Showing 90001 words to 93000 words out of 120332 words
Chapter 31 - WUTA A MASA?A COMPLETE HAUSA NOVEL BY AYSHERCOOL
hira, ta kawo musu Abinci suka zauna nan suna ci ɗaya daga cikin su tace "ke wai ni ina kishiyar taki ne, tun da nake zuwa ban taɓa ganinta ba fa, duk zuwan da mu kai bata nan"
Ɗaya tace "to ta ina zata zauna, matar da aka ce miki Karuwa ce, sufa irin wannan ba denawa suke ba, da Auren ma se subi maza"
Ihsan ta yatsina fuska tace "ba dai kishiyata ba, dan wannan ba ta kai kishiya a idona ba, Karuwace fa bin maza take, kwararo kwararo aka ɗakkota aka liƙa masa dan a temaka mata, kuma zaman gadi take dan ba ta kai mijina ya saurareta ba wallahi"
Wata uwar shewa suka saki gaba ɗaya "Lallai Ihsan ba ki da dama, wato liƙa masa ita a kai, to ai shikenan, ni dai ina son in ganta"
Suna cikin hirarsu 'yar halak sega Amira ta fito, hannunta da labulaye zata bada wanki, ta kalli Baƙin Ihsan da su kai tsit saboda fitowarta, tace "baƙi mu kayi ne? Sannun ku da zuwa"
Shiru su kai, se ɗaya daga cikin su ce tace "Yawwa sannunki"
A fusace Ihsan tace "Nabila ina ruwanki da ita? Meye na amsa mata, gurinta ki ka zo?"
"Au ko itace kishiyar taki ne?"
"Itace fa"
"Kan uba, lallai wannan ai 'yar galace, ba itace kwanaki akace za ta fito a wata rawa ba, video ɗinta ya dinga yawo ba"
Ihsan tace "to itace ta sa aka fasa Auren Uncle Hassan, ta rufeshi a banɗaki"
Wucw su Amira tai, taje ta kaiwa me wanki kayan, ta dawo ta kuma wuce su zata shiga parr ɗinta.
'gaskiya wannan annamimiyar Karuwa ce, taɓɗijan wallahi kibi a sannu kar kema tai waje dake, Allah ma ya tsare kar a samiki HIV, tunda tabi musulmi tabi Arna dan tsabara iya Akuyanci"
Amira ta juyo ta kallesu tai murmushi tace "Ai Karuwanci ya gama min Komai, nai suna nai kuɗi a dalilinsa ƙarshe kuma Allah ya bani mijin sokuwa na Aura, ai Karuwanci yai riba" ta ƙarasa Maganar tana shigewa ɓangaren ta, nan suka ɗau salati gaba ɗaya, suka dinga ziga Ihsan, suka dinga zigata akan yadda za tai da Amira, ita kuma ta dinga cika baki tana cewa ai mijinsu baya sonta, dan ko ɗakinta baya shiga, ta dinga gayamusu yadda Imran yake wulaƙanta Amira, suna shewa suna ƙara ɗorata a keken ɓera.
Yadda Ihsan tai watsi da Imran, shima haka ya shareta, dan ya gaji da aikin rarrashin ta, shima ya shiga haɗa nasa kayan, tun daren ds zasu tafi Ihsan take fargaba take faman koke koke, ta bi ta dami kanta ta ƙi cin Abinci saboda fargaba.
Amira ma ta kammala shirinta tsaf, ta haɗa duk wani abunda take buƙata, wajen ƙarfe sha ɗaya na safe, Imran ya shiga ɓangaren Amira, kai tsaye ya tafi bedroom ɗinta, ya tarar da ita daga ita se underwear tana shafa mai, da alama wanka tayi.
Ya ɗanyi turus saboda tozali da kyakykyawar surarta, fatarta se wani sheƙi take kamar bata shiga rana, Gashi ta shafa mai se ƙyalli take, gashi ta ciko da ga Wannan ramar da tayi, saurin ɗauke kansa yayi yace "ki zama cikin shiri tun ƙarfe biyu zamu tafi airport, idan kuma kika ɓatamin lokaci ba jiranki zan ba, zan tafiyata ne"
Ɗago idanunta tai tana kallonsa tai wani murmushi tace "to My zan shirya da wuri insha Allah"
"What? Waye my ɗin naki?" Yai Maganar yana kallonta
Ta ɗan kashe murya tace "Gashi nan a tsaye a gabana, namijin duniya sha gwagwarmaya, soja maganin wani sojan, ɗaya kake tamkar da goma, sadauki me abun bajinta, dogo Mijin Amira me hannun kyauta"
Imran be san lokacin da murmushi ya suɓuce masa ba, that girl is very Funny at times, duk da abun haushinta yafi yawa, yace "Kin fiye shirme, ni dai ki shirya da wuri"
"An gama ranka ya daɗe, na haɗa Akwatina ma"
Yace "good sannan ya juya ya fita"
Tabi bayansa da kallo tai murmushi haɗi da jinjina kai.
