Showing 27001 words to 30000 words out of 120332 words
Chapter 10 - WUTA A MASA?A COMPLETE HAUSA NOVEL BY AYSHERCOOL
yace "ƙyaleshi, dan ƙaniyarsa an gayamasa kowama irinsa ne, taya za'a kaiki wani Enugu, rabu dashi, yakamata ki halarci taron bikinsa"
Amira tace "ni gaskiya bana son zuwa inda za'amin wulaƙanci, ko a dinga gayamin magana, bana mantuwa ko an shekara dubu idan ina raye, in dai aka ci mutuncina bana mantawa, shiyasa bana son zuwa, kuma ni gaskiya wannan kallon da yake min tsoro yake bani, wallahi idan naje gidansu ze iya dukana, dan bashi da tausayi"
Ba Abba ba shi kansa Alhaji Hashim seda yayi dariya banda Imran da ya sake shan kunu, Alhaji Hashim yace "haka yake wannan fuskar shanun ai, ki ƙyaleshi ai ba gurinsa zaki zo ba, kuma ba dan shi zaki ba"
"Amira tace Ai da dan tashi ne cewa zanyi Al'yasa a fasa Auren, dan bashi da tausayi, ranar da yazo nan ya dinga ball dani da ƙafarsa, kuma nasan bazewa ƙanwarsa ba" tai maganar tana sake yiwa Imran kallon banza.
Abba yace "Allah ya baki haƙuri, ni dai fatana kizo ɗin kinji yarinyar kirki, ni zan aiko da mota ma a ɗakkomin ke"
Amira tace "shikenan, naji zanzo insha Allah"
"Kin tabattar zaki zo dai ko?"
'bana saɓa alƙawari" ta bashi amsa.
Imran kam ya cika yai fam, gashi an hana shi magana, maimakon su Abba su ɗau mataki, sun biye Mata se lallaɓata suke tana shirme.
Haka suka cigaba da hira da Amira, mutan gidan ma gaba ɗaya abun haushi ya basu, sun saka ran za'aiwa Amira rashin mutunci da tijara, amma an wani sata a gaba se rarrashinta ake kamar ƙwai akan Dutse.
Suna fita Yadikko tace "Kai Magaji tashi maza ka bisu, kaji me zasuce karka kuskura ka bari a tafi da yarinyar nan, maza jeka kaji me suke cewa"
Aikuwa Baba ya tashi, ya biyo bayansu.
Amira ta rakasu har gaban danƙareriyar motarsu, Banda Wadda jami'an tsaro suka rakosu da ita.
Abba yace "zan saimiki kayan anko kema a ɗinka miki, za'a ajiye miki idan kinzo seki saka kema"
Tace "Hmm gayyar soɗi kenan fa, zanzo da tsummokaran da Allah ya bani, abun masu kuɗi ina ni ina saka kayan da masu kuɗi zasu saka"
Amira akwai abun takaici, ana lallaɓata a shawo kanta, tana sake buɗewa, a fusace Imran ya daka mata tsawa yace
"ban gurizan shiga mota, Shashasha kawai"
Seda ta ɗan ruɗe saboda ko yaya yai mata tsawa seta razana, Imran yana mata kwarjini sosai, shiyasa daya mata tsawa jikinta yake tsuma.
Kallonsa tayi ranta a ɓace, annurin fuskarta ya ɗauke ta juya zata koma gida, Abba ya fara yiwa Imran faɗa, ya taka inda Amira take ya ɗakko kuɗi a Aljihunsa ya bata, Amma taƙi karɓa, sema hawaye data farayi kawai ta shige gida.
