Showing 6001 words to 9000 words out of 120332 words

Chapter 3 - WUTA A MASA?A COMPLETE HAUSA NOVEL BY AYSHERCOOL

10 Mar 2025

30337

Yahayan ta aura, ni kuma na aureka kowama ya huta"

Fa'iza tace "Amira ki aureshi mana, ga ɗaki nan a tsakar gida kizo mu zauna"

Bashir kawai yai murmushi, dan rigimar Amira bata ƙarewa sam.
Amira tace  "ni bani yarana, tare dasu zamu kwana"

Tasa hannu ta ɗauki Khalil, ta kama hannun Khairat zuwa ɗaya ɗakin.

Bayan fitarsu, Bashir ya kalli Fa'iza yace "Ummu Khairat, ki dinga haƙuri da Amira, sannan kin dinga mata Addu'a, yawan faɗan da kike mata bazesa ta dena abunda take ba"

Fa'iza tai ajiyar zuciya, amma takasa cewa komai, amma harga Allah rayuwar da Amira take tana damunta sosai.





Yana tsaye a jikin motarsa, ya ciro wayarsa ya ɗan daddana sannan yasa a kunnensa.
"My heart gani na ƙaraso"

"Alhamdilillah, shigo ciki ka jirani a guest room gani nan"

"A'a, ni sedai kizo ki tafi dani, saboda ina samu damar fanshe kallonki da banba sosai tsawon lokaci"

Murmushi tayi tace "yadda kake so haka za'ayi angon Ihsan"

Shima murnushi yayi ya katse kiran, yana nan a tsaye sega Ihsan ta fito, jikinta sanye da doguwar rigar Abaya, tana da kyau sosai Dan haka bata damu da kwalliya ba sam, sedai tayi kyau matuƙa a cikin kayan.

Tun daga nesa take masa murmushi, Yayin da shi kuma ya kafeta da idanunsa, wanda seda hakan ya ɗan sata jin nauyinsa, tana zuwa inda yake tsaye ta ɗago manyan idanunta ta kalleshi tace "Soja marmari daga nesa"

"Au kema haka zakice My Ihsan?"

"Ba kirarin da ake muku kenan ba? Amma aini a kodayaushe marmarin ganinka nake, bakaga yadda na rame ba saboda rashinkaba kusa dani, watanni huɗu fa My love, gaskiya na sha wuyar rashin ganinka, Gashi ba ko yaushe muke waya ba"

Tai maganar kamar zatayi kuka saboda tsabar shagwaɓa, ya ɗanyi murmushi yace "cigaba mana, meyasa kikayi shiru? Ni wannan rigimar taki burgeni take yi wallahi"

"Hakama zakace ko?"

"Ta ya zance idan ba hakan ba my beb? Ok let's go inside se inyi rarrashi"

Tai masa jagora zuwa falon mahaifiyarta don su gaisa, mahaifiyar Ihsan na ganinsu tare da faɗaɗa murmushinta tace "Sannu da zuwa babban ɗa, ashe ka dawo ɗin kuwa?"

Yai murmushi ya zauna akan kujera yace "na dawo, ɗazun nan"

Tace "Masha Allah, ya aikin naku ya hanya"?

"Alhamdilillah"

"Masha Allah, Allah ya ƙara tsarewa, amma kai ƙibarka kayi Imran, kamar ba wanda yaje aiki ba"

Yai murmushi yace "ƙibar wahala ce Mummy"

Ta dings masa dariya tana dama ana ƙibar wahala? Bayan sun gama gaisawane suka, tafi guest room inda suke zama suyi zance idan yazo.

"My own, Amma zaka daɗe kafin ka koma ko?"

Imran yace "gaskiya ba wani daɗewa zanyi ba, befi inyi sati uku ba zan koma daga nan kuma se bikinmu zan dawo"

"Wayyo Allah na, anya idan akayi bikin za'a barmin kai kuwa My own? Ina kewarka sosai ƙishirwar ganinka na addabar ruhina idan kayi nesa dani"

"Ihsan, gani nake Tamkar nafiki azabtuwa, bazan iya kwatanta miki halin da nake shiga ba, saboda nesan da muka yi da juna, amma inaga akwai yiwuwar idan anyi bikinmu mu tafi can tare"

Ihsan tace "kasan wani Abu love?"

