Showing 78001 words to 81000 words out of 120332 words

Chapter 27 - WUTA A MASA?A COMPLETE HAUSA NOVEL BY AYSHERCOOL

10 Mar 2025

30364

na fara jin tsoron ko wani abun tayiwa Imran, da ma na ganta tana binne wani abu rannan, Ammi dan Allah kiyi wani abu"

"Amiran ce ta dakeki?"

"Wallahi Ammi duka na tayi, har da fasan baki"

"Kina me kika tsaya ta dakeki, baki samu abu kin rusa mata a ka ba, saboda wulaƙanci, gani nan zuwa gidan naku, shima Imran ɗin ze gauraya dani, gani nan zuwa"

Ihsan ta ajiye wayar tace "wallahi ba zaka maida ni 'yar iska ba, da mahaifiyarka zan dinga haɗaka, har seka rabu da wannan banzar"

Amira kuwa zamanta tai a falon, ta cigaba da kallon TV, labarai take kallo, taga yadda ake sanar da kisan sojoji a daji, da irin wahalar da suke sha a daji, gaba ɗaya ko motsi ba tayi, ta ƙurawa TV ido, ba zato ba tsammani taji Imran ya janyota daga kan kujerar .

Kunnenta ɗaya ya riƙe yace  "ban gayamiki bna son rigima a gidana ba, ko nan yai miki kama da gurin dambe da zaki daketa, dan kinga kinfi ƙarfinta ko? Kin manta dukan da nai miki kenan kina son in sake Miki wani kenan?"

Shiru Amira tayi ta sunkuyar da kanta ƙasa, "idan kika kuma yunƙurin dukanta, ko makamancin haka sena rama mata, kin saba dambe da hauma haumarki a waje to ni ba zakimin a nan ba, na gaya miki"

Ya dungurar da ita a gurin, ya miƙe ya juya ze fita, kawai yaji sheshsheƙar kukanta, har yaje bakin ƙofa ya juyo ya ganta zaunia gurin, tana kuka girgiza kai kawai yai ya fice.

Seda akayi sallar magariba sannan Amira ta tashi ta koma ɓangarenta.

Tana nan kwance takaici yana nuƙurƙusar zuciyarta, Hasbunallahu wani'imal wakil kawai take maimaitawa don samun sassauci a ranta.

Ihsan ta gani a kanta ba zato ba tsammani, ɗaga kai tayi ta kalli Ihsan.

"Kin zata kin dake ni kim daki bulus ne, ai wallahi gidan nan ko da tsiya se kin barmin gida, kije uwar masu gidan tazo da kanta, dan in tabattar miki da na fiki power a gidan nan"

Seda ƙirjin Amira ya buga, jin Ammi ce ta zo gidan, Ihsan ta juya ta fice daga part ɗin.

Amira ta miƙe ta sanya hijjabi ta fita falo, ta tarar da Ammi a zaune, Imran na ƙasa a gefe, Ihsan ma haka.

Amira tai sallama ta nemi Guri ita ma ta zauna, Ammi ta kalleta a wulaƙance tace "ai na zata ba zaki fito bane hakima"

"Ammi sannu da zuwa"

"Rufen baki, ba sannu da zuwanki na zo ji ba, wato kin far fafutukar haɗa husuma a tsakaninsu, hadda duka kin fara gwada halin naki na 'yan tasha, ki Aure mata miji sannan ki dake ta banda binne binnen da kike dan ki rabasu ko? Wallahi ba da  ina tunanin wani abu ba, wallahi da A daren nan zan sa ya sakeki ki koma in da kika fito, 'yar marasa mutunci mara tarbiyya kawai, wallahi da wasa kika kuma gangancin dukan Ihsan seya sakeki, kuma yanzunma ba haƙura nayi ba se na kashe Wannan Auren, da ɗana baze zauna da Karuwa ba lalatacciya irinki.

