Showing 138001 words to 141000 words out of 178785 words

Chapter 47 - Babu So Complete Hausa Novel

05 Feb 2025

32818

zai basu suje su duba kafin zaman ya nema ya rasa, cikin ɗan dafe kai ya dubu Khaleel da Fharhan. “Inaga fa nama bar file ɗin nan a gida wlhy, Khaleel saika koma kenan dan dole ne mu basu suje su duba.”
“Okay bara naje ai bawani nisa bane”.
“Okay ba damuwa, kafin ka isa zan kira su ɗakko maka kawai”.
Kansa ya jinjina masa ya fice. Shi kuma ya shiga ƙoƙarin kiran layin Fadwa. Harta tsinke ba'a ɗagaba, yay mata uzirin ko bata kusa ya sake kira, amma nan ma dai hakan, ya ƙara kira har sau uku sai aka koma danna masa number busy. Ransa ya sosu matuƙa, dan ya gane tana kan sani. Amma sai ya shanye kodan baƙin dake tare da shi ya maida akalar kiran ga Anaam. Gama wayarta da su Abie kenan kiran nashi ya shigo, bugu biyu ta ɗauka har yanzu muryarta cike da farin ciki tai masa sallama. A hankali ya sauke ajiyar zuciya, ya amsa mata.
“Har yanzu murnar motar ce?”.
“Humm Yaya bazaka ganeba”.
Murmushi yayi, “Okay idan na dawo ai sai ki ganar dani, yanzu nidai nutsu na saki aiki”.
“Okay” ta faɗa kanta tsaye.
“Ki duba a study table ɗina, akwai wani file green a wajen ki ɗaukama Khaleel zai zo ya amsa yanzun”.
“Tom”.

Ta duba a kurkusa inda yace amma bataga file ɗin ba, sai dai kuma hankalinta ne kawai bai kaiba saboda ya dannesa da wani book. Ta shiga bin komai daki-daki da kallo tana ɗan ɗagawa harda buɗe drawers ɗin wajen. Saukar idonta akan wani ɗan akwati ya sata nutsuwa tana kallonsa, harta maida drawer ɗin ta rufe sai kuma ta sake buɗewa ta ciro akwatin. “Uhhm su Alhaji Yaya mm mi kuma ake ɓoyewa anan? Koma dai miye zuciyata na son gani”.
Tana ƙoƙarin buɗewa kira ya shigo wayarta, shine dan haka ta ɗaga. Kafinma yay magana tace “Yaya ban ganiba fa, inata nema kuma tun ɗazun”.
“Kamarya? Bayan nasan yana nan akusa-kusa. Ki ɗan ɗaga kayan wajen Khaleel na waje yana jiranki amfani zanyi da shi”.
“Oh sorry kamarma gashi anan ka ɗaura littafi akai”.
“Ok ki kai masa yana jiranki”.

Koda ta kaima Khaleel littafin sashen ta sake dawowa. Dan zuciyarta naga akwatin nan haka kawai batare data san dalili ba. Kiciniyar buɗewa ta shigayi, da ƙyar ta dace ya buɗu bayan ta haɗa da ƴan dabaru. Da littafi ta fara cin karo, ta ɗan jujjuyashi tana taɓe baki ta ajiye. Sai envelope brown babba. buɗeta tai ta zaro albom na hotuna mai tudu sosai sai dai bai cika girma ba a tsaho. “Hotunan sirri ne kenan su Yaya aka ɓoy....” ta kasa ƙarasa abinda ta faro. Ko'a magagin barci aka tasheta babu gilashi a idonta aka nuna mata hoton babu gargada zata bada amsar itace. Hotone da taga irinsa yafi guda ashirin a gidansu. Hoton ne da aka ɗauketa a ranar haihuwarta tun a asibiti. Tana rungume a hanun Yaya Shareff Abie da aunty Mimi sun sakashi tsakkiya suna leƙenta a hannunsa ya babbake ya hanasu gani. Da sauri ta koma na ƙasa, shi kuma a ranar sunanta ne ita da shi, na gaba itace da shi da Mamie da Abie da aunty Mimi. Ta cigaba da buɗe albom ɗin mamaki fal ranta dan ta kasa fahimtar ma'anarsa. Hotuna na gaba sun kasance a gurare daban-daban. Wani wajen ita kaɗai, wani ita da shi, wani har da su Abie. Ranar birthday ɗinta na cika shekara ɗaya. “Ya ALLAH” ta faɗa tana cigaba da kallonsu daki-daki. Jikinta ya ɗan fara rawa ganin hotunan da har tana a shekarar shiga primary, secondray, kai har jami'a ma akwai, bayan zuwa lokacin Shareff baya tare da su. Duk wani hoton birthday ɗinta akwaisa, hakama hotunan bikin salla kona wani taron makaranta kona islamiyya duk akwai. Hoton ƙarshe da yay matuƙar bata mamaki shine na ranar ɗaurin aurensa da Fadwa, itama kuma ranar nata ɗaurin auren da bata sani ba. Rubutun da yay a jikin hoton ya matuƙar firgitata..........✍




