Showing 99001 words to 102000 words out of 120332 words
Chapter 34 - WUTA A MASA?A COMPLETE HAUSA NOVEL BY AYSHERCOOL
ya durƙusa ya gaisheta ta amsa da ƙyar tace "ka g damar dawowa kenan?"
"A'a Ammi, pass ne ban samu da wuri ba"
"Rufemin baki da zancen wani pass, 'yar mutane ta na ta fama da rashin lafiya amma ko a jikinka, kaje kai zamankansabida kaka tare da Karuwa ko? Imran idan ka kuksakura na samu labarin wani abu a tsakanin ka da Yarinyar nan se nayi mummunan ɓata maka rai, wanda baka taɓa zata ba, bna son Yarinyar bana ƙaunarta, kuma ba zata cigaba da zama a cikin zuriyata ba balle a samu iri daga garera ba, sam bazan marba da ɗa daga Karuwa ba"
Gumi ne ya shiga tsatstafowa Imran, dan yasan aikin gama ya riga gama, inma cikinne wataƙila Amira ta samu, dan baya nacewa Ihsan ma kamar yadda yakewa Amira, kuma baya jin ze iya sake yadda ya nesanta kasan da ita, mussaman zamansu ɗin nan, da suka samu wata irin shaƙuwa da soyayya a tsakanin su.
"Ammi dan Allah kiyi haƙuri, kinga Amira idan lalacewar da tayi da halinta wani abun mun bada gudunmawa, ƙil da kin riƙeta ta samu kulawa ba lallai haka ta sameta ba"
"Karuwa tafi uwarka kenan da kake gayamin magana ko? To ban riƙe ɗinba kuma bazan riƙe ba, kaima kuma ba zaka riƙe ba, ina daf da datse wannan Auren dan ba sonshi nake ba"
Imran da ya sunkuyar da kai yai shiru, tai ta zazzaga masa masifa, seda tai ta gaji, sannan ya tashi ya tafi ransa a mummunan ɓace.
Da ya koma gida ya tarar da parr ɗin Ihsan a buɗe alamar ta dawo, bega Amira a falo ba, dan haka ya shiga paer ɗin Ihsan, ya sameta tana sallar la'asar, ya zauna ya jira ta idar, ta tashi ta naɗe sallayarta, ta ajiye.
"Ihsan baki ga na dawo bane?"
"Na gani mana me kake so in maka?"
Ya jinjina kai yace "ya jikin naki?"
"Ai da ka damu da jikina da baka kai wannan lokacin ba ka dawo ba, da ka dawo lokacin da nake jin zuciyata na daf da tarwatsewa, takaici da baƙinciki suka kwantar dani, amma har in kiraka a waya ka dinga rejecting, hakan ya tabattarmin da kaci amanata saboda waccan Karuwar, ka gaza cika alƙawarin da kaimin, in ba haka ba, ya za'ai in kiraka kai rejecting call ɗina, in maka magiya kaƙi dawowa?"
"Yanzu Ihsan irin wannan karɓar yakamata ki min? Wata guda da sati guda bama tare, ai idan ma laifin nayi miki kya bari ki min sannu da zuwa hakalina ya kwanta, seki min duk abunda zakimin ko, irin abunda yake haɗani dake kenan, ke ba kya uzuri, ba kya tunanin komai abunda zuciyarki ta raya miki shi kikeyi"
"Eh abunda zuciyata ta rayamin shi nakeyin, meyasa kamin alƙawarin da ba zaka iya cikawa ba? Ka dena sona kake na barwa karuwa kai"
"Karki kuma ce mata karuwa, bana son tahsin hankali daga dawowata"
"Na faɗa, ba karuwar bace, karuwa na faɗa na ƙara"
Idan Imran ya cigaba da tsaiwa, zuciya zata iya ingiza shi, yaiwa Ihsan lahani, dan haka ya fito daga part ɗinta, zuciyarsa na tafasa.
A falo yai karo da Amira, tana masa Magana amma idonsa ya rufe yai waje da sauri.
