Showing 87001 words to 90000 words out of 120332 words
Chapter 30 - WUTA A MASA?A COMPLETE HAUSA NOVEL BY AYSHERCOOL
gara ki zauna yadda kike kinfi kyau"
Ɗan ƙura masa ido tai, tai murmushi tace "dagaske ina da kyau Captain?"
"Eh kina da kyau mana, tunda kike kama dani, kuma kinga ni kyakykyawa ne"
Sosai Amira take dariya, tace "ji yabon kai, ka bari a faɗa mana, ba fa wani kyau ne da kai ba fa"
"Ki bari mata ta ta jiki, kina cewa bani da kyau, duk abunki tunda mata ta tace ni me kyaune nasan ina da kyau, kika bari ta jiki faɗa zakuyi, kuma ki ka mata rashin kunya in zaneki"
Tsaki Amira tayi tace "dan Allah wai zaman me nake da kai, tunda baka sona, dan Allah ni ka sakeni in Auri wanda yake sona".
Kallonta Imran yai yace "so kike Abba yai fushi da ni kenan?"
"Ai cewa zan nina ce ka sakeni, dan Allah ka sakeni, wallahi bayan tafiyar ka hawan jini seda ya kamani saboda ɓacin rai" tai maganar tana hawaye
"In jinin ya hau Akwai magani ai"
Kallon Imran take, sam be damu da damuwarta ba, miƙewa tai ta tafi ya barshi a gurin.
Yabi bayanta da kallo har ta shige, seda ya ɗanyi murmushi, daga ƙarshe ya koma ɗaki ya kwanta, amma da yayi juyi se Amira ta faɗo masa rai, Gaba ɗaya tunaninta ya hanashi bacci, Abincinta me daɗi, muryarta ma me daɗin sauraro.
Ihsan ta shiryawa Imran breakfast, ta fita gurin aikinta, da yake Imran be tashi daga bacci ba, ta tafi gurin aiki, Ihsan na fita, Amira ta kwashe kayan Abincin Ihsan, ta jera masa nata.
Da Imran ya tashi daga bacci, yai wanka ya fito, ya zauna ya kwashi Abincinsa, ba tare da sanin wanda yai girkin ba.
Se la'asar Ihsan ta dawo, ta shiga Kitchen da hanzari ta ɗora girki, daf da magariba ta kwaso Abincin ta kawo dining ɗin babban falo, sedai ta tarar da kwanukan Abincinta a ƙasan dining.
Mamakine ya kamata, ta bubbuɗe taga yadda ta zuba masa Abinci be taɓa ba, tana tsaye tana tunani sega Imran ya shigo, ya ƙarasa dining ɗin yana faɗin "My kin dawo? Ya aikin?"
Ta kalleshi tace "ya a kai nai maka girki ba ka ci ba?"
Imran yace "ni ɗin naci mana".
Ta buɗe foodflask sega Abinci a ciki, babu alamar an taɓa.
Yace "Aini ba wannan flask ɗin na gani da safe ba"
"Kaga irinta ko, inyi magana ace na fiye neman Magana, wanne na ajiye idan ba Wannan ba"
Amira ta fito daga sashenta, hannunta riƙe da ɗan ƙaramin kwandon shara na Kitchen, Imran yace "Amira, meyasa kika ɗauke Abincin Ihsan kika ajiye naki? Haka akeyi"
Amira tace 'Ai ba Ihsan ce kawai matar gida ba, nima matarka ce, akan me sedai ta dafa ta baka ni zaman me nake, to nagaji shiyasa nai mata haka, rashin adalcin da akemin ya fara isata saura ma raba kwana"
"Shut up!"
Imran ya daka mata tsawa, "ke duk yadda za'a lallaɓaki sekin nemi magana, meyasa ki kai haka? Ko dan kin ban Abinci ranar da na dawo naci, shine ki kai haka? Ke idan baki nemi Magana ba ba kyajin daɗi ko? Waye ya saki? Kuma da ubanwa zaki raba kwanan fitsararriya mara Kunya"?
Wata uwar harara Amira ta watsa masa tace "koma da ubanwaye"
"Ni kike gayawa haka?"
"Tsakanin wuta da Aljanna wacce mallakinka da zaka sani, wanda zesa inji tsoron gaya maka magana?"
Take ta koma masa ainihin Amiran ta, mara jin magana.
Cikin zafin nama yai kanta, amma ko gezau balle tai yunƙurin guduwa.
Yana zuwa ya murɗe kunnenta ɗaya, seda ta wani uban fitsari ya matsota, "ni kikewa rashin kunya ko? Kinga kwana biyu ina saurara miki ko? Shine kika samu damar yin wannan rashin mutuncin ko?"
