Showing 33001 words to 36000 words out of 120332 words
Chapter 12 - WUTA A MASA?A COMPLETE HAUSA NOVEL BY AYSHERCOOL
yai shiru bece komai ba, se tagumi da yayi da hannunsa bibiyu.
"Wai ba magana nake maka ba ka shareni? Ka wani yi uban tagumi kamar ance Ihsan ta mutu"
Imran ya sauke hannayensa yai ajiyar zuciya, tare da sake dafe kansa.
"Wai zaka tashi mu tafi ne kokuwa?"
"Kaga a fasa fitar nan kawai"
"Saboda me, wai kai meke damunka ne, ka wani nustu kamar marayan muzuru, ka tashi mu tafi malam lokaci yana ƙurewa"
"Kaga a fasa fitar nan kawai"
Khalid ya kalleshi da mamaki yace "Kamar ya a fasa? Ban gane ba"
Imran yace "Khalid ina cikin damuwa ne, bazan iya fitar ba".
"Damuwar me, kai da zakayi aure, ai damuwa semu gawauraye"
"Khalid mata biyu wai zan aura lokaci ɗaya"
"Kamar yaya?" Khalid ya tambaya cike da rashin fahimta.
Nan Imran ya warwarewaa Khalid komai.
Khalid yace "lallaai kana cikin tsaka me wuya mutumina, amma Allah yasa haka shine mafi Alkhairi, insha Allah zakaga sakamakon biyayya, kayi haƙuri Imran, inaji a jikina zaka samu Alkhairi a sanadin Aurenta"
Imran kawai ya tashi ya tafi ɗakinsa yaje ya kwanta, dan yama rasa abunda zeyi gaba ɗaya.
Alhaji Hashim kuwa tuni yayiwa matarsa bayani akan Amira, kuma ta bashi tabbacin ita a kawo mata Amira zata riƙe, dan gaba ɗaya yarinyar tausayi ta bata da Alhaji Hashim yayi mata bayani.
Kasancewar mahaifin Ihsan ya rasu, Alhaji Ali da waliyan Imran, a ranar sukaje suka samu wan mahaifinta akan mata biyu za'a aurawa Imran a gurin ɗaurin Aure, Ihsan da kuma 'yar uwassa, shima wan mahaifin nata be nuna fushi ko ɓacin ransa ba, sedai yace musu "komai muƙaddari ne, kuma bawa baya wuce ƙaddararsa, Allah ya basu zaman lafiya ya haɗa kansu, amma kun san halin mata, se Addu'a, dan haka karku sanar musu da zancen, ni zan sanar musu idan lokacin da yakamata yayi, idan aka gaya musu yanzu ba zasu bari ayi bikin lafiya ba"
Abba yace"Allah ya wuce mana gaba, mungode sosai da wannan karamcin naka, Allah ya albarkaci yaranmu gaba ɗaya"
Imran kam bacci ma gagararsa yayi, yana kallon Ihsan tana kiransa amma ya kasa ɗaga wayar, saboda zatonsa An sanar mata ai ita da Amira ze aura.
Amira kam ta dena shiga sabgar mutanen gidan, duk wulaƙancin da sukayi mata, amma suna ta shirye shiryen zasu bikin ɗan uwanta Kaduna, Amira kallonsu kawai takeyi, 'yan gidansu akwai son abun duniya fiye da kima, basa iya ɓoye zalamarsu sam.
Amira Ta fito tsakar gida, Sadiya nata wanke wanke, ta baje kwanuka gashi ta zubar da dagwalon ƙanzo da komai, Yadikko tazo wucewa Amira ta kauce ta bata hanya, kawai ta taka ruwan omo, santsi ya kwasheta ta faɗi ƙasa, cikin kwanuka da dagwalon wanke wanke, ta buge ƙeya da tukunyar ƙarfe.
Take ta kurma uban ihu, ta dafe kanta wai Amira ta hankaɗeta, ko takanta Amira bata biba, tai gaba abunta.
Baba ya fito ya dinga yiwa Amira tijara, yana faɗin ya gaji da wannan tashin hankalin, baza'a kashe masa uwa a banza ba, Amira seta bar musu gida.
Ko kallaonsa ba tayi ba, ta ɗauki gyalenta da jakarta ta fice ta bar musu gidan.
Da safe Imran yana kwance, yana ta tunani ranar ne za'a fara bikinsa, Amarya za tayi henna day amma baya cikin nutsuwarsa, still Ihsan tana ta kiransa amma yaƙi ɗagawa ƙarshe ma ya kashe wayarsa gaba ɗaya, dan be san meze ce mata ba.
