Showing 3001 words to 6000 words out of 120332 words

Chapter 2 - WUTA A MASA?A COMPLETE HAUSA NOVEL BY AYSHERCOOL

10 Mar 2025

30336

jikinta  ta fito, maimakon ta nemi hijjabi ta suturta jikinta, amma ta fito a haka, gajeren wando ne a jikinta, da wata matsatsiyar vest, ta baje kalbar attach dake kanta.

Baffa Salahu yace "Ke baki da hankali baki da ɗa'a ko? Shine kika fito a haka saboda baki da Kunya?"

"To waini ya zanyi? Idan na tsaya saka hijjabi masifa zakayi min, yanzuma kuma ban tsira ba".

Baffa yace "nine nake masifar ko? Amira ba kiwa kanki adalci ba wannan mumunnar rayuwar da kika ɗauka, kina 'ya mace da iliminki da komai amma kika zaɓi yawon ta zubar, duk danginmu bamu taɓa samun wanda yai abunda kika aikata ba, abun kunya kamar wanda kike ba'a taɓa samu ba wallahi".

Amira tace "Baffa wane irin abun kunya kuma? Nifa ban taɓa cikin shege ba"

"Ni kike gayawa baki taɓa cikin shege ba? To je kiyo cikin shegen karki fasa dan ubanki, idan akace a rayuwa 'yar Habiba zata yi karuwanci, za'a ƙaryata hakan amma segashi kina zubar mana da kima da martaba a idon duniya, daga uwarki har ubanki babu mutumin banza kaiconki Amira, kaico".

Wani irin abune ya tokarewa Amira a zuciyarta, taji kamar ta fasa ihu, amma tai shiru ta sunkuyar da kai, Baffa nayi Baba nayi, su Yaya Usman ma suka saka baki, aka dinga mata faɗa da tashin hankali a ka, gashi Amira ta tsani faɗa a rayuwarta.

Seda suka yi me isarsu, Baffa yace  "duk ranar data kuma fita gantali tayi dare, ko Usman ko Zailani a cikin mazan gidan nan, a samu wani yai mata dukan tsiya, sannan duk randa ra kuma yiwa wani rashin kunyar ko iyashege azo a gayamin, se naci mutuncinki Ja'ira mara kamun kai, kuma daga yau ko ƙofar gida kar a sake bari ta fita, wuce kije ki tattare wannan kwanukan ki wanke, ki ɗora abincin safe, dan matan gidan nan ba bayinki bane suda yaransu, a wanke a ɗora a dafa a baki kici, kuma ki cika musu ciki da iskanci ba"

Amira ta kalli uban wanke wanken dake zube a gurin, da uwar tukunyar da ake ɗorawa a gidan dan girka Abinci, ta kalli furfurar dake kai da gemun Baffa Salahu, tabbas ba dan wannan furfurar ba da seta yanka masa rashin mutunci.

Amma lokaci ɗaya ta sauya kamar ba ita ba, cikin ladabi tace  "zanyi insha Allah, zan wanke kwanukan sannan zan dama kunun karyawar, Allah ya baku haƙuri"

Kamar gaske ta nufi inda murhu yake, masu zagi na cigaba da zaginta, suna faɗar albarkacin bakinsu, taje ta iza wuta ta miƙe tai hanyar banɗaki, tana zuwa ta suri hijjabi a jikin katanga, tai waje da gudu....



Ayshercool
07063065680
[1/2, 11:06 AM] Ayshercool: 🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥

                WUTA A MASAƘA

              
                         Page 2


PERFECT WRITERS ASSOCIATION

(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS)

https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P. W. A

*Story and written by*

_*AISHA HUMAIRA
(Daddy's girl)*_

The experience writer of
*ABDUL JALAL*
* WATA KISSAR.... (SAI MATA)
*BAƘIN TABO (Labarin gasa)
*AƘIDATA (Paid Book)
* Anda no WITA A MASAƘA

SADAUKARWA GA ƘUNGIYAR PERFECT WRITERS ASSOCIATION, DOMIN TAYA MURNAR CIKA SHEKARU BIYU DA KAFUWA

https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=in

       



                 Page2





Amira na jin yadda aka biyo ta ana ƙwala mata kira, amma ta arta da gudu tayi waje, a ƙofar gida ta ƙarasa saka hijjabin data ɗakko akan katanga, tai titi a guje, ta hango wani me napep ta ɗaga masa hannu, ya tsaya ta shige tai gaba abunta.

