Showing 69001 words to 72000 words out of 120332 words

Chapter 24 - WUTA A MASA?A COMPLETE HAUSA NOVEL BY AYSHERCOOL

10 Mar 2025

30368

Mahaifinka nan, kamar yadda yake faɗa, ya bani riƙonta na wani ɗan lokaci, gashi na kawo maka ita na damƙa maka, ina me naka Nasiha da kaji tsoron Allah, sannan kayi adalci a tsakanin iyalinka, Ihsan matarka ce, Amira ma haka, dan Allah ka manta da wasu batutuwa da suka faru a baya, ka fuskanci iyalinka ka riƙe su da amana, Ihsan ga Amira nan, ƙanwar bayanki ce kin girmeta, dan haka hankalinku ba ze taɓa zuwa ɗaya ba, dan Allah kiyi haƙuri da ita, ku zauna kamar 'yan uwa ba kishiyoyi ba"

Kwaɓe baki Ihsan tayi ta juya ƙeya tare da faɗin taɓ, se da Imran ya kalleta.

Wata ƙanwar maman Ihsan tace "A'a fa baiwar Allah, ba wani kamar 'yan uwa ita fa kishiya duk in da take kishiya ce, waye ze wani riƙi kishiya 'yar uwa ta kassara ka, kowa dai tai zaman kanta"

Imran yace "ya haka ana musu nasiha ki na zigasu?"

Anty ba ta nuna ta damu ba ta ɗora da cewa "Amira, Ihsan yayarki ce, duk da kina da'awar kece Uwargida amma ta girmeki kuma ta rigaki shiga gidan mijinku, dan haka dan Allah ku zauna lafiya ban da rigima, kiyi wa mijinku biyayya ki girmama kishiyar ki, kin ji 'yar Anty?"

Amira ta jinjina kai tace "Insha Allah"

Anty tace "to Imran, ka na da abun faɗa ne?"

"A'a ba ni da wani abun cewa, kin gama komai ai, ni dai fatana su zauna lafiya, mussaman 'yarki dan kin san halinta, ban da ɗaukar magana, kamar yadda ki ka gayamata, Ihsan gaba ta ke da ita, dan haka dole ta girmamata"

Aikuwa Amira ta ɗago suka haɗa ido, ta gallawa Imran harara, harda fari da ido da murguɗa baki"

Imran ya ɗan girgiza kai, Anty tai musu Addu'oin zaman lafiya, suka maida Amira ɗakinta.

Anty tace "zamu tafi, ga miyarki da nai miki, da kayan snacks duk suna Kitchen ɗinki, idan garin Allah ya waye, ki ɗibarwa abokiyar zamanki nata, Allah ya baku zaman lafiya, aita haƙuri Amira, shi Aure ɗan haƙuri"

Amira ta jinjina kai tana share hawaye, ita kanta Anty seda tai ƙwalla, saboda a ɗan zamanta da Amira sunyi sabo me ƙarfin gaske, saboda Amira akwai shiga rai sosai.

Bayan tafiyarsu dama Amira ba ta tsammaci ganin Imran ba, dan haka ta miƙe taje ta zazzaga part ɗinta komai yai kyau, ta je rufe ƙofar part ɗinta ta leƙo babban falo, ta ga su Imran su ma sun rufe ƙofa, girgiza kai tayi, ta rufe ƙofar ta koma ɗaya da ga bedrooms ɗin ta, wanda aka shiryamata kayanta a ciki, ta canA kaya ta nemi Guri ta kwanta.
Ɗaya bedroom ɗin, gadon ƙarfe ne a ciki da mudubi se abun rataye jakun kuna.

Sam Amira ta kasa bacci, se tunane tuane da take, ɓangare guda tana murna, wai duk wannan kayan nata ne, ita ma yanzu matar Aure ce, ɓangare ɗaya kuma ta na jin takaicin an kawo ta gidan Aure, amma ko kalli ba ta ishi mijin nata ba, da ƙyar ta samu bacci ya ɗauke ta.

