Showing 150001 words to 153000 words out of 178785 words

Chapter 51 - Babu So Complete Hausa Novel

05 Feb 2025

32861

kalla Aysha da murmushi. “Thanks you blood”. Murmushi Aysha ta mata. Itama sai ta sake murmusawa. Har Aysha ta juya zata fita Fadwa tace, “Ki dawo mu karya mana Aysha”.
“No Aunty gashi can na baro kar a barsa ya lalace shima”. Tai maganar tana nufar hanyar fita da ɗan hanzari dan karma Shareff ya tsaidata. Batama san shi baida niyyar tanka musu ba. Abincinsa yake ƙoƙarin fara ci kawai............✍



_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*


YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:
07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇
09134848107


*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*
[11/23, 10:16 PM] My Zafafa: *_Typing📲_*




*_❤‍🔥BABU SO....!!❤‍🔥_*
_(Miya kawo kishi?)_



*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*

*_BABU SO👉🏻AREWABOOKS_*

https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718


*_70_*



........Wasa farin girki wai amarya da tuƙa tuwon tiya goma. Ashe rikici a waya tsakanin Mommy da Gwaggo Halima somin taɓi ne. Dan kuwa ba'a rufa awa guda cikakkiya ba sai ga Gwaggo Halima tazo gidan. Hakan yayi dai-dai da dawowar Daddy daga wajen aiki gidan shima. Yay sagade yana kallon Gwaggo Halima data ƙaraso garesa tana huci.
    “Halima lafiya kuwa da magribar nan?”.
    “Inafa lafiya Yaya, Shareff ya buɗe ƙwanji ya shashsheka ma Fadwa mari amma saboda son zuciya irin na matarka ta goya bayansa saboda itace ta haifesa”.
        Da mamaki sosai yace, “Mari fa dai? Ya ALLAH mike damun Shareff haka? Wannan ba maganar nan bace shiga ciki nafara zuwa salla kafin su Abubakar su dawo”.
    A maimakon sashen Mommy ko Gwaggo da da idan tazo gidan take shiga yau sai ta nufi sashen Mom.....

________________★

        Rashin fitowarsa har aka kira sallar magrib yasaka Anaam kasa zaune ta kasa tsaye. Tana son zuwa dubashi tanajin tsoro. Gani take kamar itama ɗin marin nata zaiyi. Harga ALLAH tana matuƙar tsoron duka a rayuwarta. Koda wani taga ana duka firgicewa take. Ballema har abada bazata taɓa iya manta dukan dayay musu ba ita da Aysha. Da sauri ta juyo jin motsin buɗe ƙofa. Sukaima juna kallon cikin ido ita da shi, ita ta fara janye nata tana sauke ajiyar zuciya dajin shakkar kallon fuskarsa dake a matuƙar tsuke.
     “Ki tashi kiyi salla”.
Ya faɗa a taƙaice da juyawa zai fita. Harya kama handle ɗin ƙofar zai fita ya tsaya cak, juyowa yay a hankali yana kallonta saboda ganin yanayinta. Sai dai baice komaiba ya juya ya fita. Numfashi ta saki a hankali da miƙewa ta shiga toilet domin ɗauro alwala.

