Showing 63001 words to 66000 words out of 120332 words

Chapter 22 - WUTA A MASA?A COMPLETE HAUSA NOVEL BY AYSHERCOOL

10 Mar 2025

30346

Ihsan cin abincin, duk da kuwa ta saba da gidan sosai, amma haka nan ta dinga jin nauyin cin abincin.

Ammi ta shiga ɗaki yin sallar isha'i, Imran ya kalli Minal yace "ba mu guri zan bawa mata ta Abinci"

Minal miƙewa tai tana ɓoye dariya a ranta tace "Lallai ka ga masoya"

Tana tafiya ya janyo Ihsan jikinsa yace "kin wani ƙi cin abinci, Gara tun wuri ki saki jiki kici Abincin nan, oyo open Your mouth"

Haka Ihsan ta lafe a jikinsa yana bata Abinci, tana amshewa, Ammi ce ta fito daga ɗaki Da hanzari Ihsan ta bar jikin Imran cike da kunya, Ammi tai murmushi tace "Ihsan kenan"

Imran kam basarwa yayi kamar ba wani abu da ya faru, Ihsan kam kamar ƙasa ta tsage ta shige dan Kunya.

Ammi ta zauna sannan tace "Imran naji daɗin yadda na fuskanci kuna zaman lafiya, nasan lallai a wannan dawowar ta ku Mahaifinka ze ce se waccan Yarinyar ta tare, to ina son in sake ma ka jan kunne ne, kar ka sake zuwan Yarinyar nan ya zama barazana ko silar rushewar farincikin da nake gani a Tare da ku, kasan irin zaman da za kuyi, ba kai ba shiga sabgar yarinyar nan, kuma na ga a tsaye take idanunta ba bu alamar mutunci, kar ka kuksakura ka bada ƙofar da za ta saka Ta raina maka mata, tsakanin ka da ita ido, tun da ubanka ya dage ka Aureta ka Aireta ga gida nan taje ta zauna, ni ba zan lamunci in haɗa zuriyata da Karuwa ba, ka kula kuyi hankali da ita.

Ke kuma Ihsan, karki kuskura ki biye mata, dan ba cikakken hankali ne da ita ba, zata iya yi miki illa idan kika ce zaki biye mata, ba ruwanki da ita, ki bi mijinki ku zauna lafiya duk yadda zanyi zanyi inga Auren nan beje ko ina ba, goyon bayan ku kawai nake buƙata nan kusa zan mitstsike Auren nan"

Da ƙarfi ƙirjin Imran ya buga, kawai se ya saki Amira, da wani idon ze kalli Abba idan ya sake ta?

Ammi tace "Naga kayi shiru, ko ka nada Magana ne?"

"A'a kawai ina zancen zuci ne, ba damuwa Ammi insha Allah zan kiyaye abunda kika faɗa"

"Yawwa Allah yayi muku Albarka, ina ƙara gaya muku baku ba yarinyar nan ko shiga shirginta, kuyi rayuwarku daban tayi tata"

Haka Ammi taita jaddada musu, suka tashi tafiya ta kawo kyautuaka ta bawa Ihsan.

Ko da suka koma gida Ihsan ta riga Imran yin gaba, Abba ya kira wayar Imran, Imran ya ɗaga suka gaisa da Abba.
Abba yace "Imran naji kun koma ko?"

"Eh Abba yau kwananmu uku da dawowa"

"Yawwa to dama bugowa nayi in roƙi alfarma, dan nasan idan ban nema ba baza'ayi min ba, ina so aje a duba 'uar marainiyata, kaji ko da abunda suke buƙata saboda tariyarta"

"To Abba insha Allah, kuma dama nayi niyyar gobe in Allah ya kaimu zanje gidan Antyn insha Allah"

"Yawwa yaron Kirki, haka nake son ji, ba danni ba kuma ba dan Amira ko halinta ba, a daure a taimaka a kulamin da marainiyar nan dan Allah Imran, ka ta ya ni wanke laifin da na aikata a baya, ka riƙe Yarinyar nan da mutunci, ka manta da irin nata laifukan ita ma dan Allah"

Gaba ɗaya jikin Imran yayi sanyi yace "Insha Allah Abba, zanyi ƙoƙarin kula da ita"

"Yawwa Imran Allah yayi maka albarka"

"Ameen Abba nagode".