Ɓangaren Imran ma, Yau se da yai zaman rarrashin Ihsan, dan koke koke taita yi masa, yai ta rarrashinta yana kwantar mata da hankali.

Kiraye kirayen sallar Asuba ne ya farkar da Amira daga baccin da take, tai sallar Asuba da addu'oin Azkar, ta koma ta sake kwanciya,  wajen ƙarfe tara ta tashi, tai wanka ta shirya cikin riga da skirt, ta fito babban falon, wata magazine Amira ta gani akan Centre table, da gani ta Imran ce dan duk abubuwan sojoji ne a jiki.

Tana nan zaune tana kallon magazine ɗin, aka buɗe ƙofar part ɗin Ihsan, Ihsan ce ta fito sanye da rigar bacci iya gwiwarta, kanta babu ko ɗan kwali, ta saki baƙin gashinta da alama ba ta daɗe da tashi ba, tana Ganin Amira a falo ta ja tsaki, Amira tai murmushi tace "Yayata ina kwana?"

"Kinga malama, ki riƙe gaisuwarki ina ruwanki da ni ne?".

"Haba Ihsan, gaisuwar ma ba wani abu ba"?

"Eh gaisuwar, bana son salon bariki kin gane ko? Kiyi rayuwarki in yi tawa"

Amira tace "A'a, ni baza ai haka da ni ba, ya za'ai mu zauna gida ɗaya ba gaisawa, any way nace Ya tashi ne?"

Ihsan da ke ƙoƙarin nufar dining ta tsaya cak, ta waigo ta kalli Amira tace "karki wannan gangancin, Ina ruwanki da tashin sa ko rashin tashin sa, yarinya ta ki kama kanki tun wuri, ba ki da miji a gidan nan"

Kawai Amira tai dariya tace "ƙarfin hali, aron ɗan kunnen sirika, ai shikenan zamu gani"

Amira ta sake maida hankali kan magazine ɗin da ke gabanta.

Ihsan ta dinga shiga part ɗinta tana fito da kayan Abinci, ta jere akan dining, ta kuma komawa part ɗinta, se gasu sun fito tare da Imran, ya rungumota a jikinsa, suna dariya Amira ko ɗaga kai ba tayi ba balle ta kallesu, duk da yadda taji ƙirjinta na harbawa da sauri.

Sukaje har kan dining, Imran ya ja kujera ya zauna, Ihsan tace "kayi breakfast lafiya, bari inje inyi wanka kan ka kammala"

Imran yace "Waze bani Abincin in kika tafi?"

"Haba My, yanzu zan dawo fa, kai kayi wankan ka, You know i suppose to bath, bazan daɗe ba"

Imran yace "shikenan, kiyi sauri amma zan fita"

Ihsan tace "Ok Darling" tai maganar tare da kissing ɗin Imran ta juya suka haɗa ido da Amira, ta gallawa Amira harara sannan ta wuce part ɗin ta, Amira tabi Ihsan da kallo, a cikin rigar bacci kamar balbela, Ihsan na shigewa Amira ta miƙe ta nufi dining ɗin.


*_ASSALAMU ALAIKUM WARAHMATULLAH, INA KUKE MASOYA AYSHERCOOL, MASOYA LITATTAFAN TA, KAMAR SU WATA KISSAR SAI MATA, WUTA A MASAƘA, ABDULJALAL,AƘIDATA, DA DAI SAURAN SU TO GA SANARWA TA MUSSAMAN, INA ME FARINCIKIN YI MUKU ALBISHIR DA FARA SAKIN SABON LITTAFINA NA RUƊIN ƘURUCIYA, LABARI ME TARIN FAƊAKARWA DA ILIMANTARWA GAMI DA NISHAƊANTARWA, KUMA BULALIYA GA IYAYE, RUƊIN ƘURUCIYA ZE TAƁO ABUBUWA DABAN DABAN GAME DA RAYUWAR MATASAN YARA WANDA SUKE KAN ADOLECSEN PERIOD, IRIN HATSARIN DA WANNAN SHEKARUN SUKE DA SHI, DAMA SAURAN ABUBUWA NA ILIMANTARWA DA KUMA NISHAƊANTARWA, ZAKU IYA MORE KARANTA WANNAN LITTAFIN AKAN KUƊI NAIRA ƊARI UKU KACAL, LITTAFIN ZE FARA ZUWAR MUKU BIYAR GA WATAN FEBUARY DA YARDAR ALLAH, ZAKU IYA TURA KUƊINKU TA 0009450228, AISHA ADAM, JA'IZ BANK, KU TURA SHEDAR BIYA TA 07073065680, DOMIN NEMAN ƘARIN BAYANI ZAKU IYA TUNTUƁAR WANNAN LAMBAR 07063065680*_