Kai kuma, wallahi ko da wasa na sake jin ta daki Ihsan ba ka ɗau mataki ba, ni zan zo in ɗauka kuma sena ci mutuncin ka"

"Ammi ya zanyi, kullum cikin tashin hankali suke, Ihsan ta kasa jan girmanta, ta fiye kishin tsiya...

"Rufemin baki, ya ba za tayi kishi ba? An Auro Karuwa an ƙaƙabo mata gida? Dole tai Kishi, haka kurum saboda son a sani na Mahaifinka ya ƙaƙabo maka wannan yarinyar, wadda ta gama gantalinta a waje, ta gama bin maza a bariki, ya sa ka Aureta, ai ko ba ta so seta bar Gidan nan, ba zan zuba ido ina kallo a kawomin mugun iri cikin zuriyata ba wallahi"

Amira ta ɗaga kai ta kalli Ammi, ta sunkuyar da kai, Imran ransa ya ɓaci da gayawa Ammi da Ihsan tayi, a jejjere A 'yan kwanakin nan baze iya lissafa adadin lokutan da ya ga Amira na kuka ba, shi tsoronsa ma kar wani ciwon ya kamata.

Ammi ta wanke Amira da baƙaƙen maganganu da cin mutuncin a gaban kishiya, Amira ta kawo iya wuya, dan zuciyarta raya mata take ta zagi Ammi, in yaso Auren ya mutu da hujja kowama ya huta, amma ta daure zuciyarta taita ambaton Allah.

Seda Ammi tayi ta gama, Sannan ta tashi ta tafi, Ihsan ta riga Imran dawowa falon, ta kalli Amira ta kwashe da dariya tace  "a zatonki bariki sekayi Iskanci sannan zaka iyata, wallahi na fiki Rashin mutunci kuma gidane sekin barmin shi da mijina wallahi"

Amira ba ta ko ɗaga kai ta kalleta ba, Imran ya shigo ya kalli inda take zaune, ba ta tashi ba, sosai yajiata bashi tausayi, Ammi taci mutuncinta da yawa, amma haka shima ya shareta ya wuce ya barta a gurin.

Ihsan ta zaci Imran yana shigowa zasu shirya, sedai taga sam ko kulata beyi ba.

"My wai haryanzu fushin kake?"

A fusace yace "tambayata ma kike? Idan har Amira zata iya rufamin Asiri ta ɓoye laifina a gurin mahaifina, ke meyasa kikamin haka? Am disappointed on you"

"Amma meye dan na gayawa Ammi, na faɗa mata ne dan taiwa tufkar hanci, kar inje ka zagaye ka koma gurinta"

Ran Imran ya ɓaci matuƙa, be kuma tanka mata ba ya bar mata ɗakin, ya koma ɗaya ɗakin ya rufe ƙofa.

Da Asuba ya fito zashi sallar Asuba, sedai ga mamakinsa ya ga Amira kwance a falon nan inda suka barta, a gurin ta kwana.

Seda Imran ya firgita, ya ƙarasa inda take da sauri, sedai yana dubawa yaga  Bacci take, se ajiyar zuciya take.

Ya ɗan ƙuramata ido, gaba ɗaya tausayinta ya mamaye zuciyarsa.

Tashi yai yaje salla ya dawo, sedai da ya dawo ya tarar ta tashi daga gurin.

Wani zazzafan zazzaɓi ne ya rufe Amira, ga ɓacin rai ga damuwa, se rawar sanyi take a ɗaki ita kaɗai.

Message ne ya shiga wayar Imran, ana nemansa da gaggawa turasu Zamfara aiki.

Nan da nan ya fara shiri, duk da a ƙule yake da Ihsan, yaje ya sameta yace "Ihsan, Anjima zan tafi Zamfara, an turamu aiki"

Cikin ko in kula tace "Seka dawo"

Abun ba ƙaramin mamaki ya bashi ba, duk da sun samu saɓani amma ta kasa nuna a sign of care to him.

