Showing 90001 words to 93000 words out of 180068 words

Chapter 31 - Sabo Da Kaza By Surayyah Dee

18 Dec 2025

8760

tunani, da sannu zan fahimtar da shi muhimmancin ki".
Ba ja in ja na ce "zan kiyaye Abba".
Ya ce "madallah da Halimatu ta shi ki yi, tafiyar ki, ki kwantar da hankalinki kina cikin aminci. Komai kike so kar ki 'kwari kanki".
Na dawo dakina sukuku. Na kwanta akan gado hawaye na bin fuskata. Zuciyata ta yi nauyi ainun. Fargaba da zullumi fal a raina. Shin idan Abba ya kashe mini aure ya ya zan yi ne?
Dai-dai lokacin cikina ya yi wani irin motsi mai karfi. Na saka hannu na dafe wajen da na ji ya motsa din. Rabon da ya yi mini irin wannan motsin tun ranar da aka daure mini bakin mahaifa, a ranar kam ya yi zillo sosai tabbacin ya 'kuntata.
A fili na ce "Na sani kana taya ni ko kina taya ni faragabar dutsen da ake shirin gindaya tsakanina da farin cikina. A hankali na mi'ke na yi wanka na karya sama sama. Sai da na shirya tsaf, sannnan ya zo saboda week end ne.
Kalaman Abba sun sanya mini kasala sosai.
Shiyasa ya ganni ba kuzari. Ya tambayi ina lafiya kuwa? Na bashi amsa da "lafiya lau, yanayin ne babu da'di.
Ya ce "Kin je wajen Abban kuwa?"
A hankali na ce "Na je ban jima da dawowa ba."
"To ya kuka Yi?"
Ya tambaya cikin za'kuwa.
Sai da na numfasa na bashi amsa da cewa " Ya ce ai ya fa'da maka sai na warware! Haka ya sake jaddada mini nima".
Ya zabura ya mi'ke yana nuna ni da hannu cikin fishi ya ce "Haka muka yi? Ba na ce ki ce masa kin warware ba?"
Na sassauta murya na ce "wallahi na fa'da masa. Baka ga fa'dan da ya mini ba, wai na raina shi tunda na tunkare shi da wannan maganar".
Ya rasa yadda zai yi.
Ya ce "Haka ya ce?"
Na girgiza masa kai tabbacin eh.
Ya fita yana cewa "Bari na je da kaina, na gaji da wannan kama karyar da ake mini".
*Wajen Abba*.

Kishingi'de ya same shi, yana karatun littafin Muwad'da Malik. Sai da ya kammala sannan ya ajiye ya fuskance shi.
Cikin ladabi sosai Gudale ya ce "Barka da hantsi! Ya jiki jiki, ya kuma ha'kuri da rayuwar nan mai cike da hargitsi?"
Mamaki ya kama Abba na wannan sabuwar nau'in gaisuwa da autansa ya yi masa.
Murmushin da bai shirya yi ba ya subuce masa saboda yadda ya ga Sadik cikin nutsuwa tabbacin yana cikin neman taimakon sa.
Ya amsa masa da Alhamdulillah a takaice.
Ya dinga kame kame kafin ya yi kundubalar cewa "Abba Halimatu ta ji sau'ki sosai. Likita ya tabbatar da hakan kuma."
"Na sani! Sakina ta fa'da mini bayanin likita"
Abban ya fa'da hankalinsa na kan talabijin.
Tsawon lokaci Gudale na fama da takaici, amma da yake nema yake yi sai ya ha'diye fishin ya ce "To Abba me take yi anan? Ya kamata ta koma dakinta duk abin da ba zata iya yi ba, zan yi mata uzziri tunda lalura ce".
Sai lokacin Abba ya karkato da dukkan hankalinsa kan Gudale ya ce "Ka turo ta zo ta ce zata koma dakinta tunda zirga zirgar da ka sanya ta yi bai yi tasiri ba. Yanzu kuma ka zo da kanka a karo na uku".
Kansa ya saukar 'kasa ba tare da ya cewa Abba komai ba.
Tsawon dakika goma kafin Abba ya ce "To bari ka ji na fa'da maka dan ka saurara mini da wannan bibiyar da kake yi mini".
Sai da ya numfasa sannan ya kaurara murya ya ce "waye ya baka auren Halimatu?"
Zuciyarsa ta harba ka'dan. Cikin dauriya ya ce "Kai ne Abba".
"Dama kuma dole na yi maka ko?"
Wanann tambayar kam sai Gudale ya kasa amsa ta.
Abba ya zarce da cewa "Abin da zan fa'da maka shine tunda ni na baka ita akan dole. Shine na ga bai kamata zaman na ku ya cigaba da wanzuwa ba. Har zuciyata ban kullace ka ba. Amma ka sani auren na ku ya ishe ni haka nan. Yadda na baka ita cikin girma da arziki. Ina baka umarni ka sakar mini ita a mutuntunce tun bamu rabu dutse a hannun riga ba."
Wata irin fargaba ta shige shi mussaman da ya 'dago ya kalli fuskar Abba ya ga babu alamun wasa.
Da rudani ya ce "Ta ce ina yi mata wani abin ne Abba?"
"Ko daya wlh bata ce mini komai akan zamanku ba. Ita tana da ra'ayin kanta ne? Ai komai kake so hakan zata yi, tunda ita tana sonka, ba dole na yi mata take zaune da kai ba. Duk da cewa iko kawai na yi akanta na za'ba mata miji ta karba da hannu biyu take kuma mutuntata zaman".
Kan Gudale ya daure. Shaguben na Abba ya buge shi kwarai da gaske.
Ya numfasa ya ce "Da hannu biyu nima na karba Abba, gashi nan muna zaune 'kalau komai lafiya a tsakaninmu".

