Showing 114001 words to 117000 words out of 120332 words

Chapter 39 - WUTA A MASA?A COMPLETE HAUSA NOVEL BY AYSHERCOOL

10 Mar 2025

30357

mata ido kamar wata sabuwar halitta daban.

Ihsan kuwa ta cika ta batse, ganin yadda hankalin kowa ya koma kan Amira, ta kwashi jakarta tai tafiyarta daga gidan.

Imran yana nan zaune kusa da Amira, ta motsa a hankali tana, ya zuba mata ido a hankali tayi miƙa tare da yin salati.

Imran ya matso kusa da ita yace "My Amran ya jikin?"

Ta kalli Imran tai murmushi tace "bacci nayi ne haka me nauyi?"

Imran yace "eh kusan haka"

"Ina su Antyn ko sun tafi sun barni?"

Imran yace "kin san lokacin da kuka zo ne?"

Tace "Na sani mana"

"Amira baki missing ɗina ba ko?" Ya ɗan faɗa a shagwaɓe.

'ni na isa ince bana kewar ka, tsoro nake ji kar in taɓaka inji wani abun"

Janyo ta yai jikinsa yace "ba abun da za kiji ai kin warke"

"Wallahi tsoro nake ji" ta faɗa kamar za tai kuka.

Nan Imran ya warware mata abunda yaf faru gaba ɗaya.

Sosai ta fashe da kuka tana tunanin laifin me tayi wa wani haka, da za'ai mata wannan abun.

Imran ya rungumeta yana ƙoƙarin kawar mata da damuwar da ta tsinci kanta a ciki.

Ya kalli cikinta yace "Allah sarki yarona ya sha wuya, Allah yasa karki haifeshi da lotsatsen kai, saboda yadda ki ka dinga faɗuwa da cikin nan, Alhamdilillah yana nan be zube ba"

Tai murmushi tare da shafa cikin nata.

"Imran yaya ta farka ne?"

Suka ji muryar Anty na nufo ɗakin, a sukwane Imran ya sakko daga kan gadon, ya gyara yace "eh ta farka"

Kallo ɗaya anty tai musu ta maze tace "Alhamdilillah, Amira ya kike jin jikin naki yanzu?"

"Alhamdilillah Anty"

"Kin warke dai ko yanzu ba ƙadangarun?"

Sunkuyar da kai Amira tai tana murmushi.

Anty tace "Abba ya tura ai muku saukar Alqur'ani a gida, ki fito jama'a su ganki aji daɗi, kin samu sauƙi".

Imran yace "Anty amma zamu iya tafiya gida ai ko?"

"A'a seta ƙara murmurewa"

A marairaice Imran yace "Anty, ina cikin damuwa sosai, sedai na barwa Allah komai amma dan Allah ki sa baki a bani Amira mu koma gida yau tunda taji sauƙi Please"

"Kai amma dai ba haka naso ba gaskiya, naso ka bari muga improvement ɗin da za'a samu, amma ban san dalilinka ba, zanwa Iyayen naka Magana, daga nan kawai ku tafi"

Imran yace nagode sosai Anty, Allah ya biya ki da aljanna.


Ammi kamar taiwa Imran dukan tsiya haka take ji, saboda wannan rawar kan da yake akan  Amira.

Kamar yadda ya buƙata, da magariba ya ɗau Amira suka tafi gida tare, dan ba kunya ya nuna yana buƙatar matarsa a tare da shi.

Da suka je gidan ma, nan nan ya cigaba da yi da Amira, tamkar mata ɗaya gareshi, ko da wasan wasa be kalli sashin da Ihsan take ba.

Amira ta fuskanci ko zancen Ihsan baya son ji.

Bata dame shi ba itama, ta shiga hidima da mijinta, Imran kuma fafur ya hanata aikin komai, shima ya shiga lallaɓata.

Duk da shima yana fama da kansa, ita ma warkewar ta kenan, amma tabbas sunyi missing juna Sosai da sosai.

Tun Amira na tsoron kar wata matsalar ta sake faruwa, amma taga ba abunda yafaru, tun tana fargaba harta haƙura ta saki jikinta da shi.

Imran ya dage akan kula da Amira, da Addu'oin da aka bata da sauransu, da kansa yake kaita Asibiti gurin awon ciki.

Se dai tunda Amira ta koma gidan kuma take munanan mafarkai da Yadikko, ta ja bakinta tai shiru ba ta gayawa kowa ba.

Tuni ta gyara wayarta, ta shiga waya da su Anty Fa'iza, da sauran abokan arziki, a ƙasa da sati guda tai ras kamar ba ita ta sha wannan wahalar ta watanni ba.

