Showing 102001 words to 105000 words out of 120332 words
Chapter 35 - WUTA A MASA?A COMPLETE HAUSA NOVEL BY AYSHERCOOL
47_48
Gaba ɗaya suka mai da hankalin su kan ta, ta yunƙura zata bar falon amma abun yaci ƙarfinta, haka ta tsaya ta yi shi a falon.
"La'ila ha ilalla la, Muhammad rasulillah Sallallahu alaihi Wasallama, Imran me nake gani haka? Ba dai ciki ne da Yarinyar nan ba?"
Gaba ɗaya Imran ya dirirce yace 'Amm, mm dama, dama fa bata da lafiya Ammi, ba ta jin daɗi jiya har Asibiti muka je aka ce typhoid ne da ulcer ke damunta"
"Zan ɗura maka ashar ka kuma nema ka rainamin hankali, uwar typhoid ɗin da uban ulcer, kalli yadda yarinya ta ɗashe, tai haske amma kace min ulcer"
"Allah Ammi ba su cemin ta na da ciki ba"
"Rufemin baki, ni zaka rainawa hankali, wannan uban aman da tai ne za ka ce wai ma malaria ne, ka kyauta ds tsallake umarnina Imran, amma ka tabattar ka nemwa ɗan da zata haifa wata kakar ba ni ba, dan ba zan karɓi ɗan da ya fito daga tsatson karuwai ba, dan bani da tabbas na ka ne ko ba naka ba"
Duk da Amira na fama da kanta, dan a inda ta gama amana, ta kwanta akan kujera, gaba ɗaya jikinta yai sanyi, gaɓoɓin ta na mata ciwo, ga wani irin azababben ciwon kai da jiri da ke damunta.
Ihsan kuwa ɓangaren ta tayi da sauri, tana kuka yanzu Dagaske Amira ciki ne da ita, shikenan ta tabbata Imran ya zama nata, dan yadda yake ƙawazucin ta samu ciki ba ta samu b, Amira ta samu ze sake tattare wa ne a gurinta.
Nan ta sake jinjinawa ƙarya da rashin alƙawarin maza, yanzu duk daɗin bakin nan da yai ta mata, da alwashinsa akan ba ze kusanci Amira ba, katsam se aka haihu a ragaya, wai Amira da ciki.
Ta sake rushewa da kuka hadda sheshsheƙa.
Shikuwa Imran cigaba da lallaɓa Ammi yayi da rantse rantse, "Ammi dan Allah karki sheganta abunda take ɗauke da shi, wallahi Ammi Amira ba karuwa bace ba, na rantse miki"
"Eh tunda dama taje ta maka surkullen da zatayi dole ka zo gabana kana gayamin haka, kana nufin duk gantalin da ta dinga yi, har wasu garuruwan da'awa ta tafi ko jihadi? Ina ce nan hotunan ta suka dinga yawo tana rawar gala, wace 'yar mutuncin ce za tai abunda tayi?"
"Na sani Ammi, amma maraici ne da rashin gata ya sa ta tashi a haka, amma ba karuwa bace"
"Wallahi ka kuma cemin ba karuwa bace, zan zabga maka mari, shashasha dama tunda ka saki labule da ita ai dole ka faɗi haka, kar idan ka koma ta hanaka, ka kyautawa ranka, kuma bari in naka kashedi, billahilazi duk ranar da ka kuma dukar min yarinya saboda kilaki seta bar gidanka a ranar, kuma yanzu ma ba ƙyale ku nai ba, ba zan bari a haifi wannan cikin a gidan nan ba, dan ina tantama a kansa, ka bani mamaki ka bani kunya idan har kai ke da alhakin cikin nan Imran, kuma zan maka kashedi da gargaɗi idan harka kusakura ka canzawa Ihsan, ko kai mata wani abu mara daɗi naji labari, wallahi zamu gauraya da kai.
Ta juya ta nufi paet ɗin Ihsan.
Da sauri Imran ya nufi in da Amira ke kwance, ke ta zubar da hawayw jiki ba ƙwari.
Ya sa hannu ya ɗagata cak ya shiga da ita parr ɗinta, a gurguje ya ɗakko duster ya goge aman, dan kar ma Ammi ta fito ta ganshi yana aikin aman da Amira tayi.
