Showing 42001 words to 45000 words out of 120332 words
Chapter 15 - WUTA A MASA?A COMPLETE HAUSA NOVEL BY AYSHERCOOL
hijjabi a kai.
Amma tuni hijjabin yai nasa guri ya bar Amira, "Allah kaga abunda wannan bawan naka yakemin, Allah ka sakamin wallahi na barka da Allah"
Kowa na gudun tunkarar Imran ya ƙwaci Amira, saboda duk wanda yazo gurin ze iya haɗawa da shi, Ammi ta window ta dinga kiran sunan Imran tana karya kashe mata 'ya, Amma be saurareta ba.
Anty Fa'iza ma da tuni suka dawo, ta dinga masa magiya akan ya ƙyale Amira, dan ta san idan ze kashe Amira ne bakinta baze mutu ba, dan Amira akwai taurin kai, kuma bata son duka sam.
Allah ya temaketa ta buɗe ƙofar ɗakin, tai waje da gudu jikinta na tsuma, saboda ta daku ba ƙarya.
Abba kuwa daga part ɗinsa ya dinga jiyo hayaniya sama sama, yaji abun yaƙi ƙarewa dan haka ya fito, yana fitowa yaga Amira ta fito da gudu tana kuka, tayi hanyar waje sedai tana zuwa har an rufe gate ɗin dan haka Abba ya samu damar cin mata, ya riƙo hannayenta yana faɗin "Amira lafiya kuwa? Meyasameki haka?"
Kasa magana tayi se kuka da take kamar ranta ze fita, Anty Fa'iza ce ta ƙaraso ta cewa "gaskiya ba zamu kwana a gidan nan ba, tunda munzo anyi biki Allah ya amfana, Imran ze iya illata Amira"
Cikin rashin Fahimta Abba yace "meyafaru ne?"
"Faɗa ne ya haɗa su da Minal ya dake su, Amma dukan da yai wa Amira ya wuce tunani, tana mace be kamata ya mata wannan dukan ba, kalli jikinta fa"
Gwanin ban tausayi, fatarta duk ta tara jini, wani gurin ya farfashe se rawar sanyi take tana kuka.
Abba yace "Innalillahi wa innalillahi raji'un, Imran ɗin ne yai mata haka?"
Dukda dukan da Imran ɗin yai mata, sam be huce ba ransa a ɓace yake sosai, yana fitowa harabar gidan yaga Abba a tsaye riƙe da hannun Amira, Mutane duk a tsaye a gurin.
Gabansa ne ya faɗi ya ƙarasa gurin, yana zuwa zeyi magana Abba ya dskatar dashi yace "base kace komai ba Imran, nagode gara da ka nuna min irin riƙon da za kai Mata nagode sosai"
"Abba ba haka bane, walla...
"Shuy up! Meye ba hakan ba, da ka kasheta fa? wane irin duka ne wannan, waye ma yace kasa hannu ka daketa? Ka kyauta ba abunda zance maka se godiya"
Abba yace a kawowa Amira Hijjabi, ya tafi da ita sashinsa, aka kawo hijjabi ta saka, amma still jikinta rawa yake, Anty Fa'iza zata bisu yace bakomai base ta bisu ba.
Abba da kansa ya ɗakko bargo ya lulluɓeta, ya nemi guri ya zauna yana tunani, Imran ya rasa abunda zeyi gaba ɗaya Aurensa yazo masa a baibai.
Ammi ce ta shiga sashin Abba tana faɗa "wallahi Abba ka bani mamaki, ko takan Minal baka bi ba bayan itama ya daketa, se wani abu kake akan Yarinyar nan, zan sake jadadda maka wallahi ba zata zauna min a gida ba, ka basu kuɗin mota gobe su tafi, ta kama min 'ya ta daka kuma shima yazo ya haɗasu ya daka, amma kai ta ita kawai kake baka ta 'yarka.
Abba bece mata uffan ba, ya kalli inda Amira take, jikinta na cigaba da rawa se surutai take, yaje inda take kwance ya ɗan ɗaga bargon ya dafa goshinta, jikinta ya ɗau zafi sosai.
Ran Abba ya sake ɓaci sosai, ya ɗau wayarsa ya kira Imran, ba'a daɗe ba sega Imran yazo jiki na rawa.
Abba yace "kaga sakamako abunda kayi ko?"
Imran ya sunkunyar da kai ƙasa.
