Showing 159001 words to 162000 words out of 178785 words
din ma dai harda kukanta. Amma baiyi nisaba kamar na waccan ranar. Tasha albarka kala-kala tare da daɗaɗan kalaman da suka sanyaya mata rai raɗaɗin taji ya raguma. ya taimaka mata ta shiga ruwan zafi kafin su dawo gadon ya bita da tukuycin tausar data sakata yin barci. Ajiyar zuciya ya sauke mai nauyi da sake sakar mata kiss a lips da idanunta yana faɗin, “ALLAH yay miki albarka”. Daga haka shima ya rungumeta suka lula duniyar barcin tare..
*_WASHE GARI_*
Rashin sabon ɗaukar gabaran gida kafin fita aiki yasa saida taimakonsa dana Aysha suka shirya fita akan lokaci, gashi sai langaɓewa take wai jiya ya wahal da ita. Shi dai nashi murmushi kawai, itako tana faman tura baki da tsuke fuska. Kamar kullum tayi ƙyau cikin kayan hidimar ƙasa, sai dai ta ɗaura Abaya yau a sama sannan ta naɗa veil ɗin abayar a kanta. Ƙin fitowa tai har saida ya shiga sashen Fadwa sukai sallama ya fito sannan ta fito suka wuce. A hanya take tambayarsa yaushe zata fara koyan tata motar. Shiru kamar bazaice komai ba. Sai da ya kaucema mai napep ɗin dake neman shiga masa hannu sannan ya ɗan dubeta bayan yaja tsaki da yima mai napep ɗin daƙuwa.
“Mu bari weekend, idan kuma Fadwa ta koya miki to?”.
Baki ta tura gaba sai dai batace komai ba. Hakan yasashi fahimtar zancen nasa bai amsu ba. Ya girgiza kai kawai ransa fal mamakin kishin matan nasa. Ita kanta Fadwan daru ya barta tanayi akan fitar tashi da Anaam. Wai sai dai idan ranar girkintane kawai zasuke tafiya tare. Amma ranar nata bata yarda ba. Itama baice mata komaiba yay fitowarsa, to ga Anaam ɗin ma yace Fadwa ta koya mata mota ta nuna bata so.
Ita ya fara saukewa, da gargaɗi mai girma akan Yaseer sannan yay gaba. Ya samu tarba ta musamman a wajen staffs nashi. Inda sukai ƴar gajeriyar walima lokacin break acewarsu tunda ba'ai ta aure ba. Kasancewar ya samu aiki da yawa Khaleel ne yaje ya maida Anaam gida, shiko sai bayan isha'i ma ya kona gidan. Sanda ya iso ya iske komai yanda yake buƙata, dan dawowar Anaam ɗin tayi amfani sosai.
Yau ɗin ma dai yasha sharafinsa, inda mutuniyar tasa taita masa raki, baibi takanta ba, amma yabita a sannu gudun ɓaro aiki. Washe gari har wani farin ciki takeji zai koma wajen Fadwa ta huta, duk da dai kishinsa na zaune daram a ranta babu sassauci. Safiyar talata sai dai yayma Fadwa ƙaramin hauka akan fitarsa da Anaam sannan suka samu dai-daito, dan ta dage bazai ɗauka Anaam ba dan ranar girkintane. Amma ganin ya juye mata yanda bata kauna dole tai shiru, ya fita ya barta tana rusar kuka
Haka kwanaki suka cigaba da tafiya, tun Anaam na masa raki a duk ranar girkinta harta fara zama ƴar hannu, duk salon da yazo mata da shi zata amsa kuma ta bashi haɗin kai yanda zai samu farin ciki. Babu abinda ya dameta da sabgar Fadwa, abinda ke gabanta kawai takeyi, sai dai kuma bata ragawa idan Fadwan ta shiga shirginta. Dan kuwa saita tsefeta tas ake samun zaman lafiya a gidan. Shareff yayi kurarin yayi masifar akan tsiwarta amma a banza, dan tace in ba'a shiga gonartaba bazata shiga ta mutum ba. Ita kuma Fadwa tsokanar magana ne matsalarta. Komai ta gani saita tanka. Duk kankantarsa sai tayi magana ga Shareff ɗin ko ga Anaam. Sauki ɗaya aka samu ta rage kai ƙararsa wajen iyaye, koda yake yanzu fa itada Mommy babu wani mutunci, dan kuwa ranar daya kaisu gidan su duka domin gaishesu Anaam tasha kallo, Mommy ta dinga yamutse-yamutse, abibda ya bata dariya Fadwa zata fara iyayi ita masu Mommy, mommy ta gwaleta. Aiko ta fita baki gumtse tana danne dariya. Tuni ta gudu gidansu wajen Mamie, inda ta ruƙunƙumesu harda kukanta wai tayi missing nasu. Suma sunyi missing nata matuƙa, amma sai suka dinga lallashinta. lokacin da Fadwa da Shareff suka shigo gaida su Abie ɗin kowa yayi mamaki Fadwa, dan yau babu rashin kunya ta gaishesu da girmamawa saboda tsoron butsutsun Shareff, dan kafin su taho ya buga mata warning bana wasa ba akan su Abie ɗin. Sai kuma abinda Mommy tai mata a gaban Anaam ya sake dagula mata lissafi.