_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*


YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:
07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇
09134848107


*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*
[11/15, 11:40 PM] My Zafafa: *_Typing📲_*




*_❤‍🔥BABU SO....!!❤‍🔥_*
_(Miya kawo kishi?)_



*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*

*_BABU SO👉🏻AREWABOOKS_*

https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718


*_65_*



........ *_Cikar burina shine ganin irin wannan ranar tare da ke gimbiyar mata, kece sirrin ruhuna, nima inajin raɗaɗi fiye da wanda na gani a cikin ƙwayar idanunki. I'm sorry! ranarki tana zuwa_*.
Ta haɗiye yawu da ƙyar, da sake maimata karatun kamar mai bita, dan yayisa ne da yaren maley ta tabbatar batayi kuskuren karantawa ba. Zaune takai dan ƙafarta ta kasa ɗaukarta. Ta cigaba da zaro sauran abinda ke cikin akwatin. Akwai kashi-kashi na ribbons ɗinta, ta gane hakanne saboda matuƙar son da takema wasu, wasu kuwa ta gansu a hotunanta dake cikin albom ɗin can tun tana yarinya. Sai wani ɗan abunta mai kamar kwalba cikinsa da taurari da wata suna yawo, a tsakiyarsu da alkur'ani a buɗe, idan bata manta ba Mamie ce ta bata shi as gift ɗin kammala haddar alkur'anin ta, amma saita nemesa ta rasa a daga baya duk da kuwa a side drawer na gadonta yake. Har kuka tayi na rashinsa, kai tsaye kuma ta zargi mai aikinsu ce ta fasa amma ta ɓoye. Mamie ce ta kashe wutar a lokacin ta sake saya mata wani sai dai yasha banban da wannan ɗin dan haka taita mitar batason sa har sai da Abie ya shiga zancen ya lallasheta. Ashe Yaya MM ne ya sacesa. Ta cigaba da kallon abubuwa da dama nata, kuma masu muhimmanci a gareta data nemesu ta rasa a lokuta mabanbanta, wanda a iya tunaninta ta rasa mai ɗaukar mata su, duk da har su Amrah yaran aunty mimi tasha zarga. Book ɗin ta ɗauka saboda ji a ranta shima ya shafeta. A shafin farko sunanta ne da rubutu kamar haka.
*_Juwairiyya Anaam! kece matar aurena kuma uwar ƴaƴana da izinin UBANGIJINA. Ni kaɗai aka haifawa ke, zan kuma rayune domin ke insha ALLAHU._*
Ta buɗe shafi na biyu zuciyarta na tsitstsinkewa. _Da ace wani bawa nada damar tsara labarin rayuwarsa da wanzuwarsa, zan tsara nawane kawai domin ke kaɗai a wannan duniyar. Ina roƙon UBANGIJI ke ɗin karki zama a cikin ƙaddarar abinda ALLAH bazai mallakamin ba, zuciyata bazata iya ɗauka ba, ya rabbi ka zama gatana akowane hali_.
Haka ta cigaba da karanta abubuwa daban-daban akan rayuwarta da tasa daya dinga rubutawa tamkar labarin littafi. Mafi ƙololuwar ruɗa tunaninta da saukar da hawayenta shine a gaɓar da Mommy ta takura masa auren watanta. Duk wani tashin hankalinsa ya zanashi da fargabar karta suɓuce masa. Zuwanta Nigeria da sunan hidimar ƙasa mafi girman sassauci dajin ƙwarin gwiwar yin biyayya da cusa son Fadwa a ransa matsayin sadaukarwa ko UBANGIJI zai masa tukuyci da samun Anaam. Kukanta ya ƙara ƙarfi jin cewar ya kwanta jiyyane akan jin za'a aurama waninsa ita ba shi ba, harda barazanar kamuwa da ciwon hawan jini daya nema shafar lafiyarsa. “Innalillahi...” ta shiga ambata da kifewa jikin desk ɗin nasa ta shiga raira kuka, wani al'amari mai girma na ratsa dukkan magudana da jijiya ta jikinta. Sai da tai kuka sosai harta gode ALLAH kafin ta ƙarasa ganin wasu zane-zane da yayi wanda duk fuskartace ya zana, kai kace tana tsayene a gabansa yay zanen. Da kyar ta miƙe ta tattare komai ta maida masa yanda yake ta maida a drawer ɗin sannan ta fice jikinta a saɓule.

