Showing 51001 words to 54000 words out of 120332 words
Chapter 18 - WUTA A MASA?A COMPLETE HAUSA NOVEL BY AYSHERCOOL
yanke hukunci da nayi ba tare da izinin ku ba a matsayin ku na dangin mahaifinta, nayi hakane badan in muzanta ku ba, sedai nayi hakan ne saboda sanin halin ita Amiran, muddin tasan da Maganar Auren zata iya bijirewa hakan, na duba naga Aurar da Amira ga Imran ita kaɗaice masalaha, wadda zata hanata rashin jin da takeyi, shiyasa na sama mana sauƙi ni da ku, kuma bana buƙatar komai daga gareku, yanzu haka komai da iyaye sukewa 'yarsu nayi mata, na sai komai ina jiran seta kusa tarewa sannan aje a shirya mata ɗakinta, ku kwantar da hankalinku dan Allah"
Yadikko tai maza ta fizge wayar tace "Amma fisabilillahi ranka ya daɗe baka kyau mana ba, dan akwai wanda mukayi wa alƙawarin bawa Auren Amira, amma kawai semuji ka aurar da ita, ka maida mu ƙanan nan mutane"
Abba yace "Subhanallah, ai ban sani ba, baku taɓa gayamin cewar Amira tana da manemi ba, da kun gayamin tunda fari ai da se a san abunyi tun a lokacin amma yanzu bakin alƙalami ya bushe, kuyi haƙuri ku bawa wancan ɗin haƙuri"
"Koma dai meye mutuncinmu ya zube mun zama masu Magana biyu, ƙirƙiri mun yiwa wani alƙawari amma mun gaza cikawa"
"Ai nace kuyi haƙuri, ni idan nazo ku haɗani da shi in masa bayani nasan ze Fahimta"
"Banji daɗi ba gaskiya, ace yaro kamanme kamar wannan yaron ka aira masa wannan yarinyar, bayan ga mata nutsatstu kamanmu har tayin jikokina nai maka, amma kace zeyi Aure, kawai se naji haɗashi da Amira Yarinyar da kwararo kwararo ba inda bata zuwa bin Maza"
Abba yace "Subhanallah, abar maganar nana dan Allah, ya riga ya wuce insha Allah ya zama tarihi, Insha Allah shiriyarta ce tazo a sanadin Auren nan" be jira me zasu kuma cewa ba ya kashe wayarsa.
Kwanan Ihsan uku a gidan Imran, amma sam taƙi amincewa Imran yaje inda take balle wani abu yafaru, dan fafur take nuna masa bata ta tasa yanzu.
Da daddare bayan sallar isha'i Imran yana falo yana kwance yai shiruu, ya rasa abunda yake masa daɗi, message ɗin Abba ya shigo wayarsa.
"Ku buɗen ƙofa, ina ƙofar gidanka"
Imran ya tashi da sauri ya tafi gate, yana buɗewa yaga Abba, murmushi Imran yai yace "Abba sannu da zuwa"
Abba yace "Yawwa Ango"
Imran yai masa jagora har cikin gidansa, a falo Abba ya zauna suka gaisa da Imran.
Abba yace "Ina 'yar tawa take?"
Imran yace 'bari in kirawo ta"
Jiki a sanyaye ya tafi ɗakin Ihsan, tana zaune a gefen gado yai Sallama, daƙyar ta amsa masa a ciki, Imran yace "kizo ga Abba yazo, yana son ganinki a Falo"
Ba tace masa komai ba, ta miƙe ta saka hijjabi ta bishi falon, fuskarta ba yabo ba fallasa haka ta gaida Abba.
Abba ya amsa cikin kulawa, nan yai tayiwa Ihsan nasiha tare da bata haƙuri akan abunda akayi mata, nayi mata kishiya ranar Aurenta ba tare da saninta ba, yaita mata Nasiha yana rarrashin ta.
