Showing 18001 words to 21000 words out of 120332 words

Chapter 7 - WUTA A MASA?A COMPLETE HAUSA NOVEL BY AYSHERCOOL

10 Mar 2025

30378

Please

Follow me on watpad@Ayshercool7724
What's app@07063065680

[1/7, 7:03 PM] Ayshercool: .🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥

WUTA A MASAƘA

PERFECT WRITERS ASSOCIATION

(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS)

https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P. W. A

*Story and written by*
AISHA ADAM (AYSHERCOOL)

The experience writer of
*ABDUL JALAL*
* WATA KISSAR.... (SAI MATA)
*BAƘIN TABO (Labarin gasa)
*AƘIDATA (Paid Book)
* WUTA A MASAƘA

SADAUKARWA GA ƘUNGIYAR PERFECT WRITERS ASSOCIATION, DOMIN TAYA MURNAR CIKA SHEKARU BIYU DA KAFUWA

https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=in

❌❌❌
Ƙirƙirarren labari ne, ban yadda ayi amfani da kowane sashi na labarin ba ba tare da izinina ba.


*Innalillahi wa innalillahi raji'un, ina me amfani da wannan dama, wajan miƙa ta'aziyya ga ɗaukacin al'umar musulmi akan rashin da mukayi na Shehin _malami, Dr. Ahmad banba B.U.K ina fatan Ubangiji Allah yayi masa rahama yasa ya huta, in tamu tazo yasa mu cika da imani*_






Afuwan banyi Editing ba

                               

                              6_7





A gigice Abba ya farka daga baccin da yake cikin tashin hankali, mafarki yake da mahaifiyar Amira, ta riƙe rigarsa tana kuka akan ya temaka kar 'yarta ta lalace.

Ya dafe kansa yai shiru yana tunani, can ya miƙe yaje ya ɗakko wayarsa, ya nemo lambar Imran ya kirashi, sedai wayar taƙi shiga sam.

Ya duba lambar Ammi ya kirata, a ɗan firgice ta farka daga baccin, jin wayarta tana vibrating, ta duba screen ɗin wayar ta kalli agogo, dare yayi sosai ta ɗaga wayar tace "Hello, Abba lafiya kake kira a wannan daren haka?"

Abba yai ajiyar zuciya yace "ina Imran yake?"

Cikin Rashin fahimta tace  "Imran kuma? Me Imran ze maka a wannan daren?"

"Ya kike tambayata ne? Yana nan ko baya nan?"

"Ai Imran tun safe ya koma Maiduguri, an masa kiran gaggawa"

"Yasalam"

"Amma Abba lafiya, nifa ka tayarmin da hankali"

Abba yace "Bari kawai, mafarki nayi da Zahra'u"

"Wace ce kuma Zahra'u?"

Abba  yace "'yar uwata mana, nai mafarki da ita tana kuka, tana in kula mata da 'yarta karta lalace, na tsorata ƙwarai ina ga tunda Imran baya nan, ni zan dawo gari zanje inga meya kamata inyi akan yarinyar nan"

Ji tayi kamar ta zagi Abba dan takaici, a hasale tace "yanzun Dan Allah akam wannan abun ka nemi ka tayarmin da hankali, a wannan uban daren ina bacci? Mafarki ne fa kayi ba gaske ba, kawai ka ɗagamin hankali ka hanani bacci"

"Kinga ba kowane mafarki ne kawai ba, wannan mafarkin da nayi ba kawai bane, an nusar dani kuskure na ne ta mafarki, wanda yakamata in gyara tabbas"

"To yanzu me kake nufi?"

