Showing 39001 words to 42000 words out of 120332 words

Chapter 14 - WUTA A MASA?A COMPLETE HAUSA NOVEL BY AYSHERCOOL

10 Mar 2025

30369

wallahi duk wadda ta kwashi Wannan, ta shiga uku, banjin ko ɗan rarrashin nan ya iya, banda tsawa da hantara be iya komai ba"

Fa'iza tace "kai Amira ki bari mana, ɗan uwanki ne, kuma kina cikin 'uan uwansa be kamata ki faɗi haka ba"

"Na faɗa aje a gaya masa, dan baki san da yadda ya ɗakkoni daga Kano ba, yadda kika san dabba haka yaimin, yana jana ina kuka ina masa magiya, amma ko a jikinsa sema zagina da yake"

Minal da ta fara ƙulewa da maganganun Amira, wanda dama Amiran tana sane takeyi ta ja tsaki tace "Ai dabbar ce ke, dole ai treating ɗinki kamar su"

Maimakon Amira ta nuna taji haushi, kota rama seta ɗakko wayarta tace "hey guys let's snap pics"

Nan ta shiga yin hotunanta hankali kwance, can tace "Nifa jikina tsuma yake, zanje a sakarmin sauti in cashe"

"Dan girman Allah kiyi haƙuri, ki rifa mana Asiri mu koma gida lafiya" Anty Fa'iza tai maganar tana riƙe skirt ɗin Amira.

Amira tai murmushi tace "cikani tunda ba ɓarauniya kika kama ba"

Aka sanar da isowar Amgo da Amarya, wanda sojojine zasu shigo dasu da bridesmaids.

Suna nan zaune aka saki wani kiɗan parrate, sega sojojin nan sun shigo cikin shigarsu ta ɗamara, suna taku daidai da kiɗan dake tashi, abun gwanin burgewa.

Haka suka rakasu har kan high table, Ihsan ta sunkunyar da kanta a cikin mayafi, shiyasa Amira bata ganta sosai ba.

Seda aka ɗan jima sannan Imran ya ɗagewa Ihsan mayafin kanta, ta sha make up gata fara sol, tayi kyau matuƙa.

"Taɓɗijan dama Wannan ce matar daze aura ɗin, ai na taɓa ganin wannan a Abuja, duk iyayin nasa ya ƙare a wannan skelaton ɗin, aba kamar bata cin Abinci, ga wani make up an mata kamar tsohuwa, gaskiya me kwalliyar nan ta cuceta"

Minal ta kuma waigowa tana kallon Amira, se cin zarafin Imran take da Ihsan hankalinta kwance, kuma ga wasu daga cikin 'yan uwan Ihsan ɗin a gurin a zaune.

"Da kike kushe Ihsan, kin san ko banza ta fiki komai, ita kamilalliya ce ba irinki ba watsatsiya, wadda bata san darajar kamta ba"

Maimakon Amira taji haushi se cewa tayi "matan ma dai suna suka tara, yo wannan idan tai kwalliya ta fito gaban miji maimakon ta burgeshi ai tausayi zata bashi, ya zata ko bata da lafiya, ai mace tai juyi aga tana da abun kallo shine take mace, amma wannan se kace tana cin ƙanzo, gaskiya wannan Imran ɗin bashi da wayo be iya zaɓen mace ba, gata wata busu busu da ita kamar zabiya"

Amina tace "haba Amira, dan Allah kidena mana, waike duk inda kika je sekin nemi magana, ina ruwanki ne"

Anty Fa'iza tace "Ai shine, dan Allah Amira ki bari, Minal kiyi haƙuri please"

Minal tace "ita zaki gayawa ta bari, wallahi idan bata dena zagin Anty Ihsan ba, nima bazan bar gaya mata magana ba, ina ruwanta damu, ita ya gani yace yana so, iya har tana da bakin magana, kota kushe wani, ita da take da abun faɗa, karuwar banza ballagaza"

Amira bata rama ba, sema bin waƙar dake tashi Yanzu take, sojojin nan sukaje suka canzo kaya, suka cika kan stage suna rawa, se ihu suke suna cashewa, suka janyo Imran daga kan kujera, suna ɗaga shi sama.

