Showing 174001 words to 177000 words out of 178785 words

Chapter 59 - Babu So Complete Hausa Novel

05 Feb 2025

32839

Anaam ɗin ta gaji sai hakan yay mata dai-dai. Fadwa ta tsira musu ido hawaye na silalo mata a kumatu, ji take inama Muhseenah tata ce. Hankalinta bai sake tashi ba sai da Shareff ya iso wajen. Yayi wani fresh da shi ga ƙiba da zama alhajin gaske da yayi, sai ƙyalli yake cikin shadda irin ta jikin Anaam ɗin. ko kunya bai jiba ya ƙarasa inda matarsa da ƴarsa suke. Duƙowa yay jikinta yana mai yima Muhseenah wasa tana ɓangale masa baki da miƙa hannu ita a dole ta gane Abbanta.
     Anaam ta kallesa da murmushi. “ALLAH Yaya kai ne ka koyama yarinyarnan ƙiywa ba wani ba. Ita a dole duk inda ta ganka saita ganeka”.
      “Toya son ranki? Jealousy woman”.
Ya faɗa yana mai kashe mata ido ɗaya. Murmushi tai baki a taɓe. “Fess mana, miye abin jealous anan nima nawa na zuwa zan rama”. Shima murmushi yay idonsa akan lipstick ɗin bakinta. Sarai ta ganosa, dan haka ta tura lips ɗin a baki ta shanye tas. Kafin fitowar nan tasu ta saka yafi sau biyar yana tsotsesa, yanzu ma anan gidan ta saka.
    “Kije ke da ALLAH kuma zan rama”.
Ya faɗa cikin langaɓe mata kai. Dariya take gimtsewa ita dai, ya ɗauke Muhseenah suka bar wajen. Da kallo ta bisu cike da so da ƙaunar ƴar da uban.