Amira ji tai sanyi ya dameta saboda zazzaɓin dake jikinta, fitowa tai Kitchen na Falo, dan ta dafa tea ta sha ko zata dena jin sanyi.

Imran ta gani sanye a Uniform ɗinsa na Sojoji, hannunsa riƙe da wayarsa ya sata a kunnensa yana Magana.

"Wallahi Abba nima cikin dare naga message ɗin, an turamu Zamfara ne kasan last week an kashe sojoji sosai, to ina cikin wanda aka tura, naso in biyo gida in muku sallama, amma an zo ɗaukata zamu tafi ne yanzu"

Saroro Amira tai tana kallonsa, dagaske Zamfara ze tafi.

Har ze fita Amira ta ƙarasa da sauri in da yake, ta riƙe hannunsa.

Waigowa yayi ya kalleta, ya kalli inda ta riƙe hannunsa, ya kalli fuskarta duk cizon sauro fuskar a kumbure.

"Wai Zamfara zaka tafi?"

"Eh, can zan tafi" ya bata amsa.

"Dan Allah kar ka tafi, kashe sojoji ake"

Kallon Amira yai, dagaske take maganar, mamaki ne ya cika shi, duk da tarin abun da aka mata, amma tana kiran kar ya tafi, ana kashe mutane.

"I was Born to serve my country, ko in dawo a raye ko a kashe ni, just pray for me"

Ya kai hannu ya goge hawayen da ke zubowa daga idonta, hakan yasa yaji jikinta da zafi yace "idan na mutu a can forgive me please!"

Domin gyara, Sharhi ko Shawara
Ayshercool
07063075680
[2/4, 7:37 PM] Ayshercool: 🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥

WUTA A MASAƘA

PERFECT WRITERS ASSOCIATION

(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS)

https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P. W. A

*Story and written by*
AISHA ADAM (AYSHERCOOL)

The experience writer of

*ABDUL JALAL*
* WATA KISSAR.... (SAI MATA)
*BAƘIN TABO (Labarin gasa)
*AƘIDATA (Paid Book)
* WUTA A MASAƘA

https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=in

❌❌❌
Ƙirƙirarren labari ne, ban yadda ayi amfani da kowane sashi na labarin ba ba tare da izinina ba.

               


                           37_38



Sake fashewa da kuka Amira tayi tace "ni dai ba na son ka tafi"

Ɗan shiru yai yana kallonta "meyasa ba kya so na tafi?"

"Ana kashe mutane, kuma bana so a kashe ka"

Jikin Imran yai sanyi sosai, ya kalli yadda ta riƙe hannunsa, ga idanunta na zubda hawaye.

Gyara tsayuwarsa yai, ya ɗago fuskarta, ta na kallonsa, fuskarta duk cizon sauro ga idanunta sunyi jawur"

A hankali yace "kin kwana a falo sauro ya cije ki, kinga zazzaɓi ya rufeki, kije ki kwanta zuwa anjima ki kira Anty a waya, a kawo miki magani, zan tafi abokan tafiya ta suna jirana, dan Allah ban da faɗa ko tashin hankali, ni na tafi"

Ya zame hannunsa a hankali, ya juya ya fara tafiya, bayansa ta bi da kallo, har ya fita daga falon.

Jiki a sanyaye ta koma ta Kitchen, ta leƙa window, ta ga sojoji a harabar gidan jikinsu da Uniform, suka hau mota suka fita.

Amira ta zauna a Kitchen ɗin ta haɗa kai da gwiwa tana maimaita 'Innalillahi wa inna ilaihi raji'un"

Sun yi nisa a tafiyar, Imran ya kira Anty, tana tsaka da aiki ta ga kiran nasa, amma tai ƙoƙari ta ɗaga wayar "Anty barka da safiya"

"Yawwa barka Imran, ya kake ya gida?"

"Lafiya ƙalau, ya aiki?"

