Showing 147001 words to 150000 words out of 178785 words

Chapter 50 - Babu So Complete Hausa Novel

05 Feb 2025

32826

muyi duk yanda ya dace domin ta dawo hayyacinta. Yaya baya son yanke hukunci cikin fushi, amma tunda kikaga yau yakai da marinta to idan takaisa maƙura komai zai iya lalacewa”.
(Aysha kenan, dan ma bakisan akan sani ta zubar da ciki ba akan makircin kakarku) Anaam ta faɗa a zuciya, a fili kam saita kai zaune tana mai dafe kanta.....

A ɓangaren Fadwa kam Mommy na yanke waya kiran Gwaggo Halima na shigo mata. Sabon kuka ta ɓarke da shi tana zayyana mata abinda ya faru, harda kiran Mommy datai amma ta yanke mata waya...
“Kan ubancan, mi Nafi ke nufi Shareff ya mareki ya mari banza?. A to lallai idan tace wannan layin zamubi ni da ita bazatai mana ƙyau ba. Ai dama su Malika sun tabbatar min abinda yafi hakama zai iya faruwa saboda Nafi maciji ce da fuskar tana. Aiko zan tabbatar mata Shareff bai mareki a banzaba dan wlhy saina rama miki”. Ta yanke wayar.

★Sai da Gwaggo ta gama sauraren Mommy data isa sashenta a rikice tsaf sannan ta saki murmushi irin nasu na tsoffin makirai. Domin kuwa anzo gaɓar da ta jima tana jira kenan. Kallon Mommy tai da dafa kafaɗarta. “Nafisa Halima zata iya fiye da haka domin wannan ƴar tata. Jikina ya fara sanyi da al'amarinta tun lokacin zubewar cikin Fadwa. Karki manta itace ta fara kawo shawarar a sami malamin dazai aiki akan Mustapha da yarinyarnan ta wajen Usman. Abinda yasa naƙi yarda a lokacin na tabbatar idan muka biye mata wataran zata haɗo wani abin a bama Shareff yaci a zuwan dan ana son rabashi da Zuwaira ne. Ki tuna Halima ƙudace, domin samun biyan bukatarta rai ba'a bakin komai yake ba. Tunda kuma ta haɗa kai dasu Malika to komai zai iya faruwa da Mustapha ciki harda rabashi da ke kanki uwarsa, dan kuwa ke shaidace, nice na haɗa auren Halima da Sadiqu, amma gashi nan babu mai cin dukiyarsa daga ita sai ƴaƴanta sai wanda ta zaɓa a dangi. Gasu Muhammadu nan ƴan uwanta tasan yanda zata samesu gefe ta kalallame ta dawo wajenmu tana nuna mana tana tare damu. Kin dai san duk son da Halima zatamana bai kai ya na ƴan uwanta ba tunda ba haihuwarsu nayi ba. Kuma kodan wannan dukiyar dake zagaye da Mustapha ai Halima bataso zaunawa ba tunda tasan yanda ta mallake Sadiqu dolene itama ƴarta ta mallaki Mustapha yanda koke kanki bai isa yaji maganarki ba, danni tawa mai sauƙice kwana nawa ya rage ALLAH na tuba”.
Kalaman Gwaggo ba karamin hautsuna zuciyar Mommy sukai ba. Gaba ɗaya tama rasa ina zata kama ta riƙe a wannan gaɓar. Shigowar kiran Gwaggo Halima ya saka tunaninta katsewa. Ta dubi Gwaggo, “Itace fa take kirana”.
“Ɗaga muji mizata faɗa, nasan dai ƴar tata ta kirata itama ai”.
Dagawa Mommy tayi, ta saka hansfree yanda itama Gwaggo zata iya ji. Daga can Gwaggo Halima dake a wuya muryarta a shaƙe ta fara magana batare da ko gaisuwa ba. “Yanzu Fadwa ke kirana Shareff ya mareta, tace kuma ta kiraki ta sanar miki amma bakice komaiba kin yanke waya. Kome hakan ke nufi kenan?”.
A harzuke Mommy ta maida mata murtani. “Abinda duk zuciyarki ta baki Halima. Nifa bazan ɓoye miki ba na gaji da yawan kai ƙarar Fadwa. Ita kullum bazata iya haƙuri da miji ba saita kawo kararsa. Ko haka taga wani a cikinmu nayi? Sannan kin tambayetama mita masan ya mareta? Taya zata kai masa ƙawaye ɗakinsa na sirri su gyara saboda rashin sanin ciwon kai. Ni yamun dai-dai, kinga gobe idan ta sake saiya mata dukan tsiyama ba mari ba. Sannan Halima ki sani, dukkan ƙulle-ƙullen da kukeyi ke da su Malika naji kuma na sani......”
“To idan kinji kin sani ɗin sai yaya Nafi? Kin goya bayan ɗanki akan marin da yay yarinyata ma, to wlhy ki sani da hannuna zan rama mata marin da yay mata, idan shi ɗin mahaukacine zan maidosa hankalinsa kuwa. Kuma karki manta duk wani ƙulli da tuggunki a tafin hanunna suke, ko dama wanzami baya son jarfa ne, yanda kika mallakemin ɗan uwa kike tunanin ke naki ɗan bazai mallaku ba. Hhhhh Nafi idan kikace wannan layin zamubi ni da ke akan Shareff da Fadwa wlhy muje zuwa ɗan halak ka fasa....”
“Halima idan kin isa ke tujararriyace mu zuba ɗin dan ALLAH, ni dake za'aga mai iko akan wannan auren. Shiyyasa dama ni tun farko ban so wannan haɗin ba kika katsatstsare ke da Gwaggo sai anyisa. Bayan nasa ƴarki bata da tarbiyya ko misƙala zarratin..”
“Matsalarkuce kuma wannan, ni nagama dake kuma muje zuwa ɗan halak ka fasa”. Gwaggo Halima ta faɗa da yanke wayar. Wani jijjiga Mommy tai zata maka wayar da ƙasa Gwaggo ta riƙeta.
“Kefa daɗina dake baki da hankali idan ranki ya ɓaci, ki nutsu, har mi akai kai Halima ne ma. Ai wannan yaƙin namune gaba ɗaya, shiyyasa naita nuna miki ki kwantar da hankalinki akan haukan da kike na tsinema Mustapha a banza saboda farin cikin Halima da ƴarta. To gashi nan tun ba'aje ko'inaba sun fara nuna miki halinsu”.
Kukan takaici da baƙin ciki Mommy ta fashe da shi...........✍