"Duk yadda ake ciki gobe in Allah ya kaimu zan dawo, zuwa jibi insha Allah zanje inga yarinyar nan da kaina, something is not wrong, seda Safe kawai"

Ya kashe wayarsa ya ajiye, ƙirjinsa na cigaba da bugawa da sauri da sauri, Ammi kuwa tsaki tayi, ta jefa wayar bayanta, tace  "Aikin banza, kawai ze ɗagamin hankali akan wata banzar yarinya, sekace nina saka ta yawon banzan"

Tai tsaki ta juya ta cigaba da baccinta, tana takaicin Yadda Abba ya tashe ta ya ɗaga mata hankali a wannan Uban daren.

Ana idar da salar Asuba, Amira ta ƙarasa tattare duk abunda take buƙata tai waje, su Sadiya na kallonta amma ba wanda ya iya ce mata wsni abu, dan yadda tske cika tans batsewar nan, duk wanda ya tanka mata zata iya sauke masa rashin mutunci.
Haka ta fita zuwa Office ɗinsu na rawa, ta tarar dasu Sultan sun shirya tsaf, ana jiran mutum biyu, seda suka karya wajen ƙarfe goma sannan suka tafi airport.
Sultan yana kula da yadda Amiran bata walwala sam, yaso yai mata magana amma ya fasa, saboda wani lokacin halin Amira se a hankali, tana da sauƙin kai, amma bata fiye son a shiga lamuranta ba.

Se ƙarfe biyu Sannan suka ɗaga, Amira na Jin yadda jirgin ya tashi, maimakon hakan ya sanya Amira cikin farinciki kasancewar karonta na farko kenan da ta hau jirgi, sema wani baƙinciki da ya addabi zuciyarta data rasa na menene, kawai ta jingina ta lumshe idonta, hawaye na zuba daga idonta.

"Gimbiya Amira yau an hau jirgi, ba saban ba, za'a ƙaro wulaƙancine" Sultan yai maganar yana murmushi, sedai ganin Amiran na hawaye yasa jikinsa yin sanyi.

Cikin damuwa yace "Amira lafiya kuwa? Kukan me kike haka?"

Girgiza masa kai tayi alamar bakomai.

"Amma Bakomai kike kuka haka? Karki sa hankalin mutane ya dawo kanki fa"

Ta goge hawayen ta tace "karka damu, bakomai"

Haka Sultan ya ƙyaleta, amma Amira ta kasa tsaida hawayen dake bin fuskarta.

*****************************

"Amma Alhaji Ali baka ganin tafiyatka a yau zata iya kawo matsala, kana cikin kwamitin da shugaban ƙasa ya kafa, kuma kusan kaike jagorantar kwamitin nan, be kamata ka bar garin nan yau ba"

"Dole in bar garin nan yau ɗin nan, ina da damuwa ne, kano nake son zuwa gobe in Allah ya kaimu"

"Amma wace irin damuwa ce da bazaka iya haƙuri a gama ganawar ba sannan ka tafi?"

"Hashim, bazaka gane ba sam, nasan abunda zan gayawa Excellency, Amma ƙarfe uku zanbi jirgi in koma"

Hashim yace "shikenan, Allah ya kyauta koma menene"

Alhaji Ali ya amsa da "Ameen"

Yadikko ta fito tsakar gida tana cewa "ina wannan yarinyar take ne, ta kassaramin waya wayata taƙi tashi, ta fito ta bada kuɗi a kaimin ita gurin gyara"

Amina tace  "wai wace yarinyar kike nufi?"

"Amira Mana"

Amina tace "to bayan idar da sallar Asuba ta fita"

"Ta fita taje ina?"

Sadiya tace "wa take gayawa inda zata? Gantalinta ta fita, yau hadda jaka ta haɗa ta tafi"

Yadikko tace "jaka gidan ubanwa taje? To ko ina taje ina nan zatazo ta sameni, wallahi seta biyani wayata"

Yadikko ta cigaba da sababinta, tana se Amira ta biyata wayarta data fasa mata.

Alhaji Ali daga airport be tsaya ko ina ba, se gidansa sedai sam Ammi bata wani nuna murna da dawowarsa ba kamar yadda take a baya ba idan yaje wani guri ya dawo ba, dan ya fara bata haushi akan yawan zancen Amira da yake kwanan nan.