Baffa ya tasaya yayi saroro, yace  "haka yarinyar nan ta zama? Inyi mata magana amma ta zari hijjabi ta gudu"

Baba yace  "kaɗan ma ka gani, ba abinda ka gani kai kana gefe, mutanen dake cikin gidan nan mu zamu ƙarar da iya shegen da yarinyar nan take yi, iskanci da rashin mutunci iri iri, haka take aikatawa"

Ya jinjina kai yace  "lallai lamarin yarinyar nan ya gawurta, idan ta dawo gidan nan, ɗaureta za'ayi a mata shegen duka, duk inda taje zata dawo ai, koma a sakata a mari kowa ya huta"

Nan suka cigaba da kwashewa Amira Albarka, Amira kam taiwa me napep kwatancen inda ze kaita.

Ana zuwa inda zata sauka, ta sauka ta bashi kuɗinsa, ta shiga wani layi.

Allah ya temaketa, da kuɗinta da wayarta suna cikin aljihun Wannan wandon nata.

Ƙofar wani ƙaramin gida taje, ta ƙwanƙwasa ƙofa, ta buga ya kai sau uku sannan aka zare sakata aka buɗe, namijine ya buɗe wanda aƙalla ze kai shekaru talatin da biyu, ya kalleta yai murmushi yace  "Anty Amira ashe kece, sannu da zuwa"

Yai maganar yana bata hanya, tace "Yawwa, tana nan kuwa?"

Yace "Gaskiya taje kai Khalil Asibiti baya jin daɗi, Khairat kuma na makaranta"

Abunda ya faɗa ɗin be hana ta sa kai ta shiga cikin gidan ba, kai tsaye ta wuce falo ta samu guri ta zauna, sannan tace "Abban Khalil meya samu ɗana, da har aka kaishi Asibiti?"

Abban Khalil yace "wallahi zazzaɓi yake yi, bari inje in dawo yanzun nan"

Amira tace "to shikenan"

Yasa kai ya fita, ta kunna kallo ta miƙe akan kujera abunta, ya kai mintunta goma sha biyar sannan ya dawo, daya dawo ɗinma yai sallama ta amsa kitchen ya wuce.

Amira tana ta chatting ɗinta, aka jima segashi ya shigo da faranti ɗauke da kayan tea, harda soyayyan ƙwai yace  "tunda naga kin mana dirar safiyar nan, nasan baki karya ba kuma mu mun cinye namu"

Amira ta kalleshi tace 'dana san wahala zakamin haka da tabbas bazan bari kayi ba"

"Wannan ɗinne wahala? Tashi ki karya malama kafin in fushi Yanzun nan"

Amira tai murmushi tace  "Allah ya baka haƙuri, Nagode".

Ya fita ya bar mata falon, ta zauna ta karya, ta fito da kwanukan tsakar gida ta tarar yana ta harhaɗa kwanuka ze wanke.

"Abban Khalil, me zakayi haka? Ka bari idan ta dawo tayi mana"

Yai murmushi yace "ahh haba dai, ya za'ai ta tafi kai yaro Asibiti ban rakata ba, in bar mata aikin gida bayan ban san lokacin da zata dawo ba, ai gara in rage Mata"

Amira tace "kaga ɗan aljanna, ka barshi zan mata aikin kafin ta dawo".

Yace "A'a, ke ai baƙuwa ce"

"Kaji ka wai baƙuwa, Allah ka bari zanyi ka tafi kasuwarka"

Da ƙyar ya yadda ya tafi, ta tarar har wake ya dafa saura shinkafa, ya bar kuɗin siyan salak, ta jinjinawa haƙuri da tausayi irin na Abban Khalil.