TV dake bedroom ɗinsa na tayi ita kaɗai, can aka nuno mawaƙin nan da Amira tayi hotuna dashi a Abuja, wai ze kai ƙarar Amira kotu, sunyi yarjejeniya zata fito a waƙoƙinsa, amma tai tafiyarta bema san inda ta shiga ba, dan haka 'yan sanda suna nemanta, duk inda take.
Imran ya tashi zaune, ya dafe kansa yama rasa me Yakamata yayi.
Wai wannan itace wadda ake son ya aura, wannan watsatsiyar Yarinyar.
Ya ɗakko wayarsa ya kira Baba a waya, Baba ya ɗaga lokacin yana tsaka da banbami akan Amira.
Imran yace "Ina Amira take?"
"Ai lamarin wannan yarinyar banma san me zance ba, kwana biyun nan masifa kawai take janyo mana, ta saka ƙafa ta fice ta tafi gantalinta, shekaranjiya tayiwa Yadikko zagin cin mutunci, dan an mata magana ta ɗakko wuƙa kamar wata 'yar daba, yau kuma ta hankaɗa Yadikko cikin tukwane ta kusa suma saboda yadda ta bugu a kanta, gaskiya na gaji ba.....
Imran da maganganun Baba ke sake kunnashi yace "kaga ba kira nayi ka wassafamin wannan takicin ba, duk inda take ku nemota, koku turomin lambarta inyi tracking ɗinta, zan shigo Kano anjima, idan ba haka ba ta gangamo wata rigimar, wadda ba iya kanta zata tsaya ba harku zata shafa, dan haka duk inda zaku samo labarta ku nemo ku turomin, zanyi tracking in nemota, tun kafin abun data janyo ya zama out of control"
Imran ya katse wayar yai jifa da ita akan gadonsa ya furta "Oh My God, Allah ka dubeni wai wannan ce zata zama matata, wannan yarinyar yasalam, am Sorry My Ihsan, baki cancanci haka daga gareni ba, amma dole inje in ɗakko Yarinyar nan kan 'yan sanda su kamata, abun kunyar zemin yawa, ace matar da Imran ze aura a hannun 'yan sanda, Sunan Abba ze ɓaci nima mutuncina ya zube"
Ya ɗau wayarsa ya kira Khalid, Khalid ya ɗaga, Imran yace "Khalid ka shirya zaka rakani Kano yanzu Please!"
(Oga Imran za'aje a ɗakko mana amarya 😂😂😂)
Share, Share, And share as much as you can please, masu nema daga farko yana nan a watpad a account ɗina
Ayshercool 7724
Ayi vote, ai following please
Masu san what's app group kuma ga link nan, mata kawai banda maza Please, Sannan akwai dokoki a group ɗin, in kina ɗaya daga groups ɗina karki joining please
https://chat.whatsapp.com/EAYHhAEJQPk8uGg2IeCQhX
07063065680.
[1/15, 6:38 PM] Ayshercool: 🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥
WUTA A MASAƘA
PERFECT WRITERS ASSOCIATION
(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS)
https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
P. W. A
*Story and written by*
AISHA ADAM (AYSHERCOOL)
The experience writer of
*ABDUL JALAL*
* WATA KISSAR.... (SAI MATA)
*BAƘIN TABO (Labarin gasa)
*AƘIDATA (Paid Book)
* WUTA A MASAƘA
https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=in
❌❌❌
Ƙirƙirarren labari ne, ban yadda ayi amfani da kowane sashi na labarin ba ba tare da izinina ba.
KAMAR YADDA NA FAƊA TUNDA FARI, BA LALLAI IN DINGA SAMUN YIN POSTING KULLUM BA, IDAN AN GA BAN POSTING BA AMIN HAƘURI
17_18
Imran ya kalleta a fusace yace "nan yai miki kama da gidan karuwai ne?" Murguɗa masa baki tayi ta ɗauke kai.
Khalid yace "Amira gidansu Imran ne fa, ki shiga bakomai, baki ga 'yan biki suna shiga suna fita ba"
Ta ƙarewa gidan kallo, sannan ta kalli Imran tace "muje"
Idan Imran ya biyewa Amira, ze iya yi mata dukan tsiya a gurin nan, kawai ya wuce yai gaba, Amira tabi bayansa.
Mata nata tsokanarsa suna ango ka sha ƙanshi.
Cikin gidan suka shiga, ya wuce Falo Amira na biye da shi.
Minal suna zazzaune a falo da ƙawayenta, da babbar Yayarsu Khadija wadda daga Ita se Imran, ita tayi Aure tuntuni.