Aysha dake zaune a falo tana aikin nata na tiktok data koya gun Fadwa ta bita da kallo. Ganin zata wuce bedroom batare data tanka mata ba ta riƙo hanunta da sauri. Juyowa tai tana kallonta, hawaye masu ɗumi na sauka mata a kumatu, sai kuma ta rungume Ayshan tana saki wani marayan kuka da ita kanta bata gama tantance na minene ba.
Hankalin Aysha ya ƙara tashi, ta ɗagota da sauri. “Ya ALLAH blood wai miya farune? Yaya ne ya miki wani abu?”.
Kanta ta girgiza mata.
“To minene? Ko dai maganar aurence dai har yanzu? Da zaman wannan gidan?. Dan ALLAH ki kwantar da hankalinki Anaam. Ki saurareni a wannan gaɓar na buɗe miki kanki ta yanda wlhy sai Yaya Shareff ya dawo tafin hanunki ta hanyar soyayya da bin dokokin ALLAH. Na fahimci rashin sanin minene kishi da rayuwar gidan malam bahaushe ke sakaki tafiya a haguggunce a wannan gidan har Fadwa ke jan akalarki da makirci. Ki nutsu ki saurareni Please”.
Bataƙi ta Ayshan ba, suka koma suka zauna cikin hikima da basirar da ALLAH ya bama Aysha. Da kasancewar ta tashi a rayuwane ta cikin gidan yawa dama salon kishin Mommy da Aunty Amarya. Ga karance-karancen littatafan nan na hausa duk tana taɓawa ta shiga warware mata abubuwa masu yawan gaske. Anaam irin mutanen nanne masu saurin haddace abu idan an faɗa musu, musamman akan abinda ke wahalar da su, ko wani abu da basa ƙaunar a kaisu ƙasa. Hakan ya bata matuƙar gudunmawa wajen fahimtar Aysha daki-daki babu kuskure. Sosai taji daɗin bayanin dan haka ta rungume Ayshan.
“Na gode blood, nagode, irin godiyar da babu alƙalamin dazai iya rubutawa. Sai dai ki sani duk abinda kikaga inayi a gidan nan kamar mara wayo ba rashin wayo bane sarai ina lure da komai da binsa daki-daki, sannan akan sani nake aikatawa saboda wasu dalilai nawa. Idan banyi hakaba shi kansa bazan gama fahimtar halayyarsaba balle ita. Tabbas nasan bazan taɓa iya kaiku wayon zama a irin rayuwar da kuka tashi ba, sai dai koba komai ina shigowa cikinku nima ina ganin wasu abubuwan. Daliline ya sakani zaɓar yin duk abinda nakeyi. Sai dai a yanzu kalar rubutun zai sha banban da kalar takardar. A yanzu lokacina ne, kisa a ranki lokacin Juwairiyya Usman MD Shareff zai fara a gidan Al-Mustapha Muhammad MD Shareff. Nayi alƙawarin bazanyi abinda zai cutar da kowa ba, sai dai zan nunama kowa kowacce mace da ilimin zaman gidan aure UBANGIJI ya halicceta, kuma ko wacece ita ko'a ina ta tashi zata rayuwu, ta kuma riƙe kambunta na ɗiya mace. A kwanakin da nayi biyar a gidan nan, na karanci abubuwa masu dama a cikinsu, zan kuma fara sharar fadata da su domin samun damar shimfiɗa mulkina batare da wani datti ya sha gaban cikar burina ba”.
