Showing 57001 words to 60000 words out of 120332 words

Chapter 20 - WUTA A MASA?A COMPLETE HAUSA NOVEL BY AYSHERCOOL

10 Mar 2025

30367

  🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥

WUTA A MASAƘA

PERFECT WRITERS ASSOCIATION

(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS)

https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P. W. A

*Story and written by*
AISHA ADAM (AYSHERCOOL)

The experience writer of

*ABDUL JALAL*
* WATA KISSAR.... (SAI MATA)
*BAƘIN TABO (Labarin gasa)
*AƘIDATA (Paid Book)
* WUTA A MASAƘA

https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=in

❌❌❌
Ƙirƙirarren labari ne, ban yadda ayi amfani da kowane sashi na labarin ba ba tare da izinina ba.

   






                     27_28

Imran kam seda ya ƙarewa wayar kallo, tare da jinjina kalmar Yayana da Amira ta kirashi da shi, yasan wani sabon iyayin ne yasa ta faɗi haka, wani gajeren tsaki yaja, ya ajiye wayar ya cigaba da aikinsa.

Amira kam tunda ta shige ɗakin nan bata sake fitowa ba, ta zauna ta dinga saƙawa tana warwarewa, tana tunanin irin zaman da za tai a gidan Imran, daga Imran har matarsa da danginsa babu me ƙaunarta.

Imran kam ya samu nutsuwa sosai, hankalinsa a kwance yake sosai, cin amarcinsu kawai suke da Ihsan.

Yana kwance yana kallo, Ihsan ta fito tana yamutsa fuska, ya kalleta yace "My beb, ya dai naga kina ɓata rai?"

Ƙarasowa tayi ta kwanta a jikinsa tace  "yau bana jin daɗin jikina gaba ɗaya"

Murmushi yai ya shafa dogon gashinta yace  "kodai kodai?"

Ihsan tace "kodai me?"

"Ko an gamune, kin sama mana Baby?"

Gaban Ihsan ne ya faɗi, a ranta tace ji wata Magana, daga yin Auren se maganar ciki.

"Ya naji kinyi shiru ne?"

"My, daga yin Aurenmu se ciki kuma, ko gama cin amarcin banba se ciki, kasan fa ciki yana bawa mata wahala sosai"

"To meye a ciki Ihsan? Ai Arziki ne da yawa suna nan suna nema basu samu ba, ina fatan Allah yasa ciki ne, ko biyu ki haifamin sekiyi planing ki huta"

"My D Service ɗina fa?"

"Bakomai, Allah baze hana mu yadda zamuyi ba, Allah ya bamu masu albarka"

Yai maganar yana kissing goshinta, murmushi kawai tayi ta rungumeshi sosai ta lula duniyar tunani.

Amira ta kai kwana biyu kafin ta sake sakin ranta, dan duk batun Imran ta dameta, Anty kuma tana ankare da ita, ta tausaya Amira matuƙa, ta fuskanci Amira nada kishin gaske sedai kuma ta iya siyasa sosai da sosai.

Amira tana cin Abincin Safe tana ta cakala, ba wani ci take sosai ba, Anty tace "Amira, anjima ki shirya zamuje kasuwar, idan yaso gyaran kan gobe in Allah ya kaimu se Fadila ta rakaki"

Amira tace "to Anty, bari in gama se in fara shiri"  ta kammala cin Abincin, amma maimakon ta tashi seta ɗakko wayarta ta kira layin Yadikko, amma bata tafiya, seta kira ta Usman.

Seda ta kusa katsewa sannan ya ɗaga yai Sallama.

"Yaya Usaman manyan gari, ko nemana ma ba'ayi ko, wato Allah ya rabaku dani babu me neman inda nake, bakomai rayuwa ce"

Usman yace "Ni mamakine ma ya kamani a ina kika samu lambata?"