😆Ashe haka duniya take ƙafar kazace. Aminai biyu ya hakane🤪? Yanzune fa wasan na ainahi zai fara, dan za'ai yunwa muga cikin kowa🤣🚴🏼👌🏼.



_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*


YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:
07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇
09134848107


*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*
[11/23, 10:16 PM] My Zafafa: *_Typing📲_*




*_❤‍🔥BABU SO....!!❤‍🔥_*
_(Miya kawo kishi?)_



*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*

*_BABU SO👉🏻AREWABOOKS_*

https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718


*_71_*



..........Gigitacciyar tsawa Daddy ya daka musu. “Wlhy duk wadda ta sake cewa tak sai ranta yay mummunan ɓaci, idan kuma kunji ƙarya bismillah marasa mutunci kawai. Ku har kun isa ku maidamu mutanen banza. Ku tashi kufita bama buƙatar zaman kowacce a anan”.
       Cikin ɓacin rai suka mike su biyun suka fice. Daddy ya cigaba da faɗa tamkar zai ari baki, da ƙyar dai su Abie ɗin suma suka taushesa. Haɗuwa sukai akan Fadwa da Shareff ɗin duka sukai musu tatas da faɗa musamman Fadwa a matsayinta na mace. Sai kuma suka koma nasiha a garesu. Daga nan suna jiyo hayaniyar Mommy da Gwaggo Halima, hakan yasa Gwaggo da har yanzu bata tofa nata ba ta miƙe ta fita wai zata tsawata musu. Nasiha Abie ya sake musu ta fahimta data saka zukatansu samun nutsuwa, musamman ma Fadwa da taga an nunama Shareff kuskuren marinta da yayi kuma ya nuna nadamar yin hakan da alƙawarin bazai sake ba. Duk da dai itama tasha nata, sun kuma nuna mata illar biyema su aunty Malika cikin hikima. Basu san babu abinda ke cizon zuciyar Shareff ba kamar maganar su aunty Safara'h ɗin nan. Sai dai baice komai ba dan a samu zaman lafiya, amma yay aniyar da kansa zaima tufƙar hanci insha ALLAHU.
     