“Woow vary interesting my blood. Haka nake sonki dan ALLAH. Ki haukata mana Yaya Shareff, ki kuma dawo mana da Fadwa hanya tabar bin karatun su Mommy, ta zama mai ra'ayin kanta”.
Anaam ta ƙyalƙyale da dariya, zuciyarta fes tamkar an sauke mata dukkan wani nauyi da ƙuncin da takeji a yau a yanzu yanzu. Basai amfaɗa ba, da ni da mai karatu duk zamu fahimci hakan nada nasaba da abinda taci karo da shi wannda a baya bashi take kallo a fuskar Shareff ba. Sun ƙara tattaunawa sosai akan wasu abubuwan da dama da Aysha kafin ta miƙe ta koma sashen Shareff domin gyarawa bisa shawarar Aysha.
Bata jin daɗin jikinta saboda ɗinkin da akai mata na sakata jinta tamkar a takure, ga tafiyarta har yanzu bai zama normal ba kamar da. Amma haka ta jure a daddafe na rashin sabon da wahala ta gyara ko'ina na sashen nasa, sauƙin ma babu datti mai yawa. Sai da ta tabbatar ko'ina ya mata da kamshi sannan ta rufe ta fito. Baki ta saki tana kallon yanda Aysha ta ƙara gyara sashenta itama. Ta saki murmushi da harar Ayshan dake tsaye tana karanta mata taje tayi wanka ta ɗauki ado dan Yaya Shareff na gab da dawowa. Akwai tsoro tattare da ita na abunda ya faru, amma gargaɗin likita akan Shareff ya bata ƙwarin gwiwar tabbatarma kanta babu wani abu tunda ko dai baya cikin hayyacinsa ai baya nema wani abu daga garetaba zaren ɗinki na a jikinta. Da wannan tunanin ta faɗa wanka. Koda ta fito tsareta Aysha tai wai sai ta mata kwalliya. Badan taso ba dole ta tsaya kuwa Aysha ta zaneta tsaf dasu jaja leɓe da barbaɗa kumatu na zamani. Turare kuwa har ji take yana hawa mata kai dan khumras nata sun sami haɗine na musamman daga hajiyar sudan, ga kuma *_YERWA INCENSE AND MORE +234 809 521 5215 da miss xoxo tayo mata haɗi da sai ƴar gata ke samunsa😋_*. Hakama na kanti duk masu tsadane da ƙamshi na musamman da aka zuba a lefe. Ƙanan kayan nata taso sakawa, sai dai Aysha ta hanata hakan, acewarta kayanmu na gida sunfi mata ƙyau. Dole badan taso ba ta haƙura ta shirya cikin skirt da riga na lass daya zauna mata a jiki tamkar ka saceta ka gudu. Aysha tai mata ɗauri na zamani daya saka ita kanta kasa rufe baki sai faman kallon kanta takeyi a mirror da ƙyalla hotuna da wayarta.....

