Showing 117001 words to 120000 words out of 120332 words

Chapter 40 - WUTA A MASA?A COMPLETE HAUSA NOVEL BY AYSHERCOOL

10 Mar 2025

30345

bibiyarsa in ga ta inda zan temaki rayuwarsa, kamar yadda ya temaki taki da koya miki rashin ji"

Murmushi Amira tayi da seda haƙoranta suka bayyana, a lokaci guda kuma hawaye na bin kuncinta.

Imran yan cigaba rarrashin Amira, yana sake kwantar mata da hankali da bata tabbacin zeyi iyayin sa, dan ganin ta samu farincikin da bata samu a baya ba.

Amira ta nisa tace "Amran, na yadda da duk abunda ka faɗamin, sedai haryanzu ina da sauran damuwa sosai"

"Damuwar meye?" Ya tambaye ta.

"Har yanzu Ammi ba ta ƙaunata, sannan bana son kaiwa Ihsan irin abunda kaimin nasani babu daɗi, ni idan na yafe maka ita ba lallai ta iya yafe maka ba"

Haɗe rai Imran yayi yace "me nayi mata?"

"Ka dena shiga sabgarta, ka dena zuwa inda take gaba ɗaya, ranar kwananta ba ka zuwa inda take sedai ka kwana a ɗaya bedroom ɗin nawa, baka cin Abincin ta, wannan abun babu daɗi sam, nasan ciwon hakan dan Allah kayi haƙuri ka koma mata, kar a shiga hakkinta, bana son Allah ya kama ka da laifin rashin adalci"

Kallon Amira yai, yana jinjinawa haƙurinta, yai murmushi yace "'yar aljanna kenan, Allah ya barmin ke Amirana, kullum zuciyarki fes kamar Abba haka kike"

"Naji kana neman ka maida abun jokes"

"Au aljannar ce jokes Amira?"

"A'a ba haka nake nufi ba, But atleast ya kamata ka ɗau maganar tawa da mahimmanci"

Yace "serious na ɗau maganarki Amira, Ammi zata gane abunda takeyi kuskure ne nan ba da daɗewa ba, sedai kamar yadda kika fuskanci ƙaddara a taki rayuwar, nima Auren Ihsan ne tawa ƙaddarar"

Ta kalleshi da mamaki tace "kamar yaya kenan?"

Gaba ɗaya annurin fuskar Imran ya ɗauke, damuwa ta maye gurbin fuskar tasa, idanunsa su kai jawur yace "Amira a zamana da Ihsan, na mata dukkanin adalcin da zaka iya yiwa abunda kake so, kina kallo saboda ita na biye mata na kasa sauke  naki hakkin da ke kaina, sedai ina tunanin wuta a maƙera se ga
WUTA A MASAƘA!"

Amira tace "nifa ka sani a duhu, me kake nufi ne?"

"Zaki gane very soon, but let's keep this aside, Bana son Maganar gaba ɗaya"

Se bayan la'asar sosai sannan suka isa Kaduna, a part ɗin Amira suka sauka, yai ya jasu jam'i sukai sallar la'sar tare.

Amira tace "My me zan ɗora maka ne, nasan kana jin yunwa yanzu"

Imran ya kalleta yace "No, ba zaki wahalar min da kanki da Babyna ba, zanje in mana takeaway"

Amira ta ɗan yatsina fuska tace "nifa kasan ban fiye san Abincin siyarwa ba".

"Ni kuma baza'a wahalar min da mata da ɗana ba"

Amira tace "masu mata da ɗa manya"
Tai Maganar tana murmushi ta shafa cikin nata tace "Allah ne yayi cikin na da nisan kwana, da tuni babu shi"

"Ai ba ƙaramin godiya nake wa Allah ba, ni kaina nasan ikon Allah ne ya riƙe cikin nan, ina fatan Allah ya ƙara inganta mana shi, ya rabaku lafiya"

"Ameen my Amran"

Haka suka cigaba da hira se daf da magariba sannan ya tashi ya fita salla, daga nan ya samo musu abunda zasu ci.

Amira ta tashi gaba ɗaya jikinta a sanyaye yake, ta shiga banɗaki tai alwala ta fito tai sallar magariba.

Tana kan daddumar da tai salla tana lazimi, taji ana kurma ihu a falo, da hanzari ta miƙe ta fito falon da sauri.

Sedai me tana fitowa ta ci karo da Imran ya shaƙo Minal da hannu ɗaya yai jifa da ita, yana dukan Ihsan kamar jaka.