"Gidan Alhaji Hashim zamu tafi Yanzu, ka kaita mota gani nan fitowa"
Amira ta tashi tana jiri, tabi bayan Imran, ita dai bata san ma yadda akayi taje mota ba se ganinta tai a Mota, Ammi tana ta masifa tana tambayar meye ba'asin zuwa gidan Alhaji Hashim a daren nan, amma Abba ya shareta ya fice.
Suna tafe Abba na yiwa Imran faɗa
"Imran idan bazaka iyayimin alfarmar da na nema a gurinka ba, tun wuri ka gayamin in nemi wani yayi min"
"A'a Abba zan iya"
"Aini na tsorata da lamarinka ne Imran, ka bani mamaki sosai"
"Abba dan Allah kayi haƙuri, yarinyace sam bata da kunya, dambe fa sukayi ita da Minal a gaban mutane"
"Du da haka, mata lallaɓasu akeyi, karka kuskura ka saba musu da duka mutuncinka ze zube a idonsu, mussaman duk irin wannan na rashin imani, duk randa ka kuskura ka daki wata a cikinsu duk hukuncin da nayi maka kai ka janyo shi"
"Insha Allah bazan sake ba"
Amarya Ihsan kuwa tunda suka koma gida take Kuka, aka rasa gane kanta sam, wani mugun kishi da haushin Imran suka mamayeta, ga tsanar Amira da take ji a ranta.
Yayan Baban Amira ne yazo, yace ai masa magana da Maman Ihsan.
"Kaine a tafe da daddare haka? Ina fatan lafiya ƙalau?"
Yace "eh lafiya ƙalau Alhamdilillah, ya hidima?"
"Hidima Alhamdilillah, muna ta fama daga gobe in Allah ya kaimu dai an gama kowa ya huta"
"Hakane, dama wata maganace ke tafe dani, kin san komai muƙaddari ne daga Allah, dan haka kafin in gayamiki koma meye, ina son kuyi tawakkali daga ke har Ihsan"
"Lafiya kuwa? Auren suka fasa kokuwa?"
"A'a ba Aure suka fasa ba, kamar yadda suka canza muku gidan da za'ayi jere hakan ya faru ne sakamakon wani hukunci da mahaifinsa shi angon ya yanke, ze aurawa ɗansa mata biyu ne lokaci ɗaya, bayan Ihsan akwai wata da za'a ɗaura Aurenta da Imran gobe in Allah ya kaimu, su biyu kenan !!!
Domin Sharhi gyara Ko shawara
Ayshercool
07073065680
[1/19, 2:13 PM] Ayshercool: 🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥
WUTA A MASAƘA
PERFECT WRITERS ASSOCIATION
(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS)
https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
P. W. A
*Story and written by*
AISHA ADAM (AYSHERCOOL)
The experience writer of
*ABDUL JALAL*
* WATA KISSAR.... (SAI MATA)
*BAƘIN TABO (Labarin gasa)
*AƘIDATA (Paid Book)
* WUTA A MASAƘA
https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=in
❌❌❌
Ƙirƙirarren labari ne, ban yadda ayi amfani da kowane sashi na labarin ba ba tare da izinina ba.
21_22
"Nifa ban fahimci abinda kake nufi ba, kamar yaya mata biyu za'a aura masa?"
"Da hausa fa nayi miki bayani, ba da Yarabanci ba, Mijin Ihsan da za'a ɗaura musu Aure gobe in Allah ya kaimu, su biyu za'a aura masa, ita da abokiyar zamanta"
A fusace Maman Ihsan tace "aikuwa ba zata saɓu ba sam, ni za'a ciwa mutunci a munafurta, daga ina wannan banzar maganar ta fito? Kuma ba'a gayamin tuntuni ba se ana i gobe za'a ɗaura Aure, dan cin fuska da cin zarafi"
"Kinga ki dakata mun dan Allah, gudun irin wannan matsalar da rashin tawwakalin yasa ban sanar muku ba, tun kafin a fara bikin nan, suka zo suka sanarmin ni nace kar su gaya muku, in ba haka ba bazaku bari ayi bikin nan ta daɗin rai ba, kuma nine matsayin uba ga Ihsan, Auren nan bau fashi za'ayi shi gobe insha Allah, kin sani sarai bana Magana biyu, idan kinso kije ki rarrasheta ki kwantar mata da hankali, idan kin so kije ki zigata ki tayar mata da hankali kisa idan taje gidan miji ta kaso Auren, ke zaki zauna da ƙaramar bazawara a gida, idan kuma kina ganin duk wannan dandazon jama'ar da kika tara, zasu watsene a fasa Auren, ke kika jiyo se yadda kuka zaɓa"
Yana gama maganar ya tashi ya fice.