Imran na zaune a falo, yana bawa Amira Abinci a baki tana ta zuba taɓararta.

Ihsan ta faɗo falon kamar korarriya, Imran ko ɗaga kai be ba balle ya kalleta.

Ihsan tace "wallahi Imran Allah ya isa tasakani na da kai, mugu Azzalumi kawai, abunda ka ke min se Allah ya saka min, kuma insha Allah se alhakina ya kuma kama ku, ba iya aljanu se tayi hauka tuburan ta bi bola".

Amira tace "da ikon Allah ba zanyi hauka ba Ihsan, kema kuma ba zaki ba"

Imran yace "Ihsan ni kike cewa Allah ya isa ko?"

"Eh na faɗa, Allah ya isa azzalumi mara adalci"

"Ni ban hukunta ki saboda naki halin ba, ni zaki zo kaina ki gayawa wannan miyagun maganganu haka ko? Lallai nayi ganganci na kuma godewa Allah da ya sa ban zamo daga masu butulci ga iyaye ba, Mahaifina ya zaɓa min mata ina hangen tasowar Wuta a Maƙera katsam se ga WUTA A MASAƘA, kallonki kawai nake Ihsan, na miki talala ne, akwai Ranar da dubun ki za ta cika"

Be tsaya saurarata ba ya tashi ya bar falon, Amira tabi bayansa da sauri, tana ganin rashin kyautawar abunda Imran yayi.

Sedai tana shiga bedroom ɗin taci karo da wayarta tana ringing.

Sunan Sisto ne akam wayar, ta ɗaga wayar ta kara a kunnenta, "Amira Yadikko fa babu lafiya, ita da Amina, an kasa gane kan abunda yake damun su, Yadikko na ta kiran sunanki"

"Innalillahi wa innalillahi raji'un" shine abunda Amira ta faɗa ta fashe da kuka.

Imran yace "ke lafiyarki kuwa?"

"Yadikko ce babu lafiya, gobe in Allah ya kaimu Kano zanje"

"Kano kuma, ga tsohon cikin zaki tafi Kano?"

"To kana ji Yadikko ba lafiya, idan kuma ta mutu fa ban ganta ba?"

Shi mamaki ne ma ya isheshi, yanzu dui da tarin abunda Yadikko tai mata, amma tana kuka saboda Yadikko ba lafiya, sosai ta birkice da koke koke.

Imran yace "kwantar da hankalinki, naji da kaina ma zan kaiki, ai kinyi ƙoƙari tunda aka kawo ki Garin nan baki je gida ba"

Ko bacci bata iyayi ba, da ƙyar ta iya haƙuri zuwa wayewar gari.

Wajen ƙarfe goma, suka nufi hanyar Kano, Imran ya sai kayayyakin da za su je dubiyar da su, suna tafe tana kuka Imran yana kwantar mata da hankali.

Se azahar suka isa Kano, suka tarar da mutane sosai a gidan su Amira, da sauri Amira ta shiga gidan, ta shiga ɗakin Yadikko, tana zuwa ta tarar da Yadikko a kwance, duk fuskarta ta kumbura suntum tayi baƙi, duk gashinta ya kaɗe ta zama kamar wata horror.

Ga su Baba da Kawu duk a zazzaune suna share hawaye.

Amira tace "Yadikko meya sameki haka?"

Yadikko ta fashe da kuka tace "Amira dan Allah ki yafemin"

Amira tace "Ni ba abunda ki kaimin Yadikko, meke damunki ne?"

"Amira tun tasowarki nake cutar da rayuwarki, na kasance me biye biyen malamai, tun lokacin zamana da kakarki, bana ƙsuanarta sam, malamai suka gayamin idan kin girma zaki zama wata, shine hankalina ya ƙi kwanciya, na sa aka haɗaki da aljani, dan ki lalace amma abu ya ƙi yiwuwa, shine na dinga haɗawa da makirci ina ce miki karuwa, Auren nan da ki kai a raina yake, jikokina naso mijinki ya aura ba ke ba, da naje gidanki naga daular ki ke ciki, abun ya sake ƙuleni, shine naje nasa a kai miki Asiri da ƙadangare, gashi yanzu abun ya dawo kaina ni da Amina, tana can an kulleta tana hauka tuburan, dan Allah ki yafemin Amira!!!