Zuwansu gidan da kwana biyu maganar auren Bibah da Shareff ta fito, dan kuwa a kwanakin nan dama sunata bugawa ne tsakaninsa da su Mommy, ta kuma tabbatar masa idan yana fa son zama da matansa sai ya auri Bibah, a gefe kuwa burinta ita da Gwaggo ya auri Bibahn su fidda Fadwa da Anaam kuma a gidan dan sun ɗau alwashin bazasu barshi zama da su ba.
Wannan maganar aure itace ta tada gagarumar ƙurar data tada hankalin kowa a family guda biyu, dan kuwa sarƙa-sarƙar tayi yawa ai. Saboda Shareff na ɗan gatan duniya sai a dinga haɗa masa ƴaƴan dangi yana aure dai. Mamie da Abie dai basu ce komai ba, sun kuma yima Anaam nasiha akan koda a fuska karta nunama Shareff komai. Taji ciwo a ranta, sannan taci kuka amma sai tabi maganar iyayenta.
A ɓangaren Gwaggo Halima kuwa sabon yaƙi ne ya tashi tsakaninta da su Mommy, nanfa aka shiga ƴar tone tonen asiri ta yanda har akaima Shareff asirin daya nisantashi da su Abie. Abubuwa dai babu daɗi, dan tsabar takaicinsu Daddy har sai da yaji ƙwalla sun cika masa ido. Gwaggo Halima tace sai Fadwa ta koma gida babanta yace ƙarya haramun, idan Fadwa ta rrabuda Shareff ta nema wani uban bashi ba. To itama dai tana son mijinta, duk da kuwa maganar zai ƙara aure yake, kuma da kawarta data san sirrikanta.
Ruguntsumin masifa akeci na haƙiƙa a wannan gaɓa tsakanin Fadwa da Bibah, Gwaggo Halima da su Mommy da maman bibah. A gefe kuma ga shirye-shiryen bikin Aysha, sai kuma Khaleel da tasa budurwar shima. Sosai hankalin Shareff ya kasu. Ga company, ga rikicin Mommy da Gwaggo data noƙe tabar Mommy na raba hali. Ga rikicin Fadwa, Dan ita Anaam da sauƙi. Bata fasa komai da take masa ba amma yabar ganin murmushinta gaba ɗaya itama. Dama zuwa yanzu da motarta take fita wajen aiki kasancewar ta ƙware, dan bai kulla sati biyu yana koya mataba da yake ta saka kanta sai gashi ta iya, idan zasu fita yana gaba tana biye da shi, komuma tana gaban yana biye da ita duk dai dan ta ƙara sanin hanya.
An shiga shagalin bikin Aysha ne cikin ruguntsumin maganar Bibah, amma hakan bai hana Shareff sharɗantama matan nasa zuwa taron bikin ba. To Anaam ma basai an sharɗanta mata ba. Bikin Aminiya ya wuce tace bata zuwa, hakama Yaya Khaleel. Dan haka tun ranar kamu tace masa zata koma can gidan gaba ɗaya har sai biki ya tashi. Da farko yace bai amince ba, tako saka masa kuka. Da farko shareta yayi, sai dai ganin kukan nata bana kare bane yace taje cikin fushi. Sai kuma jikinta yay sanyi.