"Hakane"
Abba ya fa'da a gajarce.
Tsawon lokaci ba Wanda ya sake magana a cikinsu. Gudale dai ya dorawa Halima laifi. Ya tsargu, gani yake wani abin ta fa'da. Takaici ya kama shi! Wanne irin aure yake yi da bashi da ikon zartar da hukuncin da yake so akan matarsa?
Murya ba amo ya katse shirun da cewa "Abba fa'da mini ranar da zata koma dan na daina damunka".
Kai-tsaye Abban ya ce "Ba zan ce ga rana ba. Amma da zarar ta warware da kaina zan saka ranar".
Kan Gudale ya daure ainun! Ya rasa gane nufin Abban, ya kasa fahimtar warwarewar da Abba yake nufin Halimatu ta yi.
Da fishi ya bar falon ba tare da ya ce uffan ba.
Amma ya gaji da wannan mulkin mallakkan da ake yi masa. Indai haka ake yiwa mutum iko idan an yi masa aure to gara a bari ya yiwa kansa komai sai ya yi iko da iyalinsa.
Ya gaji da wannan kama karyar. Ya kai gejin wajen ha'kuri da alkunya. Tabbas idan Abba ya cigaba da ri'ke masa mata zai gurfana a gabansa ya fa'da masa yana bukatar matarsa. Idan ya so ace ya yi rashin ta ido.
Kwanaki biyu a tsakanin maganar sa da Abba ya zauna gaban Umma yana sakin maganganun ri'ke masa mata da aka yi.
Ta kalle shi cikin kunan rai ta ce "waton dai so kake ka nuna mini kana son yarinyar nan ko?"
Ba shakka bare nauyi ya ce "ko ba na sonta tunda akwai amfanin da take yi mini ai dole zan bu'kaci ta dawo dakinta".
Jikinta ya yi sanyi. Ba dan komai ba sai dan yanayinsa ya tabbatar mata, baya cikin hayyacinsa. Kuma Gudalenta yana cikin soyayya mai zurfi. Sai dai kuma shi kansa bai fahimci irin deep din da ya yi akan soyayyar Guduyo ba.
A fili ta ce "Allah ka shiga tsakanin duk mai son shiga tsakanin 'da da mahaifi. Allah ina nemawa Gudale tsari da kaidin mace da makircinta."
Ya murmusa ya ce "Ameen Ummah! Ina son ki gane duk duniya ke ce farin-cikina. Ba abin da zan nema baki mini ba. Ina son ki taimake ni ki mini uzziri."
Ga'ba daya ta 'dora hankalinta a kansa.
Ya yi kasa da kansa ya ce "Ba da rashin kunya ba Umma! Ina bu'katar matata gaskiya. Dan haka ki gajarce mini wahalar nan ki sanar wa mijinki, na gaji da ri'ke mini ita da yake yi babu dalili. Akan ta aka fara jinya?
Shin haka yake yiwa mazajen su Sakina?
Ko dan ni bai dauke ni surukinsa ba?
Alhalin yadda yake nunawa shine uban Guduyo ai kamata ya yi ya mayar da mua'amalata da shi irin yadda yake yi da surikansa".