Se sha biyun rana Sannan matar gidan ta dawo, tai sallama Amira ta amsa, ta shiga falon ta tarar da Amira.

"Ke kuma saukar yaushe?"

Amira tace "tun safe nazo, ba kya nan se Abbansu Khalil, kin tafi kin barshi da aikin gida saboda rashin tsoron Allah"

"Ke dalla yimin shiru, ba ɗansa na tafi kaiwa Asibiti ba?"

"To kuma se akace ki bar masa aikin gidan?"

"To dakeni uwata, kona sa shi, ko ban sashiba in dai Abban Khairat ne se yayi, ba ruwansa"

Amira tace "Allah Sarki, Anty Fa'iza kinyi dacen miji wallahi, ana cewa da anyi aure wata ɗaya biyu ake dena wannan soyayyar da kulawa, amma ke gashi haihuwar ki biyu, shekaru shida da aurenku, amma haryanzu sonki yake kamar lokacin da yake neman aurenki"

Fa'iza tace "bari kawai Amira, shiyasa tun a wancan lokacin na dage seshi, su Baffa suka sani gaba da zagi da cin mutunci dan nace bazan auri Alhaji Yahaya ba, kin san ɓarin kuɗi ya dinga musu, kowa ya juyamin baya a gidan nan, Inna ma ƙiri ƙiri ta dinga zagina da cin mutumci wai na mannewa matsiyaci na liƙe ni se Bashir nake so, Wallahi da Alhaji Yahaya na aura baze dinga tarairayata haka ba"

Amira tace "bari Anty Fa'iza sha'anin gidanmu se Allah kawai, amma munyi rayuwar wahala, kamar ba'a gidan aka haifi iyayenmu ba, ni kaina yau da Sassafe akaje aka taho da Baffa zasu min tijara, yazo yana wassafamin wasu ƙa'idojinsa na banza, ni kuwa na zari hijjabi na arto nan, se sun sake ganina a gidan ai, sun taru a kaina suna ta cin zarafina suna zagina, danma Allah ya temake ni Inna bata nan, tsohuwar nan kallonta kawai nake, idan naje da abun duniya na kaimata, ta karɓe tana dariya, idan wulaƙancinta ya ciyota kuma ta kama cemin karuwa, ni kuwa nace ta dena cin abina"

Fa'iza tace  "Amira maganar Allah da ma'aiki, abubuwan da kike aikatawa basu dace ba, kuma kema kin sani Amma....

Amira ta dakatar da ita ta hanyar ɗaga mata hannu tace  "ba shawararki nake nema ba ko wa'azi, indai zan samu namiji me kirki nagari kamar Bashir wallahi zanyi aure in dena abunda nakeyi, muma ajiye wannan maganar aside Please karki ɓatamin rai, sakkomin yarona naga ya tashi, kin bar yaro duka ya rame"

Fa'iza ta girgiza kai, ta sakko Khalil ta miƙawa Amira, Amira ta karɓeshi ta rungumeshi a jikinta, tana shafa kansa tana "Sannu kaji My Boy, mamanka ta barmin kai duk ka rame"

Fa'iza tace 'tunda gaki kinzo ai shikenan, ki kula dashi"

Amira tace "tabbas zakiga yadda zan kula da Yarona, naga sha biyu da rabi, ban kayanki in saka muje mu ɗakkko Khairat daga makaranta, dan daga ni se kayan baccina na fito"

Fa'iza ta bawa Amira kaya ta canza, ta ɗau Khalil ta goyashi suka fita.

************************

Sannu a hankali yake tuƙa motar, kamar yana jin tsoron hanyar, yanayi yana kallon agogon hannunsa, lokaci lokaci yakan lumshe idanunsa, tare da buɗesu yana  ɗan kalle kalle.