Jikin Abba gaba ɗaya yayi sanyi, Alhaji Hashim yace "Imran da alama tana shakkarka, amma be kamata ka dinga mata tsawa ba, yarinyar da ake lallaɓawa a gano bakin zaren zaka dinga yiwa tsawa haka? Irin wannan yaran ba kowane lokaci ne tsawa ko kurari ke aiki akansu ba, sema dai ya tunzura su, ita tarbiyya ba ko yaushe take buƙatar tsanani da takura ba, wani lokacin seda rarrashi da jan yaro a jiki, wannan yaro faɗa da zare ido baze mata aiki ba, attention take buƙata da rarrashi, yanzu babban abunda yakamata shine mu samu ta zo Kaduna, kar ace za'abi ta tashin hankali da hayaniya, mu bita a sannu, da tazo shikenan"
Abba yace "to idan tazo Kadunan meye abunyi na gaba?"
*Zan gaya maka, idan na gama nazari"
Suna shirin shiga mota su tafi, Baba ya fito ya samesu yace "Masha Allah, Alhaji baku tafi ba kenan?"
Abba yace "eh, amma yanzu zamu wuce insha Allah"
"To amma nace ya batun Amiran, wani mataki zaka ɗauka akan lamarin nata"?
Alhaji Hashim yai sauri yace "karka damu, abunda muke tattaunawa kenan, idan mun tsaida maganar abunda ya dace zamu sanar muku insha Allah, amma dai a cigaba da haƙuri da ita dan Allah, mun san ana haƙuri amma a ƙara, zamu san abunyi a kai insha Allah"
"Amma ina fatan dai ba ɗauke mana ita zakuyi ba?"
"Haba dai, ya za'ayi ku raini yarinya ace za'a rabaku da ita, za dai a duba ne mugani tunda tana son karatu zamu maida ita makaranta, kuma a sama mata koda wata sana'ar ne"
Baba yace "shikenan, hakan babu laifi, Allah ya maida ku lafiya"
Suka amsa da Ameen, suka masa ihsani, sannan suka tafi.
Suna cikin tafiya Alhaji Hashim yace "amma wannan tsohuwar ba ita ta haifi baban yarinyar nan ba ko?"
Abba yace "Eh, kishiyar kakarta ce"
Yace "shiyasa no wonder"
Abba yace "meka gani?"
"A'a bakomai, ni wallahi yarinyar ma birgeni tayi, wannan ba zatayi wahalar saitawa ba da taimakon Allah da jajircewa, rashin ji ne kawai, amma tana da sauƙin hali, sedai akwai mulki" yai maganar yana murmushi.
Abba yace "wani sauƙin hali tana wannan aika aika haka?"
"Ai zata shiryu insha Allah"
Amira kuwa harta shiga gidan bata kula kowa ba, ta shiga ɗakinsu ta zauna tayi shiru tana saƙawa tana warwarewa, tana tuno abubuwan da suka wuce, da wanda suke faruwa a yanzu.
Jiki a sanyaye, ta tashi taje ta ɗauki buta ta shiga banɗaki, ta fito ta zauna a tsakar gida.
Amina ce ma ta taho zata shiga banɗakin, Sadiya tace "ke Amina, kisa gishiri da omo ki wanke banɗakin nan kafin ki shiga, karki je ki tsuguna ki kwashi cuta, dan yanzu likkafa ta cigaba, har da Arna ake iskancin"
Yafikko tace "ƙwarai kuwa, kisa Omo ko wanke banɗakin nan da kyau, Allah ɗai yasan me taje ta yayimo mana, karku tsuguna ku kwashi koren Sanyi"
Amira tai shiru, kamar bada ita ake ba.
"Yo banda rashin mutunci da Akuyanci, ace biye biyen ya wuce kan musulmai, sekin dan gana da kiristoci masu fitsari a tsaye, basa wankan tsarki, basa tsarkin gasu da biye biyen tsiya, amma suma kije kina binsu, Babu abunda ze hana ki shiga banɗaki a kwashi Sanyi, harda ma abunda yafi Sanyi"
Suka dinga cashewa Amira, tana zaune tana jiksu bata ce musu uffan ba, kuma bata tashi daga inda take ba.