Riƙe hannunsa da ya riƙe mata kunne tai tana kuka, ya dungurar da ita a gurin, ya nufi inda Ihsan take, ya riƙo hannunta yace
"Am sorry my, kiyi haƙuri wallahi ban san yadda a kai haka ta faru ba"
Ya ja hannun Ihsan zuwa ɗakinsu, yaje yaita lallaɓata yana tunanin yadda ze gaya mata ze tafi da Amira Lagos.
Seda ya tabattar ta haƙura, sannan ya tashi ya fita sallar magariba, ya wuce Amira a falo tana kuka, shi har mamakin yadda Amira ɓarin hawaye kamar ba daga jikinta yake zuba ba yake, ya wuce ta ya tafi masallaci.
Ihsan ta fito ta kalli Inda Amira take ta yatsuna fuska tace "Wallahi in dai zaki cigaba da takara da ni a gidan nan, baƙi ciki Yanzu kika fara kwasa"
Amira bata tanka mata ba, tai ta gama ta koma ɗakinta.
Imran ya dawo daga salla, ya kuma hango Amira a zaune, yana nan tsaye be shigo ɗakin ba, se aka ɗauke wuta, nan da nan ta miƙe da sauri, tan waige waige tana ƙoƙarin laluben hanya, dan ba laifi Amira akwai tsoro.
Jin ta tayi a jikin mutum, ware murya tai za tayi ihu, amma ya haɗe bakinsa da nata, ƙoƙarin ƙwacewa take daga jikin Imran, amma ya riƙeta gam.
Seda yai me isarsa sannan ya kai bakinsa kunnenta yace "to fitsararriya, ga rashin kunya ga tsoro, ki shirya kayanki jibi in Allah ya kaimu zamu tafi Lagos tare"
"Bazanje ba, ka tafi da Wannan ƙandararriyar"
"Ni kike cewa ba zaki ba, ai ƙandararriyar ta fiyemin ke, Abba zaki cewa ba zaki ba, saboda idan na tafi dake ba wani amfani da zakimin, kuma a ƙandaren nake sonta"
"Eh kaita son nata, ni cikani in tafi, ka murɗemin kunne ban maka Komai ba"
"Cigaba da ɗaga murya, ta zo ta ganki a haka zaki mata bayani ne, hadda saura raba kwana saboda baki da kunya"
"To tsoron ta nakeji? Ai ba tsoronta nake ji ba, kuma ina kai ina tunanin Kunya a tare da Karuwa, ni ka ƙyaleni dan Allah"
Ɗan saroro yai yana kallonta, duk da a duhu ne tana sauke numfashi a fuskarsa shima yana sauke mata, a hankali ya cikata ya juya ya nufi part ɗin Ihsan.
Yana shiga ya zauna, sega wayar Abba nan, ya ɗaga ya gaida Abba, Abba yace "Imran yaushe ne tafiyar ka Lagos ne?"
"Abba jibi in Allah ya kaimu ne"
"To kasan dai yadda mu kai da kai, wannan karon tafiyar ta Amira ce, dan haka kai mata Magana ta fara shiri, nayi waya da kakarta da zasu zo da weekends, amma na gaya musu zaku tafi lagos, se Allah ya dawo daku tukuna"
"To Abba, zan gayamata insha Allah"
Ihsan ta kafe Imran da ido ko ƙiftawa ba tayi
SHARE PLEASE
A ko yaushe ina alfahari da ku, ina jin daɗin sharhin da kuke akan littafin nan, ina matuƙar godiya sosai, masu gyara, sharhi da ƙorafi duk ina godiya, wanda ban samu amsa saƙonninsu ba a dinga min Afuwa, abubuwane da yawa, sannan dan Allah masu bina pc suna in basu daga farko, ko in basu oage kaza, dan Allah ku dinga min uzuri, abubuwa sun min yawa sosai, ku dinga tambaya a groups ko Ku duba a watpad, nasan sone yasa kuke neman littafin, amma dan Allah a dinga min uzuri, sannan ga wanda suka turan kuɗin ruɗin Ƙuriciya kuma, su sakemin magana Please in saka su a group, this week zan fara free pages insha Allah, Nagode"
Domin Sharhi, gyra ko shawara
07063065680
[2/8, 7:57 PM] Ayshercool: 🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥
WUTA A MASAƘA
PERFECT WRITERS ASSOCIATION
(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS)
https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
P. W. A
*Story and written by*
AISHA ADAM (AYSHERCOOL)
The experience writer of
*ABDUL JALAL*
* WATA KISSAR.... (SAI MATA)
*BAƘIN TABO (Labarin gasa)
*AƘIDATA (Paid Book)
* WUTA A MASAƘA
https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=in
❌❌❌
Ƙirƙirarren labari ne, ban yadda ayi amfani da kowane sashi na labarin ba ba tare da izinina ba.