"Kai gaskiya ma dai wasu sojojin mahaukata ne, kalli abinda sukeyi kamar basu da hankali, bayan rashin imani harda shirme, wai waɗan nan sojoji ne taɓ"

"Sojojin ne marasa hankali?"

Amira tace "eh sune, kuma hadda Yayanki, su marasa hankali shi mara Imani, na faɗa tashi kije ki gaya masa, tun da nazo ƙyaleki kawai nakeyi, kuma ina ji a zuciyata in ba wani iko na Allah ba se Amira ta bar miki babban tabo, kallonki kawai nake sokuwa da baki kamar jaɓa"

Wata ƙawar Minal tace "kinga taso mu bar gurin nan, wannan'yar jaraba ce wallahi, neman abokin yi take nema, Minal ƙyaleta mu farinciki ne ya tara mu ba tsiya ba"

Minal tace "kamar kuwa kin san 'yar matsiyatan ce, shiyasa take abu  a haka, ni ba inda zanje, ina nan idan ta faɗi ɗaya in gayamata goma"

Tun Anty Fa'iza tana ƙoƙarin shiga tsakani ta rabasu, Amma abu ya gagareta, Minal ta kasa gane Amira tana sane take kunnata tana bala'i, seda ta tabattar ta ɓatawa Minal rai yadda ya kamata sannan ta miƙe ta nufi filin rawa, inda yake ango da Amarya ne kawai a tsakiyar filin, Imran yanawa Ihsan liƙi tana sunkunyar da kanta ƙasa.

Tana tunakarar inda suke, Ihsan ta ɗago kanta, aikuwa sukayi ido huɗu da Amira, Amira ta sakar mata murmushi, tunda Amira ta taho hankalin mutane Ya dawo kanta.

Takaici ne ya kama Imran ganin yadda ta taho jikinta babu ko mayafi, Amira na ƙarasowa ta fara dariya, se dariyar da take tai mata wani mugun kyau, ta kalli Ihsan tace

'Yayata liƙi nazo yi muku, Allah ya sanya Alkhairi, ya baki ikon haƙuri da juriya akan halin mutumin da kika aura"

Nan gaban Ihsan ya shiga harbawa, ta ɗaga kai tana wa Imran kallon tuhuma, gaba ɗaya Imran ya rasa mema zeyi.

Amira ta buɗe jakarta ta ɗakko kuɗi, ta fara liƙa musu, tana yi tana murmushi, gaba ɗaya Ihsan tausayi da dariya take bawa Amira, a ƙalla Ihsan zata kai shekaru Ashirin da biyar, amma ƙirjinta kamar 'yar shekara sha huɗu, siririyace sosai sedai fara ce tas ajin farko.

Khalid ne ya hau kan stage ɗin yace, "Amira matsa kusa dasu in muku hoto"

Amira tace 'to bari a temaka musu, suyi hoto da celebrity"

Wani sojane ya ƙaraso shima, yace Amira ta kawo wayarta a ɗaukar mata hotunan, se cewa tay "Allah ya kiyaye ta ajiye hoton Imran a wayarta"

Imran ya kalleta kawai ya ɗauke kai, ta tsaya a jikin Imran, yayin da ya tsaya yana kallon Amira, Ihsan kuma tanawa Amira kallon tsana da takaici.

Imran ya kalli Amira yace "malama ina mayafin kayan da na haɗa miki dasu?"

"Ni ajiye shi" ta bashi amsa

"Dama dan ki ajiye na baki?"

"Kaga malam karka takuramin mana, haba ka barni in huta nagaji da wannan ƙarfin halin naka"

Imran kawai ya bita da kallon mamaki da takaici.

