Showing 144001 words to 147000 words out of 178785 words
_(Miya kawo kishi?)_
*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*
*_BABU SO👉🏻AREWABOOKS_*
https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718
*_68_*
........Yau ta kasance cikar kwana bakwai na kwanakin Anaam a gidan, miji zai koma hanun Fadwa kenan. Sai dai kuma tunda garin ma ya waye bata ganshi ba. Tunda sassafe ya fice sakamakon kiran daya samu daga Engineer ɗin dake kula da aikin ginin wani ƙaton mall da sukeyi na wasu larabawa da suka buɗe branch anan kano. Shine ya zana mall ɗin kamfaninsu kuma ke ginawa, to yanzu a dalilin wani mai musu zagon ƙasa wata matsala ke neman shigowa.
Su dukansu ma babu wanda ya san baya gidan sai zuwan Khaleel tare da mai haɗama Anaam tv. Anaam taji wani iri dan a tunaninta ko abinda ya faru a daren jiya ne ya sakashi fitar tunda sassafe. Amma sai batace komai ba dama duk sukuku ta tashi. Itama Fadwan ta jingina fitar tasa ne akan abinda ya faru jiya da dare, sai dai saɓanin Anaam ita tsorone ya kamata da tunanin kodai ya gano tana tiktok ne? To amma idan hakane ai ba fita zaiba wayarta zai fara bincike. Sosai ta shiga taraddadi, cikin tsaida mafita ɗaya ta nema zuwan su Sima gareta. Cikin ƙanƙanin lokaci kuwa sai gasu sun iso harda Bibah da Siyyah suka ƙulle a ɗaki suna tattaunawa. Maman Abu ta girgiza kai da jinjina wautar Fadwa matuƙa, abinda duk ya faru tsakaninta da Shareff jiya ta gani, ta kuma fahimci raye-rayen da Fadwan keyi Shareff ɗin bai sani ba. Shiyyasa ta tsorata da tunanin ya ganta a jiya. Inama Fadwan zata saurareta data bata shawarar dawowa kan hanya domin gujema zuwan ranar dana sani, dan ta tabbata waɗan nan ƙawayen nata data bama amanar rayuwarta sune waɗan da zasu fara kaita ƙasa kafin su Aunty Malika. Mata irin Fadwa da yawa rashin alƙiblar kansu ke tarwatsa musu rayuwa da nasarori koda ace akwai wasu ƙyawawan halaye abin dubi tattare da su, kafin su farga taurarinsu ya gama disashewa a idon duk wanda zai kasance zagaye dasu, a lokacin kuma dukkan damanmakinsu sun kufcewa yunƙurinsu da taɗesu ga zuwa nasarar da su suke kallo a cikin idanunsu duk da suna ƙoƙarin cimmatane a cikin kuskure na son zuciya.
Anaam kam dai sukuku ta yini har yamma akan rashin ganinsa, zuwa la'asar sai zuciyarta ta kasa dauriyar ɗauka dan koba komai shi ba abin yadawarta bane ba. Wayarta ta ɗauka, ta gwada kiransa yafi sau goma kafin tai ƙuru ta danna number da ko saving nata ta gagarayi amma ta gama haddaceta tun a kiran da yay mata jiya bayan ta gama ganin kundin sirrinsa mai ɗauke da sirrikan da ita kaɗai suka shafa.
A lokacin yana zaune ne ya gama yin liƙis da gajiya da yunwa. Dan duk yau ruwa kawai yake iya kaiwa bakinsa tsabar zafin da kansa ya ɗauka akan al'amarin dake zagaye da su. Bashi ba hatta Fharhan da Khaleel da wasu a cikin staff ɗinsa a jigace suke. Juma'a guda haka ta riskesa ko wanka baiba da kayan dake jikinsa kanana sukaje sallar juma'a. Baiko duba waye mai kiran ba ya kai kunnensa. Can ƙasan maƙoshi tai sallama kamar maijin tsoro. Curo wayar yay a kunensa da mamaki, ganin tabbacin ita ɗince ya maida yana sauke wata nannauyar ajiyar zuciya da har tana iya jiyowa. Ta ɗan murmusa daga can, tare da langaɓe kai kamar tana a gabansa.
“Yayaaa!”.
Yanda ta ambaci sunan cikin ƴar shagwaɓa ta saka tsigar jikinsa tashi, yaja numfashi a slowly.