Hakan ya tabattar mata da Faɗa sukayi da Ihsan, Amira tace 'cigaba da wulaƙantashi, ke da gatanki da mahaifiyarki amma ni da nake marainiya ai dole in rungume shi hannu bibbiyu.
Amira ta zauna a falon, tana cin Abinci, Ihsan ta fito kamar wadda aka watso, ta kalli Amira tace "aikin banza jaka ƙazamar bariki"
Amira tace "naji nagode"
'jahila daƙiƙiya me bin maza a kwararo, wallahi se nayi maganinki zaki ga abunda zan miki, sena miki abunda ba zaki taɓa mantawa ba, idan ma wani Asirin ki kai masa idonsa ya fara rufewa ki saurari abunda zan miki"
"Alhamdilillah da kika fara ɗanɗan abunda kika min a baya, kuma wannan baƙin cikin yanzu kika fara shi, idan kin so zamu zauna lafiya, zamu Zauna lafiya ƙalau dake, amma idan akasin haka kika zaɓa na shirya, ina daidai dake wallahi, karya kawai"
"Uwar ki ce karya bani ba"
Amira tace "kin biya babarki ladan haihuwa, ita ki kaiwa wannan zagin"
Ihsan ta kawao iya wuya tace "Karuwa kawai"
"Suna ne, Karuwar Imran ba"
Ihsan taga alama kamar kalmar karuwan ta dena ɓatawa Amira rai, ra dena jin haushi sam idam ta gaya mata, taji Tamkar ta zuba ihu ko taji sauƙi a zuciyarta.
Imran se wajen ƙarfe tara na dare sannan ya koma gidan, Ihsan ta rufe ƙofar ɗakinta, ya shiga nasa ɗakin dake part ɗinta, ga wata yunwa da take damunsa, ya dawo falo ya zauna ya dafe kansa.
Amira idonta biyu dama, ta fito da wata shu'umar riga a jikinta, ta zauna kusa da Imran tace "Babyna kaci Abinci kuwa? Meya ɓata maka raine?"
Girgiza kai kawai yayi ba tare da yayi Magana ba.
"Dan Allah koma meye kayi haƙuri, in kawo maka Abinci zaka ci?"
"No bana jin yunwa"
"Haba major, kalli cikinka meka ci tyn da muka dawo? Gaskiya se kaci Abinci bari in kawo maka"
Ta tashi ta zubo Abinci ta kawo masa, da kanta ta dinga bashi a baki yana ci, daga ƙarshe kuma ta lallaɓa ta janye shi zuwa part ɗinta.
Se da Amira ta tabattar ta mantar dashi wata Ihsan, Suka kwana tare seda Asuba ya bar part ɗinta ya tafi masallaci.
Wasa2 kusan sati guda da dawowar su Amira, amma kullum se Ihsan sunyi rigima da Imran, ita kuma Amira na ta sake lallaɓa kayanta.
A haka Imran ya bawa Amira dubu ɗari uku na kayan lefe da be mata ba.
Suna kan sati na biyu da dawowa, su Yadikko suka zo gidan, da su Amina da Sadiya da Anty Fa'iza, sunyi mamakin yadda suka ga Amiran ta canzan, ta ƙara ƙiba tai shar da ita.
Ɗan uwa ɗan uwane, duk lalacewarsa Amira tai murnar ganinsu a gidnta, ta dinga farinciki ta rasa inda zata tsoma ranta dan daɗi.
Ihsan na gurin aiki, Imran ma baya nan amma yasan da zuwansu.
Yadikko tace "yanzu Amira kece a wannan danƙareren gida haka Amira?"
"Wallahi kuwa Yadikko, haka lamarin Ubangiji yake ai, ya kuke ya gida yasu Yaya Usman"
Fa'IZA tace "dui suna lafiya, yau Allah ya nufa Yadikko ta zo ɗakin Amira hankali ya kwanta"
Su Amina anata yaƙe, amma ƙasan zuciyarsu baƙin ciki ne fal, kamar su fitar da Amira daga gidan, suna can sun tsaa ruwan ido sun kasa fidda miji, saboda babu wani me ɗan abun hannu da yazo.