"Aiki Alhamdilillah, mun fito tun ɗazu"

"Masha Allah, dama Anty nace dan Allah idan ban takura ki ba, kinga an turani aiki Zamfara ne, kuma na bar Amira ba lafiya, ban san lokacin da zan dawo ba, nace in ba damuwa ko zata zauna a gurinki, kan inga yadda Allah zeyi damu, tunda babu me kula da ita a gidan"

Anty tace "Ni da 'yata amma ka dinga cewa in ba zaka takuramin ba, ai gara da ka gayamin inje in ɗakko abata, yanzu Zamafaran aka turaku Imran?"

"Wallahi kuwa Anty, kin ganmu a hanya ma"

"Subhanallah, to Ubangiji Allah ya tsare mana ku, ya kaiku lafiya ya dawo da ku lafiya, Amirana kuma Allah yasa rabo muka samu"

Imran yace "Rabon me kuma Anty?'

"Rabon Baby mana, zan ɗau jika"

"Hmmm Anty kenan, ai mana addu'a dawowa lafiya"

"Insha Allah zamuyi, Allah ya tsare"

"Ameen Anty nagode"

Ya katse wayar.

Duk da yasan Ammi tana jin haushin sa amma ya kirata a waya, suka gaisa ta amsa masa sama sama, yace "Ammi ina buƙatar addu'rki, ina hanyar Zamfara ne"

Ba shiri ta ware murya tace "wace irin Zamfara kuma?"

"An turamu aiki ne, na so in biyo muyi Sallama, amma kiran na gaggawa ne, kuma abokan tafiya ta suka zo, shiyasa kawai na taho"

Ammi tace "Innalillahi wa innalillahi raji'un, To Imran Allah ya tsare mana ku, ya kiyaye ku, Allah ya dafa muku ya shiga lamarinku, Allah ya dawo mana daku lafiya" tana maganar se hawaye.

"Ammina ki kwantar da hankalinki, ba abinda ze faru insha Allah"

"Ai hankalina ba ze kwanta ba, se Allah ya dawo da ku lafiya, Allah ya tsare"

"Ameen Ammi nagode"

Ta ajiye wayar jikinta a sanyaye, Minal ta shigo ɗakin Ammi ta ganta wani iri, tace "Ammi meya sameki naga kamar kinyi kuka?"

"Bari kawai, Imran ya tafi Zamfara yanzu mu kai waya da shi"

"Zamfara kuma Ammi?"

"Eh Wai Zamfara, suna hanya ma"

"Mun shiga uku Ammi, kashe sojoji ake sosai a gurin faɗan nan fa"

"Hmm, Nifa tuntuni bana son aikin sojan nan, Babanku ya goyi bayansa yaje ya nema masa, mutum yayi masters meye na wani aikin soja maimakon ya nemi aiki, duk wani abun tsiya babanku ke gayyato masa shi, ko taya shi aikatawa"

"To Ammi yanzu haka ya tafi ya barsu a gida ɗaya, Anty Ihsan da wannan 'yar damben"

Ammi tace "aikuwa, taɓ aikam baze yuwu ba, taje taiwa 'yar mutane lahani a banza"

"Wallahi kuwa dan kin san zata aikata"

"Aikuwa ta taɓa ta se ta bar gidan nan, bari kawai mayi Magana da Maman Ihsan ɗin ta koma gida kawai, ta bar mata gidan kafin ya dawo"

"Aikuwa dai da yafi, ni dama anjima zanje gurin Mummyn".

"Shikenan, bari inje gurin babanku inji meze ce, bana son inyi abu ya zo yanamin sababi, na ga kwanan nan tun da ya aurawa Imran Yarinyar nan yabi ya canza, amma canzawarsa ba ze canza ƙudurina akan Auren nan ba"

Minal tace "nima dai na gani Ammi, bari inje in fara shiryawa"

Anty se la'asar ta tashi daga gurin aiki, kai tsaye gidan Amira ta wuce, dan ta duba jikinta kamar yadda Imran ya buƙata.