Yayi zaton zai taso aiki ya tarar ta wuce, sai ya samu tana gida babu ma niyyar tafiyar tare da ita. Ganin kallon da yake binta da shi ya sata tunzura baki gaba ta ɗauke kanta gefe.
Baki ya ɗan taɓe, “Motar ce babu mai komi?”.
“Ni na fasa”.
Ta faɗa idonta na cikowa da ƙwalla.
“Dalili?”.
Kuka ta fashe masa dashi. “Toni ya kake so nayine dan ALLAH Yaya. Taya zanje wani waje kana jin haushina. Salon kawai kasa ALLAH ya sakani a wuta”.
Ɗan murmushi yayi da girgiza kansa yana furzar da huci. “Ni bance ina fushi dake ba kar kimun sharri, kune dai kuke fushi dani akan abinda na tabbatar muku nima bana ra'ayinsa. Mi zanyi da wata Bibah can da har zamu zauna kuna dagula min lissafi. Kun haɗe kai ku a dole bakwa son kishiya. Kun san tun yaushe ake maganar nan ina ta yaƙin ganin bata fitaba? amma kuke ɗaukar laifi kuna ɗauramin. Koda yake ke nagama kamar baki damu da zuwan amaryar tawa ba, dan kwanakin nan wata ƙiba kikeyi da haske ƙyawu na musamman na fita a fuskarki, kamar wata black American”.
Throw pillows ta ɗauka ta fara jefa masa. Ya shiga karewa yana dariya. Ganin haka ya sata mikewa ta haye kansa tana cigaba da kai masa kananun duka da pillow. Dariya yake mata da son kwace filon yana karewa, har dai ALLAH ya bashi sa'a ya damƙe hanun ya mirgina ta koma ƙasa yana a sama. Turesa ta farayi shi kuma yana kai mata kisses a wuyanta zuwa ƙirji. Kukan shagwaɓa ta fara masa ya koma mata cakulkule dole ta fara ƙyarƙyala dariya. Daga haka labarin ya canja aka koma neman lada. Dama a kame yake kwanakin nan ko nauyi bai iya saukewa saboda zafin da kansa ya ɗauka matuƙa............✍
_ZAFAFA BIYAR_
*_INAYAH_*
_MamuhGee_
*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_
*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_
*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_
*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_
_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*
YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾
ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070
SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:
07040727902
IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇
09134848107
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*
[11/23, 10:16 PM] My Zafafa: *_Typing📲_*
*_❤🔥BABU SO....!!❤🔥_*
_(Miya kawo kishi?)_
*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*
*_BABU SO👉🏻AREWABOOKS_*
https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718
*_76_*
..........Sun iso gidan biki inda yake tanƙam da jama'a. Dan maza nata shirin wucewa massallaci saboda an haɗe ɗaurin auren waje guda har na Khaleel domin sauƙaƙawa mutane. Cikin takama da isa Gwaggo Halima da Fadwa suka shigo cikin gidan, anan fa kallo ya koma sama dan ko makaho ya shafa yasan naira ta zauna. Kai tsaye sashen Mom suka nufa dan ko kallon sashen Mommy a yanzu Gwaggo Halima batayi a gidan balle Gwaggo. Mom da babu ruwanta dama tai musu tarba ta mutuntawa duk da kuwa tunda aka tsira bikin sai yau kowa yaga idon Gwaggo Halima a gidan. Tadai aikoma Abba da Daddy Da mom gudun mawa. Shi kansa Khaleel mota ta danƙara masa duk dan cusama Mommy haushi. Tuni ƴar rahoton Gwaggo taje ta sanar mata isowar su Fadwan. Tai murmushi mai alamomi da yawa tana mai miƙewa, cikin toilet ɗinta ta shiga, duk da kuwa ta hana kowa shiga mata bedroom dama. Amma duk da haka bata yarda ta tsaya iya bedroom tai wayarba. Daga can aka ɗaga, fuskarta ƙawace da murmushi cikin bada umarni kuma tace, “Ki tabbatar da an ɗaura aure ki tura masa, dan ina son maimakon su iso gida da labarin farin cikin an gama ɗaurin aure lafiya, labarin ya canja”. Batako jira amsa ba ta kashe wayar gaba ɗaya.
