Showing 66001 words to 69000 words out of 120332 words

Chapter 23 - WUTA A MASA?A COMPLETE HAUSA NOVEL BY AYSHERCOOL

10 Mar 2025

30356

ba seki min Magana".

Fa'iza tace "dubu ɗari biyu Amira, ina kika samu kuɗi haka?"

"Motar da aka bani a Abuja na saka Sultan ya siyar, ya turan kuɗin account ɗina, kuɗin da suke account ɗina sun kusa million Uku wallahi"

A tsorace Fa'iza tace "million uku Amira?"

"Ƙwarai kuwa, zan turomiki ma da kuɗin kayan sallar yarana"

"Lallai, sannu Attajira, Yayan naki ya sai miki bedsheets guda uku da plasma, yace a baki,  kiyi haƙuri ba shi da kuɗi ne, Sultan ma ya kawo wata ƙatuwar MP da Dinner set, se babban frame da agogo yace in zanzo a kawo miki, ince yana miki fatan Alkhairi, dan ya goge lamabarki daga Wayarsa, tun da kinyi Aure, ni kuma na sai miki turaruka da flask na tea, kiyi haƙuri Amira bani da kuɗi wallahi, amma ban so Aurenki yazo min a haka ba, kiyi mana afuwa"

Kawai Amira ta fashe da kuka, "Amira ya da kuka kuma?"

"Anty Fa'iza, wallahi kukan daɗi nake, ashe haka kuka damu dani? Nagode sosai da kulawarku Allah ya saka da Alkhairi, ki miƙamin saƙon godiya ta ga Yayana, Sultan kuma zan kirashi in masa godiya, nagode Anty Fa'iza"

"Bakomai Amira, ai kanmu mu ka yiwa, idan ba muyi miki ba waza muyiwa? Ki dena kuka Ina jiran ki turomin ɗin, zanje in miki siyayyar insha Allah"

"To shikenan Nagode sosai, Allah ya saka da Alkhairi"

"Ameen seda safe"

Amira kashe wayar, ta ajiye tana murmushin jin daɗi, duk da yadda dangin mahaifinta sukayi watsi da ita, amma a hakan wasu suna ƙoƙarin faranta mata rai.

Washegari da rana Anty tana ta shirin zasu fita, su Ajiye Amira a gurin gyaran gashi, se ga Anty Hadiza tazo Yayar su Imran.

"Khadija kece a gidan sannu da zuwa"

"Yawwa Anty, kice har kun shirya?"

"Eh fita zamuyi yanzu"

"Allah yayi zan sameku kenan, Abba ne ya kirani a waya yace inzo muje tare, ni kuma ban kiraki a waya ba nasan kina zuwa gurin aiki, nace in bari in bari se Bayan sallar Azahar"

Anty tace "Aikuwa Abba ya kyauta da ya turoki muje tare, Bari ki sha lemo ki huta semu tafi"

"A'a ni da nazo a mota, ai ba wani hutu mu tafi kawai"

Amira ta fito cikin doguwar baƙar riga, ta naɗe kanta da mayafin doguwar rigar, ta riƙo ƙaranar jar jaka, sam bata san da zuwan Anty Hadiza ba, Amira na ganinta tai murmushi ta ƙaraso falon tace  "Anty sannu da zuwa"

"Yawwa Amaryarmu, na miki laifi rabonmu dake tun ranar da aka baro gidanmu dake ba wanda ya kuma zuwa, kiyi haƙuri dan Allah"

Amira tace  "bakomai Anty, ya gida"

"Lafiya ƙalau Amarya, kinyi kyau sosai Amira Masha Allah"

Fadila tace 'tana jin kunyarki ne, da haka za tace miki uwargida sarautar Mata dai"

Anty Hadiza tace "Ahh hakane fa, ita ce Uwargidan sarautar Mata kam, masha Allah, Ubangiji Allah yasa ki shiga a sa'a"

Amira tace Ameen.

Anty ta fito suka tafi, a gurin Saloon suka ajiye Amira su kuma suka tafi gurin siyayya.

Ba ƙarya sun yiwa Amira siyayya ta gani ta faɗa, kama daga kan furnitures, kayan Kitchen, electronics ba abunda basu sai mata ba, kaya na gari masu matuƙar kyau, ba su cika mata tarkace da yawa ba, sedai an sai mata kaya masu tsada da kyau.

Furnitures ɗin Amira light and dark purple, kujerun dining ɗin ta da labulaye duk purple ne, daga nan shagon da sukayi siyayya, Anty Hadiza ta kira Imran a waya, ya ɗaga tare da yin sallama, ta amsa sannan tace "Angon biyu ya kana ina ne?"