Domin gyar, sharhi ko shawara
Ayshercool
07063065680.
[2/28, 6:24 PM] Ayshercool: 🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥

WUTA A MASAƘA

PERFECT WRITERS ASSOCIATION

(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS)

https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P. W. A

*Story and written by*
AISHA ADAM (AYSHERCOOL)

The experience writer of

*ABDUL JALAL*
* WATA KISSAR.... (SAI MATA)
*BAƘIN TABO (Labarin gasa)
*AƘIDATA (Paid Book)
* WUTA A MASAƘA

https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=in

❌❌❌
Ƙirƙirarren labari ne, ban yadda ayi amfani da kowane sashi na labarin ba ba tare da izinina ba.


*_Assalamu alaikum warahmatullah, ina miƙa saƙon ta'aziyya ga ɗaukacin dangi na bisa ga rashi da mukayi na Kakana, ina fatan Ubangiji Allah ya jikansa da rahama, ya gafarta masa. Ina miƙa saƙon godiya ta ga wanda suka kirani a waya, da wanda suka turamin saƙonnin ta'aziyya, na gani Nagode sosai Ubangiji Allah ya bar zumunci ya bada lada, Nagode sosai_*


                           53-54


Rawa jikin Amira ya fara yi, ta matsa gefe daga kusa da Yadikko tana bin ta da ido kamar ta ga wata aba daban.

Baba yace "dan Allah Amira kiyi haƙuri, ki yafewa mahaifiyata, tabbas nasan mun biye mata gurin muzgunawa rayuwarki da tsangwamar ki, wanda haka kakarki ta fuskanta daga gare mu zuwa mahaifinki da ke kanki, amma ban zaci Yadikko zata iya yi miki Aisiri haka ba, amma dan girman Allah ki yafewa Yadikko Amira"

Amira kam kasa magana tayi, se fashewa da wani irin kuka na tausayin kanta, Yadikko ta cutar da ita cuta me munin gaske, ba dan Allah ya temake ta ba da yanzu tana can tana hauka.

Imran da yake tsaye a bakin ƙofa ya ji komai, ya tako cikin ɗakin ya kalli Yadikko yace "da yawa abun da mu bayi ke mantawa da shi shine, ita duniyar ba matabbata bace ba, ita wadda ki kai kishin da ita yau tana ina? Shi wanda ki kai kishin akansa yana ina? Shi mahaifin Amiran shina da kika azabtar yana ina? Tunaninki ke kiyi gadin Duniyar kenan? Meye a cikin duniyar gaba ɗayanta, meye laifin da Amira tai miki a rayuwa? Ba ita ta tsarawa kanta irin ratuwar da za tai ba, Allah ne ya tsara mata dan me zaki ce se an canza? Ke da Allah dan ƙarshen cutarwa kin mata, tunda kika so haukata ta, kuma ko da Amira ta rasa hankalinta ba zan taɓa yadda in auri jikokokin ki ba, saboda na gane duk abunda kike faɗa akanta sharri ne kawai da makirci Amira ba mutuniyar banza bace, wahala ce ta maida ita haka, kuma insha Allah in har ina numfashi, Amira ba zata tagayyara ba, zan zame mata uwa uba ɗan uwa sannan kuma miji, insha Allah wahalarta ta zo ƙarshe, ba zata sake kukan maraici ba"

Yana gama maganar yasa hannu ya ɗago ta tana ta uban kuka, ya janyo hannunta za su fita daga ɗakin.

Baffa Salahu ya riƙe ƙafar Imran yace "dan girman Allah Imran kuyi haƙuri,  kasa baki ta yafewa Yadikko"

Imran yace "wannan ba hurumi na bane, ruwanta ne ta yafe mata, ruwanta ne ta ƙyaleta, amma da kasan iya wahalar da ta sha tsayin watanni uku zuwa huɗu akan larurar da tayi ta isa Allah ya kamata, banda azabtar da ita da ku kai tun ƙuruciyarta banda yarfe da ƙage da kuka dinga mata, dan kawai marainiya ce, mahaifiyar ta ta auri mahaifinku, ni ba zan tulasta mata ba, tana da damar yin abunda ta ga shine dai-dai"

Ya ja hannun Amira suka fito, Sadiya ta taho da sauri gaban su Amira tana kuka tace "Amira dan Allah ki yafemin, kar inje abun da ya samu su Yadikko nima ya sameni, dan Allah ki yafemin Amira"

A fusace Amira tasa hannu ta haɗa Sadiya da jikin bango tace "duk irin azabtarwar da kukamin a gidan nan, na yi iya ƙoƙarina akan in danne zuciyata, in maida komai ba komai ba, saboda mun fito tsatso ɗaya da ku, duk ƙyama da wariya da kuka dinga nunamin, amma ban taɓa zaton zaku iya aikatamin abunda ku kai min yanzu ba, bazan yafe muku ba na barku da Allah, Allah ya bi min hakkina"

Imran ya janyo Amira, dan yaga a zuciye take matuƙa kar tai masa asarar Babynsa, dan yaga yadda jikinta yake rawa, da yadda ta janyo Sadiya kamar ita kaɗai ce ba cikin a jikinta.