Nan da nan Amira ta shiga gabatar musu da Abinci, da yake tun kan suzo ta ɗora musu girki, ta gabatar musu da Abinci yaji nama, ga lemuka suka ware ciki suna zubawa, ƙasan zukatansu baƙin ciki kamar ya kashe su, sam ba haka Yadikko tai zaton tararwa ba, saboda ta zaci zata tarar da Amira a tagayyare a wahala, amma ta ganta a nutse cikin kwanciyar hankali.
Imran ne ya fara dawowa, Amira ta tsareshi tun a falo, tace "Sweet Amran, su Yadikkon sunzo"
"Ok muje ciki mu gaisa"
Suka jero zuwa falon tare, gwanin sha'awa, ganinsu tare seda Sadiya ta ƙware dan haushi.
Imran yace "Ashe mayan baƙin namu sun ƙaraso, Fa'iza ya hanya Sannu Yadikko"
Fa"iza tace "Alhamdilillah, mun sha hanya kam"
"Ya megidanki kuwa?"
"Wallahi yana nan lafiya duk yana gaisheku"
Yadikko tace "Sannu Imrna"
Yace "Yawwa ya hanya, an saki doguwar tafiya ga jikin girma"
"Ai wannan bakomai, ya haƙuri ya fama da halinta"?
Imran yace "Alhamdilillah, halinta na kirki ba"
"A'a, ai kasan abunne se a hankali dole se ana tambaya, kasan me hali wasu lokutan ba fasa halinsa yake ba, se ana bibiya ana saka ido tukuna, eh ai naga ƙoƙarin ka da na Mahaifinka da yasa ka Aureta, duk da kun san hali irin wannan se ka dinga taka tsantsan kana sa ido, mussaman da akace tafiye tafiye kakeyi, ka dinga saka nata ido sosai da sosai, kasan irin wannan ba denawa suke ta daɗin rai ba, idan yarinya ta saba yawon banza dariƙe kuɗi a hannunta...
Fa'iza a fusace tace "haba Yadikko meye hakane wai? Wannan wace irin magana ce?"
Duk da Imran yasan Amira ba karuwa bace, Amma abunda Yadikkon tai ya baƙanta mata rai, kuma dan cin fuska a gabanta.
Yadikko tace "barni in faɗa, ai da ba tai ba ba za'a faɗa ba, ba yadda ba'ayi akam ta dena harkar bin maza ba...
Tuni mutuncin tsohuwar nan ta gama zubewa a idon Imran, mussaman da Amira ta bashi labarin rayuwar da tayi a hannunta, da alama itace karuwar tsohuwa me fuska biyu.
Imran ba kunya yace "dan Allah bana son kuma jin wannan maganar, ya riga ya wuce, kuma ni na yarda da Amira ɗari bisa ɗari, saboda nasan ba karuwa bace, ni ne mijinta ni zan tabattar da haka, ana ta cemin Karuwa ce, ni ba haka na tararar ba, dan haka wannan maganar ta wuce, bana son in sake jinta, kar a kuma jifarmin mata da wannan mummunar kalmar dan Allah, in aka ci mutuncin ta mutuncina aka taɓa, nikuma ba zan lamunci cin zarafinta ba"
Hawaye ne suka shiga zubowa a idon Amira, hadda ajiyar zuciya, kawai ta rungume Imran tana kuka, Yadikko ta fusƙi da kai, cike da borin Kunya, Imran yaja Amira Zuwa bedroom ɗinta, ya janyota jikinsa yace "meyasa kuma kike kuka? So kike su rainamin ke?"