Khadija ce ta fara ganin Imran da Amira, ta kallesu tai murmushi tace "Imran kai da wa nake ganinka haka kamar Amira?"
Amira dai tayi turus, tana kallon Anty Hadiza.
Jin ance Amira yasa Minal waigowa, duk yadda ake faɗar rashin jin Amira da yadda ta ganta a hoto, ba ta zaci zata ganta a haka a fili ba, tafi kyau da class Sosai a fili.
Imran yace "eh ita ce"
Hadiza tace "masha Allah, Nikam yaushe rabon da inga Amira tun tana ƙarama sosai, yanzu waze ce ita ce, ta zama hamshaƙiyar mace"
Wata a ƙawayen Minal tace "wannan ba ita ce wani mawaƙi yace zata fito a vidon waƙarsa ba?".
Minal ta kwaɓe baki tace "ita ce"
"Wow Gaskiya naji daɗi dana ganta, ashe 'yar uwakku ce, wallahi ni burgeni tayi"
Cikin isa Imran yace "ke minal, ki bar abun da kike kije ki kaita ɗakinki, ki nuna mata toilet tayi salla, Sannan ki bata babban hijjabi"
Amira kuwa kamewa tayi a gefe, tana binsu da kallo ɗaya bayan ɗaya.
Minal ta zumɓura baki, cikin ƙunƙuni tace "ɗakina, toilet ɗina, kuma kayana, taɓɗijan Allah ya kiyaye inyi sharing da wata"
Cikin muryarsa me razanarwa wasu lokutan yai mata tsawa "dan ubanki me kike cewa? Ni nake miki Magana kike min ƙunƙuni?"
A hargitse Minal tace "A'a Yaya, dan Allah kayi haƙuri, wallahi ba da kai nake ba"
"Kai Sarkin masifa, tun daga ciki ake jiyo hargowarka, lafiya kake wa 'yata shouting haka?" Ammi ce ke maganar lokacin da ta fito daga wani ɗaki.
Ba tsammani ta kalli inda Amira take, sukai ido huɗu da juna, ko za'a naɗe ƙasa a dawo, Amira ba zata manta fuskar Ammi ba, da wasu abubuwa da suka shuɗe shekarun da suka gabata ba.
A wulaƙance ta ƙarewa Amira kallo ta kalli Imran tace "lafiya wannan fa?"
"Abba ne yace inje in taho da ita yau, a fara biki da ita"
"Saboda bikin nata ne, kokuma na ƙanwar uwatta?"
Amira ta ɗago ta kalli Ammi, ta maida kanta ta sunkunyar.
Anty Hadiza tace "Ammi, Amira ce fa ko baki ganeta bane?"
"Ke zam cewa baki ganeta ba, baki da labarin rashin jin da yawon ta zubar ɗin da takeyi, babu inda hotonunata da rashin kunyarta basu shiga ba, kawai se a ɗebo jiki a kawomin ita cikin gida, saboda me to baze yuwu ba, ba a gidan nan ba sedai wani gurin"
Hadiza tace "Haba Ammi, koma menene dalili ne ya kawota, kuma na ɗan lokacine, ana gama biki fa zata tafi"
Gaba ɗaya hankalin mutane ya dawo kansu, aka dinga bawa Ammi rashin gaskiya da nuna mata illar abunda tayi, jin mutane nata surutu ba yadda ta iya, haka ta ƙyale Amira, saboda gudun surutan mutane.
Imran ya kuma kallon Minal yace "bakiji me nace bane?"
Miƙewa Minal tayi, Imran ya kalli Amira yace "ki bita kije ta baki masauki, a baki hijjabi ki rife jikinki"
Duk da sanyi da jikin Amira yayi, hakan be hanata zumɓura baki ba, dan da ta san gidansu Imran ze kawota, da duk tunballen tsiyar da za'ayi sedai ayi ba zata yadda taje gidansu ba.
Minal tai gaba Amira tabi bayanta, suna shiga ɗakin Minal ta juyo ta gallawa Amira harara tace "ga toilet nan ki shiga, kuma ki kula karki sake kimin taɓe taɓen abunda ba shikenan ba, kuma karki min fitsari a ƙasa, kinji na gaya miki"
Amira ba tace uffan ba, dan ta san kome akayi mata Imran ne ya janyo da ya kawota gidan, dan da tana gidansu babu me mata wannan rashin mutunci haka.
A masallaci Imran ya sake haɗuwa da Khalid, suka wuce gidansu Khalid, a hanya Imran ya bashi labarin irin karɓar da Ammi tayiwa Amira.