Tunda ta masa sannu da zuwa, ta bashi Abinci bata bashi chance, ko fuskar da zasu tattauna maganar Amira ba.

Minal ce ta shigo falonsa tana faɗin "Abba, ya kuma ka dawo gida yau, base jibi in Allah ya kaimu zaka dawo ba?"

Abba yace "na dawone saboda batun 'yar uwarku"

Minal tace "wace 'yar uwa tamu? Anty Khadija?"

"A'a, 'yar uwaku dake Kano, Amira"

Ammi tace  "Dan Allah ka dena haɗamin yara da wannan yarinyar, ni yarana nutsatstsune"

"Koma dai menene, ni 'yata ce kuma dole in damu akanta"

Ammi tace  "eh kai ta zamewa dole ba yarana ba, ka dena haɗata dasu"

Abba yai shiru yana tunani, sam Ammi bata masa kara a kan 'ysn uwansa, Magana in dai bana 'yan uwanta ba, sam bata son taga yana morawa wani nasa komai, be kuma  cewa komai ba ya tashi ya shiga bedroom ɗinsa, ji yake kamar ya tafi Kano a lokacin, sedai Yamma ta riga tayi, ba damar yin hakan lokaci ya ƙure sosai.

Amira kuwa tuni suka sauka a babban birnin tarayya, Sultan yai musu jagora zuwa Hotel ɗin da aka kama musu, Amira ɗakinta ita kaɗaice, Babban ɗakine sosai dan yafi nasu Sultan girma da kyau, hatta Abincin da zasu ci ayi bikin a gsma, seda aka biya musu, Sedai gaba ɗaya Amira a damuwa take, kawai dai gata nan ne dai, ji take kamar ko rawar ma bazata iya ba ranar bikin

Washegari da wuri Alhaji Ali ya shirya ya tafi Kano, be tsaya ko ina a ba se ƙofar gidan kakanin Amira, da shida jami'an tsaron dake masa Rakiya, a wasu rantsatsun motoci na Alfarma, wanda seda aka mutane suka fara tunanin waye wannan ya kawo musu ziyara haka layinsu.

Yai Sallama ya shiga gidan, a ƙofar ɓangarensu Yadikko ya tsaya yana Sallama, Baba ne da kansa ya fito dayake daf yake daya fita, yayi mamakin ganin Abba, dan rabonsa da gidan nan a ƙalla ya shekara shida, tun kafin a masa muƙami a gwamnatin tarayya.

Baba ya washe baki yace "Alhaji Ali kaine ke tafe da kanka haka? Masha Allah yau mun karɓi babban baƙo Bismillah shigo"

Alhaji Ali ya shiga yana faɗin "Ayi haƙuri munyo sammako haka ba sanarwa"

Baba yace "haba dai bakomai, sha ɗaya na Safe ai ba sammako bane, sannu da zuwa Yallaɓai"

Kana kallon Alhaji Ali zaka san shine mahaifin Imran, saboda suna kama sosai.

Aka masa iso har ɗakin Baba, nan Yadikko ta shiga rawar kai tana washe baki tana  "Sannu da zuwa, Sannu da zuwa Alhaji Ali, ya hanya sannunka da zuwa Sannu Sannu, kai Zailani zokaje ka siyo masa ruwan roba, manya basa shan irin ruwan da muke sha"

Abba yace  "A'a bakomai, na taho da ruwana a mota, nagode sosai"

Suka shiga gaisawa da yaushe gamo, can Abba yace "nifa banga 'yata ba, nazo ne in gani inda yuwuwar in tafi da ita, saboda labarai marasa daɗi da naji a game da ita, sam abun be min daɗi ba, na turo Imran yazo shima, sedai feedback ɗin dana samu daga gareshi sam banji daɗinsa ba, abun ya tsayemin shiyasa na ajiye ayyukana na taho kawai"