Aka dinga hotuna, Khalid seda yasan yadda yayi yaiwa Imran hotuna akan high table harda Amira, saboda itama Amrayar ɓoye ce.

Ana gama hotuna ta sakko, an saka waƙar da take so, nam ta fara takawa, cikin salonta na burgewa da jan hankali, sedai bata girgiza jikinta wannan karon, amma rawar ta ta ta bada kala.

Nan fa ta fara shan liƙi, Imran ya dafe kansa yana fesar da numfashi, Ihsan kamar zata fashe da kuka tace "Imran wace wannan yarinyar?"

"Amira ce" ya bata amsar kai tsaye.

"Amma Imran, kai kace min yarinya ce, kuma na nuna maka hotonta kace ba ka santa ba, ashe ita ce Amiran, itace kake zuwa gurinta a Kano? Imran dama zaka iya ɓoyemin wani abu?" Hawaye suka fara bin idon Ihsan.

Dan wata muguwar tsana da kishi ne suka baibayeta, ba namijin daze wa Amira kallo ɗaya ya kauda idonsa, mussaman surar jiki da Allah yai mata, amma a haka Imran ya dinga ce mata ai Yarinyace ƙarama, kuma yazo yai mata ƙarya, Amira 'yar galace luma Karuwa, kallo ɗaya zakayiwa idonta kasan fitsararriya ce.
Wani irin gumi ya shiga tsatstafowa Ihsan, hawaye wani na bin wani

Imran yai ƙasa da murya yace "dan Allah Ihsan kiyi haƙuri, zan miki bayanin komai"

"Bana buƙatar bayaninka Imran, ka bani kunya wallahi" tai maganar kanta a ƙasa tana goge hawayw ta cikin mayafinta.

Hankalin mutane yana kan Amira, dan haka ba kowa ya lura da abunda ke faruwa ba.

MC ne yace "kai Masha Allah, 'yar baiwa muna godiya da wannan gudunmawar ta hanyar nishaɗantar damu da kikayi, ga tsabar farinciki Amarya tana zubar da hawayen farinciki, Amarya Wannan rana ce me girma ya farinciki a gareki, dan haka be kamata aga kina hawaye ba, ango yakamata ka Share mata wannan hawayen mana.

Imran kam ji yayi gaba ɗaya taron bikin ya fita daga ransa, yaji dama Amira bata zo gurin taron ba, Abba ne ya matsa Lallai taje, ga abubuwa na shirin kwaɓewa, yana ƙoƙarin ya rarrashi Ihsan amma a hasale tace masa "dan Allah malam ka ƙyaleni"

Yana ɗaga kai ya hango Amira a zaune, Matasan sojojin nan zarata, sun kewaye kujerar da take, suna ta mata surutu, wani lokacin tayi murmushi wani lokacin kuma ta bisu da kallo.

Wayarsa ya ciro yaiwa Khalid message ya maida ita cikin Aljihunsa, Ƙannen mahaifiyar Ihsan suka je suka kamo hannunta daga kan high table, suka sakata a tsakiyar filin rawa suna jujjuyata suna mata liƙi.

Maman Ihsan ce tace "ke Ihsan wannan wane irin sakarci ne haka, sekace wadda za'aiwa Auren dole? Kukan me kikeyi haka?"

"Ahh ki ƙyaleta, ze iya yuwuwa kukan farinciki ne, kuma ze iya yuwuwa tana tunanin sabuwar rayuwar da zata shi ne" cewar ƙanwar mahaifin Ihsan.

Aka shigo da Imran ma tsakiyar filin, Ammi da su Minal suna masa liƙi.

Khalid ya ƙaraso inda Amira take, yace yana son Magana da ita, tana ganin mutuncin Khalid dan haka bata musa masa ba, ta tashi suka koma gefe ya kalleta yace "Imran yace  a maida ke gida yanzu"

"Saboda me, naga ba'a tashi ba?"