Umma da ba'kin cikin kalamansa suka turnike ta tamkar ta rushe da kuka.
Murya na rawa ta ce "shi ka kasa cin mutuncinsa a gabansa, amma ni ka zo ka tasa ni a gaba kana tozarta ni. A gabana kake wannan tijarar akan Halimatu?
Ashe dai zanga ranar da zaka so Kumbusar nan har haka?
Ashe zaka iya fifita farin-cikinka akan nawa? "
A sanyaye ya ce "Ba sonta nake yi ba Umma! Amma ita ce halal 'dina a halin yanzu. Kinsan nan duniya ba wanda nake so na yi sharing damuwata sama da ke. Saboda ba soyayyar da nake da garantin amintacciya ce sama da wacce kike yi mini. Ina 'kara yi miki alwashin babu mai shiga tsakanina da ke. Ki zuba ido zaki gane 'kaddara ce kawai ta ha'da ni da Guduyo".
Ta saki ajiyar zuciyar samun nutsuwa. Ta ce "Zan fa'da masa, amma ka dage da addu'a, mutanan nan basu da tausayi bare su yi kawaici. Makirai ne na gaske, yan gadon kanainaye namiji ne".
Ba damuwa tare da shi ya ce "Yo ni Umma idan aka ga an mallake ni ba 'karamin asiri ne zai kama ni ba. Domin kuwa ina addu'a sosai, sannan ni din masifaffe ne na gaske. Asiri yafi cin laku laku ai".
Da haka ya lallabata suka bar maganar, suka shiga wata.