"Ihsan dan Allah ki dena wannan kukan, ki zuba ido zan ɗau tsatsuran mataki akansu, wannan cikin baza'a haife shi a gidan nan ba, ban taɓa tsammanin Imran ze kaucewa magana ta ba, yaje ya aikata abunda ya ga dama ba, amma kiyi haƙuri dan Allah"
Ihsan dai kasa magana tai, saboda batun cikin nan ya girgiza ta, Ammi ta dinga rarrashin ta,
sannan tace "gaskiya Ihsan dole ayi wani abu, idan da yiwuwar aje Asibiti a dubaki, ya za'ai ita harta ɗau ciki ke kuma haryanzu shiru, ko dai wani abun ki ke yi ne?"
"Ni ba abunda nake yi"
"Amma abun da mamaki gaskiya, gaskiya ki shirya kije Asibiti, dan tunda ita ta samu Imran lafiyarsa ƙalau maybe matsalar daga gare ki ne, kije a bincika"
Ihsan ba tace komai ba, dan abun ma haushi ya bata, kwata kwata yaushe akai Auren da za'a fara wannan maganar, ai yadda ba ta samu ciki ba dole Amira ma ta rasa nata.
Ammi dai ta gama maganganunta ta tafi, a harabar gidan ta tarar da Imran, yace "Ammi kin fito?"
"Bam sani ba, sakarai wanda ya rako maza duniya, har kake rawar kai akan karuwa, ka mari ƙanwarka Saboda ita, kake wulaƙanta matar da take sonka saboda Allah, nutsatstiya kamila duk saboda karuwa ko Imran? Ka kyauta nima ka saurari matakin da zan ɗauka, saboda gaza cika umarnin da na baka"
Ya sunkuyar da kai yai shiru, tayi ta gama sannan ta tafi.
Tana tafiya Imran ya koma part ɗin Amira da sauri, ya tarar tana nan in da ya kwantar da ita.
Da hanzari ya kulle ƙofar part ɗin ya haɗa ruwan zafi, ya cire mata kayan da tai aman a jiki, ya ɗauke ta zuwa banɗaki.
Wanka ya taya ta tayi, sannan ya kamo hannunta zuwa bedroom, ya zaunar da ita a bakin gado ya shiga share mata hawayenta yace "Amran, dan Allah ki dena kukan nan haka, insha Allah komai ze wuce, kinga Amm tazo ta ɗagamin hankali, ga rashin lafiyarki ga kuka kina yi, da wanne zanji? Dan Allah ki dena kuka Amira"
Ya dinga share mata hawaye, yaje fridge ya ɗakko tuffa, ya zauna ya yayanka mata ya bata, ya samu ta karɓa ta ci sosai.
Ya bata wasu kayan ta saka sannan ya rungumota zuwa mota.
Ihsan na jin ƙarara motar Imran, ta tashi da sauri ta leƙa, ga hango ya saka Amira a gaban motar sun fita.
Kuka ta fashe da shi tace "wallahi da ni kake zancen Imran, za ka gane ba ka da wayo, zaku ga abunda zan muku, daga kai har ita se na ga baya Wannan cikin, Allah ya isa tsakani na da kai Imran!"
Tai maganar tana dukan bango, ta zube ta cigaba da kuka a gurin.
Imran ya kalli Amira yace "Amran, ko Asibitin su Anty zamu?"
Amira tace "A'a"
'saboda me"
"Gaskiya kunya nake ji, kar inje cikin ne da gaske"
Imran yace "to da da wasa ne? Ai tun da kika ji Ammi ta faɗa cikin ne Amira, ni dai Allah ya tabattar"
Ajiyar zuciya tayi, ta tuno da kalaman Ammi, na ba zata karɓi duk wani jika da ga tsatson karuwa ba.
Gaba ɗaya jikinta yai sanyi, rai shiruu ba ta kuma cewa komai ba.
Wani Asibitin kuɗi sukaje, suka ga likita aka rubutawa Amira teses, Sedai sakamakon ya nuna tana ɗauke da juna biyu na watanni biyu.
Imran ya dinga washe baki yana murna, yace "Allah ya raba lafiya ya in ganta mana my Wife"
Murmushi tai kawai ta sunkuyar da kai, dan ba wani murna take da cikin ba, mussaman idan ta tuna da kalaman mahaifiyar Imran.
Aka basu magunguna, aka ƙara mata ruwa da allurai, sannan suka nufi gida.
Da suka koma gidan ma dai, kwanciya Amira ta kuma yi duk da ɗan ji ƙarfin jikinta ba kamar da ba.
Imran yace "Amran, Sannu kinji, Allah ya raba ki da cikin nan lafiya, ya nunamin abun da zaki haifa"
Tai murmushi cike da damuwa tace "Ameen, Amma"
"Amma me?"