Shiru Imran yai yana jujjuya maganganun Ammi da na Abba, ƙarshe dai ya wuce cikin gidan shima.

Da safe Amira ta kira Anty Fa'iza video Call, tana nuna mata ɗakin da take rayuwa a gidan Anty, suna ta hira suna dariya, sega Anty tayi sallama, Amira tayi sallama da Fa'iza tace "Anty ina kwana?"

"Bazan amsa ba bayan baki fito mun gaisa ba har gashi zan fita aiki"

"Yi haƙuri Anty"

"To na haƙura, sarkin bada haƙuri, daɗina dake kenan, in ance kinyi laifi ba jayayya se bada haƙuri, ina ga yau mijinki ze zo, nayi magana da Abbanki, sedai ban san lokacin da ze zo ba, sonake ku shiga Kitchen keda Fadila ku yi masa Abinci, in case ze zo ina gurin aiki so nake ki kashe kala ki ɗau wanka dan Allah, ban da tura masa baki banda rashin kunya, kiyi Kwalliya ki shafa turarukan ki, yadda seya kasa tafiya"

Aikuwa zumɓura bakin Amira tayi tace "Anty ban da kunya kenan?"

"A'a kina da kunya mana, Amma shi kina masa rashin kunya wasu lokutan shiyasa bakwa jituwa, ki tashi ku shiga Kitchen tare kiyi masa abinci"

"Taɓ shine ze ci Abincin da na girka, ni da ba sona yake ba, Anty kawa ki bari in yazo a bashi Ruwa da lemo"

"Musu zaki dani kenan?"

"A'a waceni musu da ke Anty, an gama bari in wanka inje inyi abunda kika ce"

"Yawwa Amirana, shiyasa nake sonki ai, akwai biyayya, irin wannan biyayyar indai ita za'ayiwa Imran, ba yadda zeyi yace baya son 'yata, son kowa ƙin wanda ya rasa"

"Anya Anty Imran ze soni? Jikina na bani zan sha wahala a gidansa, Ihsan yake so"

"A'a Amira, meye na wani karaya, kina mace ta na mace, Imran ɗin me, I beg ki shirya karɓarsa, very soon zaki tare insha Allah, weekend zamuje ganin gidan nan da 2weeks insha Allah zaki tare a ɗakinki"

Murmushi kawai Amira tayi tace  "A dawo lafiya Anty"

"Yawwa 'yar Anty, Allah yasa"

Bayan fitar Anty Amira ta fito, ta karya suka shiga Kitchen tare da Fadila, snacks ne sukayi se fruit salat suka saka a fridge, da ga nan kuka Amira ta ɗora girkin rana.

Sedai har Antyn ta dawo Imran be zo ba, Anty tace "Amira Imran ɗin ya zo kuwa?"

"A'a Anty be zo ba, ina ga fa baze zo ba tun da la'asar tayi"

"No Babansa ne yacemin zezo, insha Allah ze zo, idan kuwa be zo ba a wannan karon to tabbas sena gayawa Babanku"

Ita dai Amira ba tace komai ba, ta koma ɗakinta ta ɗakko rani tayi wa Yatsunta ado da jan rani.

Ta fito daga ɗakinta zata buɗe ƙofar da zata shigar da ita falon taji muryar Imran, komawa tayi ciki ta sake shafa turaruka, sannan ta fito saye da riga da skirt na Atamfa, ta ɗora ɗankwalin kawai a kanta bata ɗaura ba ta fito, tai pretending kamar ba ta san da zuwansa ba.