“Uhhum autar mata”.
Ta saki siririyar dariyar data ƙara tunzurashi. “Yaya ka rufamin asiri da sunan nan kar mata sumin duka”.
Murmushi yayi a karon farko, da ɗan gyara zamansa. “Kice na faɗa da shela ko hakan zaisa su tabbatar ke ɗin ta ƙarshe ce tabbacin Autarsu”.
“Nidai ba ruwana gaskiya. Wai kaje ina ne?”.
“Yawo mana”.
“Yawo fa Yaya? Ai nasan baka yawo, kai da kullum kana company ina zaka aiki, ina ka dawo aiki”.
“Oho shaidar da kikamin kenan?”.
“ALLAH gaskiya na faɗa. Dan ALLAH ina kaje?”.
“Kina kewata ne?”.
Kamar tana a gabansa ta rufe fuskarta da filo. “Ɗan kaɗan”.
Dariya yayi kam yanzu har Fharhan na kallonsa.
“Wato ɗan kaɗan? Autar mata kiji tsoron ALLAH fa”.
“To ai nama daina ji yanzu gaba ɗaya”.
“Oh-oh, maimakon na samu ƙari sai a kwashemin ma duka? Aji tausayina mana diamond girl”.
Sosai take dariya sai dai a nutse, (kece farin cikin duniyata) ya ayyana a cikin zuciyarsa yana mai lumshe idanunsa. Ji yake tamkar yaga kansa a gabanta kawai. Daga can Anaam data tsagaita dariyarta da iya gaskiyarta tace, “Am serious gidan babu daɗi dan ALLAH ka dawo”.
Da ƙyar ya iya danne zuciyarsa dake tsalle-tsalle, murya can ƙasan maƙoshi yace, “Mi kika tanada min ne?”.
“Duk abinda kace kana so”.
“Kin tabbata ko minene shi zan samu?”.
“Ga wani ma tun kafin kazo”. Ta faɗa dayin kissing wayar. Har tsakkiyar kansa yaji saukarsa. Kafin ya samu damar cewa wani abu ta yanke wayar ƙit. Ƙoƙarin dakatar da ita yake amma bataki jisa ba, yay ƙoƙarin sake kiranta taƙi ta ɗaga, hanunsa ya kai yana murza goshinsa da cije lips.
Itako dariya takeyi daga can zuciyarta cike da farin ciki mai ban mamaki. A haka Aysha ta shigo falon ta sameta. “Blood wai kin san wace kwamacala na gani kuwa?”.
“A ina kenan?”.
Anaam ta faɗa tana tashi zaune da ƙyau. Cikin tsananin ɓacin rai Aysha takai zaune. “Wai ƴan iskan ƙawayen can na Fadwa fa naga takai sashen Yaya suna masa gyara”.
“What!! gyara fa?”.
“Wlhy na rantse miki gasu can ma kuwa”.
Miƙewa Anaam zatai Aysha ta maidata. “Kinga kwantar da hankalinki ba so nake kije ba. So nake kiyi duk yanda zakiyi Yaya ya dawo gidan nan yanzu shine kawai maganinsu. Dan yanzu in bai gani ba su Mommy zasu iya ƙaryatawa tunda ba san laifin Fadwan suke ba”.
Shiru Anaam tai tana kallon Aysha. Tabbas maganarta haka take, sai dai kuma ta yaya zata saka Shareff ɗin zuwa bayan yanzu suka gama waya ma.......
A lokacin da su suke shawarar yanda zai dawo gida a garesa ma akwai himmar hakance tattare da shi. Jiyay gaba ɗaya tattaunawar tasu ta gundiresa. Ya miƙe yana tattare takardun gabansa. “Fharhan kubar abinda ya rage zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu a ƙarasa. Tunda namayi magana da Abie sai zuwa gobe zamu tattauna da shi yau yana Abuja shi da su Daddy”.
Mamaki shimfiɗe a fuskar Fharhan yake kallonsa. “Dude amma kaine fa kace sai an ƙarasa komai yau miye na canja shawara?”.
“Na gaji ne, ga yunwa na neman fara katsamin hanjin ciki”.
“Uhhmyimm!!. Kodai soyayya malam. Lokaci yayi da zaka bar wani ɓoye-ɓoye ka buɗe mana mu kalla ko ma samu na kwaikwayo”.
“Banza ɗan sa ido”.