Daga ƙarshe yace Imran ze rakashi unguwa, ba daɗewa zasuyi ba.
Imran ya tashi yabi Abba, ya rufe Ihsan ta waje, ya shiga motar Abba, Suka tafi.
Suna tafe a hanya Abba yace "Imran ka sake duba ya jikin Matarka kuwa? Bana jin kota waya ka kira kace ya jikinta? Imran ina sake jan kunneka da kaji tsoron Allah akan riƙon da zakayiwa marainiyar nan, kayi adalci a tsakaninsu, tunda baka san yakamata ba shiyasa nace ni bari inzo in ɗaukeka muje a sake duba jikinta"
Imran yai shiru ya cigaba tuƙinsa.
Suka isa gidan Alhaji Hashim, sukai parking sannan suka shiga, a falo suka tsaya sukai Sallama akayi musu izinin shiga.
Anty na ganin Abba tare da Imran tace "gaskiya munyi fushi, fushi muke daku irin sosai ɗin nan, haka akeyi ai mana laifi amma ba ban haƙuri ba dubiya ko ta waya"
Abba yace "tuba muke, Allah ya bada haƙuri"
Alhaji Hashim ne ya shigo falon yana faɗin "Ƙyalesu zamu haɗe a Human rights tunda abun hakane"
Abba yace "wannan kuma kai da shi, ɗanka ne yai maka laifi bani ba"
Suka zauna suka gaggaisa, suka ƙara yiwa Imran Allah ya sanya Alkhairi, Abba yace "ina Amiran ne? Ya jikin nata?"
Anty tace "'yar tawace akwai zuciya, ta bi ta damu kanta ba irin rarrashin da bana yi, amma ta damu kanta da koke koke, ga zazzaɓin nan ko sauka bayayi saboda damuwa, ina tsoron ta jawa kanta wani ciwon"
Imran a ransa yace 'ni banyi kuka na sa abun a raina ba se ita, se taje taita yi ai"
Abba yace "Yasalam, nasan a rina ai, yanzu tna ina?"
Anty tace "Imran shiga ka taso ta tana ɗakin kusa da dining"
Imran kamar yace baza shi ba, haka ya miƙe ya shiga ɗakin da Amira take, tana zaune akan gadon, ta rame sosai mussaman a fuskarta, ya ƙarasa cikin ɗakin gaban gadon da take, ɗago idonta tayi ta harareshi sama da ƙasa ɗauke kanta, se a lokacin ya lura da raunin dake gefen idonta, da tabon hannayenta da suka fara baƙi, a lokacin ya tabbatar da dukan da yai mata bana wasa bane.
"Kizo ana nemanki a Falo"
Ko gezau ba tayi ba balle ta motsa.
"Ba kyaji ina miki Magana?"
Kawai ta shige cikin bargo tai kwanciyar ta, wani takaici ya ƙule Imran, yana mata magana amma ta maida shi wani banza, kawai ya hau kan gadon ya janyota, aikuwa ta ware muryarta tace
"Wayyo Allah ciwona! Dalla ni Ka cikani".
Cikata yai da sauri yana kallonta da mamaki, Wannan ai salon Ace wani abun yai mata ne.
Muryar Anty suka jiyo tana "Imran me kake mata ne? Kar muyi haka da kai fa"
Amira kuwa hararasa tayi, ta sakko daga kan gadon ta fito falon, haka nan cike da kunya da takaici ya shima ya biyo bayanta, a ƙasa ta zauna ta sunkunyar da kanta tace "Abba ina wuni"
"Lafiya ƙalau Amira, Amira haka zamuyi dake, kalli yadda kika rame fa, meyasa?"
Aikuwa kamar ya fama mata inda yake mata ƙaiƙayi ta fashe da kuka tace "Abba ni bana son Auren nan, dan Allah a maida ni gida"
Imran ji yayi Kamar yai tsaki, amma ya daure.