Da saurin gaske Amira tai kansa, tana faɗin "lafiyarka kuwa? Meye haka kake matarka ce fa da ƙanwarka"

Ba shi da niyyar saurarar Amira, dan tamaula kawai yake da Ihsan, Amira ta nufe shi ta riƙe shi, amma ya hankaɗeta Allah ya temake ta ta faɗa kan kujera akan hannunta, amma duk da haka seda taji ɗan cikinta ya juya.

Seda ya dake su iya yinsa, tun suna ihu har suka kasa gashi Imran ya kulle ƙofar falon.

Kawai ya koma gefe ya zauna akan kujera yana zub da hawaye.

Amira ba tayi fushi ba ta sake jan jikinta, ta ƙarasa in da yake tace "haba dan Allah, meyasa zaka mus wannan dukan haka? Me sukayi maka? Kuma ka zauna kana kuka why? Ka sani a duhu"

Imran kasa Magana yai, ya kuma kallon Ihsan baƙin ciki ya kuma mamaye masa zuciya.

Ya sake tashi a fusace ya dinga takata da ƙafarsa.

Amira ta firgice Sosai, ta koma part ɗinta, ta ɗau waya ta kira Abba yana ɗagawa tace "Abba dan girman Allah idan kana gari ka zo gudanmu, wallahi Imran ze kisan kai, ya sumar da Ihsan yana nema ya kashe Minal, dan Allah ka zo"

Abba gaba ɗaya ya rikice yana ƙoƙarin sake tambayar ta, amma ta kashe wayar, ya miƙe a razane Ammi tace "lafiya kuwa?"

"Ina fa lafiya wai Imran yana can ya sumar da Ihsan, ya shaƙe Minal"

"To me sukai masa?"

"Nima ban sani ba, bari inje gidan inji"

Ammi tace "A'a muje dai tare inji ba'asi, in ka barni ai hankalina baze kwanta ba"

Nan ta ɗakko hijjabinta suka nufi gidan Imran.

Amira na katse kiran ta fito falon da sauri, amma babu alamar sassauci a tare da Imran, dan yanzu Minal yake ta gwarawa a bango.

Sake gigicewa Amira tai, ta kira Anty a waya tana kuka, tace "Anty dan girman Allah idan Daddy yana nan ko wani yazo yaiwa Imran Magana, ze kisan kai wallahi"

"Amira wace irin kisan kai kuma?"

"Wallahi Anty ze kashe su Ihsan na kira Abba haryanzu be zo ba"

Gaba ɗaya hankalin Amira ba a kwance yake ba, dan haka ba tai mata wani Bayani sosai ba, hakan yasa itama Antyn ba shiri ta nufi ɗakin Daddy ta taso shi.

Gaba ɗaya Imran a gigice yake, zuciyarsa wata irin tafasa take ji yake tamkar ya kashe Ihsan ya huta.

Dan Ihsan ko motsin kirki ba ta iyawa, da ƙyar take sauke numfashi, dan tasha duka, Minal kuwa bakinta se fidda jini yake.

Imran ya koma gefe ya zauna ya dafe kansa, jikinsa na wata irin tsuma.

Amira kam komawa gefe tayi ta zuba masa ido, tare da bin su Minal da ido, tana mamakin laifin da sukai masa haka.

Suna nan zaune aka fara buga ƙofar falon, Amira ta kalli ƙofar taga a rufe take, bata san in da ya ajiye mukullin ba.

Yana ji ana bugun ƙofar, amma yai banza se da ya gaji da jin bugun, sannan ya tashi jiki a sanyaye yaje buɗe ƙofar falon, Anty ce da Alhaji Hashim, Anty ta shigo tana faɗin "Imran lafiya kuwa? Meke faruwa ne haka?"

Imran be ce komai ba ya wuce cikin falon ya zauna.

Alhaji Hashim ya kalli inda su Minal ke baje, suna numfarfashi yace "Imran meke faruwa haka a gidanka?"

Imran yai shiru be Magana ba, ana cikin haka sega su Abba sun iso gidan.

Mamaki ne ya kama Ammi ta nufi inda Minal take da sauri tace "Imran meye haka? Me kai musu me sukai maka haka?"

Shiru Imran yai ya zubawa Ammi ido.

"Ba Magana nake maka ba? Me kayi haka? Ina fatan ba akan wannan ballagazar Yarinyar kai musu wannan abun ba?"

Abba yace "Imran, kai magana mana"

Imran ya share Hawaye yace 'bazan Magana ba, se an kira mahaifiyar Ihsan da wan mahaifinta tukuna"

Alhaji Hashim yace "meyasa se an kirasu mu bamu isa ba?"