“Naji ba komai. In ka isa kace ƙarya na faɗa mana. Da an langare ana mana ciwo tunda kaji ka samu sai mukaji tsitt”.
Spoon dake cikin kofin daya sha coffee ya dauka ya jefa masa. Fharhan yabar wajen da gudu yana dariya. Gaba yay shima yana faɗin, “Munafuki mai barci da ido ɗaya. Haka zaka ƙare rayuwarka a bibiyar tawa bakai aure ba tuzurun banza”.
“Aniyarka ta bika wlhy, insha ALLAH nanda 2months zaku kaini”. Fharhan ya faɗa daga jikin motarsa yanama Shareff dakuwa.
Murmushi yay da buɗe mota ya shige batare daya sake tanka masa ba....
Tafiya yake amma ji yake kamar motar bata sauri, ya ƙara gudu tamakar mai shirin barin garin na kano. Cikin ƙanƙanin lokaci ya iso gidan, horn yayi har sau biyu amma maigadi bai buɗe masa ba. Yay dan tsaki da buɗe motar ya fita ya ƙarasa shiga da ƙafa da niyyar yima maigadin faɗa sai ya samu ashe yana bayi ne. Kansa kawai ya girgiza yay gaba, dan ya gwammace zuwa anjima ya shigo da motar kawai.
Harya nufi sashen Fadwa ya fasa, kai tsaye nasa sashen ya nufa dan yafi buƙatar watsama jikinsa ruwa kafin komai. Tun a ƴar barandar gaban sashen nasa yaci karo da takalman mata. Mamaki yay matuƙar kamashi wani gefen zuciyarsa kuma na ayyana masa ko Mommy ce da muƙarraban ta, to amma takalman basuyi kama da wanda Mommy zata iya sakawaba dan duk hills ne. Kamar mai tsoron shiga ya tura ƙofar a ɗarare.
Dai-dai nan Amal dake goge-goge a falon ta ɗago da tunanin Fadwa ce da taje ɗakko turaren mopping ta dawo. “Yauwa baby kin ɗakk....” sauran maganar ta maƙale a harshenta. Ƙaf yawun bakinta ya ƙafe ta saki towel ɗin hanunta ƙarami da take goge-gogen da shi.
Ana haka itama Bibah dake gyara bedroom ta kawo jiki zata fito, ai ba shiri ta koma da sauri cikin harbawar ƙirji. Sima dake kitchen ce ta shiga ƙwalama Amal kira, sai dai Amal ta kasa amsawa saboda tsabar firgita datai da ganin Shareff. Cikin ƙanƙanin lokaci idanunsa dake cike da gajiya sun matuƙar kaɗawa zuwa launi mai razani. Duk da baice da su komai ba kowacce a cikinsu jikinta rawa yakeyi, Amal sarkin tsoro ta fara daga hannaye sama cikin rantsuwa da rawar murya..
“Wlhy tallahi ba laifinmu bane ba yallaɓai, Fadwa ce ta sakamu mu taimaketa da aikin, amma ALLAH ba mune muka kawo kammu ba, kuma aikin kawai muke maka ba wani abu ba...”
“Eh wlhy aikin kawai mukeyi Yaya Shareff”. Cewar Siyyah cikin son karfafa kai dan ita bata ruɗe kamar Amal ba, amma daka ganta kasan a firgice take. Sima kam tuni ta fice a kitchen ta ƙofar baya, itace taje a birkice ta sanarma Fadwa dake kitchen tare da Mmn Abu ana haɗa abincin tarbar Shareff ɗin. Ita kaɗai ta nufo sashin a rikice, sai dai tana ƙoƙarin hana ruɗewar tata a zahiri saboda shawarar Sima.
Bibah dake bedroom kam taƙi fitowa, da sauri ta shiga kiran Gwaggo a waya. Tana ɗagawa ta sanar mata komai. “Bibah k mahaukaciyar inace da zaki biyema wannan sakarar yarinyar keda ke shirin shiga gidan matsayin matar gida. Duk yandama za'ai karki sake ki yarda Mustapha ya ganki a cikinsu. Inba haka ba kini sai k da shi sai dai kallo”.
“Gwaggo kar kimun haka dan ALLAH”.
“To laifinama zaki gani kenan? Yanzu banda ku shashshune taya zaku zauna ƙawa na baku aiki”.
