Showing 135001 words to 138000 words out of 178785 words
batayi dai-dai bane ɗazun daya sshigo.
*_(Mata ku daina ruɗar da kanku da wannan zoben da kuke saya, wai miyasa munada ilimi amma basirarmu ke toshewa akan kayan matane?. Kwanaki nai wata baƙuwa, kamar wasa muna hira sai aka kai har kan illar shaye-shayen maganin mata da wasu mata suka maida tamkar ibada a rayuwarsu har ana ribatarsu da su ana basu kayan tsubbu a zuwan maganin mata kamar dai fadwa. Sai kawai take bani labarin ai wani zobe ma ya shigo wai na mallaka. Ana saidawa dubu uku har sama da haka. Ban ɗauka abin serious ba sai a wajen wani taron suna. Hhh abin dariya, mu anan yankin ma tsabar dukan hancin da akema mata zoben ana saida musu ne a 5k 6k 7k har 10k idan aka tabbatar ke hamshaƙiya ce, kunsan kuma su wannan manyan matan sunfi son ace abu nada kuɗi mai yawa sunfi bashi daraja. Humm abin mamaki wai sai ga mata na mugun rububin zobe kamar ƙiftawar ido ya ƙare, har wasu na shiga damuwa basu samu ba. 🤦🏻haba mata mi muke son mu zama ne wai dan ALLAH? Shin wai mallakar nan mizata amfana miki? Nasan kowace mace tana so mijinta ya sota ya kuma ƙaunaceta, amma sai nakega akwai hanyoyi masu ƙyau da zakibi shi namiji ya soki domin ALLAH. Sannan ku fahimta da ƙyau wlhy namijin bahaushe komin son da yake miki da wahala ya lalace a jikinki koda yaushe kamar wasu a cikin ƙabilun nan. Ɗabi'ar da suke nuna mana kuma ba itace rashin so ba, dan kinga mace na nanaye a media da miji bashike nufin ita ƴar gata bace, dan kinji mijin novel ya lalace jikin mace karki ɗauka dole naki mijin sai ya kasance a haka ki yarda yana sonki. Wani abun ana sakashine kawai dan nishaɗi. Mu kiyayi zantuka ko labarai ga ƙawayenmu su gidajensu kaza kaza ta yanda hankalinki zai tashi kiga gazawar mijinki, wlhy koyaya mijinki yake sunansa jan gwarzo, idan kika nutsu yanada tasa baiwa da kalar soyayya da farin cikin da yake baki kema ba sai lallai irin wancan da kike hange ba. Idan kina cikin wani ƙunci a gidan aurenki ki ɗauka harabawace ke kuma bautar ALLAH kikeyi sakamakonki nagaresa, idan kikai haƙuri sai ya sakaki a aljanna. Amma mu kiyayi zurmawa akan shaye-shayen magungunan matan nan da bamusan kansu ba suzo suna mana illa a banza a wofi, su kansu wasu a cikin masu saidawar basu da ilimi a kansu bamu kawai sukeyi. Ki samu mai inganci wanda kika yarda da hadinsa da mai saidashi ki saya kisha gwargwado bata yanda zaki saka kanki a dana saniba kizo kina jama kanki illa da kwasar imfection a banza a wofi. Kuyi hakuri masu magani nasan akwai nagari acikinku dan kowane sana'a akwai na kwarai akwai na banza. Masu na banzar suke bata na kwarai da disashesu akasa ganinsu a idanun al'umma. amma dan ALLAH mata a kiyaye, zoben nan da sayensa gara ki samu kazarki kici tai miki amfani babu abinda ke tattare da son zuciya dake zama ɗorarre).
Sashensa ya nufa rai ɓace, ya zube a falo yana cigaba da jan tsaki, shi ya rasa mike damun waɗannan yaran, musamman ma Fadwa, dan Anaam ita kai tsaye take abunta bata iya ɓoye-ɓoye ba. Kuma tunda ya santa haka take, tunda ko'a shigowarta gidan nan ya hukuntata sau da yawa akan yima Fadwa abu amma hakan bai hana ta ƙara gobe a zahiri babu wani ƙumshe-ƙumshe. Itako Fadwa yau ta nuna ita mai kirki ce, musamman idan da Anaam a waje, anjima ya sameta tana baƙin rai da ƙananun magana akan Anaam kaza-kaza. Ya rasa mike damun tunaninta, shi kuma ya tsani wannan banzan halin dan yana kamanceceniya dana munafukai. Ƙwafa yay mai ƙarfi, a ransa yana ayyana zaima tufƙar hanci....