"Ka na ji Ammi tace ba ta son abun da zan haifa, dan bata yadda ma naka bane"
"Shh, ya isa haka, ni da nai ai na san nawa ne, kuma Allah sheda ne,dan haka ki dena damuwa masoyiya, Ammi ma zata gane abunda take miki ba daida bane, amma dan Allah ki yafe mata saboda nasan hakkinki ze kamata"
Ta ɗan gyara kwanciyarta tace "Hubby, bani fa kowa se Allah seku, ina son in riƙi Ammi uwa a matsayin matar da ta kawo mijina duniya, kuma matar uba a gurina, wato wan mahaifiyata, dan haka ban taɓa riƙonta da Allah yai mata wani abu saboda abunda take min ba, ina fatan Ubangiji Allah ya sa ta kalleni a matsayin 'ya kuma matar ɗa ne kawai"
Imran yai ajiyar zuciya yace "Your heart isa always different Amira, nagode Sosai Ubangiji Allah yai miki tukuici da gidan aljanna"
"Nima nagode Sosai, Ubangiji Allah ya tsaremin kai a duk in da kake, yasa ka gama da duniya lafiya"
"Ameen sweetheart" yai maganar yana kissing goshinta.
Ya miƙe ya fita daga ɗakin, Amira ta lumshe idanunta ta na tunanin maganganun Ammi, anya akwai lokacin da ze zo Ammi ta so ta kuwa? Bata ƙaunar ta ba ta taɓa tunanin wannan ƙiyayyar za ta gushe da ga ran Ammi.
Kiran Anty ne ya shigo wayarta, ita ta manta da batun wata wayana dan kusan kwana biyu ba ta ko ta;a wayar ba.
Ta miƙa hannunta ta ɗakko wayar, ta saka a kunnenta "hello Anty"
"Amira lafiya kuwa, tun ɗazu nake kiran wayarki baki ɗaga ba"?
"Am sorry Anty, munje Asibiti ne na bar wayar a gida"
"Subhanallah waye ba lafiya haka?"
"Anty nice"
"Ahh to ko dai abun ne ya samu?"
Amira tai shiru cike da jij nauyin Antyn, Anty tace "Masha Allah Alhamdilillah ala kulli halin, Allah kai ne abun godiya, amma meyasa baku zo Asibitin mu ba?"
"Eh yace muzo nan, nikuma gaskiya ni na ce kar muzo nan"
"To meye a ciki Amira, ai abun farinciki ne, abun jin daɗi ya same mu, Ubangiji Allah ya raba lafiya, irin wannan ai seki gayamin, ko Abinci in dinga aiko miki, dan nasan irin wannan situation ɗin bakomai zaki iya ci ba"
Amira tace "hmmm" a ranta tace dama Ammi ce ke wannan farinciki haka, duk da cikinta ba halak ne, amma tana jiyewa abunda zata haifa ƙiyayyar da ze fuskanta daga dangin ubansa.
Anty tace "Amira lafiya kuwa, naji kin ce hmmm kuma kinyi shiru?"
Kawai Amira ta fara kuka, cikin damuwa Anty tace "Ya salam, Amira menene? Ki gayamin meyafaru?"
"Anty bana son in dinga gayamiki abun damuwa, amma har ga Allah bana farinciki da cikin nan"
"Kai Amira baki da hankali ne? Wasu an nema ido rufe da kuɗinsu kice ba kya murna da cikin? Kina kallon abokiyar zamanki ban sani ba in ba yanzu ba, Amma Allah be bata ba, ke kuma kin samu zaki ce ba kya murna? Meye hujjarki bayan da Aure kika samu"
"Anty, Ammi tazo gidan nan da safe, a gabanta na dinga amai sedai ta nuna ba ta maraba da hakan, kuma tace ita tana doubting idan na Imran ne" ta ƙarasa maganar cikin kuka.
"Innalillahi wa innalillahi raji'un, ni wai meke damun Hajiya Jamila ne kamar ba taje makaranta ba? Wane irin abu ne haka take yi kamar ba musulma ba? Idan ita bata maraba da shi mu munayi, kuma ɗanta yasan ai ɗansa ne, dan haka kark kuma sa wanan a ranki, mu mun gode Allah da ya raba baiwar sa ya bamu, Allah ya rabaku lafiya in ba sa so kema kuma va kya so, in kin haifa ni ki bani, dan Allah ki kwantar da hankalinki, ki raini cikin ki ki haihu lafiya, idan kika kuskura jininki ya hau da ciki, zaki iya jijjiga idan kin haihu, dan haka kar inji ko in ga kince ba kya son ciki, ki lallaɓa abunki kiyi Addu'a Allah ya rabaku lafiya kin ji jo?"