"Ji wata tambayar rainin hankali, dama can ina da ita ai"

"Kina da ita amma baki taɓa kirana ba ai, kuma wake da lambarki a gidan nan? Ba wanda yake da lambar ki"

"Hmm duk da haka wannan ba uzuri bane, ai da kukaji labarin Aurena haka ba shiri, kwace bari kuji ya wannan marainiyar take ciki, meyakamata ayi mata? Koda yake ai ba sona kuke ba, nice dai duk inda na shiga kuna raina, yanzu ya kake ya gidan?"

"Lafiya ƙalau Alhamdilillah, ya amarci ina mijin naki?"

"Yana Lagos gurin aiki"

"Naji ance ai baki tare ba ko?"

"Eh ban tare ba, amma nakusa insha Allah, Ina su Sadiya da Yadikko uwar faɗa"

"Kowa lafiya ƙalau"

"Kai musu wayar mu gaisa, na kira ta Yadikko bata shiga"

'to bari in kai musu"

Ya shiga cikin gidan da wayar a hannunsa, ya tarar da Yadikko na shan koko da ƙosai, ya miƙa mata waya yace "gashi za'ai magana dake"

Ta kalleshi tace "waye?"

"Karɓi kiji mana"

Yadikko ta krɓi waya ta saka a kunnenta.

"Hajiya Yadikko me abun mamaki, ba faɗa meya kawo gaba? Har labarin Aurena ya riskeki amma ki gaza nemana, ko kice ya nake ciki?

"To in nemeki ince miki me? Ko in miki me?"

"Ba abunda zakimin, amma ko yaya ai kyanuna kin damu dani, amma dai shikenan ya kuke yasu Baba da kowa da kowa?"

"Ji yadda kike wani tambaya ya suke, irin kin damu dasu ɗin nan, aifa kin damu dadu da baki haɗa kai da wan uwarki anmiki Aure ba izininmu ba"

"To ni meye nawa a ciki, yadda baku san da labarin Auren ba nima ban sani ba, sama taka naji wai an ɗauramin Aure da Imran"

Yadikko tace "to amma kuma kika zauna? Aida seki ce masa bakya son sa, akanme za'a miki Auren dole, ni kik ban mamaki m, ina bakin nakinda tsiwar taki, da har zaki bari a miki Aure ba saninki kuma ki zauna kiyi shiru?"

"To Yadikko idan ban zauna nayi shiru ba me kike son inyi?"

"Ai irin haka ski ce masa bakya so, ko kina son Imran ɗin ne? Ina kwanaki har nan gida yazo ya sameki ya dinga tamaula dake a gidan nan, kuma nan akazo aka bania labarin ana gibe ɗaurin Aure ya kamaki ya zane, to da irin wannan zaki zaman Aure, ai irin haka kamata yayi ki gayawa babansa bakya son sa"

Amira tai murmushi tace "Yanzu Yadikko, kawai se in dubi tsabar idon Abba ince masa bana son ɗansa, to ai duk isaknacina wasu lokutan nasan abunda yakamata da wanda be kamata ba"

"To Yanzu dai zama zakiyi dashi kenan? Ya dinga muzguna miki yana dukanki? Nifa da cewa nayi ko ƙararsa zamuyi, ya Aurar dake ga ɗansa ba izininmu, kuma ɗan nasa ma har dukanki yakeyi dan a ƙwatar miki haƙƙin ki, idan yaso ko raba Auren ne ayi, ki fito ki auri wanda kike so yake sonki"