"A'a sekin faɗa"

"Nifa saura sati biyu in tafi Abuja, zamuje bikin wani ɗan uwan su Mummy, kuma ina kyautata zaton kafin in dawo zaka koma"

Kalar tausayi Imran yayi yace 'yanzu tafiya biki zakiyi ki barni?"

"Jinake kamar in fasa tafiya fa, ina son inta kallonka, in fanshe tsawon lokacin da ban ganka ba, ga kuma Islamiyya ma bana son inyi missing sam, amma idan banje ba, Mummy za tayimin gorin rashin zumunci ne"

Imran yace "karki damu, kije bikinki My love, babban Abinda ke sake burgeni dake shine riƙo da Addininki, yanzu dai ina abunda kika ajiye min?"

"Bari in kawo maka"

Ta shiga cikin gida, tazo ta gabatarwa da Imran Abinci da abun sha, aikuwa yaci sosai sunayi suna hira cike da shauƙi da ƙaunar juna.

Seda ya kammala ta kwashe kwanukan, suka cigaba da hira kamar karsu rabu, tana ta masa shagwaɓa, jiyake inama ace gobene ɗaurin aurensu, ya shammaceta ya riƙo hannayenta biyu cikin nasa, take ta rikice tace

"Dan Allah kabari, bana so kasan ba kyaufa Love, dan Allah ka dena taɓani"
Idonya harya canza, saboda yadda take a tsorace, ya zuba mata idanunsa da suka sake hanata sukuni, ya sumbaci hannayenta yace  "Allah ya mallakamin ke cikin Aminci Ihsan, ina sonki sosai"

Tai ajiyar zuciya tace "naji, amma dan Allah ka bari, kar wani abu na saɓon Allah ya shiga neman aurenmu, kar Auren yaƙi albarka"

Murmushi yayi ya sakar mata hannu yace  "Allah ya ƙara hasken makaranta malamata"

"A'a ɗaliba dai" tai maganar a ɗan sanyaye tana sunkuyar da kai.

Imran yai mata Sallama ya tafi, cike da shauƙi da soyayyar Ihsan.

Da Imran ya tafi seda ya tsaya a masallaci yai sallar magariba, sannan ya ɗau motarsa ya tafi gida.

Yana zuwa ya tarar da ƙannensa duk a falo suna hira, sunata jiran dawowarsa, yana yin sallama suka amsa cike da fara'a da shauƙin ganin ɗan uwansu, suka shiga jera masa sannu da zuwa.

Cike da basarwa yake amsa musu, ya ƙarasa kusa da mahaifinsa ya durƙusa yace "Abba ina wuni"

Abba yai murmushi yace "wato shine daga dawowarka, maimakon ma ka bari inzo in ganka, baka tsaya ba kai ficewarka ko? Ko dai gurin sirikartawa aka tafi ne?"

Kunyace ta kama Imran, ya sunkuyar da kansa, yana sosa ƙeya.

Mummy tace "dan wulaƙanci yaran nan nata jiran ka dawo, sunata ɗokin ganinka, Amma suna maka sannu da zuwa kana amsa musu da ƙyar"

Imran yace "Kai Mummy, nafa amsa musu"

Abba yace "ƙyale wannan Mummyn taka, ya aikin ya kuma hanya?"

"Lafiya ƙalau Daddy, aiki kam an shashi Alhamdilillah"

"Masha Allah, to barka da zuwa".

Nan suka cigaba da hirarsu, cike da ƙaunar juna, da kuma kewar junansu gaba ɗaya.