"Wallahi ba zata saɓu ba wai bindiga a ruwa, dan bala'i Auren fari yarinyar ba zata zauna ta huta taci amarcinta ba, za'a haɗata da wata a auren fari, Lallai Jamila ta munafurceni, dani take zancen".
Ta ɗakko wayarta ta kira layin Ammi, sedai Ammi bata ɗaga ba, saboda tana can tana rarrashin Minal, saboda dukan da ta sha, gashi a ƙule take jiran su Abba take su dawo ayi wadda za'ayi akan Amira, Dan duk abunda za'ayi se Amira ta bar gidan nan a gobe.
Maman Ilham ta dinga surfa masifa, tace sedai a fasa Auren baza'a ci mata mutunci ba, hankalin mutane'yan biki ya fara dawowa kanta, aka fara ƙoƙarin jin ba'asin abunda ya sata masifa haka a wannan daren, bayan dawowa daga dinner.
Yayarta ce taja hannunta suka uwar ɗaki, ta rufe ƙofa tace "Ke Murja, ki rufawa kanki Asiri kamar yadda Allah ya rufa miki, karki yadda a fasa Auren nan, ki taushi yarinyar nan taje ta tsuguna a ɗakinta tunda Yaron nan yana sonta tana sonshi nasan ba'ayi muku adalci ba, da ba'a gayamuku da wuri ba, amma bari kiji bar ganin Ihsan na da wannan kyan, samun miji irin wanda ta samu yana da wuya a wannan zamanin, dan haka kuyi haƙuri, taje ta zauna sedai kawai ki tashi tsaye ki gyara 'yarki ta riƙe mijinta, ki tabattar ta zama Mowar gida, idan ba haka ba kin san yadda muke cikin 'yan Uba da maƙiya, duk dangin nan namu gashi wasunmu na da kuɗin amma babu yarinyar da ta samu miji kamar na Amira, gashi ɗan shahararren mutum, ga kuɗi da kyau suna dashi, dama Auren nan na Ibsan a wuyan wasu yake, idan kika sa aka fasa Auren nan wallahi a cikin maƙiya za'a samu wanda ze lallaɓa ya bashi tashi 'yar ya haɗa biyun, Mussaman ke da Akuyarki tayi kuka a dangi gara ki rufawa kanki Asiri"
"Amma Yaya Atine an min adalci kenan? 'yar guda ɗaya a haɗata da kishiya, kuma a kasa gayamin se ana gobe ɗaurin Aure?".
"Kiyi haƙuri, kedai ki samu tayi aure ta tashi daga gaban ki, wallahi aka fasa Auren nan sekin rasa inda zaki sa kanki saboda surutan mutane, gara ayi surutan akan su biyu ya aura, da ai surutan kin hana Auren, da azo daga baya taje suyi miki aika aika, dan ni na tsorata da yadda suke son juna, tunda tazo gidana hutu, na gane ba ƙaramin so take masa ba"
Jiki a sanyaye Maman Ilham tace "shikenan Yaya Atine, amma ya zan gayawa Ihsan? Ina jin tausayinta sosai"
"Ki ƙyaleta karki gayamata yanzu, naga kamar tana cikin damuwa yanzu haka, kuma zata iya bijirewa tace ta fasa auren, kuma abunda bama so kenan"
Haka Yaya Atine taita kwantarwa da Maman Ihsan hankali..
Imran kuwa har suka je gidan Alhaji Hashim, be kuma cewa uffan ba, sam baya nadamar dukan da yaiwa Amira, saboda ƙiriniyarta da rashin jinta yai mata yawa, duk da kusan ƙarfe sha biyu na dare, suna zuwa gidan Alhaji Hashim aka buɗe musu gate, dayake Abba ya sanarwa da megidan zuwansu.
A harabar gidan, suka tarar da Alhaji Hashim, ya ƙaraso inda sukayi parking ɗin mota, Abba ya fito suka gaisa ya kalli Abba yace "Ali lafiya dai ko? Meke faruwa ne haka?"
"To lafiya amma ba lau ba, Imran ne ya kama Amira ya zaneta wallahi, yanzu gaba ɗaya jikinta ya ɗau zafi, nayi tunanin kaita Asibitin da me ɗakin ka take aiki, se kuma na tuna sunje gurin Dinner ɗazu, kuma ba lallai tana night duty ba, kuma daɗin daɗawa dai, gobe in Allah ya kaimu za'a ɗaura Aure, bana son a samu wata matsala sam"
Alhaji Hashim yace "Eh gara daka kawota nan ɗin, dukda dama munyi da kai bayan an ɗaura zata zauna a nan ne.