Ta shirya cikin riga da skirt na shadfa, ta fito falo, tana ta kaiwa tana komowa tana shiri, ta fita farfajiyar gidan ta tarar da Ihsan tana waya, Ihsan ta watsa mata wani Mugun kallo, Amira tai murmushi tace
"Wai ke dama da na gayamiki se zaki san kin tafi da mijina Lagos kinyi wata biyu, ba ki zaci zan rama ba kenan? Ai dama na gayamiki tuntuni gara tun da wuri ki dena wannan harare hararen, he is now my not yours, don't ever under estimate the power of a Woman like me, Karuwancina me license ne, kuma lokaci ne yazo da zan ɗanɗana miki abunda kika min, wallahi Ihsan se kin zubar da hawaye fiye da yadda kika sa na zubar, bana riƙo ina da manta abu, amma kin shiga sahun Mutanen da har in koma ga Allah ba zan manta abunda su kai min ba, ni ba zan cutar da ke kamar yadda kika min ba, Amma daga yanzu ki rubuta ki Ajiye cewar Imran namu ne mu biyu ba ke kaɗai ba, Ihsan iliminki na addini da larabcin da kike ba suyi miki amfani ba, idan har son tsakani da Allah ki kewa Imran, bekamata ki zuba masa ido ya kai kansa ga halaka ba, hakkina kawai ya isa ya nesanta shi rahamar Ubangiji, Amma son zuciya ya katange miki idanunki, kanki kawai kike kallo, Yanzu zan nuna miki match ɗin da kika tari ba ki da 'yan wasa sam, yanzu za'ai playing game ɗin yadda yakamata, zan nuna miki kishi da Karuwa se macen da ta shirya" ta ƙarasa Maganar tana huci, ta bar Ihsan a gurin baki a buɗe tana kallonta.
Amira ta koma ɗaki ta kwaso Akwatinta, ta fito dasu harabar gidan ta ajiye, da duk abubuwan da take buƙata.
Ihsan kuwa ɓangaren ta ta koma, ta fashe da kuka hadda sheshsheƙa, ji take kamar ta kunnawa gidan wuta duk su mutu a ciki saboda baƙin ciki, Imran se biyu saura ta shigo gidan, a gurguje ya leƙa ɓangaren Amira, ya tarara ta shirya tsaf, yace "yawwa gara da kika shirya ai, an sa miki kayanki a mota, kaya kawai zan canza mu tafi"
"Ya ma za'ai in tsallake maganar Husband ɗina, na shirya tuni"
Bece komai ba ya wuce part ɗin Ihsan, aikuwa ya tarar tana ta uban kuka, idonta kamar an zuba mata barkono, sunyi jawur kamar ba ita ba, ya zauna ya dinga bata haƙuri yana kwantar mata da hankali, Wani Mugun haushin Imran take ji, ji take tamkar ta shaƙeshi, dan ita gani tai Kamar yana ɗokin tafiyar, ya miƙe a gurguje ya watsa ruwa, ya canza kaya yace "Ihsan ko bakin mota ba zaki rakani ba?"
Girgiza kai tayi tace "A'a kuje kawai"
"No taso ki rakani"
Haka ya janyo Ihsan suka fito, yana ta cigaba da rarrashin ta yana rungumeta, Amira kuwa ta sha ɗaurin ture kaga tsiya, tayi parking ɗin gashinta.
Fuskarra babu kwalliya amma shar da ita tai kyau se ƙamshi take.
Amira gani tai Imran ya lalace a gurin Ihsan, se hawaye take yana goge mata yana Magana ƙasa ƙasa.
Amira tace "My love kace kar in ɓata maka lokaci, na shirya da wuri amma kai ka tsaya Sallamar ta isa haka"
Gaba ɗaya suka tsaya suna kallon Amira, kalmar my love ɗin da Amira faɗa ce ta daki ƙirjin Ihsan, ba shiri ta zame hannunta daga na Imran ta koma cikin gida, Idan Imran yace ze bita yasan faɗa zasuyi babu lallai ma ta saurareshi, ga lokaci yana ƙurewa dan haka kawai ya nufi inda motar take.