       Bayan kammala halartar kowa aka buɗe taro da addu'a. Abbah ya fara da nasiha mai ratsa jiki game da muhimmancin da zuminci keda shi a rayuwarmu, tare da son zuciya akan abinda kai baka isa sakawa ko hanawa ba a ƙaddarar waninka ko kai a karan kanka. Ya ɗora da roƙo da fatan su zama 1family, tsintaiya ɗaya maɗauri ɗaya. Tare da illar nunama juna wani abu wai shi ƴan ubanci. Ƴan ubancin nan babu abinda yake zama a family sai kassara rayuka da maidasu koma baya. Duk family ɗin da babu haɗin kai bazasu taɓa zama masu cigaba ba, dan kuwa zasuyita gabane suna taɗo juna akan ƙanƙanin abu. Sannan iyaye mata na Family ɗin su kiyayi kansu wajen tsaurara ƙiyayya tsakaninsu da ƴan uwansu har ƴaƴansu su fahimta hakan kuskure ne. Kowa yay haƙuri da ɗan uwansa yayin daya ɓata masa rai, dan mai haƙuri baya taɓa faɗuwa sai cin nasara a rayuwa. Su Abie sun isa zama manuniya a garesu. Sosai nasihar ta shigi kowa. Sai faman sauke ajiyar zuciyoyi akeyi musamman Gwaggo Halima. Bayan gama jawabin Abba Abie shima ya amsa. Ya ƙara da musu tashi mai ratsa jiki, tare da shawarar sakama yaranmu ido domin sanin abinda suke aikatawa a wayoyinsu. Dan sakacin rashin bibiyar shike saka yaran ɗoruwa a hanya irin wadda Fadwa tabi a baya. A yanzu tangal-tangal din tarbiyyar yaranmu ta riga ta koma ne a tsinin ƙaddarar yanar gizo da wayoyin hanu suka kawo mana, kenan ya dace iyaye su sakama wayoyin hannun ƴaƴansu ido, karkuma suce bazasu basuba dan in kin hanasu zasuje suga ta ƙawaye ko aboki ko saurayi, baki san kuma minene a ciki ba. Sannan tarbiyya babu ruwanta da inda ka taso, a duk duniyar da kake, a kuma kowacce ƙasa idan kaso ɗanka ya zama na ƙwarai zai zama. Bawai dole sai ya shiryuba, a'a ALLAH ne kaɗai mai shiryarwa, suma waɗanda nasu ƴaƴan suka kauce ba'a son ransu bane, karka ga gazawarsu koka aibanta waɗan nan yaran, akwai ƙaddara amma wasu lokutan akwai sakaci sosai na iyaye. Karka matsawa ɗanka, kar kuma ka sakesa da yawa. Dan matsi na saka lalacewa tunda zai koma a tafin hanun neman sharar ƙawaye ko abokai ne, sannan saki gaba ɗaya ma kuskurene, zai koma a tafin hanunun tarbiyyar ƙawaye ko abokai. A wannan zamanin iyaye sun kashi kaso uku ne zuwa huɗu koma nace biyar ko fiye da haka, masu raunin talauci da komai yaron yayi dan an sakar masa komai ne. (Kamar dai su Sima da Amaal) kaso na biyu rashin wayewar kan sanin mi yaran ke aikatawa ma ko ilimin sanin illar wayoyin ko yanar gizo. Kaso na uku ƴan boko wayayyu da komai akai su a wajensu ba komai bane zamanine. Kaso na huɗu masu tsananin tsaurarawa har ƴayan suna fakar ido suna aikata abinda sukema tsaurin. Kaso na biyar ƴan fifita aiki ko kasuwanci fiye da saka ido akan al'amuran ƴaƴansu komai na hanun ƴan aiki kosu yaran a karan kansu. Iyaye mata suna ƙoƙari matuƙa, duk da a wani ɓangaren akwai sakacinsu, sai dai kuma laifin iyaye maza yafi rinjaye. Da yawa ƴaƴa suna matuƙar shakkar iyayensu maza fiye da matan, sannan a wani fanin iyaye mata nada rauni akan ƴaƴa, dan haka idan kana son ingantuwar tarbiyyar ɗanka yanda ya kamata dolene a matsayinka na uba kaima ka tsaya tsayin daka wajen taimakawa uwa mace ku gyara kuma ku tsawatar, sannan ku haɗa da addu'a. A wani fanin Gwaggo halima tayi matuƙar ƙoƙari wajen tarbiyyar su Fadwa, domin kuwa bata barsu kara zube ba akan wasu fanonin, hakan zaisa mai karatu ya fahimci itafa uwa uwace koyaya take tana buƙatar ganin ɗanta a ƙyaƙyƙyawar nasara bawai faɗuwa ba. Su Fadwa na tsoron mahaifinsu, amma maida hankalinsa a kan hidimarsa da siyasarsa yasa bai maida hankali wajen sanin dukkan motsinsu ba, shi dai kawai idan ya samo ya basu sunci sun sha sun samu komai basu da matsala ya gama nashi. Ba mahaifin Fadwa kawai bane a irin wannan halin, mazanmu na yanzu musamman yarena hausa dana sani wannan shine babban rauninsu akan ƴaƴansu gaskiya. Namiji ya fita tun safe sai dare ko yamma