Abba yace "haba Amira, ba muyi miki Auren nan dan cutar dake ba, kiyi haƙuri ki kwantar da hankalinki kinji, Muna so ki samu lafiya da wuri ki Tare a ɗakinki, Insha Allah Imran ze kula dake"
Alhaji Hashim ya ciro sadakinta dubu hamsin a aljijunsa, ya miƙawa Imran yace ya bawa Amira.
Ya karɓa ya ajiye mata akan cinyarta, Amira ta ɗago idanunta da suke ta zubda ruwa ta gallawa Imran harara, ji take tamkar tai masa Allah ya isa ta huta.
Akai tayi musu Nasiha ita da Imran, sedai daga ita harshi ba wanda ya maida kai akan abunda ake gaya masa, kowa da abunda yake saƙawa a ransa, suka gama aka sallami Amira, ta miƙe zata tafi ɗaki Kuɗin jikinta suka zube ƙasa.
Alhaji Hashim yace "Zoki tafi da kuɗin mana, naki ne haƙƙinki ne"
Amira ta durƙusa ta ɗau kuɗin kawai ta tafi jikin Anty ta ajiye mata kuɗin a jikinta, Anty ta rungume Amira ta cigaba da rarrashin ta, wato Amira sam bata gajiya da kuka.
"Anty ni wallahi irin mijin Anty Fa'iza nakeso, wallahi wannan Imran ɗin cin zalina ze dingayi".
Alhaji Hashim yace "A'a baze ci zalinki ba, Yayanki ne fa yana sonki ze kula dake sosai, Imran rakata ɗaki taje ta kwanta"
Ya rasa meyasa aketa wani sake cuso masa Amira, Anty tace "tashi kije kuyi sallama"
Tana tashi tai gaba abunta bata jira Imran ba, Imran yabi bayanta dan ba yadda zeyi.
Suna zuwa ɗakin ya ƙarasa da sauri ya cinmata, ya kalleta yace "Ni kike cewa zan ci zalinki a gaban su Abba saboda makirci ko?"
"Dukan da kayi min Adalci ne? Ka dinga dukana ka ƙyale ƙanwarka wallahi Allah yana kallonka"
"Allah ya isa kike min kenan?"
'"ni ban maka Allah ya isa ba"
"Ƙarya nake kenan?"
Ta girgiza masa kai, ya ƙare mata kallo daga sama har ƙasa yai tsaki ya juya ya fita.
Domin Sharhi, gyara Ko shawara
Ayshercool
07063065680.
[1/23, 4:41 PM] Ayshercool: 🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥
WUTA A MASAƘA
PERFECT WRITERS ASSOCIATION
(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS)
https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
P. W. A
*Story and written by*
AISHA ADAM (AYSHERCOOL)
The experience writer of
*ABDUL JALAL*
* WATA KISSAR.... (SAI MATA)
*BAƘIN TABO (Labarin gasa)
*AƘIDATA (Paid Book)
* WUTA A MASAƘA
https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=in
❌❌❌
Ƙirƙirarren labari ne, ban yadda ayi amfani da kowane sashi na labarin ba ba tare da izinina ba.
25_26
Imran na fita Amira Tayi tsaki, ta kwanta akan gadonta taja bargo, kwata kwata da ta tuna dukan da Imran yai mata se taji ta tsaneshi bata ƙaunar ganinsa.
Imran kuwa a harabar gidan ya tarar dasu Abba, sukayi Sallama dasu Alhaji Hashim suka tafi.
Suna dawowa cikin gidan, Anty Nafisa ta tafi ɗakin Amira, tana shiga tai sallama Amira ta amsa, Anty tace Amira tashi zaune Magana zamuyi.
Amira ta tashi zaune, Anty ta zauna kusa da Amira tace "Amira wace irin sallama kukayi da mijinki ne?"
Amira tace "mijina kuma?"