*🌈NIMCY'S LIBRARY🌈*
_Readers gareku, masu tambayar old books na NIMCYLUV SARAUTA, tayi shiru ne domin tana bada bunus kafin azumi, to Finally the day is here, tana sai da littafan ta gaba ɗaya akan 3k gaba ɗaya littafan guda 14 ne, to bisa Bunus ɗin da tayi na tsayin sati guda dukkan mai so zai biya 1500 mai makon 3k😍, nasan baku karanta littafan ta na baya ba, da am sure za kuce sunma fi na yanzu daɗi❤️🤨_
So what are waiting for.....??? Go and subscribe your own...
Abu Maleek
Sirrin mu
Uncle ne
The new emir
Izzar so
Sai na aureta😍
Tsintacciya
E.t.c guda 13 via 0116886423 sulaiman Naima s union bank evidence of payment 08119237616 a biya asha karatu Tabbas za kuyi farin ciki littafan babu baya #Love #Romance #Destiny
Bonos ya fara 6/2/2022
Share fisabilillahi😍
41_42
Ya ajiye wayar, ya kalli Ihsan zeyi magana ta ɗaga masa hannu, "Yanzu Imran da ita za ka tafi, ina ji ina gani ka barni a nan? Ka ɗauketa ku tafi, Imran ina alƙawarin da kai min? Nasan ba zaka taɓa cikawa ba".
Tai maganar zuciyata na matuƙar tafasa.
Imran ya gyara zamansa Sannan yace "Ihsan, wallahi dan ta ni kin san ba zan ɗau yarinyar nan in ce zan tafi da ita ba, da kunnenki kin ji ai, Abba ne ya bada umarnin nan ba wai ra'ayina ne hakan ba, ki fahimceni mana".
"Ni ka ƙyaleni, ba abunda zan fahimta, wannan ai cin fuskane taya zaka je ka zauna daga ita se kai a gida, kuma hankalina ya kwanta ba abunda ze faru? Gaskiya ni ban yadda ba"
"To me ki ke so ayi? In cewa Abba bazan tafi da ita ba ko kuma yaya?, Da da bani da Aure mutuwa nayi? Ko kuma kwanakin da nayi a daji ba mace wani abu ta sameni, ke kanki da nake so in ki kamin laifi muna kwana shimfiɗa ɗaya kuma in ƙaurace miki, meyasa kike tunanin wani abu ze haɗani da ita, haryanzu kin kasa yadda dani"
Gaba ɗaya maganganun Imran jin su take a matsayin kalaman yaudara da rainin hankali, ta miƙe ta ɗau wayarta, ta tafi ɗayan ɗakin ta rufe ƙofarta.
Imran ya shafi sumar kansa, ya kwanta akan gadon, ya fuskanci idan ya biyewa matan nan zasu maida shi mara hankali, kowacce da kalar tata rigimar, ba ƙaramin kwarjini ne da shi ba ko a wajen aiki, amma idan ya dawo gida mata su dinga caza masa kai, ya ɗakko wayarsa ya hau chatting.
Yana dubawa ya ga Khalid online, yai masa sallama Khalid ya amsa yace "kai Angon biyu ya? Ka wartsake kenan?"
"Tun yaushe, zan dawo aiki ma"
Khalid yace "Haba? Yaushe zaka zo?"
"Jibi in Allah ya kaimu, zan taho insha Allah"
"Masha Allah, wannan karon kai ɗaya zaka taho ne?"
"Ina fa, Abba yace sena taho da Amira"
Khalid ya tura masa emoji na dariya yace "gaskiya Abba ya kyauta, ka ga an biyata kwanakinta da Ihsan tayi"
"Wallahi Khalid mata na da matsala ta gaske wallahi, Ihsan ta ɗau fushi da kumbura baki Abba yace in tafi da Amira, ban taɓa sanin haka Ihsan take ba, ban san da yawa daga halayenta ba se da na Aureta, ta fiye ƙorafi da rashin haƙuri, ina tausaya mata da ɗaga mata ƙafa amma ba ta gani sam"
"Ai dama hakane, kai ma nasan ba ta san da yawa daga halayenka ba se yanzu da ku kai Aure, sedai ku cigaba da haƙuri da juna, ka dai rarrasheta kar ka tafi ka barta a damuwa"
"Ai na fara gajiya da rarrashin nan, anyway na san dai abunyi"
"Aikam ya kamata kasan abunyi tun da wuri"
"Shikenan sena shigo Lagos ɗin"
"Allah ya kawo ka Angon Amira"
Imran yace "za kaga Angon Amira, idan Ihsan ta jika"
"Ai ni Amira nakeyi dama"
Suka cigaba da hirarsu ta abokai.