★★★
“Blood zan baki wata shawar dan ALLAH ki fahimceni”. Aysha ta faɗa tana direma Anaam plate na abinci data dafa musu a gabanta.
Wayar da take latsawa ta ajiye, da maida hankali ga Ayshan. “Tofa shawarar mi kuma blood?”.
“Ta zamanki a wannan gidan. Na fahimci gaba ɗaya a haguggunce kike, sai dai na miki uziri domin rayuwace da baki saba da ita ba kuma baki santa ba. Kin tashi a rayuwar da kowa yana komai akaran kansa kuma kai tsaye batare da wani munafunci ba ko boye-boye, dolene a wannan gaɓar kisha wahala sai dai nai alƙawarin bazan bari hakan ta faru ba. Blood daga yanzu dan ALLAH komi Fadwa zatai miki ki daina nuna ƙinsa a gaban Yaya koda ace bai miki ɗin ba, domin na fahimci da wannan makamin take amfani wajen kai miki duka a tsakaninki da Yaya. Ki duba ranar yanda ya nuna jin haushinsa akan abinda kikayi, wlhy ina ganinta sanda take murmushi, hakama yau da muka dawo, dan munafunci hardafa rakomu nan”
Murmushi tayi da ɗaukar spoon ta fara cin abincinta dan tafi son cinta da zafi. “Amma blood ban katseki ba, miye amfanin kwaikwayon halin wani bayan hanyace mara ƙyau, ɓoye ƙinta kamar yanda take ƙina bashine zaisa na birgeta ba ko shi na birgesa. Tsakanina da ALLAH idan nace zan zauna shanye haukar wannan matar zan kamu da ciwon hawan jini, nafi yarda da kamun na maka a wuce wajen dan nasan itama munafunci kesata yimin wani abun”.
Sallamarsa ta tilasta Aysha haɗiye abinda tai yunƙurin faɗa, dole ta juya tana amsa masa. Anaam kam kallo ɗaya tai masa ta ɗauke. Shiko kasa ɗauke nasa idon yay a kanta, ko sannun da Aysha tai masa hannu kawai ya iya ɗaga mata. Kujerar dake facing Anaam ya zauna. Hakan yasa Aysha miƙewa a ɗan ɗarare tace, “Yaya a kawo maka abincin?”.
Abincin ya kalla na wasu sakanni, sai kuma ya miƙe daga inda yake ya koma kujerar da Anaam ke zaune kasancewar 2sitter ce. “Bara naci kaɗan anan kawai”.
Cikin jin daɗi Aysha tai murmushi, Anaam kuwa ɗagowa tai idanu a ware tana kallonsa, ya ɗaga mata gira da kashe mata ido ɗaya yanda Aysha bazata lura ba, da sauri ta kalli sashen da Ayshar take, sai dai ita hankalinta ma ba kansu yake ba.
Spoon ɗin hanunta ya zare da sakin guntun murmushi, yana motsa lips ɗinsa a hankali alamar akwai abinda ya faɗa. Batai tunanin da gaske yake ba, sai ganin ya ɗiba yakai bakinsa tayi.
“Wai da gaske kakeyi?”.
Ta faɗa cikin magana ƙasa-ƙasa dan kar Aysha taji tana waro masa idanu da ƙyau.
Shima ƙasa yay da muryar tasa cikin kwaikwayonta da kashe mata ido yace, “Bayan wannan zahirin kina buƙatar ganin wani ne?”.
Idanun ta ƙara warowa sosai “Are you ok?”.
“I'm not...”.
Ya bata amsa a taƙaice yana danne dariyarsa dan da gaske tayi bala'in diriricewa. Tsabar son ƙureta abincin ya ɗibo yakai bakinta. Da sauri takai hannu zata kare. “Idan kikaƙi amsa ALLAH cak zan maidoki jikina sannan na baki wanda na tauna a bakina kuma a gabanta harda tsotse lipstick ɗina”.