“Wlhy Gwaggo na biye musu ne kawai dan dan tace ɗakinsa ne, nidai ki taimakeni yaya zanyi na fito gashi can a falo ya tsare su Amal.”
“Humm sai ki jira matar gidan ta shigo, kiyi amfani da wannan damar kiyi wuff ki fita batare daya ganki ba”.
“To to...to Gwaggo nagode sosai, idan da wata matsala zan kiraki dan ALLAH”.
“Naji”.
Gwaggon ta amsa tana yanke wayar. Cikin laɓe baki.
Shigowar Fadwa tayi dai-dai da saukema Siyyah data matsoshi cikin kwarkasa lafiyayyen mari da sai da taga taurari masu maƙata😆😜. Ba ita da aka maraba hatta Amaal sai da ta dafe kuncinta da zabura baya kaɗan ya rage ta faɗa kan kujerar dining.
“Ya salam! Soulmate mari kuma? Shamsiyya ce fa?”.
Wani matsiyacin kallo ya jefeta da shi fuskarsa na wani irin fusatar azabar dake soya masa ƙirji. Ƙasa tai da idanunta, amma saita matso garesa cikin dauriya ita a dole tana son fahimtar da shi.........✍
_ZAFAFA BIYAR_
*_INAYAH_*
_MamuhGee_
*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_
*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_
*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_
*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_
_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*
YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾
ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070
SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:
07040727902
IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇
09134848107
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*
[11/23, 10:16 PM] My Zafafa: *_Typing📲_*
*_❤🔥BABU SO....!!❤🔥_*
_(Miya kawo kishi?)_
*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*
*_BABU SO👉🏻AREWABOOKS_*
https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718
*_69_*
............“Soulmate! Please ka s......”
Da sauri ya ɗaga mata hannu, da karkaɗa mata yatsarsa manuniya lips ɗinsa na rawa alamar gargaɗi. Sai dai ya kasa furta komai saboda takaici.
Dole ta dakata jikinta na wani irin tsumar tashin hankali, hawaye rige-rigen sakko mata sukeyi.
Har zai shige ya sake juyowa “Ku kuma na baku minti ɗaya tak, ku kwashi tarkacenku ku ficemin anan kafin na fara ɓallaku ƴan iska!!”.
Ai har turereniya ake na fita tsakanin Amaal da Siyyah, dai-dai nan Bibah ta fito daga bedroom ɗinsa fuskarta a lulluɓe yanda bai ganta da ƙyau ba. Da gudu itama ta fice. Kansa dake sara masa ya dafe da sauri, jin jiri na neman kwasarsa ya dafe bango da sauri yana ambaton sunan ALLAH, da ƙyar ya iya ƙarasa kai kansa cikin ɗakin ya zube a kujera yanajin raɗaɗi da ƙunar zuciya.....
Fitowar su Amal da gudu daga sashen Shareff ɗin ya saka Anaam da Aysha kallon juna baki buɗe, Aysha ta zunguri Anaam “Blood jeki kiga mike faruwa? Naga oganiyar tasu ita bata fito ba”.
“A'a blood babu buƙatar haka, wannan tsakaninta da mijinta ne ai. Dama su nafi buƙatar yaci ubansu, amma ita matsalartace ita da shi”.
“ALLAH k banza ce, wlhy idan kece hakan ta faru a kanki ba ganowaba har dariyama sai tayi zamanyi”.
Dariya Anaam ta saki da kaima Aysha duka. “Kefa wlhy muguwa ce”.
“Babu wani mugunta, dan ALLAH kije”.
“Okay ina zuwa”.
Ta faɗa da nufar sashen maigidan. Hango Anaam yasa da sauri Fadwa dake ƙoƙarin fitowa komawa ciki, bedroom ɗinsa ta nufa da ƴar sassarfa. Zuwa yanzu ya miƙe yana cire kayan jikinsa, shigowarta baisa ya juyo ya kalleta ba, hakan ya ƙara sanyaya jikinta, amma sai ta danne ta ƙarasa gabansa. Tasanshi mai saurin karayane da ganin hawaye, dan haka ta fara matsosu. “Soulmate dan ALLAH ka saurareni na maka bayani. Wlhy ba.....”
“Get out of my room!! Idan ba hakaba duk abinda nai miki ke kika saya stupid!!”. ya dakatar da ita a matuƙar tsawace.
“Please Soulmate n...”