Su Alhaji Ali kuwa, daga gidansu Amira, seda suka tsaya rabon IV ga Manyan mutanensu dake Kano, sannan suka kama hanyar Kaduna,Se bayan la'asar su Abba suka koma, Imran ya sauka a gida, su Kuma su Abba suka wuce wani gurin.
Imran ya shiga gida, kai tsaye cikin gidan ya fara zuwa, ya tarar da Ammi a falo, ya zauna yace "Ammi sannu da gida"
Ta ɗago ta kalleshi tace "daga ina kake?"
"Tare da Abba muke, munje Kano ne rabon IV"
"Ƙarya kakeyi, kunje gurin wannan yarinyar ne ko?"
Imran yace "Eh munje gurinta, daga nan kuma mukayi rabon invitation, Amma Ammi meya faru?"
"Au tambayata ma kake ko? Za'a haɗa kai da kai a munafurceni, yana son ya ɗakko yarinyar nan ya dawo da ita gidan nan, to baze yuwu ba wallahi, bame ajiyemin Karuwa a gida, ina da 'ya Mace a lalatamin ita a banza, baze yuwu ba"
"Ammi bafa cewa yayi zata dawo gidan nan ba, hasali......
"Rufemin baki" tai maganar a hasale.
Naga kafi goyon bayan ubanka a kaina, kome zeyi seka dinga rufa masa Asiri, koma dai menene a baya ban karɓeta ba ba zan karɓeta a yanzu ba data zama 'yar gagara"
Imran dai yai shiru, bece komai ba, taita mita tana faɗa, harta gaji tayi shiru, Sannan ya tashi ya bar falon.
"Kai kai kai kai! Waye ya kashe wutar girkin nan? Umma! Umma! Waye ya kashe wutar girkin nan wai"
Umma daga ɗaki tace "kamar yaya? Ki iza wutar mana, amma se ƙwalamin kira kike"
Sadiya tace "bafa mutuwa wutar tayi ba, jiƙa murhun akayi da ruwa"
Umma ta fito da sauri, ta nufi gurin murhun, an jiƙeshi sharkaf da ruwa Babu yadda ma ze kama, ga itacen da yake ajiyema wanda ake girkin dashi an jiƙashi da ruwa.
Yadikko ce ta fito da carbi a hannunta tace "wai meke faruwa ne, Abincin haryanzu be gamu ba?"
Sadiya tace "wane irin Abinci ya gamu an jiƙe murhu da ruwa"
Yadikko tace "innalillahi wa innalillahi raji'un, Yanzu ɗan wakem be dahu ba?"
"Ina fa ya dahu, yanzu na gama jefawa fa na shiga inyi salla"
"Ina Amira take?"
Sadiya tace "waya san mata?"
"To wallahi itace da wannan aikin, Babu wanda zeyi wannan Haukan idan ba ita ba, shikenan Abincin nan ya ɓaci dan baze ciwu ba" cewar Umma da ranta ya gama ɓaci.
Yadikko tace "yanzu idan an siyo wani icen baze ba?"
Sadiya tace 'ta yaya zeyi? Tafa jiƙe murhun gaba ɗaya, ta jiƙe itacen da ruwa, yanzu kafin a siyo wani, a hura wutar ai aiki ne jawur, ɗan wake dai ya riga ya gama ɓaci, se a nemi abunyi"
Yadikko tace "wannan yaro ko matsiyaciya, an mutu an barmu da jaraba, da masifa ita duk wani abun da za'a ce mata Allah wadaranta shi takeyi, shegiyar yarinya watsatsiya, ta sani sarai babu wanda yaci ko Abinci rana a gidan nan, ni ji nake kamar an kwashemin hanji saboda yunwa, shine ta mana wannan baƙin zaluncin, Allah wadaran wannan sheɗaniyars yarinyar"
Usman yace "to ance a lallaɓa wan uwarta ya ɗauketa kowa ya huta, kimce ba haka ba, baza'a ɗauketa taje ta huta ba, dan haka dole mu haƙura mucigaba da kwasar baƙin ciki da takaici, yanzu dai ɗan wake ya ɓaci, sedai a bawa Awaki, kowa kuma yayi ta kansa"
Amira kam bayan tayi wannan aika aika, ficewarta tayi tai nata guri, tasan koba komai ta haɗa musu zafi da takaicinta zasu kwana, duk da abunda tayi musun, besa ta huce daga abunda suka yi mata ba, na zagi da cin mutuncinta da suke ba yau ba gobe ba.
