Showing 54001 words to 57000 words out of 120332 words

Chapter 19 - WUTA A MASA?A COMPLETE HAUSA NOVEL BY AYSHERCOOL

10 Mar 2025

30360

an ƙyaleni na tafi gida, in yaso daga baya na dawo"

"Zama da mune bakya so kenan ko?"

Tai saurin girgiza kai tace "A'a wallahi, ina da kaya a gida da nake buƙata"

"Karki damu, duk abunda kike buƙata kiyi Magana"

Amira bata amsa ba tace  "bari in tayaku aikin"

Fadila tace "A'a, kar Anty ta fito tace an samata ke aiki"

Amira tai murmushi tace "ba abunda za tace, ta karɓi ferayr dankali a hannun Fadila"

Wayarta ce ta fara ringing, wayar da se yau ta kunnata tunda aka kawota gidan, tana son ta kira su Anty Fa'iza amma taga yayi Safiya da yawa ta fasa.

Ta ɗaga tace "Hello My blood"

"Gimbiya kina lafiya kuwa?"

Amira ta murmusa tace "lafiyata ƙalau Sultan, ya kake ya aiki?"

"Amira wai da gaske An miki Aure?"

"Eh Sultan, an min Aure"

"Amira wane irin Aurene haka ba shiri ba labari? Dagaske kuma wannan da yazo ya tafi dake ɗin shiya Aureki?"

"Eh Sultan shine, ɗan uwana ne"

"Anya Amira an miki adalci kuwa? Wallahi ina tsoron mutumin nan karya dinga cutar dake, sam bashi da tausayi wallahi shaƙar da yaimin lokacin da yazo Office ɗin ji nai kamar na mutu wallahi"

Ƙwallace ta taru a idon Amira, Sultan ya damu da ita sosai, ta kalli tabon dukan dake jikinta, ta haɗiye kukan dake shirin ƙwace mata tace  "Karka wani damu, babu wata matsala lafiya zamu zauna dashi insha Allah"

"Anya Amira, kina ganin babu Matsala?"

"Babu wata matsala malam, Baza'a zaɓamin abunda ze cutar dani ba, ya labari harka tana garawa kokuwa?"

Sultan yace "ina wata harka babu ke, nifa tunda ya tafi dake ban sake samun nustuwar zuwa gurin wani sha'ani ba, harga Allah bana baƙinciki da Aurenki Amira, hasali ma ina murna kin samu miji kinyi Aure, sedai naso ace kin samu miji nagari me sonki sosai, bana son ki sake wahala a rayuwarki"

"Allah sarki ɗan uwana rabin jikina, bani da wata alaƙa ta jini da kai, sedai ka damu dani sosai Sultan, karkaji komai Zan zauna lafiya da Imran insha Allah"

"Shikenan Amira, Ina miki fatan Alkhairi, Allah ya baku zaman lafiya, Amira banda rashin ji da taurin kai kinji, kiyi haƙuri kiyi masa biyayya, Allah ya baku haƙurin zama da juna"

Duk da hawaye ya cika idon Amira, amma ta ƙaƙaro murmusa tace "Nagode sosai Sulty guy, karka damu zan zauna lafiya da mijina insha Allah, take care of yourself kaji"

"Rufan Asiri kar mijinki yaji kina faɗin haka, yasa azo a casani se anjima"

Amira ta kashe wayar tana murmushi, Fadila tace "Amira wannan kuma waye? Hala saurayinki ne?"