        Da ƙyar wajen ƙarfe goma suka baro gidan, dan kuwa rikici ne na gaske ya ɓarke tsakanin Gwaggo Halima da Mommy har sai da Baban Fadwa ya kira waya dan baya ƙasar ne shiyyasa harta samu damar fitowa. Ya kuma janye mata wancan sharaɗin lokacin da zaiyi tafiyar saboda haƙuri data bashi akan komai ya wuce. Ashe akwai wani a gaba. Mommy dai taci alwashin sai ta nunama Gwaggo Halima itace ta haifi Shareff ba wani shege ya haifa mata ba. Haka itama Gwaggo Halima ta tabbatar mata cewa ita bata isa komai ba domin Shareff ɗin ba nata bane ita kaɗai..
     Kuka Fadwa ke masa tunda suka taho, dan kuwa rikicin Mommy da Mamanta ya matuƙar ɗaga mata hankali kuma, tana matuƙar tsoron abinda zai rabata da Shareff, tana masa so ne mai tsanani, wanda takejin in har aka rabasu zata iya rasa har ranta. Ya gaji dajin kukan, saboda shima zuciyarsa a wuya take kuma yanajin ƙuna da raɗaɗin abubuwa masu yawa. Sai dai shi jarumin mutum ne mai maida komai ba komai ba koda kuwa a ce ya zame masa komai. Dan haka har suka iso gida bai ce mata komai ba. Shine ma ya fara fita ya barta a motar, saida ta kai kusan minti huɗu a ciki tana cigaba da kukanta sannan ta fito ta rufe motar. Sashensa ta bisa kai tsaye, yana a falo zaune cikin yanayi na wanda baka iya ganemawa. Cikin jan ƙafa ta ƙarasa gabansa, ta tsugunna tare da dafa guyawunsa.
      “Ina tsugunne ne gabanka a matsayin ƙanwa Yaya Shareff, nasan ni mai laifukace a gareka tari-tari, na kuma yarda nayi kuskuren da kake son na fahimta tun kafin akai ga wannan gaɓar. Wlhy bana son zumincin iyayenmu ya lalace saboda aurenmu......”
    “Garama ya lalace, dan ta hakane kawai dake da su zaku dawo rayuwar hankali irin ta mutane. Ke kam rayuwarki naban mamaki matuƙa, mamaki irin wanda nake shiga kokwanto. Ba haka nai miki zatoba sam-sam a rayuwata ba, amma bazance ki dainaba kiyi tayi, shawara ɗaya zan baki kuma ta ƙarshe. Ya rage naki ki dawo akan ƙyaƙyƙyawar hanya ɗaya tak ki gyara halayenki muyi zaman aure na gaskiya, idan ba hakaba wlhy wlhy zan ɗauki mataki ne na ƙarshe dan bazaki maidani mahaukaci ba. Shawara ta rage gareki, ki cigaba da biyema duk wani mai zuwa gidan nan yana ɗauraki a hanyoyin da shi yake ado da su, koki zama mace tagari ki gina taki rayuwar a karan kanki. Idan kuma kika sake amfani da wani abu na kauce hanya domin mallakata, ko bani wani abu a cikin ruwan sha ko abinci ALLAH ya isa ban yafe ba!”. Ya ture hanunta tare da miƙewa ya shige bedroom abinsa.
     Hawayen da take son su zuba ma sam sunƙi zubar a yanzu, sai dai tasan gaskiya ya faɗa mata, dan kuwa a yanzu tana rayuwa ne da rayuwar su aunty Safarah, a baya komi za'a bata ta zubama Shareff a abinci bata taɓa yin hakan tunma tana gida, duk ma yanda zatai ƙoƙarin hanawa sai tayi, sai dai in Mama ta aikata bada saninta ba. Amma a wannan gaɓar ta rikice, idonta ya rufe saboda kishiya da kanta take aikata komai dan taga haske. Sai dai saɓanin hakan duhu take gani, sannan mai makon mallakarsa suɓuce mata yakeyi, kenan su magungunan na ƙarya sunfi yawa a cikinsu kenan? Ƙalilanne ake dacewa suyi aikin kuma basa wani jimawa sai kaga abubuwa sun ƙwaɓe. ‘Ya ALLAH’ ta faɗa tana mai fashewa da kukan zahiri.