Anty tace  "'yar halak, ai gata nan ma ina shirin a kiraki, gashi yazo"

Waiwaya yayi inda Amira ke tsaye, ya ga tayi wani ƙalau da ita, duk da dare ne amma haka be hanashi ganin kyan da ta ƙarayi ba tayi ƙiba abunta, kayan jikinta tamkar a jikinta aka ɗinka su, sun zauna cif a jikina ta bada wani shape me ɗaukar hankali, tahowa tayi cikin falon fuskarta ba walwala ta kalleshi tace "Sannu da zuwa"

Shiru yayi be amsa mata ba, Aikuwa haushi ya kamata ta nemi guri kusada Anty tai zamanta tana kallo.

Imran da Anty suka cigaba da hirar lokacin da zataje taga gidan, aje ayiwa Amira jeren kayanta.

Anty tace "tashi ki kai masa Abincin ɗakin varrender"

Amira ba tace Komai ba ta miƙe ta tafi Kitchen, ta na shiga Kitchen ta fara haɗa tray sega Fadila ta shigo da hoda da turare a hannun ta tace  "malama tsaya ki sake kintsa fuskarki, ni ya ganki fes ya fiye min Wannan Abincin da kika girka masa"

"Wai meyasa ku ka damu da shi hakane?"

"Wai muka damu da shi, muka damu da ke dai ba shi ba"

Ta shafawa Amira powder, ta sake fesheta da turare, dama bakinta akwai jambaki Tun rana da ta saka, aka gyara ɗaurin ɗan kwalin nan, se Amira ta ƙara kyau, kamar wata matar hamshaƙin attajiri.

Ta haɗo tray da kayan Abinci ta fito, sedai daga Antyn har Imran ba kowa a falon, Fadila tace "kai masa ɗakin, nasan yana can, banda tsiwa dan Allah"

Amira ta kwaɓe baki irin taji ɗin nan amma ba lallai ba, ta shiga ɗakin da Imran yake, yana zaune yana daddana wayarsa, ya ɗago ya kalleta ya basar, ta zo ta ajiye masa tray ɗin akan Centre table, ta janyo table ɗin gabansa, sannan ta zauna a kujerar kusa da tasa.

Sun kai mintuna goma, ba wanda ya kula Wani, Can Imran da turarenta ya hana shi sukuni yai ta maza yace  "baki iya gaisuwa ba ko?"

"To ba na maka magana ɗazu ka ƙi kulani ba, shiyasa naga kar yanzun ma in gaishe ka kaƙi kulani" tayi maganar a ɗan shagwaɓe.

Imran yace "dakyau"

"To ai dai ba laifi nayi ba, amma ina wuni"

Kamar yadda tai tasammanni shirun yai mata, ya kuma maida hankalinsa kan wayarsa.

Ƙasa tayi da murya tace  "ba zaka kulani ba ko?"

Nan ma be amsa mata ba.

Wayarsa ce ta fara ringing taga an rubuta Lovely.

Ko ba'a gaya mata ba tasan Ihsan ce, aikuwa ran Amira ya ɓaci ya ɗaga wayar yasa a kunnensa yace  "Hello My Wife"

Kan ya kuma cewa wani abu Amira ta fizge wayar da ga kunnensa tana huci, ta katse kiran.

A fusace ya kalleta yace "ke meye haka? Rashin hankalin zaki min kenan?"

"Eh rashin hankalin zan maka, ai naga nima matarka ce, ka ɗauketa kun tafi lagos kuyi wata biyu ina nan ko ta kaina baka bi, kuma kun dawo ka zo tun ɗazu nake maka magana amma ka shareni, ita tana kiran wayarka shine ka ɗaga"

"Zaki bani wayata ko sena tattaka ki a gurin nan?"