       Bai dawo gidan ba sai bayan sallar isha'i, kai tsaye kuma sashenta ya zarto. Tunda ta idar da salla ta kasa tashi a wajen, babu abinda ke mata kaikawo, haka kawai marin nan na ɗazun da yay ma Fadwa ya matuƙar tsaya mata a rai, duk da kuwa ƙararsa kawai taji bawai yinsa akan idonta ba. Harya ƙaraso gabanta bata san da shigowarsa ba, ya kai tsugunne gabanta, tare da ɗago haɓarta. Cikin idanunsa ta zuba raunannun nata da babu gilashi, bata ganinsa fes yanda ya kamata, amma hakan bai hanata tsaidasu a tsakkiyar nasan ba...
      “Mike damunki?”.
   Ƙoƙarin janye idanunta tai a cikin nasa ya hana hakan, taso kauda kanta gefe nanma ya hana, saita ƙara tsuƙe fuska da tura baki. A karon farko ya saki murmushi, tare da kai yatsansa ya ɗalli lips ɗin nata. “K wai baki san shekarunki sun girmi wannan taɓaran ba Autar mata?”.
      Hanunsa ta ture zata tashi, yay saurin damƙota yana dariya, jikinsa ta faɗa, dan haka suka zube ƙasa gaba ɗayansu. Ƙafarsa ɗaya ya kwanta, tare da jawota ya kwantar a cinyarsa ita kuma. Ya tokarar da ɗayar ta jingina kanta. “Nayi laifi ne wai?”.
          Hanunsa dake kan cikinta ta kamo, ta saka babban ɗan yatsan a bakinta ta ciza. “Wai wai shiii! Wace mugunta ce muka wannan?”. Dariya ta ƙyalƙyale da shi. “Noorie muguntafa babu ƙyau sam sam”. Ka ɗan ta murguɗa masa baki “Punishment ɗin mai yawo ne ai”.
      “Shi kuma punishment ɗin mai rashin kunya fa? yaya ya kamata ya kasance?”.
      “Sai an binciko a littafin shara'a”.
Ta faɗa tana ƙoƙarin mikewa ta gudu. Riƙota yay yana ƙaramar dariya. “Sarkin wayo ai ni tuni na binciko. Yanzu kuma zan ƙaddamar da shi”.
      “Wayyo yaya! Wayyo ni yunwafa nakeji, tun safe banci komai ba.”
   “Nima ita nakeji ai”. Ya ƙare maganar da manne lips ɗinsu waje guda. Ko sau ɗaya batai ƙoƙarin hanashi ba, saima gudunmawa data fara bashi, burinta kawai taga ya huce daga fushinsa. Cikin ƙanƙanin lokaci ta gama hautsina masa kwanyar kansa, tun yana binta a salon jarumta harya fita a hayyacinsa ya ɗauka wata hanya da ban da karatun da ya kasance mai girma ga Anaam. A yanzu kam ita ya nema gigitawa, yayinda shi tuni ya fita hayyacinsa har baya gane ita ɗinfa ƙanwarsa ce. Sunyi matuƙar shagala a farantama junansu ring ɗin wayarsa ya shammacesu. Da ƙyar Anaam ta iya janye jikinta dake rawa gefe. Shima nashin rawar yake fiyema da tata, sai dai jarumtar ƴan mazan ta ɓoye haka, ya rimtse ido da ƙarfi ya sake buɗewa saboda ganin mai kiran. Ko'a turu a kwantosa bai isa ɗaga wayar nan ba, dan babu makawa sai Daddy ya gane halin da yake a ciki. Haka ya barta harta tsinke wani kiran ya ƙara shigowa. Yanzun ma kasa ɗagawar yay har saida ta yanke, da ƙyar ya samu iya ɗan dai-daita kansa bayan wasu mintuna sannan yay kiran Daddyn Back.
      Koda Daddy yaji muryarsa a shaƙe a zatonsa duk ɓacin rai ne, dan kuwa yasan wanene Shareff idan yay fushi. “Ka sameni a gida yanzun nan kai da Fadwa”. Bai jira cewarsaba ya yanke kiran. Shima ɗin baice komaiba ya koma kwance tare da mirginawa jikin Anaam data juya masa baya ya rungumota da ɗaura kansa a gefen wuyanta yana shinshina, ga sanyin tiles na ratsasu dan harya huda sallayar tana iya jinsa a jikinta shima haka..
Jin saukar hanunsa a ƙirjinta tai saurin riƙewa. “Yaya kirankafa Daddy yakeyi”. Iska ya ɗan hura mata cikin kunne da ture hanunta ya ɗaura a inda yay niyya tun farko. “Koratama kikeyi kenan?”.
“Eh mana, Daddy ba abin wasa bane ai, umarninsa yana sama da muradanmu”.
Sassanyan murmushi ya saki da sake ƙanƙameta a jikinsa, a hankali ya furta *_Ina ƙaunarki da yawa_*”. Sosai tsigar jikinta ta yamutsa saboda yanda yay furucin a cikin wani irin wahalallen sauti. Taja numfashi mai kauri da cije gefen lips ɗinta sakamakon saukar kiss ɗinsa saman wuyanta. Bata iya ta ɗago ta kallesa ba harya fice daga ɗakin. Ta sauke sassanyar ajiyar zuciya da sake kananneɗe jikinta waje guda wani abu mai girma na tsikarar ƙasan zuciyarta....