"Ba saurayi na bane, kuma ba ɗan uwana bane, kawai Allah ne ya haɗani dashi, abokin kasuwanci na ne, yana jin tausayina ne sosai, ya sha shiga riski saboda ni, bazan manta da Sultan ba"

"To Amma dai kiyi a hankali, kar Mijinki yaji kina waya dashi ya zaci wani abune a tsakaninku"

Amira tai murmushi tace  "Ya daɗe be zata ba, ai yasan wadda aka aura masa, dan haka meye na zargi ko wani tunani"

Fadila tace "Amira, Aure fa ba abun wasa bane ba, rayuwar da kikayi a baya daban, wadda kika shiga daban, karki kuskura ki ɓatawa kanki suna a sameki da wani mummunan aiki da Aurenki, dan Allah ki kiyaye"

Amira tai murmushi me cike da ma'anoni daban daban tace  "to insha Allah zan kiyaye"

"Yawwa ko ke fa"

Ba Anty ba hatta Alhaji Hashim yaji daɗin yadda Amira ta fara sakewa, ba kamar da yadda ta takure kanta ba.

Yadikko kuwa baƙin cikin duniya yabi ya ishe ta, wai Amira tayi Aure, duk da yawon ta zubar ɗin da tayi amma ta samu danƙareren miji kamar Imran ta aura, da fari cewa tayi su Baffa Salahu su kai ƙarar Abba, wai akan ya Aurar da Amira, ba da izininsu ba alhalin suke da hakkin Aurar da ita tunda mahaifinta baya raye, dangin uba suke da maganar Aure bana Uwa ba.

Usman ne ya ankarar da ita yace "Yadikko, ki rufawa kanki Asiri tun wuri, Allah kaɗai yasan meya tsara tunda akayi Auren nan faka faka haka, kuma idan kika sa suka kai ƙarar me kikeso ayi? Na farko dai Aure ya ɗauru tunda ya cika dukkan sharuɗan da addini yazo dasu, sedai ace anyi ba daidai ba daya aurar da ita, na biyu Kuma kin san dai ba raba Auren nan za'ayi ba, ga uwa uba shi wanda ya aurar da ita ɗin wani ne a sama, baki da kuɗin da zakija dasu, kawai kiyi haƙuri ki koma gefe kiyiwa su Amina Addu'a suma Allah ya basu maza nagari wanda yafi na wanda Amira ta samu"

Yadikko tai ajiyar zuciya tace 'ni babban abun takaicin, yadda suka dinga sintiri a gidan nan shida ɗansa, amma aka rasa wanda ze buɗe baki yace mana ga abunda ake shiryawa, da kunturun makirci, suka auri karuwa suka bar na ƙwarai"

"To ke meye naki a ciki, suje su ƙarata an rage mana Matsala ma"

"Wane rage matsala, ni ba gara ace tana gidan nan a cigaba da matsalar ba, su Sadiya su Auri yaron ba"

"To koma dai yane, Yanzu jabbal ƙalam, tunda an riga an Aureta se haƙuri"

Haka Yadikko ta kasa ɓoye bƙin cikinta da Auren Amira, Sosai take nuna tana adawa da Auren, yayinda labarin Auren Amira ya cika gari, kiwa ya dinga mamakin irin yadda Amira tai Aure lokaci ɗaya haka, duk da irin tarin fitinarta da rashin jinta.

Tafi tafi rayuwa na cigaba da tafiya, Imran sam ya dena shiga sabgar Ihsan, yai watsi da ita ya dena nuna yasan da zamanta a gidan, wataran da sassafe kafin ta tashi ya fice, baze dawo ba se dare, ya ajiyemata duk wani abun buƙata, amma fa ba ruwansa da ita.

Ranar wata laraba da Safe, Ihsan ta tashi daga bacci ta fito falo taga takadda akan Centre table na falonta, ta ɗauka ta duba taga Imran ne ya ajiye mata saƙo  "Na koma gurin aiki, in kina buƙatar wani abu na bar kuɗi a wardrobe ɗina"

Gaban Ihsan ne ya faɗi, tai shiru tana tunani To yanzu idan gurin Amira ya tafi fa? Take taji wani gumi yana tsatstsafo mata, jiki na rawa taje ta ɗakko wayarta ta kira shi, sedai be ɗaga ba, se a yanzu take tunanin wautar da tayi na share Imran, hakan ze iya bashi damar tafiya gurin Amira.