Sannu a hankali ya ƙaraso ƙofar wani ƙaton gida, sau biyu kawai yai hone ya ɗan tsaya, buɗe gate ɗin akayi ya shiga cikin gidan da motar tasa, ya ɗan ɗau lokaci a cikin motar sannan ya fito daga cikin motar.

Megadi yana tsaye a jikin motar, yana jiran fitowarsa, koda ya fito ridinawa dattijon yayi yana faɗin 'barka da dawowa ranka ya daɗe"

"Yawwa barka, mutan gidan suna ciki ne?"

Megadin yace "Eu yallaɓai, Suna nan"

Yace "Good, buɗe bayan mota akwai trolley ɗina, ka kaimin ɗaki"

"To yallaɓai"

Sanye yake da wandon sojoji, sekuma baƙar shirt me gajeren hannu, dogone na gaske me siffar ƙaƙƙarfa, kallo ɗaya zaka masa ka san bashi da fara'a sosai, dan ransa a haɗe yake babu annuri, wani irin taku yake kamar wani boss, ya nufi ƙofar da zata sada shi da cikin gidan.

Yana tura ƙofar falon, sanyin AC da ƙamshin turaren wuta ya bugi hancinsa, ya ɗan lumshe idonsa sannan ya shiga falon da Sallama.

Ba kowa a falon, ya nemi Guri yai zamansa, ya kwanta akan doguwar kujera ya ɗora ƙafarsa ɗaya kan ɗaya, dan ko takalmin be cire ba.

Ya kai mintuna shabiyu sannan aka buɗe wata ƙofa a cikin falon, wata babbar mace ce ta fito daga ƙofar hannunta ɗauke da ƙaramin robar youghurt.

Tana ganinsa a kwace tai turus, tace "kai dan ƙaniyarka saukar yaushe? Maimakon ka kirani a waya kawai se in ganka?"

Murmushi yayi ya tashi zaune yace  "Hajiya Ammi, maimakon amin sannu da zuwa amma an tareni da ƙorafi, dama cewa nayi let me suprise you, Amma tunda bakya so bari in koma"

Tai dariya tace 'eh tashi ka koma ɗin, dan tunda ka tafi 'ya'yana suka sake, dodonsu baya nan"

"Aikuwa gani na dawo, kowa ya kintsa zamansa"

Ammi tai dariya ta samu Guri ta zauna, tace  "sannu da zuwa ya hanya?"

"Alhamdilillah Ammi".

"Ya fama da bindinga ya fargaba?"

Yai dariya yace 'haba Ammi, fargaba se mata, mu idan muka fita aiki ai mun san a ɗayan biyu muke, ko mu kashe ko a kashe mu, dan haka Bama fargabar komai, ina Boss ne?"

Ammi tace  "yau kuma Uban naka ne Boss? Yanzun nan ya fita Allah yayi bazaku haɗu ba, mhmm Kodayake ma ban sani ba ko shi yasan yau zaka zo, dan naga kafi sonshi a kaina, jeka kayi wanka ka canza kaya, kafin nan na kammala Abinci kazo kaci"

Yace "to Ammi, ina mutan gidan ne?"

"Yaufa ranar aikice, duk suna makaranta ai"

Yace "ok"

Daga nan ya fito daga falon yabi kan wata baranda, dan zuwa ɗakinsa. yana shiga  ya ƙarewa ɗakin kallo, duk da baya cikin ɗakin amma ɗakin fes dashi, komai tsaf tsaf da alama ana shigowa a gyara dukda baya nan, beyi mamakin hakan ba tunda dama tsafta ɗabi'ar Amminsu ce, be taɓa tafiya ya dawo ya tarar da ɗakinsa da datti ba.

ya ciro wayoyinsa ya ajiye ya cire kayan jikinsa, ya ɗauki towel ya ɗaura da nufin ya shiga wanka, amma wayarsa ta fara ringing.

Ringing tone ɗin wayar ne ya sanar da shi me kiran wayar, dan haka yai murmushi ya dawo ya ɗauki wayar yasa a kunnensa sedai beyi Magana yai shiru.