Waje yai da ita, ya sakata a mota ya rufe ya zaga ya shiga ya kunna yaja motar.

Suna tafe tana kuka, Hannu ɗaya yana tuƙi ɗaya kuma ya rungumota yana rarrashin ta yace "Haƙiƙa rayuwarki darasi ce Amira, gaba ɗaya mutane na miki kallon baibai, a yayin da idan aka duba aka zago laifin na masu aibataki ne, kinyi rayuwa a wahale ba tare da mataimaki ba se Allah, ni kaina ina Nadama akan abubuwan da suka faru a baya, amma Please and please Amira, kiyi haƙuri ina ƙara naman afuwarki a karo na babu adadi, saboda nayi zaton WUTA A MAƘERA katsam sega WUTA A MASAƘA.

Amira zuciyarki me kyau ce, kina da haƙuri da yafiya, nasan an cutar dake, amma insha Allah ba zan sake bari ki zubda hawaye akan rashin wani abu ba, insha Allah zan rayu da ke da zuciya ɗaya, zan faranta miki iya gwargwadon iyawata, kiyi haƙuri ki dena kuka"

Cikin kuka tace "Imran"

"Na'am Amira"

"Imran me na yiwa Yadikko? Laifin me nayi mata? Meyasa zata min haka? Imran duk yadda zan kwatanta maka ba zaka gane azabar da sukamin ba, why? Laifin me nayi mata haka?" Tai maganar tana sake rushewa da kuka.

Parking Imran yai ya shiga share nata hawayen yace "ba abunda ki kai musu, sedai ki gode Allah ke 'yar gatan Allah ce, ya dubi zuciyar ki ya sa abunda sukai miki be tasiri akanki sosai ba ya mayar musu abunsa kansu, kuma ya ganar da mijinki abunda suke faɗa akanki ƙarya ne, ina sonki Amira son da bazan iya musalta miki ba, kuma har gobe ina jin nauyin ki akan laifin da nai miki, ki kwantar da hankalinki kinji Cwthrt, ki dena kukan nan komai ya wuce, mu koma gida mu buɗe sabon shafin rayuwa me cike da Soyayya da ƙaunar juna"

"Thank you my Brother"

Tai maganar tana murmushi, cikin son nunawa Imran ta gamsu da maganganun sa.

Yace "Never mind Dear, me zamu tsaya mu siya kici ne nasan kin fara jin yunwa yanzu?"

"Muje gidan Anty Fa'iza" ta bashi amsa.

Imran ya ja mota zuwa hanyar gidan Fa'Iza, duk da haka suna tafe Amira na share hawaye, ya fuskanci zubar da hawayen shine samun sauƙinta, dan haka be cigaba da takura mata ba ya ƙyaleta.

Suna zuwa gidan Fa'iza yai parking, ba ta ce masa komai ba ta buɗe motar ta fita, ta shiga gidan.

Da sallama ta shiga ta tarar da Bashir yana wankin kayan su, Fa'iza kuma na Kitchen tana girki.

Itama Fa'iza na ta cikin ya tsufa, dan yafi na Amira tsufa ma, da ƙyar take tafiya haihuwa ko yau ko gobe.

Fa'iza na ganinta tai murmushi, tace "lallai yarinyar nan, zuwa ba sanarwa to koma bana murna da Zuwan"

Bashir yace "ba ina da zata koma, duk da ni kunya ma naji, ban taɓa zuwa gidanta ba amma ina maraba da zuwan nata"

Yaran Anty Fa'iza kuwa da gudu suk tafi suka rungume Amira, Amira ta rungume su, sedai ta kasa Magana.

Fa'iza tace "Khairat ƙyale Amira baki ga halin da take ciki ba, kar ki buge mata kan ɗa"

Duk yadda Amira ta so dakewa kasawa ta yi, ta fashe da kuka a gurin.

Bashir yace "Subhanallah, Amira Lafiya kuwa? Meyafaru kuma?"

Kasa magana Amira tayi, se cigaba da kukan tana daga tsaye.