Amira tace "To Anty Insha Allah"
"Yawwa Amira, me kike buƙata in sa Fadila ta girka miki a kawo miki?"
"Bana son komai Anty, naci Abinci"
"To shikenan, da kinji kina son wani abun ki kirani a waya kinji Amira"
"To Anty insha Allah, nagode Sosai"
"Yawwa, Allah yayi albarka"
Amira ta ajiye wayar.
Imran kam ɓangaren Ihsan ya nufa, yaje ya tarar da ita tasha kuka, duk tayi wani iri saboda azabar kishi, tausayinta ne ya kama shi, duk da wasu lokutan halinta ne yake ja mata komai, amma yaje ya zauna a kusa da ita, sedai yana zama ta matsa daga kusa da shi.
Hannu ɗaya ya saka ya janyita ta ƙarfin tsiya, tana fizge fizge amma ya riƙeta gam ya zuba mata ido, cikin kwantar da murya yace "haba Ihsan, wallahi kin bani mamaki, yanzu duk da tarin soyayyar da ki ke min amma zaki iya juyamin baya haka? Gaba ɗaya kin watsar dani, ta yaya Hankalina baze karkata wani gurin in nemawa kaina mafita ba?"
"Dan Allah ka ni ka ƙyaleni, kaje ka ƙarata ka rabu dani bana son ganinka ma, maci amana kawai, ka min alƙawarin da ka san ba zaka iya cikawa ba, kuma kana nema ka juyamin baya"
Imran yace "tabbas nayi dana sanin yi miki alƙawarin da na gaza cikawa, amma ni ko sau ɗaya bani da niyyar juya miki baya, kece ma ki kai watsi dani gaba ɗaya, kuma karki kalli tarayyata da Amira a matsayin cin amanarki, Ihsan na biye miki a baya nayi kuskure, saboda Amira itama matata ce tana da hakki a kaina, ama na take na dinga biye miki dan kar hankalinki ya tashi, amma ni haryanzu ina sonki a raina, matsayin Amira daban a gurina, kema matsayin ki daban a gurina dan Allah ki kwantar da hankalinki mu rayu cikin kwanciyar hankali"
"Ba dai dani ba, kaje can dai ka rayu da ita ba da Ihsan ba"
Riƙe ta yai ya fara kissing ɗinta a hankali, amma ta dage iya ƙarfinta tana tureshi, Imran ya kalleta yace "Ihsan meke damunki hakane?"
Ta tofar da yawun bakinta tace "ban sani ba, Allah ya kiyaye ka haɗa baki da Karuwa sannan ka samin bakinka a nawa Allah ya suttura"
Murmushin takaici yayi Yace "she's virgin, ba Karuwa bace, idan ma karuwar ce ta fiki sona duk da yadda ki ke da'awar kina so na, da Amira ce ba zata mik abunda kike min ba, duk da tarin laifukana a gareta ba ta taɓa watsar dani kamar yadda kike ba, satina biyu da dawowa amma kin ƙauracewa shimfiɗa ta gaba ɗaya, na biyoki amma still kin min wulaƙanci, dan me ba zanje in da za'ai maraba da ni ba? Amira na da wata daraja ta mussaman a idona, saboda halayenta, abunda tai a baya ma kuskure ne, ina fatan Ubangiji Allah ya yafe mata, kiyi wa kanki faɗa Ihsan kishi ba hauka bane, gidan Annabi Sallallahu alaihi Wasallam mata goma sha ɗaya ne, duk da son da yake wa Nana A'isha radiyallahu anha, abokan zamanta goma ne, balle ke Ihsan, ina ilimin ki da na sanki da shi? Ina tarin karatunki na addini, duk kishi yasa kin ajiye a gefe? Allah ya ganar dake akan lokaci, ki shirya jibi insha Allah zan tafi Lagos, tare zamu tafi"
"Ba zani ba, ka ɗau barbaɗaɗiyyar matarka ku tafi tare"
"Ai kuwa ko a ƙafa na jata bina za tayi, matar aljanna kenan"
Ihsan taji kamar tabi Imran ta shaƙeshi.
Yana fita ta kuma rushewa da kuka, ta sa hannu ta ɗauki wayarta tana kuka ta kira Mummy.