Yanda ta saki baki da hanci tana kallonsa ya sashi dungure mata kai yana murmushi, tana buɗe baki da nufin yin magana ya juye mata shi. Dole tai saurin rufe lips ɗinta dakai hannu ta kare bakinta. Dai-dai nan Aysha da ta wuce kitchen batare da sun sani ba ta dire babban tray data shirya abinci kamar yanda akema kowanne magidanci a saman centre table ɗin gabansu. Lokaci guda suka sauke ajiyar zuciya, Anaam ta kalleta shiko ya fiske fuskarsa na komawa normal kamar ba shine ke murmushin ba.
Aysha na ƙoƙarin barin falon Anaam tai saurin faɗin, “Blood ina kuma zaki? Kizo muci abincin mu”. Da sauri Aysha ta shige bedroom ɗin baƙi kamar ma bata jita ba.
“Yaya ka gani fa ka koreta?”.
“So take ki samu ladan da mata ke samu kema, tunda garden ɗina kin haɗa baki da doctor ɗin can kar naje barruwa.”
Maganarsa ta farko kawai ta fahimta. Dan haka cike da basarwa ta bashi amsa. “Matarka ai tana dafa maka ta samu ladan, kaga ya wadatar da kai ai”.
Shima fahimtar hakan ya sashi juya harshe zuwa yaren Maley.
“Ke minene naki sunan?”.
“Kanwarka kaima da kowa an sani”.
“Really?”.
“Yap!”.
“Idan suka ganki da tsarabar furen garden sai su cireni a jerin Yayun naki ai ok”.
“Kai ka san wani garden Yaya”.
“Kema kin sanshi sai dai ƙari. Ni fa janbakin nan ya tsolemun ido a bani na shanye kayana k......”
Abincin data ɗebo ta juye masa a baki kamar yanda yay mata shima ɗazun, dole ya haɗiye sauran maganar itako ta shiga ƙyalƙyala dariya dan lauma babba ne........✍
_ZAFAFA BIYAR_
*_INAYAH_*
_MamuhGee_
*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_
*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_
*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_
*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_
_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*
YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾
ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070
SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:
07040727902
IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇
09134848107
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*
[11/15, 11:40 PM] My Zafafa: *_Typing📲_*
*_❤🔥BABU SO....!!❤🔥_*
_(Miya kawo kishi?)_
*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*
*_BABU SO👉🏻AREWABOOKS_*
https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718
*_64_*
........Dariya take tana masa gwallo. Fuska ya ɓata, da harɗe hannayensa a ƙirji irin yayi fushin nan. Yanda yay ɗin sai ya saka Anaam shiga ƙyalƙyala dariya da faɗin.
“Kai Yaya shagwaɓa kuma?! ALLAH kamafi ƙyau a haka fuskanka so cute”. Ta ƙare maganar da kashe masa ido dariyarta mai ƙaramin sauti na bayyana fararen haƙoranta. Ta nuna lips ɗinta da kaɗa masa idanunta dake cikin gilashi.
“Indai lipstick ɗin nan ne Yaya ba shansa zakai ba garama ka haƙura”.
“Oh oh haba princess kiji tausayina mana”. Yaya maganar da matsar da fuskarsa gab da tata.
Baya taja dasa hanunta ta kare bakinta, “Babu wani princess na daɗin baki fa Yaya, barima kaga na shanye abuna, idan baka ganiba ai dole ka haƙura”.
Yana ƙoƙarin riƙota ta tura lips ɗinta cikin baki da sauri.. Idanunsa ya waro sosai yana kallonta cikin langaɓe wuya. Ta fito da lips ɗin tana dariya da masa gwalo.
“Sai kaci abinci yanzu babu”.
“Ni ko? Yarinya zan rama ne”.
Dariyarta ta cigaba dayi ƙasa-ƙasa, shiko ya ɗauka spoon ɗin ya cigaba da cin aincinsa fuskarsa da ɗan murmushi.
“Nifa yaya karka cinye min abinci na”.
Idanunsa ya ɗago yana kallonta, sai kuma ya ɗibo abinci ya nufi bakinta, “Ba marowaci bane irinki ai hahh”.
Bakin ta buɗe ba musu ya zuba mata, a hankali ta shiga taunawa da faɗin, “Nima ai bana rowa”.
“Kika min yanzun?”.
“Baga abincina kana ci ba”.
Murmushi kawai yayi batare da yace komai ba. Itama bata sake magana ba, ya cigaba da bata abincin shima yana ci. Suna gab da kammalawa wayarsa tai ring, ɗauka yay ya duba, ganin Khaleel sai kawai ya ɗaga. Bata san mi'akace masa a wayarba, sai gani tai ya miƙe da kama hanunta....