Da sallama ta shiga falon, amma shiru ba'a amsa ba, ga mamakinta Ihsan na falon a kwance tana kaɗa ƙafa.

Anty tace "Barka da gida, ina sallama amma baki amsa ba"

Ɗagowa Ihsan tayi ta kalli Anty, ta ɗan yatsina fuska tace "banji bane"

"Allah sarki, ya gidan fatan kuna lafiya"?

"Lafiya ƙalau" Ihsan ta amsa da mata da ƙyar.

Anty tace  "Nace Amira tana nan ne?"

"Bani da tabbas, tunda ba'a kaina take zaune ba"

Mamaki ne ya cika Anty, tace "to Allah ya baki haƙuri"

Ta wuce ɓangaren Amira, ta shiga da Sallama amma shiru ba kowa a falo, kiran sunan Amira tai, amma taji shiru, ta ciro wayarta ta kira Lambar Amira, amma bata ɗaga ba.

Kai tsaye ta nufi bedroom ɗin Amira, tai Sallama sannan ta shiga, A duƙunƙune ta hango Amira akan gado, tana ta rawar sanyi ga sautin kukanta da yake tashi ƙasa ƙasa.

Da sauri ta ƙarasa bakin gadon tana kiran sunan Amira, Amira da ƙyar ta iya ɗaga idonta ta kalli Anty.

"Amira lafiya meya sameki haka?"

Tai maganar tana yaye bargon jikin Amira, Amira dai kasa magana tayi se kuka, Anty tace "yi shiru ya isa kukan, bari in haɗa miki ruwa kiyi wanka, kin ci Abinci ma kuwa?"

Amira ta girgiza kai.

Anty ta jona ruwa a heater, ta haɗawa Amira ruwa, ta rakata banɗaki, ta dawo ta gyara mata gado ta canza mata bedsheet.

Tayi mamakin yadda Amira ke Rashin lafiya har jikinta ya zama haka, kuma bata gaya mata ba, Amira ta rame sosai idanunta .

Ta shiga Kitchen ɗin Amira, amma babu kayan Abinci a ciki, ta dawo ɗakin ta tarar Amira ta fito daga wankan.

Ta kalli Amira tace "na duba Kitchen ɗinki, Banga komai na Abinci ba, se ɗan abunda ba'a rasa ba"

Cikin muryar marasa lafiya tace "suna Kitchen ɗin falo"

"Amma Amira ya akai kika bari jikinki yai haka bakije Asibiti ba, kuma baki gayamin ba? Ko dai ciki ne?"

Amira ta girgiza mata kai alamar A'a.

Anty tace "wani irin A'a, in ba ciki ba to wani rashin lafiya ne ze maida ke haka lokaci ɗaya duk kin rame, kamar bake ba, yanzun me kike son ki ci?"

"Bakomai"

"Kamar yaya bakomai? Gayamin abunda kike so maza"

"Anty bana jin yunwa fa"

"Aikuwa dolen ki kici Abinci"

Anty ta tashi ta fita falo, Ihsan ta ɗaga kai ta kalleta, ta ɗauke kanta ta cigaba da kallo, tana faman hura hanci.

Anty tace "Ashe Amira ba lafiya haka?"

"Banda abunki Anty, ni na Aureta da zan san tana da lafiya ko kuma babu?"

Anty ta sake tabattar da ba zaman lafiya Amira suke da Ihsan a gidan ba, ba ta kuma kula Ihsan ba ta wuce Kitchen ɗin, tuwon semovita da miyar ganye taiwa Amira, ta zo ta sa Amira a gaba da ƙyar taci Abinci, sannan ta ɗauki sample ɗin Amira na jini, tace zata tafi dashi, a kai lap a binciki meke damunta.

Amira ta fashe da kuka tace "Anty dan Allah mu tafi tare"

"Mu tafi tare saboda me, bayan ga ɗakinki, kuma ba muyi haka da mijinki ba?"