[1/31, 2:02 PM] Ayshercool: 🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥

WUTA A MASAƘA

PERFECT WRITERS ASSOCIATION

(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS)

https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P. W. A

*Story and written by*
AISHA ADAM (AYSHERCOOL)

The experience writer of

*ABDUL JALAL*
* WATA KISSAR.... (SAI MATA)
*BAƘIN TABO (Labarin gasa)
*AƘIDATA (Paid Book)
* WUTA A MASAƘA

https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=in

❌❌❌
Ƙirƙirarren labari ne, ban yadda ayi amfani da kowane sashi na labarin ba ba tare da izinina ba.


*_ASSALAMU ALAIKUM WARAHMATULLAH, INA KUKE MASOYA AYSHERCOOL, MASOYA LITATTAFAN TA, KAMAR SU WATA KISSAR SAI MATA, WUTA A MASAƘA, ABDULJALAL,AƘIDATA, DA DAI SAURAN SU TO GA SANARWA TA MUSSAMAN, INA ME FARINCIKIN YI MUKU ALBISHIR DA FARA SAKIN SABON LITTAFINA NA RUƊIN ƘURUCIYA, LABARI ME TARIN FAƊAKARWA DA ILIMANTARWA GAMI DA NISHAƊANTARWA, KUMA BULALIYA GA IYAYE, RUƊIN ƘURUCIYA ZE TAƁO ABUBUWA DABAN DABAN GAME DA RAYUWAR MATASAN YARA WANDA SUKE KAN ADOLECSEN PERIOD, IRIN HATSARIN DA WANNAN SHEKARUN SUKE DA SHI, DAMA SAURAN ABUBUWA NA ILIMANTARWA DA KUMA NISHAƊANTARWA, ZAKU IYA MORE KARANTA WANNAN LITTAFIN AKAN KUƊI NAIRA ƊARI UKU KACAL, LITTAFIN ZE FARA ZUWAR MUKU BIYAR GA WATAN FEBUARY DA YARDAR ALLAH, ZAKU IYA TURA KUƊINKU TA 0009450228, AISHA ADAM, JA'IZ BANK, KU TURA SHEDAR BIYA TA 07073065680, DOMIN NEMAN ƘARIN BAYANI ZAKU IYA TUNTUƁAR WANNAN LAMBAR 07063065680*_






                               33_34

Kan Amira ta ƙarasa Imran ya haɗa tea yana shirin fara cin Abinci, Amira ba fagabar komai ta ƙarasa ta nemi Guri ta zauna a kan kujerara da ke facing ɗin Imran, ta ɗan ƙura masa ido.
Ɗagowa yayi ya kalleta, tai murmushi tace "Ina kwana"

"Lafiya" ya bata amsa a taƙaice ya fara cin Abincin sa.

"Ka kwana lafiya?"

"Da ban kwana ba za ki ganni a nan?"

"No Allah ya huci zuciyarka"

Ta ɗauki spoon dake kan plate, tai Bismillah ita ma ta fara cin dankali da miyar ƙwan da ke gabansa.

Ya kalleta yace "meye haka?".

Ta ɗan tura baki tace "Yunwa nake ji, tun ɗazu na tashi amma baku fito ba, kuma Kitchen ɗina bakomai se snacks ɗin da nazo da su, kuma ni abu me ɗumi nake so"

Tai maganar tare da janyo kofin gaban Imran, ta kai bakinta ta na shan tea ɗin.

