Showing 45001 words to 48000 words out of 120332 words

Chapter 16 - WUTA A MASA?A COMPLETE HAUSA NOVEL BY AYSHERCOOL

10 Mar 2025

30358

Ihsan da yake ji, saboda yasan yadda take kishinsa da ƙaunarsa, yasan tabbas an mata ba daidai ba, haka Khalid yazi ya same shi a kwance a ɗakinsa.

"Imran meye hakane? Anjima fa ɗaurin Aure amma kana kwance kamar wani ruwa, dan Allah tashi mana"

Imran ya tashi zaune yai ajiyar zuciya ya dafe kansa yai shiruu.

Khalid ya dafa shi yace "Imran ya dai? Akwa matsala ne?"

Imran yai ajiyar zuciya yace "Khalid, wallahi sam bana murna da wannan ranar, ina jin tausayin Ihsan, ina ji a jikina ban mata adalci ba, na cutar da rayuwarta, na ɓoye mata abubuwa yanzu tana min kallon mayaudari maƙaryaci, ban san wace irin karɓa zan samu a gurinta yau ba, gefe guda waccan mahaukaciyar jiya dan rashin nutsuwa suka hau dambe da Minal, a gaban mutane jiya a gidan nan, naje na rabasu amma yarinyar nan taƙi jibharda cizona, zuciya ta ɗebe ni, na mata duka jiya, a daren Abba yasa muka tafi kaita gidan Alhaji Hashim, kusan a sume ta kwana, saboda ko kafin mu bar gidan nan, zazzaɓi ya rufeta tana ta layi, yanzu haka Abba kusan fushi yake dani, ni ji nake dama ban ɗakko maganar Aure ba, komai ya kwaɓemin ya lalace".

"No karka faɗi haka, ka kwantar da hankalinka komai ze wuce, tabbas Ihsan abar tausayi ce ta cancanci a tausaya mata, duba da irin son da take maka, amma a zahiri Amira ce abar tausayi, kuma gaskiya dukan ta da kayi baka kyauta ba, dan ba shine mafita ba sam, ni dai ina baka shawara da kaji tsoron Allah Sannan ka kamanta adalci a tsakaninsu duk da nasan Amira ba zaɓinka bace zaɓin Abba ce, amma kayi haƙuri Auren Amira da zakayi tamkar Jihadi ne, ko da baka sonta ka ji tausayinta ka riƙeta tsakani da Allah, ko dan Saboda maraicinta da kuma 'yan uwantakar dake tsakanin ka da ita"

Imran yace "ita wannan yarinyar tana tausayin kanta ne ko duba maraicinta, ni ina tsoron zamansu Guri ɗaya da Ihsan ta cutar min da mata a banza"

"Itama ai matarka ce, kuma bana jin duk abunta idan Ihsan bata kulata ba ba zatayi mata ba"

"Kaga Khalid ƙyaleni, bata wannan nake ba, ni ta Ihsan nakeyi itace a raina"

"Ita waccan ɗin daka sumar bata gabanka kenan?"

"Wallahi ko tausayinta banji ba, ina dukanta tanamin Allah ya isa, kai Yarinyar nan idan mutum ya biye mata, seya kusa kasheta ma"

"To kai waye yace ka dake ta? Baka san irin Amira rarrashi suke buƙata ba"

Tsaki Imran yayi ya miƙe ya nufi banɗaki, dan ko zancen Amira baya son ji, a ganinsa a dalilinta ne yake neman rasa farincikinsa.

Amira se wajen ƙarfe Bakwai ta farka, ta ƙarewa ɗakin da take ciki kallo, tunanin tayi ta tuna abunda ya faru jiya da daddare dukan da ta sha a hannun Imran, da kuma yadda suka zo wannan gidan, ta tashi zaune a hankali, ɗakin ɗan madaidaici me kyau, ta kalli hannunta taga ruwa a jikinta, ta sunkunyar da kanta tai shiru tana jiran taga ta inda wani ze shigo ta nemi yadda zatai, tayi salla.