**************************
Kwanan Amira Biyar a gidan Yaya Fa'iza, a zaton Fa'iza an san Amira tana gidanta.
Amira na jin daɗin zama a gidan Fa'iza, dan ba takura sam, musamman yadda Bashir yake lallaɓata, Bashir bame kuɗi bane, se wadatar da zuci da son kyautatawa iyalinsa, Amira ta ƙudiri anyiar zata koma gida, amma seta tabattar da ta sake ɓata musu rai tukuna.

ya kasance za'ayi bikin wata classmate ɗinsu Fa'iza, tare sukaje ƙunshi da kitso, Amira duk ta biya kuɗin, tace seta bi Fa'iza gidan biki.

Fa'iza ba yadda ta iya da Amira haka suka shirya suka tafi gurin bikin nan tare, suna nan a zaune a gurin taron, Amira ta kushe kwalliyar wannan ta kushe ta waccan, tayiwa wasu ba'a se dariya takewa mutane, se iya shegenta take son ranta, daga tace kalli acucin waccan kamar kwano ko kalli ɗinkin waccan kamar balbela, se tace kalli fuskar waccan kamar tayi gobara, seda Fa'iza taji dama bata zo gurin bikin ba, saboda wulaƙancin Amira, can Fa'iza hankalinta ya ɗauke ta nata gaisawa da ƙawayenta, ana cafkewa ana hirar yaushe gamo.

Amira ta silale ta tafi gurin me DJ ta sameshi tace "Dj naga ba a wani liƙi a gurin nan, ka samun waƙa nasan in dai na taka nayi rawa, dole za'a zuba kuɗi saboda ga abokan ango nan sun fara zuwa, kuma naga wannan 'yan matan duk basu iya rawa ba, se wani tsalle suke suna lanƙwashewa kamar wasu kwaɗi"

Ya buɗe baki yace  "Allah dagaske? To bari mu gwada wace waƙar zan saka miki?"

Amira tace "Aiba kyauta zan maka ba, biyana zakayi"

Dj yace "baki da matsala"

Kawai Fa'iza na ɗaga kanta ta hango mituniyarta ta a tsakiyar filin rawa, cashewa kawai take ba kunya ba komai, Fa'iza ta dafe kai, nan da nan wanda suka santa suka fara kiran sunanta, Gimbiya Amira a kori 'yan gala.

Fa'iza ta rasa abunda yake mata daɗi dan takaici.

seda kowa ya dare ya bawa Amira filin rawar nan, aikuwa kamar yadda ta faɗa abokan ango sun zuba mata kuɗi sosai.

Isowar ango da Amaryane, yasa ta tsahirta aka basu fili Domin su shigo, ta zaga gurin DJ ta karɓi 'yan canjinta tai waje, duk da yadda wasu suka biyota wai suna sonta, babu wanda ta saurara, ta tari me Napep tace  ya kaita gidansu, dan tasan idan ta koma gidan Anty Fa'iza zasu haura, dan ranta ya gama ɓaci sosai.

(Nikam nace ta manta cakwakiyar da ta baro a gidan, kwana biyar bata nan🙄)

Ayshercool
07063065680
[1/3, 5:22 PM] Ayshercool: 🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥






                WUTA A MASAƘA

              
                        



PERFECT WRITERS ASSOCIATION

(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS)

https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P. W. A

*Story and written by*

_*AISHA HUMAIRA
(Daddy's girl)*_

The experience writer of
*ABDUL JALAL*
* WATA KISSAR.... (SAI MATA)
*BAƘIN TABO (Labarin gasa)
*AƘIDATA (Paid Book)
* WUTA A MASAƘA

SADAUKARWA GA ƘUNGIYAR PERFECT WRITERS ASSOCIATION, DOMIN TAYA MURNAR CIKA SHEKARU BIYU DA KAFUWA

https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=in

   

❌❌❌
Ƙirƙirarren labari ne, ban yadda ayi amfani da kowane sashi na labarin ba ba tare da izinina ba.
  




                           Page3







Tana zuwa unguwar su ta sauka, ta biya me napep kuɗi, ta shige gida kanta tsaye, seda ta shiga ma ta fara tunanin tijarar da zata sha yau, kwana biyar bata gida, dakewa tayi kanta tsaye ta shige, da sallama ta shiga abunta lokacin ana ta kiraye Kirayen sallar magariba, ta tarar ba kowa a tsakar gidan se Babarsu Sadiya tana iza wutar girki.