"Taɓɗijan aikuwa da kun kai ƙara da kunji Kunya, dan bazan yadda a kashemin Aure ba, kinga kajin da nake ci kuwa, Allah ya hutar dani ya rabani da Karuwanci da kuke faɗa ya rufan Asiri in tonawa kaina, ai ba dani ba, zamana zan in lumui a gidan, koda ze dinga dukana kuwa, balle ba duka ba zagi tsakanina dashi, lallaɓani ma yakeyi, kin san Karuwa da shiga rai, mussaman yadda na goge a iya duniyanci, nan komai available baki ga da kazar dana karya ba yanzu haka, ga shayi me kauri falo da AC, ga luntsumemen gado, anjima in tashi in saka matsatsun kaya, koma tsirara in taka masa rawar gala a gabansa ya kalleni yana murmushi, yaushe zan yadda amin sagegeduwa, an rabani da bin kwararo da wannan gidan namu gidan tashin hankali, aini Allah ya rufan Asiri, su Sadiya ma ina musu Addu'a Allah ya ɗaga su daga wannan gidan ko dan tijararki"  Amira tai maganar tana wani makirin murmushi.

"Yanzu Amira ni kike gayawa, kina rawar gala tsirara a gaban miji?"

"Au nayi a gaban wasu banzaye ma balle mijina, meye amfanin ƙirar da Allah yaimin in dai bazan juyasu a inda ya dace ba, gari banza ma naje nayi an min liƙi, balle yanzu da nake me dalili na ibada"

Yadikko tace "Amma kuwa idan hakane wannan Imranan munafuki ne, yaita nuna yana jin haushinki, baya ƙaunarki amma ya aureki, harma ya saki jiki dake?"

"Au kina mamakine Hajiya Yadikko, Amira ce fa ai bari kawai wani abun baze faɗu a waya ba, kusa lokacin da za kuzo kema kici kajin nan da nake ci, da ina kusa da sena dinga aiko miki ki adana tsufanki, yanz idan nace na gaji da naman kaza, anjima Imran ze aiko da na zabi, aini Alhamdilillah Allah ya 'yanto ni"

Wani irin baƙin ciki ne ya tikare zuciyar Yadkko, wato Amira ma jin daɗinta takeyi, taso ace tana can tana wahala amma taji saɓanin haka.

"Yadikko ya naji kinyi shirune? Ki gaida Mutan gidan gaba ɗaya, zanje in ɗorawa Mijina sanwar rana"

"Amma naji kina da kishiya ko?"

"Eh, ina da kishiya mana"

"Kuma lafiya kuke zaune da ita?".

"Ai ba ruwan wani da wani nida ita, kowa zaman kansa yakeyi, Yadikko se anjima, zanyi girki in gyara jikina, sannan Anty Fa'iza zata zo ta ɗebar min kayana na nan gidan Please, duk abunda aka san nawane kar a taɓamin"

Amira ta katse wayar, ta ɗan tsurawa wayar ido, wasu hawaye suka cika idonta, ta rasa meyasa Yadikko bata son ganin duka wani abu na cigaba ya raɓeta, ta fison ta ganta a wahala da tashin hankali, tafi son taga ta wulaƙanta, sama batayi murna da jin abunda Amira ta faɗa ba, so tai taji Amira tace tana cikin wahala.

Amira tace "ya Ubangiji Allah, ka jiɓanci lamurana, kaimin ɗauki akan zaman da zanyi a gidan Bawan Allah nan, Allah karka kawo dalilin da zesa maƙiya suga hawaywna ko su ganni a rana, Allah yadda suke ƙina kar bani ikon ƙinsu ko cutar dasu, Allah ka shiryesu ka ganar dasu ka maida su kan tafarkin ka madaidaici" ta ƙarasa addu'ar a hankali cikin karaya.