A sashen Fadwa kan duk da yaji a ransa itace takai ƙararsa wajen su Daddy bai mata magana ba, umarnin kawai ta samesa a mota ya bata ya juya ya fita abinsa. Taja wasu mintuna kafin ta fito dan har ya kunna mota ma.
Tafiya suke amma kowanne fuskarsa na gefe, ita tana kallon mutane shi kuma titi har suka iso. baiyi mamakin samun Gwaggo Halima ba, Fadwa ta nufeta ta rungumeta tana sakin kuka. Lallashinta ta shigayi tana shafa bayanta da fuskarta wai tana neman tabon marin. Abin sai ya girmi kan kowa amma babu wanda yay magana sai Mommy ce taja tsaki da taɓe baki. Shareff kam zama yay ƙasa a tsakkiyar ƙafafun Abie da Abba. Kansa a ƙasa batare daya kalla kowa ba ya gaishesu. Haka kawai yakejin tsananin kunyar Abie da Mommynsa fiye da kowa a wajen.
Abba da yaga mulmular da Gwaggo Halima kema Fadwa na neman yin yawa ya magana a kausashe. “K Fadwa tashi ki zauna da ƙyau bama son shashanci”.
Tashin tai zaune, sai a sannan kuma take gaidasu. Iya su mazan kawai suka amsa. mommy da Gwaggo babu wanda ya tanka. Gwaggo Halima tai ƙaramar ƙwafa da ayyana (Zanyi maganinku) a zuciyarta.. Abie ne ya buɗe taron da addu'a, kafin ya maida hankalinsa ga Shareff cikin serious matuƙa.
“Al-Mustapha miya haɗaka da matarka harda mari? Bayan wannan ba ɗabi'ar dakaga wani a cikinmu nayi a gidan nan bane?”.
Ƙasa Shareff ya ƙarayi da kansa, cikin matuƙar girmamawa. “Kuyi haƙuri Abie nayi kuskuren aikata hakan, sai dai saida na umarceta ta tashi tabar inda nake dan bana son yanke hukunci cikin fushi, amma taƙi yin hakan har takai nayi marin”.
“Amma banda abinka Babana ai kai babbane, da taƙi tashi sai kai ka tashi ka bata waje tunda kasan baka iya controling kanka a yanayin fushin. Su mata haƙuri ake dasu a kowane hali, domin hangenka da nasu sam ba ɗaya bane ba, sai dai sunada sauƙin sha'ani kuma ba koda yaushe ake cizawa a kansu ba”.
“Hakane Abie, insha ALLAHU hakan bazata sake faruwa ba......”
“Tama sake faruwar mana. Wlhy da kaina zan rama mata mara mutunci kawai. Kai yanzu dan baka da kunya Shareff har kanada hanun ɗagawa ka daki Fadwa a gidanka?”.
“Yaya Halima! Ya kamata kiyi shiru abi komai a sannu”.
“Wane kuma sannu Abubakar, bayan kanaji yana lallaɓashi saboda ba ƴarsa aka mara ba”.
Murmushi Abie yay da girgiza kansa. Cikin dattako da nutsuwar da kowa ya sansa da ita ya fuskanci Gwaggo Halima. “Ba haka bane Yaya Halima. Da Shareff da Fadwa da Anaam duka su ɗin ƴaƴanmu ne, bazamu taɓa sakaci da cutuwar ɗayansu ba ai. Da kinyi haƙuri zan kai inda kike buƙata nima ai”.
Baki ta taɓe da juya kai gefe. Nanma Murmushin Abie ya saki kawai ya sake maida hankali kan Shareff da ransa ya ɓaci. “Babana ina jinka miya haɗaku takai ga mari?”.