Tana nan tana wannan zulumin taji ana buga gate, ta saka hijjabi taje ta buɗe ƙofar, tana buɗewa taga Ammi ce da Minal suka zo.

Murmushi tayi tare da yi musu sannu da zuwa, ta jagorancesu zuwa falonta.

"Ammi sannunku da zuwa, da kun kirani na ɗora muku wani abun ai"

Ammi tace  "A'a sauri mukeyi, nace mu biyo inzo in dubaku zamu wuce ta wajen gidan nan nace bari in leƙoku, ina Imran ɗin?"

"Ammi ai ya koma aiki yau".

"Kamar ya ya koma aiki yau? Amma ya akayi be gayamin ba? Hutun nashi ya ƙare ne?"

Ihsam tace "kiran gaggawa akayi masa shiyasa ya tafi be miki sallama ba"

Ammi tace  "shikenan, na biyo ne dama inga komai lafiya kafin inyi zuwa na musamman, sannan ki kula ki kwantar da hankalinki, waccan Yarinyar da ita da babu duk ɗaya, karma ki a ranki kina da kishiya, ki sake kiyi rayuwarki a gidan mijinki, na yiwa Imran kashedi sosai akan Yarinyar nan, jira nake ta tare inga ta inda zan ɓullowa lamarin in kashe Auren ba tare da mahaifinsa ya zargi wani abuba, karki kuksakura ki bata damar da zata ga kafar da zatai masa shishshsigi, kin san karuwai a waje ma ƙwacen miji suke balle tana matarsa, duk ds na lura shima ba shi da interest akanta, mahaifinsa ne duk ya haɗa wannan kwamacalar, shiya tursasashi ya Aureta, shikuma ya amince ba tare da ya nuna baya so ba, kowane ɗa yafi son uwarsa amma shi kam, yafi son ubansa a kaina"

Ihsan ji tayi kamar Ammi tai mata allura, tabbas idan tai wasa hankalin Imran ze iya karkata kan Amira, Dan haka dole tayi wani abu a kai, ashe dagaske dai takura masa akayi ya Auri Amira ba dan yana sonta ba.

A gurguje Ammi tayi sallama ds Ihsan suka tafi, tunda suka tafi abun duniya ya ishi Ihsan, ta ɗau waya ta kira Imran kusan 5missed calls anma yaƙi ɗagawa sam.

Baƙin da ta dingayi ne suka dinga ɗauke mata hankali, amma wani sashi na zuciyarta na can tunanin mafita, dan bata zaci Imran ze iya watsi da ita haka b, harta kirashi yaƙi ɗagawa ba.

Ɓangaren Abba ma hankalinsa ya kwanta, mussaman daya sake zuwa gidan Alhaji Hashim ya tarar da Amira ta saki jikinta, ta dena koke koke da damuwa, yanzu bashi da wata fargaba na za'a kirashi ace masa ga Amira ta aikata wani lafi, dan haka ya samu nutsuwa harya koma bakin aikinsa.

Ihsan kam abun duniya ya isheta, kwanan Imran biyar da tafiya amma yaƙi ɗaga wayarta, ta tura masa message ba adadi amma beyi responding ɗin ko guda ɗaya ba.
Rana ta shida da Safe ta sake jarraba kiran wayarsa, Babu tsammani taji ta ɗauka, kawai ta sa masa kuka.

"In kuka zakimin zan kashe wayata, meyafaru?".

"My meyasa zaka tafi ka barni dan Allah?".

'saboda ba kya buƙata ta, babu amfani cigaba da zaman namu shiyasa na bar miki Gidan"

"Haba My, kishinka ne yasa nai abunda nayi, But i regret it, Ammi tazo ranar da ka tafi, ta gayamin takura maka akayi ka Aureta, dan Allah kayi haƙuri, wallahi ina sonka mijina".