Ta girgiza masa kai "to ki dena kuka, ai Allah sheda nima kuma sheda ne, matata budurwa na samu abata, dan haka ba zan sake lamuntar a zagarmin ita ba, ko aci mutuncinta ba, saboda ina son abata"
Rungumeshi Amira tai tace "i love You too Amran"
Rarrashin ta ya dinga yi, gashi ita ba wuya ka rarrasheta, ko faɗa sukai da ya ɗan rarrsheta ya mata kalamai shikenan ya wuce a gurinta, saɓanin Ihsan me azababben taurin kan tsiya.
Fa'iza tace "gaskiya Yadikko abun da ki kayi baki kyauta ba sam, ya za ai abu ya riga ya wuce ki dinga dawo da shi baya, anyi abun nan inma karuwarce in ma ba ita bace, shi yacw yaji ya gani, meye kuma na dawo da bara bana?"
Yadikko tace"Ke rufemin baki, bana son sakarcin banza dana wofi, na faɗa ɗin ki dakeni"
Fa'iza tace "ba haka bane Yadikko, amma dai abunda ki kai be dace ba wallahi"
Se da Imran ya tabattar da hankalinta ya kwanta, sannan suka fito, ko da suka fito ɗinma, Amira tai pretending kamar ba wani abu da Yadikkon tai mata.
Ana haka se ga Ihsan ta dawo gida, ta tarara da gidan da mutane, ga su Yadikko da Fa'iza, bata manta fuskar su ba, ta gansu a gurin Dinner bikinta.
Ko kallo basu isheta ba, Fa'iza tace "laa Yadikko ga kishiyar Amira, sannu Ihsan ko?"
Kallonsu tai sheƙeƙe tace "ba dai kishiyata ba, dan wannan kucaka ce a gurina sauran titi"
Fa'iza tace "toooo ikon Allah"
Amina tace "wai da ganin wannan kishiyar Amiran a tsaye take, ita ce dai dai da ita ai"
Fa'iza ta tashi tabi Amira kitchen inda take wanke kwanukan da suka ci Abinci tace "Amira yanzu kishiyar ki ta dawo"
Jiki a sanyaye tace 'Allah yasa kar Yadikko tai wani abu da zata zubarmin da mutunci a idonta"
"Amira ba ksa zaman lafiya da ita ne? Daga na mata Magana ta faɗan baƙar Magana"
Amira tai nannauyar ajiyar zuciya tace "ina fa zaman lafiya Anty Fa'iza, kin ganta nan kullum cikin neman tashin hankali take, abun dai se godiyar Allah, ga mahaifiyar Imran ma ta sani a gaba duk na rasa abunyi"
Fa'iza ta dafa kafaɗar Amira tace "kiyi haƙuri Amira, taki jarrabawar kenan, daga wannan se wannan amma ina fatan Ubangiji Allah ya kawo miki ɗauki da gaggawa"
"Ameen Anty"
Imran kuwa jin motsin dawowar Ihsan, yasa ya shiga ɗakinta yace "Ihsan kin gaisa da 'yan uwan Amira a falo kuwa?"
"Nice zan gaisa da wannan matsiyatan? Ahalin tarkace da jaraba, Irin karuwai Allah ya kiyaye"
"Ihsan da farko na roƙeki akan kiran Amira da Karuwa da kike ki dena kinƙi, to Yanzu zan gargaɗeki na gaji da abubuwan da kike min na gaji, idan kika kuma kiranta da Karuwa ko bata ɗau mataki ba ni zan ɗauka"
Kallonsa tai da mamaki tace "me kake nufi?"
"Ina nufin karki sake kiranta da Karuwa" yana gama faɗin hakan ya juya ya fice.
Nan tai turus, ta ƙara tabattarwa da kanta Amira taiwa Imran Asirine, duk kwanan da Imran yake a ɗakin Amira ba ta taɓa sani ba, ita zaton ta kawai a ɗakinsa a yake kwana.
Ya raba musu kwana amma sam bata gane hakan ba, a nata haukan be bari ta gane hakan ba.
Su Yadikko seda suka wayi gari a gidan Amira, da safe Imran yai musu Alkhairi me yawa, Haka Amira ma sannan suka tafi rakasu tasha a motar Imran.