"Eh haka dai yace min"

"Gaskiya bazan tafi yanzu ba, kowa yana nan a maida ni gida ni kaɗai, wallahi bazan tafi yanzu ba se an tashi"

Khalid ba yadda beyi da Amira ba, amma tace fafur ba zata koma gida yanzu ba.

Khalid ya zaga yaje kunnen Imran ya gaya masa yadda sukayi da Amira,  Imran yaiwa Khalid raɗa a kunne, Khalid ya koma inda Amira take, Imran ma ya koma gefe.

Imran ya kira wayar Khalid, Khalid kuma ya bawa Amira, Imran yace  "Malama ni nace a maida ke gida yanzun nan, ki bar gurin taron nan"

"Wai saboda me? Naga dai bani nace zanzo ba, kasa aka kawoni, kuma  kowa yana nan sekace a maida ni gida, wallahi bazan tafi yanzu ba, sedai in tashi akayi"

Imran yace "ni kike gayawa haka?"

"Toni me nace, idan kuma baka son in zauna seka zo ka maida ni gida, Amma baza'a maida ni gidan nan inje in zauna kamar mayya ba"

Yana ƙoƙarin sake yin Magana, Amma Amira ta katse kiran ta bawa Khalid Wayarsa.

Khalid yace "Amira ki dena yiwa Imran haka baze ji daɗi ya baki umarni kiƙi bi ba"

"To me nayi masa, kawai ina zaune yace sena koma gida haka akeyi?"

"Yi haƙuri, baki san dalilinsa na faɗar hakan ba, kiyi haƙuri a maida ke, nida kaina zan maida ke gidan ma"

Amira ta tura baki irin bata so ɗin nan ba, Khalid yace "yi haƙuri Amaryarmu, tashi muje karya miki faɗan nasa idan kuka koma gida"

'Amaryarku kuma? Wuce nan ga amaryarku can bushashshiya kamar karan dawa"

Tai maganar tana jujjuya idonta, tuna sakin layin da yai yayi, yai saurin cewa "Ai kyan da kikayi baza'a banbanceki keda Amrayar bane"

"To bari in kira su Yaya Fa'iza, se ka maida mu tare"

"A'a, akwai motocin da zasu maidasu, keɗin dai ki taso mu tafi"

"To ai banci Abinci ba, kuma ina jin yunwa dan azabtar dani yai tayi, sedai ya bani cake, ko abunda bazan ƙoashi ba"

Khalid yai dariya yace "an ajiye miki komai naki, yana mota taso muje in kaiki"

Haka ta miƙe tai gaba, jikin nan nata bako mayafi suka fita daga hall ɗin, seda suka fita akan idon Imran sannan hankalinsa ya kwanta, amma ya ƙule ƙwarai da Amira yau, dan ji yai tamkar ya maƙureta a gurin nan.

Har cikin gida Khalid ya shiga da motar, sannan ya fito ya buɗe mata motar ta fito, ya bata babbar leda cike da duk wani abu da'aka raba a gurin nan, ta karɓa ta kalli Khalid tace "Nagode sosai Allah ya saka da alheri, kana da kirki sosai ba kamar wancan masifaffen ba"

Khalid yace "ba ruwana kumfi kusa"

"Ba wani kusa, waze raɓi wannan masifaffen, seda Safe" tana gama faɗin haka ta tafi.

Khalid yai murmushi, wato gaba ɗaya Amira simple ce, babu babban abunda yake biyar da ita cikin sauƙi irin rarrashi, bata son faɗa dan shi ke sata taurin kai, sedai kuma Imran is very serious Man, be fiye son shirme ba.

Khalid ya hau motarsa ya koma gurin bikin, sedai yana zuwa ya tarar Dangin Ihsan sun ɗauketa sun tafi da ita gida, dan ta kasa kwantar da hankalinta kuka kawai take, ga jiri yana ɗibarta, ƙarshe ba Amarya aka ƙarasa dinner, seda Ammi ta tambayi Imran ko dai wani abun yai mata, yace shi be mata komai ba.