"Ina tantama akan son da kike min Ihsan, tunda kika gaza yimin uzuri ki saurareni"

"Dan Allah kayi haƙuri My Own, kishine ya rufemin ido, ina sonka sosai"

"To yanzu me kike son ayi?"

"Dan Allah ka dawo"

"Na riga na dawo bakin aiki, se ƙarshen wata zan dawo"

"Dan Allah kayi haƙuri, am missing You am sorry please"

Imran yai ajiyar zuciya yace  "Shikenan naji, ki kwantar da hankalinki, zaki biyoni nan ne?"

Da sauri tace "Eh zan biyo ka"

"To shikenan, zan turomiki kuɗi ki biyo jirgi ki taho"

"Alhamdilillah, insha Allah zan taho, amma kamar baka haƙura ba My Own"

"Ya wuce mana, karki damu take a very good care"

Ihsan taji daɗin ɗaga wayarta da Imran yai, nan da nan ta fara shiri, domin zuwa ta riski masoyinta a Ikko.

Anty kuwa tana matuƙar jan Amira a jiki, hakan yasa ta saki jiki da Anty sosai, suna matuƙar mutunta ta da girmamata, ba hantara ba tsangwama ba Komai, Anty tana ta monitoring ɗin Amira da son gano matsalolin Amira, sedai a zaman da sukai Babu wata alama da ta gani da take nuna rashin jin da ake faɗa akan Amira.

Tana girmama kowa, sedai kusan kullum setayi zancen dama irin Mijin Anty Fa'iza ta Aura.

Yanzuma suna zaune a falo suna kallo, Fadila da Amira suna hira, Anty Fa'iza ta kira Amira  "Amarya bakya laifi ko kin kashe ɗan masu gida"

Amira tace  "Malama uwargida dai sarautar Mata, ko kin manta ni aka fara ɗaurawa Aure"?

Seda Anty ta kalli Amira tai murmushi, tare da girgiza kai.

Fa'iza tace  "mara kunya, Allah ya baki haƙuri, Uwargida Imran, ya kike ya mutan gidan?"

"Lafiya  ƙalau, ina 'ya'yana ina ɗan aljanna?"

Fa'iza tace "duk suna lafiya, ɗazu ya gama zancenki kan ya fita, yace in kira ki ince yana gaisheki"

"Allah sarki Yaya Bashir nawa, kice ina amsawa ya dena nemana ko?"

"Haka kurum ya nemeki yai miki me? Ranar da Sultan yazo nemanki ya bani labarin shaƙar da Imran yai masa, haka kurum nima a shaƙen miji"

Amira tai dariya tace  "haba dai, ai duk ke kika jamin wannan abun, da tun farko kin Auri Alhaji Yahaya, nikuma na Auri Abu Khairat da ba shikenan ba"

Fa'iza tace 'mara mutunci, ai gara da aka miki Auren, na fuskanci da zaki samu dama sekin Auri mijina kin zama kishiya ta"

"To tun yaushe ma, ke Allah ne yasa mijinki ne, da mijin wata ne ai da sedai taji wani zancen"

"Taɓ kishi da irinki se macen da ta shirya ai, gara dai da kika Auri Imran ɗin shine dai dai dake"

"Kyaji dashi dai, anjima zan kiraki ki haɗani da Khairat a waya, inji muryarsu"

"Zan haɗaku Insha Allah, dan kusan kullum se sunyi zancenki suce min wai yaushe zakizo, gidanku kuwa sunata sababi wai an Aurar dake basu sani ba"

"Mhmm, ni nama rasa me zance, kuma suna raina wallahi, duk cikinsu ba wanda ya kirani ko a waya, ni zan nemesu insha Allah zan kira su in gaishesu"

"Shikenan, ds kin kyauta ki gaida mutan gidan".

"Zasuji insha Allah"  Amira ta kashe wayar.

Anty tace  "Amira wai ya kuke da Fa'izan nan ne?"