Ya ƙarasa gaban motar ya kalli Imran yace "Imran meyasa ka dakarmin 'ya ne, ka fiye zuciya da saurin fushi, dole ka rage wasu abubuwan da kake yi, tashe ta naga kamar bacci take yi, ka shigo da ita, bari in taso matar gidan"
Abba yace "Afuwan fa, zamu takurata"
Alhaji Hashim yace "No karka damu, ai ita tana nan tana jiran zuwan Amira dama, bari in mata Magana"
Imran ya buɗe ƙofar motar ta baya, ya daddaki Amira yace "Malama ki tashi"
A hankali ta motsa, dan baccin wahala ne ya ɗauketa, ga jikinta yayi zafi zauu, ko ina na jikinta Banda raɗaɗi, ba abunda yake mata.
A hankali ta fito daga motar, jiri na kwasarta, ta jingina da jikin motar, taji yadda jikinta ke zugi, ta tuna yadda Imran ya dinga jibgarta ɗazu kawai ta fashe da kuka, harda sheshsheƙa.
Abba yace "yi haƙuri Amira, zaki iya tafiyar ko a riƙeki?"
Ta girgizawa Abba kai, Alhaji Hashim ya fito yace "Bismillah ku shigo"
Abba yace "Imran riƙe hannunta karta faɗi" takaici ne ya kama shi ganin yadda Amira ke wani sake lanƙwashewa, tana tangaɗi.
Baya son yin musu da Abba, dan haka ya riƙe hannunta, suna tafiya a hankali amma kuka take, Abba yai gaba ya rigasu shiga, Amira ta fuzge hannunta daga nasa, taƙi shiga cikin falon ta tsaya ƙyam a waje tana kuka.
"Zaki wuce ki shiga ko sena ɓarar dake a gurin nan?"
"Bazan shiga ba ɗin, ba ɓararwa ba yanka ni zakayi, Mugu kawai"
Muryarta ta shaƙe saboda kuka, ko fita bata yi sosai amma bakin yaƙi mutuwa.
Aikuwa ya shige ya barta a gurin, yana shiga ya tarar har matar Alhaji Hashim ta fito falon, Abba yace 'ina Amiran kuma?"
"Tace ba zata shigo ba, tana tsaye a waje" ya basu amsa.
Abba ya girgiza kai ya taso ya fito wajen, tana tsaye jikinta nata rawar sanyi se kuka takeyi, Abba yace "Amira ki shigo mana, dubaki za'ayi a baki magani ai"
Girgiza kai tayi tace "dan girman Allah a maidani gida, dan Allah kayi haƙuri ku maida ni gida kafin ɗanka ya kasheni, dan Allah kayi haƙuri ku kaini inda zan hau mota in koma gida"
Abba yace "naji amma ki tashi mu shiga a duba lafiyarki, nan gidan Alhaji Hashim ne fa, kin tuna shi"
Matar Alhaji Hashim tace "Ohh dama wannan ce 'yar tawa? Ai na ganta ɗazu a gurin biki, kizo mu shiga ciki kinji"
Maimakon ta tashi, sema ta zube akan gwiwowinta tana yiwa Abba magiyar ita dai a maida ita gida, sedai kan Abban ya kuma magana, Amiran ta faɗi a gurin sumammiya.
Gaba ɗaya sukayi kanta suna kiran Innalillahi wa innalillahi raji'un.
Imran ne ya ɗauketa ya shiga da ita falon aka kwantar da ita, ta ɗakko ruwa me sanyi tana shafawa Amira a fuska, ta cirewa Amira hijjabin jikinta, seda Imran ya ɗan tsorata ganin illar da yaiwa Fatar Amira.
Duk fatarta tayi taruwar jini, harda wani sashe na fuskarta, akwai almar duka.
Hajiya Nafisa matar Alhaji Hashim, wadda suke cewa Anty ta ɗago ta kalli Abba tace "waye yai mata wannan dukan haka?"
Abba yace 'gashi nan ɗanki ne Imran"
Anty tace "da wani ne ba kai ba Imran, da tabbas sena kai ka Human rights, haba Imran kamar ba wayayye ba? Ya zaka zage ƙwanjinka akan mace kamar haka, kuma ma wadda zaka aura, 'yar uwakka ce fa, ai kamats yayi kowani kaga ze mata haka, ka tsaya mata amma kai da kanka, dan abun kunya, kuma da alama jikinta baya son duka, dan shine ya samata wannan zazzaɓin, amma karku damu zata farfaɗo insha Allah, zanyi amfani da wannan damar ma, a ɗibi jininta a daren nan a kaishi lap, ayi mata duk gwajin daya dace"
Abba yace "to shikenan Nagode sosai, Allah ya saka da Alkhairi ya bar zumunci"
Suna nan zaune a daren, aka sakawa Amira ruwa bacci ya ɗauke ta.