Cike da farin cikin sake aurar da yaransu lafiya su Daddy suka bar gida, tare da tawagar sauran ƴaƴansu su Shareff da ango Khaleel da tarin abokansa da ƴan uwa da abokan arziƙi. An fara yin sallar juma'a, sannan aka ɗaura auren Khaleel matsayinsa na babba, sai na Aysha da nata angon. Nan fa bakin kowa ya washe anata gaisuwa musamman su babban Yaya Shareff da Maheer. Anguna kam ai ba'a magana. Bakunansu har kunne ko gonar audiga albarka. Daga massallaci aka kwashi tawaga zuwa hall ɗin da aka shirya walimar cin abinci ta iya mazan kawai kamar yanda su Daddyn kanyi a duk aurarrakin ƴaƴansu.
Ana tsaka da cin abinci saƙo ya shigo masa. Shi dama ba abincin yakema ci ba, yana charting ne da Anaam ta WhatsApp. Baibi takan saƙon ba ya fita da nufin rufe datan sai Anaam ta sake turo massege, ya koma da nufin buɗewa ya gani hanunsa ya buɗe wancan a mistake. Ganin videos da yawa ya bashi mamaki, sai yay tunanin shiga ɗaya a ciki yaga minene. Gabansa yay wani irin faɗuwa sakamakon cin karo da Fadwa, best ce sanye jikinta fara da dogon wando, kanta babu ɗan kwali, da sauri ya fito, mikewa yay zai bar hall ɗin dan bai kamata ya gani a gaban wani ba. Ya fito sai ya samu wasu a abokan Khaleel tsaye su kusan huɗu tsaye, da alama suma sun fitone susha iska. Suka gaisheshi ya amsa musu da fara'a, harya gota su sai ya tsinkayi muryar wani a cikinsu na faɗin,
“Tabb bala'i, Mubeen da'alama yau zamusha kallo a tiktok. Gasu Sufi nan sun taɓo mutuniyarka Fady Babie”.
Wanda aka kira Mubeen yaja tsaki, “Shegiyar yarinyar nan ai su Sufi ɗinne dai-dai da ita. Ƙawartace jiya taima Ɗan soja wani Comment ɗin rainin wayo shine fa yay mata tatas ya kuma ce yanada video ɗinta da taje ɗakin wani guy, idan bata kama kantaba ana gab da cin kasuwarta a tiktok, shine ita mai bakin akku Fadwan ta maida murtani jiya da dare, ai shagalin nan ne yasa bakama luraba, tun jiya aka fara faɗan har suna zasu ɗakkoma su M soja ƴan sanda, shine shi Sufi ɗin ya shiga faɗan”.
“Oh dama haka akai, taɓɗi jan. Ai dama ina fatan naga wanda zai kawo ƙarshen ƴan iskan yaran nan, musamman Fadwa ɗin nan ta cika ɗaukar kanta wata tsiya. Ƴar iska tayi auren ma kamar batai ba”.
“Ai bazaka ganeba yarinyarce ta haɗu, wlhy da farko ban yarda bahausa bace ƴar arewa. Irin zuƙaƙan matan nan ai dole suyi girman kai dan ALLAH ya basu. Idan fa tai shigar ƙanan kaya kamar wata balarabiya”.
Dariya mai maganar farkon yayi, “Shege ka ƙyasa kenan, to tana dai da aure, akwai wani room mate ɗina, ya rantsemin idan yaga yarinyar nan har hankalinsa tashi yake, har saida takai sai ya dinga wassafata a ransa ya buƙatarsa ta biya yake samun nutsuwa”.
A tare suka kwashe da dariya. ”Kai wlhy bashi kaɗaiba. Akwai lokacin datai wani shegen shiga tabi waƙar mara mutuncin nan ranar jinai inama-inama, bara kaga video ɗin ALLAH yasa bata gogesa ba.”