zai dawo miki, komai ya sakar miki akan tarbiyyar yara, masu ƙoƙarin ciki sune ke ɗan zama da yaran weekend, wanima da sun raɓesa zai korasu shi an takura masa yana son ya huta, ko wani ya ɓato masa rai a waje ya shigo gidan yayta tambotsai. Komai sai uwa dai, tayaya uwa zata iya da komai? musamman akan yaran yanzu da sai dai addu'a. Abu mafi girma shine maida nauyin gidajenmu a hanun ƴaƴanmu musamman ga iyayenmu talakawa. Taya zakice yarinya budurwa baliga ko bazawara itace zata nema kuɗi ta ɗauka nauyin rayuwar gida? Ko namijine a wannan zamanin dole ka kasance cikin taka tsantsan balle mace, anji neman nakai nada daɗi, amma komi ƴarka zatai tayi a gaban idonka, bisa control naka kona yayunta domin ceto rayuwarta daga faɗawa wata ƙazamar rayuwa. Tabbas wasu iyayen basu san ƴaƴansu na abubuwan nan a media ba, saboda su basu da wayewar kan sanin mima wayoyin suka ƙunsa ko yanar gizo, wasu kuma masu wayewar hakan basu cika zama masu bin ƙwaƙwƙwafin yaran nasu ba. A ganina hakan duk kuskure ne, akwai abinda baida ƙyau ka cika masa bin ƙwaƙwƙwafi kam, akwai kuma wanda saida bin ƙwaƙwƙwafin komai zai tafi dai-dai. Karmu hana yaranmu wayoyi, kar kuma mu barsu da su su zame musu komai. Idan baku da wayewar kai akan waya samu wasu da zasu dinga bibiyar yarinyarki a kowane shafi nata/nashi suna kawo miki rahoto, idan kunada ilimin bibiya a kowanne dare wayar yaranki musamman mata ko matasan samari masu tasowa dan nasan na manyan gwasaken zaiyi wuya ta kwana a hanunki, dan dare shine mafi girman fili dake basu damar aikata komai a yanar gizo. Sannan ki dage da addu'a da yawaita nasiha mai tsoratarwa ga yaran akan irin waɗan nan abubuwan. Mu kammu iyaye mata da muke shiga a irin waɗan nan abubuwan dan ALLAH muyima kammu faɗa mana, kina tunanin zakiyi ƴaƴanki su kasa koyi dake? Shifa hali naso yakeyi, Fadwa ta fara tiktok tun bata da aure, amma saboda ya zame mata jiki har taje gidan aure tanayi a duk yanda taso. Wlhy wlhy maza da yawa na faɗawa a tarkon sha'awa a kalle-kallen videos na yanar gizo da mata ke yaɗawa a duk shigar da suka gadama. Karku manta wanifa abu kaɗan ke tada masa hankali, shiyyasa zinace-zinace sukai yawa yanzu muka rasa gane daga inane, ada yarinya saita ɓalle daga gida ta shiga duniya ake kiranta karuwa, wlhy yanzu a gabanki za'a maida miki yarinya karuwa ko matarka ko ƙanwarka ko yayarka😭, dan wasu matan a dalilin abinda sukeyi wasu mazan ke hillatarsu harsu bata musu rayuwa. Duk yanda mace take tana son a yaba mata, shiyyasa maza mayaudara ke saurin samun galaba akan ɗiya mace saboda su duk hanyar yabo da gwarzantawa sukebi, suna kuma samun abinda suke so su watsar dake su koma gefe suna zagin iyayenki dake kanki matsayin mara tarbiyya. To hakane ke faruwa a duniyar tiktok dama sauran kafafen sada zumunta, waɗan nan masu zugaki a Comments kin haɗu, kin isa, kin kai, wlhy ba ƙaunarki suke ba, dan daza'ace ɗaya daga ciki ya fito ya aureki sai kin nemesu kin rasa sun gudu. Maza dake kawo matansu ana video su wai soyayya ban taɓa ganin waɗanda basu san ciwon kansuba irinsu wlhy, matarka ta aure sirrinka itace kuma abin ado a shafin sada zumunta?, anya wannan soyayya ce kuwa ta gaskiya? Muji tsoron ALLAH, mu dunga tunawa da mutuwa, mu dinga tunawa akwai kwanciyar kabari, akwai hisabi, dubinki sunyi amma basuci ribaba, tayaya ke kike tunanin zaki ribantu?, bazaku gane illar abinda kukeyiba sai kinje gidan aure namiji na miki kallon zargi ko yana bin irin hanyar daya ganoki wajen gani wasu matan duk da yana dake a gidansa. Ki dauka abu mai amfani ki yaɗa sai kici riba, amma mummuna zakiyi bayani idan baki tubaba. Dan Fadwa a novel ta fito shiyyasa wani a cikin hukuncunta yazo a bayyane, amma ke a zahiri kike ALLAH shine zai hukuntaki idan baki tuba kin koma garesaba, ba kuma kisan ta hanyar dazai hukuntakin ba ma. ALLAH ka shiryemu badan halinmu ba.😭🙏🏻