Saukar lafiyayyen mari a saman fuskarta ya hanata ƙarasawa. .
Cak Anaam dake ƙoƙarin shigowa ta tsaya, ba ƙaramin harbawa ƙirjinta yay da jin ƙarar marin ba. Wani irin ihun kuka mai ƙarfi da Fadwa ta saki, ya sata toshe kunenta, da sauri ta juya ta fice zuciyarta na bugawa da sauri-sauri. Shiko baiko nuna yasan Fadwa tanai ba ya shige bathroom abinsa. Hankali tashe Fadwa ta fita zuwa sashenta dafe da fuskarta datai jazur abinka da fara. Mamanta ta fara kira tana kuka, sai dai ba'a ɗaga wayarba, sai kawai ta koma kiran Mommy.
Mommy dake zaune ta kalla wayar taja tsaki, haka kawai takeji a ranta ƙofari Fadwa ta kawo mata. Kamar karta ɗauka sai kuma dai ta ɗaga takai kunne batare da tayi magana ba. Maimakin sallama da kuka ta fara cin karo, Fadwa dake kiran ta shiga uku ta shiga zayyanoma Mommy cewar Shareff ya mareta, dan kawai ƙawayenta sunzo Anaam ta tunzuroshi. Dama kwana biyun nan babu abinda yake mata sai wulaƙanci akan Anaam ɗin....
“Mari!!?”.
Mommy ta faɗa a razane.
Kuka Fadwa ta sake mashe mata da shi, hakan yasa Mommy yanke wayar da sauri. Aysha ta kira, cikin sa'a kuwa wayar na'a hanunta ta ɗaga.
“K faɗamin, mike faruwa Yayanku ya mari matarsa? Akan ƴar iskar yarinyarnan ne ko?”.
Aysha da dama yanzu Anaam ke faɗa mata cikin tashin hakanli ta taɓe baki. “Wlhy Mommy babu ruwan Anaam. Ƙawayenta ta kawo suna masa wai gyaren sashensa shine ya shigo ya samesu, harda su Shamsiyya”.
“Shine dan bata da kunya ta kirani tana kawomin ƙararsa, to lallai ya kamata a wannan gaɓar na takama yarinyarnan birki dan na kula neman maidani ƴar isaka takeyi.”
Aysha tace, “To Mommy bakece ke biye mataba da su Gwaggo. Kamarma itace kika haifa bashi Yayan ba. Ita Gwaggo Haliman ma ba tanayin komai bane dan ɗiyarta, ki duba akan auren Anaam yanda kika biye mata kuka hau kansa kukaita zagi gashi kinaji kina gani Abba ya hanashi zuwa ki gansa ma amma ita kullum tana waya da ƴarta. Kuma wlhy yanzu kusan kullum su Aunty Malika suna gidan nan kawo mata magani anata zubama Yaya a abinci....”
“Na shiga uku, magani kuma Aysha?”.
“Wlhy Mommy da gaske nakeyi, to duk kusancinki dasu Aunty Malika matsayinsu na ƴan uwanki dasu ake haɗa kan cutar da Yaya, jiya bakiga abubuwan da suka kawo mata ba harda zoben mallaka wai bazai sake kallon wata mace ba a duniya sai ita sai abinda tace masa ko ke albarka, na rasa yaushe suka ɗinke da Gwaggo Halima haka har suke abu batare da ke kin sani ba keda Gwaggo”.
“Na shiga uku, ni halima zataci amana ta haɗa kai dasu Malika a sabautamun yaro saboda ƴarta tayi farin ciki?....”
Fitt Anaam ta ƙwace wayar daga hanun Aysha ta kashe. “Blood kinada hankali kuwa? Ya zaki faɗama Mommy irin wannan maganar?”.
“Ya bazan faɗa mataba Anaam. Kin san ko suwaye su aunty Safarah? Wlhy rashin faɗar shine mafi munin kuskure dan hatta ke da kanki sai sun sabauta rayuwarki, ɗan sauran zuminci kuma da muke tattali su ɓarar mana da shi. Ita kanta Fadwa ɗin taimakonta nayi, dan wata ƙungiya garesu ƴan baza'a zauna da kishiya ba, inma an zauna da ita saita koma tamkar babu ita a wajen miji, kina tunanin a hankali bajan ra'ayinta zasu cigaba dayi ba harta koma cikinsu. Koba komai ita ɗin jininmu ce, yana da ƙyau