Ihsan kuwa zuciyarta na tafasa ta kira mahaifiyarta a waya, kusan missed calls uku bata ɗaga ba, ta ajiye wayar tana safa da marwa a ɗakin, tana jin Kamar zuciyarta tai bindiga.
Mamanta ce ta biyo kiran da tai nata, da hanzari ta ƙarasa ta ɗauka, ta na ɗagawa tace "Mummy na shiga uku"
"Innalillahi wa innalillahi raji'un, kika shiga uku da me?"
"Mummy wai da Amira ze tafi lagos, na rasa me naiwa tsohon nan ya tsaneni, baban Imran sam baya ƙaunata, baya sona da ɗansa, akan mw za'a ɗau Amira a tafi da ita? Me nayi masa haka fisabilillahi, kin san Yarinyar nan karuwa ce, wallahi tsaf zata iya jan hankalinsa"
Mummy tace "tsaya, wai waye ya gayamiki da ita ze tafi ne?"
"Ammmi yanzu fa yai waya a gabana da Abban, ya sake maimaita masa ashe tun da ya dawo aka tsara in ze tafi Lagos ya tafi da ita, amma be gayamin ba, wallahi Ammi tsoro nakeji, karya tafi da ita kashina ya bushe yaje tai masa wnai abun"
"Ke kwantar da hankalinki, ba abunda zefaru nasan abunyi"
"Mummy meye abunyin to?"
"Ki ɗan sauraramin, zan waiwayeki Insha Allah"
"To amma fa Mummy jibi zasu tafi"
"Ba abunda zefaru tsakanin su, nina gayamiki"
"Amma Mummy, wane tabbaci ki ke da shi akan hakan?"
"Ke ina ruwanki ne? Ina da abunyi ni a kai"
"To Mummy, Allah yasa abun yayi".
Ta kashe wayar a sanyaye, ta gayawa Ijsan hakanne dan kawai hankalinta ya kwanta, amma ba ta da wani abu da zata iyayi a kai, tasan halin Ihsan da damuwa da saka abu a rai.
Lambar Ammi ta kira, seda ta kusa katsewa sannan ta ɗauka tace "Afwan bana kusa da wayar ne,barka da dare"
Mummy tace "Yawwa barka, ya iyali?"
"Alhamdilillah, ya zafin nan?"
"Gashi nan Alhamdilillah, nace kin san kuwa Imran jibi in Allah ya kaimu ze tafi Lagos da matarsa?"
"Bari kawai, naji wallahi ba yadda ban ba akan in shawo kan mahaifinsa a janye maganar nan, amma abu ya gagara duk ta in da na ɓullo masa seya kange, kwana biyu na kasa gane kansa, amma ku kwantar da hankalinku, Shi Imran ɗin na san yadda zan dashi, tunda nina haifeshi dan Allah karku damu akan Wannan Yarinyar"
"To shikenan, dama Ihsan ɗin ce ta kirani a waya hankalinta a tashe, shiyasa nace bari in kiraki, amma tunda kince haka shikenan"
"Bakomai, dan Allah ki kwantar mata da hankali, ba wani abu Insha Allah"
Mummy tace "shikenan, seda safe, ki gaisarmin da daughter na please"
"Za taji insha Allah".
Amira kuwa cike da nishaɗi ta koma ɓangaren ta, tana ji a jikinta burinta na daf da cika tunda Imran ya fara sakin layi, ga kuma tafiya za suyi tare.
Anty ta fara kira a waya ta sheda mata cewar zasu tafi Lagos jibi tare da Imran, Anty taji daɗin hakan sosai tai murna, Antyn tai ta yiwa Amira Nasiha, sannan ta gargaɗeta da anyi mata wani abu na ba daidai ba wanda ba ta gansu da shi ba ta sanar da ita.
Amira tace Anty ta bawa direba Akwati ya kawo mata, ta haɗa da tata dan tata ƙarama ce, wadda zata haɗa kayanta a ciki.
Imran haka suka kwana ɗaki daban daban shi da Ihsan, da sassafe Ammi ta kirashi a waya, wai ta na son ganinsa, ko karyawa beba ya tafi gidansu.