Washagari ya zo ya same ni na yi wanka fes da ni duk da ban yi kwalliya ba.
Ya tsaya bai zauna ba, yana mini irin kallo.
A hankali na ce "sannu da zuwa ina kwana?"
Bai amsa ba ya ce "Guduyo wato ke baki da matsalar zaman ki anan ko? Na gane kin mance da ni. Kin fi enjoying din gidan nan akan gidana. Menane bana yi miki ban da goyo?"
Na murmusa na ce "shima idan ka daure din ai zaka iya, fafalo ce ba ni da nauyi sosai".
Ya dan murmusa ya ce "kawai ki ce so kike na zama mijin novel".
Na ce "A zahirin ma ana goyon fa".
Kai tsaye ya ce "Yan shawalwalai ba".
Daga haka na bar maganar.
Ya ce "Na rantse na kusa na daina yi miki magana, na baki daga nan zuwa gobe ki san yadda zaki yi a dawo mini da ke. If not mun 'bata, kuma zan iya yin komai, har da budurwa zan yi".
A raunane na ce "Ba yadda zan yi Yaya Gudale. Kar ka jingina mini laifi, ba zan iya watsa wa Abba k'asa a ido ba. Duk abin da yake yi saboda cigabanmu ne, Babinmu yake tattala mana".
Ya hassalo ya ce "To ni watsa mini 'kasar tunda ya fini hakki akan ki. Wallahi idan baki yi a hankali ba, yau dai kam ba zaki rabauta ba, tunda kin gardame mini. Wai Babinmu yake tattala mana! Mai iyayyin tsiya, to mu ba zamu tattala shi ba da muka yi sanadin samuwarsa? Sai kaka ne zai yi wannan karambanin. To ki fa'da masa Uban Bebin ya ce zai tattala abinsa".
Na yi shiru, amma zuciyata sai harba wa take yi a dalilin fusata da na ga ya yi.
Murya na rawa na ce "kar ka ga laifina da gangan. Ni kaina na matsu na dawo".
Ya kyabe baki ya ce "kal ka ga yaifina da yayyan".
Na sauke kaina 'kasa dalilin dariyar yadda ya yi magana tamkar ta yaro dan karami, wai kuma nufinsa nine na yi hakan.
Ya ce "idan fa kika wuce jibi a gidan nan, nasan inda kika ajiye ni"
Ya fice ya bar ni da zullumi. Tsakani da Allah na tsani duk abin da zai jagula ran Gudale. Sonsa nake yi da dukkan zuciyata. Ina gudun bacin ransa fiye da komai. Babban farin-cikina na ganshi cikin walwala da sukuni. Bacin ransa kuma na nufin nawa bacin ran da zama cikin fargaba.
Na rasa yadda zan yi na tunkari Abba. A ranar da ya diba mini idan ta wuce ban koma ba, zai dauki mataki Sakina ta zo. Yanayina ya tabbatar mata kiris nake jira na koma dakina da kaina. Na dinga yi mata kukan ta roki Abba na koma gidana. Gudale ya ce aure zai yi ya manta da ni.
Cikin kuka na ce mata "Ni na gaji gaskiya, ni ban ce mijina ya mini laifi ba. Akan me za'a janyo mini rikici?"
A sanyaye da dinbin mamaki take cewa "kar ki biye shi, kara ha'kuri. Abba ba zai bari a cutar da ke ba, bare shi ya yi miki sanadin cutarwar".
Ta dinga lallaba ni, tana cewa na sassauta wannan zazzafar soyayyar, 'karya yake mini ba wata budurwar da zai yi.
A daddafe na yi kwana biyu. Cikin dare ya 'kira ni a waya ya dinga fa'din "Na gode sosai Guduyo! Na gode da tozarci. Banda ina duba abu guda tak! Da na yi miki baki. Annabi ya ce da zai umarci wata halitta ta yiwa wata halittar sujjadda da ya ce mace ta yiwa mijinta saboda girman hakkinsa da yake kanta.
Amma ke saboda gata kin yi watsi da sababin da zaki sami aljannah. Na gode sosai".
A sanyaye na ce "Yaya Sadik kasan dai ina maka biyayya, ina kuma son ka".
"A baki ba, ina soyayyar take? Banda musu da raini baki iya komai ba. Amma babu damuwa zan yi maganin wannan sha'kiyancin na ki. Billahillazi zan nemo wacce zata girmama ni, wacc zata bi ra'ayina koda ya ci karo da ra'ayinta".
Nan da nan na fara yi masa kuka ina cewa "Ya zan yi ne? Abba fa! Babanmu ne dukkanmu"
"To fa'da mini aljannarki a 'kafarsa take ko a 'kafata?"
Na ce "a kafarka?"
"Madallah! To indai hakane kina son na daga miki sawuna babu 'kwange, kawai ki je ki samu Abba ki ce zaki dawo dakinki. Idan kika yi hakan, to na gamsu kina sona, kina mini biyayya. Kuma in-dai miji na zamewa matarsa sababin shiga aljannah. To wajabat a gareki Yah Halah".
Cikin kuka na ce"To".
Yauwa Bebina ki kwanta ki yi barci, ki ji a ranki Yaya Gudalenki na son ki fiye da son da mijin bahaushe yake yiwa mai dakinsa"
Wani irin Da'di ya kamani karon farko da ya bu'de baki ya ce yana sona. Tuni na manta komai, na dinga tunanin yadda zan yi na gamsar da Abba ina son komawa gidana.
Washagari ta yi dai-dai da komawa asibiti. Umma Abba ya ce ta raka ni. Sanin da ya yi zai iya tare mu a waje ya a tafi da ni. Ya sanya ya wakilta Ashiru ya zo ya kai mu asibitin.
Ashe kuwa Abba ya fahimci Yaya Gudale da kyau.
Muna dawowa a kofar gidan muka tarar da shi.
Sai dai ganin Ashir na tuka mota ya yi kicin kicin da fuska. Ya rasa inda zai tsoma ransa.
Muna bakin gate kafin a bu'de gate ya le'ko ta windon da Umma take. Ya ce "sannunku Ummah."
Ya kallo ni ya ce "Sauko ba sai kin shiga ba".
Na saka hannu da nufin bude kofar, sai na ji Yaya Ashir ya yi locked dinta.
A tunzure ya ce "Ashiru bude mata kofar".
Bai ko kula shi ba, ya ja motar zuwa cikin gidan.
Ina ganin yadda ta sake daure fuskarta.
Bata son na koma gidan Gudale. Fata take yi auren ya balbalce a hakan. Amma kuma ta damu da damuwar da ta gani a fuskarsa a dalilin wulakancin da Yaya Ashir ya yi masa.
Na sani kuma da Yaya Abbas ko Yaya Alamin ke tu'ka motar sai Gudale ya tafi da ni tunda ya raina su, su kuma basa tsananta fa'da da shi.
Amma shi da Yaya Ashir kar tasan kar ne.
Bugu da 'kari Yaya Ashir 'kashi daya ne da shi. Ma'ana irin karfafan mutanen nan ne. Idan suyi maka mahangurba sai ka je 'kasa. Hakan kuma yake zage dukkan 'karfinsa akan Gudale shiyasa yake kiyayarsa domin yasan baya cin riba a hannunsa kamar yadda yake yiwa su Yaya Al'amin.
Yaya Ashir baya ba jin nauyin ya cakumi Gudale da fa'da matu'kar ya nemi yi masa iya shege ko isgilanci. Shiyasa har yanzu basa shiri da juna.
Gane hakan da Abba ya yi shiyasa ya 'dora shi akan tafiyar, ya tabbatar Gudale bai isa 'daukata a gaban Yaya Ashir ba, duk tsagerancinsa kuwa.
Dan kuwa ba zai zame wa Yaya Ashir komai ya na'de kafar wando su daku ba. Domin tamkar borkonon tsidugu haka yake wajen fa'da.
Kuma abin mamaki Gudale kawai yake yiwa wannan bala'in. Su Yaya Abbas zasu zolaye shi su kwana 'kalau amma ban da Gudale.
Ko dan Gudalen yana yi masa iyashegen shi 'dan mace ne?
Shiyasa shi kuma yake nuna masa iyakarsa a cikin gidan da yake alfaharin nasu ne tunda shi 'dan namiji ne.
Har gaban Abba ya kai ni. Ya damka masa mukallin motar tare da cewa "Gata nan na dawo da ita Abba! Zan koma, na bar aiki muhimmai a office. Ubangiji ya 'kara maka lafiya". Yaya Gudale na gefen falon a raku'be tunda ya biyo mu mun shigo tare, Umma ce ta shige wajenta.