Saboda gudun rigimar Ihsan, ya sa Imran miƙewa ya barwa Amira kayan breakfast ɗin, ya koma sashin Ihsan.

Yaje ya tarar da ita ta shirya ta na ƙoƙarin fitowa, ta kalleshi tace "ya dai My d, are you done?"

'yes dear"

"Anya ka ƙoshi kuwa? Ko dai rashina a kusa da kai yasa ba ka ci da yawa ba"

Yai murmushi yace "No, na ci sosai na ƙoshi ne"

"To shikenan na yadda, amma muje ni ka bani inci".

"Ok amma base mun koma falon ba, inda saura a Kitchen ɗakko in baki a nan"

"Meyasa?" Ta tambayeshi tana kallonsa.

"Saboda tana falon, ni kuma bana son rigima"

"Amma meye haka se kace ana tsoronta, shikenan saboda zuwanta se in dena walwala da sakewa a gidana?"

"Ihsan, bana son duk wani dalili da ze ɗagamin hankali, ƙarewa Abincin nawa ma ita na barwa take ci, na ƙyaleta bana son abunda ze disturbing peace ɗina, kiyi haƙuri"

Kamar Ihsan za tayi kuka tace "Yanzu in dafa maka Abinci dan cin fuska ka bata ta cinye"

"No Baby, ni na isa inci fuskarki saboda ita, ina cikin mood na soyayya ne, ba na son ta ɓata mana shiri, ko tai sanadiyyar da zamu samu rashin jituwa, muje Kitchen ɗin in dafa miki wani abun da kaina in baki"

Ihsan ba ta son ya hasala, dan shi idan yai rarrashi ɗaya biyu baya na uku, tsaf ze ɓata rai ya fita harkarta, dan haka ta haƙura ta haɗa sauran Abincin suka koma falonta suka ci.

Wajen ƙarfe sha ɗaya da rabi, Suna falon Ihsan suna shan soyaya, aka ƙwanƙwasa ƙofar falon.

Imran yace "shigo"

Amira ce ta shigo, da kwanukan da tai breakfast ta wanke su tsaf, se wasu manyan plate da ta zuba snacks ta saka poil paper tai wrapping ɗin su.

Ihsan na jikin Imran yana wasa da gashin kanta, amma ganin Amira ya sa ta miƙe zaune, tana bankawa Amira uwar harara.

Amira kam murmushi ta saki ta ƙaraso inda suke, tace  "Ihsan ga kwanukan ki, na wanke miki nagode Sosai, ta ajiye kwanukan a gaban su, sannan ta ɗau plate ɗaya ta ajiyewa Imran, tace
"Captain ga naka, Ihsan kema ga naki"

Ihsan tace "Me zanyi da wannan abun? Dalla ɗauke ki fita da shi ko mun ce miki muna jin yunwa ne?"

Amira tace "Haba Ihsan, meye na wani Maganar kalar yunwa a nan, ai kyauta ce ba wani abu ba fa"

"Eh na faɗa mu ba kalar yunwa bane, ba ma so ɗau abunki ki ƙara gaba, idan ma wani abun ki ka sa a ciki dan ki mallake shi to wallahi kinyi ƙarya, munfi ƙarfinki wallahi, sedai ki kalleshi daga nesa, dan ba kalarki bane"

Amira tai murmushi tace  "naji shi mijin namu ba kalar yunwa bane, amma kefa, dan Allah idan ana Maganar yunwa ko makamancin yunwa, ki dena saka baki, dan ba ki da maraba da kalar yunwar"

"Amira!"

Imran ya kira sunanta da ƙarfi, "Matar tawa kike gayawa haka?"