Ta ɗago ta kalli Amira tace 'ke daga ina? Kwana biyar Amira Babu wanda yasan inda kike? Yanzu kinwa kanki adalci kenan?"

Tsaki Amira tayi ta shige ɗakinsu, ta tarar da Sadiya da Amina suna salla, ta ajiye mayafinta taje tayo alwala ta tada salla, bayan ta idar tana lazimi tana jin yadda su Sadiya keyi da ita.

Amina tace  "hmm lalacewa ta ƙaru, likkafa ta cigaba, su O'o yanzu har kwana ake a waje"

Sadiya tace "kwanaki dai, yau kwananta nawa bata gidan nan, ni azo a gayawa Baba gaskiya a raba mana ɗaki da ita, baze yuwu ba, kar muje mu kwashi cuta wallahi"

Banza Amira tayi musu, ta ƙarasa laziminta, tana tunanin abunda zata fuskanta idan Baba ya dawo.

Tana cikin wannan tunanin ne akayi Sallama da Sadiya, saurayinta yazo ta tashi ta fita.

Baba ne yai Sallama ya shigo shida Usman, sun dawo daga masallaci, suna shigowa Maman su Sadiya ta fara kora bayani.

"Baba, se yau Allah yayi wannan mara albarkar ta dawo, kwana biyar cif bata gidan nan, Babu wanda yasan inda take kwata kwata, kaga alamu sun bayyana ƙarara tafi ƙarfin kowa yanzu, Babu alamar nadama a tare da ita balle asa ran tuba"

Baba yace "ni nama rasa abun faɗa akan wannan yarinyar wallahi, har kunyar shiga cikin mutane nake, saboda abunda take aikatawa"

Wata matar ce ta fito daga wani ɗaki tace  "Ai Malam dole a san abunyi, tun bata kwaso mana abun kunya ba, ko ta kwaso wata cutar taje ta gama mana a gida ba"

Maman Sadiya tace "kokuma ta hana yaranmu auruwa ba, tunda gidansu ɗaya kar ace duk halinsu ɗaya"

Saboda tsabar ƙarfin hali irin na Amira, bata nuna tasan da ita suke bama, ta fito abunta zata wuce gurin da ake girki.

Tsawa Usman yai mata yace "Ke! Gidan ubanwa kika tafi tsawon wannan lokacin?"

"Gidan Uban mutum" ta bashi amsa

Amira ta bashi amsar cikin natsuwa.

"Ni kike zagi?' yai maganar yana nunata da yatsa.

"Kai ka ɗaine Mutum a gurin nan? Bana son kalen jaraba fa tom, ban kula kowa ba dan haka a sauraramin"

Baba ne ya kawo wuya, yace  "ke wace irin yarinya ce mara albarka haka? Ke yanzu bakiji kunyar haɗa ido damu ba ma? Kin tafi gantali babu wanda yasan inda kike? Kwana biyar Amira ba wanda yasan inda kike?"

"Wai Baba sekai ta min iƙrarin abun Kunya, haryanzu fa ba cikin shege ba ɗan dakan kuka ba ƙanjamau, ba wanda na ajiye balle aji daɗin nunawa, amma kun isheni, nifa wannan abun da kukemin ne yasa na bar gidan nan naje na sarara na dawo"

Usman ya kai mata duka, yace  "Amina, maza jeki ki rufe min ƙofar gidan nan, yau sena tattaka wannan ƙaramar mara mutuncin, yadda in akace gobe ta kuma fita bazata fita ba"

Be rufe baki ba, Amira ta dafe ƙeya tai waje, aikuwa Usman ya biyo ta, bata zame ko ina ba se inda Sadiya ke zance ita da saurayinta, tana ihu tana "na shiga uku, zasu kasheni, dan Allah yayanmu kasa baki"

Ta tattake daddumar da suke kai, taje bayan saurayin ta tsaya tana cigaba da ihu, miƙewa saurayin Sadiya yayi yana faɗin lafiya kuwa?