Turo ƙofar ɗakin akayi, aka shigo da Sallama wata matace ta shigo, ta kalli Amira tace "ashe kin tashi ya jiki?"

"Da sauƙi" Amira ta amsa a hankali.

Ta ƙarasa shiga cikin ɗakin tace "bari in cire miki ruwan, ki shiga banɗaki kiyi wanka kizo kiyi salla kafin Antyn ta fito"

Amira ba tace Komai ba, ta cire mata Ruwan, ta nuna mata banɗaki, ko ina na jikinta yayi tsami se raɗaɗine ke ratsa fatarta.

Matar ta bata hijjabi da towel, Amira ta shiga banɗaki, ta haɗa ruwa me ɗumi ta fara zubawa a jikinta, wani irin zafi ya ratsa ta, kawai ta fashe da kuka, ƙarshe da ƙyar tai wankan ta fito.

Tana fitowa ta samu an ajiye mata ƙaton Hijjabi da sallaya, ta zira hijjabin nan tayi salla, ta idar ta zauna tayi Azkar.

Sedai jikinta ba ƙwari sam, ta miƙe ta nufi gaban mudubin dake ɗakin, ta cire hijjabin jikinta ya zama daga ita se towel, ta soma ƙarewa jikinta kallo fatarta tayi ruɗu ruɗu tayi ja, wani gurin a kumbure ya fashe, kawai ta fashe da kuka, hakan yai daidai da shigowar Anty, tana faɗin "Amira Ashe kin tashi?"

Ta tarar da Amira a gaban Mudubi tana kuka, ko ba'a gayamata ba tasan dalilin kukan nata, dan haka ta ƙarasa inda Amira ke tsaye tace "haba Amira ya kuka haka? Kiyi haƙuri nasan Boss be kyauta ba daya dakeki, nima ya bani haushi amma kiyi haƙuri kinji"

Tai maganar tana kamo hannun Amira, ta zaunar da ita a bakin gado tace, ga kayanki nan ki saka, yanzu za'a kawo miki abun karin kumallo da magani, ki dena Kuka kinji yarinyar kirki?"

Amira ta jinjina mata kai, tana cigaba da Share Hawaye, ta kalli Anty tace "dan Allah ki bugawa Abba waya, kice yace wa Su Anty Fa'iza su taho mu tafi gida, koni kisa a kaini tasha in koma gida, dan bazan ƙara zuwa garin nan ba, wannan ne karo na biyu da nayi dana sanin zuwa garin nan" tai maganar tana sake fashewa da kuka.

Anty tace "yi hakuri Amira, insha Allah wannam zuwan naki Kaduna, shine zuwa Mafi Alkhairi kiyi haƙuri". Haka Anty ta zauna taita aikin rarrashin Amira.

Abba yana ta shirinsa, sega Ammi ta shiga ɗakinsa ta sha shadda, tayi rasa da ita kamar ba ita ta haifi su Imran ba.

"Gani naga ka aika a kirani"

Abba yace "eh, dama na aika a kiraki ne dan in sanar dake wata mahimmiyar magana, yakamata tuntuni ki san maganar amma sanin halinku ku mata musamman ke yasa ban gayamiki tuntuni ba"

'meye halin nawa da kake kashedi a kai?"

Abba yace "ba wannan ba, kamar yadda a baya naso in riƙe Amira amma kika ƙi yadda shi......