Ya buɗe gaban motar ta shiga, sojan da ya kai Amira gurin Kwalliya shine Yake jan motar, Imran be cewa Amira uffan ba, itama ba ta tanka masa ba, har sukaje airport.
Ƙarfe biyar da mintuna goma suka isa Lagos, se wajen shida saura sannan suka isa gidan Imran da ke barikin soja na Ikoyi.
Amira ta san tazo Lagos saboda bambancin al'ada, tunda syka shigo cikin Barack ɗin take ganin mutane kala kala, har suka isa gidan Imran.
Da alama akwai kyakkyawar alaƙa tsakaninsa da abokan aikinsa, dan tun daga gate da suka taho, yake gaisawa da mutane.
Gidan ɗan madaidaici ne me kyau, kan Imran yazo yasa aka gyara gidan, amma duk da haka gidan yayi ƙura sosai, ba wani gayara a kai masa na musamman.
Imran ya kalleta yace "ki shiga wancan ɗakin akwai toilet kiyi alwala kiyi salla.
Ta amsa masa da to.
Ya shiga ɗaya ɗakin, yai alwala yayi salla, saboda lokacin salla ya ƙure ba ze samu wanda za suyi jam'i a masallaci ba, ya idar da salla ya fito ya tarar da Amira a zaune a inda ya barta ya kalleta yace
'Ke sallar ma ba zakiyi bane? Nace ki shiga kiyi alwala kiyi salla amma kin zauna"
A gajiye take ta ɗan zumɓura baki, kai tsaye tace "period nake"
Ɗan taɓe baki Imran yayi yace 'ai seki tashi ki shiga da kayan, ko a nan zaki ta zama?"
"Nifa gani nai gidan duk ƙura, a haka zan saka kayana?"
"Zauna in zo in gyara miki" yai maganar cikin gatse.
Knocking ƙofar falon a kayi, Imran yaje ya buɗe wata mata ce me ɗan shekaru ta shigo hannunta ɗauke da flask na Abinci, suka gaisa da Imran cikin broken English Matar tace "Oga wannan kuma sister ɗin ka ce?"
Imran yace "A'a matata ce itaama"
Matar tace "Ka rabu da waccan ne?"
"A'a matana biyu ne ai"
Matar tace "yayi gata kyakykyawa, ga Abinci na kawo muku, dama megidana ne yace ai muku girki zaka zo"
Imran ya karɓa yana murmushi yace "mungode sosai Iya Bola" ya karɓi flask ɗin ya shiga dasu, ya ajiye ya kalli Amira yace "bagidajiya baki iya gaida Mutane ba ko? Kina kallonta tana kallonki amma ki kasa gaisheta"
"To ni me zance mata, ni iya turanci nayi? Ni ba wani gane me take faɗa nake ba"
"Ai dama ina zaki gane, tunda ki ka ajiye makaranta kika dena zuwa, ki ka kama shirme"
Amira tace "ni wallahi ban ajiye makaranta ba, dan nayi Candy kuma Anty tace min ma zan cigaba da makaranta, naga ma dai a makarantar tamu ba irin wannan turancin ake ba"
Ta ƙarasa Maganar hadda murguɗa masa baki, gajeren tsaki yayi yace "Nan barrack ne ba inda kika saba haukanki ba, idan kika kuskura ki kayi shirme casaki za suyi kuma ba abunda ya shafeni, ta shi kije Kitchen ki ɗakko plate kizo kici Abinci"
Tashi tai tana yatsuna fuska, ta shiga Kitchen ɗin duk yayi ƙura, ta ɗauki plates ta ɗauraye ta fito falon.
Ya karɓa ya buɗe flask ɗin Abincin, teba ce da miyar shuwaka, ta sha bushshen kifi da ganda, se ƙamshi take.
Imran ya ɗibi nasa ya tura mata sauran, yaje ya wanko hannunsa yazo ya zauna, ita dai se binsa take da ido kamar wata sokuwa, ya fara cin Abincin yaƙi kulata, Yunwa ta isheta dan haka ta matsa gabansa ta sa hannu, be kulata ba ya cigaba da cin Abincinsa.
Loma ɗaya tayi da ƙyar ta haɗiye, ga tsamin garri, ga miyar ɗan banzan yaji ga ɗacin shuwaka, ja da baya tayi tana suɗar baki saboda yaji
"ni gaskiya ba zan iya cin wannan Abincin ba, ba daɗi ga yaji, ni gaskiya bana cin teba"
Imran sake jan plate ɗinsa yayi, ya cigaba da aika tebarsa, Amira ta koma gefe ta zuba masa ido, ya gama ci yaje ya wanke hannunsa, ya fita ya barta.