Jiki a sanyaye ta bashi wayar, ya kalleta yace  "karki taɓa tunanin haɗa kanki da Ihsan, Ihsan mata tace kuma mace me kima da na aura dan ina sonta, ke kuwa fa umarnin Abba yasa na Aureki dan haka karki kuskura ki sake haɗa kanki da mata ta dan ba sa'arki bace, ba kuma matsayin ku ɗaya a zuciya ta ba"

Abunka dame Arhar hawaye, tuni ta lumshe idonta, wasu hawaye masu ɗumi suka biyo kyakykyawar fuskarta, ta ɗago fararen idanunta, tana masa wani irin duba tai murmushi tare da taune gefen leɓenta ta kamo hannun Imran ɗaya cikin nata tace 

"Dan Allah da me Ihsan tafi ni?, Me nayi naka kake min Wannan ƙiyayar hakane?duk fitinar fa da ka ga ina yi nima ina da msu sona, ban rasa masoya ba, Amma meyasa kake son yi min wulaƙanci ne?"

Zare hannunsa yai daga nata, sakamakon wani abu da yaji ya ziyarci zuciyar sa ba shiri, ya kalleta yace "Ihsan nutsatstiya ce kamila, ke kuma....

"Ni kuma Karuwa ce ballagaza ko?" Tai saurin ƙarasa masa maganar.

"Nasan abunda zaka faɗa kenan, amma ita Rahama ta Allah ce, se kaga ya shiryeni ya yafe min" ta ƙarasa maganar tana share hawaye, ta share hawayenta tsaf sannan tace "mijinmu me zan zuba maka a cikin Abincin ka ci"

"Bana ci, ki kwashe kayanki"

Amira ta watsa masa wani kallo tace "Yadda ka gani, da kaci da karka kaci wannan matsalar ka ce, tunda ba abunda yai saura zan iya tafiya?"

"Ni kike gayawa haka?"

"Ai ba wani abun nace ba, kawai cewa nai zan iya tafiya?"

"Tsaya mu fita tare, bana son tamabayoyin Anty"

Amira tai gaba, Imran yana binta a baya, sedai ya ƙurawa bayanta ido, yadda take tafiyar kamar tana sane, ta fito Falo.

Anty tace "Ba dai har zaka tafi ba Imran?"

"Eh Anty tafiya zanyi"

Amira tace  "Anty kinga yaƙi cin Abincin ko, dama seda na gaya miki kika sa na wuni ina faman yi masa girki amma ya ƙi ci"

"Haba Imran, tun Safe take aikin karɓarka amma ka ƙi cin Abincin, jeki ɗakko ki kawo masa nan, ba a haka Imran, wata nawa bakwa tare duk da tana matarka ai seka ci, ba'a gwasale mace kaji ko"

Lallai Amira ta iya tsiya, yanzu tace kar Allah yasa yaci, amma ta fito ta haɗa shi da Anty.

Haka ta ɗakko Abincin ta dawo da shi Falo, seda yaci tukuna saboda yana kunyar Anty sosai.

Se kusan tara na dare sannan ya tashi ze tafi, su kai sallama Amira ta tafi raka shi, sedai kan ya ƙarasa inda motar take ta rigashi ƙarasawa, ta jingina a inda zesa mukulli ya buɗe ƙofar ta kalle shi tace  "dan Allah, idan na tare a gidanka ka zama me min adalci, nafi kowa sauƙin kai, sedai ban yadda in cutar da kowa ba nima kar a cuceni, idan har zakayi adalci a tsakaninmu kuma matarka ta kiyayi gayan magana mara daɗi ka sai zaman lafiya a gidanka, nafi kowa farinciki da son zaman lafiya, saɓanin haka kuwa, za'aga ba dai-dai ba, sannan ka gayawa Ihsan da ni take zancen, naji tana cewa anmin alfarma an Aureni, ni wannan be dameni ba, amma zata gane ta bi mijina lagos sunyi wata biyu nikuma an shanyani a nan, zaku biya laifin da ku kaimin"

Mamaki ne ma ya kama Imran, Amira sam ba kunya ba ta ido, wai anbi mijinta Lagos, kenan itama kishin za tayi a kansa?

"Bani guri zan tafi gida kar in dare a hanya, na bar ta a gida ita kaɗai"

Ƙara lafewa tayi a jikin motar tana kallonsa, tace  "ni da ka bari a nan watanni biyu ban ganka ba baka damu ba ko? Ihsan itace mace ko?"