Khalid yace "ai nasam za'ai haka, ni babbar fargabata ma suzo su san wannan maganar, akwai fa sauran rikici"
Imran yace "bari kawai, aini na zubawa sarautar Allah ido kawai, dan ban san abunyi ba"
"Ka kwantar da hankalinka, Allah ze baka mafita insha Allah"
Seda suka raba dare suna hira, Sannan Imran ya tafi gida, lokacin duk an rurrufe ko ina, kuma be haɗu da Abba ba sam balle ya gayamasa ya ɗakko Amira, dan haka kai tsaye ɗakinsa ya wuce yaje ya kwanta.
Amira kam duk a takure take, ba wanda ya kulata balle ya bata Abinci, ga gajiyar hanya data ɗebo, gashi bata san ko ina ba, Minal da ƙawayenta se wulaƙanci sukewa Amira, Minal tana gaya musu ai Amira karuwace, se wannan guda ɗayar ta farko da tace Amira tana burgeta itace bata biye musu ba.
Da daddare akazo gurin kwanciya, Minal ta kalli Amira tace "kinga, me aiki zata shigo yanzu ta kai ki inda zaki kwana, nan ɗakin zamu kwana ne nida ƙawayena, bama son takura ina fatan kin gane?"
Amira ba tace komai ba, ga kaya tana son canzawa, bata ɗakko komai nata ba, kawai Imran ya kawota ya ajiye yai tafiyarsa, taji kamar ta haɗiyi zuciya ta mutu dan takaici.
Me aikin ta shigo ɗakin ta kalli minal tace "Anty gani"
"Yawwa, dama zaki wanke min banɗakina ne bana son sharing da jagwalgwalo, kin sanni da ƙyama, kuma an shiga banɗakin But before that, ki kaita inda na gayamiki za ta kwana"
Me aikin ta kalli Amira tace "taho in rakaki"
Ba musu Amira tabi bayan me aikin nan, sedai inda me aikin ta kaita ne ya bata mamaki, abun ya ɗaure mata kai, da faɗi da girman gidan nan, a rasa inda za'a kaita se Kitchen, kitchen ɗinma a cikin store, duk ga kayan Abinci a jibge kamar abun banza, an saka mata tsurara katifa wai ta kwana a gurin.
Amira ta ƙarewa gurin kallo, ta ja tsaki ta fice ta koma falo ta bar me aikin a gurin, ta samu guri a gefen kujaerun falon ta zauna.
Mutane kowa ya samu gurin kwama amma Banda Amira.
Haka ta kwana a falon nan a zaune, ga garin da sanyi ga baƙunta, da Asuba can waje ta fita tai alwala, tana ƙarewa gidan kallo da yadda zata bar gidan nan, ko Imran ya sani kobe sani ba, ta ƙudirce gari na yin haske zata gudu, ta koma Kano.
Yadikko kam ta bugu sosai, dan se an rirriƙeta take iya tashi, amma sam bakinta yaƙi mutuwa, banda zagi da kwashewa Amira albarka ba abunda takeyi, wai itace tai silar faɗuwarta ƙasa.
Umma da su Sadiya suna ta haɗa kaya, zasuje biki ita kuwa tana kwance, duk jiki yayi tsami.
"Wai yanzu niba yadda zakuyi dani, a lallaɓa a tafi dani gurin bikin nan?"
Zailani yace "ina za'a kaiki, ki zame musu kaya? Ya zasuyi dake? Jinyarki za suje suyi kokuma bikin zasu? Kawai ki haƙura ki zauna, a yaran gidan Baffa Salahu ko su Habiba ne suzo su dinga tayaki zama, kafin su dawo Amma wallahi kikace zaki bisu ma wahala zaki sha"
Haka sukayi ta fama da Yadikko, akan lallai se an tafi da ita gurin biki, seda taga ba sarki se Allah ta haƙura da zuwan.
Washegari da Safe suka gama shiri tsaf, suna jiran Fa'iza taje su haɗu a nan gidan su tafi gaba ɗaya.
Amira kuwa gari na fara hasake, wajen ƙarfe takwas na Safe tana tunanin idan ta fita ina zatayi, Anty Hadiza ta fito daga ɗakin Ammi tace "Amira, ya baƙunta?"
Amira ta kalleta tace "lafiya ƙalau, ina kwana?"
"Lafiya ƙalau Amira, naga kina ɗari ɗari ki saki jikinki fa, nan gidanku ne, ki saki jiki da kowa duk 'yan uwanki ne"
"Gidansu a gidan ubanwa? Gidana dai gidan mijina, gidansu yana Kano, kuma 'yan uwan 'yan uwana ne, ta nemi nata 'yan uwan ba nawa ba, mu babu kalarta a 'yan uwana"
Amira tai shiru ta sake sunkunyar da kai, zuciyarta na tafasa, Hadiza tace "Ammi why?"
