hidima ba wai ita ta yi mini ba. Ban son raini Abba".
Murmushi sosai Abban ya yi har ha'koronsa suka bayyana ya ce "To ai tasan baka da aikin yi, komai naku yana karkashin kulawata ne. Kuma daga ni har ita ka fahimtar da mu baka son auren. Ka ga kuwa ni da nake son auren ai ba zan barta cikin kuncin rashin kudi ko kayan amfani ba, komai tana da shi inka dauke miji da soyayyar sa".
Jikin Gudale ya mutu murus domin ya gano akwai wata a 'kasa a zuciyar mahaifin sa.
A hankali ya ce "Abba! Ba'a cewa komai a sha'aniniji da mata fa".
"Au haba?" Abban ya fa'da a tunzure.
Nan da nan Gudale ya fara cewa "Ni dai ban ce bana son ta ba. Kuma yanzu da na dawo zan bata soyayyar da aka ce ta rasa, ba sai a taimake ni, a gode mini ba".
"To bazan baka ku'dina ba, indai da gaske rainin ne baka so, ka fita ka yi kwadago, ko leburanci ka samo ku'din, sai ka yi mata hidimar yadda kake so".
Ya rarrafa ya matsa jikin mahaifin nasa ya 'dora kansa a 'kafarsa yana cewa "Dan Allah ka bani Abba! Kar ka sani kuka bayan so nake na girma".
Dariya ta so kwacewa masa, amma ya cije ya ce "Dan Allah Sadik yi ta kururuwa ba kuka ba. Idan ka so ka fasa girman ka koma jinjiri sai na ji dadin yi maka sabuwar tarbiya ma".
Bai dago ba ya ce "Ha'kuri zaka 'kara yi Abba! Ubangiji zai mayar maka da ni yadda kake son ka ganni! Kada ka yi fishi dan Allah".
Jikin uban ya yi sanyi sosai, soyayyar 'da da mahaifi ta taso masa.
Ya shafa kansa ya ce "kana 'kona mini rai Sadik! Bana jin da'dinka sam, yan uwanka mata sun fiye mini kai, domin basa sani damuwa, basa tayar mini da hankali. Sun fika tausayina, sun fika giramama ni. Kai baka san komai ba, sai bu'katarka. Tausayinka nake ji Sadik shiyasa ban sallamaka ba, amma al'amarinka ya fara kai ni bango".
Ya dago idanuwan sa sun ka'da a hankali ya ce "Na yi tuba Abba! Kar ka sallama ni, kai 'din Malami ne mai ta'kawa 'kara yi mini Addu'a da sannu Ubangiji zai karba".
Tsawon lokaci falon ya yi shiru sai fama suke da sake saken zuciya.
Sadik ne ya katse shirun ta hanyar cewa Abba "yanzu dai so kake na ri'ke maka 'yarka da soyayya mai sanyi da tsaya wa a zuciya ko?"
Girgiza kai Abba ya yi ya kasa bashi amsa domin bai san gaba mai zai sake 'baro wa ba.
"Abba ka yi shiru kuma".
Da'kuwa ya yi masa tare da cewa "Tashi ka bani waje mashiriricin yaro kawai".
Ya marairaice ya ce "Ka kubutar da ni kunya ta a idon yarinyar nan Abba! Na ce mata ta shirya zan kai ta shopping fa".
"Zan baka! amma bashi".
Da sauri ya ce "Na yarda! Amma Abba zan karba ne bisa sharadin sai na samu damar biya, bana son a deba mini lokaci, na kasa bayar wa a wannan lokacin. Sannan idan na mutu kafin na biya, ka yafe mini".
Ga mamakin Abba sai jikinsa ya yi sanyi ya ce "To".
Ya tashi ya dauko masa ku'di mai auki ya bashi yana cewa "Ubangiji ya shirya mini kai, ya baka ikon biyan bashi".
Ya sunkuyar da kai yana godiya domin yawan ku'din ya matu'kar faranta ransa, bai yi zaton zai bashi masu nauyin haka ba".
Suka yi sallama ya tafi, ko wajen Umma bai shiga ba, saboda yadda yake cikin zumudin komawa gidan sa.
Ya fito kenan wayar abokinsa Faruk Bello ta shigo masa.
Ya amsa