"Ina gida"

"Lallai ɗan hutu, haryanzu ba'a gama cin agwancin ba, gashi zamu kawo maka wata matar"

"Wace matar?"

"Wace matar kuwa ban da Amira, gamu nan mun gama siyayya zamu shigo jere tare da su Anty Nafisa"

"To sekun zo"

"Yawwa, ka gaida min da Ihsan ɗin kan mu zo"

"To zataji"

Imran yana babban falo, ya tashi ya ɗakko mukulli, ya buɗe ƙofar da ɓangaren Amira da babu komai a ciki, se ƙamshin sabon fenti dake tashi, ya koma ƙofar ɓangaren Ihsan, ya tarar da ita a kwance a kan gado tana chatting, ta kalle shi tace 'hey my D, any problem?"

Ƙarasowa yayi ya zauna a kan gadon da take yace  "Khadija ce ta kirani a waya Yanzu, wai za su shigo su yiwa Amira jeren kaya"

Ras! Gaban Ihsan ya faɗi, take taji duniyar ta mata duhu tana juya mata, tace "wai wace Khadijan?"

"Anty Hadiza na, za suzo da matar Alhaji Hashim suyi jeren".

Ji tayi ƙirjinta yai mata nauyi, tai shiru tasan tunda akayi jere to tariya ma tazo, ta so ace gaba ɗaya dangin mijinta ma na bayanta, amma alamu sun nuna Khadija ma na bayan Amira kenan, tunda take rawar ƙafar zuwa jere.

Imran yace "ya naji kinyi shiru ne?"

"To ni me zance, ince wani abu ranka ya ɓaci, shikenan Allah ya kawo su Lafiya"

"Yawwa my wife, gara ki dinga ɓoye kishinki, dan Allah karki wani abu da zesa su raina min ke kin ji masoyiyata"

Ta jinjinawa Imran kai tana murmushin yaƙe, ƙasan zuciyarta kuwa kamar ta fasa ihu, Imran ya jinjina mata kai, ya sumbaci goshinta ya ta shi ya fita daga gidan.

Yana fita ta Ihsan ta fashe da matsanancin kuka me ratsa zuciya, ta dinga kuka tayi me isarta, sannan ta janyo wayarta ta kira Mummynta.

Mummy na ɗagawa taji kukan Ihsan, a gigice tace  "Ihsan lafiya kuwa? Kukan ne kike yi haka? Wani abun ne ya faru?"

Cikin kuka tace "Mummy, wai yau zasu zo mata jere tarewa za tayi fa Mummy"

"Kai amma kin ɗagamin hankali gaskiya, shine kika zauna kina asarar hawayenki  akan aikin banza, me akayi akai wata banzar karuwa da zaki tashi hankalinki kina wannan kukan kamar uwarki ta mutu? Dalla ki share hawayenki karki bari su zo su raina ki, su zi suyita jeren mana a akanki zata zauna? Ki jirayi zuwanta ki san irin zaman da zakiyi da ita shikenan fa, dalla kiyi maza ki wanke fuskarki karsu zo suga alamar kinyi kuka ma, idan ba haka ba kuwa zaki zubarwa da kanki kima"

"Mummy kin san wani abun takaici kuwa? Wai harda Anty Hadiza za'azo jeren da wulaƙanci, ni na fuskanci kamar ita murna take da wannan tariyar, in ba haka ba neye na zuwa jeren"

"Ke ina ruwanki, ba se taita yi ba, tunda tai uwatta tana bayanki ba shikenan ba, rabu da ita itama za'a san abunyi a kanta zan san yadda za'ayi da ita, ki tashi ki kintsa tunda wuri kinji ko?"

"To Mummy"

'yawwa, maza ki share hawayenki"

Haka Ihsan ta tashi, ta wanke fuskarta ta kintsa jikinta, cikin wani rantsatsten leshi.

Babu jimawa sega su Anty sun ƙaraso gidan, su suna motar gida kayan kuma suna babbar motar kantun da suka je.

Tun daga harabar gidan Anty take yaba tsaruwar gidan, suka shiga katafaren ƙaton falon me ɗauke da manyan kujeru da labulaye, ga dining a gefe, da Kitchen da extra ɗaki a falon se Manyan ƙofofi guda biyu, ɗaya ɓangaren Ihsan ɗaya na Amira.