Ihsan kuwa dama tunda ta wucesu a falo, ba ta sake fitowa ba har suka tafi.
A hanyarsu ta dawowa Amira tai shiru kamar tana tunani, Imran yace "gimbiyar meke damunki ne?"
"Bakomai, kaina ne kemin ciwo, kwana biyun nan haka nake fama"
"Amma baki gayamin ba, ko dai damuwa ce?"
"Ba wata damuwa, kawai na rasa meke damuna ne, gashi bana iya cin Abinci"
"Amma meyasa baki gayamin ba?"
"Ai naga ba wani abun damu bane"
"A'a abun damune mana, bari muje Clinic a duba min ke"
Wani Clinic suka je, aka duba Amira aka bata magunguna, suka taho gida.
Da suka je gida har ɗaki ya kai Amira yace ta kwanta ta huta, saboda likitan da ya duba ta yace akwai buƙatar ta dinga samun isasshen bacci.
Washegari lahadi ce, Amira ta tashi gata nan ga ta nan jikinta ba daɗi, ga jiri dake damunta.
Minal ta zo gidan ita da wata ƙawarta, Ihsan suka zauna suna hira.
Amira taga kwanciyar ba zata kaita ba, dan haka ta tashi ta fito.
"Ahh Minal ke ce a gidan namu yau, ya Ammi?"
Minal ta kalli Amira tace "Ji wani munafurci, meye haɗinki dani kike wani yau nice a gidan?"
"Ohh Sorry, Allah ya baki haƙuri"
Ihsan tace "haka take, shegen shishshsigin tsiya, da munafunci ita lallai se an shiga harkarta"
"Anty Ihsan waze hulɗa da Karuwa, ba gaira babu dalili yanzu ma banda ƙaddara da Abba ya ƙaƙabo mana ita, waze so haɗa kansa da wannan tsohuwar kilakin?"
"Ke Minal me kike cewa!?
Suka ji muryar Imran da ke shigowa, jikinsa sanye da farar jallabiya.
"Meye haka kuke yi ne, baki da hankali ki ke faɗar wannan maganganun akan matata, kuma 'yar uwakki?"
"Wallahi ni ba 'yar uwata bace"
"Ni kike gayawa haka?"
"To Yaya ba karuwar bace? Ai kowa yasan haka"
Ba zato ba tsammani Imran ya kwashe Minal da mari.
"Dan ubanki ni zaki dinga gaywa wannan maganar, tashi ki bar min gida"
Ai gaba ɗaya buɗe baki sukayi dan mamaki.
Nan da nan jikinsa ya hau tsuma, dan sam baya son raini.
"Imran, Minal ce fa dan me zaka mareta dan tace mata Karuwa? Ba karuwar bace?"
Imran yace "saura kema, Na dena ɗaga miki ƙafa, ya isa abunda kukewa Amira ya isa haka? Amira ba mata ta bace kawai, jinina ce kuma ba karuwa bace na tabattar da Hakan"
Amira kuwa tuni ta fara kuka, saboda tasan abunda ze biyo bayan marin da yaiwa Minal, ba ƙaramin tashin hankali bane.
Minal kam ɗaukar jakarta tai waje tana kuka.
Sedai abun takaicin, da taje gida Ammi ba ta nan.
Ta zauna ta dinga rizgar kuka ita kaɗai a gida.
Amira kuwa zama tai tana kuka, saboda tashin hankali.
Imran yace "Amran ɗina meye kuma na kukan baki da lafiya fa"
"Ka mari Minal, kasan Ammi zata zo, zamu fuskanci fushinta"
"Amira, na gaji da cigaba da jin ana jifanki da munanan kalamai, nafi kowa sanin ke ba karuwa bace, dan haka zanyi iya yina a dena kiran ki da wannan sunan"
Girgiza kai tayi tace "Amran na riga naiwa kaina tabo"
"No zan goge tabon nan da kaina insha Allah, my wife is not prostitute"
Yai maganar yana goge mata hawaye, seda ta dena kukan sannan ya ƙyaleta.