"Bakaji ni me tace min bane, har tana wani Maganar zan zuba wani abu in mallake ka, ai idan har zanbi malamai dan mallakar miji ban kai karuwa ba, mu zuba mu gani ni da ke, na ɗaga miki ƙafa ne saboda be kamata daga zuwana ace mun fara samun saɓani ba, amma am ready for you"

Amira ta miƙe ta tafi, Imran ya dafe kai yace "Ihsan why? Na gaya miki duk yadda zaki kija girmanki kar yarinyar nan ta rainaki, amma kin kasa hakan, da ta kawo abu kika san ba kya so se ki karɓa ki bayar, amma abun da kike ze sa ta rainki, ni kuma bana son hakan, kuma ba zan iya haushi ba yau ba gobe ba, saboda gidana ba ba gurin aiki bane, ko filin daga da zan ta ɗaga maƙogwarona ba, shiyasa tun farko nake fargabar zama da mata biyu matsalolinku ba sa ƙarewa"

Ya miƙe ze fita saboda ransa ya gama ɓaci, Amma Ihsan ta riƙeshi ta marairaice fuska tace "am sorry dear, ba zan sake ba insha Allah"

Da ƙyar ta lallaɓashi ya haƙura, dan Imran akwai zuciya.

Amira kam tun da ta koma ɗaki, ranta yake a ɓace, bata sake fitowa ba har magariba, saboda yadda zuciyarta ke ƙuna, tun Abincin safen nan bata sake cin komai ba.

Bayan ta idar da sallalr magariba ne, sega kiran Anty ya shigo wayarta, cikin murna ta ɗaga tace "Antyna"

"Na'am, Amira na ya kike?"

"Lafiya ƙalau Amarya, au uwargida ya kike ya Gidan, ina fatan ba wata matsala?"

"Ba matsalar komai Anty, ya Anty Fadila"

"Tana lafiya ƙalau, ya mijin naki?"

"Yana lafiya, ya fita sallar magariba ma"

"To masha Allah, duk ki gaishe su, aita haƙuri kinji Amirana?"

"To Antyna, nagode sosai"

"Yawwa, seda Safe ki gaishe min da Imran ɗin".

"Zeji insha Allah"

"Allah yasa wata tara cif in zo in ɗau jikana"

Amira cikin jin kunya tace "kai Anty"

Ta katse wayar tana murmushi, ta kalli wayar tai shiru, be kamata ta gayawa Anty yadda Imran yaƙi saurararta ba, kawai ta ajiye wayar tana ajiyar zuciya.

Tana nan kan dadduna, har akayi sallar isha'i, bayan tayi salla ta idar ta tashi tai wanka, ta shirya a doguwar rigar baccinta ta kwanta, harta fara bacci amma yunwa ta tashe ta, taji cikinta ya ƙulle.

Duk kayan soye soyen nan basa kanta, saboda taci tun a gida, maiƙonsu ya isheta.

Miƙewa tayi ta fito babban falo, taga Imran a zaune da matarsa suna kallo, a yanayin da ta gansu ba ƙaramin ɓata mata rai yai ba, suna kallo ta buɗe ƙofar ta fito, amma basu fasa abunda suke ba, da sauri ta juya ta koma, aikuwa a falon ta ta zube ta fashe da kuka, taji wani irin baƙinciki ya dinga taso mata, tana ayyana abubuwa daban daban a ranta, a ƙa'ida ita ke da miji, amma ta sharesu ta ƙyalesu, amma shine dan wulaƙanci ganin idonta ma be sa sun bar abunda suke ba.

Haka ta ja jikinta ta koma ɗakinta, ga yunwa ga kishi yana cinta, da ƙyar bacci ya ɗauketa.

Da safe duk da bata son cin kayan snacks ɗin nan, haka ta tura su a haka ta karya.

Ya zamana duk lokacin da Amira zata falo, in dai zata haɗu da Imran da Ihsan, se Ihsan tayi wani abu da ze ɓatawa Amiran rai, dan seta ga Amira seta fara tsirar rungume Imran, tana shagwaɓa.