“Ban taɓa fatan dan na samu matsala da wata a cikinsu sai munzo gabanku ba. Amma tunda ita tafi zaɓar hakan a koda yaushe fine. Fita nai a gida tun safe ina wajen matsalar can data taso a company, na dawo kawai na samu ta cikamin sashe da ƙawayenta wai suna min gyara. A yanda suke komai kai tsaye ya tabbatar min ba yau ce rana ta farkon hakan ba. Korarsu kawai nai na ƙyaleta domin ita tasan bana son yanke hukunci cikin fushi, amma saita biyoni bayan nace ta ƙyaleni a yunƙurin farko da tai. Taya zata kawomin wasu ƴan iska sashe, ta san adadin abubuwan dana ajiye masu muhimmanci a ciki? Ko bamma ajiye komaiba ita bazatai tunani da hankalinta rashin dacewar kai wani can ɗin”.
“Inafa zata san abinda ya dace tunda a nuna mata barbaɗa magani shine kawai zaman aure”.
A harzuƙe Gwaggo Halima ta dubi Mommy mai maganar. “Nafi wlhy ki iya bakinki domin zai kaiki ya baroki allura ta tono galma”.
“Yo ta tono mana dan ubanta, abu mai sauƙi bayan ta tono ita galmar ta turbuɗata cikin ƙansa yanda ko mayen ƙarfe ƙaryarsa sake ganinta”.
Aifa nan take falon ya harmutse da hayaniya tsakanin Mommy da Gwaggo Halima. Mamaki al'ajab sukabi suka sanya Shareff cikin madaukakin imani. Yau kuma aminai biyune kema juna tujara haka akan abinda suke ganin shine mafi ƙololuwar alkairi a garesu idan suka ƙulla. Kai duniya ina zaki kaimu ne haka?. Da ƙyar su Daddy suka samu sukai shiru. Gwaggo kam tayi kamar bata a falon tai muƙutt da cuno baki gaba ita a dole takai maƙurar ɓacin ran abinda su Mommyn ke aikatawa. Acan ƙasan ranta kuwa dariya taketa kwasa. Yanzu kam Abba ne ya amshe da zancen yana mai fuskantar Fadwa.
“K shashashar inace da zaki bama ƙawaye damar shiga ɗakin mijinki? Haka kikaga iyayenki na mana? Wace irin mace ce ke da baki kishin mijinki? Ai wannan jama kanki rainine ma wajen su ƙawayen naki da shi kansa mijinkin. To saurara ki jini, daga rana mai kama irin tayau, hakan ta sake faruwa ni da kaina zan hukuntaki sannan shima nasa ya hukuntaki tunda koba aure tsakaninku Yayanki ne.. Kinaji na da ƙyau?”.
Hawaye ta ta share tana jinjina kanta. “Zan kiyaye Abba insha ALLAHU. Amma Abba dama fa haushina yakeji, dan dama a kwanakin nan banda wulakantani babu abinda yakeyi saboda ya ƙara aure. Baya ganin kowa a gidan sai ita ƴar gwal.....”
“Shiyyasa kuka dage boka da matsubbata ke da uwarki domin sabautamin ɗa. Su Malika na kawo miki barbaɗe-barbaɗe kina faman zuba masa dare da rana. To wlhy babu lallai babu dole tun kan ai nisa sai ya datse igiyar auren tunda bake kaɗaice mace ba a duniya......”
“Dan ALLAH Nafisa idan baki sakashi ya datse igiyar aurensu ba baki cika uwarsa ba, kuma shi din bai haifuba a cikinki...”
“Haka kikace?”.
“Eh na faɗa. bandama ƙaddara mi Fadwa zatai da wani Shareff can. Ko dama kun ƙulla a haɗasu aure dan ku dinga maidamin yarinya baiwarku”.
“Hahaha yo baiwa kuma ta nawa Halima. Sai dai wata kuma dan ita kam ta riga ta gama zama labari”.
Ƙara hargitsewa falon yay, da ƙyar yanzu kam Abie da Abba suka sakasu yin shiru, dan Daddy dai ya mugun shaƙa zuciyarsa har wani zallo takeyi, gata tokare a maƙoshinsa kamar yay amanta ya huta.............✍