"Eh mijinki Imran mana" ita Amira mantawa take wai Imran yanzu mijinta ne, idan ma aka faɗa se taji wani banbarakwai.
Maimakon ta bata amsa se tayi shiru ta sunkuyar da kai.
Anty tace "Amira, duk da Imran ba sonki yake ya aureki ba kefa zaki nemo soyayyar nan da kanki"
Ɗan tura baki Amira tayi a ranta tace "ji wata Magana mara ma'ana, ni zan bishi ya soni lallai"
"Ki dena tura baki, kamar yadda na gaya miki ke zaki nemo soyayyar nan da kanki, sannan karki kuskura ki kuma ce masa mugu, ko yana cin zalinki yanzu mijinki ne shi, ki manta da abunda yafaru gaba ɗaya, ki fuskanci rayuwarki, banda gaya masa baƙar magana ko abunda ze tunzurashi, ko kin fiso ya sakeki ki zama ƙaramar bazawara?"
Ba Kunya Amira ta ɗaga kai alamar eh, "au kin fiso ki zama bazawara, ya sakeki?"
Amira ta kuma jinjina mata kai alamar Eh.
"Lallai Yarinta na ɗawainiya dake, amma meyasa kike so ya sake ki?"
"Ni wallahi ba irinsa nake so in aura ba, bashi da tausayi"
"To ke wane iri kike so?"
"Irin mijin Anty Fa'iza nake so"
Anty tai murmushi tace "wane iri ne wai wannan mijin na Anty Fa'iza?"
Amira ta gyara zama tace "kinga fa shi mijin Anty Fa'iza yana lallaɓata sosai, gashi da sauƙin kai, yana da matuƙar haƙuri, kuma yana son yai abunda ze burgeta, gashi da fara'a da yawan murmushi, amma ba irin wannan Imran ɗin ba da ko dariya bayayi"
Wani ƙasaitaccen murmushi Anty tayi, ta fuskanci Amira 'yar soyayyace tafi son wanda ze dinga lallaɓata yana biyewa taɓararata.
Ta kalli Amira tace "Ai baki san wani abu ba, sufa maza tamkar yara suke a gurin mace, duk yadda kika so zaki sarrafa su, amma bata ƙarfin tuwo ba ta hikima da rarrashi, idan kin so seki maida Imran ɗin irin yadda kike so"
"Taɓ, wannan sarkin hantarar baze taɓa zama irin Mijin Anty Fa'iza ba, inaga irinsu basu da yawa ma a duniya"
"Ke waye ya gayamiki haka, kiyi tayiwa Imran Addu'a, ze zama irin yadda kike so insha Allah kinji yarinyar kirki"
Amira ta gyaɗa kai ba dan ta gamsu ba, Anty tace "naga tunda kika ga Imran harkin ɗan sake, anya ba zamu tataraki mu kaiki ba?"
Ɗan zaro ido Amira tayi tace "a'a ni kawai na ɗanji ƙwarin jikina ne, ba zuwan sa bane, in dan zuwansa ne bakiga yadda ya janyo ni akan gadon nan ba kamar wata kaza"
Dariya Anty tayi tace "bari in aiko Fadila ta kawo miki ko tea ne ki sha, seki samu ki sha magani"
Fadila ƙanwar Alhaji Hashim ce, Aurenta ya mutu ta dawo nan gidan da zama.
Amira tace "Aa karki sata aiki, bari inzo in karɓa"
"Meyasa zaki ce kar in sata aiki, ƙanwata ce fa"
Amira tace "Ai ta girmeni, be kamata ina zaune tayimin abu ba"
Anty ta ɗan yi shiru tana nazartar Amira sannan tai murmushi tace "tashi muje Kitchen ɗin tare, ai nafison in ga kina tattakawa jiki yana ƙara ƙwari"
Amira ta sakko daga kan gadon tabi Anty, tunda Aka kawo Amira gidan yaune ranar farko da ta ɗan saki jiki da Anty haka, har sukayi doguwar magana, amma da ba ruwanta dasu sam.