"Yayata ce, cousin ɗina ce"

"Amma kike gayamata  zaki Auri mijinta?"

Amira tai murmushi tace  "tasan tsokanarta nake ai"

"Anya baza taji ba daɗi ba, koda yake ai kema kinyi Aure yanzu".

"Idan ma tana ji sedai tayi haƙuri, dan mijinta yayi a rayuwa, irin wannan mijin haƙurinsu idan baka musu biyayya ba se su kaika wuta, baya fushi sam da wuya, ko faɗa sukayi bata da gaskiya amma dan a zauna lafiya se yaita bata haƙuri, idan nike da mijin Anty Fa'iza, ai binsa zan yi sauda ƙafa, bazan bari ma yai fushi ba, itama ta sha wahalar rayuwa Allah ya musanya mata da mafi Alkhairi"

Fadila tace  'to shi Imran ɗin da Allah ya baki, ba zaki bishi sau da ƙafan ba?"

Murguɗa baki Amira tayi ta ɗauke kai, alamar ba wannan maganar.

Anty tace "A'a shina zata bishi sau da ƙafan mana, ai Amira Yarinyar kirkice, next week insha Allah Ina son muje dake Kasuwa ki zaɓi abunda kike buƙata, amma za'a kirashi ki fara tanbayarsa tukuna"

Amira tana jin abunda Anty ta faɗa amma ta basar kamar bata ji ba.

Ranar juma'a da yamma, Ihsan ta sauka a garin Lagos, Imran da kansa yaje ɗakkota a airport, tana ganin Imran ta tafi da gudu ta runguneshi, shima rungumetan yayi yana murmushi yace 'i miss You my Ihsan".

"Miss you too Hubby"

Suka shiga motarsa suka tafi, tun kan ta sauka tuni yasa anyi order Abinci ya ajiye mata.

Gidansa a cikin Barrack yake, flat ne madaidaici me kyau sosai, gidan ya burgeta sosai, tai wanka ta canza kaya suka zauna suna cin Abinci, tana sake lallaɓa Imran tana bashi haƙuri, dan ta lura be huce gaba ɗaya ba.

Ihsan an haɗu da maza, dan yau Imran ya samu abunda yake so a gurin Ihsan, hakan yasa ta wanke duk laifin da tayi masa, sedai Ba laifi ta ji jiki, gaba ɗaya Imran ya manta sunyi faɗa, suka jone suka shiga sabuwar Rayuwa shida Ihsan, me cike da soyayya da kulawa, gaba ɗaya ya manta da wata Amira a rayuwarsa, se daga baya ma Ammi tasan Ihsan tabi Imran.

Amira tai waya da Anty Fa'iza tace "taje gidansu ga kwasar mata kayanta gaba ɗaya, ta haɗa mata dana wajenta ta ajiye mata"

Da la'asar Amira ta fito ta samu Anty a Falo tace  "Anty, ina son zani wankin kai, dan Allah kisa a rakani"

Anty tace  "Eh gaskiya yakamata kam, dam kuma nayi miki zancen zuwa kasuwa, bari a kira Imran ki nemi izninsa"

Haɗe rai Amira tayi tace "Izini kuma?"

"Eh mana ba mijinki bane, seda izininsa sannan zaki fita"

Amira ta ɗan kumbura fuska, wai mijinta tunda sukazo da daddare shi da Abba, be ƙara bi takanta ba, ko ya kira yaji halin da take ciki ba, se yanzu za'a wani kirashi wai a tambayeshi zata fita, fan tana jin nauyin Anty ne da wallahi ba zata kulashi ba itama.

Ganin lambar Anty tasa Imran ya ɗaga wayar, dan seda yaga lambar Antyn ne Amira ta faɗo masa, ya ɗaga da fatan Allah yasa ba wani abun tayi musu ba.