_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*


YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:
07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇
09134848107


*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*
[11/23, 10:16 PM] My Zafafa: *_Typing📲_*




*_❤‍🔥BABU SO....!!❤‍🔥_*
_(Miya kawo kishi?)_



*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*

*_BABU SO👉🏻AREWABOOKS_*

https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718


*_72_*



.........Abincin yakeci cike da nazarin kowaccensu. Fadwa nayin komaine a taka tsantsan na gudun yin kuskure fatanta komai ya wuce. Yayinda Anaam ke komanta kai tsaye hankalinta kacokan naga abincin da takeci tamkar ta manta da zaman kowannensu a wajen ma. A haka dai suka kammala Fadwa ta fara gyara wajen, dakatar da ita yay dan haka ta koma ta zauna. Anaam data ɗauka waya yayma magana, itama ta ajiye suka bashi hankalinsu. Nasiha ya fara musu a nutse tare da jan gargaɗi. Daga ƙarshe cikin kaushin murya da tabbatarwa ya ɗan bubbuga table ɗin da yatsansa.
       “Bazan lalace wajen zargi akan ku balle ƙin cin duk abinda kuka bani ba, sai dai zan tabbatar muku, duk wadda ta zuba wani abu koda a ruwan sha ɗinane domin samun wani cikar burinta ban yafe mata ba. Kuma idan na kamata bazan yafe mataba ko iya cigaba da zama da ita duk da babu tsarin rabuwa da ɗayanku a zuciyata. Shawara ya rage naku, kumu haɗu mu zauna don ALLAH cikin soyayya da mutunta juna, ko kuma kowa ya ɗauka layin da yaga zai dace da shi a shirye nake wajen maganin duk wadda take tunanin zata iya fin ƙarfi na. Na ƙarshe respecting juna da kuma iyayenmu. Wlhy idan wata a cikinku ta sake kuskuren yin abinda bai dace ba akan wani ko wata a cikin iyayrenmu sai na sakata nadama ta har abada, ya rage naku ku dawo hankalinku kokuma ku ɗaura daga inda kuka tsaya”.
       Har ƙasan zuciya kausasan gargaɗinsa sun shigesu, sai dai sunfi ratsa Fadwa musamman akan zuba masa magani a abinci fiye da Anaam da wannan gaɓar bama komai ta fahinta ba. Amma dangane da girmama iyayensu da juna ya shigeta matuƙa, dan yanayinsa ya tabbatar musu zai iya komai. Bayan ya sallamesu kowacce ta nufi ɓangarenta tana ƙullawa da kwancewa. Shima fita yay a gidan zuwa can gidansu gaida su Mommy tunda yanzu Daddy ya janye masa sharaɗin hana zuwa gidan. Sai dai koda yaje ya samu Mommy da Gwaggo basa nan. Bai so haka ba, dan yazone takanas ya lallashi mommy ɗin da bata haƙuri akan komai ma daya faru, sannan ya yini da ita yau. Gidan su Anaam ma ya iske Mamie da aunty Mimi sun fita, dole dai ya koma gida dan gwara yaje ya huta kawai shima.

      A ɓangaren Mommy da Gwaggo gidajen su aunty Malika sukaje sukai musu tatas, inda akai hargitsi bana wasa ba har saida takai an gurfana a kotun baba Ibrahim. Shima al'amarin ya ɓata masa rai, dan yajima dajin tsiyatakun da su Malikar keyi a gidajen aurensu. Sai gashi yau suna neman saka Fadwa itama kuma abin takaicin harda haɗin kan mahaifiyarta. Sosai yayima Gwaggo Halima dake matsayin matar ɗan uwansa faɗa, ya nuna mata kuskurenta na son ɗaura ɗiyarta akan bigiren da zai rusa rayuwarta a dunuya da lahira. Suma kuma su Mommy yay musu nasu faɗan, dan tun farko da basu nunama Fadwa komai tayi a gidan aurenta dai-dai bane daba haka ba. Yanzu gashi sun ɗanɗana mata tana niyyar zartasu kuma sun shiga damuwa, ta riga kuma ta ɗanɗana ba lallai abin ya iya barinta ta sauƙi ba.
       Nasihar Baba Ibrahim bata canja komai a jin haushin juna da Mommy da Gwaggo Halima keyi ba. Sai ma ƙara jin zafin juna dan kowacce nada sirrin ƴar uwarta a tafin hannu. Kuma kowacce taci alwashin nunama ƴar uwarta fawa ɗinta akan ƴaƴan nasu da kuma mazajensu da suke amsa yayanninsu. Da haka aka sake rabuwa baran-baran.....

____________________________

          Ga Shareff kam tun

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login