Imran kam gaba ɗaya beji daɗin Abunda Ammi tayi ba akan maganar Amira, idan bata yadda Amira ta dawo Gidan nan ba an tsareta an sa mata ido ba, to lalacewa kam Yanzu ta fara, duk da shima baya goyon bayan dawowar Amiran gidan nasu, saboda kar tayi silar lalacewar ƙanwarsa, amma be kamata a ƙyaleya ta cigaba da wulaƙanta ba.
Gefe guda kuma ga tunanin Ihsan, wadda a wayar da sukayi ya lura ranta yayi matuƙar ɓaci, dan ya kirata bata ɗaga ba, yana yin Sallar isha'i, ya canza kaya ya tafi gidansu Ihsan.
Ya kirata a waya Amma bata ɗaga ba, ya tura mata saƙo "Ina gidanku yanzu, ina jiranki"
Tana ganin message ɗin kamar ta share, amma taji ba zata iya ba, dan haka ta zira hijjabinta ta fito, yana tsaye a jikin motarsa, ya ƙarasa inda take, ta cigaba da tafiya yana bin bayanta har sitting room ɗin da suke zance.
Ta samu guri ta zauna, amma ba tace komai ba, seda ya ɗan ƙura mata ido na wasu lokuta Sannan yace "Mu Ihsan dama zaki iya fushi dani haka? Har in kiraki ki ɗaga wayata? Why"
Kasa Magana tayi, sedai ta girgiza masa kai.
"Anya kuwa kina sona, har naje Kano na dawo tunanin yadda zan ɓullo miki nakeyi, duk na shiga damuwa, kinƙi ɗaga wayata balle inji muryarki hankalina ya kwanta, baki san muryarki ce cikamakim nutsuwata ba? Gaba ɗaya wunin yau haka na wuni ba daɗi, kin dena sona ko?"
Da sauri ta girgiza masa kai, "to meyasa kika ƙi ɗaga wayat? Kina fushi dani ko?"
Tai shiri ba tace komai ba.
"Kiyi haƙuri kinji Babyna, nima ban san da tafiyar bane, ina Bacci da Safe Abba yazo ya tasheni yace in shirya zan rakashi Kano, na kira wayarki a kashe, shiyasa ban sanar miki ba, ko kinfi son in saɓawa Abba ince ba zanyi abunda yace ba?"
Girgiza masa kai tayi tace "ba haka nake nufi ba, wallahi My haka kurum duk lokacin da kace min zaka Kano se inji gabans yana faɗuwa, bana son zuwa kanon da kake yi, kawai se inji kamar wani abu mara daɗi ze faru, wanda ze zama barazana ga Soyayyata da kai"
Imran yai murmushi yace "My Wife, kishi kawai ke damunki fa, yarinyar nan na gayamiki halin da takeyi, ta yaya ina da mace kamarki zan kalli wata, duk wasu qualities da manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ya lissafa game da mace tagari kina dasu, Ubangijin Allah ya baki, tayay zanyi tunanin kallon wata mace? Kinfi kowa sanin bana kalle kalle, kuma ta yaya zan kalli wadda take yawace yawace, kawai Yarinyar ko bana son ƙanwata ce, kuma mun haɗa jini da ita, kinga ba yadda na iya, Akwai alaƙa me ƙarfi a tsakaninmu, amma ni ba wani abu mummuna daze faru akan Soyayyar mu, nibke nake so kawai, kuma ni bayan ke bazanyi wani Auren ba, kin san bana ra'ayin ajiye mata fiye da ɗaya, ke ɗin kawai kin isheni, Amira ƙanwata ce kawai"
Gaban Ihsan ya faɗi tace "Ameera kuma?"