"Ke dalla rufemin baki ko in zageki yanzun nan"
Suna barin falon Amira ta miƙe daga inda take zaune, dama jakarta na jikinta, ta zira takalmanta tai waje.
Mutane nata shiga suna fita, Amma tana zuwa bakin gate, ɗaya daga masu gadin ya taso ya kalleta yace "ina zaki?"
"Fita zanyi" Amira ta bashi amsa.
"Zuwa ina?" Ya tambayeta.
"Kamar yaya? Su sauran wanda suke fitan tambayarsu kake yi?, Kokuma ni ka raina, dan Allah ka bani guri in fita"
"Gidan ubanwa zaki idan kika fita?" T muryar Imran taji ba tsammani, waiwayowa tayi da sauri ta ganshi a tsaye, sanye da jallabiya fara.
Haɗe rai tayi sosai tace "Ni gida zan tafi, gidanmu zan koma"
"Hmm tunda dama ke kika kawo kanki ko? Kin ɗauka haka nan na kawo ki nan ɗin kina da damar da zaki fitane? Da kin matsa kin fita da se sun harbe ƙafarki da bindiga, sakarya kawai wuce muje ciki ni"
Ai kawai Amira ta sa masa kuka, harda hawaye tace "gaskiya ni ba zan koma ba, haka kawai ni ban san kowa ba ka kawoni ka ajiye ni, se wani kallo na ake ana gayamin magana, ni gaskiya gidanmu zan koma, duk da bamu da komai Amma ni ya fiyemin nan"
Imran ya ƙare mata kallo sannan yace "waye yake gaya miki maganar? Koda yake koma me akayi miki aike kika janyo, ubanwa yace kiyi abinda za'a gaya miki maganar, wuce muje ba gidan uban da zaki, in kinga kin fita daga gidan nan to ni ko Abba ne wani ya fita dake, amma daga nan har ƙarshen layin nan, kika fita zasu dawo dake, wuce mu koma"
"Dan Allah kayi haƙuri, ni wallahi bazan iya zama a gidan nan ba, ka ƙyaleni in koma"
Attention ɗin mutane ya fara dawowa kansu, wata mata tace "Imran yau fa ranar farinciki ce a gareka, banda cin zali dan Allah, nam ba barikin soja bane"
Imran kawai yai murmushi, matar na wucewa ya bugawa Amira wata irin tsawa, me matuƙar razanarwa, a gigice ta nufin cikin gidan da sauri, ya riƙo hannunta, yabi ta bayan gidan da ita zuwa sashin Abba.
Minal kuwa da akan idonta, Amira ke kuka, Imran ya riƙe hannunta se cewa tayi "Ahha baɗala, kar dai Yaya Imran ake gwadawa karuwancin, aikuwa bari inje in gayawa Ammi"
Sashin Abba suka shiga, Amira tana kuka amma tana ƙarewa gurin kallo, dan ita bara taɓa shiga gida me kyan wannan ba a rayuwarta.
Abba yana ganinsu yace "oyoyo 'yar gidan Abba"
Jin muryar Abban ce yasa ta dawo hayyacinta daga kalle kallen da takeyi.
Taje ta samu guri ta zauna, Imran ma ya zauna, Abba yace "ki hau kan kujerar mana" girgiza kai Amira tayi ta sunkunyar da kanta ƙasa.
Abba yace "ai ni be gayamin ɗakko ki ya tafi yi ba, ai da tun daren jiya mun gaisa, se yanzu da safen nan fa ya gayamin" jikin Abba ne ya ɗanyi sanyi, ganin hawaye a idon Amiran.
Abba yace "lafiya kuwa Amira? Imran ko kayi mata wani abun ne?"
Imran yace "Niba abunda na mata"
Amira ta ɗago ta harari Imran, Abba yace "gayamin me yai miki?"
"Ni kawai yake ya ɗakkoni, ban shirya ba ban komai ba, ban taho da komai nawa ba, daga ni se kayan jikina,yazo ya ajiyeni ya tafi, tun a hanya nace ina jin yunwa Amma ya ƙyaleni yazo ya ajiyeni ya tafi, kuma banci Abinci ba, kuma ni dan Allah kace ya maida ni gida, ko tasha a kaini in hau mota in koma, ni bana son zama a nan gidan" tai maganar cikin kuka.
Abba yace "yi haƙuri ya isa haka, besan baki ci Abinci ba, amma ga nawa cna kije ki zuba kici, za'a kawo miki kayan