"Abba nifa maganar yarinyar nan ta isheni haka wallahi, naga ƙarewa ka ɗauketa bata kwana a gidan nan ba, yau za'a gama biki ta tarkata tabi 'yan uwanta su koma gida mungode Allah yasaka da Alkhairi, nifa ban riƙe Yarinyar nan a baya ba, a yanzu fa bazam riƙe ba gaskiya"

"Inke ba zaki riƙe ba ɗana Imran ze riƙe"

'kamar yaya kenan? Yaron daze Aure yanzu za'a kwashi wannan kwazgwamemiyar Baligar a kai masa gida, gata Karuwa, ina Ihsan zata iya riƙe Wannan yarinyar, da yaya Ihsan ta girmeta? Ba tafi Ihsan girma ba, dan Allah Abba ka dinga faɗar abunda ze yiwu mana, 'yan uwa ta ma ba zasu yadda ba, nima bazan goyi bayan hakan ba"

Abba ya kalleta yace "Amira ba a 'yar riƙo zata je gidan Imran ba, a matsayin matarsa zata je ita ma"

"Kamar Yaya? Kana nufin Imran ze auri Karuwa ya haɗa da 'yar mutane?"

"Ƙwarai kuwa, idan ke ban isa dake ba, na isa da ɗana, dan haka Imran ze Auri Amira"

"Amma kaima kasan wannan abun bame yuwuwa bane, wallahi in dai da raina Imran baze Auri wannan fitsararriyar ba, yaje ya auro duk wadda yake so, amma Banda wannan yarinyar".

"Aikin gama ya gama Jamila, saboda a gurin ɗaurin Aurensa da Ihsan, za'a ɗaura Auren sa da kuma Amira!.

Aikuwa a kiɗime tace  "akan me zaka yanke wannan ɗanyan hukuncin saboda me? Nima fa ina da haƙƙi akan Imran kamar yadda kake da shi, saboda me zaka min haka? Baka gudun lafiyar ɗanka da na 'yar mutane daze aura, kuma ka kasa sanar dani tuntuni se daidai wannan lokacin da awanni suka rage a ɗaura Aurensa, saboda me zaka yimin haka? Akan me? Wallahi baka min adalci ba kuma ba kayiwa 'yar mutane Adalci ba kum....

"Ya isheki haka Jamila, da Imran da Amira duk 'ya'yana ne, kuma na yanke hukuncin da naga ya dace ba wanda ya isa ya canza min, this is my final decision"

Wani irin gumi ya dinga karyo mata, fuu ta koma cikin gida ɗakinta ta wuce, tana zuwa ta ɗau wayarta ta kira Maman Ihsan, ta kirata ya kai sau Uku Sannan ta ɗaga a hasale tace "Wai meye kike ta kirana haka? Ni da na kiraki jiya kika ƙi ki ɗaga se yanzu zaki isheni da kira, bayan kin san abunda kuka ƙulla ke da ɗanki, kun shirya wulaƙanta mun 'ya"

"Dan Allah Murja kiyi haƙuri, ashe ke kinma san meke faruwa, to ni Wallahi Allah kenan ban sani ba se yanzu, Yanzu da suke shirye shiryen tafiya ɗaurin Aure sannan ya gayamin, saboda yasan idan ya gayamin bazan bari duk yadda zan se na hana, shine be gayamin ba se yanzu, wallahi gaba ɗaya hankalina a tashe yake"

Maman Ihsan tai ajiyar zuciya tace "to Ihsan ma yanzu aka gayamata, gaba ɗaya ta birkice tace ita ta fasa Auren, ta haƙura da shi ta barwa waccan ɗin, naji tana cewa wai Yarinyar Karuwa ce"

"Eh Karuwa ce wallahi, 'yar ƙanwarsa ce, Yanzu haka jiya da daddare baki ga dukan da Imran ɗin yai mata ba, amma dan Allah ki tasuhi Ihsan ki kwantar mata da hankali, nasan matakin da zan ɗauka akan lamarin, amma dan Allah kuyi haƙuri, ban san da Maganar nan ba se yanzu, ku ƙyaleni dasu, ai Imran ni na tsuguna na haifeshi, ba inda Auren nan zeje nina gayamuku, ki kwantar mata da hankali dan Allah, kuyi haƙuri nasan ba ai muku adalci ba"

"Shikenan Allah ya kyauta, ni dai tsorona kar a sawa yarinyata wata cutar daban"

"Wayace miki za'a kai ga nan ma? Ki bar komai a hannuna kawai kuyi haƙuri"

Suka gama wayar, ta kira Imran, Imran na ganin kiran Ammi gabansa ya faɗi, ƙirjinsa ya finga bugun uku uku, yasa hannu ya ɗaga wayar.