Usman ya ƙaraso yana "Wallahi yau zaki gane kurenki, tunda ke rashin mutunci shi kika saka a gaba, zaki yabawa aya zaƙinta"

Cikin marairaicewa da karairaya, Amira ta cewa Saurayin Sadiya "Yaya dan Allah kasa baki, dukana zeyi dan Allah ka hanashi"

Baba ne ya ƙaraso inda suke shima, wanda hakan yai daidai da shigowar Zailani, Zailani yana dubawa yaga Amira yaga su Usman a tsaye cirko cirko kamar zakaru.

Yace "Wannan almirar uwar gantalin ta dawo kenan, shine daga zuwanta zata fara ɗagawa mutane hankali, tun daga waje ake jin ihunta, gidan ubanwa kika tafi?"

Saurayin Sadiya yace "dan Allah kuyi haƙuri, macece kubita a hankali karku daketa, zaku iyayi mata illa kuyi haƙuri dan Allah"

Usman yace "baka san halin wannan sheɗaniyar bane, shiyasa kake kareta"

Sadiya kam gaba ɗaya takaici ya cikata, ta rasa mema zatayi ta huce, kawai tana zaune tana tsinkar furen soyayya, wannan mahaukaciyar ta watsa komai, kuma ta zubar Mata da mutunci a gaban saurayin.

Amira kuwa kan saurayin ta kalla, ya sha uwar zanna bukar ɗinsa, kawai a ranata taga kansa ma ɗan dakon kara, ga dogon wuya kamar raƙumin dawa, ga yadin jikinsa duk ya tashi saboda tsufa, ji tayi kamar ta ƙyaƙyace da dariya, amma ta haɗiye dariyarta, saboda tasan a jazabar da take.

Yace "koma me tayi ina nema mata afuwa dan Allah, ayi haƙuri a ƙyaleta"

Suna can suna maganarsu tai cikin gidan, da sauri ta shige ɗakinsu ta banko ƙofar ta saka sakata.

Suka koma cikin gida, suna tunanin meye mafita akan Amira, dan lamarin nata sam ba sauƙi kullum ƙara taɓarɓarwa lamarunta sukeyi.

Amina taje zata shiga ɗakinsu, amma ta tarara Amira ta garƙame ƙofa da sakata, tai bugun duniya amma Amira taƙi buɗewa, tun tana bugawa harta koma magiya amma Amira tayi burus da ita.

Zailani ne yace "wai bakyaji ne? Bazaki buɗe ƙofar ba?"

Amira daga ciki tace "bazan buɗe ba, yau ni kaɗai zan kwana a ɗakin nan, kowacce ta tafi ɗakin uwarta ta kwana"

Amina tace "Ai naga ba ubankine ya gina gidan ba, danme zaki kulle ƙofa wane irin wulaƙancine wannan, dalla malama ki buɗe mana ƙofa"

"Bazan buɗe ba, kuma wallahi aka cigaba da takuramin a gidan nan, sena gangamo abunda duk zesa a haɗamu a kullemu"

Zailani yace 'anya wannan yarinyar ƙwaƙwalwarta bata fara samun matsala ba kuwa?"

Maman Amina tace "zunzurutun iya shege ne, ba wani taɓin ƙwaƙwalwa"

Amina kam tasan tunda Amira ta furta baza su kwana a ɗakin ba tasan bazasu kwanan ba, ba yadda ba'ayi ba Amira tace bazata buɗe ba.