Baba yace "to Amira dai iya ƙoƙari munyi a kanta, ɓangaren kulawa da ita, cinta shanta suturarata da kuma makaranta, munyi iya ƙoƙarin mu bata tarbiyya nagartacciya kamar wadda muke bawa duk wani ɗa dake gidan nan, Amma Amira taƙi, hankalinta na kan wani abu daban"

Yadikko ta ɗora da cewa  'Sam Amira bata jin magana, ga fitsara da rashin Kunya, taurin kai ga neman magana, ga rashin ta ido da gantali na tsiya a cikinta, ranar da yaron wajen ka yazo nan ma, ba kaga yadda suka fafata ba, seda ta masa rashin Kunya ya bubbigeta, bayan tafiyarsa a garin yawonta ta kwaso juna biyu, ta sha magani ta zubar ya dinga wahalar da Ita, seda muka kaita Asibiti, idan ta bar gidan nan se tayi kwanaki fiye da goma Babu wanda yasan inda take, samari kuwa babu kalar wanda basa zuwa gurinta, lamarin nata dai ba arziki a cikinsa sam"

Alhaji Ali ya dafe kansa cikin damuwa yace  "yanzu ina Amiran take ne?"

"Eh to, yaron gurinka ya kira waya aka gaya masa ga abunda tayi, yace ze kaita makarantar kangararru, tun jiya da farar Safiya ta bar gidan nan ba wanda yasan ina ta tafi"

Abba yai shiru na wasu 'yan daƙiƙu, yana tunani gami da nazari akan yadda ze ɓullowa lamarin, can yace  "Shikenan, yanzu dai duk yadda ake ciki dan Allah idan ta fawo, a kirani a waya a sanarmin, zanga abunda zanyi idan ta kama mu koma can Kaduna da ita shikenan, semu tafi ta koma can a nema mata makaranta"

Baba yace "ai ta gama sakandare bana"

Abba yace "eh high institution nake nufi"

Yadikko tace  "amma bazamu so ka ɗauke mana ita ba, dukda rashin jinta bazamu so ka rabamu da ita ba, muma muna ƙaunarta"

Abba yace "sedai yadda ta yuwun kawai"

Ya miƙe da nufin ya tafi, Yadikko tace "to Yallaɓai sedai Amiran ta lalata min sabuwar wayata, idan ta dawo ban san dame zan kiraka in sanar maka ba"

Abba yace "ai wannan ba Abun damuwa baane"

Yasa hannu a aljihunsa ya ɗakko kuɗi ya ajiye mata yace "gashi nan, ki sai wata wayar sauran kici goro"

Ta amshe tana washe baki tana dariya, suka fito tsakar gida, Su Sadiya suna gaisheshi, suma duk yabi ya basu kuɗi.

Yadikko ta kuma karkacewa tace  "ai Yallaɓai wannan sune 'yan uwan nata, ba wadda ba tayi saukar alƙur'ani a cikin su ba, wallahi nutsatstsune gasu nan, baka ga yadda ake yaba tarbiyyar su a unguwa ba"

Abba yace "Masha Allah, Allah ya ƙara tsare mana su gaba ɗaya"

Yadikko ta sosa kai tace  "Ai naga shima yaron gurin naka ya girma sosai, masha Allah gashi nutsatstse ne"

Abba yace "Au Imran, ai shi yanzu haka sojane"

Yadikko tace "Soja marmari daga nesa, masha Allah, to Yallaɓai meze hana a ƙara ƙulla alaƙa da danƙon zumunci, a yaran nan yazo ya nemi ɗaya daga cikinsu ko Sadiya ko Amina?"