Suka dinga kwaɗa sallama, amma shiru babu wanda ya amsa, Anty ta tura ƙofar da alamu suka nuna ba komai a gurin, hakan ya tabbatar Mata da nan ne ɓangaren Amira ne.

Da ta shiga nan ma falo ne, da ɗakuna biyu da Kitchen a falo, a cikin Kitchen ɗin da store,  se kuma toilet a kowane ɗaki.

Gidan Imran masha Allah yayi kyau sosai, Anty Hadiza ce ta shiga ɓangaren Ihsan ta tarar da ita tana kallon TV.

"Iyee Ihsan kina nan dama muke ta sallama kika ƙi amsawa, kina jin motsinmu amma ki kayi shiru, yanzu da sata ma muka shigo shikenan Sedai muyi mu fita?"

"To me zance ne?"

"A'a ba'a haka, fito ku gaisa da Anty Nafisa ai be kamata muyi sallama kina ji ki sharemu ba"

Haka Ihsan ta fito tana cunkusa baki, tana Zuwa ta tarar Da Anty Nafisa da Fadila a babban falo, ta ƙare musu kallo sannan ta yastina fuska tace "sannunku"

Anty tace "Yawwa Ihsan, ya kike ya gida?"

Ihsan ta ɗan keɓe baki tace "lafiya"

Ta nemi guri ta zauna a falon, ta kunna kallo ko ta kansu ba ta sake bi ba.

Nan ma'aikatan shagon nan suka shigarwa da su Anty kayan nan, suka taya su jera furnitures ɗin nan, kan wani lokaci tuni shashen Amira ya ɗau kyau, suka jere mata Kitchen ɗin ta, suka gyara komai tsaf.

Suna gidan har bayan sallar isha'i, se wajen tara na dare suka kammala komai, Ihsan ko ruwa bata basu ba, haka ta ƙyalesu su kai aikinsu suka gama, suna shirin tafiya ne se ga Imran ya dawo.

Cikin girmamawa Imran suka gaisa da su Anty, Ihsan ta fito tana ta wani iyayi da rawar kai ita a lallai ga me miji, Anty tace "Imran shigo kaga ɓangaren Uwargidan naka mana, dan in nace Amarya ba ta so tace ita uwargida ce sarautar Mata"

Faɗin haka da Anty tayi, ba ƙaramin baƙantawa Ihsan rai yaiba, Imran ya bisu yaga ɓangaren Amiran, komai yayi normal, Imran yace "gaskiya kaya sunyi kyau masha Allah"

Anty Hadiza tace  "Imran babban falon nan ma Kayan furnitures ɗin Na Ihsan ne?"

Imran yace "No nata suna ɓangaren ta, ni na saka Wannan".

Tace 'nifa ince, ranar da muka zo ai babu furnitures a babban falon, waye ya tayaka zaɓan Kayan nan ne? Sunyi kyau sosai".

"Ammi ce ta zaɓe su".

Anty tace  "ba wannan ba, ya batun kayan lefen 'yata Imran? Ga tariya za'ayi shima yakamata ka biya kuɗin gyara"

"Anty na kashe kuɗi sosai da bikin nan, bani da kuɗi yanzu"

"Amma ka iya siyan furnitures ɗin falo ko?"

Imran ya ɗan sosa ƙeya yana murmushi, "to gaskiya muna binka bashin kayan lefe, a gida na yi mata siyayya amma wannan daban, kaima zaka mata lefenta"

Suka fito falo suna maganar, Imran yace "to Anty, idan Allah ya horemin zanyi Insha Allah"

"Yawwa haka nake son ji, yanzu kawo abunda ya sawwaƙa, za tayi kitso da lalle da gyaran jiki na tariya"

"Anty bani da kuɗi fa, just recently na biya harajin shaguna na kasuwa, kuma kinga yanzu tsakiyar wata ne ba'ayi salary ba empty nake"

"Allah Imran seka kawo abunda ya sawwaka"

Imran yana ji yana gani yace wa Anty, kan Amiran ta tare ze turo kuɗin, Ihsan kamar ta rusa ihu, ji take kamar ta maƙurewa Anty wuya yadda take ta cusowa Imran Amira.

Daga nan ya raka su har mota suka tafi, suna tafe a hanya suna hirar jeren da sukayi wa Amira, Anty tace "gaskiya Khadija, matar Imran ba ta da ta ido, duk da an san abun da aka mata babu daɗi, amma be kamata tai mana irin wannan karɓar ba sam ban ji daɗin hakan ba"

"Mhmm Anty kenan, Allah dai ya kyauta, ni kaina da ta sanni farin sani baki ga yadda tai min ba?"