Amira kam setai kamar bata gani ba, sedai ƙasan zuciyarta Kamar ta fasa ihu haka take ji, dan wani lokacin seta koma ɗaki take ɓuya tayi kuka, bata taɓa zaton zafin kishi ya kai haka ba se yanzu da take ɗanɗana"

Amira Babu wanda ta gayawa halin da take ciki, a haka a daddafe har tai sati guda, gashi suna waya da Abba, yana ce mata ya kusa zuwa gari zezo ya gansu, amma bata taɓa gayamasa ga abunda ke faruwa ba, ta lura Imran yana matuƙar son Ihsan, dan haka ya kan kaucewa abunda ze ɓata mata rai.

A haka a daddafe, Amira tai sati guda a gidan Imran, tana ƙoƙarin kaucewa fitowa lokacin da duk tasan zata haɗu da su Imran a falo.

Yauma Amira tana kwance tana baccin safe, kasancewar yau weekends, ta duba agogo ƙarfe sha ɗaya, miƙewa tai ta fito tana tunanin Imran ya fita, dan haka da rigar baccinta a jikinta ta fito, sedai tana fitowa taga Imran yana nan yana falo be fita ba, kallo ma yakeyi shi da Ihsan.

Imran ya ɗaga ido ya kalleta daga sama har ƙasa, ya saki ajiyar zuciya ya ɗauke kansa.

"Ina kwananku?" Ta gaishesu.

Imran ya kalleta ya jinjina kai, yayin da Ihsan ko motsawa ba tayi ba, balle ta kalli inda Amira take ba, seda Amira ta nufi dining, sannan Ihsan taga shigar dake jikin Amiran, ai ba shiri Ihsan ta miƙe zaune, ta kalli Imran amma taga ba Amira yake kallo ba, hankalin sa yana kan TV.

Amira taje ta bubbuɗe kwanukan dake kan dining, ta samu sun rage Abincin ta kama ci.

"Ke kika ajiyemin da zakije ki taɓa min kaya ba izinina?".

Kunnen uwarshegu Amira tai da Ihsan, ta cigaba da cin Abincin ta.

Imran ya kalli Ihsan ya girgiza mata kai alamar tai shiru.

Imran satar kallon Amira yake ba tare da Ihsan ta sani ba, Amira ta kammala cin Abincin ta, maimakon da ta gama ta koma ɗakinta, se ta tashi ta koma kujerar da ke facing ɗin Imran, ta zauna tana kaɗa ƙafa tana danna wayarta.

Imran ya kasa dena kallonta, saboda kusan sashi mafiya yawa na rigar Net ce, gashi ta baje kitson attachment ɗinta, ta haɗe rai kamar ba ita ba.

Tana ɗaga ido sukai ido huɗu da Imran, hararasa Amira tai ta kashingiɗa a jikin kujearar ta lumshe idonta.

Takaici ne ya kama Imran, ganin ta kama shi yana kallonta har da hararsa, Cike da salon tura takaici, ya fara kissing ɗin Ihsan.

Duk yadda Amira ta so ta daure kasawa tai, se ga hawaye na bin fuskar Amira, Ihsan ta bawa Amira baya dan haka bata ganin Amira, Imran ke facing ɗinta Imran yaiwa Amira murmushin mugunta, ganin tana kuka.

Nan da nan tai sauri ta goge hawayen, dan kar ma Ihsan ta gani ta rainata, duk taɓarar da suke  a gabanta ta maze, ta cigaba da dannan wayarta, sedai ƙirjinta har wani nauyi yake mata saboda azabar kishi, Imran ya riga ya fara gano Amira ma na da tsananin kishi.

Seda suka tashi suka bar falon sannan Amira ta bawa hawayenta damar zubowa sosai, tafi jin haushin Ihsan fiye da yadda take jin na Imran, jiki a sanyaye ta tashi ta tafi ɓangaren ta itama.

Amira ta tsiri se suna falo, za tai shigar matsatsun ƙananun kaya ta fito, ta fito musu a Karuwarta da suke faɗa.

Da safe Amira ta sanya wani ƙaramin wando da wata 'yar ƙaramar riga,ta fito tana ta gyara babban falo tana goge TV, se ga Ihsan ta fito, ita kanta da tai arba da Amira seda gabanta ya faɗi, ta kalli Amira tace "ke meye

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login