"Kana ina ne?"

"Ina gidansu Khalid" ya bata amsa

"Kana sane da Mahaifinka ze aura maka wannan Karuwar Yarinyar?"

Imran yace "wace Karuwar kuma Ammi?" Yai maganar a saɓule.

"Wace banda wannan sheɗaniyar 'yar ƙanwar tasa"

Imran yace "Na sani Ammi"

"What! Dama ka sani amma baka gayamin ba? Kuma ka amince zaka Aureta?"

"Ammi ya zanyi? Abba be taɓa roƙata wata alfarma ba se wannan, se ince bazan masa ba? Ni kaina bana son Auren nan ba yadda zanyi Ammi.

"Dalla rufemin baki, Shashashan banza, algungumi ni zaka gayawa baka son Auren? Da baka son Auren ai da tuni ka sanarmin, musan matakin da zamu ɗauka, amma ba a tashi gayamin ba se Yau, ya rage awanni a ɗaura maka Aure da Ihsan kawai se inji hadda wannan Yarinyar, ka bani kunya ka bani mamaki Imran, gashi can kasa 'yar mutane a damuwa tana ta haƙura da kai ta fasa Auren, Yarinya me nutsuwa da tarbiyya kayiwa kanka, indai karuwace gaka ga ta nan"

Cikin karaya Imran yace "Ammi dan Allah ki saurareni kiji" kashe wayarta tayi ta ƙyaleshi.

Ya ajiye wayar ya zauna Ya dafe kansa, ya easa mema zeyi yaji daɗi.

Khalid ne ya dinga rarrashinsa, yana kwantar masa da hankali.

Tuni sakamakon gwaje_gwajen da akayiwa Amira ya fito, bata ɗauke da Kowace matsala da ka iya kawo tangarɗa ga Aure, kama da gwajin cuta me karya garkuwar jiki wato HIV, ciwon hanta HEPATITIS B, Rukunin jininta BLOOD GROUP, Genotype, Gwajin ciki, PREGNENCY TEST gaba ɗaya lafiyar Amira ƙalau.

Ɗaurin Auren da aka saka ƙarfe sha ɗaya, ƙarshe se bayan da aka idar da sallar Azahar aka ɗaura shi, masallaci ya cika maƙil da manyan mutane, waliyyan Ihsan sun ɗanyi jinkirin zuwa ga mutane sun fara ƙosawa, dan haka aka bada sakamakon gwajin Amira aka fara ɗaura Auren Imran da Amira, ana cikin ɗaurawa ne waliyyan Ihsan suka ƙaraso, bayan an gama na Amira aka ɗaura na Ihsan da Imran.
    Amma Ihsan tana can gida tana bori akan ita lallai bata son Imran yanzu ta barwa Amira shi, dan ko an ɗaura an kaita seta dawo.
Seda "yan ɗaurin Aure suka dawo Sannan mutanen gida suka san mata biyu aka Aurawa Imran, ciki harda Yarinyar da ya zane jiya da daddare.
Nan gida ya ɗau cece kuce, su Fa'iza sam basu san meke faruwa ba, ita gaba ɗaya hankalinta yana kan ya Amira ta kwana, ga jakarta da wayoyinta duk a nan ta barsu, ita Fa'izan ce ta ɗauke mata su.

Duk yadda abokan Imran sukayi dashi akan suje gidansu Amarya ayi hotunan ɗaurin Aure ƙi yayi, dan be san da wani idon ze kalli Ihsan ba, da suka dawo gida ma, suka yi walimarsu ta angwaye sam baya walwala, kuma ya kasa shiga cikin gidansu, wanda basu san mata biyu ze aura ba se ranar suna ta zolayarsa, suna ya akai ko a gurin Dinner Amarya ɗaya suka gani, se ranar ɗaurin Aure suji Amare biyu ne.
Shi dai Imran ba wanda ya tankawa, dan shikaɗai yasan meke damunsa.