Anty tace "Ango wannan shiru haka, ba amo ba labari baka ko waiwayar matar taka"

Cikin jin nauyi Imran yace "wallahi Anty Nafisa abubuwa ne suka ɗanmin yawa, harkar aikin namu ne ba sauƙi"

"Ka koma bakin aikin kenan?"

"Eh na koma tuni"

"Ahh to masha Allah, kace Ihsan ɗinma tana nan ka barta?"

"A'a Ihsan tana tare dani, da ita na taho muna nan gaba ɗaya"

Kasancewar wayar a hansfree take, Amira tana jin maganar da suke, aikuwa nan da nan Amira ta haɗe rai.

Rainin hankali, ita am barta a nan bata ga tsuntsu bata ga tarko, ita ba matar Aure ba ita ba sakakkiya ba tana zaune a gidan mutane, dan ita bata ma san zaman me take a gidan ba, Amma ya ɗau matarsa sunyi tafiyarsu, irin zaman da zataje tayi a gidan nasa kenan? Ta tambayi kanta.

Anty tace "dama Amira ce tana son taje gyaran kai, kuma ina son taje Kasuwa zamuyi 'yan saye saye, nace bari in kira mu nemi Izini"

Imran yace "seta dawo"

"A'a bari in baka ita ku gaisa, ta tambayeka da kanta"

Anty ta miƙawa Amira wayar, Amira kamar karta karɓi wayar nan, zuciyarta se wani tafasa take kamar ta tsaga ƙirjinta ta fito.

Tasa hannu ta karɓi wayar, ta danne fushinta tace "Yayana barka da yammaci ya aiki?"

Imran a ransa sabon salon rainin wayo.

Ya basar yace "Alhamdilillah"

"Dama zanje a gyaramin kai ne, Shine nake neman Izini"

"Sekin dawo" Imran ya bata amsa.

'Nagode, ka gaishemin da ƙanwata kuma Yayata, wato Amaryata"

Daga nan ta kashe wayar, ta sake haɗe rai ta miƙawa Anty wayarta.

Ba ƙaramin mamaki Amira ta bawa Anty ba, ga kishi nan ƙarara a fuskarta, amma ta danne taiwa Imran magana cikin nutsuwa.

Anty tace  "Amira kishi haka?"

"Anty wane irin kishi kuma? Ni ba kishi nake ba"

"To me kikeyi?"

"Bakomai" ta faɗa kamar za tayi kuka.

Anty ta jinjina kai tace "lallai gidan Imran akwai kallo, Amira kishi ne gashi nan ƙarara a fuskarki, sedai kin birgeni da kika ɓoye kishin naki, baki nuna masa ba"

Amira kasa magana tayi, kawai ta tashi ta tafi ɗakinta, danji take kamar an ɗora mata dutse a ƙirjinta, jin Imran na can shi da matarsa, ita kuma an barta a nan.

Anty ta jinjina kai tace "taɓɗijan Amirana kishi tun yanzu?"

Amira kam tana zuwa ɗakin ta rufe ƙofa ta tsaya tana sauke numfashi, tace  "Lallai ma an rainamin hankali, zaman da zanje inyi a gidan nasa kenan, ita yana sonta ya bata kulawa ni kuma ina kallonsu? Baze yuwu ba, ba zanyi boranci a gidamu, inzo gidan miji ma inyi boranci ba, dani suke zancan da shirina zan tare a gidan Imran, ba zan ɗau kowane kalar cin kashi ba, zan nuna musu WATA KISSAR..... Sai mata!!!

(Wanda be karanta littafin wata kissar sai mata ba, an barshi a back 😜😜😜🤪)

Gaskiya ba ƙaramin jin daɗin sharhin ku nake ba, shiyasa nake muku dogon page, ina godiya da kulawa masoya 🥰😍😍😍😍🥰

Share Please

Follow me on watpad@ Ayshercool7724
Domin gyara, Sharhi ko shawara
07063065680
[1/25, 8:34 PM] Ayshercool:    

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login