"Anty ni dai dan Allah ki tafi dani"

"Amira ina na taɓa jin anyi haka, ai bamu nemi Izini ba"

"Anty in kin tafi waze kula dani? Kuma bani da lafiya sosai fa"

Anty tai murmushi tace "shagwaɓaɓiyya 'yar gidan Anty, Amira in cikin ne ma haka za'ayi rainon cikin da wannan taɓarar? Bari in kira mijinki a waya, idan yake da network in tambayeshi inji me ze ce"

Amira ta jinjina kai, Anty taiwa Imran missed calls sun kai biyar, amma wayar taƙi shiga.

Tace "Amira wayar Imran ba ta shiga, yanzu meye abunyi?"

Gaban Amira ne ya faɗi, kar dai har sun shiga daji? Wata irin ajiyar zuciya tayi, tare da faɗin Hasbunallahu wani'imal wakil.

"Amira na lura akwai damuwa a tare da ke, mu tafi taren kawai, in wayar tasa ta shiga na masa bayani, ko in kira Abbanki in gayamasa"

Cike da farinciki Amira ta jinjina kai, Anty ta ɗakko hijjabi ta bawa Amira ta saka, ta ɗaukar mata duk abunda take buƙata, suka fito.

Ba kowa a falo, Anty tace muje mu yiwa abokiyar zamanki sallama, kan mu tafi"

Amira ta girgiza kai tace "A'a Anty, mu tafi kawai, ki ƙyaleta"

"No ba za'ai haka ba, ba ze yuwu mu tafi ba muyi Mata sallama ba"

Anty na cikin Maganar se ga Ihsan ta fito, hannunta riƙe da plate ɗin Abinci, kallo ɗaya tai musu ta ɗauke kanta.

Anty tace "Ihsan, zan tafi da abokiyar Zamanki, bata da lafiya sosai, zan kaita Asibiti, idan da halin dawowa zan dawo da ita, idan babu kuma zan riƙeta se ta warke"

"To ni kuma meye nawa a ciki?, Naga bani na Aurota ba kuma ba zamana take ba, ai ba lallai senaji in da zata ba"

A ɗan hasale Amira tace "Anty dan Allah ki rabu da ita, taho mu tafi ni jiri nake ji"

Ihsan tace "Allah ya raka taki gona, yasa daga nan ba zaki dawo ba"

Mamaki ne ya cika Anty sosai, Lallai zargin ta ya tabatta, babu zaman lafiya tsakanin Amira da abokiyar zamanta.

Anty ba ta kuma cewa komai ba, suka ƙarasa mota ta saka Amiea a mota suka tafi, suna tafe Amira na ta kuka da ciwon kai da jiri, hakan yasa suka wuce Asibitin da Anty take aiki.

A kai mata duk tasa tasan da za'ai mata, amma ba'aga komai ba, babu ciki ba malaria Babu typhoid.

Antu ta saka aka gwada BP ɗin Amira, sedai tayi mamakin sakamakon da aka gaya mata, seda ta karɓa ta sake yi da kanta, But still thesame result.

Anty ta kalli Amira tace "Amiea, zan tambayeki wani abu, kuma gaskiya nake so ki gayamin, idan kikamin ƙarya, zan ɓata miki rai"

Amira tace"to insha Allah ba zan miki ƙarya ba"

"Meke damunki haka da yasa jininki ya hau?"

"Bakomai" Amira ta bata amsa.

"Bance karki min ƙarya ba? A baya an taɓa cewa kina da hawan jini"?

Amira ta girgiza kai alamar a'a.

"To ne yake damunki da har zaki haɗu da hawan jini a wannan shekarun naki haka? Ki gayamin me kike ciki a gidan Imran?*

"Anty bakomai fa, kawai an turashi Zamfara ne, shine na damu kuma ana kashe mutane a can"

Anty

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login