Fadila tace "ai sauƙinta ita ma Amiran ba kanwar lasa ba ce, amma wannan da sokuwar kishiya zata samu, zata ga wulaƙanci"

Anty tace "hakane kam, sedai duk da haka zan ja wa Amiran kunne a kanta, kuma Khadija da alama dai Amminku ba ta son Amira da  Auren ta da Imran, dan tun ranar Dinner da muka haɗu aka kawo Amira gida na ba ta sake kira na a waya ba"

"Gaskiya ba zan ɓoye miki ba bata so, an taɓa kawo Amira tun tana ƙarama ta riƙeta tace ba zata riƙe ba, duk da ni ba Ammi ce ta riƙeni ba mahaifiyarta ce ta riƙeni, amma Ammi ba ta son dangin Abba suje sam, kuma Yanzu da aka aurawa Imran Amira, ba ayi shawara da ita ba, kuma gashi ana ta cewa Amira karuwace, shine duk dalilin da ya sa ba ta son Auren"

Anty tai ajiyar zuciya tace "Ai shikenan, ni Allah ya bani 'ya ina so, iya zama na da ita ban ga wani abu da zesa in tabattar da Amira Karuwa ba ce, ke hatta wayarta na karɓa chats ɗimta da komai, ba abunda ban duba ba, ina doubting ace Yarinyar nan karuwa ce, na dai yadda ba ta ji tana da rawar kai, amma gaskiya ban tabattar da maganar karuwanci ba"

Hadiza tace "to Allah ne dai masanin gaibu"

Suka cigaba da hira, suka kai Hadiza gida suka sauke ta, sannan suka tafi.

Bayan tafiyar su Anty, Ihsan tace  "wai da gaske tura musu kuɗin nan za kayi?"

"To idan ban tura musu ba ya kike so inyi?, Ko so kike ta gayawa Abba yazo yana fushi da ni?"

"To in hakane nima se ka bani, wannan shine adalci"

"Ihsan a gabanki fa na ce bani da kuɗi, bani da kuɗi wallahi, kuɗin kenan zan ɗauka in basu, saboda kar a samu matsala, kuma naga ke lokacin bikinmu ma baki, kiyi haƙuri mana"

"Yanzu matsayina ɗaya da ita kenan? Dan ka bani lokacin bikina, shine yanzu ba zaka bani ba,ita ka bata"

Shareta Imran yai, yai mata shiru yaƙi kulata.

Da su Anty suka koma gida, Amira harta koma tuni, wannan karon ma, kan nan ya sha kitso ko tsaga baka gani, saboda yadda sukai ƙanana sosai, ga yawa an mata ƙari sosai.

Washegari Imran ya tura musu dubu hamsin, ya lallaɓa Ihsan ya bata dubu Ashirin dan a zauna lafiya, ba tare da tasan nawa ya turawa su Amira ba.

Tuni Amira ta turawa Anty Fa'iza abunda take so ta sai nata da kuɗi, tai mata siyayya ta sako a mota zuwa Kaduna, Amira ta gayawa Anty, aka aika direba ya je ya karɓo mata kayan daga tasha.

Amira taji daɗin abubuwan da suka sai mata taita murna tana jin daɗi.

Har gida me lalle taje ta zanawa Amraya Amira, Amira tai shar da ita se sheƙi take kamar ba ita ba, ga wani sassanyan ƙamshi dake tashi daga jikinta duk inda ta ratsa, tun ana gobe zata tare jikinta yai sanyi sosai, Alhaji Hashim baya gari, amma ya kira a waya yai mata fatan Alkhairi, tare da yi mata nasihohi masu ratsa jiki kamar 'ya da uba, Amira ba zata taɓa mantawa da kara da mutuncin da Alhaji Hashim da Anty Nafisa sukayi mata ba, ba dangin iya bana Baba, amma sun mata kara da nuna mata soyayya.