Yadikko kuwa cewa tai "ni ungo wayarka, munafukar yarinya 'yar hau, ni zata kira ta gayawa daɗin Aure, dan ubanta tun kan a haifi uwarta nai Auren nan nima, amma dan fitsara harda gayamin tana zama tsirara a gabansa, yo aikin banza ma, tsirara nawa tayi a gaban ƙarti daban daban, shima shashasha soloɓiyo, namijin hotiho ya rasa wadda ze Aira se Wannan karuwar, dama tana tafiya tuɓi tuɓi da mazaunai ai dole su tsole masa ido ya Aureta, duk wannan hantarar da zagin da yake mata ahse kurin banza ne"

Amina tace "ai bazaki san kurin banza bane, se kinga irin shegen dukan da yayi mata daren da za'a ɗaura musu Auren nan, ya farfasa nata jiki da duka, ke bakyace Aurarta ze ba"

Sadiya tace "nifa ban yadda da abunda ta faɗa ba, wannan Yarinyar makirace maƙaryaciya, ya za'ai mutum yana sonkabya maka wannan dukan"

Amina tace "ke bar maza da gulma, kin san uwarsa fa ba son ta take ba, se iya dukan nata dan yai pretending, amma ai a ɗakinsa ta dinga kwana, kuma takanas yazo har garin nan ya ɗauke ta, ke ƙaddara ma baya sonta, Yarinyar da ta saba bik mazama, ina ga shi, shima barikin zata masa ya manne mata"

Yadkko tace "dan abun takaici, kalli koko nake sha babu ko sikri, ƙosan nan kamar a jefi gardi dashi dan tauri, shi kansa yajin ƙosan kafi zabi yasha babu maggin kirki a ciki, amma wai tana can tana cin kaza, kai Allah ya isa, yanzu da kuke Auren yaron nan, ai da ɗaki za'amin a gidan wallahi inje in tare nima in ɗan murmurw"

"Yanzu dai ki dena cin zarafin ƙosan nan, ki daure ki cigaba da tura abunki" cewar Aminaa.

"Ke barni ni takaici baze bari in ƙarasa cin wannan gardin ƙosan ba, 'yar banza Allah yasa duk lokacin da taci kazar taita zawayi, ya zamana ba ita ba cin kazar gaba ɗaya.

Haka Yadikko taita soko burutsunta, taita bayyana hassadarta ƙarara akan Amira, ba tare da kunya ko tsoron Allah akan hakan ba.

Amira kuwa wanka taje tayi, ta shiraya a cikin riga da skirt da dogon hijjabi.
Ta fito domin su tafi kasuwa, suna tafe a hanya suna hira, Anty tace  "Amira, me kike ganin za'a saimiki da sadakin ki ne?"

"Bakomai" ta bata amsa.

"Kamar yaya bakomai, ki faɗi me kike so, inya kama ayi ciko a saimiki, Abbanki ne yaimin waya yace a tambayeki"

"Nifa Anty kome kuka siya yayi shikenan"

"Ke a ranki babu wani abu da kikeso?"

"Eh, bana son komai ni dama ki riƙe na bar miki"

"Tunda tare zamuyi zaman Auren dake ko? Yarinya gara kici Sadakinki, Addini ne ya halarta miki abunki"

Amira bata sake cewa komai ba, ta dinga kallon titi da gurare, tana sake ƙarewa garin kallo har  suka kai wani ƙaton shagon saida kayayyaki.

Bayan sun isa ne Anty tace "muje duk abunda kike so ki ɗauka, banda alkunya naga wasu lokutan akwaiki da kawaici, An bada isashen kuɗi ayi miki siyayya"

Amira tace "to"

Suka shiga, sukayi siyayya sosai, suka taho hanya aka bada kayan Amira ɗinki, da wanda Antyn ta siya suka nufi komawa gida.

Misalin ƙarfe tara na dare, Ihsan ta gyara gado ta shiga wanka, ta fito sannan Imran ya shigo ɗakin, ya nemi guri ya kwanta yana kallon Ihsan tana shiryawa.

Ta kalleshi tace "ya da kallo hakane?"

"Au to kar in kalleki? Idan ban kalleki ba wa zan kalla?"