Ta gaji ga yunwa tana ji amma ta tashi ta shiga ɗakin da ya nuna nata, sauran kayan Ihsan ta gani a ɗakin, ta kwaso kayan ta ƙulle ta ajiyesu a gefe ta shiga aikin gyaran gidan nan, tun daga ɗakunan, har zuwa banɗakuna falo da Kitchen, haka ta gyara ko ina yai fes.
Se da Imran yai sallar isha'i sannan ya dawo Gidan, ya sissiyo kayan Abinci da kayan amfani, yai makin ganin uban aikin da Amira ta sha, yaje bakin ƙofar ɗakin da take, yai knocking.
"Yes come in"
Ya ɗaga labule yace "ga kayan Abinci can na kawo, ki tashi ki dafa wani abun ki ci"
Tace "to in dafa da kai ne?"
"A'a zan ƙarasa wannan tebar"
"Zafa ta ɓata maka ciki, ka bari in dafa Abinci da kai"
"Nace miki zanci wancan"
"Shikenan" ta bashi amsa.
Duk wani abu da yakamata Amira tana yiwa Imran, gyaran gida yi masa girki, ruwan wankansa da duk abunda yakamata tana masa, sedai gurin kwanan kowa daban, Kwanakin su Huɗu a Lagos, amma Ihsan bata taɓa kiransa a waya ba ko da wasa, ya zuba ido yaga iya gudun ruwanta amma, ko flashing ba tayi masa ba.
Ya ɗau wayarsa da kansa ya kirata amma taƙi ɗagawa, yai mata missed calls sun kai goma amma taƙi ɗaga ko guda ɗaya, haushi ya kamashi ya harzuƙa yai jifa da wayar cike da jin zafin abunda Ihsan tai masa, hakan yai daidai da fitowar Amira da kwanuka.
Ta kalli Imran tace "lafiya kuwa?"
Banza yai mata ya cigaba da sauke numfashi, ajiye masa Abincin tayi tace "Koma meye Allah ya baka haƙuri" ta ajiye masa Abincinsa ta bar masa falon dan kar koma meye ya huce a kanta.
Hankalin Amira ya ɗan kwanta, duk da ba shiga shirginta yake ba amma ta sarara da ɓacin ran da take shiga saboda Ihsan, da yadda yake wulaƙantata saboda Ihsan.
Da safe Amira ta na cikin aikace aikacenta Imran ya shiga gurin da yake motsa jiki, ta kammala breakfast ta bishi ɗakin bata taɓa shiga ba se yau, manyan ƙarafa ne a gurin da yake Gymming da su, a ranta tace "taɓɗijan bayan wahalar da ake basu gurin training, har wani Gymming yake saboda tsabar wahala" ta zuba masa ido tana kallonsa, ya ɗago ya kalleta yace ya dai.
"Bakomai na gama girki"
"Ok ina zuwa" ya bata amsa ya cigaba da abunda yake.
"Ka dai ɗaga ƙarfen nan a hankali, kar ƙirjinka yai ciwo" ɗan murmushi yai bece mata komai ba.
Wasu lokutan idan Imran ya fita tun safe se dare yake dawowa, kaɗaici yafara damun Amira, taji gaba ɗaya zaman garin ya isheta, ga maƙotanta duk ƙabilu ne taji gaba ɗaya zamab garin ya isheta, ga Imran ba ruwansa da ita.
Yau be dawo da wuri ba, dan harta gaji ta kwanta bacci, can ta farka taji motsin Imran a Falo, ta taso ta fito ta sameshi a Falo, yana kallon Ball.
Taje ta zauna a kusa da shi tace "Baby ashe ka dawo, bacci ne ya ɗaukeni"
Yamutsa fuska yai yace "Baby kuma?"
"Eh mana Baby"
Hmm kawai yace, yana ƙara volume ɗin TV.
"Wai meyasa yau baka dawo da wuri ba?"
"Kinfa isheni, ki ƙyaleni da wannan surutan naki"
Ɗan rausayar da Kai tayi tace "hmm shikenan, nasan da Ihsan ce ba zakace mata haka ba, ban san dalilin da yasa ka tsaneni haka ba, shikenan good night"ta tashi jiki a sanyaye ta tafi ɗakinta.
Kawai se yaji be kyauta ba, yaji tausayinta, tana ta ƙoƙarin yin abunda ze faranta masa amma yana gwasale ta, se yaji ba daɗi.