Shima Daddy koda ya amsa maganar dai ɗaya ce akan zuminci da tarbiyyar ƴaƴanmu. Mu daina sakarma abokai ko ƙawaye ƴaƴayenmu hakan kuskurene. Dan zai zama kina tufƙa wasu na warware miki, yanzu lalacewa basai a zahirin rayuwa ba. Daga budurwa har bazawara da saurayi ko magidanci ko matar aure inhar suna biyema ƙawaye ko abokai zama samu rayuwarsa tana tangal-tangal, dan zai koma ne baida ra'ayin kansa sai nasu, hakan kuma babban kuskure ne.........✍



_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*


YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:
07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇
09134848107


*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*
[11/25, 12:22 PM] My Zafafa: *_Typing📲_*




*_❤‍🔥BABU SO....!!❤‍🔥_*
_(Miya kawo kishi?)_



*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*

*_BABU SO👉🏻AREWABOOKS_*

https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718


*_83 End_*




.........Matsalar ba'a raye-raye bane kawai ko abinda bai dace ba ko mara amfani. Akwai canja abokai, dan dole ne yay abokai a wannan yanar gizon, tun ana ƴar nesa da juna har a kai ga haɗuwa, bai san tarbiyyar waɗan can ba ko inda suka fito, sai kiga an koya masa sabuwar ɗabi'ar da baki san yaronki ko yarinya da shi ba. Shaye-shaye ne, maɗigo ne, luwaɗi ne, fashi ne, sata ne, yahoo ne, kai da ire-irensu daban-daban. Wlhy ko a film naga yarinya na shan shisha inajin zafi a zuciyata, dan wata daga wannan abinda ake ɗauka faɗakarwar zataji daɗi ta cigaba, saboda mu a namu wautan ɗaukar shisha muke ba shaye-shaye ba ma. Daga faɗakarwa an koma feɗe tarbiya, an gyara goma biyar bata gyaru ba. Kullum ƴarki abokai da ƙawaye na janta/jansa bin joint-joint, inda anan zata haɗu da wasu masu buɗaɗɗen idon da yafi nata kuma ko yafi nasa. Ya ALLAH, iyaye dan ALLAH mu dake da addu'a. Sannan muma a karan kammu mu gyara halayen da muka san munayi marasa ƙyau. Dan ba media bace bala'i kawai muma a karan kammu bala'in kammu da kammu ne. ALLAH yasa mu dace.

       Ba Fadwa ba kowa ma a falon jikinsa yay sanyi matuƙa, hankalin iyaye da yawa da ba ɗaukar komai suke matsayin komaiba ya tashi matuƙa, dan kamar an farkar da su ne abinda suka kasa hangowa a tsayin hangensu. Fadwa kuka take matuƙa tana mai dana sani da nadama mara misali. Dan kuwa yanar gizo bata bata komai bai sai komawa baya da sakata a gurbin nadama saboda batabi hanyar da zata amfana da ita ba. Inama sauran wanda suke hali irin nata suma zasu farga da wuri kafin su rasa abinda ta rasa koma fiye da ita. Inama zata iya goge abinda ya wuce a zuciya da idanun mutane?. Sai dai kaico, duk da ta daina a yanzu ko waya bata riƙewa haka bai hana videos nata cigaba da yawo ba a media, saboda wasu sun adana a wayoyinsu, kuma suna cigaba da zama illa a garesu tunda suna koyi da su matsayin abin birgewa. Duk wanda ya koya daga gareta kuma ya lalace tanada kamasho na zunibi itama. Kenan ita baɗala koda kayita ka daina sharrinta na biye dakai har bayan ranka, wani lokacin ma har jikokin jikoki? Ya ALLAH ka ganar damu gaskiya tun kafin ta ƙuɓuce mana. Ka shiryar damu tun kafin guri ya ƙure mana, ka ƙuɓutar damu tun kafin ajali ya riskemu. Ka goge laifukamnu tun kafin ƴayanmu da jikoki su riskesu😭🙏🏻.