Anty tace "bamu san meyasa yace haka ba, a kira su kawai"

Haka akayi aka kira Iyayen su Ihsan, sedai lokaci lokaci Imran yana share hawaye.

Gaba ɗaya abun ya ɗaure musu kai.

Ba jimawa se ga Mummyn Ihsan da wan mahaifinta.

Suma abun ya basu mamaki ganin yadda aka hallara haka da yawa a falon.

Mummy tace "lafiya kuwa?"

Anty tace "muma abunda muke son ji kenan yace se kunzo"

Abba ya kalli Imran yace "to muna sauraren ka"

Imran ya ƙurawa Ihsan ido sannan yace "ki gaya musu abunda ki kai min"

Girgiza kai ta shiga yi tace "Imran dan Allah kayi haƙuri ka rufamin Asiri, karka tona min Asiri"

"Ihsan na baki duk wata dama da zan iya, kallonki kawai nake, amma hakan be sa kin fuskanci na san me kike ciki ba, yau an kai point ɗin da ba zan iya jurewa ba, kuma ina tabattar miki daga gurin nan, zaki ƙara gaba ki barmin gida na"

A gigice Ihsan ta shiga girgiza kai tace "dan Allah Imran kayi haƙuri, kar kaimin haka"

A fusace Imran ya kalli Minal yace "ke  se ki gaya musu abunda ku kai"

Girgiza kai Minal tayi tana kuka, amma ta kasa Magana.

Abba yace "to kai ka gaya mana, mana muna jinka kuna tai mana wasa da hankali"

Imran yace "Abba, lesbian na kama Matata da ƙanwata su nayi red-handed, a gadona na Aure bayan ta ƙauracemin sama da watanni, Abba matata da ƙanwata fa"

Tsit kowa yayi, se tashin salati da Sallama da ke tashi a falon.

Amira kuwa gani tai be dace ya musu wannan tonon Asirin haka ba, dan tun kan ya sani ta san Abunda Ihsan take, tun lokacin da suka haɗu a Abuja, ta ganta a Hotel ɗin da ta sauka, tare da wata hamshaƙiyar mace dai tai suna a dandalin sada zumunci, kuma wadda ake raɗeraɗin sana'arta kenan.

Ammi tace "ƙarya kake Imran, wannan sharri ne ban yadda ba"

"Ammi wace riba zan tsinta idan na musu ƙarya? Ga su nan ki tanbaye su mana, Ana zaton WUTA A MAƘERA sega WUTA A MASAƘA, wane irin cin mutuncin ne ba'ayi wa Amira ba ana ce mata Karuwa? Duk da ku Iyaye ne a gurina, amma ranar wanka ba'a ɓoyen cibi, ni na fara sanin Amira mace, ba karuwa bace, yau daga Kano muke gurin duba kakarta, duk rashin lafiyar da Amira tayi ita tai mata Asiri, kuma da bakinta take faɗar Amira ta yafe mata saboda ƙagen da ta dinga mata, Ammi ki tambayesu idan ƙarya nayi musu?"

Ammi tace "Minal da gaske ne abunda yayanki yake faɗa?"

Minal ta jinjina kai cikin kuka, Ammi ta ɗora hannu a ka ta fashe da kuka tana salati.

Anty tace "Alhamdilillah ala kulli halin, tunda Allah ya wanke Amira, kuma ni tun zamanta a gurina na tabattar da ba karuwa bace, wannan shine abun da turawa ke cewa 'Never judge book according to it's cover' sannan Magana ta biyu Imran haƙuri za kayi, ka rufawa matarka da ƙanwarka Asiri, ka cigaba da zama da ita kayi haƙuri"

Imran yace "over my dead body, i already write her divorce, bata ne kawai ban ba, ina tunanin in bata ko in yafe mata, Yarinyar nan ba kalar rashin mutunci da cin fuskar da ba tai min ba, a fari na biye mata ita da mahaifiyata na dinga muzgunawa Amira, daga baya komai ya daidaita, ita kuma ta juyan baya da wulaƙanci da cin mutunci, da fari Ihsan was not virgin, seda ga baya na gane, amma na rufa mata Asiri ban nuna mata ba, secondly na ganta da ɗinki a cikinta nace mata meya sameta, tace min an taɓa mata aikin appendicitis ne, ashe ba haka bane, mahaifa aka cire mata, amma ya Aureni a haka ban sani ba, badan mahaifina ya auramin Amira ba haka zan cigaba da zama da ita ban sani ba, likitan da yai mata aikin was a military doctor, mun haɗu a Lagos muna tare da ita, daga baya ya gayamin shine likitan da yai mata tiyatar nan, se kuma yau na kamata red handed da ƙanwata, Ihsan me nayi miki haka?"

