Showing 120001 words to 120332 words out of 120332 words
Chapter 41 - WUTA A MASA?A COMPLETE HAUSA NOVEL BY AYSHERCOOL
mutumin da ya fara ɓata ta, wanda ya kwaso cutar ƙanjamau itama ta samu, ƙarshe tazo kyan da take taƙama da shi ya gushe, saboda larura, kuɗin da suka tara ta wannan mummunar hanyar suka ƙare, ga rashin lafiya ga babu.
Imran kam Seda Amira ta sake haihuwa, sannan ya nema mata makaranta, ta samu Admission taje tai karatun midwifery.
Suka zauna cikin kwanciyar hankali da ƙaunar juna, ga zuriya da Allah ya albarkace su da ita, kuma suka shirya da uwar mijinta suka zauna lafiya, Minal ma ta Khalid yana sonta, sedai itama Allah ya jarabceta da fitinar ƙannen miji, duk da ga gida ga gida suka zauna, amma suka sata a gaba basa ƙaunarta.
Zumuncin su Amira ya ɗore, ita da Fa'iza, Abba ya samawa Bashir aiki a wani babban kamfanin abokinsa a Kano, kasancewar yana da degree yayi karatu.
Sultan ma ya bar sana'ar DJ, ya koma makaranta.
Amina kuwa harta koma ga Allah, tana hauka tuburan, Sadiya ta samu wani me mata uku ita ta huɗu ta aura, kishiyoyi da 'ya'yan miji suka maida ita tamkar baiwa, sedai duk da abun nan da sukaiwa Amira, baya hanata temaka musu.
Jajircewar Imran da gaskiyarsa akan aiki, yasa ya kai har muƙamin General na Sojoji, gefe ga kasuwancin sa yana yi, ga mace ta gari da tarin zuriya.
TAMMAT BI HAMDILLAH, DUK DA NACE GAJEREN LABARI N, SE GASHI YA KAIMU IN DA BAN ZATA BA, INA FATAN AN AMFANA DA DARUSSAN DAKE CIKIN LABARIN, KUSKUREN DAKE CIKIN LABARIN KUMA INA FATAN UBANGIJI ALLAH YA YAFE MANA BAKI ƊAYA.
HAR ILA YAU ƘOFATA A BUƊE TAKE DOMIN GYARA, SHARHI KO SHAWARA KO TUNTUƁENI KAI TSAYE
AYSHERCOOL
07063065680
KAR KU MANTA LITYAFIN RUƊIN ƘURUCIYA SHIMA YAZO DA NASA SALON NA MUSAMMAN, DAN ZAN IYA CEWA NASA SALON YAFI WUTA A MASAƘA MA, KU HAZARTA KUYI SUBSCRIBING AKAN NAIRA 300 KACAL KAR AYI BABU KU.
NAGODE ƘWARAI DA ƘAUNAR DA KUKA NUNAMIN AKAN LITTAFIN NAN. KU KASANCE DANI DON CIGABA DA SAMA MUKU DA LITTATAFAI MASU ILIMANTARWA DA FAƊAKARWA.
TAKU HAR KULLUM AISHA ADAM (AYSHERCOOL)
0706306568.