Yace "Eh sunanta kenan"
Tunawa tayi da Yarinyar da tayi rawa a Abujan nan, kuma itama sunanta Amira, ga kuma kaminin da suke ita da Imran, anya ba itace wannan Amiram ba?.
To amma ai ta nunawa Imran ɗin hoton yarinyar, yace shi be santa ba, bashi da wata alaƙa da ita, kawarda wannan tunanin kawai tayi daga ranta, ta barwa ranta cewar, suna ne kawai yazo ɗaya.
Ta kalleshi tace "to ya kuka dawo ya hanyar?"
"Alhamdilillah, mun kai invitation ma, Minal tacemin Mummy taje gidanmu Ɗazu ta taho da naku"
"Eh taje ɗazu, akan maganar gurin Dinner ne, kuma anyi settling komai"
"To Alhamdilillah, ya biki kuma da kikaje, kinyi kyau sosai a hotunan da kika turomin, seda naji kishibya kamani kar wani ya gani ya ƙyasa"
Ihsan tace "hmm ai daga dinner ɗin nan, akayi mother's event washegari, aka fasa auren nan"
Ya kalleta da mamaki yace "kamar Yaya aka fasa Auren?"
"Ni dai wahsegarin Dinner, Mummy tace lallai mu dawo gida saboda shirye-shiryen namu bikin, se waya akayiwa Mummy ranar ɗaurin Aure wai ba'a ga Ango ba ya ɓata, ana ta cigiya se bayan kwana biyu aka ganoshi a Hotel, yaje gurin Karuwa ta kulleshi a banɗaki"
Imran yace "Subhanallah, banda ganganci ga Matarka za'a kai maka, meya kaishi zuwa gurin Karuwa? Meyasa mutane bamu maida Zina komai bane? Muke rintse ido ga bala'in dake cikinta muke abunda muka ga dama?"
"Mhmm kaima dai ka faɗa, yanzu duk zancen ya bazu, dan baka hawa social media ne sosai, da ka gani"
Imran yace "Abun ba daɗi gaskiya, Allah ya kyauta"
Ta amsa da Ameen.
Ya sake kallon Ihsan yace "My kinga yadda fatarki ke sheƙi kuwa? Me kike shafawa hakane se ƙyalli kike fa"
Rufe fuskarta tai tana murmushi.
"Gaskiya nima a bani kayan gyaran jikin im dinha gyarawa, ko kinfi som a kawo miki ni a haka?"
Dariya Ihsan tayi tace "kaji ka, tome zaka gyara ai a gyare kake already my Own"
Nan suka cigaba da hirarsu cike da nutsuwa da farantawa juna rai.
*****************
"Alhaji Ali, mafita ɗayace ta rage maka akan yarinyar nan, idan ba haka ba wallafa idan abokan adawa suka ɗagoka, to tabbas se sunyi me yuwuwa sun zubar maka da mutunci a idon duniya, se sun watsa siyasar ka"
"To meye abunyi yanzu?" Abba ya faɗa cikin damuwa.