Fa'iza ta kama hannunta suka shiga ɗaki, tace "Amira lafiya kuwa? Ko Imran ɗin ne yai miki wani abun?"

Ta girgiza kai tace "tare muke yana waje ma"

Bashir yace "Amma kika barshi a waje? Amma ina fatan lafiya dai"

"Anty Fa'iza, kin san rashin lafiyar da nayi aka ɓoye miki kusan taɓin hankali na samu, wata na uku ko in da nake ba na son Imran ya zo, wai ashe Yadikko ce tai min Asiri, aka kirani jiya ba ta da lafiya na tayar masa da hankali se da ya kawoni yau, shine take gayamin asiri tai min? Me nayi mata haka?"

Amira tai maganar hawaye na zuba daga idonta, Fa'iza tace "Amira ki ɗauka wannan jarrabawar ki ce a haka, shekaranjiya naje gidan, da bakinta nima take gayamin ita tai miki Asiri, wanda ni ban san ma takamaiman rashin lafiyar da ki kai ba, Abba ya ɓoyemin kema da kika warkw baki gayamin ba, ance min kawai laulayi ne kike, na kaɗu matuƙa da jin abunda Yadikko ta gayamin, sedai ban miki zancen bane dan bana son tayar miki da hankali, Ba abunda za muce wa Allah se godiya da Allah yasa abun beyi tasiri akanki sosai ba"

Amira tai shiruu tana cigaba da jin yadda zuciyarta ke cigba da bugawa, da zunzurutun mamakin abunda Yadikkon ta aiakata mata.

Bashir ne yaiwa Imran iso, ya shigo Gidan, nan suka cigaba da tattaunawa gami da jajantawa juna akan abunda ya samu Amiran.

Fa'iza tai musu girki, suka ci Abinci su kai salla, sannan suka kama hanyar komawa Kaduna, sedai suna fitowa daga unguwar su Fa'iza sega Sultan a babur ze wuce.

Da sauri Amira tace "Amran tsayar min da Sultan mu gaisa dan Allah"

Imran ya sha gaban hanyar da Sultan ze wuce da mota, aikuwa a fusace Sultan yace "malam meye haka? Ko dan kaga kana mota shine zaia min wannan gangancin?"

Imran na sauke glass Sultan ya ganshi, gabansa ya faɗi dan be manta shaƙar da Imran ya taɓa masa ba.

Imran yai murmushi ya miƙa masa hannu, a tsorace Sultan shima ya miƙa masa hannu, yana son tabbatar da ko dai ba Imran bane gizo yake masa.

Imran yace "ƙanwar ka ce tace in tsaya ku gaisa"

Yana gama maganar sega Amira ta fito daga motar, Sultan na ganinta ya kafe babur ɗin ya sakko yace "Gimbiya Amira kece?"

"Nice Sultan, ka watasar dani gaba ɗaya"

Sultan ya sosa kai yace "ke tsoron mijinki nake ji shiyasa, kuma kinga kinyi Aure be dace in dinga bibiyar ki ba"

Imran ya fito daga motar yace "ka de na tuna baya, wannan ya wuce ai, kuma Amira ta gayamin dukkanin alaƙar dake tsakanin ku saɓanin ni wadda aka gayamin, kuma nagode Sosai da gudunmawar da ka bata a rayuwa, duk da ta wani fannin gudunmawar ba ta arziki bace, amma duk da haka ka temaketa, Nagode sosai, kuma ba zan yanke zumuncin da ke tsakanin ku ba, insha Allah duk ran da muka zo Kano, zan nemeka ku gaisa"

Sultan yace "Alhamdilillah, Allah sarki rayuwa, inaiwa Amira burin Auren mutumin daze kula da ita, saboda wahalar rayuwa da ta sha, da fari banji daɗin Aurenka da ita va, amma yadda na ganta ya tabattar min tana cikin nutsuwa sosai, Allah ya ƙara haɗa kanku ya baku zaman lafiya"

Imran yace "Ameen ya Allah, nagode Sosai Sultan" yaiwa Sultan alheri sannan suna tafi.

Amira tace "meyasa ka yadda muka gaisa da Sultan, har ka masa alheri ka yadda da cigaban zumuncinmu?"

Imran yace "Saboda na baki dukkanin yarda Amira, na san ko bana raye ba zaki zubar da mutuncinki ba, sannan Son da Sultan yake miki gamon jini ne kawai, ba sonki yake dan ya Aureki ba, yana sonki dan tausayin ki ne, kuma tare na ganku, dan haka be kamata in datse zumuncin ba, kuma insha Allah zan cigaba da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login