Da mamaki take kallonsa zatai magana ya girgiza mata kansa. Baki ta ɗan tura dan ita dai bata ƙoshi da abincin ba, sai dai babu yanda zatai dole ta bisa. Hango Khaleel jikin wata mota mai ƙyau fara tas jingine ya sata zare hanunta cikin nasa, bai ce komai ba har suka ƙaraso. Ita ta fara gaida Khaleel ɗin, ya amsa mata fuska da murmushi sannan ya maida hankalinsa ga Yayansa. Gaisheshi yay da girmamawa. Ya amsa masa da kulawa.
“Daga ina haka mazan fama?”.
Murmushin Khaleel ya faɗaɗa dan yana son Yayan nasa ya kirasa da sunan nan. Wani ɗan ƙaramin gift🎁 ya ɗakko a gaban motar, ya dubi Anaam dake kallon motar da ita kanta an naɗeta da zaren gift. Sai kuma ya sake maida kallonsa ga Shareff ɗin da shima dai motar yake kallo. “Saƙone daga Abie. Abawa Granny”.
Idanu ta waro matuƙa da kai hannunta duk biyu saman bakinta, sai kuma ta dubi Shareff da shima murmushi ke shimfiɗe akan fuskarsa. Shine ya amsa ya buɗe key na mota ya bayyana. Ai batama san sanda ta rungume Shareff da faɗin, “Wayyo Yaya daɗi zai kasheni”.
Rungumeta yay shina da sakin dariya kamar yanda Khaleel shina ke dariyar. Ɗagowa tai ta amsa key ɗin tana kallo, sai kuma ta ɗagasa a saitin fuskar Shareff tana kaɗa masa. Murmushi ya sake saki mai faɗi da faɗin, “ALLAH ya sakama Abie da alkairi Congratulations dear”.
Da amin ta amsa, Khaleel ma ya amsa da kallonta. “Congratulations Granny. Saura kuma tukuyci na, k ko Yaya wazai bani?”.
“Karka damu Yaya Khaleel, saika zaɓa”. Ta bashi amsa da shigewa motar da Shareff ya buɗe mata, daidai nan Fadwa ta fito hakama Aysha. A tare suka ƙaraso wajen, Fadwa da gaba ɗaya ranta ke'a jagule tun maganganun da Shareff ya yaɓa mata ta dubi Khaleel fuska a tsuke. Kafinma tai magana ya nuna musu motar ita da Aysha yana murmushi. “Ƙyautace daga Abie aka kawoma Anaam”.
“Woow!!” Aysha ta faɗa cikin zaro ido da shafa motar tana kallo, Fadwa kam mutuwar tsaye tai. Dai-dai nan Shareff da Anaam dake cikin motar suka fito kowanne fuskarsa har yanzu da murmushi. Khaleel ya miƙa mata hannu, “Nifa a tafamin tukuycina”.
Kafin tace komai Shareff dake danna wayarsa ya miƙa masa, saka details ɗinka”.
“Woow da kyau babban yaya da gudu kuwa”.
Yanda Yay ɗin ya saka Anaam da Aysha kwashewa da dariya. Shigar saƙo a wayarsa yasa bai tankasu ba, ya buɗe da sauri, “What!”. Ya faɗa yana ɗago kai da sauri ya kalli Shareff. “Yaya duk tukuyci?”.
Murmushi Shareff yay da kallon Anaam, “Idan tace a ƙara maka ma sai a ƙara maka ai”. A salon da yay maganar da ɗage mata gira ya sakata rufe fuskarta da dukkan tafin hanunta dan taji kunya. Matsota yay tare da ranƙwafawa saitin kunenta. “Nima ina jiran nawa tukuycin yanzun nan, inba hakaba a gaban Khaleel zanyi.....”