Abba ya riko hannunsa ya ce "madallah da jarumi irinka Ashir! A duk sadda na kalle ka na kan tuna sadda muke yara. Uwarka jarumace ta gaske.
'Kanwata ce ta nisa amma ta sha tara ku'dinta ta bani idan zan tafi makaranta
Na sani daga siffa har jarumtar Binta ka dauke su tsaf, har jarumtar murkushe iyashegen mai iyashege duk ka dauko.
Ina jinka a raina tamkar yadda nake jin ta.
Na gaji da zaman ka hakan. Ka je gidan Babanku na Gusau ku daidaita da Farisa na baka ita".
Ya koma 'kasa ya tsugunna ya ce "Na karba da hannu biyu Abba, dama ina son ta. Idan ina gaban ka na kan yi dakacen inama na fito ta tsatsonka? saboda tsananin karamcinka, wanda ka zamewa mahaifi tabbas masu sa'a ne, duk da ba lallai wani ya fahimci irin gam da katar din da ya yi ba. Bare ya yi koyi ya zama abin misali. Madallah da kai Abbah! Madallah da mutane irin ka. Allah ya shiryi masu halin albasa! Kar a gaji da addu'a, da sannu komai zai daidaita maka Abba".
Albarka kan albarka Abba ya dinga sanya masa.
Yana sake jinjina jarumtar Yaya Ashir har cikin zuciyarsa. Yana kuma gode masa yadda yake wanke masa Yaya Sadik. yake kuma hana shi kuzari indai yana wajen.
Ya mi'ke ya fice da sauri bai ko kalli gefen da Gudale ya safare ba.
Sai da ya fice Yaya Gude ya gaida Abba a raunane domin ya kai matu'kar ka'duwa da abin da suka yi masa shi da Ashir.
"A fusace ya ce "Gata nan Abba ta warware! Zan tafi da ita".
Kai tsaye Abba ya ce "Kai Sadik! Bude kunne ka ji ni da kyau. Komawa ne ba zata yi ba.
Ai ni na baka ita, yanzu kuma tunda na gane cutar ka na yi, to na janye cutarwar".
A matu'kar razane ya kallo ni ya ce "Daga yi miki wasa Guduyo shine kika zo, kika ha'da mini gurnet?
Ai dai sau 'daya na fa'da, kuma kalmomin yabo nawa na fa'da miki?"
Baki ma rawa na kalle shi na ce "Billahillazi ko point ban

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login