    _____________★

       Harta fara jin barci a jiya bai dawo ba, dan ita bata san tare da Fadwa ya fita ba. Koda ta shirya ɗakin da Aysha ke kwana taje ta kwanta abinta. Ayshan batace da ita komai ba dan tasan yau Shareff ya koma wajen Fadwa. Ta ɗanyi murmushi ganin Anaam ɗin sukuku, ko bata fito ta faɗa ba tasan kewar Yayansu ke nuƙurƙusarta. Sai dai sanin itama Anaam nada halin I don't care wasu lokutan yasa babu wannan alamar akan fuskarta sam. Sai dai kuma koda suka kwanta ta jima batai barci tanata juye-juye. Sai da Ayshan ta ɗauke hankalinta da wasu labarai  sannan ɓarawon yay mata kamun kazar kuku. Ajiyar zuciya Aysha ta saki mai ƙarfi da kai hannu ta riƙo na Anaam ɗin. Tausayinta da ƙaunar ƴar uwarta na ratsa mata zuciya matuƙa....

       ★Kamar yanda ya saba da asuba sai da yazo ya tada su, Anaam ƙin yarda tai ta kalla inda yake taima shigewarta toilet. Juyawa yay ya fita shima yana mai sakin guntun murmushi. Itama Fadwa sai da yaje ya tadasu sannan ya wuce massallaci. Daya dawo bai shiga sashen kowacce ba ya koma nasa sashen ya kwanta dan jiya ya jima bai barci ba yanata faman ƙullawa da kwancewa akan yanda zai ɓulloma matan nasa. Barci yasha sosai dan sai kusan goma da wasu mintuna ya iya tashi, baiyi mamakin ganin an gyara ko'ina ba ga ƙamshi na tashi, sai dai yaji sassauci a ransa dan Fadwa ta nuna masa ta yarda ta gyara abinda take shirin ɓararwa a idanunsa. Wanka ya farayi ya shirya tare da baje jikinsa da ƙamshin turarurrukansa masu ƙamshin daɗi. Koda ya fito a falo ya sami Fadwa zaune cikin kwalliya mai ɗaukar hankali. Tabbas ta ɗauka hankalin nasa da gaske, sai dai ya basar abinsa. Gaisheshi tayi, ya amsa a daƙile, bata gazaba wajen sake jero masa kalaman ban haƙuri da tabbatar masa zata canja fiye da yanda yake buƙata. Har cikin rai ya ɗanjin tausayinta, dan yasan ya mata hukunci dai-dai da laifinta da har idan ita ba ibilisiya bace ya kamata yaga canjin. Huci ya ɗan furzar tare da ware mata hannayensa. Ai da gudu tazo ta shige jikinsa. Ya saki ƙaramin murmushi tare da sauke hannayensa akan bayanta ya fara shafawa alamar lallashi. Hawayene suka dinga silalo mata, ita kanta ta ƙara shaidawa Soulmate ɗinta zuma ne, ga zaƙi ga harbi. Ya ɗagota yana kallon fuskarta har yanzu dai babu fara'ar da take muradin gani a garesa.
“Kin san bana son kukan nan ko?”.
Kanta ta jinjina masa tana sharewa, ya raɓata ya wuce yana faɗin, “Ina zuwa bara na duba waɗan can ya suka kwana”. Kanta ta jinjina masa, ta bisa da kallo tana ƙara tsane hawayenta dake sakkowa. Ta san bawai ya gama hucewar bane, amma ko yanzu ta samu sassauci. Zakuma tabi duk hanyar data dace domin ganin ya huce baki ɗaya sun koma rayuwar farin cikinsu....