A bedroom ya iske Ammi, tana karyawa, ya gaisheta ta amsa masa sama sama, yace "Ammi naji kince kina nemana, Allah yasa lafiya?".
"Lafiya ƙalau, da ma ba wani abu bane ba, batun tafiyar ka da Yarinyar nan da ubanka ya dagw a kaine na kiraka in maka kashedi, kamara yadda na sha gaya naka da farko, ni ba zan taɓa murna da haɗa zuriya da tsohuwar kilaki ba, dan kowa irin Arziki yake bibiya bana tsiya ba, ina me ja maka kunne da kiranka da babbar murya, ba kai ba Wannan Yarinyar kar inji ko inga abunda ze ɗagawa matarka Ihsan hankali ko ya ɓatamin rai, ina Ganin mutuncin mahaifiyar Ihsan dan haka ba zan taɓa bari ko in goyi bayan a wulaƙanta mata 'ya ba, idan kuka je Lagos ka nemi wani gidan a Barrack ko a waje ka ajiyeta, karka kuskura ku zauna a gida ɗaya tare"
Da mamaki ya kalli Ammi yace "Amma Ammai, idan na ajiyeta ita kaɗai wani abun ya sameta Abba ze ɓatamin rai".
"'yar yayace ita da swka kula da ita ko kuwa? Kabi umarnina ka zauna lafiya, idan ka kuskura wani abu ya shiga tsakinka da Yarinyar nan zan iya mummunan saɓa maka, bana ƙaunar yarinyar nan so nake yadda tazo gidanka ta fita ba tare da wani abu ya haɗaka da ita ba"
Imran ya jinjina kai yace "to naji zan kiyaye insha Allah"
Ammi tace "da yafi maka, ka tashi kaje falo ka karya"
Tai maganar tana miƙewa tsaye, falo suka fito jikin Imran duk a saluɓe, suna fitowa Abba yana shigowa falon, ya kalli Imran yace "kai lafiya kuwa, kake tafe a safiyar nan?"
Imran ya dake yace "lafiya ƙalau Abba, nazo yi muku sallama ne kasan gibe in Allah ya kaimu da la'sar zamu tafi"
Abba yace "Au ai na zaci wani abunne ya faru, maimakon ka taho dasu ko ka tabo da ɗaya se ka taho kai kaɗai? Ko da kwaɗayin girkin mamanka ne ya kawo ka?"
Imran ya ƙaƙalo murmushi yaiwa Abba yace "A'a Abba"
"To shikenan, ina Minal ta kawo mana kayan Abinci nan mu ci gabaɗaya"
Aka kawo musu Abincin nana, suka ci tare, suna ci Abba yana sakewa Imaran Nasiha daban daban akan Rayuwa, da kuma riƙe matansa da amana da gaskiya gami da adalci a tsakaninsu...
Anty kuwa da kanta ta kaiwa Amira akwatin, ta nunnuna mata abubuwan da sukafi mahimmanci ta tafi dasu.
Sannan tace "Amira, you got a very nice to win your husband heart, kin samu cikakkiyar dama daga ke seshi, ba wani shamaki ko damuwa da zata gifata muku, ki tabbatar da kinyi duk me yiwuwa ki janyo hankalin sa kanki, sannan ki duƙufa da addu'a kin san itace gaba akan Komai, ki jajirce ki ƙwatarwa kanki 'yanci a gidan miji, kishiyarki ba ta fiki Komai ba, duk abunda ake nema agurin mace kema Allah ya baki, dan haka ki dage kiyi ƙoƙarin yin duk wani abu da zw janyo hankalin sa kanki kinji ko?"
Amira ji tai tamkar Anty ta san halin da take ciki a gidan, duba da yanayin nasihar da take nata, Amira tace "to Anty insha Allah, zanyi abunda kika ce"
Anty ta bata wasu zafafan turarraykan, da kayan gyara jiki sannan tai mata fatan Alheri ta tafi"
Amira ta raka Anty har bakin motarta, suna tsaye suna magana Ihsan ta dawo, tana zuwa ta gansu a tare da Anty ta ja wani uban tsaki ta wuce, daga Amira har Ihsan ba wanda ya kulata, suka cigaba da maganarsu bayan sun gama, sannan Anty ta hau mota ta tafi.
Tafiyar Anty babu daɗewa sega wasu 'yan uwan Ihsan sunzo, cousins ɗinta biyu da ƙawayenta biyu.
Ihsan ta saukesu a Babban falo, suka baje suna