Nana aka shiga kallon kallo, aka rasa wanda ze fara Magana, da kyar Alhaji Hashim yai jarumta yace "Ihsan muna son ji daga gareki, meye gaskiyar abunda Imran ya faɗa?"

Ihsan tana hawaye tace "Imran be ƙarya ba duk abunda ya faɗa hakane, bayan rasuwar mahaifina babu wanda ya damu dani da mahaifiyata, ba wanda yake kula damu, kowa ta kansa yake kawai, ana haka Mummy ta fara bin gidajen Manyan masu kuɗi tana wanke wanke, idan na tashi daga makaranta ina binta gidan aikinta, abunda ake biyanta na albashi be taka kara ya karya ba, baya isarmu buƙatunmu na rayuwa.

Katsam megidan yaje mata da wani batu, yace akwai aikin da aka bashi zeyi, amma da ƙaramar Yarinya ake so kamar ni, lokacin ina da shekaru goma sha biyar, yace ze bata kuɗi naira dubu ɗari biyar, ba tunanin komai ta amince, mutumin nan ya tafi dani, ya dinga amfani da ni ta bayana, da sunan yana neman wata biyan buƙatar da bokaye sukace se yayi hakan.

Nayi kuka nayi kuka akan hakan, amma dana gayawa mahaifiyata sam bata damu ba, hankalinta yana kan abunda mutumin nan yake bata ne kawai, ya canza min makaranta zuwa ta kuɗi, ya sani a Islamiyya me tsada wadda a nan na sauke Alqur'ani na haddace wani sashi, duk lokacin da ya bushi iska ze nemeni ya danƙara mana kuɗi masu yawan gaske, wasu lokutan har Abuja yake tafiya dani.

A haka ana wannan haramtacciyar alaƙar matrsa bata sani ba, ita kuma ta janyo mahaifiyata tana sama mata 'yan aiki ta kaisu gidan ƙawayenta, amma a baɗini less ake dasu, itama matar gidan ta fara bibiyata tana nemana, tana kashemin maƙudan kuɗaɗe, nasan manya manyan matan da take hulɗa da su, ba abunda ban sani ba na sirrinta, gefe guda ga alaƙar dake tsakanina da mijinta, wadda bata sani ba, babu wanda ya isa yace yasan ina wannan harkar saboda a zahiri ina iya yi na inga na tsare mutuncina.

Na tarawa mahaifiyata maƙudan kuɗaɗe, ta wannan ƙazamar hanyar, sedai a wannan harkar da nake, na gamu da larura wani ƙari ya fitomin a mahaifa, a yadda ba yadda za'ai da shi sedai a haɗa da mahaifata a cire, haka a kaimin aikin nan cikin sirri ba wanda ya sani.

Ranar da na fara ɗora idona akan Imran naji duk duniya ba namijin da nake so sama da shi, nai aniyar tuba daga waccan mummunar rayuwa da nake yi, da taimakon Allah da mahaifiyarsa na samu soyayarsa harya Aureni.

Amma a hakan sheɗan ya cigaba da ƙawatamin ƙanwarsa Minal, sedai lokacin da mukaje gidan uwaɗakina da Minal tare, ita ta rigani bayyana nata buƙatar akan Minal, kuma bamu wani sha wahala gurin shawo kan Minal ba.

Tun da Imran yai watsi dani ya fara tatara hankalinsa akan Amira, ni kuma kishi yasa na koma ruwa, na cigaba da saƙa a mugun zare na, ba tare da sanin Asiri na ya daɗe da tonuwa ba, amma dan Allah Imran ka yafemin, ku rufamin Asiri.

Tsit sukai suka kasa Magana, se Ammi da ta fashe da kuka hadda sheshsheƙa.

Imran ya miƙe tsaye ya nufi part ɗin Ihsan, ya dawo da takadda a hannunsa ya jefawa mahaifiyar Ihsan, yace "ki tattar 'yarki ku barmin gida"

Ihsan tace "dan Allah Imran kaimin afuwa, ka rufamin Asiri"

Ammi tace "wallahi baze miki afuwa ba, muguwa Azzaluma kawai, kun cuceni kun ɓatamin 'ya, kun sa na tsaya ya auri Ihsan, ashe abun naku zalunci ne"