Haka aka tarkata kowa ya fara kama gabansa, saboda dare yayi ga Amarya ta tafi.
Su Sadiya da Amina aka samu banza, Abinci kamar zeyi Magana haka suka dinga lodar Abinci, suka dinga fakar idon mutane, suna kwashe lemuka da kajin da 'yan gayu suka bari, Ummma kuwa dama teburi teburi ta dinga zagawa, Sauran cake ne ko donut ko kaza haka ta dinga tattaresu a leda, shinkafa kuwa duk haɗamarsu seda syka tureta, haka lemuka ma suka sha iya shansu, suka dinga saye sauran.

Amira kuwa kayanta na ɗakin Imran, tana son ɗaukar doguwar rigar daya sai mata ta saka, ta canza wannan kayan na jikinta, Amma ɗakin na rufe dan haka ta haƙura.

Akwatin Anty Fa'iza ta gani a wani ɗaki, taje ta buɗe sega shi hadda kayanta irin wanda take zuwa ta bari a gidanta tazo mata dasu.

Tai murmushi ta ɗauki wata riga da wando na bacci, taje ta watsa ruwa ta sauya kayan jikinta, ta cire wannan leshin daga jikinta, tai alwala tai sallar magariba da isha'i taci Abincin ta, sannan mutane suka fara dawowa gidan daga gurin dinner.

Taje ɗakin Ihsan, ta kwantar da wata katifa, ta ɗauki bargo akan gadon Minal ta kwanta, ta ciro wayarta ta hau chatting.

Ji tayi hayaniya na ƙaruwa, alamar mutane nata dawowa, yau a shirye tale da duk wani Iskanci na Minal, yau idan ta taɓata ba zata ɗaga mata ƙafa, shiyasa ma tazo ɗakin ta kwanta.

Aikuwa babu jimawa sega Minal ta shigo, ta kunna fitilar ɗakin sega Amira tayi lumui a cikin bargo, akan katifa ga wayarta tana chatting.

"Kan Uba, ubanwa ya baki izinin shigomin ɗaki harki kwanta"

"Ubanki ne" ta bata amsa, sannan ta maida kanta kan wayarta.

"Ni kike cewa Ubana?"

Amira tai mata banza, bata kulata ba.

"To wallahi sekin bar ɗakin nan, ai ba da babanki aka haɗu aka gina ɗakin ba, Karuwar banza data wofi, har zaki zo ki naniƙarmin bargo haka, mara mutunci mara tarbiyya, kece me kushe mutane da raina mutane, bayan kece me abun faɗa*

Jin hayaniya yasa Anty Hadiza ta shigo ɗakin tana faɗin "Ke Minal, ke da wa haka? Muryarki kawai ake jiyowa kina masifa, lafiya?"

"Ina fa lafiya wannan ƙaramar karuwar tazo ta kwantamin a ɗaki, wallahi seta barmin ɗakina, mar tarbiyya kawai baki ji yadda ta dinga zagin Yaya Imran ba, tana kushe Ihsan, dan tana taƙama da ƙaramin Iskancinta"

Amira ta miƙe ta kalli Minal tace "karki ƙara cewa ina taƙama da ƙaramin iskanci, da babban nake taƙama, kuma na zagi Imran ɗin waye yace yamin abunda zan zageshi? Ki kiyayeni wallahi" Amira tai maganar cike da kashedi tana nuna Minal.