Kashe Kayan kallon yayi, ya tafi makwancinsa, ya zauna ya ɗakko System ya shiga dube dube, sedai ko mintuna goma be ba da shiga ɗakin, Amira tayi Sallama.
Ya amsa mata, ta shiga ta zauna amma tai shiru ba tace Komai ba, "ya akayi ne?"
"Alfarma nazo nema a gurinka"
"Ina jinki"
Hawaye ne ya fara bin fuskarta tace "dan Allah ka barni in koma gida, ka kaini inda zan hau ko motace, ban san in takuraka da yawa, naga kamar biyoka garin nan na takura maka da yawa, kuma dama kace ba wani amfani zan maka ba, dan Allah kayi haƙuri zan koma in yaso se matarka ta biyo ka, kuma dan Allah kan in tafi Imran ka sakeni dan girman Allah, tunda nai Auren nan na buɗe sabon shafin ƙaddara a rayuwata, ban taɓa jin daɗin Auren nan ba, dan Allah ka sakeni"
Ƙura mata ido yai yana kallon yadda take kuka, "na miki kama da namijin da ze Auri mace ya saka?"
"Ni dai koma mene kawai ka sakeni dan Allah, banga amfanin Auren nan ba, na gaji! Na gaji! Am tired wallahi, duk da nasan ni ba wani zurfi nayi a ilimin addinin ba, amma nayi iyayina gurin yin biyayyar Auren nan, amma zuciya ta ta fara rayamun wani abu daban, baka ƙaunata baka tausayina hankalinka yana kan Ihsan, ka sakeni in samu wanda ze Aureni duk da laifin da nai a baya tunda na dena yanzu"
Kashe System ɗin yai, yai kwanciyar sa yaja bargonsa, yaƙi kulata.
Aikuwa ta ƙule, ta janye bargon daga jikinsa "Imran wallahi ba zaka maida ni mahaukaciya ba, am so much tired na gaji, dan girman Allah ka sakeni tun da ba ka ƙaunata, ni ka ƙyaleni in samu me sona in Aura" kuka take iya ƙarfinta
Imran yace "A hakan zaki samu me son naki ya Aureki? Waze Auri 'yar gala?".
"Eh a hakan wani ze Aureni ya zauna dani, ya soni a yadda nake"
Cikin son cusa takaici Imran yace "au haba?"
Fashewa ta sake yi da kuka, hadda sheshsheƙa, sosai ta bawa Imran tausayi, ya miƙe zaune ya shiga ƙoƙarin sake janyo bargonsa, amma ta riƙe bargon tana kuka.
Haɗawa yai da ita da bargon a jikinsa, yace "rufemin baki ki dena min kuka, me nayi miki zaki dinga min kuka a daren nan? Saboda tsabar baƙin kishi da ke damunki zaki ce sena soki, to baza'a sake ki ɗin ba, zama kuma yanzu kika fara"
Kuka ta cigaba da yi kamar wata ƙaramar Yarinya.
Amira ta fuskanci kunnata kawai Imran yake.
Tsaki tayi ta miƙe daga jikinsa, "ni kike wa tsaki?"
"Na maka tsakin, mugu mara adalci kawai, wallahi Allah yana kallonka, kuma wallahi sena gayawa Abba duk abunda kake min, na dena rufa maka Asiri, Baka da adalci Imran ina ga baƙin cikin ka ne da na matarka ze kasheni, dannewa kawai nake ina maka biyayya dan cika umarnin Ubangiji, Amma wallahi na gaji"
"Ni kike cewa mugu mara adalci?"
"Na faɗa na kuma, mugu mara adalci! Mugu! Na faɗa Allah ya sakamin abunda kuke min"
Miƙewa zaune yai ya fizgo ta da ƙarfin gaske yace "bari in gwada miki adalcin da kike so ɗin...... 🙄🙄🙄🚶🚶🚶)
Ina Ganin sharhinku yana sani nishaɗi godiya nake 🥰🥰🥰😂 masu zagin Ihsan kuma, zan cireku a group ɗina dan a team ɗinta nake 😎😎😎
Gyara Sharhi ko shawara
Ayshercool
07063065680
[2/11, 3:25 PM] Ayshercool: 🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥
WUTA A MASAƘA
PERFECT WRITERS ASSOCIATION
(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS)
https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
P. W. A
*Story and written by*
AISHA ADAM (AYSHERCOOL)
The experience writer of
*ABDUL JALAL*
* WATA KISSAR.... (SAI MATA)
*BAƘIN TABO (Labarin gasa)
*AƘIDATA (Paid Book)
* WUTA