Abba yace "Ai shi Allah ba Azzalumin sarki bane, yadda kika takurawa Amira, da tsana da Mugun fata, sega WUTA A MASAƘA, Yarinyar da kika ƙallafa ranki a kai, sega sakamakon ki nan, kisa a ranki wannan alhakin Amira ne, Ubangiji ya nuna miki shi shiriyar 'ya'ya ba a hannun mutum take ba, a hannun Ubangiji take"

Ammi tana kuka tace "tabbas maganar ka haka take, Amira dan Allah ki yafemin, nasan na cutar dake, rashin sani ne dan Allah ki yafemin"

Amira ta share hawaye tace "ni Ammi ba abunda ki kaimin, komai ya wuce"

Alhaji Hashim yace "shiyasa Annabi Sallallahu alaihi Wasallam yace mu faɗi alkairi ko muyi shiru, shiyasa aibata mutum dan yana aikata wani laifi be kamata ka aibata shi ba, seka nemawa al'ummar musulmi shiriya gaba ɗaya, sannan kai ɗan uwan mahaifin Wannan Yarinyar ko kana da ta cewa?"

Yace "A'a me kuwa zance, sedai ince Allah ya kyauta, tunda lokacin da suka ƙulla wannan sharrin ban sani ba, Allah ya kyauta kawai zance"

Ihsan tana kuka, haka mahaifiyarta ta sa ta a gaba suka bar gidan.

Ammi ta tashi zata sake rufe Minal da duka Abba yace "A'a ki ƙyaleta haka, kema magninki ki ɗau yadda ki bawa ƙawa, har in bana gari ki barta taje ta kwana a gidan ta, wake me ƙawa, Allah yasa hakan ya zame miki darasi"

Haka suka tafi gida, Anty kuwa riƙe hannun Amira tai tace "Congratulations my dear, Allah ya wanke ki yau"

Amira murmushin yaƙe kawai tayi, suka tafi gida.

Ranar kusan kwana sukai Amira na rarrashin Imran, dan kuka ya dingayi sosai kamar ƙaramin Yaro, ya rungume Amira yana  "Am sorry my wife, ko yafemin Amira, nayi zaton wuta a maƙera ne, ta shammace ni ta tashi a MASAƘA, ki yafemin Amira"

"Amran, mungama wannan maganar ai, ni ba abunda kai min"

Ammi tayi kuka sosai da sosai, akan abunda Ihsan ta aikata mata na lalata mata 'ya.

Khalid ya taɓa nuna yana son Minal, Ammi ta nuna se tayi karatu me zurfi.

A satin Abba yaiwa Khalid magana, akan in dai haryanzu yana sonta suzo ayi Magana.

Aikuwa Khalid jiki na tsuma ya sanar da iyayensa aka aika gidansu Minal.

Sati guda da zuwan su Amira Kano, Yadikko ta rasu, sedai mutuwar ta girgiza Amira sosai, Imran yace ba inda zata ta'aziyya.

Amira tace "nima bance se naje dole ba, amma na yafewa Yadikko duniya da lahira, Allah ya yafe mana gaba ɗaya"

Imran ya jinjinawa haƙurin Amira da tausyi, Ammi kuwa sosai take son wanke laifukan ta a gurin Amira, dan haka mussaman take zuwa ta rakata awo, tayi mata girki tai ta bata haƙuri tana neman yafiyar ta.

Da Imran ya koma Lagos kuwa, Ammi tace Lallai Amira ta koma gidanta da zama, Anty kuma tace bame ƙwace mata 'ya, da ƙyar a kai sulhu Anty ta ƙyale Amira a gidan Ammi.

Sosai Minal ta dinga jin kunyar Amira, Amira kuma ta nuna mata tamkar ba abunda ya taɓa faruwa, kamar bata san Minal ta aikata wani abun ba.

Da fari Ammi ta dena shiga sabgar Minal gaba ɗaya, amma Amira ta nuna mata illar yin hakan, Minal ta nemi afuwar Amira, Amma Amira tace ta manta da Wannan zancen, ta ɗauka ba wani abu da ya taɓa faruwa.

Watan cikin Amira tara da kwana uku ta fara naƙuda, Ammi ta kaita Asibitin su Anty, aka karɓi haihuwar ta a can, ta haifi kyakykyawar 'yarta mace wadda ta ɗebo kamannin Ammi sosai.

Washegarin haihuwar Imran ya dawo Kaduna, yai murna sosai da haihuwar, yaiwa Jaririyar huɗuba da sunan mahaifiyar Amira Fatima zahra.

Haihuwar tai daidai da lokacin bikin Minal, dan haka aka haɗa bikin da Sunan.

Ihsan kuwa komawa tsohuwar harkarta tayi gaba ɗaya, ta koma gurin wannan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login