Abba yai mutm yace  "Allah sarki, ai Imran ya kusa Aure, befi sati biyu ya rage bikinsa ba, za'a aiko muku da katin gayyatar ku har gida"

Seda Yadikko ta canza fuska, amma ta maze tace  "Ahhh Alhamdilillah, kace mun kusa zuwa Kaduna garin gwamna, to Allah ya kaimu lokacin lafiya"

Haka suka raka Abba har gaban motacinsu, ya shiga sukayi Sallama ya tafi, Yadikko ta koma gida tana mita, "yo ni tunda an kusa auren ɗansa base ko shi ya auri wata daga yaran nan ba, muma mu dangwali arziki amma shikenan daga ƙwauri se gwiwa, har yana batun ya ɗauke wannan watsatsiyar wato taje ta huta, mu mu zauna a wahala, daga nan ma a rufa ta samu wani hamshaƙin ya aureta, to wallahi baze yuwu ba, baze yuwu ta bar gidan nan ba, gara mucigaba da zama, taita gurza Rashin mutumcin, mu zauna a wahalar tare.

Umma tace "Yadikko naso mutumin nan ya amsa ɗansa ya auri ɗaya daga yaran nan, ai da mun rage zafi da sun fita zakka, duk 'yan matan gidan nan ba wadda ta taɓa auren wani me ɗan abun hannu, duk se talakawa"

Yadikko tace  "waccan makirar Fa'iza, ba yadda ba'ayi da ita ba ta auri Alhaji Yahaya amma taƙi fafur, da ko ba komai ko umarar nan naje, da an rage wasu wahal halun, shiyasa nakeson ko Sadiya ko Amina wata ta samu me ɗan maiƙo"

Umma tace "to Ubangiji Allah yasa a samu ɗin"

"Bari kawai, ai idan suka kawo katin bikin nan, dole ne mu tafi gaba ɗaya harsu ɗin, idan yaso ko a cikin manyan mutanen fa zasuje a samu su samo miji nagari, ba wannan samarin da suke binsu ba, basu ajiye komai ba basu bawa wani ajiya ba, banda ƙaddara aisu Sadiya kalar manyane"

Nan kansu ya dinga kumbura, Sadiya ta fara raya abubuwa a ranta, fan harga Allah Imran yayi mata musamman zuwan nan da yayi, ya burgeta sosai.

Amira na kwance a ɗakinta na Hotel, tayi shiru tana tunani, taji ana knocking, tashi tayi taje ta buɗe ƙofar, Sultan ne tare da wani mutum, bata ce komai ba ta saki ƙofar suka shigo, a nan falo suka zauna, ita ma ta nemi guri ta zauna a wata kujerar.

Mutumin ya kalleta yace  "gimbiyarmu, fatan kinzo lafiya?"

"Ƙalau" ta bashi amsa a taƙaice.

Ya ɗan gyara zama yace  "A gaskiya naji daɗin amsawa da kikayi, har kika baro Kano kika taho Abuja halartar taron bikina, naji daɗi sosai nayi farinciki"

Se yanzu Amira ta gane ashe shine wanda ya gayyacesu bikin, oho ita bata san waye bama, ita dai babban abunda yasa ta ƙarfafa ta taho garin Abuja shine tazo a huta, ta rage baƙin cikin dake damun ta a zuciya.

Ta dubi mutumin tai murmushi tace "Naga saƙonka an bani waya, harna fara amfani da ita, nagode sosai kuma insha Allah zamuyi iya ƙoƙarin mu mu nishaɗantar a gurin nan, Allah ya sanya Alkhairi ya baku zaman lafiya"

Yace "Ameen ya Allah gimbiyarmu, ko zaki iya bani lambar wayarki?"

Amira ta girgiza kai tace "No need, duk abunda kake buƙata ka gayawa Sultan ya gayamin"

Ya jinjina kai yace  "Shikenan yadda kike so haka za'ayi, sedai zan gayamiki garin Abuja garine na samun kuɗi sosai, performance ɗinki ze janyo miki mutane sosai, dan haka ki dage ki ƙara shiri"

Amira tai murmushi tace "bana buƙatar wani shiri, wanda nazo dashi ya isheni".