"Hello Mummy kina ina ne?"
"Ina gida lafiya?"
"Mummy Ina fa lafiya, Mummy Imran ya yaudareni mugu ne, bayan tafiyar su Lagos kinga ta dawo da ciki, gaba ɗaya wulaƙanci yake min, ya dena saurarata ya dena shiga harkarta na shiga uku Mummy ta ƙwacen mijina"
"Innalillahi wa innalillahi raji'un, dagaske ciki ne da ita?"
"Ciki ne da ita Mummy, kuma yau a gaban Ammi ta dinga amai"
"To me Jamilar tace?"
"Mekuwa tace? Ta yi musu hargowa ta tafi, na abunda yafi damuna shine da tace min wai inje Asibiti a dubani, ɗanta lafiyarsa ƙalau tunda matarsa ta samu ciki, ni shikenan na shiga uku"
"Ki kwantar da hankalinki Ihsan, ba ki shiga uku ba"
"Wallahi na shiga Mummy, shikenan Bani da wani amfani yanzu, zuwa nan gaba duk da tace ba zata krɓi jika da ga gurin karuwa ba, nan gaba idan ban haihu ba, ko dai ta karɓi 'ya'yan Amira, ko kuma ko ta sa ya ƙaro Aure"
"A'a ki kwantar da hankalinki, hakan ma ba zata faru ba insha Allah"
"Mummy k ka ce in kwantar da hankali na, how? Ta yaya Hankalina ze kwanta, bayan ni da ke mun san batun kwanciyar hankali babu shi? Shikenan ni na san abunyi, sedai a zauna kowa ma ya rasa"
Ta kashe wayarta ta zauna a gurin tana cigaba da kuka.
Da daddare Imran yana gurin Ihsan, sedai fafur taƙi sauraron sa, shikuma ya gwada mata ƙarfi, gaba ɗaya Abun duniya ya sake ƙule Ihsan, ya tashi yai tafiyar sa ya barta, nan ta ƙara tabattar da Imran yanzu ba ta gabansa.
Ya kints jikinsa ya shiga gurin Amira, ya tarar tana bacci amma jikinta raɗau da zazzaɓi, ya shafa gashin kanta ya sumbaci goshinta sannan ya bar ɗakin.
Da safe ma seda ya koma gurin Amira, ya tarar idonta biyu ya dafa tea ya bata, tai wanka yace "ko kina sha'awar wani abun in siyo miki"
Tace "A'a bana son komai, idan naci ma amai zanyi"
"Sannu Amira"
"Yawwa my dear"
"Bana jin daɗin rashin cin Abincin nan da kike yi"
"To ya za'ayi larura ce ai, kasan me nake sha'awar ci?"
"Se kin faɗa"
"Ina wannan tebar da aka kawo mana, ranar da muka je Lagos?"
"Eh na gane"
"To da zan samu ita nake so"
Imran yace "bari in fita zan duba gurin masu sai da Abinci, ko zan samu"
"No i don't mean you should buy it for me, kawai dai gaya maka nayi"
"Da na iya da da kaina zan miki Amira"
Amira tai murmushi tace "Never mind"
Imran ya gyara zama yace "Amira, zan koma Lagos , amma Ihsan ta ƙi yadda mu tafi tare, kinga dama ba ki da lafiya ko zamu tafi tare?"
Girgiza masa kai tayi tace "A'a, ai wannan zuwan da ita ya kamata ka tafi, idan ka tafi dani ba kayi adalci ba".
"Amma kin san haryanzu akwai sauran sati uku da ya kamata muyi tare, watanmu biyu da sati ɗaya da ita lokacin da muka tafi Lagos"
Amira ta harareshi tace "meya hana a biyani tun a wancan lokacin se Yanzu?"
Yai murmushi yace "Allah ya baki haƙuri"
"Yawwa Amran, dan Allah nace ina son zuwa Kano, ko sati biyu inyi kan ka dawo"
"Wa kika ajiye a Kanon da zaki je?"
" 'yan uwana mana"
"To ban yadda ba, ko zaki ba Yanzu ba"
"But Why?"
"To banda Fa'iza gurin wa zaki je? Kuma ko sati biyu ba'ayi da barin su nan ba"
"Haba Amran, ko ba komai Yakamata in je, tunda na baro Garin ban kuma zuwa ba fa"
"A yanzu dai ban yadda kije ba, sedai ko nan gaba"
"Shikenan"
"Yawwa tawan, shiyasa nake yinki, duk