Can Amina ta gama zancenta, ta dawo gida tana masifa  "Wallahi idan Amira ta kuma shiga sabgata, sedai ayi mutuwar kasako, koni ko ita wallahi, wanne wane irin rashin mutunci ne? Tazo har kan sallayar da nake zance tana kurma ihu, ta nemi ta tattake mana ƙafafuwa, sauran ƙiris ta take masa cinya, gaba ɗaya ta zubarmin da mutunci yau, ji nayi kamar ƙasa ta tsage in shige wallahi"

Amira ta leƙo ta window tace "to maƙaryaciya, ɗuwawunsa na kusa takewa ba cinya, wani abu a tsomale kamar an jiƙa tsimma, zakizo ki ishi mutane yan yen yen, Wallahi in dai baza'a dena min cin kashi a gidan nan ba, kunya yanzu kuka fara jinta"

Sadiya tace "to dan ubanki ke ina naki tsomalallen? Waye yake zuwa gurinki banda 'yan iska irinki?"

"To ai da sauƙi, tunda dai ana zuwa ɗin, ina zaune zaki sha mamakin wanda ze Auri Amira, ƙasaitaccen mutum dan ni me tsadace"

"A gidan ubanwa wani me tsada ze kwasheki? Kara da kiyashi, ya kwashi cuta?"

Bata kulata ba, ta  jefowa Amina wayarta ta window tace "ke kuma ga wayarki nan, wannan matsiyacin saurayin naki Na'ibi yake ko liman ya ishi mutane da kira, be iya komai ba bashi da ko sisi se kiran wayar tsiya, ƙazami me yawo da silifas"

Maman Sadiya ce da suke cewa Ummma tace "dan Allah ku ƙyaleta, idan ba hakaba a banza ranku ze cigaba da ɓaci, bazata canza hali ba"

Sadiya tace "malama ni buɗe ƙofa zan canza kaya"

Amina tace "tun wuri ki nemi nayi, dan tace bazata buɗe ƙofar nan ba"

"Saboda me bazata buɗe ba"

Tace "kowa sedai ta kwana a ɗakin uwarta, yau ita kaɗai zata kwana a ɗakin"

"Saboda ɗakin na ubanta ne? Wallahi seta buɗe"

Sadiya taje ta shiga jijjiga ƙofar, tana wani irin mahaukacin bugu, da gudu Baba ya fito daga ɗaki yace  "Au Halima, kema biye mata zakiyi kuyi? Shikenan maza biye mata ku taru ku haukatani, koku ɗoramin wani ciwon daze ajali na"

Amira tace "ko ciwo be kamaka ba zaka mutu, dama gashi ka tsufa, ai da ka ƙyaleta, wallahi naso ta jijjige ƙofar ɗakin nan yau, dama ga damuna ta kusa, nikuma in jijjige tagar kowama ya huta, in damuna tazo kowa yaji jiki"

Suna ji suna gani haka suka yiwa Amira Allah ya isa, suka tafi ɗayan ɗakin cikin ƙanensu, wanda harda masu fitsarin kwance a cikin yaran, haka suka shiga suka kwanta, dan Amira bazata taɓa buɗe ƙofar ba kome zasu yi, dan idan ta furta zatayi abu se tayi, sedai ai mata duk abunda aka ga dama.

Sadiya tai ƙwafa tace "ai dai bazata dawwama a ɗakin ba, wallahi gobe in Allah ya kaimu sena mata dukan tsiya kona samu in huce, yau bala'in nata kusan a kaina ya sauka, gara mu daku a kece raini dan uwatta"

Amina tace "kedai bari, wallahi ina da abubuwan yi da yawa a ɗakin nan, amma saboda hatsabibanci tai mana wannan iskancin, wallahi karki saurara mata ki mata shegen duka, zan tayaki , dan ni kaina yau na gama ƙulewa, tafa fasamin waya jefomin ɗin da tayi"

"Kema seki fasa mata baki ki huce, naga gidan nan kamar tsoronta akeji, zamu koya mata hankali"

Ɗakunan iyayensu duk da ƙannensu, ga kakarsu bata nan balle su kwana a ɗakinta, haka suka kwanta cikin yara, shimfiɗar banda zarnin fitsari ba abun take, ƙarshe a ƙasa suka kwana, Sadiya nata tsinewa Amira tana mata Allah ya isa.

Da Asubar fari, Kafin kowa ya tashi, Amira ta tashi, taje tai alwala ta ɗau sallaya tai waje, ta bar gidan,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login