A falo ya samesu su duka. Anaam na tsaye riƙe da cup na shayi idonta a tv tana murmushi. “Wato blood film ɗin nan fa zaiyi daɗi, sai dai guy ɗin film ɗin sam baimun ba shegen kunensa uwa na zomaye ALLAH”. Dariya Aysha ta sanya harda ƙyaƙyƙyawa tana leƙowa daga kitchen. “Amma wlhy kinci zarafin mutumin nan, ni banga wani kunen da kike masa sheri da su ba.”
“ALLAH da gaske yanada kunnuwa gasu nan, ga shegen rawan kai a wajensa uwa dangin makaɗan zamanin jahiliyya, ALLAH an cuceta da aka haɗata da shi”.
Alamar komawa yay ma Aysha data leƙo zatai magana, tai saurin komawa cikin bin umarninsa harda turo ƙofar kitchen ɗin dan ta tabbatar wata taɓarar za'ai. Rayuwar Yayansu na birgeta tun akan Fadwa, gashi dai mutum miskili da baya ɗaukar raini amma matansa nashan sharafin soyayyarsa. Cigaba yay da tsayawa a bakin ƙofar hannayensa harɗe da ƙirjinsa yana kallon Anaam ɗin kawai. Ita ko sam bata san da zamansa ba amma tanajin ƙamshin turarensa a hancinta wanda take ganin hakan normal ne tunda dama yana shigowa maybe tunna baya ne. Juyowa tai zata koma saman kujera suka kusa cin karo da shi dan ya baro ƙofar. Da sauri ta ɗanyi baya a zabure dan tsoroma ya bata. Cikin zafin nama ya riƙe cup ɗin shayin dake neman antayewa a jikinta.
Baki ta tura gaba da ƙwaɓe fuskarta da tasha kwalliya. “Kai Yaya ALLAH ka tsoratani”.
Idonsa akan lips ɗinta ya ɗage mata gira ɗaya, “Kin dai so ki tsorata madam”. Bakin ta ƙara tura masa tana ƙoƙarin janye jikinta. Hanata hakan yay ta hanyar riƙo ƙugunta, ya zuba mata mayun idanunsa cikin nata idon, tare da matso hanunta da nasa dake rike da kofin shayin yakai bakinsa. “Wayyo Yaya ni ALLAH zaka shanyemun tea ɗina”.
“K miyasa rowanki yayi yawa ne?”.
“To kai miyasa kwaɗayinka yay yawa ne”.
Murmushi yayi da kai yatsarsa ya ɗalle mata baki, “Magananniya da ba'a kadata. Sammin lipstick ɗin shima Please”.
“Tab ni ban saka da kai ba ni kaɗai zan shanye abuna”.
Dariyarsa ya danne da ƙyar, ya ɗan ƙwaɓe fuska da langaɓe kai gefe, “Babie Please mana”.
“Naƙi wayon”. Ta faɗa dayi masa gwalo tana tura lips ɗin cikin baki. “Ni kikama rashin m ko? Zan rama ALLAH”. Dariya ta ƙyalƙyale da shi da masa gwalo. “Kafin ka rama na ƙara wani rashin m ɗin ma”. Ta zille, riƙota yasoyi amma tai tsalle gefe tana masa gwalo. “Zan rama ne yarinya ai zaki zo hannu. Oya muje breakfast”..
Idanu ta ɗan waro, “Gashifa Aysha na mana anan”.
“Kin manta tsarina kenan”.
Shiru tai cikin ɗan tauke fuska. Dan ta ƙwallafa rai a abinda Ayshan keyi. Amma sai batai musu ba ta kaɗa masa kai. Tare suka fita, sun iske Fadwa na ƙara gyara dining ɗin. A yau ma babu wacce ta kalla ƴar uwarta a cikinsu. Dan haka ya duba kowacce fuskarsa a tsuke. “Kun gaisa da juna?”.
Shiru duk sukayi kowanne idonsa a ƙasa dan a serious yay maganar. Fadwa ce tai ƙoƙarin dannewa a shaƙe tace “Kin tashi lafiya?”. Baki Anaam ɗin ta taɓe da amsawa a shaƙen itama. “Alhmdllhi”. Komai bai sake ce musu ba, dan yasan a haka a haka watarana zai ci nasara. Wayarsa da yake latsawa ya ajiye, Fadwa ta fara haɗa masa abincin. A daidai nan Aysha ta shigo da ƙaramin tray. Wani irin ajiyar zuciya Anaam ta saki a hankali. Ya ɗan saci kalonta ta gefen ido sai yaji tausayinta. Ya fahimci tana son abinda Ayshan ke musu amma tabi umarninsa ta taho, shiyyasa yayma Aysha text yace ta kawo mata. Kasa ɓoye farin cikinta tayi har sai da ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login