A gajiye ya iso gidan bayan idar da sallar isha'i. Ya fiddo ledojin daya shigo da su na fruits kashi biyu. Sashen Fadwa ya nufa, ya sameta zaune a falo ƙafa ɗaya kan ɗaya tanata cika da batsewa. Kallo ɗaya yay mata ya ɗauke kansa dan ko sallamarsa bata amsa ba. Ledar ya ajiye batare daya ce ko a ba yay ficewarsa yana ƙwafa. Dan a yanda ta masa ya bashi tabbacin tana kan sani taƙi ɗauka masa wayarsa. Sashen Anaam ya nufa da ɗayar ledar yanata faman furzar da hucin ɓacin rai......✍


_🤪🤪Shike nan an shiga tsakaninmu da Soulmate 🙆🏻, dolene mu koma gidan.... Basai na faɗa ba😭_.
         



_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*


YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:
07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇
09134848107


*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*

[11/23, 10:16 PM] My Zafafa: *_Typing📲_*




*_❤‍🔥BABU SO....!!❤‍🔥_*
_(Miya kawo kishi?)_



*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*

*_BABU SO👉🏻AREWABOOKS_*

https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718


*_66_*



.........Fitowarsu falon kenan suma babu jimawa, Anaam dafe da kanta dake mata ciwo saboda kukan da tasha ɗazun, ga jikinta har yanzu sam baya mata daɗi irin na shiga sabuwar rayuwar da ba'a saba ba. Aysha ce ta amsa masa sallamarsa, ya ƙaraso ciki idonsa akan Anaam. Ya miƙama Aysha dake masa sannu ledar hanunsa.
     “Ita wannan lafiya kuwa?”.
“Kanta ne ke mata ciwo, nayi-nayi tasha magani kuma taƙi”. Zaune yakai kusa da ita, ya janye hanunta dake dafe da kanta. Kasa kallonsa tai, dan haka kawai take jin wani irin matsanancin kunyarsa. Shiko ya matuƙar shagala ne a kallon kwalliyar dake zane akan fuskarta, a kasalance yakai hannunsa kan haɓarta ya ɗago fuskar da ƙyau, hakan sai ya tilasta mata ɗago nata idanun dake cike da ƙwalla ta kallesa. Ba ƙaramin jarumta yay wajen jawo numfashinsa dake neman kufcema ƙirjinsa ba, ya matsota jikinsa tare da ɗaura hanunsa saman goshin nata.
      “Wannan idon naki kinyi kuka da shi, ko muje asibiti ne?”.
Ya faɗa a hankali cikin kunenta. Kanta ta girgiza masa da ƙara lafewa a jikin nasa har hakan ya so bashi mamaki. Dan yasan dai koshi ya ringumeta turesa take kota janye jikinta, amma yanzu ga saɓanin hakan yana gani, koda yake tunda abin nan ya faru ya fahimci ta zama wata shiru-shiru, tsiwar taɗan ragu kaɗan ko likimo ne, mata sunji maza kenan. Fitowar Aysha ta sakata janye jikinta, shima sai ya miƙe yana faɗin, “Bara na watsa ruwa sai a samo miki magani”.
   Baki ta ɗan tura masa da kaiwa kwance. “Ni basai nasha magani ba fa”.
       Juyowa yay daga niyyar barin falon da yayi, “Oh tunda hakane tashi na fasa barinki anan ɗin”.
  Dole badan taso ba ta miƙe, dan ya tsuke fuska babu alamar wasa, duk da dama dai tunda ya shigo babu fara'ar tattare da shi. Aysha da tuni ta koma kitchen yay kira. Fitowa tai da sauri tana amsawa.
     “Gyaramin fruits ɗin nan”.
“To Yaya. Ko'a haɗa salad?”.
“Duk yanda kikai is ok”.
Kanta ta gyaɗa masa, shi kuma ya kama hanun Anaam suka fice. Ta bisu da kallo murmushi bayyane akan fuskarta. Tana fatan ALLAH ya hana su Mommy raba wannan auren har abada. Dan sun kasance abin birgewa best couple ever matuƙa”.
       Koda suka iso sashen nasa a falon ya zauna, ya riƙota saman cinyarsa ya zaunar. Yanzun ma cikin mamaki yaga ta lafe a jikinsa. Ya ɗan murmusa da shafar fuskarta idonunsa na bin fuskarta dake ƙwaɓe alamar rashin jin daɗi da kallo.
    “Kodai har yanzu garden ɗin na zafinne? Noorie!?”.
   Kanta ta sinne a ƙirjinsa da riƙo hanunsa dake kaiwa jikinta, dan zuwa yanzu ta fahimci mi yake kira garden ɗin. “Yaya Please ka daina”.
        “No Aunty babu wannan zancen”.
Ya faɗa cikin kwaikwayon muryarta. Murmushi ya kufce mata tare da ƙara cusa kan nata cikin jikinsa. Dan yanda yay maganar ya matuƙar bata dariya. Shima murmushi yay da kaima wuyanta kisses. Tsoro ne ya kamata, tai ƙoƙarin jan jikinta baya amma ya hana hakan.
    “Wayyo kaina zai fashe Yaya”.
Dakatawa yay daga ƙoƙarin cusa hanunsa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login