Haka nan a daren Abba da Imran suka kuma komawa gida, suna tafe Abba yana ƙara yiwa Imran Nasiha.
Ammi kuwa bata ga kiran Maman Ilham ba se bayan sha biyun dare, bata bi kiram ba saboda a ganinta dare yayi, tace bari ta bari seda Safe ta kirata.
Imran kam kasa bacci yayi, yana tunanin ya Ihsan zataji idan taji labarin su biyu ze aura, ya tabbata maƙaryaci kuma mayaudari kamar yadda ta faɗa, tun farko yakamata ace ta sani, ba yanzu da lokaci ya ƙure ba, Amira ta ɓata masa komai, ga Yadda ran Abba ya ɓaci saboda dukan da yai mata, wannan yarinyar a sanadinta Komai na tafiya ba yadda ya so ba.
Haka ya wayi garin Allah duk da tarin gajiyar da yake ɗauke da ita, amma ya kasa bacci, ranar ɗaurin Aurensa ne, amma sam baya murna da ranar, gaba ɗaya jikinsa a sanyaye yake.
Da Safe wajen ƙarfe takwas da rabi, aka takurawa Ihsan taci Abinci, haka nan gabanta yake ta faɗuwa, maimakon tayi farinciki da ranar ita ma faɗuwar gaban ce ke damunta.
Bayan ta gama cakalar Abinci, ana cewa me kwalliya zata zo ta mata kwalliya, kafin 'yan ɗaurin Aure suzo, Yaya Atine taje ta sameta ta cewa ƙawayenta su ɗan basu guri, aikuwa suka fita suka basu guri.
Ta rufe ƙofa ta dawo ta zauna a kusa da Ihsan tace
"Ihsan ina son ki buɗe kunnuwanki da kyau ki saurareni, ina son ki ɗau abunda zan gaya miki a matsayin ƙaddara kamar yadda muka ɗauka ni da mahaifiyarki, jiyavda daddare wan Mahaifinki yazo bayan an dawo daga gurin Dinner, ya gaya mana wani abu da ya girgiza mu, amma kamar yadda na taushi mahaifiyarki ta haƙura ta kwantar da hankalinta, kema haka nake so kiyi haƙuri ki kwantar da hankalinki, kamar yadda kika sani anjima za'a ɗaura miki Aure da Imran, sedai ku biyu zaku aure shi"
Ihsan ta kalli Yaya Atine tace "Kamar yaya kenan?"
"Eh, haka wan mahaifinki yazo ya gaya mana jiya daddare, amma dan Allah ki kwantar da hankalinki, amma keda abokiyar zamanki za'a ɗaura Aurenku yau"
"Innalillahi wa innalillahi raji'un, meyasa Imran zemin haka? Dama abunda yake shiryamin kenan? Duk yadda na bashi yadda amma shi ba haka bane a gurinsa, dama nasan za'ai haka, tuntuni nake ganin take takensa amma soyayya ta rufemin ido, to yaje ya auri duk wadda yake so, amma Aure ni da Imran babu shi, na haƙura na barwa kowa cece na bar mata Imran, na haƙura, bazan Auri Imran ba wallahi na haƙura!!!"
Tai maganar cikin kuka me ban tausayi, Yaya Atine tace "Ihsan karki wa kanki biyu babu, wan mahaifinki yace ɗayar Umarnin mahaifinsa ne yasa ze Aureta, kiyi haƙuri ki kwantar da hankalinki"
"Ni ba wani hankali na da zan kwantar, an cuceni an yaudareni, idan 'yarsu ce ni zasu min haka ne, ba wani Auren biyayya dama can an shirya wulaƙantani ne, ni ba zan zauna da kishiya ba, na haƙura da Imran na fasa Auren"
Nan da nan Ihsan ta birkice, ta dinga koke koke tana bori, tace Allah karta ba zata auri Imran ba, jikinta ya riga ya gama bata Amira ce matar da ze Aura su biyu.
Rarrashin duniya amma Ihsan fafur taƙi sauraren kowa, se kuka da takeyi kamar zata shiɗe, nan da nan idanunta suka kumbura, ta fita hayyacinta kamar wadda akace za'a kashe.
Imran kuwa ya kasa komai, se aikin tunani harya faɗa saboda damuwa da tashin hankali, ga tausayin