Muryar mace ce tace "Hello, Hello, My own kana jina kuwa?"

"Ina jinki Babyna, ya akayi ne?"

"Wai zaka dawo yau ɗin kuwa?" Tai maganar a kasalance.

"Shagwaɓaɓɓiya kawai, ban taho yau ba, bazan samu dawowa yau ba, sedai zuwa jibi in Allah ya kaimu zan dawo"

"Haba dan Allah, wai yanzu ma ba zaka dawo ba? Haba My ni gaskiya..

"Ke gaskiya me? Jibin ma ba tabbas na zan dawo"

"Wallahi ji nake Kamar inyi kuka, wallahi bakaji yadda nake so in ganka ba, wata huɗu fa bamu haɗu ba, zanyi kuka, ni duk raina ya ɓaci duk na damu in ganka"

"Dallacan shagwaɓaɓɓiya kawai, na shigo gari anjima zanzo insha Allah"

"Wayyo Allah daɗi, dan Allah ka taho yanzu kaji my love?"

"Gaskiya sena huta, yanzun nan fa na dawo, Gashi Ammi zatamin girki"

"To naji, amma kaci na Ammi kaɗan, idan kazo kaci nawa kaji My Own"

Yai murmushi ya shafi sumar kansa yace  "As you wish my Ihsan, yadda kike so haka za'ayi, amma amin izini inzo anjima, in ɗan samu hutu, saboda na sha hanya"

Ihsan tace  "Shikenan My Own, ka huta sosai kaji, ina nan ina jiranka kazo inta kallonka, bari in ƙyaleka ka huta"

Yace "Ba dan wanka zan shiga ba da mun cigaba da wayar, in cigaba da jin muryar nan taki me saukar min da nutsuwa"

"Nima sauraron muryarka yana samun nutsuwar zuciya my, ka kasance cikin farin ciki semun haɗun"

"Jinake Kamar kizo ki tayani wankan nan, Allah dai ya kaimu lokacin bikinmu, ya nunamin Ranar da zaki zama mallakina Ihsan"

Katse kiran tayi, dan idan ta ƙyaleshi ze fara sakin layine, shima a ɓangarensa yayine dan ya tsokaneta, dan yasan take zata kashe wayar, dan Ihsan akwai Kunya.

*********************

Amira tana gidan Fa'iza har yamma, dan bata da niyyar tafiya, Fa'iza taji daɗin zuwan Amiran, suna zaune sunata uwar hirarsu suna dariya, wayar Amira ta fara ringing, sunan Sultan ne ya fito akan screen ɗin wayarta.

Ɗaga wayar tayi tace "Ya ake cikine?"

Fa'iza tace "maimakon kiyi Sallama?"

Harararta Amira tayi tace "Ina jinka"

Sultan yace "Ke maimakon ki kirani, kiji ya ake ciki, ko kuma kizo ayi lissafi amma koki nemeni a waya?"

Amira tace "nasan kuɗina bazasu ciwu bane, idanma anci se an fitar dasu"

Sultan yace "waya isa cin kuɗin gimbiya? Ai anyi kyakkyawan samu jiyan nan, wallahi kina wuta Amira kina bada kala fa, mun samu kuɗi sosai jiyan nan, sake turomin account Number ɗinki, zan turomiki kuɗi sannan akwai wani zazzafan News"

"Wait, nawa ma zaka turamin ne inji?"

"Dubu ɗari da hamsin ne".

Amira tace "meya cinye hamsin ɗin su zama ɗari biyu"?