Da sauri ta buɗe idanunta... “Kayi mi?”. Maimakon amsa sai ya nuna mata lips ɗinsa cikin kashe ido. Sarai tasan zaiyi ɗin, amma sai ta kauda ido da nufin cewa a'a. Akan Fadwa da sam bata san da wanzuwarta a wajen ba ta saukesu. Sukaima juna kallon ido cikin ido, ita ta fara kauda idonta da sakin wani tattausan murmushi mai ma'anoni da yawa ta maido dubanta ga Shareff. Murmushi ta sakar masa shima ta ɗan saci kallon Aysha dake a mota hankalinta baya kansu, ta maida ga Khaleel, ganin shi ɗin dai zaiga komai sai ta ɗanyi jimm na tunani. “Yaya Khaleel kalla can”. Ta faɗa da sauri tana mai ɗane Shareff a bazata ta manne tausasan lips ɗinta kan nasa lips ɗin.
Numfashinsa neman shiɗewa yay saboda rashin zaton hakan daga gareta. Baya ta nema janyewa ya ƙara cafkesu da saka hannu biyu saman ƙugunta ta zuba masa mintsini a gefen ciki da janye jikinta kunya kamar ta nutse..
Khaleel daya waiga baiga komai ba ya juyo da nufin hararar Anaam, ai babu shiri ya sake maida kansa gefe da sauri yana dafe bakinsa da sakin siririyar dariya. Aysha da bata san mike faruwa ba ta fito a motar tana rungume Anaam da faɗin, “Wayyo blood motar nan ta haɗu wlhy ALLAH yasa a kashe da kai”. Wani bahagon tari ya sarƙe Fadwa, cikin sassarfa kamar zata kife ƙasa dan sauri tabar wajen hawaye masu azabar zafi na kufce mata.
Gaba ɗayansu kallonsu suka maida gareta, dan sai yanzu ma shi Shareff yasan Fadwar na'a wajen. Cike da son basarwa itakam Anaam ta rungume Ayshar. “Thanks you blood, thanks you”. Shima dai gogan ya basar a binsa kamar komai bai faru ba, ya nunama Khaleel hanya alamar su shiga ciki idonsa akan Anaam. Anyi sa'a itama ta ɗago suka haɗa ido. Baki ta ɗan murguɗa masa. Ya taune lips dinsa da sakin murmushi alamar azakizo hannu. Kafaɗa ta ɗage masa da labe baki irin na i don't care taja hanun Aysha suka koma motar...
Da ƙyar Fadwa ta iya kai kanta sashenta saboda jiri dake ɗibarta da lulluɓe ganinta gaba ɗaya. “Subahanalillhi. Hajiya lafiya?”.
Mmn Abu ta faɗa da nufo Fadwa da sauri dake neman zubewa ta tareta. Kuka ta sakar mata kamar wata karamar yarinya, maman Abu duk sai ta rikice. Kamata tai har bedroom. Tana son tambayarta mike faruwa tana jin tsoro, dole ta fito ta barta cikin damuwa. Tadai san labarin kitse baya wuce ƙoƙi dan ta jima da fahimtar Fadwa na cikin jerin mata masu tsananin kishi. Gata da hali irin na ɓoye abu a rai da idan bakai dogon nazari akanta ba saika ɗauka kishiya cutarta take musamman irin Anaam da bata iya ɓoye abinda ke ranta. “ALLAH ya ƙyauta”. Ta faɗa da komawa kitchen ta cigaba da aikinta.....
Anaam kam da tuni sun koma ciki tana can cikin farin ciki tana waya da Mamie da Abie ta video call. Addu'a take zubama iyayen nata harda hawaye, yayinda suma suke kallonta murmushi shimfiɗe a fuskokinsu da tsananin ƙaunarta da tausayinta harma da alfahari da ita na kai mutuncinta gidan aurenta. Dan aunty mimi ta sanarma Mamie komai, hakama Mamie ta sanarma Abie, shiyyasa ya danƙara mata mota najin alfahari da ita akan riƙe tarbiyyar da sukai mata. Sai dai su kansu sun san sun kaita wani filin gwagwarmayar rayuwane na yankin kaddararta, amma sukanji sassauci da tunawa zumincin ALLAH suke son karfafawa insha ALLAHU sadaukarwarsu bazata taɓa zama a banza da wofi ba..
______________________________
Tafiyar dai Aysha bata yuwu a yau ba, dan tuni Shareff ya fice gidan tare da Khaleel yin godiya ga Abie, Anaam kuma sai ta ƙara samun sauƙin jikinta insha ALLAH zai kaita. Sai da suka fara biyawa ta office yin wasu muhimman baƙi, ba wani dogon zama sukai ba sai zuwa monday idan ya dawo aiki. Takardar da