"I like your confidence dear, Akwai manyan mawaƙa daga kudancin Nigeria suma zasu halarci taron bikin, amma gaba ɗaya nafi farinciki da zuwanki akan kowa gurin nan, nasan ba zaki bani kunya ba"

Amira tace "Allah yasa"

"Kamar yaya Allah yasa?"

Sultan yace "Ai zuwanta garin Abuja bashi ne ba, kayi addu'a taje gurin taron, dan wannan gimbiyar, gimbiyarce ta gaske, komai nata ganin dama ne"

Mutumin yace  "Ahh tofa kace aiki be ƙare ba, dan Allah gimbiyarmu ki halarci bikin nan Please, kece gishirin bikin nan Please"

Murmushi tayi seda haƙoranta suka Bayyana, tace  "idan har ina raye kasa a ranka naje taron bikinka, dan bana karya alƙawari"

Ba laifi sun sha hira sosai, Sannan mutumin nan ya tafi.

Abba kuwa shiru shiru, ya dinga sauraren kira yaji ance Amira ta dawo, amma shiru gashi haryanzu yana yawan mafarki da Ƙanwarsa, akan ya kula da 'yarta karta lalace, abun se damunsa yake ya rasa inda zesa ransa, gashi ta kasa ta tsare akan lallai ita baza'a kawo mata Amira gidanta ta zauna ba, shi dai Abba bece komai ba ya cigaba da yiwa iyayen Amira addu'a, da fatan duk inda take Allah ya karkato hankalinta ta koma gida, dan yana nadama akan rashin tallafar rayuwar Amira, dukda a yadda ya gani dangin mahaifinta sunyi ƙoƙarinsu akan taribiyyarta amma ta lalace, ƙila suna takurawa ne gurin tarbiyyar shiyasa ta kangare musu.

Rana bata ƙarya sedai uwar ɗiya taji kunya, hall ya kai hall, ƙaton hall ne wanda yaji kayan ado sosai, ba ƙarya ma halarta taron 'yan hutu ne, ankon dake jikin 'yan matan dana iyaye ze tabattar maka da masu kuɗi ne, gashi da yawansu farare ne tas kamar basa shiga rana.

Tuni manyan mawaƙa suka fara baje kolin baiwar murya da Allah subhanahu wata'ala yai musu, Ango da amarya tuni suka iso, tun a hanya yake kiran waya yaji idan su Amira sunje, amma aka sanar masa basuje ba.

Ango da Amarya na zuwa gurin taron, hall ya ƙara yamutsewa, da ɗaukar hotuna da shagulgula kala kala.

Da mota akaje aka ɗakko su Amira, harabar gurin kawai abun kalloce, Amira ta tsaya tana ƙarewa harabar gurin kallo, doguwar rigar abayace a jikin Amira, ta yafa mayafin a kanta, sannan ta saka face mask ba a iya gane fuskarta, suka sakko daga motar, har zasu shiga gurin wayar Amira ta fara ringing, tace su shiga zata biyo bayan su.

Ta ɗaga wayar ta saka a kunnenta
"Hello Amira, ina kika shiga ne, naje gida yau ance bakya nan, gashi Abban  Kaduna yanata kiran waya yana tambayar kin dawo?"

Amira tace  "meye nasa na inda na tafi? Meye damuwarsa bayan ɗansa daya tura shine kuma ya wanke ƙafa yaje da kansa?"

"Amira Yanzu dai kina ina ne? Nazo gida ance kwananki huɗu bakya nan, ina zuwa akace an san ina da lambar ki, in kira inji kina ina?"

Amira tace "somewhere in the world"

"Wane Irin somewhere in the world? Amira kina ina?"

"Anty Fa'iza kin dameni fa, ina ruwan wani da inda na tafi naje in huta ne"

"Malama ɗan matsa kinzo kin cikewa mutane hanya" wata siririyar murya ce tai maganar, Amira ta ɗago ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login