"Bazan kiyaye ki ɗin ba, kuma kema na zegeki karuwa kawai 'yar gidan karuwai mara tarbiyya"

Amira tace "Naji nagode, amma nikaɗaice Karuwar, banda iyayena"

Ta koma ta kwata, Anty Hadiza tace "gaskiya banji daɗin abun nan da kukayi ba, kamar ba 'yan uwa ba da giemanku da komai kamar wasu ƙananan yara, Minal karki kuma ce mata karuwa kinjibna gayamiki"

"To Anty Hadiza ba karuwar bace? Ai karuwar ce mara amfani, kai kuma wallahi seta barmin ɗakina"

Tai kan Amira, ta janye bargon jikin Amira, tana ƙoƙarin fizgo Amira akan katifa, aikuwa Amira ta shaƙoata, take kokowa ta ɓarke a tsakaninsu

Anty Hadiza da sauran mutanen dake gurin suka kasa rabasu, aka samu wata taje ta gayawa Ammi, wadda dawowarta kenan, aikuwa a sukwane Ammi tai ɗakin Minal, jin ana can ana tumurmusar autarta.

Tana zuwa taga an taru akansu, amma sunƙi rabuwa, da an rabasu Amira ta haƙura se Minal ta kuma dako tsalle Lallai seta rama abunda Amira tai Mata.

Shikuwa Imran tunda suka taho da Khalid, baya jik me Khalid yake faɗa, dan hankalinsa baya jikinsa sam, tunani daban daban ya cika masa zuciya, harya rasa wanne zeyi ma.

Suna zuwa gida Imran ya fito daga motar, sega Anty Hadiza tace "Yawwa, gara da Allah ya kawoka, wallahi Amira da Minal ke dambe tun ɗazu an kasa rabasu"

"Kamar yaya dambe kamar wasu maza"?

"Ni dai zo muje, ƙil in suka ganka su bari"

Cikin sauri ya shiga cikin gidan, Ammi na ganinsa tace "maza zoka ƙwatarmin 'yata daga hannun wannan azzalumar da kuka haɗa kai da mahaifinka kuka kawomin gida, ta saba dambe da maza a bariki shiyasa take da ƙarfi kamar namiji, nibkarta kashemin 'ya dan idan ra kashe ta bazan yadda ba"

Imran wani takaici ya mamaye zuciyarsa, yaje yana ƙoƙarin janye Amira da gaba ɗaya idonta ya rufe, Amma ta gasa masa wani lafiyayen cizo a hannunsa, aikuwa yasa hannu ɗaya ya fizgota a jikin Minal, yai jifa da ita gefe guda.

Cikin kuka Minal tace "Na faɗa na kuma, Karuwa 'yar gidan Karuwai, ballagaza mara tarbiyya kawai"

"Shut up!" Yaiwa Minal tsawa yace "banzaye sekace karnuka, dambe a gaban jama'a dan abun Kunya, Ke Minal ubanwa yace ki biye mata kin san ba ƙarfinku ɗaya ba, ta fiki girma ita faɗa a cikin ta kamar Karya, tai da maza tayi da mata"

"Niba karya bace, karka sake cemin karya, dan ban taɓa faɗa da maza a titi ba, kuma wallahi ta kuma zagina sena maƙure mata wuya, kuma in kana da zuciya ka ƙyaleni in tafi gidanmu a daren nan, dan nan ba gidan ubana bane kamar yadda ake goranta min"

'ni kike gaywa haka?" Yai maganar yana nuna kansa.

Cikin kuka tace "eh na faɗa ɗin"

Hanyar waje yayi ya ƙyaleta, ta zauna tana kuka, Minal ma kukan take tana cigaba da mita se Amira ta bar mata ɗaki, mutane kuwa kowa da abunda yake tofawa, ai sega Imran ya dawo da wata wayar wuta a hannunsa, ya rufe ɗakin nan, wanda suke ciki suna ciki ya soma zuba musu ita su biyun.

Dama gashi a ƙule yake da Amira, yau duk ransa a ɓace yake.

Minal na ihu tana bawa Imran haƙuri, tana kiran Amminta tana bashi haƙuri, Amira kuwa Ihu take tana Allah ya saka mata.

Hakan kuwa ya fusata shi, ya koma kan Amira ya dinga zuba mata wayar nan a jikinta, ga kayan baccin jikinta Nylon ne, ta ɗora

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login