         Abie ne ya katse tunanin kowa cikin gyaran murya. Hakan yasa kowa maida hankali a garesa. “Babban abinda ya taramu anan shine sake bada haƙuri da roƙo ga iyayenmu, yayunmu, ƴaƴanmu, kuma ƴan uwanmu. Yaya Muhammad, Alhaji Sadiq, Babana Shareff. Musamman abinda ya faru ya rigada ya faru, kuma hukuncinku dai-dai ne dan duk ɗan halak idan an zunguresa ya dace ya nuna yaji zafi kuma ya ɗau mataki.  Sannan wanda yay laifi idan anga nadama a cikin idanunsa da ayyukansa ya kamata ai masa afuwa koda kuwa bazai samu girman daraja irin ta baya ba. Kamar yanda na roƙa a tun sanda kukai sakin nan kuka maidasu bada sanin kowa ba har su a karan kansu dan mu barsu su horu muga kuma idan zasu gane gaskiya, to Alhmdllh sun gane, a tsahon kusan shekara guda. Ina roƙon alfarmar ku maidasu ɗakunansu, ya rage nasu su riƙe igiya ɗaya data rage musu kosu barta itama ta katse a yanzu. Fatanmu zuminci ya cigaba da gyaruwa ba ɓaci ba, sannan dama shi mai laifi ana masa gargaɗi idan yaji to falillahil hamdu, idan ya nuna kunen ƙashi sai a barsa da halinsa ALLAH ya hukuntashi da ikonsa. Halima da Nafisa kunada sauran igiya ɗaya na aure kuma mun roƙa alfarma an maidaku tun kan ku kammala idda, amma bawai hakan na nufin ku cigaba da abinda ranku ke so ba a wannan family, dan a wannan gaɓar mun shirya ɗaukar mataki akan kowacce dazata zame mana iblis wlhy, babu kuma wani cikinmu dazai sake mata alfarma.”
     Sosai Mommy da Gwaggo Halima ke hawayen daɗi, har basu san sun fara zuba godiya da addu'a akan Abie ba. Yay murmushi kawai dan kuwa bai taɓa tunanin ganin irin wannan ranar ba. Hankalinsa ya maida ga Shareff dayay kicin-kicin da rai, sai dai wani sashe na ransa ya masa daɗin maida Mommy, ya kuma sake jin kima da mutuncin Abie a cikin idanunsa da ransa.....
    “Babana”.
Abie ya katse masa tunani.
Ɗagowa yay ya dubesa, sai dai baice komai ba. Abie ya murmusa ganin yanda ya tsuke fuska. “Nasan a gareka abune mai matuƙar wahala iya manta komai, shiyyasa ko a wancan karon ban tunkareka ka maida Fadwa ba, na barka ka huce sosai da sosai kafin muzo a wannan gaɓar. Babu mai tilasta maka a cikinmu, amma zamu roƙeka alfarma. Dan ALLAH ka maida matarka tunda tayi nadama.....”
     Kansa ya shiga girgizawa a hankali. “Abie batai nadama ba, tana muku lumbu-lumbu ne kawai. Koda zan iya maidata domin darajarku bazan taɓa sake sonta ba, bazan taɓa ganinta da mutunci ba, bazan taɓa iya sauke dukkan hakkinta ba. Har yanzu ina ganinta a idona mai ɓakar zuciya, mai mummunan hali, mai karancin tarbiyya, ballagaza da bata san kima da mutuncin kanta ba, Abie mazafa kallonta sukeyi sunaji wani abu a ransu, shin yara matasa nawane da magidanta sukaji hakan? Mutane nawane suka kalleta a hakan? Ta daina amma har yanzu abinda ta shuka na yawo a wayoyin mutane? Bazan iyaba Abie, wlhy ko tunata bana sonyi, bana son ganinta sam......”
     “Karka tsaurara da ƙarfi babana. Nasan akwai ciwo, akwai ɗaci, akwai raɗaɗi. Sai dai muɗin ba masu shiryarwa bane ba. Sannan samun miji na gari na ƙwarai a gareta a yanzu abune mai wahala, duk da nasan wasu zasu iya amfani da nasibin da ALLAH ya bama mahaifinta na suna da dukiya suce zasu aureta, tunda wasu a gurunsu abinda ta aikata ba komai bane a wautarsu, sai dai bai zama lallai su zama na ƙwarai ba......”
     Fadwa dake kuka ta ƙatse Abie ta hanyar rarrafowa gabansa. “Wlhy Abie bazan iya zama da wani namijiba inba shiba. Ina sonsa, kuma ni kaina ina kaico wa rayuwata ta baya. Na ɗauka abinda nake ba komaiba sai nishaɗi kawai, na ɗaukesa matsayin zamanine kawai, na ɗaukesa matsayin lokacina ne kawai. Wasu tsurarun mutane da bazasu amfaneni da komai a duniya da lahiraba kwarzantawarsu a gareni na ingizani inajin babu yani. A tunani na abinda nake ba komai bane tunda ba'a zahiri baneba. Ashe mummunar rayuwace mai wargaza ƙyawawan ayyuka. Ashe ƙofofin matakin zuwa ga zina ce, ashe raguwar darajace a gareni matsayin ɗiya mace, ashe tanadin abin faɗa ne ga ƴaƴana ga ƴan uwana. Ashe makullun rusa dukkan farin cikina ne da rayuwar aurena. Ashe ƙanƙantar da kaina nake tamkar dabbar da bata san inane rufe ko buɗe ba. Kaico na da wannan rayuwa, kaicon duk wata mace mara kamun kai da fahimtar rashin daidai matsayin nishaɗi ko birgewa. Kaicon mace irina dake nuna rashin ingancin tarbiyya da mutuncin iyayenta wa duniya. Nima bazan matsa maka ka maidaniba, amma bazan daina son ka ba, zan mutune da sonka Soulmate, zan amshi wannan hukuncin domin nasan UBANGIJI ne yake horani ta hanyar aza sonka a raina fiye da komai. Na godema ALLAH daya saka maka da mace tagari

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login