"Babu, gara kaita kallona"

Yai murmushi yace "yakamata ki tsahirata wannan shafe shafen, kizo ki kwanta haka"

"Ka barni in kinatsa a hankali kayi baccinka ban hanaka ba"

"Bazan iya bacci ba kya jikina ba"

Wani murmushi ta kuma yi masa sannan tace "to shikenan my D, gani nan"

Ta saka night gound ɗint, sannan ta nufo gadon tana masa murmushi, tana ƙarasowa ya janyota kan gadon yana murmushi yace "the beautiful lady my eyes ever saw in the earth"

"Kaji ka, duk kyawawan matan da suke garin nan?"

"Ihsan kawai idanun Imran ke iya hangowa, Ihsan ce kawai macen da Imran ke iya gani a cikin dubabbanin jinsin da ake kiransu da suna Mata"

Kalaman Imran suka dinga Ratsa kwanya da jinin jikin Ihsan, wayarsa ce ta fara ringing, yan ɗago wayar yaga My Dad, seda gabansa ya ɗan faɗi yai fatan Allah yasa lafiya.

Ya tattara dukkanin nutsuwarsa yace "Abba yana kira, bari in amsa wayar"

Ihsan ta jinjina masa kai, ta gyara kwanciyarta a jkinsa.

"Salamau Alaikum, Abba barka da dare"

"Yawwa barka, kuna lafiya?"

"Lafiya ƙalau Alhamdilillah Abba"

"Ya wajen aikin naka, ya Ihsan ɗin kuma?"

"Komai lafiya ƙalau Abba, ya aiki"

"Lafiya ƙalau Alhamdilillah, ai ban san da Ihsan ka tafi ba, munyi Magana da Hajiya Nafisa akan kayan ɗakin Amira, tace akwai buƙatar a bar wancan dana zaɓa a sauya da wani, ya danganta da tsarin ɓangaren Amiran, a samo kayan da zasuyi kyau, kasan sha'anin  mata da tsarabe tsarabe, wayarka bata shiga na kira ema inji ko kana gida yacemin ai baka nan daga kai har Ihsan ɗin, ina son jin yaushe zaku dawone? Za suzo su duba ɓangaren Amiran"

"Amm....amm Abba da ni cewa nayi, se Allah ya kaimu ƙarshen next month zamu dawo"

"No Amira zata tare before then, kuma ina son ka dawo kan lokacin tariyar, saboda su duba abunda zasu duba kana nan"

"To Abba, insha Allah za'ayi yadda kace, amma Abba nace meze hana ita Amiran ta zauna a gidana da zan zauna da farko, kowacce ta zauna gidanta daban?"

"A'a, ai nan gidanma yalwatacce ne, ze isheku karka raba kan iyalinka, ni anya makuwa kana kira kaji halin da take ciki kokuma kaji lafaiyarta?"

"Eh Abba, muna waya da Anty"

"Ba kana waya da Anty ba, da Amira ya kamata kayi waya tunda itace matarka, kaji lafiyarta tunda tana da hakki akanka"

"To Abba insha Allah, zan kira"

"Idan na tuntuɓa naji baka kira ba zan ɓata maka Imran"

"Insha Allah hakan ba zata faru ba, zan dinga kiran"

"To shikenan, ka gaisarmin da Ihsan ɗin dan Allah"

"To Abba zataji insha Allah"

Ihsan kuwa tuni ta bar jikin Imran, jin ana masa maganar Amira, da batun Amira zata tare, ta juya masa baya.

Imran ya ajiye wayar ya matsa kusa da ita yace  "My dear meyasa kika juyamin baya?"

Banza tai dashi kamar ba taji meyake cewa ba.

"Ihsan magana fa nake miki"

A ɗan hasale tace  "to me kake so ince maka? dan Allah ni ka ƙyaleni "

"Yanzu meye abun fushin kuma Ihsan? Ya kike son inyi, Abba ya haɗamin zafi kema ki haɗamin me kikeso inyi in bijire masa?"

Kawai Ihsan ta fara kuka, hadda sheshsheƙa.