Imran da ya koma gida har Ihsan tayi bacci, ya wuce ɗaya ɗakin yai wanka, ko ta kan Abinci baya bi, dan sam baya jin daɗin komai a bakinsa, ya bi lafiyar gado ya kwanta, sedai fara baccinsa ke da wuya Amira ta dinga masa gizo a cikin bacci, ya dinga mafarki da ita,farkawa yayi a hankali hankali ya buɗe idonsa, ya ɗakko wayarsa ya ga ƙarfe biyu da rabi na dare.
Ya ajiye wayar yai shiru yana tunani, ya daɗe yana jiran ranar daze zama inuwa ɗaya da Ihsan dan nuna mata irin ƙaunar da yake mata, sedai kash ranar tazo masa da ƙalubale, be samu damar cika burinsa ba, Amira tayi kutse a ratuwarsa ta kassara komai, haka ya cigaba da juyi akan gadon nan, yana tunani ta ina ze ɓullowa al'amura, ga Ihsan sam taƙi saurararsa, miƙewa yai zaune a hankali ya sakko daga kan gadon, ya buɗe ƙofa ya nufi ɗakin da Ihsan take.
Ya tura ƙofar a hankali, ɗakin ya gauraye da duhu, ya kunna fitilar wayarsa ya hangota kwance tana bacci, a hankali ya taka yaje ya hau kan gadon da take, ya kwanta ya hasakata da fitilar ƙaramar wayarsa zubawa kyakkyawar fuskarta ido, wadda tai fayau saboda kuka da damuwa.
A hankali ya matsa inda take, ya janyota jikinsa, kamar a mafarki Ihsan taji Imran a jikinta, a zabure Ihsan ta farka tana neman ta kurma ihu, ta dire daga kan gadon nan da sauri tana zazzare ido.
"Ihsan meye hak? Nine fa Imran ne kina nema kimin ihu a daren nan"
"Akan me zaka zomin ɗaki ban sani ba, kawai ka fara rungumeni haka akeyi?"
"Dama na Aureki ne dan inzo mu dinga kallon juna? Ihsan meyasa haka ne? Ina tarin ilimin addinin dana sanki dashi?"
"Idan ba Aurena kayi dan ka kalleni ba, ai naga bani kaɗai ka Aura ba, kaje gurin karuwar da aka aura maka mana, dan Allah Imran ka ƙyaleni ni babu wani sauran abu ko fahimta daya rage tsakanina da kai, ka ƙyaleni inyi jinyar zuciyata akan yaudarar da kaimin"
Maganganun Ihsan sun ɓatawa Imran rai matuƙa, ya ƙare mata kallo tsaf, dudu Ihsan idan yai niyya duk Wani abunta baze hana shi abunda yai niyya ba, sedai baya son cutar da ita, ya rasa wace irin zuciya ce da ita haka, yadda sukai soyayya be taɓa tunanin dan wani abu ya gifta na ƙaddara zata masa haka ba.
Be ce mata uffan ba, ya ɗauki wayarsa ya fita ya bar mata ɗakin, saboda tsabar takaici a Falo Imran ya kwana, ya rasa abunda yake masa daɗi, ana Aure a samu nutsuwa da kwanciyar hankali, amma shi banda damuwa ba abunda ya fuskanta a Auren.
Ƙarfe tara na Safe Ihsan tana can tana baccinta, ya shirya ya fice ba tare da yabi ta kanta ba, be zame ko ina ba se gidan su Khalid.
Yaje ya tarar da Khalid yana breakfast, Khalid na ganinsa ya fara murmushi "Angon biyu, Kai angwaye na ƙyalli suyi ƙiba kaikuma naga kamar ramewa kayi, lafiya kuwa?"
Imran kawai ya nemi guri ya zauna yai shiruu, yama rasa ta ina ze fara.