Gida ya cika da jama'a, ana ta shiga ana fita, ana Allah ya sanya Alkhairi, Abba yasa Anty Hadiza ta nemo masa Fa'iza.

Ko da Fa'iza taje Abba ya sanar da ita halin da ake ciki seda ta girgiza, tasan tabbas akwai daru, nan ta shiga tunanin ko ya Amira zata iya zama da Imran, shi zuciya ita taurin kai da rashin kunya, ta wani fannin an temaki rayuwar Amira, amma ta wani ɓangaren akwai ƙalubale.

Abba yace "Yanzu ki ɗakko mata kayanta da tazo dasu nan, direba ze kaiki Gidan Alhaji Hashim, ki kai mata kayanta, za'a maida ku Kano, sannan zanzo da kaina har Kano, in yiwa su Yadikko bayani in Basu haƙuri akan hukuncin dana yanke ba tare da saninsu dangin mahaifinta ba"

Ita dai Fa'iza ta kasa cewa komai, jiki a sanyaye taje ta tattaro kayan Amira, da nasu kayan Aka haɗasu da direba zuwa gidan Alhaji Hashim.

Har suka tafi hanya basu san meyafaru ba, sun ɗauka zasuje su ɗakko Amira ne su tafi gida.

Suna ta murna da irin shatara ta Arzikin da aka basu, da wanda suka sato a gidan, sam dukan da akayiwa Amira baya gabansu, sema murna da sukayi suna Allah ya ƙara.

Da sukaje gidan Alhaji Hashim kuwa, dama direban sojan nan ne daya kai Amira gurin make up, yace "mutum ɗaya ce zata shiga, dan ita kaɗai aka san da zuwanta ku ku zauna a Mota"

Amina tace "ooh ji wani makirin iyayi".

A sanyaye Fa'iza ta shiga gidan, a falo ta tarar da Anty suka gaisa tace "dama nice wadda nazo gurin Amira"

Anty tai murmushi tace "Sister ɗinta ce ke?"

Fa'iza tace "Eh"

Aka nuna mata ɗakin da Amira take, Amira na ganin Fa'iza ta miƙe ta fara share hawayenta tace "Yawwa muje, dama tun ɗazu ke nake jira, gara mu bar garin nan kan a kasheni"

"Amira ba dake zamu tafi ba, kayanki na kawo miki, keda Garin Kano sedai kije da ziyara"

A fusace Amira tace "Kamar Yaya? Me kike nufi?"

"Saboda yanzu ke Matar Imran ce, an ɗaura Masa Aure dake da Ihsan!!!"

SHARE PLEASE

(Nayi dogon page yau, am expecting your Comments.
Ko ya Amira zata karɓi Wannan batun Auren? Ku kasance da Alƙalamin Marubuciyarku wato Ayshercool, domin gyara Sharhi ko shawara ku tuntuɓeni akan 07063065680 or Follow me on watpad@ Ayshercool7724)
[1/21, 6:08 PM] Ayshercool: 🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥

WUTA A MASAƘA

PERFECT WRITERS ASSOCIATION

(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS)

https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P. W. A

*Story and written by*
AISHA ADAM (AYSHERCOOL)

The experience writer of

*ABDUL JALAL*
* WATA KISSAR.... (SAI MATA)
*BAƘIN TABO (Labarin gasa)
*AƘIDATA (Paid Book)
* WUTA A MASAƘA

https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=in

❌❌❌
Ƙirƙirarren labari ne, ban yadda ayi amfani da kowane sashi na labarin ba ba tare da izinina ba.