Jiyay kamar jiri na ɗibarsa. Amma kun san halin ƴan mazan sai ya dake ya nufi samarin domin tabbatar da Fadwa ɗinsa ko wata. A hankali ya iso ta bayansu batare da sun fargaba. Wanda aka kira Mubeen na nuna musu video da yake faɗa. Ba ƙaramin tsinkewa zuciyarsa ta shigayi ba, dan ko'a magagin barci aka nuna masa video ɗin zai shaida wacece a cikinsa. Da baya-baya ya dinga tafiya har ALLAH ya bashi ikon jingina da motar dake kusa da shi, dai-dai nan Khaleel ya fito da babban abokinsa. Cikin salo irin na abokai yake ƙundumoma abokan nasa zagin mi sukeyi anan. Ganin basuma ko jisa ba ya karaso inda suke.
A firgice yace, “What!!?”.
Yana mai fisge wayar. Shi kansa zuciyarsa ce ta shiga tsitstsinkewa, idanunsa sun gaza cigaba da kallon videon dan koba komai matar Yayansa ce. Yayan nasa kuma mai tsananin kima da mutunci a idonsa....
“Kai lafiya kuwa?”.
Mubeen ya faɗa yana fisge wayarsa. Dariya sauran suka kwashe dashi. Anas yace, “Ka sani ko shima ya shiga tarko ne. To ka rufa mana asiri an jima zamu kaika ga taka wannan dai kwalelenk....”
Ai Khaleel baima san ya kaima Anas ɗin mari ba. Su duka suka zabura da waro idanu. Khaleel ya nunasa a zafafe. “Ka iya bakinka Anas, kasan ɗin ita wacece a wajena? To matar yayana ce, idan ƙazamin bakinka ya sake faɗar wata magana mara daɗi zan fasashi”.
Sun tsorata ƙwarai da gaske da rikicewar tasa. Mubeen ya dubi Khaleel ɗin a karo na farko cin son yin tunani. “Khaleel dan ALLAH kwantar da hankalinka. Wlhy sai yanzu dakai maganar matar yayanka wani abu ya ɗan dawo min a zuciya. Tabbas sanda ta ɗaura wani hoto nata tunanin a ina nasan mutumin, hakama da take daurasa matsayin mijinta na jima ina son hasasowa amma sai na kasa. Saboda sau ɗaya na taɓa ganin Yayan naka shima ba wani mun jima bane. Da gaske wannan shashashar yarinyar ce matar Yayanka? Kasan kuwa wacece Fadwa a tiktok? A ɓangaren shaiɗanun tiktok da a kullum ake ALLAH wadai da su da ganin sakacin duk wani na kusa da su wlhy Fady na sahun farko, dan ita a karan kanta mata uwar shaiɗanuce mai zaman kanta. Amma domin tabbatarwa maza ka shiga shafin nata ka duba zakafi yarda dani dai”.
Gaba ɗaya Khaleel yayi mutuwar tsaye, dan kuwa tun fara maganar Mubeen idanunsa suka hango masa Shareff dake tsaye alamar komai da suke yana jinsu. Shi a karan kansa Khaleel ɗin baya tiktok, bawai dan yana kallon tiktok ɗin baida amfani bane, a'a, a komai na rayuwa akwai mutanen banza a waje akwai na kirki. Shi bai taɓa ƙalubalantar tiktok ba ko yima jama'ar dake mu'amulantarsa kuɗin goro. Ya tabbata idan aka shiga tiktok za'aci karo da abubuwa masu amfani kamar yanda za'a samu na banza marasa amfani. Kawai dai shima bamai ra'ayin yawan biye-biyen shafuka bane kowanne iri. idan ma ya kama sai yabi abinda ya kaisa kawai yake zuwa yayi saboda aikinsa na cimasa kaso mafi yawa na lokacinsa. Da sauri yabar inda su Mubeen suke ya nufi Shareff daya shiga mota da alamar barin wajen zaiyi. Buɗewa yay ya shiga gefensa.
“Please yaya k.....”
Hannu ya ɗaga masa alamar kar yace komai. “Ka gafarceni Yaya, ka bani to na tuƙaka”. Bai sauraresa ba ya tada motar ya fice dasu da gudu. Duk magiyar da Khaleel ke masa bai nuna yaji ko daya ba har suka iso gidansa cikin ƙanƙanin lokaci.