"Abunyi ɗayane, kaga a yadda na lura da yarinyar nan, kulawa take buƙata, da wanda ze dinga saurararta, tana da ambition me kyau a ranta, tana son karatu, kuma ni banga alamar wannan gidan nasu ana kula da ita ba gaskiya, ni gaba ɗaya Tsarin mutanen gidan bemin ba, da alama ka banzatar da ita a baya, kuma rashin gata yasa ta zama haka, amma idan ta samu gata da janyowa a jiki, ta samu tsayayyen me kula da ita, insha Allah zata nutsu"
"To banƙi ta taka ba Hashim, amma wallahi Jamila ba zata bari yarinyar nan ta zauna a gurina ba, tun tana ƙarama akace in ɗauke ta, Jamila yace bazata riƙe ta ba, kuma na lura haryanzu abun yana ran Amira, kuma a yanzu haka ma, bata shiga sabgata saboda kar ince zan kawo Amira gidan nan ta zauna, gaba ɗaya kaina ya kulle"
"Ai Ali ka sakarwa matar nan da yawa, ba gidanka bane ko kuɗi kuka haɗa kuka siya, kana da ikon da zaka kawo wanda kakeso ya zauna, amma tunda ka saba mata a haka ba yadda zakayi, seka samu ka aurar da ita nan kusa, inba haka ba kuma wallahi lalacewar da zatayi nan gaba se tafi ta Yanzu, kana ji tana tara kuɗi take zata tafi ƙasara waje karatu, me kake tunani idan ta tafi? Kuma ko a nan ƙasara ka barta, aka nema mata makaranta idan ba ayi dagaske ba, lalacewa zata cigaba dayi, dan haka kodai ka dawo da ita gidanka ta zauna koka aurar da ita"
"Ya salam, Hashim wa zan aurawa Amira? Bana son in aurawa wanda ze mata gori ko ya dinga wulaƙanta ta, wallahi ban san ina ƙaunar yarinyar nan ba se yanzu da aka cemin ta lalace, kuma nasan ina da laifi a lalacewar tata, kuma yanzu kullum se nayi mafarki da mahaifiyar ta, tana min magiya"
Alhaji Hashim yace "kaga, Asiri a rufe ka Aurawa Imran, ka haɗa masa biyu ai yana da kuɗin riƙesu, in yaso a ɗaura auren karta tare se tayi Istbra'i, ta zauna ko a gidana ne, bani da matsala da maiɗakina, zata fuskanta, a mata gwaje gwajen da duk yakamata"
Alhaji Ali yace "Mata biyu lokaci ɗaya, idan nai haka nawa Imran adalci kuwa?"
"Ali baka da wata mafita idan ba wannan ba, Duk wanda zaka aurawa Amira Asirinka baze tonu ba, tana jin tsoron Imran, kuma yin hakan kamar Jihadi ne, tunda Addini be haramta ba, amma idan ba haka ba ban san meye abunyi ba"
(😂😂😂 Godiya ga masoya, Comment ɗinku ke bani ƙarfin gwiwa da nishɗi, Wato idan kukayi Comments daya girgizani, bana gajiya da typing, amma idan nai posting naji shiru, da na fara typing nake fara hamma in ajiye)
Ayi share saboda Allah.
Ayi following ɗina a watpad akan
Ayshercool7724
Ina maraba da sharhi gyara ko shawara, banda biyoni ace in bada page kaza 🙄
07073065680
.
[1/12, 2:04 PM] Ayshercool: 🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥
WUTA A MASAƘA
PERFECT WRITERS ASSOCIATION
(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS)
https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
P. W. A
*Story and written by*
AISHA ADAM (AYSHERCOOL)
The experience writer of
*ABDUL JALAL*
* WATA KISSAR.... (SAI MATA)
*BAƘIN TABO (Labarin gasa)
*AƘIDATA (Paid Book)
* WUTA A MASAƘA
https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=in
❌❌❌
Ƙirƙirarren labari ne, ban yadda ayi amfani da kowane sashi na labarin ba ba tare da izinina ba.
Afuwan banyi Editing ba
KAMAR YADDA NA FAƊA TUNDA FARI, BA LALLAI IN DINGA SAMUN YIN POSTING KULLUM BA, IDAN AN GA BAN POSTING