(INA WA INNALILLAHI RAJI'UN, NA SADAUKAR DA WANNAN PAGE GA YARAN DA AKA SACE AKA MUSU KISAN GILLA A KANO DA KUMA ZARIYA, UBANGIJI ALLAH YAI MUSU RAHAMA YA KAWO MANA TSARO A ƘASAR NAN, ALLAH YA BAWA IYAYENSU HAƘURIN JURE RASHIN SU)

*_Masha Allah, gaskiya ina jin daɗin yadda kuke Comment da nuna soyayyar ku ga littafin WUTA A MASAƘA, nagode sosai Ubangiji Allah ya bar ƙauna, ina jin daɗin sharhin da kuke akan labarin_*

                            22_23

A fusace Amira ta sake cewa "inji ubanwa? Ke waye ya gaya miki wannan shirmen dan Allah bana son wasan banza, ni mu tafi kawai"

Haɗe rai Fa'iza tayi tace "duk wasan da muke dake na taɓa miki irin wannan ne? Ni karɓi wayoyinki da sauran kayanki, suna waje suna jirana zamu tafi"

"Can ta matse musu su da wanda suka ɗaurawa Auren ba dai Amira b, kuma wallahi bazan kwana a garin nan ba"

Kan Fa'iza tai magana tuni Amira tai waje abunta, Anty dake Falo ta tashi da sauri tace "A'a, Amira ya haka? Ina zakije kuma?"

Amira tace "gida zamu koma, an gama biki ga mota can a waje zamu tafi gida"

Anty tace "wani gida kuma Amira? Ai babu ke ba komawa gida baki san an ɗaura miki Aure bane? Kiyi haƙuri ki koma ki kwanta kin san baki da lafiya"

Aikuwa Amira ta ɗora hannu a ka tace "Na shiga uku ni Amira, wai dama dagaske An ɗauramin Aure da wannan Mugun? Meyasa za'amin haka? Dan anga ni marainiya ce shine za'a Auran wanda ya kusa kasheni? Wato idan ya kasheni ba wanda yake da Asara? Meyasa za'amin Auren dole? Ni wallahi gida zan tafi, gara zaman gidanmu da zama da wannan Mugun mara imani, wallahi ni gida zan koma"

Ta rirriƙe Fa'iza tana rusa kuka, tuni hawaye ya wanke mata fuska, Alhaji Hashim ya sakko daga kan benensa, jin kukan Amira da yayi.

Yana zuwa ya tarar Amira ta riƙe Fa'iza tana kuka, itama Fa'iza seta saka Kuka ta rungume Amira tace "Amira kiyi haƙuri, ki rungumi ƙaddara kinji, dan Allah karki kuma aikata wani abun daze rusa rayuwarki, ina miki fatan Alkhairi da fatan Imran ya zame miki Mijin marainiya"

"Wane mijin marainiya Anty Fa'iza? Kalli jikina fa kalli dukan da yaimin, babu tausayi ba imani, ni wallahi bana sonsa, meyasa za'amin Auren dole dan babana ya mutu, Fa'iza kinfi kowa sanin wahalar dana sha, yanzu na cancanci sake faɗawa wata wahalar? Meyasa kuka bari akamin wannan Auren? Meyasa?"

Kasa magana Anty Fa'iza tayi, ita kanta Anty jikinta sanyi yayi dan Amira ta bata tausayi sosai.

Alhaji Hashim ya ƙarason inda suke, yace "Amira cikata su tafi kar suyi yamma a hanya"

"Dan Allah ku barni in koma gidanmu, wallahi niba matar Aure bace bana son wannan Auren, karku rabani da 'yan uwana alhalin bani da kowa a nan se Allah, wanda kuka saka ya Aureni baya ƙaunar ko ganina, ku dubi maraicina ku rabu dani dan Allah"

Alhaji Hashim ya haɗe rai sosai yace "ki cikata su tafi nace"

Amira ta saki Mayafin Fa'iza, ta durƙushe a gurin ta sake fashewa da kuka, Anty Fa'iza tanayi tana waigowa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login