"Haba Amira, wallahi naki yafi na kowa yawa, kin san bazan cuceki ba, saboda in bake ba DJ Sultan, wallahi ban cuceki ba, su muti duk dubu talatin suka samu"

"Shikenan naji, turomij haƙƙina"

"To ai bakiji sauran zancen ba, wani Alhaji ya bada iPhone a baki, yace kin burgeshi sosai, akwai bikinsa da za'ayi a Abuja, yana gayyatarmu kuma wallahi zamu samu kuɗi sosai Amira, dan bikin ɓrayin gwamnati ne basa jin kuɗi Sam"

Amira tace "kai Sultan Abuja kuma? Gaskiya Iskancin nawa be kai nan ba, a yadda ake sace mutane inje a saceni bame karɓoni, idan na tafi Abuja kuma ai se a koreni daga gidan gaba ɗaya"

"Haba Amira, kina abu kamar baki waye ba, satin da za'a fara bikin zamu tafi kuma idan ta jirgi kikace jirgi za'a biya mana, za'a kama mana Hotel ɗakinki daban, idan sun koreki daga gidan seki sai naki, dan nasan Idan Alhazan nan suka ganki zasu saki bakin aljihu"

Amira tai ajiyar zuciya tace "senayi shawara tukuna, Yanzu dai fara turomin wannan kuɗin".

"To yanzu zan turomiki insha Allah, amma dan Allah ki yanke shawarar da wuri, saura sati biyu bikin"

"Kai dan Allah karka isheni mana, nace zanyi Shawara"

"Shikenan ai girmanki ne Gimbiya, ina saurarenki"

Tunda Amira ta fara wayar nan Fa'iza take binta da kallo harta gama, tana ajiye wayar Fa'iza tace  "Amira yanzu seki tafi Abuja yawon rawa? Wakike dashi a Abujan? Kinga Amira ki kiyayi kanki"

"Anty Fa'iza, ko naje Abuja ko banje ba sunana Ƙaruwar, babu abunda ze canza sema gyaramin kasuwancina, dan can ne zan haɗu da manyan attajirai in samu kuɗi sosai"

"Amira, wataran fa ke uwace, meyasa baza kiyiwa kanki faɗa ba, ki dena wannan abun da kike? Ɓatawa kanki suna kike sake yi fa, kuma labarin abunda kika aikata har 'ya'yanki, ki samu ki nutsu ki nemi miji kiyi aurenki"

"Anty Fa'iza aikin gama ya gama fa, abu kan yafaru ake maganinsa base yafarau ba, na riga nayi nisa karki tsammaci zan ji kiranki"

"Amira, haryanzu baki makara ba, ni kaina bana jin daɗin abunda kike fa, gaba ɗaya...

Amira bata bari Fa'iza ta ƙarasa ba taja tsaki, ta miƙe tace "na fuskanci dan nazo gidanki ne kike nema ki takuramin, gara in tafi in barmiki gidan"

Fa'iza ta riƙeta tace "haba Amira, ya za'ai ince bana son zamanki a gidana"

Fizge hannunta tayi, tai waje sedai tana fita tsakar gida, Sega babur ɗin Bashir mijin Fa'iza ya dawo, yana shigowa ya kalli fuskar Amira yaga ranta a ɓace, yace "Anty Amira, lafiya kuwa?"

"Lafiya lau" ta bashi amsa a ciki.

Yace"A'a ba lafiya ba, naga ranki a ɓace, ko Ummu Khairat ce ta miki wani abun?"

"Eh itace".

Yace "Subhanallah, metayi miki?".

"Dan nazo gidanta shine zata dinga min faɗa, shine nace tafiyata zanyi"

"A'a baza'ayi haka ba ai, Ummu Khairat kina inane?"

Fa'iza na jinsu amma tayi banza dasu, Bashir yace "muje falon mu same ta"

Suka shiga cikin falon, suka tarar da ita a zaune tana jinsu, ya kalleta yace "Maman Khairat, meyasa zaki dinga yiwa Anty Amira faɗa? Laifin metayi ne?"

"Ta gaya maka kome tayi mana"

Yace "A'a, ni base naji ba, amma dan Allah tunda bata so a dena mata faɗa, haba tana Maman Khalil ki dinga mata faɗa a gaban 'ya'yanta, Anty Amira ƙyale wannan Yayar taki, yi zamanki Ranar da kikeso seki tafi"

Amira tace "shiyasa nafi sonka a kanta ai, kai bakamin faɗa se ita, ni dama Alhaji

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login