Ihsan kuwa kamar za tayi hauka, ganin Imran ya mari Minal saboda Amira, kuma gashi itama ya fara mata kashedi.
Gaba ɗaya hankalinsa ya koma kan Amira.
Abunda ya farun ya hana Amira bacci sam, ga wani zazzaɓi da ya rufeta, gaba ɗaya ta rasa meke mata daɗi, gashi a lissafinta yau ba kwananta bane, balle Imran yazo ya ɗan lallaɓata ta samu tayia bacci.
Fitowa tayi babban falo, tai sa'a Imran yana kwance yana kallon ball, aikuwa ta ƙarasa inda yake ta zube a jikinsa.
Da sauri yace "subhanallah, Amrina lafiya kuwa, wannan zazzaɓin fa?"
Shiru tayi tana juya kanta a ƙirjinsa.
"Ko mu tafi Asibiti ne?"
"No"
"Jikinki yai zafi da yawa, ko in shafa miki ruwa?"
Ta jinina masa kai alamae eh.
Ta tashi zaune, yaje ya ɗebo ruwa a wata roba, da ƙaramin towel, yazo ya zauna a kusa da ita.
Ya zare rigar jikinta, ya shiga jiƙa towel yana shafa mata a jikinta.
Ihsan kuwa yau kasa jurewa tayi, duk da haushin Imran da take ji, ta miƙe ta tafi ɗakinsa, amma baya ciki.
Da sauri ta nufo falo, tana zuwa tai tozali da baƙin gani a falon.
Take ta zunduma uban ihu, wanda yasa Imran saurin sakin Amira suna kallon Ihsan.
"Wallahi se na kasheki, ni zaki yiwa haka? Ni zaka ciwa amana, wallahi sena ga bayan ku, nafi ƙarfin aci amanata, wallahi sena miki illa"
Tayo kan Amira gadan gadan tana ihu, Imran ya tare ta, yace "wallahi ba zaki taɓata ba, me tai miki? Tunda kin watsar dani kince ba kya sona, ai ba laifi bane dan na koma gurinta, tunda Allah yasa bake kaɗai nake Aure ba"
Ranar dai babu wanda yai rintsawar kirki, saboda bala'in Ihsan ga Amira ba lafiya, haka ta dinga masifa a daren nan maƙota naji.
Da sassafe Imran ya taya Amira ta shirya ze kaita Asibiti, sedai suna zuwa falo suka tarar da Ammi ga Ihsan da Minal.
"Sannunka ɗan banza mara mutunci, yanzu Imran ni zaa kaiwa haka, ka nunamin ban isa ba? Ka fifita karuwa akan matarka da ƙanwarka, ka mararmin Minal, Imran kana tsoron Allah kuwa? Wato kasa ƙafa kai fatali da sharaɗin da na gindaya maka ko?"
"A'a Ammi ba fatali nayi da maganarki ba, dan Allah ki tsaya ki saurareni in miki bayani"
"Bayanin ubanka zakamin, ka fara bijiremin saboda 'yar iska karuwa..
Kan Ammi ta rufe bakinta, Amira ta fara sheƙa amai a gurin 😲😲😲
Domin gyara, sharhi ko Shawara
Ayshercool
07063065680.
[2/16, 8:15 PM] Ayshercool: 🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥
WUTA A MASAƘA
PERFECT WRITERS ASSOCIATION
(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS)
https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
P. W. A
*Story and written by*
AISHA ADAM (AYSHERCOOL)
The experience writer of
*ABDUL JALAL*
* WATA KISSAR.... (SAI MATA)
*BAƘIN TABO (Labarin gasa)
*AƘIDATA (Paid Book)
* WUTA A MASAƘA
https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=in
❌❌❌
Ƙirƙirarren labari ne, ban yadda ayi amfani da kowane sashi na labarin ba ba tare da izinina ba.