Rungumeta yayi a jikinsa yace  "is Ok, na gane kiyi haƙuri in dai Amira ce ni ba ruwana da ita, ba dai gida bane tazo ta zauna, nike ce kawai mata ta ke nake so Ihsan, ni tsakanina da Amira ido, dan Allah karki ɗaga hankalinki kinji my wife"

Yai maganar yana share mata hawaye.

"Imran dan Allah ka riƙe Min amana, wallahi bazan iya jure sharing ɗinka da wata ba, ina matuƙar sonka da kishin ka dan Allah karka ci amanata, ban san ya zanyi ba randa na buɗi ido naga kana zaman Aure da Amira ba"

"Kwantar da hankalinki, Ni ke kaɗaice tawa, ke kaɗai zuciyar Imran ke so da ƙauna, Auren Amira Auren biyayyane da bin umarni, ke kuma Auren soyaya mukayi dake" yai maganar yana sake hugging ɗinta a jikinsa.
Da haka ya lallaɓa Ihsan, kalamansa sukayi tasiri a zuciyarta, harta haƙura ta biye masa.

(🙄🙄🙄)

Washegari Amira ta shirya, Fadila zata rakata gurin kitso, Anty tace "Yawwa Amira, Abbanki yamin waya Imran zasu dawo very soon insha Allah, ana so ki faɗi kalar kayan da kike so a samiki, koma muje dake ki nuna wanda kike so, se kuma kayan Kitchen duk Abbanki ya turomin kuɗi ki kirashi ki masa godiya, sannan kuɗin kitsonki ma nayiwa Imran magana, shine yakamata ya biya kuɗin, ya turo dubu biyar, shima ki kirashi ki masa godiya"

Tura baki Amira tayi tace "Nifa bani da lambarsa"

"Eh ni ina da ita ai, kije ku dawo zan baki"

Amira bata kuma cewa komai ba, tai gaba abunta.

Sukaje saloon, akai mata kitson attachment ɗinta kamar Yadda ta saba, tai ras da ita sannan suka dawo gida.

Taje ta tarar Anty tayi baƙuwa, an kawo mata wasu kaya, bata damu da ta san komeye ba suka gaisa da baƙuwar Amira tai wucewarta.

Bayan tafiyar matar Anty ta kira Amira ɗakinta, tace  "baki nunamin kitson ba"

Amira ta cire hular kanta, kitsone ƙanana na attachment yayi matuƙar yi mata kyau.

Anty tace "masha Allah, kitso yayi kyau sosai, i wish mijinki yazo yaga kitson nan, amma Amira kin san ba kyau kitson ƙari ko? Gashi kema kina da gashi kiyi ƙoƙari ki dena"

Amira ba tace Komai ba se sunkuyar da kai da tayi, Anty ta ɗakko wasu manyan robobi se ƙamshi suke ta ajiyewa Amira a gabanta tace  "ga wannan kayan sabulai ne nasa aka haɗo miki, ga na wanka nan dana mayukan shafawa, ga turarukan wanka nan dana shafawa, dan Allah Amira karki wasa, ki kula kiyi amfani dasu yadda yakamata, na kashe kuɗi sosai akan kayan nan, sonake kiyi tsaf dake kafin ki tare in gyaraki Sosai, dama gashi naga kema 'yar gayu ce, kayanki gobe in Allah ya kaimu za'a karɓosu daga gurin tela, ki dage da kayan gyaran jikin nan sosai kinji Amira"

"Insha Allah zanyi Anty, nagode Sosai Allah yasaka da Alkhairi"

Ta ɗebi kayan nan ta tafi dasu ɗakinta, yanayin robobin kawai sun isa kasan an kashe kuɗi sosai akan kayan nan ba kaɗan ba, daga sabulan mayukan zuwa kayan turaren, Banda kayan mayukan gyaran jiki da suka siyo a kasuwa.

Hatta Abincin da Amira take ci seda Anty ta daidaita mata shi, ganye

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login