"Kayi shiru, ko da akwai matsala ne?"
"Khalid a satin nan zan koma gurin aiki insha Allah"
"Kamar yaya zaka koma gurin aiki? Harka gama hutun angwancin ne?"
"Wane hutun angwanci Khalid? Na rasa mema zanyi inji sanyi a raina, gara in nesa da Ihsan, kwata kwata taƙi saurarata, ta sawa kanta damuwa da tashin hankali akan Amira, taƙi saurarata taji wani uzuri daga bakina gaba ɗaya, jiya Abba yasani a gaba wai dol se munje mun duba Amira, itama mukaje ta cazamin Kai, se koke koke take wai an Aura mata Mugu, ni dana san hakane da tunda fari banyi Auren nan ba, gara in nesa dasu in bar musu garin, suje su ƙarata"
Khalid ya ɗanyi murmushi yace "Imran kenan, tun yanzu fa kenan, ina ga in Amira ta tare suka zama su biyu, a gaskiya Ihsan ta bani mamaki sosai, ban zaci za tayi maka haka ba, amma ka sake bata chance kayi haƙuri kasan tana da matuƙar kishi sosai, amma ka jinkirat tafiyar nan ko zaku daidaita"
"Khalid ba abunda zan jinkirta, Insha Allah bakin aikina zan koma suje su ƙarata, zan nunawa Ihsan ko babu ita zan iya rayuwa saboda na fuskanci kamar lallaɓata da nake ne yasa take nema ta wulaƙanta ni, dama ita waccan bata tata nake ba, da ita da babu duk ɗaya"
"Kaga Imran ina rabaka da nuna halin ko in kula ga Amira, karka bari ta gane kana ƙinta, in ba haka ba ba ruwana, karkazo nan gaba Allah ya jarabceka da soyayyar ta"
"Soyayyar wa, wannan mara Kunyar banzan fitsararriya, kai kaga abunda ta dingayi jiya, bata da ta ido sam, a gabana take cewa bani da imani, zataga rashin imani kuwa"
"Ita wannan da ta san kai me Imani ne kake kyautata mata ai gashi tana baka wahala, itama Amiran dan baka janta a jikine yasa take maka kallon mara Imani, kuma ga yadda kake treating ɗinta babu tausayi, dole tace baka da imani ai"
Imran ya miƙe yace "malam niga mota ta nan zan bari a gidanku, zan ƙarasa gida inje ɗakin in huta, bana son Abba yasan nazo"
Khalid yace 'Yadda kace Angon biyu"
Imran be kula shi ba yai waje, gidansu ya nufa kai tsaye, yana zuwa ya wuce sashensa yai kwanciyar sa ba tare da kowa yasan yaje gidan ba.
Jikin Amira da sauƙi sosai, ta tashi tai wanka ta canza kaya a cikin wanda aka bata, ta fita falo seda ta gama ƙarewa falon kallo, sannan ta nufi inda Kitchen yake, ta tarar da Fadila nata aiki tana ƙoƙarin haɗa abun karin kumallo ita da Me aikin gidan.
Amira tace "Anty Fadila ina kwana?"
Fadila ta kalli Amira da fara'a tace "Alhamdilillah, 'yar gidan Anty jiki yai sauƙi, ya ƙarfin jiki kuma?"
"Alhamdilillah, naji sauƙi sedai ina kewar gida sosai"
"Allah sarki, haka Aure yake Amira ki kwantar da hankalinki zaki saba ne"
"To wai a nan zan ta zama?"
Fadila tace "A'a haba dai, kin matsu ki tare a gidanki ko?"
Amira ta zare ido tace "rufamin Asiri, kawai tambayarki dai nayi"
"Ba a nan zaki zauna ba, zaki tare a gidanki nan da wani ɗan lokaci insha Allah"
Amira ta ɗan taɓe baki tace "ni dama