Ana gobe Amiran zata tare, Anty Nafisa ta kirata ɗakinta, ta zaunar da ita, ta kalle ta tace "Amira, yanzu lokaci yayi da zaki shiga sabuwar Rayuwar Aure, wadda ta sha bamban da irin wadda ki kayi a waje, kin san da yadda akayi Auren nan naki, fatana a gareki shine, kiyi haƙuri, kiyi haƙuri, kiyi haƙuri, duk matar da kika gani a gidan Aure haƙuri take, kuma ita ma haƙuri ake da ita, dole kiyi haƙuri Amira, nasan zaki fuskanci ƙalubale a gidan Imran, amma nasan komai ze wuce nan ba da daɗewa ba insha Allah, in dai hasashen da nake a kanki ya zama gaskiya, komai ze wuce amma sekinyi haƙuri, kishiyarki Ihsan ba sa'arki bace, ta girmeki dan haka banda mata rashin kunya, ko neman Magana, bance ki yadda a wulaƙanta ki ba, amma ban da neman rigima, ki yiwa mijinki biyayya, ki san da irin lafazin da zaki dinga masa Magana, kiyi duk yadda zakiyi ki ja hankalinki kansa, karki ce baya sonki ki zuba musu ido, Flight for your right, you are such a beautiful lady Amira, kuma kina da kirki, duk wannan cika bakin da yake ze dena ne, na yadda da 'yata bana shakkar ta kara da kowace mace a gurin miji, Allah ya bada sa'a ya albarkaci rayuwarki  am gonna Miss you dear"

Anty tai maganar tana gogewa Amira hawayen dake zubowa kan fuskarta, Amira ta rungume Anty tana kuka tace "Nagode, Nagode Anty Allah ya saka miki da mafificin Alkhairi, Ubangiji Allah ya biyaki ladan kula da marainiya, kina cikin sahun mutanen da suka fuskance ni, suka fuskanci abun da na ke so, zama na dake kin kula dani, kamar 'yar da kika haifa, ba kyara ba hantara, ba ki taɓa kallona da laifin da akace ina aikatawa kin ƙyamace ni ba, at least nima naji wani abu na daga daɗi da farinciki da masu iyaye a raye suke ji'

Jiki a sanyaye Anty ta shiga sharewa Amira hawaye tace  "Amira karki sani kuka mana, nima marainiya ce, i knows what you go through, i know the feelings, shiyasa ni duk in da ɗa yake nawa ne, saboda nasan da ɗa da dukiya ba'a mugunta a kansu, se in moreki fiye da yadda zan mori 'ya'yan dana haifa, dan haka karki damu, You Are my daughter, tashi muje in rakaki ki kwanta, dan ki tashi gobe in Allah ya kaimu da wuri, dan na ɗan gayyaci mutane, za'azo ayi ƙwarya ƙwaryar walima kan a kaiki"

Haka Anty ta raka Amira ɗakinta, har da rufeta da bargo ta kshe mata fitilar ɗakinta tare da rufe mata ƙofa.

Amira ta lumshe idonta Hawaye na zubowa tace  "Allah ka jiƙan iyayena, ka sakawa da Anty da gidan Aljanna, ka kareta ka tsare mata zuriyarta ita da mijinta"

Washegari da safe 'ya'yan Anty, suka iso gidan suma, Anty ta na da yara mata 'yan biyu, ɗaya lawyer ce ɗaya likita, suna Auren wasu manyan attajirai suma 'yan biyu, Anty ta gayyaci mutane abokan aikinta da maƙota, cewar za tayi walimar tariyar 'yarta.

Sun san halin Anty da kwashe kwashen yaran mutane, ta riƙe 'ys'yan 'yan uwa da dama, ba ruwanta ita duk in da ɗa yake nata ne, shiyasa ba wanda ya damu da in da ta samo Amira.

Yadda halin Anty yake na kirki haka 'ys'yanta suke, dan su sa kai wa Amira kwalliya ma, suka dinga hotuna, Anty Hadiza ma a gidan ta wuni ita da yaranta, gaba ɗaya jikin Amira a sanyaye yake, da magariba Anty ta sa Amira tai wanka, aka saka mata kaya sannan aka naɗa mata lafaya, fuskarta ba make up amma tayi kyau sosai.

Zuwa sallar isha'i, suka tafi raka Amira, tana ta kuka, hadda Anty aka tafi raka Amira, se tashin ƙamshin turare take.

Duk da Amira kuka take, amma ta yaba da tsaruwar gidan, mussaman yadda aka kashe mata kuɗi a ɓangaren nata, kayan ta duk 'yan waje ne komai yayi kyau.

Akwai wasu da cikin 'yan uwan Ihsan a gidan, sun zo su tayata zama da sa ido, saboda kawo Amira, se wani harare harare suke, suna yada baƙaƙen maganganu, yadda suka zaci Amira ba haka su ka ganta ba, duk da tana cikin lafaya, amma hakan be hana idanunsu ganin kyan diri da Allah ya bata ba.

Wanda suka rako Amarya na ta yaba kyan ɗakin Amiran..

Imran ya koma gida, Anty ta fito da Amira babban falo, ga Imran a zaune ga Ihsan, tace "Imran ga Amanar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login