Yau Imran yake ganin duniyanci a gurin Amira, matar da ta dinga kuka tana an Aura mata mugu ita seya saketa, amma ita ce take wannan abun"

Gani yai wankin hula ze kaishi dare, dan haka ya sa hannu ze janyeta daga jikin motar, dan duk jikinsa ya mutu, ba shi da energy ɗin daze cigaba da mata shouting, dan idan yayi ma ko a jikinta.

Sedai wani shocking yaji daya riƙota, wanda hakan yasa shi saurin sakinta yace  "dan Allah ki matsa ki bani Guri zan tafi"

Tace "To Mijin Amira"  ta bashi Guri ya shiga motarsa ya fita.

Ta gyaɗa kai tace "zaku gane baku da wayo, daga kai har skelaton ɗin matarka"

Amira ta koma cikin gida, a Falo Anty tace "Amira Imran ya fasaltamin gidan, base munje ba, na turawa masu shagon kalar kayan da ya dace, gobe in Allah ya kaimu za'aje a karɓo kayan da sauran siyayya, daga nan za'a wuce jere, ranar Friday insha Allah zaki tare!!!

"Anty in tare kuma?"

"Eh ki tare Amira, hakane yakamata, babu amfani zamanki a nan, saboda abunda ake hasashe ba haka bane, kuma na fuskanci rashin zama guri ɗaya dashi ne yake sake saku wani abun, gara ki tare da wuri"

Gaba ɗaya se jikin Amira yayi sanyi, Anty tace "ki kwantar da hankalinki kinji Amira, bakomai Allah ya iya mana ya baku zaman lafiya"

Fadila tace "Ameen Anty"

"Gobe in Allah ya kaimu, da kaina zan ajiyeki gurin masu gyaran gashi, ki fara shirin tarewa"

Imran ma a hanyar tafiya gida tunani ya dinga yi, lallai Amira ma ba baya ba gurin kishi, gata da tsiwa da neman maganar tsiya, ita kuma Ihsan ga rashin haƙuri da saurin hasalar tsiya, ga Anty tace masa Ranar juma'a Amira zata tare, koya zeyi da wannan gwaramar da rikicin?......



Share Please

Domin Sharhi, gyara ko shawara
07063065680.
[1/29, 1:51 PM] Ayshercool: *_ASSALAMU ALAIKUM WARAHMATULLAH, INA KUKE MASOYA AYSHERCOOL, MASOYA LITATTAFAN TA, KAMAR SU WATA KISSAR SAI MATA, WUTA A MASAƘA, ABDULJALAL,AƘIDATA, DA DAI SAURAN SU TO GA SANARWA TA MUSSAMAN, INA ME FARINCIKIN YI MUKU ALBISHIR DA FARA SAKIN SABON LITTAFINA NA RUƊIN ƘURUCIYA, LABARI ME TARIN FAƊAKARWA DA ILIMANTARWA GAMI DA NISHAƊANTARWA, KUMA BULALIYA GA IYAYE, RUƊIN ƘURUCIYA ZE TAƁO ABUBUWA DABAN DABAN GAME DA RAYUWAR MATASAN YARA WANDA SUKE KAN ADOLECSEN PERIOD, IRIN HATSARIN DA WANNAN SHEKARUN SUKE DA SHI, DAMA SAURAN ABUBUWA NA ILIMANTARWA DA KUMA NISHAƊANTARWA, ZAKU IYA MORE KARANTA WANNAN LITTAFIN AKAN KUƊI NAIRA ƊARI UKU KACAL, LITTAFIN ZE FARA ZUWAR MUKU BIYAR GA WATAN FEBUARY DA YARDAR ALLAH, ZAKU IYA TURA KUƊINKU TA 0009450228, AISHA ADAM, JA'IZ BANK, KU TURA SHEDAR BIYA TA 07073065680, DOMIN NEMAN ƘARIN BAYANI ZAKU IYA TUNTUƁAR WANNAN LAMBAR 07063065680*_
[1/29, 3:47 PM] Ayshercool:     
🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥

WUTA A MASAƘA

PERFECT WRITERS ASSOCIATION

(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS)

https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P. W. A

*Story and written by*
AISHA ADAM (AYSHERCOOL)

The experience writer of

*ABDUL JALAL*
* WATA KISSAR.... (SAI MATA)
*BAƘIN TABO (Labarin gasa)
*AƘIDATA (Paid Book)
* WUTA A MASAƘA

https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=in

❌❌❌
Ƙirƙirarren labari ne, ban yadda ayi amfani da kowane sashi na labarin ba ba tare da izinina ba.





                          31_32

Da farko Amira ta shiga fargaba, jin Anty ta ambaci tariyarta a kurkusa, daga baya kuma gara ta tare idan yaso ayi duk wadda za'ayi, wayarta ta ɗakko ta kira Anty Fa'iza, tayi sa'a kuwa ta ɗaga.

"Malama lafiya zaki kirani a yanzu, ina tare da mijina?"

"Iyee seki gayawa wanda bashi da mijin ai, Anty Fa'iza na wuce wannan yanzu fa"

"Ke dalla can, ya akayi ne?"

Amira tace "Normal, tun da yana kusa ba shi mu gaisa"

Fa'iza ta miƙawa Bashir wayar, ya karɓa tare da faɗin "Assalamu alaikum"

"Wa'alaikum salam, Yaya Bashir barka da dare"

"Yawwa Amira barka, ya kike ya gidan?"

"Lafiya ƙalau Alhamdilillah,  ya yarana ya aiki?"

"Alhamdilillah kowa lafiya Amira, fatan dai komai lafiya babu wata matsala?"

"Babu wata matsala Yaya Bashir"

"To Alhamdilillah, Ubangiji Allah ya banu zaman lafiya me ɗorewa"

"Ameen ya Allah Yaya Bashir, nagode sosai"

Ya miƙawa Fa'iza wayar, ta karɓa tace "ina jinki"

"Anty Fa'iza ranar juma'a in Allah ya kaimu zan tare fa"

"Haba dai"

"Wallahi dagaske nake"

"Allah sarki, to Ubangiji Allah ya nuna mana yasa ki shiga ɗakin Aure a sa'a Amira"

"Ameen Anty Fa'iza, but am scared"

"Scared of what kuma?"

"Kin san ba sona yake ba, ina tunanin irin zaman da zanyi da su, ga zuciyata da rauni, kin san wasu lokutan bana iya jure wasu abubuwan, mussaman wulaƙanci da tozarci, ni gaba ɗaya na rasa me yake min daɗi ma"

"Amira ki kwantar da hankalinki kinji, babu abunda ze faru insha Allah, sedai dole kiyi haƙuri da wasu abubuwan da zaki gani, amma kiyi haƙuri na ɗan lokaci ne Komai ze wuce insha Allah".

"To shikenan Allah yasa, zaki zo tariyar ne?"

"A' gaskiya, sedai bayan an kaiki zanzo, bani da lafiya ne Amira"

"Kice an gamu kenan?"

"Aka gamu dame fa?"

"A'a Allah ya kaimu nan da watanni mu zo suna"

"Ko dai mu muzo suna Kaduna ba"

Amira tace "Idan Ihsan ta haihu kenan?"

"Idan kin haihu dai, ke ba kya fatan ki haihun ne?"

"Mhmm Anty Fa'iza kenan, ni dai zan turomiki kuɗi account ɗinki, da list ɗin abunda nake son kin siyomin, a kai tasha ki sakomin a mota"

"Me kike buƙata haka?"

"Zan turomiki ta message, kin san bani da lefe, kuma gidan nan sun min iya yinsu, wallahi baki ga kuɗin da suke kashemin ba, zan sako miki dubu ɗari biyu a account kimin siyayyar, idan basu isa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login